Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 13

Uwar y'an mata complete - Chapter 13

Uwar y'an mata complete Chapter 13: Uwar y'an mata complete Chapter 13. Ɗakin su ka koma kowa ya yi zurum duk sun rame saboda kai kawo da fargaba,ko yunwar…

3,813 words

Ɗakin su ka koma kowa ya yi zurum duk sun rame saboda kai kawo da fargaba,ko yunwar cikinsu kaɗai abin a tausaya masu ne,Ya ce"Kamar na ga Hajiya ta motsa ko?matsawa tayi kusa ga inda Hajiya take ƙwance ta kai kunnenta gurin ƙirjinta, daidai nan Hajiya ta buɗe idonta da suakyi jajur abin da idonta yay karo da shi ne bata gazgata ba,ƙara lumshe idon tayi ta buɗe ganin Halima ce a zahiri yasa ta ƙwallah ƙara,da sauri ta dawo baya daga inda Alhaji Bello ke tsaya,a gigice Hajiya Babba ta tashi zaune ta ce"Jama'a ku taimakeni ƴar sikiro zata cije ni,koma ince zata shaƙeni ta kasheni,Inda take ya nufa yace"Haba Hajiya karki tara mana mutane ki daina wannan magana,hannu ta aza aka ta ce"Wato ɗan Inna ashe ma kana kusa,a gabanka zata kasheni?Bayan tayi asiri ta kashe magajin yanzu kuma ni taso kashewa,ta nuna Hajiya Halima wcce ta soke kai ƙasa,Ta ce" muguwa mai baƙar aniya ,rayuwata tsawo gareta wake nan ki kawo ƙarshenta ta Allah ba taki ba,idan keyi nasarar kashe Magaji to kisani wani na nan zuwa ba zan mutu har sai ya sani mota ya tuƙa ya yi yawo dani a ganiyar Kano."Saukowa tayi daga saman gadon tana surfa masifa tare da tazge robar ruwan da aka ƙara mata,ya ce"Hajiya ina zaki?ki cire ruwan ba tare da izinin su ba,kinsan basa son haka."Hararar shi tayi ta ce"Zanje in ga Zillaziya,murmushi ya yi ya ce"Ai tana lafiya Likita ma ya ce"Tawaye ne ta haifa,da babbar murya Hajiya Babba ta ce"Tawaye fa kace Ɗan Inna?"Wannan ƙarar tayi sanadiyar farfaɗowar Karima dake ƙwance gefen gadon Hajiya,itama ruwan ta cire ta ce"Alhaji maza ko mata?"Da mamaki Hajiya Halima ta dubeta abu kamar hauka?Ta ce a ranta tare da musu fatan shiriya.

Ya dubeta tare da cewa" Halima shin ya faɗa miki ko waɗanne ne?"Da sanyin murya ta ce"Ai ban tambaya ba,yana ce min tawaye ne sai yace"Aje ai maganar sa mata jini shi ya hana na tambaya."Tsaki Hajiya Babba tayi ta wuce fuuuuh tana faɗin tsabar hassada da baƙin ciki dai ya hana ki tambayi ko me aka samu,Karima wayarta da jikka ta ɗauka tana faɗin nidai Allah yasa maza ne ko namiji da macce ba mata ba ita ma tayi tafiyanta,kallon Alhaji tayi tare da yin murmushi ta ce"Abban Zeenat barka Allah yasa ƴaƴan nan da aka haifa maka masu Albarka ne,ya baka ikon masu tarbiyya ita kuma Zillaziya Allah ya bata lafiya da ladar shayarwa.Ameen ya ce"yana murmushi."

Hajiya da Karima suna rige-rigen isa ƙofar ɗakin,da Zillaziya take sai da babu kowa duk ma'aikatan suna ciki kuma sun saki labule,shiyasa au ka fita da Albishir haihuwar ƴan biyu,kowanne sashe sai murna suke tare da hamdalla har guɗa daga nan habaici ya tashi,tambaya suke inji macce da namiji ne ko maza?Nan kam ba amsa,sai dai jiran tsammani.

