Uwar y'an mata complete - Chapter 11
Uwar y'an mata complete Chapter 11: Uwar y'an mata complete Chapter 11. ********************** *BAYAN MAKO BIYU* Abubuwa da dama sun faru, ciki har ƙwance…
4,491 words
********************** *BAYAN MAKO BIYU* Abubuwa da dama sun faru, ciki har ƙwance ƙafar Hajiya Babba,saboda Allah ya kawo sauƙi da wuri kasancewar bata da mugun jiki. Sai dai a inda gizo ke saƙa gefen Zillaziya ne,don Allah ya jarabce ta da wata irin jarabta mai wuyar Al'amari,don laulayi ya sakota gaba komai bata so kuma ko ta ci,nan ta ke zata amayo shi,duk duniya idan da abincin da zai iya zaunawa a mazaunin tunbinta ba zai wuce girkin Hajiya Halima ba,sannan ba ƙamshin da tafi so irin na sashen ta.A hankali Zillaziya ta fara ba da kai buri na hawa,don ta kasance tururin tukunya ita bata tafasa sannan kuma bata kashe wutar ba,garin kar a ɓata goma biyar gyaru ba,shiyasa a cikin mako ɗaya,ta ƙwantar da kai gurin Hajiya Halima da biyu,Don ta cika cikinta sannan ta samu gurbin zama.
Hajiya Halima da zuciya ɗaya ta ƙarɓi Zillaziya,a zaton ta ko ta tuban da gaske,wannan yasa ta dage damtse tsakani da Allah,ba kissa ba munafunci ta dinga kyautata mata da ƙayatattun girke-girken duniyar ƙwaɗayi.Tana kula da ita sosai tare da tarairayar cikin don ko ɗaar bataji ba,farin ciki tayi tare da fatan Allah yasa asamu Magaji a gidan.
Hajiya Babba ganin kusancin Zillaziya da Halima yasa ta fusata,ta tattara ita da mai aikinta su ka bar gidan,don taga Zillaziya ta watsa mata ƙasa a ido,tana hulda da maƙiyarta kuma abokiyar gabarta,shi kam Alhaji Bello abin yay masa daɗi don hankalinsa ya ƙwanta,shiyasa su ka ci gaba da rainon abinda Amarya ke ɗauke da shi cike da so da ƙauna.
Kamar kullum yau ma tana sashen Anty Halima su na fira,anyi mata ɗan wake sai ci ta ke,yaran kuma wanda su ma yanzu tana yinsu su na yinta,su ma zaune su ke su na cin ɗan waken tare da Anty Amarya.Wayar da ke saman jikinta ta ɗauki ƙara,ganin Mommah ya bayyana a gilashin wayar ya sa ta ɗauka, Ta ce"Hello Mommah."
A ɗayan ɓangaren ta ce"Ke shashasha ki fito daga sashen ƙanwar uban ki Buzu,gani sashen ki sakarya."Daga nan ta kashe wayar,ta ƙasan ido ta duba tayi sa'a Uwar ƴan maata hankalinta na kan wayarta da ta ke dannawa,yaran kuma su na kallo,shiyasa tayi murmushi ta ce"Anty zan tafi nayi baƙuwa."Tana ƙoƙatin tashi tare da ɗaukar ɗan wakenta,To shi kenan Amarya sai kin shigo ki gaida baƙuwar inji Hajiya Halima,daga nan Zillaziya ta fice tana fargabar haɗuwarta da Mommah don ta lura ranta ya sosu.
