Uwar y'an mata complete - Chapter 12
Uwar y'an mata complete Chapter 12: Uwar y'an mata complete Chapter 12. TOUFA ZARAN YA ƘWANCE A LOKACIN DA NAKE ƘOƘARIN ƘULLAWA ME KU KA HANGO?ME KUMA ZAI…
4,385 words
TOUFA ZARAN YA ƘWANCE A LOKACIN DA NAKE ƘOƘARIN ƘULLAWA ME KU KA HANGO?ME KUMA ZAI FARU?KAR KU MANTA DUK SANADIN ƳAƳA MAATA NE....KU DUMULMULE ACIKIN DUNIYAR RUƊU DA RIKITA RIKITAR RAYUWAR DUNIYA DOMIN KAMO MANA BAKIN ZARAN...
Taku har kullum idan ba comments ba post
ƳAT MUTAN DIKKAWA😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*
_Home of Brilliant Writers forum_
_LABARI_
_TSARAWA_
_RUBUTAWA_
_HAƘƘIN MALLAKA_
_ƳAR MUTAN DIKKAWA_
BABI NA 46/47
A ƙwana a tashi babu wuya akace"Inda rayuwa"cikin Zillaziya ya tsufa sosai,har watan haihuwar sa ya kawo, yana batun shuɗewa.Duk wani shirye-shirye da ya kamata ayi domin suna,Hajiya Babba ta gama shiryawa haihuwa kawai ake jira,Alhaji Bello yay bajinta sosai,don ya ware maƙudan kuɗi ya ba Hajiya aka sayi komai,hakan gefen Hajiya Halima duk ya bata kuɗin ɗinki ita da yaran,don mafi yawan kaya a shagunan sa ya zaɓo masu na kece raina.Tsakanin Hajiya Halima da Zillaziya sai san barka don sun ƙara samun fahimtar juna,ga wani zaman lafiya da ke wanzuwa atsakanin su har asibiti Hajiya Halima ke kai Zillaziya gurin awo su dawo tare,ɗawainiya sosai ta ke mata duk wani kulawa da tarairaya ita ce,don rabon Zillaziya da dafa ko ruwan shayi a gidan har ta manta duk abin da ta ke son ci,ko sha Hajiya Halima ce,da yake su Zeenat duk sun jona makarantar gaba da sakandare kowa kuma ya zaɓi ƙwas ɗin da ya ke da burin karantawa.Su Mamu iyayen iya yi,da tsiwa ne ƴan maatan gidan,kowa dai yaci buri akan haihuwar Anty Amarya.
************Fitowa tayi sanye da ƙaton Hijab shuɗi har ƙasa da niƙabi,kafafunta sanye da safar ƙafa su ma shuɗi,ɗakin da Gwaggo take ta shiga da sallama,sai dai kawar da kanta tayi gefe ba tare da ta amsa ba,da sanyin murya ta ce"Gwaggo ni zan wuce makaranta,abin ci na nan falo na ajiye miki sai na dawo..."Ke Uwar Biyar ni ba mai gadin ku bace,na gaji ke kullum sai ke fita makaranta,Habibu ya fita makaranta,ita Rabila(Nabila ta ke nufi)da Shatu(Aysha)duk suna can kun kai uwa duniya karatu sauran kuma in sun fita tun safe sai yamma zasu dawo ?Wai karatu su ke,karatu kodai lalata?Nikam na gaji da zaman kaɗaici haka kawai kun ɗauki rayuwat yahudawa kun sawa rayuwar ku to bari Habibun ya dawo na san yadda zanyi."Gwaggo ta ƙarashe zancen tana huci
Juwairiyya ta dubeta tana nazari,don tabbas aƙwai kaɗaici musamman ga mutuɓen ƙauye wanda ya saba da hayaniyar 'ya'ya da jikoki ko da yaushe,tunda ba karatu suke ba,ajiyar zuciya tayi ta ce"Gwaggo kiyi haƙuri yadda ki ke tunani ba haka bane,yaran su na karatu haka tsarin su yake,amma ki fito falo ga wa'azi can na kunna miki(Sunna t.v) Don Allah kiyi tafiyarki kawai indai tafiya zaki ki barni,in zauna kallon wa'azi ko in saurari makomata,malamai ne birjit a talabijin ɗin nan babu lokacin da za'a daina nuno su,wasu gani zaune zasu kaɗa ni wutar jahannama ke shekaranjiya wani malami sunana Mariya kaɗai a bai jayo ba,amma wallahi nasan dani yake sdon haka ban koma kallon wa'azi in kina Ado gwanja kisa min ko takawa ina yi,don na ƙwan biyu ban danshe ba daman a abin waƙar jummala ne muke sauraren shi shegen ƙwai ya iya waƙa haddai Ayyyyeeeh mata a ƙame ƙaam inji Gwaggo tana dariya. Cike da mamaki ta ce"Juwairiyya ta ce"To Gwaggo nidai ban san tasoshin mawaƙa ba,amma muje in kamo miki Arewa24,washe baki Gwaggo tayi ta ce"A ai ko ita ina so kinga mai lomis lomis ji zafafan nan ya iya magana."Ita dai Ammi ta ƙosa ta bar gidan,tana kamowa Gwaggo tashar,ta fice daga gidan tana mata fatan shiriya don duk dattijiwa kamar ta aka samu da rayuwar son duniya da waƙoƙi abin a tausaya mata ne.