Saman kujera Nurse ɗin ta samesu tana murmushi ta ce"Yallaɓai,Hajiya ga ƴan biyu amsar su Hajiya Halima tayi duka, tana faɗin Ma Sha Allah,tana dariya ta ce"Nurse injin sojoji ne ?murmushi tayi ta ce"Fata nagari ki sara a daidai kan gaɓa gasu nan ko barkalla"sannan ta wuce,Alhajin ta miƙawa ɗaya tana faɗin" Allah abin godiya Sareena ta samu ƙannai maza,yana farin ciki ya dubesu farare tatas masu cike da ƙoshin lafiya,kyawawa dasu Likita ya fito ya ce"Ranka shi daɗe an gama komai har ma ta samu bacci zuwa gobe,za'a iya sallamarta."

Da murna ta runguma su, tana ƙara yiwa ubangijin rahma godiya da kirari ta fita,inda su Hajiya ta isa ta ce"Hajiya Barka ga ƴan biyu tana miƙa mata su tana murmushi,Karima da sauri ta ƙaraso har da dafa Hajiya Halima ta ce"Mata ko maza ko shinkafa da wake?Tana dariya ta ce"Duk maza ne,Inna Karima"wata irin guɗa Karima tayi nan wurin ya ɗauki murna,Hajiya Babba har da takawa Alhaji Bello fitowa yay baki har kunne,ya ce"Hajiya kinga ƴan maza...Da karaɗi ta ce"Na gani Ɗan Inna ka ga amfanin bin umurnin uwa,gashi ka samu mazaje har biyu kai Allah yay ma Zillaziya Albarka,ta biyani Allah ya biyata daga nan sai abin da Hajiya Babba ta mance,Ran Hajiya Halima ya kai ƙololuwar ɓaci,amma a hakan ta kanne,Karima ma ta shirya abin da zata aikatawa Hajiya Babba,ganin cin fuskar yay yawa yasa Alhaji Bello ya ce"Zasu koma gida,nan Nurse ta fito tana faɗa ta amshe yaran don basu bari a fito dasu waje,Karima da nata mutane wurin ƙwanciya suka nema, don sauran sun koma gida,Hajiya Babba da Hasiya suka rage shiyasa su ka haɗe dasu Karima,Hajiya sai maida zance take tana jan Karima da fira amma tayi mata banza,don ita idan ta manta da cin mutuncin da tayi mata,ita bata manta ba da hakan suka raba dare ana faɗi banza,faɗin wofi.

ƳAR MUTAN DIKKAWA😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 50/51

*Washe Gari* Da misalin ƙarfe tara da rabi na safe,Gwaggo ta karya daga nan ɗakin da ta sauka ta koma,daman tun daren jiya ta kimtsa kayanta tsaf,don haka fitowa tayi sai dai bata samu kowa a falon ba,kasancewar yaran duk sun wuce makaranta,Abbu yana sashensa yana shirin fita aiki yayin da Ammi ke madafa tana ɗaura girki saboda fita Islamiyya da takeyi.

Tsakiyar falon ta ja daga, ta tsaya tare da ƙwalawa Abbu kira,daga ɗakin sa ya dinga jiyo kiran Gwaggo shiyasa ya fito yana danne maɓallan rigarsa ya ce"Na'am Gwaggo."sai da ta ƙwashe shi da wani kallo,sama da ƙasa ta juye ƙasa,sannan ta ce"to nikam dai na tashi zan wuce,ALLAH ya sadamu da alheri inda rai da rabo ma ƙara haɗuwa da kai,amma ka rubuta ka ajiye Habibu,ni da gidanka hayatan-hayatan don ka nuna min matarka da Zainabu sunfi mu daraja,su ne kasan ciwon su banda mu dangin ubanka."Dubanta ya yi da damuwa ɗauke da fuskarsa ya ce"Gwaggo don Allah kiyi haƙuri...Dakata Habibu ai magana ta ƙare,ai wanda ke kan dutsi baya tsoron wasan jifa,don anyi walƙiya duhu ya haska na ɓarke laya,na gane zuwa na gidan nan baiyi maka daɗi ba, don haka tafiyata shi a zaman lafiyarku,jikatta ta ɗauka tayi ficewanta wajen gidan,da sassarfa Ammi ta fito daga madafa ɗakinta ta faɗa ta harhaɗo ƴan abubuwan da take dasu tayi waje,ta samu Abbu nata rarraahin Gwaggo ta shiga mota ya sauketa amma ta turje sai zuba masifa take,da sanyin murya ta ce"Gwaggo don Allah kiyi haƙuri ga wannan a gaida gida."Riƙe Baki Gwaggo tayi ta ce"To salon gwaɗare sahin ƙwalli da reza,ke har kina da abinda zaki bani ki koma da kayanki ni ba matsiyaciya bace ban kuma yi gadon tsiya ba kije ki tambaya duk karkarar mu ba mai arzikin ubana yanzu haka kema arzikin gadon mu kike ci ke ɗiyanki mata,haka uwata ba attajira irinta don haka ni tsiya bata ɗaura min zane ba."Ranta ya sosu amma murmushi tayi ta niyyar juyawa ta shiga ciki,sai Abbu ya ce"Umman Nabeela bani kayan an gode."Ledar ta miƙa masa sannan ta wuce tana jiyo muryar Gwaggo na faɗin ko ya amsa ba zata karɓa ba.