Zaune ta sameta kan kujerar ta haɗe girar sama da ta ƙasa,gaisheta tayi amma ta ƙi amsawa, sai ma wani mugun kallo mai ɗauke da taƙaici da tayi ma ta. Ta ce "Anya Zillaziya ba hurhuraki akayi ba?Ashe duk abubuwan da Meri ta rattaba min akanki gaske ne?Lallai gurbi ya ɓata sha ke ma Uwar ƴan mata ta gama da ratuwarki ke yanzu in ke san ciwon kanki ko inda ta gitta kina wucewa,ai mugun mutum abin gudu ne ko don kariya ga cikinki,amma wai yanzu har abincinki da abin shan ki ya dawo hannunta hmnnn...Ba aikin kai sake ba ne,wannan Annoba ta addabi mutane ace macce sai ta gama da kowa,to bari kiji daga yau kar na ƙara gani ko jin labarin kina bin ta karki ƙara cin komai nata don ta nan ne ta ke samun ƙwance ƙullunan ta."Hannu tasa ta fizge farantin ɗan waken da Zillaziya ke fama ci,ɓata rai tayi" Doɗon Allah ki bani ɗan wake na Mommah,ni fa nan da ku ke gani na, na san abin da nakeyi,kuma na tabbata Uwar ƴan Maata ba zata taɓa cutar da ni ba,kawai dai kinsan idan mutum yana abu tunanin ya ke wani nayi masa."Ke dallah gafara har gobe ke ƙarama ce Zillaziya,ki daina min gaddama,ba zaki gane halin ƴan duniya ba inji Karima
Gyara zamanta tayi tana dubanta dariya tayi har da shewa sannan ta ce"Mommah wai ke manta wacece ni?Ki cire komai a ranki,duƙawa wada baya hana ka tashi da tsawonka, hakan idan buƙatar amfani da wani ta taso a cikin rayuwarka,kana sa shi a jiki domin ka ribaci buƙatar ka,idan ka kai gaci sai ka watsar da shi a ƙwandon shara,Hajiya Halima tamkar baturin fitila ta ce,zanyi amfani da ita domin ta haska idanuwa na,in samu ƙwanciyar hankali da zarar amfaninta ya ƙare zan cire in watsar."Duban ta Karima tayi da mamaki ta ce"Ƙwarai,sanin kanki ne laulayin nan bana iya cin abinci,sannan rashin cin abincin matsala ce wacce zata kawowa rayuwata,da abinda ke cikina barazana,sai gashi ita idan tayi girki ina so kuma ina iya ci,sannan ƙamshin sashenta na ƙwantar min da hankali,waɗannan dalilin yasa na ke ƙwanta mata da kuma adana da makaman yaƙin ƙare dangi tsakanin ni da ita a wuri na musamman.Kuma duk a zaton ku da gaske na saduda to me akayi?Ai yanzu ne nake ɗaukar karatun kawo ƙarshenta da labarinta,ko tsakiya ban kai ba,balle Babin ƙarshe kuma daina wani nazari akai na ina sane da duk abinda nakeyi wannan ma wani murɗaɗɗen makami ne."
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Idan har haka ne kinyi dabara don ba za'a taɓa yaƙi a gurin da babu mayaƙi ba,sai da lafiya ake komai idan babu ta fa zance ya ƙare,sannan yunwa babbar cuta ce ke kanki kin fito daga azabarta,amma duk da haka ina son ki kiyaye."Mommah na yarda da matar nan bata neman magani,amma ta kuma ni shaidace akan mamallakin komai da kowa shi ne majiɓancin Al'amurranta kuma ta saki kowa da komai ta kama wato"ALLAH"kinga ko dole sai mun tashi tsaye,Zillaziya kenan ai da ba'a gwaji jirgi ba zai tashi ba,sannan duk mai saƙa idan yay tufkar ƙwarai bazata warware ba,wannan karon zamu mata babban ƙullin da zata dawo ƴar kallo a gidan nan don mallam matashi ya yi min alƙawarin hakan.Dariya tayi ta ce"Kutukku mugun sure,ga yami ga ƙyaiƙayi Mommah kinyi baki da matsala.
Dariya tayi su ka tafa,ta ce "Ni a wasa ko aikina?Karimar Fagge ce fa ikon Allah nidai tashi yunwa nikaji ban tsaya Safara'u ta ƙarasa girki ba,na fito samo min abin da zan sawa cikina,ɓata rai tayi ta ce "Uhumnnn Mommah ni yaushe rabona da madafa?Kullum ina gurin ƴar wahalar can in ci in sha,sai dai in haɗa maki shayi amma ko ƙamshin madafa ta ban so,To haɗa min ai ba komai idan da soyayyin kaji sai ki haɗo da su,gaskiya yau kam baki taki sa'a ba don ba soye ai na daina cin kaza bana sonta ni kaina ina cikin alhenin hakan,don abin azo ai ɓin jaje ne rashim cin naman kaza babban cuta ne,tunda aƙwaita ba babuta ba amma ki bari idan kin tashi na haɗaki da ɗanyu da ke firijin." inji Zillaziya,washe baki Karima tayi tana falin to ai babu laifi duk abinda baki so sai ki gaggama min in tafi da su,daga ta haɗo mata lafiyayyen Shayi da Biredi,gyara zama tayo ta dinga sha kamar an aikota,sai da ƙoshi sannan ta fara shirin wucewa,abubuwan ci da sha Zillaziya ta haɗa mata sannan ta mata rakiya ta wuce.