Safara'u da Tasi'u ne su ka shirya acijin shiga nai kyau,don yayar su ta riƙe ma gidan Buzu kan maciji yanzu su na damawa tun kan abin ci,abin sha da sutura masu kyau,tsaf su ka fito su na zuba ƙamshi.Safara'u ta ce"Mommah ga mu zamu tafi,daga madafa ta fito ɗauke da katuwar kular da suke zuba abincin rana,Ta ce "To bari na baku saƙo ku kai mata,Firijin ɗin da Zillaziya ta saya musu ta buɗe tare da ɗauko gora cikin leda,Sarafa'u ta amsa suka wuce."Mai adaidaita su ka samu su ka shiga bai ajiye su ko'ina ba,sai ƙofar gidan bayan sun sallame shi shiga sukayi gidan,sashen Hajiya Halima su ka fara shiga don anan ne ake ganin Zillaziya,da fara'ah Hajiya ta tarbesu cike da girmamawa Safara'u da Tasi su ka gaidata,jim su ka zauna ganin Yayar bata nan yasa su ka wuce,Kuɗi Hajiya Halima ta ɗauko ta basu har da turare,godiya su kayi mata sannan sun ka shiga sashen Yayar su. Basu sameta falo ba,shiyasa Safara'u ta ce"Tasi ya zauna ita ta shiga uwar ɗaki ta dubota,ƙwance ta sameta saman makeken gadonta tana chat, dariya take kamar zautatta,sallamar ƙanwarta ce ta dawo da ita hankalinta,bayan sun gaisa ta ce"su Safah dai yau a gidan nawa?Lallai duniya tafi bagaruwa iya jima...daman ance idan masara taji wuta ita ga kuka,komai batace da ita illah saƙonta da ta ajiye mata a gefen gado,ta ce"Inji Mommah."ɗauka tayi ta buɗe rubutu ne na sauƙin naƙuda da Mommah ke amso mata wurin Mallam Matashi,ya mutsa fuska tayi ta ce"Wai ita Mommah bata gajiya da amshe-amshen nan nifa wallahi har na gaji da jiƙa wannan sha wannan mtssssw gashi ciki wata goma sha ɗaya ba amo ba labari kuma asibiti kamar an dabalbalasu sun ƙasa gane komai,ƙara ɓata fuska tayi kinganni Safah har na gaji da shan abubuwan nan ko yanzu da wasu a firijin,gani duk na ƙabe,tafiya ma wahala ta ke min,bare yau da nauyin jiki na tashi."Hamma tayi ta ce"muje falo."Safah ta ce"Allah ya saukeki lafiya"Ameen Zillaziya ta amsa har sun fara tafiya ta juyo tare da riƙe ƙugunta ta ce"Wasssh!sannan ta riƙa hannun Safah ta ce"Ke san ku mallamai magadan annabawa ne Safah injin dai kina min addu'ah Allah ya bani Namiji."Yaya Zillaziya kenan,ina miki addu'a Allah ya saukeki lafiya ya baki mai albarka nidai kullum ita ce addu'a ta,amma kinga Momma babu dare ba rana ina jin tana addu'a tana faɗin "Allah ka bata Namiji,Namiji,Namiji ya Allah."Na gyarawa Mommah ta dinga faɗin kowanne mai Albarka amma bata bari ko ranar naji Papa yana mata nasiha akan hakan,ba'a nunawa ubangiji ga abinda ake so domin ilimin sanin gaibu na gareshi..."Kedai Safah kin shiga uku wallahi" Inji Zillaziya tare da sake hannunta ta fice falon don bata jin daɗin maganar ba.Ganin Tasi zaune yana kallo yasa ta saki fuskarta tana faɗin"Ashe da kai aka zo Autan Mommah?Dariya yay ya ce"Tare mu ke da ita ba kun barni nan ba,kuna can kuna fira.To kai haƙuri Tasina je ka ɗauko muku lemo da ruwa,firijin ya nufa ya ɗauko lemuka da ruwa ya yi zaune ya dinga sha,ta gefen idon ta ce"Safah kije ku ɗaura idomie kafin Anty Halima ta ƙare girki,daga nan ta ci gaba da chat ɗinta da abokiyar cin moshe wato"Uwar Daba"wacce ke ta ɗaurata akan matakalan ɓarar da Uwar ƴan maata da Hajiya Babba.