Da ƙyar ya shawo kanta ta shiga motar, sai dai duk inda ya tsaya don mata sayayya ba'a buɗe kantunan ba,shiyasa ya wuce gidan Umma da ita don suyi banƙwana,duk da ba hakan ta so ba,don rabonta da Umma tun ranar da ta kawo ta gidan,bata dawo ba itama bata koma ba,sun sami Umma tana faman gyarawa mai aiki gyaɗar miya,bayan sun gaisa da Gwaggo sama-sama don har yanzu Gwaggo atakaice take da Umman.

Ganin hakan yasa Umma ta ƙwantawa Gwaggo don arabu lafiya,goma na arziki ta haɗa mata sannan sukayi sallama,a zuciyar Umma daɗi taji tare da yiwa ɗanta murna,suna fita Abbu ya tsaya wani kanti ya yi ma,Gwaggo sayayyar kaya iri-iri har da su Jummala wanda haka yay mata daɗi har takeji a ranta ya fara son ƴarta ta.Da hakan ta fara sake ranta har ɗauki hanya sosai,har ƙara sako Jummala a firar su duk da yana kaucewa,amma dai yana sara yana duban bakin gatari,don dai a rabu lafiya.

Bayan likitoci sun duba lafiyar mai jego da yaranta,cikin sa'a ba'a wata matsala,shiyasa aka sallame su,Alhaji Bello daman tun safe yay sammako,don Hajiya Halima ta haɗa abincin kari tun da wuri ya kawo musu,su Hajiya Babba sun ɓararraje sun ƙwashi gara,amma suna gamawa aka buɗe sabon shafin zagin Halima.Har ƙofar fita zuwa haraban asibitin Nurse ta raka Zillaziya tana masu sallama, kana ta koma,Alhaji Bello da Hajiya Hajiya Babba ne riƙe da mazajen,ita kuma Karima da ƙanwarta riƙe da Zillaziya wacce duk ta zabge kamar wadda ta fito daga gidan kaso,tunanin Hajiya Halima take a ranta ko tana ina?Amma ba halin ta tambayi kowa a gurin da wannan tunanin suka isa inda aka ajiye mota ɗayan motar ta Alhaji ɗayan kuma ta Hajiya sai Napep ta ƙanan Karima wanda shi ma ya iso Asibitin tunda safe,Hajiya bakinta har kunne sai wasa take ma jaririn da bai san tana yi ba,mota ta shiga tare da amsar ɗayan na hannun Alhaji su ka shiga mota,har Zillaziya zata wuce gaba amma Karima ta riƙeta ta ce"Ke shiga nan...Da mamaki ta dubeta ta ce"Mommah ga mota mai sanyi kice in shiga wannan abar yaushe rabo?Murtuƙe fuska Karima tayi tare da faɗin"Shashasha girma zanja miki,da kesan rashin mutuncin da Meri tayi min a ƙofar gidanmu har kawowa asibitin nan da wallahi ko kallon arziki bazaki mata ba,maza shige muje ki barta da yaran sai ta sha magani Mama ya kawo ta basu,Alhaji da ke jiran su ya ƙaraso ya ce"Inna muje ga mota can,idan kun gama sallama da Kawu...Ba sallama muke ba Alhaji a ciki zamu tafi,kuma daga nan zan wuce da ƴahta gida,sai ita waccan da bata san halacci ba,ta shayarda yaran.''inji Karima ranta a ɓace,Kash!Inna wallahi ni ban gane me ki ke magana akai ba,koma meye kuyi haƙuri idan munje gida za'a sasanta...Hajiya ce ta ƙaraso bayan ta barwa Hajja Hasiya yaran a mota,ta ce"Wai tsayin me ake kuma,me ake jira anan ne Ɗan Inna naga kunyi wani tsumu-tsumu kamar tsummah a randa?Tsaki Karima tayi ta ce"Alhamdulillahi Meri don ga matar direba ta haifi taya,ke ko ga faɗuwa tazo daidai da zama,amma kisani nikam da Zillaziya zani don in kin manta darajata zan nuna miki na isa da ita kuma ni mai daraja ce,don na haifawa ɗanki mata ta kuma haifa masa zaƙwa zaƙwan maza har biyu ke ga ƴa ta cika ƴar halak,tunda kece idan ta haifi macce zakisa ɗanki ya saketa saboda ke kura ce bakida sabo,kuma baki san meye halacci ba,to yanzu sai kisa ya saketa don nasha alwashin idan ta haifi namiji ba zata zauna ba,don baki da tabbas...Kiyiwa ALLAH Karima ki rufa mana asiri ,duk abin da nayi ta faɗi subul da bakane ke sanni da magana ba kan gado don ALLAH kiyi haƙuri,inji Hajiya Babba wacce idonta har ya kawo ruwa.