*ISLAMIYYA* Malama Juwairiyya ce zaune akan kujera yayin da ɗalibanta matan aure ke fuskantarta daga ƙasa su na ɗaukar karatu,Ta ce kamar yadda nayi muku bayani,a baya ana Taimama na a inda babu ruwa ko kuma ga matadiyin da ke tafiya a sahara da dai sauran su ga dai bayani akan ita kanta Taimama sai kowa ya saura BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
*HUKUNCIN TAIMAMA*
Allah maɗaukakin Sarki yana cewa: "وإن كنتم جنبا أو على سفر ولم تجدوا ماءا فتيمموا صعيدا طيبا وامسحوا بوجوهكم وأيديكم" الآية. (المائدة: 6). "Wa'in kuntum junuban au ala safarin walam tajiduu maa'an fatayammamu sa'idan ɗayyiban wamsahuu biwujuuhikum wa'aydeekum…" (Al-Ma'ida:6) Ma'ana: Idan kun kasance a halin Janaba, ko kuna halin tafiya baku sami ruwa ba, to kuyi taimama da ƙasa mai tsark,i ku shafi fuskokinku da hannayenku". (Surar Ma'ida Aya:6).
Anan ina son ku fahimta ita dai "Taimama tana wajaba saboda rashin ruwa, a halin tafiya. Haka ma tana wajaba idan ya zama akwai ruwan amma ba za'a iya tabashi ba saboda rashin lafiya." Idan matafiyi ya tabbatar zai sami ruwa a gaba, to ya jinkirta Sallah zuwa ƙarshen lokaci,amma idan ya sakankance ba zai samu ruwa ba, to ya yi Taimamarsa tun a farkon lokacin sai yay Sallah, wanda kuma yake zaton zai samu, ko ba zai samu ba, to yayi Taimamar a tsakiyar lokaci. Wanda ya yi Taimama a cikin waɗanda za'a ambata; idan ya sami ruwa, to ga hukuncinsa kamar haka:
1- Mara lafiya wanda bai sami wanda zai ɗebo masa ruwa ba, har ya yi Taimama ya yi Sallah, idan ya sami ruwa lokaci bai fita ba, an so ya yi alwala ya sake Sallah.
2- Mai tsoron zakoki Idan yaje inda ruwan yake akwai namun daji ko 'yan fashi to daga baya sai wannan tsoron ya kau. Idan ya je ya ɗebi ruwan kuma lokaci bai fita ba, shima an so ya yi alwala ya yi Sallah.
3- Matafiyi, wanda yake zaton ba zai sami ruwa a farkon lokaci ba, sai a ƙarshe shima idan ya yi Taimamar kuma sai ya samu a tsakiyar lokaci anso ya sake. sannan ku lura Ba'a Sallar farilla biyu da Taimama guda ɗaya, sai dai kowace Sallar farilla ai mata taimamarta daban.Ina fatan kun gane? "In sha Allahu Malama, inji Ɗaliban. Ta ce"To Ma sha Allah,sai abu na gaba wanda ina ga daga gareshi zamu dasa Aya, sai kuma Ranar Litanin idan mai kowa ya kaimu, saboda Assabar da Lahadi ba ma shigowa ranakun ayyukan gida ne."Idan mun san Hukuncin Taimama sai;
*YADDA AKE YIN TAIMAMA*
Ita dai Taimama ana yinta ne da ƙasa mai tsarki, ko duwatsu, ko rairayi, da sauransu. Da farko idan mutum zai yi Taimama zai yi niyyar halatta sallah. Daga abinda kari yake hanawa, sannan sai ya bugi ƙasa da tafukansa biyu,idan wani abu daga turbaya ya maƙale masa,sai ya kakkaɓe, sannan sai ya shafi fuskarsa gaba ɗayanta tun daga sama har ƙasa. Sannan sai ya sake bugar ƙasa karo na biyu ya sanya ƴan yatsun hannunsa na hagu a bayan ƴan yatsun hannunsan a dama.Kamar haka"Malama Juwariyya ta nuna masu don an tan nemi ƙasar da zata nuna masu."Daga nan sai ya taho yana shafawa a hankali har yazo guiwar hannu,Ta ce "Kunga nan sannan sai a juyo da tafin hannun na hagun birbishin hannun na dama ana shafawa har yazo kan 'yan yatsu, sannan shima hannun hagu ai masa kamar yadda nayiwa na dama.ku lura Idan an fara shafar hannun hagu sannan na dama ya isar masa, matukar dai ya game ko'ina da shafar. Ina ga anan zance Bissalam.Godiya Ɗaliban sukayi mata sosai sannan akayi addu'a kowa ya nufi gida.
ƳAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*
_Home of Brilliant Writers forum_
_LABARI_
_TSARAWA_
_RUBUTAWA_
_HAƘƘIN MALLAKA_
_ƳAR MUTAN DIKKAWA_
BABI NA 44/45
Tabbas Addu'a babban makami ce,don gashi Allah ya yi iyawarsa,yau da gobe bata bar komai ba Ɗan gidan Hajiya Arziki da ke zaune a Abuja,ya shigo garin Kano da ƙyar ya gane kantamemen gidan na mahaifiyarsa don ya yi kusan shekaru uku ba tare da ya waiwayeta ba.Kasancewar an samu canje-canje da yawaitar gine-gine shi ya hana shi saurin gano gidan,a ƙofar gidan ya tsaya yana danna Horn,mai gadi ya leƙo don duba ko waye ganin fuskar da bai sani ba yasa ya rufe babbar ƙofar ya fito su ka gaisa,wani kallo ya yi ɓasa yace "Ka buɗe hanyar mana."Ranka ya daɗe ban sanka ban san daga ina ka ke ba,tayaya zan buɗe maka ƙofa dattijuwar nan amana ce a gurina ina kula da ita kamar uwata,don haka ka faɗi sunan in shiga ciki in faɗa mata,idan ta bani izini ka shigo sai na barka ka shiga,don ba zanyi saken da za'a cutar da ita ba."Mai gadin ya ƙarashe yana goge bakinsa da asawaki.
Ajiyar zuciya ya yi don ya ga da gaske mai gadin ba zai barshi ya wuce ba,ya ce "Kai yaushe ka fara aiki gidan nan?Don na san wani dattijo ne ke aiki anan shekarun baya da shi ne da ba zai tsaya ɓata min lokaci ba
Murmushi yay yace"Allah Sarki Baba tsohu ka ke magana ai yanzu shekaru uku da mutuwar sa,ni ya barwa gadon gadin gidan nan,Kakana kenan mutumen kirki yana jin daɗin aiki a ƙarƙashin Hajiya Arziki,don ya faɗa min tana kirki sosai.A cikin labarin da ya barma a matsayin tarihi bai faɗa maka tana da ƴaƴa ba?daga nan ya fito daga cikin mota ya cigaba da faɗin "Ni ɗan ta ne..."Ware ido mai gadi yay ya ce"Mallam ɗan damfara ka ke,mugu Hajiya bata da ƙwai bare dunge shekarata nawa a gidan nan ban taɓa ganin ko mai kama da kai ba,ka zo kace wai Hajiya ce mahaifiyarka,da bakinta ta taɓa faɗa min bata da ƴaƴa a duniya.Kuma na yadda da hakan don ban taɓa ganin wani ko wata sun zo sun ce ƴaƴanta ne don haka ka shiga motarka ka bar nan gidan,Wani zafi yaji yana taso masa a ƙasan zuciya to me hakan ke nufi? Ya tambaya a ranshi
Dubinsa yay tare da dogon nazari sannan ya ce"To naji mu shiga tare da kai,na san zata tabbatar maka da gaskiyar magana,shi kenan mu shiga,daga nan mai gadin ya tasa shi gaba sai cikin falon Hajiya..."