"Ya kamata ku gane wani abu ɗaya...Ita ƙwalliyar macce abu ne mai kyau,ana son macce ta dinga tsafa,tare da kula da jikinta, amma kamar yadda Mama Lamir ta tambaya baya hallata,saboda mata da yawa na wannan kuskuren na sa turaruka ajikin su a lokacin da zasu fita unguwa,abin haushi mafi yawa masu aikata hakan mu ne wato "matan aure."Inji Ammi tana sauke numfashi,Maman Sharif ta ce"Malama yana halatta asa turare idan muna cikin gida kamar gidan miji,ko gidan iyaye hakan?"Babu komi kina iya sa turare cikin gida,kamar ke matar aure kiyi ƙwalliyarki son ranki amma fa sai an kula,saboda aƙwai gidajen da maza ke shiga ba kan ta,don mutane da dama da ke shigowa gidajen,wasu a addinance baya halatta su ga ƙwalliyar matan aure amma suna gani,kamar Abokan miji da sauran waɗanda ba muharraman macce ba."Maman Sayyid da ke gaba zaune ta ce"Malama kamar su waye ya kamata su ga ƙwalliyar mu?"Ammi tayi murmushi sannan ta ce"Ita ƙwalliyar macce iya muharramanta kaɗai aka aminta su gani domin macce al'aura ce daga fuska,hannaye,ƙafafuwa kaɗai ne ba al'aura ba,yana halallata mijinta ya ga ƙwalliyarta ko Babanta,Surukinta,'Ya'yanta,'Yayan mijinta,'Yan uwanta mata,ko Ƙananun Yara da basu san meye al'aura ba da dai sauran su.Don haka mu kula haka mu kula da 'Ya'yan mu 'yan maata idan zasu fita su daina saka turare iya turare hammata ya isa wanda ba zai tashi ba,marar ƙarfi wanda ko an wuce wani ba zai jiyo ƙamshin sa ba."
Buɗe wani littafi Ammi tayi ta ce"Sai abu na gaba wato shugabancin macce,ita macce tana shugabanci a wurare uku"Tana kula da gida,sannan tana kula da mai gida,kuma tana kula yaran gida,duk waɗannan a ƙarƙashi macce su ke haka nauyi da ɗawainiyar na ta ne."Shiyasa mafi yawan lokaci idan ina magana ina faɗa muku idan yaran mu zasuyi karatu to fa mu tura su "karatun aikin koyarwa ko na asibiti,don kowanne macce tayi acikin zata ƙara sanin meye gida,sannan kuma zata taimaki yaranta,da al'umma,ku lura da kyau idan macce tana aikin asibiti tana baiwa gidan muhimmanci don har matsuwa ta ke bata gama dutynta ba,ta koma gida,haka idan malama ce zaku ga idan tana gida to littafan yaranta na hannunta tana duba musu karatu da ayyukan da ake basu....Hayaniya ta ƙaure a ajin suna faɗin"Wallahi haka ne ko malama wance hakan ta ke ma yaranta har allo a gida,ai nasan Nurse ɗin nan maƙociyata tana ba gida da yaranta muhimmanci duk da tana aikin asibiti."Da haka dai Ammi ta katse zantukan su suka rufe taro da addu'a.