Babu zancen inyi haƙuri wato Meri ina da cikinki ba yau kike wulaƙanta ni ba,to kisani yadda kike taƙama Alhaji ɗanki ne nima ɗana ne,kuma surukina sannan uban jikokina ke zuwa gaba haƙƙina sai yafi naki akansa don haka ki taka a sannu don ruwa ba sa'an ƙwando bane har gobe gaba tayi gaba baya ko sai biyar sau...Ƙannan Karima ne suka katseta tare da bata baki da ƙyar ta haƙura bayan ta juyewa Hajiya duk abinda ke cikinta tana faɗin"Da ku barni sai taje tasha sassaƙe da da sabara ta shiga biƙi kawai ta shayarda su kamar yadda ta shayarda uban su."Hajiya Babba bakin magana ya mutu,don ƙaunar jikokinta ya saye duniyar cin mutuncinta liƙis tayi har Karima ta gama cin kasuwarta tayi shiru,da lallami Alhaji ya sasanta su,sannan ya ce"Zillaziya ta fito daga cikin Napep ɗin da take ƙwance." duk da taji komai sarai,kuma ranta ya sosu sosai da irin abin da Hajiya Babba tayiwa Mommanta,amma kuma ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu don basu ci bashin cin zarafinta ba.

Ko da suka isa gidan ko'ina tsaf har sashen Zillaziya duk Hajiya Halima ta gyare tsaf,ko'ina sai daddaɗan ƙamshi ke tashi,ga shi yaran na makaranta ga aikin abinci ta ɗaura,amma a hakan take ta hadahadar tarbon su take,da yake Alhaji ya kirata suna hanya,da yake suna da hitar banɗaki shiyasa ta cikata da ruwa ta kunna,ko da zasu ƙaraso ruwan ya tafasa sai ai ma mai jego wanka,A lokacin da suka shigo falon gidan da ƙamshi suka fara cin karo,ganin sashen Zillaziya yasa Karima ta jinjina mata da ƴan uwanta amma Hajiya sai tsaki tayi,Da fara'ah ta shigo tana masu sannu da zuwa,Karima amsawa tayinan Hajiya Halima ta ce"Zillaziya ya jikin?"Jiki ba ƙwari ta ce"Da sauƙi Anty.Ina su Mamu?"sun tafi makaranta ai jiya basuyi bacci ba sai murna suke inji Hajiya Halima,Zillaziya ta ce"Anty nafa gode da addu'oinki na zahiri da baɗini wallahi duk azabar da nakeji ina shan addu'ar da kika ba Nurse naji wani sauƙi sai ga haihuwa ta zo,ba zan manta da wannan taimakon naki ba,don naga ƙarfin addu'a."Dariya tayi ta ce"Ai ba komai yiwa kaine,inda yaran suke rungume da Hajiya ta duba sai dai tana tsoron cewa Hajiya ta bata su,shiyasa ta ce"Sojojin mu bacci ake?"Ƙanwar Karima ta amsa"ta ce ragwaye sai bacci suke tana dariya." don Hajiya da ƙanwarta Hasiya ko kallin arziki Hajiya Halima bata ishesu ba,saboda ko gaisuwarta basu amsa ba, Ta ce"A'ah ai sojoji ne Inna,ga ruwan wanka can na haɗa mata a bayi sai ki mata,zanje ma ƙarasa girki inji Hajiya Halima.