Umma da wata Gwaggon su Habibullah ce,su ka shigo gidan,sun sami Ammi don bata jima da dawowa daga makaranta ba,da murna fal a ranta ta tarbe su bayan sun gaisa ta tashi ta kawo masu ruwa da lemo domin su jiƙa maƙoshin su,Sai dai Ammi ta lura da yadda Gwaggo ke mata wani kallon banza ba yabo bare fallasa,sanin halinta yasa ta fara karanto addu'oin tsari daga kaidinta,don sam Gwaggo babu arziki a ranta sai tsiya. Umma ta ce"Juwariyya yau baki tafi makaranta ba?Ina ce araina kar mu zo bamu sameki ba.'A ladabce bata amsa da "Na tafi Umma dawowa kenan."Allah sarki,ai kina ƙoƙari Allah dai yay Albarka shi Habibu ya fita aiki ko?Eh ya fita amma na san ba zai jima zai dawo cin abinci inji Ammi Daman Gwaggon shi ta zo daga ƙauye tana son ganin sa kin san ba gari ta sani ba,shi ne nayi mata rakiya kar ta ɓace,ace ni ce...Umma ta ƙarasa maganar tana dariya,Uhumnnn ai ni kam ba zan ɓata ba,ɗana na cikin Kano ke wagga ina Ɗiya Maata har yanzu dai babu labarin wani rabo balle mu sa ran samun jikalle inji Gwaggo tana yatsina fuska da turo bakinta,Ƙasa da kanta tayi tana wasa da hannunta ta ce"Har yanzu dai Gwaggo...Umma kawar da zancen tayi ta hanyar faɗin"Ina ma mutanen nawa?Na ga yau Assabar ba makaranta,Umma sun tafi gurin kitso su ma na san ba da jimawa ba zasu dawo,ɗazu ma naji su na faɗin "Da yamma gidanki zasuje su ƙwana."To ai sai mu wuce tare idan sun dawo Umma ta ce tana murmushi tare da jan Gwaggo da fira,don ta lura sai cika ta ke tana batsewa,bari na ta duba girki...Juwairiyya ta ce a lokacin da ta tashi ta nufi madafa.
Tsaki Gwaggo tayi ta ce"Amma Zainabu kina da matsala!Meye abin so acikin wannan matar?macce ta haiho ƴaƴa buyar mata ba canjin jinsi amma a haka ki ke wani sonta?Bayan ta kalailaye Habibu sai abinda ta ce,ke fa kin koma ƴar abi yarima asha kiɗa,to wallahi nikam dai ba zata saɓu ba,ba zan zauna na zuba ido ana cutar ɗan, ɗan uwana ba,haka kawai macce sai kininbibi har da dasa wata malan ta,bari ya zo na san meye mafita...Haba Gwaggo ki sassauta muryarki Juwairiyya ba ta da matsala ko wata makusa batayi min ba,sannan bata yiwa Habibu ba,batayi ma dangina ko naku komai ba,to me zaisa na canja mata?Ko na ƙyamace ta idan aƙwai abinda yafi Macce Tagari to da hakan zan kirata nidai ina ƙaunarta,kuma mijinta na sonta,to banga dalilin da zai na tsaneta ba,akan wani abu dabam ke ba matan gareki ba har shidda?Ko ina da mata Zainabu ai Allah ya banu maza ƙarfafa har huɗu don haka Alhamdulillahi na gane mu ne baki son mu nuna mun isa ga Habibu to wallahi baki isa ba,ki aiko min kayana da a gidan ki,daman nan yafi kamata in samu masauki,duk a can gidan ki ma na isa da shi son ɗan yayana ya gina shi,amma tunda da sunanki ya gina ya zama naki,ke ga nan ko zan daki ƙirji in nuna na isa don gidan ɗana ne,zama daram dan dandam a gidan ba zan koma gidanki ba,bare ki min wulaƙanci...don marigayi baya da rai ɗanki ya yi kuɗi dole ki canja...Har Umma zatayi magana sai ga Juwairiyya ɗauke da ƙaton ture ta jero kayan abinci da kayan cin abincin ta dire a gaban su Umma,sannu da ƙoƙari mun ma ci abinci ban sani ba ko Gwaggo tana ƙarawa inji Umma fuskarta a sa ke,Gwaggo ta ce "Ke zubo min don ni ban ƙoshi ba"tana hararen inda Umma ta ke zaune.Juwairiyya ta zuba Gwaggo abincin da duk naman da ta ɗebo a miyar,madafa ta koma ta haɗo cake da cin-cin da soyen nama ta ce"Umma ga wannan,amsa tayi tana godiya ta fara ci,waigowa Gwaggo tayi ta ce"Zainabu karki haɗa da nawa ki cinye don zanci...Gwaggo aƙwai shi idan kin gama zan ɗebo maki,wannan ai na Umma ne inji Juwairiyya tana murmushi.