Yuni su Safara'u su kai mata sai Yamma suka wuce, bayan tayi musu sha tara na arziki,bayan sun wuce ba da jimawa ba wani azababben ciwo ya taso mata,in banda kalmar wayyo!ba abinda ke fitowa daga bakinta daga uwar ɗakinta da rarrafe ta kawo falo tana sharara kuka,inda ta ajiye wayar ta take nema amma ciwon ya hanata tunanowa. A gefen Hajiya Halima ko duk yunin yau bata ga Zillaziya ba sai ta ajiye akan ƙannanta sun zo ne shiyasa bata leƙo ba,don ko abinci da ta gama a waya ta kirata sai ta tura Safara'u ta amso masu.Har wajajen magariba duk yaran sun dawo daga makaranta basu ga Anty Amarya,wasan su sukeyi Mamu aikin gida da aka bata a makaranta ta zauna tanayi,can ta dubi Mommynsu ta ce"Momy wai ina Anty?Ba tare da Hajiya Halima ta dubeta ba,don aƙwai shirin da take kallo,ta ce"Idan kin gama kije kice mata ina gaidata,ta zo an fara "TARA"
Momy ƙila a falonta zata kalla yau inji Mamu tana wani faar da ido tana juya baki,Tsaki tayi ta ce"A can kin ka ga ta saba kallon,ko tashar aƙwai a ɗakinta,kar dai a mutu ba'a shura ba?To kin ida hali wuce inda na aike ki."Dariya tayi ta wuce daga falon na Mommyn su tana karkaɗa kugu,Da kallo Hajiya Halima tabi Mamu don al'amurran yarinyar kamar mai ifiritai gata nan bata da kunya ko kaɗan,ga ta tsiwa ko Daddynsu tsoron lamarinta yake.Fatan shiriyan da take mata babu dare babu safiya tayi mata sannan ta ci gaba da kallonta.
Fitar Mamu ba da jimawa ba,ta dawo da gudu tana haki don ganin halin da Anty Zillaziya ta ke ciki,tana haki ta faɗawa Mommy"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!"Hajiya Halima ta ce da sauri ta ɗauki mayafi,waya da mukulan motar ta,yashe ta sameta tsakiyar falon ta juye baki gefe tana darjar kuka,sai Wayyo!take ambata,Rungumota tayi ta ce"Subhanallah ina ga haihuwa ce Zillaziya ki dinga Ambato Allah,tashi muje Asibiti,da taimakonta Zillaziya ta ɗaura zanenta,taimaka mata tayi su ka fito daga cikin gidan,yaran sai sannu suke ma Zillaziya amma ko ganinau batayi,bayan mota Hajiya Halima ta shinfiɗe ta,sannan ta ce"Yaran su koma ciki yanzu suna dawowa,ta da motar tayi mai gadi ya wangale get yana faɗin"Allah ya kiyaye Hajjaju,Halima mai Hali dubu kyawawa kuma uwar kyawawa,Murmushi tayi ta fice da gudu daga gidan,Mai gadin cigaba da cewa ya yi"Allah yasa ki haifi mata dozin Hajiya Zillaziya ,yau ba sai gobe ba, in ga ƙaryar ku, ke da Hajiya Babba me kiran ki da uwar magaji,ni nasan sai dai uwar magajiya, don ba'a yiwa Allah shishshigi a al'amurran sa."Dariya yay yana kunna rediyo ya ce"Sai buɗar baki take kamar an buɗe ƙofa,daman mai rashin kunya yafi kowa raki,kamar kanta aka fara haihuwa."
Bayan sun isa asibiti da taimakon ma'aikata aka wuce da Zillaziya ɗakin haihuwa,kaf wurin kowa yaji hargowarta wasu sai dariya suke wasu kuma takaici ta basu,Hajiya Halima sai addu'a take Alkah yasa ta sauka lafiya,daga nan wayar mai gidan ta kira sau huɗu ba'a ɗauka ba,ga magriba ta kawo jiki,Wayar Hajiya Babbba ta kira da ɗayan layinta da bata da ahi,don idan zata yiwa Hajiya kira miliyan da lambarta ba zata ɗauka ba,jim kaɗan ta ɗauka da isar nan ta ta,ko gaiaheta Hajiya Halima bata tsaya ba,ta faɗa mata Zillaziya ba lafiya su na Asibiitin Mallam Aminu Kano,da sauri Hajiya ta katse kiran ta fara shiri,kiran Alh.Bello ne ya shigo ɗauka tayi suka gaisa ya ce"Uwargida ran gida,wayana cikin shago ina waje ina alwala...Faɗa masa halin da ake ciki tayi da sauri ya ce"Gashi nan zuwa."Hajiya ko ta gidan su Zillaziya ta fara biyawa sai dai Karima na wurin tawon layi,kusam Safara'u da ƙawayenta huɗu da suka taso islamiyya,sai da suka rarrabu aka samo ganota wani gida,Hajiya tsaki tayi ta ce"Ke kam yaushe zaki godewa Allah ?kibar yawon gidajen mutane wasu a haife kin haifesu amma ki zauna kina banzatar da kanki akan mugun ƙwaɗayinki da tsabar gulma da ke cin ƴan hanjinki....mtswww ki shiga mota ɗiyarki na can na naƙuda kuma munafukar can ce ta kirani kar a haife namiji abata ta kashe shi,don baƙin ciki ba abinda baya sa wa."Gaban Karima ya faɗi ta ce"To Allah ya gyara bari in ɗauko zanna da roba ko?kayan zuwa wurin haihuwa...Dan Allah Karima ki shiga mota bana son shirmen banza,na tanadi komai sannan a Asibitib zaki ƙwashi kaya kamar mahaukaci?iIni Hajiya Babba a ɗan hasale.