Ƙanwar Karima da ita kanta Karima har suna haɗa baki gurin yi ma Hajiya Halima godiya,sannan ta wuce fitarta ke da wuya Hajiya Babba ta ce"Wai ku har kunga abin so anan?Duk fa na gulma ne don a yabeta ai da gangan naƙi bata su sai satar kallon su take kamar mayya,ina zan bata su nasan shirinta a kansu...Uhumnnn gaskiya ne Yaya ai mutum abin tsoro ne,tana iya illata su tunda asiri sana'arta ce da tafi ƙwarewa,inji Hasiya tana taɓe baki.

Zillaziya satar kallon yaranta tayi wata ƙaunar su na fizgarta,sai dai har yanzu Hajita taƙi ta bawa kowa su ta rungumesu sai wasa take musu,addu'a tayi a ranta Allah yasa suyi kuka ko itama zata ɗauka ta laguda don gasu tana gani ba halin ɗauka uwar ubansu na neman nuna mata tafi ta son su. Zagin da suke ma Hajiya Halima ne ya dawo da ita hankalinta da ya tafi gurin tunani,Karima ta ce"Gaskiya yabon gwani ya zama dole,Halima na da ƙoƙari kuma ta kyauta don haka duk mai tsoron Allah dole ya yaba mata,ke Meri ai kona munafunci ana mata kamar yadda kike ganin tayi "ai yaba kyauta tukuici."ta ci a gode mata shiyasa,baku san halinta ba shiyasa inji Hasiya daga nan aka wuce da mai jego zuwa ɗakin wanka Hajiya ma ruwa tasa azuba mata tayiwa yaran wanka tatas,Alhaji yana ajiyesu sashensa ya faɗa yay wanka,ya ƙwanta don ya samu hutawa ita kuma uwargida tana madafa tana haɗawa mai jego abinci naji na gani na faɗa.

BAYAN MAKO ƊAYA

Abubuwa da dama sun faru ciki har da shige da fice ɗinbim jama'a masu zuwa da dawowa barka a gidan Alhaji Bello Babale,daga gefen Hajiya Babba har Karima da ƴan gulma da mutanen unguwa da abokan arziki kowa ya taka rawa,gurin zuwa yowa su Hajiya barka da arzikin samun ƴaƴa maza a tarihin gidan.

Ranar wanka akace ba'a ɓoye cibi haka Rana bata ƙarya da yardar ALLAH a yau ɗinbim mutane sun shaida da zanen sunan SHADDAD DA SHAHID wanda akayi buduri aka kuma ɓatawa naira rai,Hajiya tayi tsaye ƙyam,an tittilawa Zillaziya kaya kamar tsaba haka tagwayen kowa da saitin aƙwatunan sa,kysan saiti uku akayi tun daga uwarsu har su,sai akayiwa kowa kala ɗari da sauran tarkacen da ba zasu faɗu ba,kattin bajiman sa biyar da raguna huɗu aka yanke ranar suna,Alhaji Bello ya nuna yana da masu gidan rana ciki kuwa harda canja ma su Karima gida mai kyau aciko sukayi bukin sunam,haka ya biya mata makka ita Zillaziya da Buzu duk da shi tun bayan auran ƴar yay zuciya ya koma Niger yana da matarsa sai yaga dama ya zo inda suke. Karima taji daɗi matuƙa haka sukayi bajakolin jin daɗi ita da yaranta da danginta dan jikoki sun zo mata da sa'a.