Ƙawar Zillaziya da su ka haɗu a yanar gizo ce,ta kawo mata ziyara domin ta duba lafiyar jikinta,Mabruka Sa'eed shi ne ainihin sunanta amma a group an fi saninta da ''Uwar Daba."Fira sukeyi sosai ita da Zillaziya,har su ka kawo kab firar Hajiya Babba da ya ke sun san komai,duk Zillaziya ta labarta musu,Uwar Daba ta ce"ki ƙwantar da hankalinki Zilly labarin Hajiya Babba zai gushe,don sai mun mayar da izzarta da masifarta tarihi,ita ma wannan kishiyarta ki nayi miki alƙawari banza ma zatafi ta amfani a gidan nan,kedai ki buɗe sabon babin ƙyanƙyashe ƙwayaƙwayinki a gidan nan daga yanzu zaki fara haife hanjinki har lokacin da zaki gama tara kaddaraki...Dariya Zillaziya tayi tare da tafawa da Uwar Daba ta ce"Kai ƙawata baki da sauƙi shiyasa na ke sonki,Allah dai ya kawo ɗan bazawarin da za'a gasawa Aya a hannu,murmushi tayi mai ɗauki da ma'anoni ta ce"To ameen,don gaskiya auren da zanyi yanzu bana fitowa ba ne,Zilly nayi aure shidda duk na neman duniya zallah,wanda zanyi nan gaba kaɗan na neman duniya da lahira ne,kuma duk wanda zan aura ko a duniyar bayi marasa gata to tabbas sai ya fishi samun ƴanci...Uwar Daba ta mu "ki ce dai aƙwai ƙura." inji Zillaziya,Uhumnnnn "Ba ƙarama ba kuwa,don ni bana wasa da abin wasa bare wanda ba na wasa ba, Uwar Daba ta ce tana kurɓa lemo lumshe idonta tayi tare da ƙarewa falon kallo sannan tayi ajiyar zuciya,domin tuni ta nutse tsundum a diniyar tunanin daular rayuwa.
Da sallama suka shiga falon,a gabanta ya faɗi yana ƙwasar gaisuwa ya ce"Hajiya anyi baƙo duk da dai ya ce"Shi ɗan gida ne."Tunda su ka shigo ta ɗaura idonta akan shi,ta watsar bata sake bari ƙwayar idonta ya haɗu da nashi ba,bare ta san ran zuciyarta zata karaya,dubin mai gadi tayi zatayi magana sai ya gurfana a gabanta yana cewa "Hajiya ina wuni."wani kallo tayiwa mai gadi ta ce"Wai meye haka?Ina ka samo wannan?Don nikam ban san shi ba,meyasa bakaji ?Ba na hanaka shigo min da mutane barkatai a gida ba?Dallah ku fice ku bani wuri...Hajiya cewa ya yi shi ɗan ki ne fa,ka taɓa ganin wani ɗana a gidan tsawo shekaru uku kana min aiki a gidan nan?Da sauri ya girgiza kan shi,ta ce"to kuma sai ka kawo min wani kace ɗana ne...Da sauri ya ƙarasa gabanta don ya lura tana cikin ɓacin rai,ƙafarta ya riƙe ya ce"Haba Hajiya idan idonki ya rufe don Allah ki buɗe su ki gani ɗanki Brr.Sama'ila ne agabanki na san nayi laifi Hajiya amma na tuba ki yafe min...Mari mai rai da lafiya ta watsa mishi tare da faɗin ka fice min daga gida?Idan kuma kana tunanin kun haɗa hannu gurin gina min shi sai na fita ni nasan inda zan tafi Hajiya Arziki ta ce a fusace tare da ɗaukar Hijab ɗinta da ke saman kujera,ganin hakan ya tsorata mai gadi kuma tɓya tabbatar masa da sanayya atsakanin su,shiyasa ya sulale ya fita daga falon yana mamaki kar dai da gaskiya Hajiya na sa ƴaƴa?Da zancen zucin ya isa kofar sa yana jiran abinda zai faru. Cikin ƙaraji ta ce"ka sake min ƙafa in wuce!"Hajiya ko da zaki kasheni ba zan sakeki ki fita akaina ba,ki dubi girman Allah kiyi haƙuri ki saurareni na yarda daga baya ki ɗauki duk matakin da zaki ɗauka a kaina,wani irin ƙuna zuciyarta keyi idont ya kaɗa yay jajur ba abinda ke ranta illa so da ƙaunar ɗanta,amma a hakan ta ce"Sama'ila tuni na manta da ku yadda ku kayi watsi dani akan duniya,ƴaƴan ku da matanku sun fini kana Abuja amma shekaru uku rabon da na ganka,ka koma abinka kawai rai baya gushewa sai lokaci ya yi,ko mutuwa nayi ba ku da asara don kun tara komai na jin daɗin duniya...Hajiya ai wanda baiji bari ba yaji hoho,amanarki da haƙƙinki nidai kam ya cinye min komai,na rasa dukiyata da ƴaƴana sanadin gobara na talauce matata ta gujeni har tayi sabon aure,duk abinda nayi ƙoƙarin nema sai ya lalace,gurin aiki an koreni akan na janyowa ma'aikata asarar wasu manyan takardu da su ka ƙone,bana jin daɗi da sukuni rayuwata duk da a yanzu na koma samun wani aiki,amma kullum mafarkinki na ke don Allah ki yafe min haƙiƙa bamu kyauta ba,wayewa da rayuwar bariki ta mantar da Hajiyar mu,ni dai na dawo gareki domib duk abinda na amu ko na nema a duniya idan babu albarka ki ba zai moru ba,ki yankebmin duk wani hukunci da ya dace dani a shirye na ke da amsawa zan miki biyayya,daman aƙidar yahudu da nasara da muka sawa rayuwar mu ne,yanzu na gane ina sauraren wa'azi da dama na mallamai na ƙara sanin wacece uwa da muhimmancin ta...."Kukan da yake ya ci ƙarfinsa ya dinga rusawa har gunji tare da ƙara ƙanƙame ƙafar Hajiya Arziki sai magiya yake yana roƙonta da ta yafe masa.
Tafasa zuciyarta ke yi yayinda ƙirjinta ke kukan ɗauki ba daɗi,bata ankare ba sai jinta tayi jagab saman kujera tana rusa kuka!Da sauri ya tashi zuwa gareta ya ce"Mun shiga uku mun lalace Hajiya ki daina yi mana kuka,Innalillahi dole duk in kira su Yaya Idris,Musa,Isah da Kabir,don zamu zo duniya a banza mu koma a wofi!"Hajiya don Allah ki daina mana kuka."dole nayi kuka Sama'ila ina ji araina da ina da ƴa macce aduniya da ban shiga wannan hali na maraicin ƴaƴa ba?Da kuma banyi kaɗaici ba,da yanzu nima ƴaƴanta zasu kirani da Kakar su,aini na daɗe da far muku kuka saboda kun zaɓi mata a kaina,na haifawa iyayen su,ina d ƴaƴa maza biyar a duniya amma wacce bata taɓa haihuwa ba,tafi ji jin daɗi!Ni nasan duniya makaranta ce yanzu da ta fara zayyane maka babban darasi ka zo gareni....Hajiya kice ke yafe mana shu ne ƙwanciyar hankalina Sama'ila ya ce muryarsa na rawa. Tashi tayi daga inda su ke zaune tare d cire hannunta cikin na shi,tayi shigewarta ɗaki tana goge ƙwallah,Sama'ila ko haɗe kai da gwuiwa yay yana darzar kukan da yafi maɗaci ɗaci sannan yafi wuta iya ƙonar zuciya.Duk yayyen sa da ke ƙasashen waje zaune da iyalansu ya turawa saƙo mai taɓa zuciya,sannan ya yi zaman jiran Hajiya ta fito sai dai ko alaɓun fitowanta babu,ganin hakan ya sha ya nufi ƙofarta amma ta rufe,yay juyin duniya ta buɗe tayi masa banza,shiyasa yay gurfane a wurin yana rusa kuka,ita ma acikin ɗakin kuka take don abubuwa da dama sun dawo mata sabo,kamar lokacin da ƙaddarar rayuwarta na sabuwa.