"Allah ya baki haƙuri ya huci zuciyarki,Karima ta ce"tare da shiga gaban motar fefen direba kamar yadda Hajiya ta umurceta,ita kuma tana baya ta kame sai kiranbƴan uwanta takeyi a waya tana faɗa musu adai tayasu da addu'a."Karima ma ƙannanta ta kira ta faɗa musu tana ajiye wayar Hajiya Babba ta ce"Ke bata kiyi addu'a ta haifi ɗa namiji ki ke ba ?Ta shelawa ƴan uwanki su sameki asibiti kamar gidan ku?Nifa yau a shirye nake don gurin hawa gurin sauka wallahi in ɗiyarki bata haifi Namiji ba,zan sa ɗan Inna ya saketa ya auro wata har sanda za'a dace don na lura daku cin duniya da tsinke ya kawo ku,daga taimako amma yarinyar nan ta fara watsa min ƙasa a ido,shiyasa naji duk ta fita raina,ga sata kamar ɓeran masallaci komai ta wawashe ta aika miki ko kinzo kin ɗauka,kuna neman tsiyata mu duk abinda kukeyi akan idona...Haba Meri yanzu dai ba lokacin wagga magata ba don Allah mu barta inji Karima wacce duk abubuwan da Hajiyar tayi mata tun ɗazu sun tsaya mata a wuya gashi agaban direba tana ta wulaƙanta ta.Ke kika sani inji Hajita Babba daidai nan suka shiga asibitin,daga nesa Hajiya Babba da Karima su ka hango dangin su cike da harabar asibiti don tun ɗazu ma'aikatan suka fidda su waje kamar gidan biki haka suke faɗi banza faɗi wofi,tsaki Hajiya tayi don ƴan uwanta sunfi a ƙirga awurin,Karima inda ƙannanta ta nufa su ka gaisa nan suka faɗa mata Hajiya Halima da Alhaji Bello kaɗai aka bari a ciki,su kuma ance su tsaya a harabar asibiti.ƙwallan da ya maƙale mata ya zubo mata,haƙuri suka bata don duk zaton su matsalar Zillaziya ne amma ita sam Hajiya Babba ce ta babbake mata rayuwa don tana neman ruguza masu buri.
Hankalin su a tashe yake,don sun lura da yadda ma'aikatan ke kaiwa da komowa,ga ƙarar ƙuwwa Zillaziya ta karaɗe gurin,Har anyi magariba da Isha har ƙarfe tara daren yayi ba labarin komai,Addu'oin da Hajiya Halima tayiwa Zillaziya ta miƙawa nurse don a bata,Alhaji Bello tambayarta ya yi amma nurse lin batace da shi komai ba,ta wuce da sauri don yanzu har motsin Zillaziya an daina ji,Hajiya Babba aikowa tayi kiran Bello,yana zuwa ta ce"Halima ta fito daga ciki ita ta shiga don tayi juyun duniya masu tsaron hanyar su barta sunce"Da macce ɗaya gurin mai haihuwar."Duk da baiji daɗi ba,amma a haka ya ce"Hajiya Halima ta fita sai Hajiya ta shigo,cewa tayi zata wuce gida saboda yara,ya ce"A'ah"Halima idan kika wuce zasuce kishi ki ke,kinsan halinsu ki zauna mu gani har Allah ya ida nufinsa."Cike da gamsuwa ta aminta da maganarsa ta fito Hajiya har mangajeta tayi gefe ta ce"Munafuka...sannan ta wuce."Tunda ta doshi wajen asibiti kasancewar aƙwai haske ta ga kaf mutanen ita suke kallo,har da nunata,nesa dasu taje ta samu wuri ta zauna,tana jin suna zagin ta tare da jifanta da mugun alkabae amma sharesu tayi,Azkhar ɗin yamma ta buɗe a wayarta tana karantawa don salloli ta samu yi,batayi Azkhar ba."Bayan ɗan lokaci Karima ta zo ta sameta suka gaisa tana tambayar jikin Zillaziya?Hajiya Halima ta ce"Da sauƙi,godiya tayi mata sannan ta koma inda ƴan uwanta,nan ƙannan Hajiya Babba, mata suka dinga mamaki wai har da Karima an asirance tana bin Uwar 'yan mata ga Zillaziya ance ta koma kamar jela,surutan su suka ci gaba dayi tare da gulmarmaki har na Hajiya Babba da Bello.