A gefen Hajiya Babba idonta ya rufe ruf bataji bata kuma ganin kowa sai su Shahid da Shaddad,ita ma tayi ɓarin naira masu kalangu ta ɗauko ta danshi rawa a gidan,ita da ƴan uwanta sai liƙi take abin dai sai wanda ya gani,Zillaziya ma ba'a magana duk ƙawayenta na yanar gizo sun halarto,uwar daba da kanta ta ɗauko makaɗan kalca da yamma lis sukaci ado naji da gani don ba ƙarya Zillaziya ta wanku an sha ƙumshi,ado da ƙwalliya na kece raini nan fa wasa ta dawo sabuwa,har su limcy da sauran ƙawayen Zillaziya sun garzawo don biyanta bashin rawar da take masu a matsayin buki,su Safara'u suma kalar ankon su dabam sun haɗu don kowa da nashi kalar Ankon su Hajiya Babba nasu ja ne,su Safara'u kore yayin da ƙawayen Zillaziya sukayi leshi kalar madara da ɗan ƙwali baƙi anyi garali na bam mamaki daga can na hango ƴan group ɗin ƳAR MUTAN DIKKAWA sai gulmar Zillaziya sukeyi tare da hararanta suna tsaki a ƙarshe dai sashen Hajiya Halima suka nufa.

Itama dai tayi kyau sosai ita da yaran cike da farin ciki take ita da danginta da suka zo dasu lubabatu wacce Labaran ne ya kawota da kanshi shima dai yana wurin Alhaji Bello ana cin buki,komai Hajiya Halima ta tanada a sashenta wani lesi tasa mai kyau ta zuba ado ita dai kamar Amarya sai ƙamshi take zubawa,bayan anci an sha ta canja wanka ita da su Zeenat sun sa leshi mai kyau fari da ɗan ƙwali jinin kare itama wani shadda ta canja ruwan jinin kare da mayafi fari,sunyi kyau sosai kamar ka sace su dan kyau don ba ƙarya su ma Alhaji Bello ya tsaya masu ya kuma sake madu kuɗi sosai don su sayi abin da suke buƙata.

Filin ya cika ya batse ana ta rawa,tunda Hajiya Halima ta doso farfajiyar gidan kallo ya koma garesu don yaran su dafa mata baya,gwanin sha'awa ga yanayin fitar kamar iri ɗaya dukan su laces ne ajikinsu sai dai natan yafi tsada don duk wurin ba mai irinsa,amma ita jinin kare ne, su kuma nasu fari,mayafinta fari yayin da ɗan ƙwalinsu ya kasance jinin kare. Da isar su fili da wasa ya dawo nasu kun san dai mawaƙi,nan ya dinga waƙe Hajiya Halima Uwar ƴan mata jallin iyaye, sai koɗata yake yana yabonta tare da yabe kyawawan yaran, rawa ta dinga yi tana juyi a hankali tare da sake naira,yaran kewayeta sukayi suna zuba mata kuɗi sai daria sukeyi Zillaziya shigowa tayi tana mata liƙi,da yaran nan fa makaɗi ya ƙare kashe kiɗa yaran Hajiya Halima ta rungume ajikinta shahid da Shaddad tana rawa a hankali,Mamu kam zagewa tayi ta dinga tiƙar rawa har da mulmular baya,masu hoto sai ɗaukar su sukeyi gwanin sha'awa duk da wasu sunji haushi amma kam zuwan uwar ƴan maata ya ƙara haskaka taro tare ƙayata shi,an sha shagulgula kam sai san barkah Allah ya raya SHAHID DA SHADDAD.

More comments more post

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM(EWF)*

_Home of Brilliant writers forum_

LABARI

TSARAWA

RUBUTAWA

HAƘƘIN MALLAKA

'YAR MUTAN DIKKAWA😍

BABI NA 52/53

_ALLAH SARKI MASOYANA WANNAN PAGE NAKU NE,NA BAKU SHI KYAUTA, A BISA SO DA ƘAUNA TARE DA KULAWAR DA KU KE NUNAWA A KAN DUKKAN LAMARINA,BURINA NA FARANTA MUKU,LALURA KA ƊAI ZATA SA KU DAINA GANIN POST ƊINA,DON HAKA ANA TARE MUTU KA RABA, SON SO FISABILILLAH NA GODE._

_Bismillahir Rahmanir Raheem._

Komawar Gwaggo cikin fushi,ya haifar da abubuwa marasa daɗi da dama,dangane da alaƙar su da kuma zumuncin su,don kuwa Abbu "Ya baro baya da ƙura."bayan dawowar shi daga ƙauye,Gwaggo ta shirya maƙarƙashiya mai muni wanda sanadin hakan yasa dukkan ƴan uwa suka juya musu baya shi da Umma.