Shigowar su gidan ya ɗaukuɓi hayaniya don sun ga Umma,ita ma da murna ta tarbesu,ganin Gwaggo zaune ta haye kamar fulawa,yasa su ka rage rawar kai,su ka gaisheta,daga nan gurin Ummi su ka zauna kowa na nuna mata kitso har cewa"ta zaɓa na wayafi kyau?''Dariya tayi ta ce"Ai duk na kowa ma baiyi kyau ba"nan fa su ka dinga janta bayan sunci abinci kimtsawa su ka farayi don Umma ta ce"ta tashi su kuma daman gidan ta zasu ƙwana,kayan su ka ɗauka direban gidan ya kai su,yayin da Gwaggo ta gyara zama kayanta Umma taba direba ya dawo mata dasu,ba jimawa suna zaune falon ita Ammi da ke kallon wa'azi,sai ga Abbu ya dawo ganin Gwaggo ya ƙara faɗaɗa murnarsa sun gaisa sosai sannan ya nufi ɗakin sa,da taimakon Ammi ya kammala shirinsa ya ci abinci sannan ya dawo falon su ka ci gaba da firar bayan rabuwa da Gwaggo.Gyara zama tayi ta fara zayyano masa matsalolin su,da irin halin da su ke ciki wanda mafi yawa na ƴaƴanta da jikoki ne,Abbu ya ce"Gwaggo babu matsala in shaa Allah zan san abinda za'ayi."Duk da a zuciyarsa mamakinta yake,ita kullum cikin roƙo n abata take,duk da yana iya bakin ƙoƙarinsa gurin taimakon duka dangin Baban sa da ke ƙauye da abinci,sutura,kuɗi,da abubuwan sana'oi amma a hakan ko da yaushe cikin kukan babu Gwaggo ta ke duk mafi akasarin abubuwan a hannunta yake damƙasu ta damƙawa sauran dangi...maganar ta ce ta dwo da shi daga dogon tunanin da ya ke ta ce"Daman ba wata magana bace illa akan ina son ka ƙara aure,ka auri ƴar auta ta Jummala...Duk da baiji farkon maganarta ba,sai ƙarshen amma da sauri ya ce"Gwaggo aure fa?kuma in rasa wacce zan aure sai Jummala?"Murmushi yay ya ce"Kiyi haƙuri Gwaggo ni sam ba tsarin ƙarin aure a rayuwata idan ba wata ƙaddara ta gitta ba,Habibu ƙaddarar haihuwar ƴaƴa mata ce ta gitto shiyasa nace ka auri jummala kaga ƙafarta duk ta ƴaƴa maza ne,aurenta uku duk inda ta fito tabar ƴan maza uku namijin tara,to kagada zarar ka aureta ta haifo ma Namiji,wani abu na tsikareshi ya tashi tare da duba agogonsa ya ce"Zan wuce makaranta Gwaggo na kusa makara ina son ki dangane zancen auren nan don babu muhallinsa bana tunanin a samu ko nan gaba sai na dawo.Yana fita ta dinga zaginsa tana faɗin zata ɗauki mataki,har Ammi ta dawo falon ta zauna,don tana ganin ya zauna inda Gwaggo ta tashi ta basu wuri,a hankaɗe ta dubeta ta ce"Ke wacce makaranta Habibu ke zuwa,Ammi da sanyin muryarta ta ce"Islamiyya Gwaggo."Da girman shi?ta tambaya tana riƙe baki,murmushi tayi ta ce"Eh, su na zuwa da yamma sai bayan magrif su tashi kin san ba'a tsufa da neman sani kuma shi sani baya da kaɗan sannan baya kuma waya,tsuke baki Gwaggo tayi tare da girgiza kai ta ce"Ku kusani sannan ina miki albishir da Habibu aure zanyi din kisani kuma amarya shi autaletale Jummala ta sha tabara ta sha yasin sannan anyi mata tofin ƙyaiƙayi koma kan masheƙiya,ta ƙasan ido Ammi ta dubeta kana ta ƙara gyara zama ta ce"Gwaggo da gaske?Amma ko naji daɗi zan samu abokiyar zama tana murmushi,Harararta tayi ta ce"To da wasa ni sa'anki ce da zanyi wasa da ke?Babu tantama jinin shi zata shigo gidan nan kuma ta haifo masa ƴaƴa maza ba adadi inji Gwaggo sannan ta kishingiɗa saman kujera tana cigaba da maganganunta.Uffan Ammi bata ƙara ƙoƙarin furtawa ba a fili sai dai a zuciyarta ita kaɗai tasan me take ayyanawa.