Har ƙarfe goma babu labarin haihuwar Zillaziya,Hajiya Babba ta ce"Anya ɗan Inna babu saka hannun uwar ƴan mata a lamarin nan?Ka duba cikin nan yau kusan watan shi goma sha ɗaya da rabi,ba'a haifeshi kardai mugunyar matar nan tasa an danne shi ya koma ƙwance ni gaskiya ita nake zargi...Don Allah Hajiya ki daina maganar nan,dole kace in bari tunda an taɓo rayuwarka,idan kai zuba ido zakayi ni ba zan yadda a asara ni ba,dole taje a ƙwance kowanne ƙulli ne,tayi wanda ya hana haihuwar nan...Nurse ce ta zo da sauri ta ce"Wacece Mommah?tsaki Hajiya tayi tare da karkaɗa kai,Alh.Bello ya ce"Tana waje,Nurse ta ce"Ka kirata da sauri."Ba jimawa ya dawo shi da Karima wani kallon banza Hajiya tayi mata ta ce"Kema wurin yawonku ƙila ke bata wani mugun abu da ya hana ta haihu,kiyi ƙoƙari ki kira shi malamin ya warware in ba haka ba,ƴarki ta mutu kece da asara don ko wata ba'ayi zan sa ɗana yay sabuwar amarya...Haba Hajiya,kai rufe min baki mugun yasan maɓoyar mugu kaji da zuwa neman kuɗinka ni kuma zanji da baka kariya da masu asiri da jifa magauta na gida da kasuwa inji Hajiya,Nurse ta zo ta shiga da Karima ba jimawa ta fito tana ƙwallah!don gafara Zillaziya ta roƙeta ta ce"kuma aroƙa mata uwar ƴan mata ta yafe mata da Alhaji da dai sauran mutane,don tana cikin wani hali,Alhaji Bello haƙuri ya dinga ba Karima da ta durƙushe ƙasa tana kuka!
Bayan lokaci Likita ya buɗe ƙofa ya fito duk yay zufa,ya ce"Alhamdulillah ta sauka daga Hajiya Babva har Karima suna rige-rigen ƙarasowa inda Likitan ke tsaye shi da Alhaji Bello,a tare sukace Me aka samu ɗa ko macce?"
Goge zufa yay tare da mayarda gilashin idon sa,ya ce"Sai dai aƙwai matsala!Da Hajiya da Karima tare zuciyarsu ta buga kowa da abinda yake tunani"Hajiya gani take macce ce,duk burin da ta ɗaura akan ɗa namiji...Wani jiri da duhu ya mamaye idonta nan take ta faɗi,Karima ta shiga firgici aranta ta ce"Shi kenan sun shiga tara,asirinsu zai tonu don ƙaryarsu ta ƙare,burinsu ya faɗi ƙasa kenan ba zai cika ba?wani sulu tayi sai ƙasa duk suka faɗi rai ya fita,Alhaji Bello ya shiga ruɗu gashi bai tambayi likita wace matssala ce ba,ga kuma wata matsakar ta faru,Likita hankalinsa ya ƙara tashi nan saurab ma'aikata au ka zo aka ƙwashi su Hajiya,Ƙwallah ta zubowa Alhaji Bello kalmar"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!"ita ya dinga maimaitawa da ya shiga ruɗu!
RASHIN COMMENTS ƊINKU YASA NAJE HUTU NA DAINA POST INA GA BAKUDA RABON GANIN ƘARSHEN LITTAFINNAN MAI ƊAUKE DA DARUSSAN RAYUWA😍
ƳAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*
_Home of Brilliant Writers forum_
_LABARI_
_TSARAWA_
_RUBUTAWA_
_HAƘƘIN MALLAKA_
_ƳAR MUTAN DIKKAWA_
BABI NA 48/49
Allah Sarki, abin ƙaunata ƳAR MUTAN DIKKAWA na son ku, son so fisabilillah.Ina jin daɗin yadda ku ke nuna min ƙaunar ku da kulawar ku,Gaskiyar lamari ina nan lafiya, sai dai rashin network mai kyau da nepa ya samu gaba, ku ƙara haƙuri In Shaa Allah komai zai daidaita,masu kirana awaya da turon saƙonni na gani ina godiya,Tabbas ina matuƙar alfahari da samun ku a ratuwata my FANS.❤️
********************* Alhaji Habibullah ne zaune acikin iyalan sa,bayan Ammi da yaran sun kammala karatukan su,nan aka buɗe sabon babin firar duniya suna kallo labarun duniya,Gwaggo tana gefe zaune ta cika fam,sai girgiza ƙafafuwanta take.Ganin Abbu ya baiwa iyalan sa fuska sai abin ya ƙara ɓata mata rai,Ta ce"Shin Habibu baka san ina cikin falon ga bane?Ai wannan wulaƙanci ne,yanzu gani zaune kamar dai bani?Sai dariya ku ke hatta kallon nan ban san abin da ake ba,sai turance ni kukeyi,talabijin turanci ku kuma turanci kai da matarka da ƴaƴanka,wa ma ya sani ko duk kun haɗe kai ni ku ke zagi a fakaice don kunga banji da ganin dariyar da ake nasan dani ake,idan kun gaji dani ba sai anyi min kora da hali ba,Allah ya kaimu gobe lafiya tafiyata zanyi..."Abbu ya katse mata magana ya ce"Haba Gwaggo ke fa uwa ce agareni,tayaya zamu taru mu zage ki,kinga talabijin(ya nuna)labaru sukeyi fa na ƙasashen duniya,idan an nuna wani abu ne nake ƙara masu bayani."To ai da sai kai bayani da Hausa mana yadda nima zanji in ƙaru idan naje ƙauye na samu abin barbaɗawa daga nan sai darajata ta ƙaru."Inji Gwaggo,murmushi Abbu yay tare da gyara zama ya ce"To yanzu kiyi haƙuri zan dinga fassara miki"Ahto nikam ai dole in tafi,na baka shawara kayi aure...Duban su yaranta Ammi tayi ta ce"Ku zo muje ai wanka a ƙwanta"tashi sukayi dukan su suka bi bayan Ammi,Tsaki Gwaggo tayi ta ce"Ƴar baƙinciki ko kiso ko karki so aure anyi an gama shi ne hadda tarkata ƴaƴanki kuyi gaba,an taɓo abin da baki so"Gwaggo kin san ba kowacce magana ake a gaban yara ba,tayi hakan ne domin ta kawar da yaran da sauraran maganar da ta girmi kunnensu,wannan wata hikima ce wadda mata masu ilimi keyi,amma yadda kike zato ba haka bane,sun bamu wurin don mu tattauna da kyau Abbu ya ce"Fuakarsa ɗauke da damuwa don dai Gwaggo ta fara isar shi.
Riƙe baki tayi tare da taɓe shi ta ce"Uhumnnnn lallai iya gani iya ƙyalewa,to ni taimakon ka zanyi Habibu mai matar gwal,ba don haka ba da na ƙyaleka don naga bakinka ɗaya da Zainabu,ita ce uwarka mu banza ne in ba haka meye aciki?Dan nace ga Jummala ta wajena ka aura,amma ka murje ido kace ba zakayi ba,nidai nasan ance"Bin na gaba bin Allah"babu laifi ni tafiyata ma zan gobe,don naga babu wata hanya da ta rage min wadda ban bita ba amma ka bijire,daman mai zuciya ake faɗawa biki,ga ka ga UWAR ƳAN MAATA kufi mai da garin rogo soyewa..."Daga nan Gwaggo ta tashi ta wuce ɗakinta a fusace,dafe kai Abbu yay tare da faɗin "Hasbunallah"nazari yake shin meye mafita kodai ya karɓi auren na jummala? Don gujewa tashin hankali da kace nacen dangi.
****************** Daga inda ta ke zaune ta jiyo muryar Alhaji Bello yana tambayar ƙannan Hajiya Babba ko sun ganta?Tana jiyo ɗaya daga cikinsu ta ce"Ahaaf sai ka nemo ta kasan ta zama mujiya acikin mata,wa ma zai zauna da ita guri ɗaya ta shafa masa,mugun kashi na haihuwar mata bila adadin...Bai tsaya sauraren su ba ya fiddo wayar shi,kira ɗaya ta ɗauka tana tasowa zuwa inda yake,ƙanwar Karima ce,ta iso gurin ta ce"Alhaji ya ake ciki daidai nan Hajiya Halima ta iso ya ce"To ance ta haihu amma yanzu zamu ƙara jin bayani,ya dubeta ya ce"Sadeeya muje daga ciki,gaba ta shige yana biye da ita baya har suka shiga. Autar su Hajiya Babba ta tashi tsaye tana kallon su har suka ɓace tana faɗin Wa innahu min Sulaima ta riƙe baki ta ce"Yaya Hasiya kiɓuna gani ɗan ƙwali yaja hula,a ah lallai wagga mata shu'umar gaske ce,tana gaba ɗanta ya bi bayanta shegiya mai kalar ƙarshen zamani ni wallahi na tsaneta tsaki tayi tare da ɗaukar ɗanta da ke tsala kuka ta saɓa a baya,ta ce"ni kunga tafiyata tunda haihuwar ba wani gamsasshen bayani,wataƙil ma tasa an kashe ɗan aciki,nikam dai ba zan jure ganin wanga ɓacin rai ba,Hajiya Hasiya ta nisa tare da kallon ƙanwarsu Sahura dake ƙoƙarin tafiya ta ce"To sai da safe mukam dai dole mu haƙuri,har mu ga yadda hali ya yi, kinsan halin Meri kura ta bata da sabo,idan mun tafiyar mu duka ta fito ta samu ba kowa zata mana rashin daraja...Ohhhtoooh ita ta sani ai sabo yafi iyawa kar ta san kar ni da ita ni na wuce Sahura ta ce tayi tafiyanta,a hanya sai zagin Hajiya Halima take.
*************** Suna shiga ciki ya dubeta fuskarsa ɗauke da damuwa,ya ce"Mommyn Zeenat Hajiyata da Inna Karima fa duk dun faɗi...Subhanallah ta ce"tana fiddo ido cike da tsoro ta ce"Me ke damun su?"Haka kawai fa ina ga fargaba ne,don ni kaina ina ganin kamar Zillaziya ta rasu bayan ta haihu don Likita ya ce"Aƙwai matsala gasu su kuma har yanzu basu farfaɗo ba,Ta ce"Ima likitan yake?Ƙofar inda suke ya nuna mata don ransa ya taɓu sosai don baya jimirin tashin hankali,nan take sai zuciyarsa ta kare,duban shi tayi da tausayi ta ce"Daddyn Sareena ka zamo jajirtacce akoda yaushe ina faɗa maka karyayyar zuciya ba ta namiji jarumi bace,fon Allah ka ƙwantar da hankalinka,In shaa Allah babu abinda zai faru,yanzu muje inda Likitan ta ce"tana wucewa gaba,jiki ba ƙwari ya mara mata baya sun sami likitan na rubutu ya ce"Alhaji ga takardar magani sannan muna buƙatar jini da gaggawa yanzun nan zamu shiga aiki,za'a ƙara mata jini kasancewar tayi zubar jinin da yawa,Likita ta haihu ne?Hajiya Halima ta tambaya ya ce"Eh,ta haihu kuma babu wata matsala ta samu ƴan biyu...tun kan ya ƙarasa magana ta ce"Alhamdulillah,ta dubi Alhaji Bello tana murmushi,har zata koma tambayar Likita sai ya katse mata hanzari ya ce"Aƙwai wanda za'a ɗebi jininsu ko saye zakuyi?Alhaji Bello ya ce A nemo jini daidai da nata a samata kowa nawa ake buƙata zan biya,nan da nan Likita ya ce"Babu matsala"Daga nan akai cike-ciken da za'ayi Alhaji Bello ya biya aka shiga sama Zillaziya jini wacce har yanzu ta ƙasa gane a duniya take ko lahira.
************