********Zaman Sama'ila da Hajiya Arziki ku san na tsawon wata ɗaya, zama ne na shariya da kawar da kai,babu yanda baiyi ba don ya samu Hajiya ta kula shi,amma sai ta dinga kawar da kai tamkar ma bata san yanayi ba,Sama'ila ya dage da yiwa Hajiya biyayya,kasancewar ya rasa komai nashi sanadin gobara,matar shi ta guje shi akan talauci, bugu da ƙari ga haushin ƴan uwan shi, da har yanzu basu ba labarin su. Zuwa Sama'ila ya shiryu sosai kuma ya gane cewa"Duniya da abin da ke cikinta babu tabbas akan su."shiyasa ya dangana ya kuma miƙawa Ubangijin talikai lamarinsa,tare da tuba zuwa gareshi akan dukkan abin da ya aikatawa mahaifiyarsa.A ɓangaren Hajiya Arziki taji sauƙi aranta don zafi da raɗaɗin da takeji ya fara raguwa,wataran har tausayin Sama'ila takeyi,amma a hakan ta ci gaba da gasa masa Aya a hannu domin ya ƙara karatun ta nutsu. Duk da Hajiya Zainab(Umma) tana bata baki har kullum,akan tayi haƙuri ta sake ma Sama'ila ta yafe masa,don yanzun ya gane gaskiya, kuma Allah ma gafoor raheem ne.

****************** Zillaziya mai jego an gama wanka,ta fito tsaf ita da yaranta sunyi kyau kamar ka sace su gwanin sha'awa,saboda a dangin Hajiya Babba ta samu matar da ke kula dasu tana kuma taimakawa Zillaziya. Zaman Hajiya Halima da Zillaziya zama ne mai daɗi, don su Abdul da yawan lokuta suna gurin Mommy ko su Mamu,wannan haɗin kan da aka samu a gidan yana yiwa Alhaji daɗi wanda tuni arzikinsa ya ƙaru har ya fidda Zeenat da Khaleesat ƙasar India karatu yayin da Bilkeesu da Hajara ke karatu Dubai,duk da fitan yaran ƙasashen waje yayi ma Hajiya zafi don a ganinta kamar ɓatar da kuɗi ne,ilimin ƴa macce ba ilimi bane wanda za'a amfana da shi,amfanin su ɗaya a aurar da su haka dai tayi ta masifa da ɓacin rai,a lokacin Alhaji Bello bai tsaya sauraren ta ba,ya tura su karatu,gefen Hajiya Halima ba haka taso ba,saboda taso yaranta su zauna kusa da ita amma yanzu nisanta da su zai haifar mata da maɗuwar gaba ko yaushe,a ganin ta ƴa macce koyaushe ta kasance jikin idon iyayenta.Idan kuma tana aure to tana kan idon maigidanta,saboda hali baya da wuyar canjawa duk da ALLAH ne mai shiryawa a lokacin da yaso ya ga dama shi ɗan Adam baya da wani tsumi ko dabara,wannan yara ta tarasu dukan su tayi masu nasiha mai ratsa zuciya,akan su kula da kan su,sannan su kama mutuncin su"Don shi mutunci madara ne."har da hawayen Mommy tana basu baki akan dai su riƙe mata amanar kan su har suka wuce kullum jawabin ta ɗaya ne.

Hajiya Babba kakar ƴan biyu tamkar ba'a taɓa haihuwa a gidan ɗan nata,don duk wata soyayya da kulawarta tana kan ƴan biyu,kullum sai ta zo gidan take yuni tana masu tawai da kirari iri-iri ba kalar habaici da shaguɓen da bata yiwa Hajiya Halima mai taken UWAR ƳAN MAATA. Zillaziya ko ta murmure tana damawa a gidan,don Hajiya da Alhaji da kuma Anty sun tsaya mata shiyasa bata da wata sauran damuwa ga yaran ta tubarkallah sun girma ba laifi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull