Uwar y'an mata complete - Chapter 14
Uwar y'an mata complete Chapter 14: Uwar y'an mata complete Chapter 14. Watarana Uwar daba ta kawowa Zillaziya ziyara, don tun ranar suna rabonta da…
4,071 words
Watarana Uwar daba ta kawowa Zillaziya ziyara, don tun ranar suna rabonta da gidan,Zillaziya taji daɗin zuwan uwar daba shiyasa suka dinga fira bayan sunci sun sha sunyi hani'an,murmushi tayi tana duban fuskar Abdul Rahman da ke rungume a jikinta ta ce"Ke kam Zilly ke haifo kadararki,wallahi ke samu babban rabo a gidan nan ko yanzu ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu,ga yara kyawawa. Dariya Zillaziya tayi ta ce"Uwar Daba tawa,wai kinsan ni nafi ganin kyaun Abdul Raheem yafi haske kuma sai in ga idon sa kamar nawa,Kul ba'a cewa hakan inji Uwar da Daba tana ƙara kallon yaran,waigawa tayi ba kowa a falon sai su ta sassauta murya ta ce"Zilly ya ake ciki?Ina fatan dai kin fara tara kadarori,ke san yanzu fa sai kinayi kina wawara kafin mai afkuwa ta afku ke tara...Bangane ba me kike nufi ta tambayeta da sigar mamaki,ɗan murmushi tayi tare da gyara zama ta ce"Ina nufin ki fara yagar rabonki,kiyi ƙoƙarin kawar da Hajiya da Uwar ƴan mata kinga su hegun matan nan yaranta sai kisa ya aurar da duk wadda ta gama sakandare,daga nan kinga ke rufe babin kowa daga rayuwar mijinki sai ki buɗe sabon shafuka ke da ƴaƴanki.Jim tayi tana nazarin maganar ƙawarta ta,ta ce"Gaskiyar magana daga ni har Mommah akan abin duniya da ƙwaɗiya yasa na aure shi,amma kuma ra'ayi na ya fara canjawa tun ranar da nagane rayuwar duniya ba komai bace,ranar da na shiga ɗakin gane kurakurai,ranar da nayi kuren zuwa ƙiyama,to daga ranar na saduda na tuba don rayuwata da mutuwa ta ba'a hannuna suke ba,amma duk da hakan" ba'a ƙi ta mutane ba,ancewa ɓarawo gudu."zanyi ƙoƙari in ƙara tara dukiya don in taimakawa iyayena da ƴan uwana amma yanzu na canja ra'ayi zan zauna da mijina da abokiyar zamana da zuciya ɗaya,ki duba uwar daba"Duk fa rawar kai da rashin mutunci da makircin da nayi zaman yi mata a gidan nan,bata taɓa kullata ta ba ko tasa ƴaƴanta su min,ko Mamu da ke min rashin mutunci har nake zargin uwarsu ke turo ta daga baya na gane halinta ne,bata shayin kowa kuma tana ma kowa bani kaɗai bace take ma,to daga sannan na daina mata wannan kallo yanzu na gyara mu'amulata da Anty don na gane ita da zuciya ɗaya take sona,yaran nan da kike gani babu abinda bata yi masu babban taimakon da tayi min rayuwa taimakona a lokacin da nake naƙuda,don haka nayi alƙwari ba zan ƙara cutar da Uwar ƴan mata ba,Hajiya Babba kuma daidai nake da ita zanyi maganinta ba boka ba mallam zan dai nuna mata idan ita uwar zamani ce,to nima ƴar zamani ce duk ta dake ni nima zan daketa mugun dukan da ba zata gani ba sai dai taji zafi aranta don wallahi zan mata rashin mutuncin da zai hanata baccin dare...Amma Zillaziya kina da wauta ke har kishiya ce abin yarda?Inji uwar daba tana ma Zillaziya wani kallon banza,dariya tayi ta ce"Uwar Daba nidai na yarda da tawa don inda tana neman magani da yanzu Mommah ko Hajiya cikinsu wani yaje wurin malaminsa ya ce"Tanayi to batayiwa kowa,duk dubi sai dai ace"tana da addini da tsari ajikinta wanda nima shaida ce don har Azkhar da takeyi safe da yamma ta koya min,yanzu hakan kullum sai ta zo ta tofawa su Abdul kuma nima ina karantawa don haka dole naso mai so na tsakani da Allah."Tsaki Uwar Daba tayi ta ce"Allah wadaran naka ya lalace,kicr kema Uwar ƴan mata tabarbaɗe ki,ta tofe ki shiyasa kika sauya nan take,ajiye Abdul tayi tana ƙoƙarin ƙaramin mayafint a ta ce"To nikam zan wuce,gidan Sabeera ƙamshi zanje,Allah ya sauwaƙa daman wani sabon malami ya fito to shi ne naso ki bada haɗin kai na amso miki taimako wurin sa,amma tun da kin bijire shi ke nan,sai dai karki manta kishiya ba abin yarda bace sannan yanzu duk wadda ta san ciwon kanta ƙoƙarin yakito rabonta takeyi,bare ke da Allah ya ba makaman ƙare dangi kina da daraja a gidan nan don kece mai gida ina ƙoƙarin nuna miki ga hanya kina kaucewa,idan baki hattara sai ke dawo ƴar kallo a gidan nan Zillaziya,kinga ya fidda yaran sa har huɗu ƙasashen waje,suna karatu masu tsada yanzu da sun dawo ya narka dukiya yay masu aure,sauran ma hakan ne kafin akawo kan ƴaƴanki duk ƙarfinsa ya ƙare wurin ƴaƴa mata,to kiyi tunani ita meye matsalarta ko da su yaran zasu ƙunsi su kawo mata ke ko labari ba kida,sai dai kita wahala ke da yaranki tunda sun zo daga baya sun tarar da wasu ke ga sune dai baya amaimakon su zamo a gaba.
Numfashi Zillaziya ta sauke saboda duk jikinta yay sanyi,don maganar uwar daba gaskiya ne,don yanzu Alhajinta ƴaƴan nan mata kaɗai yasa a gaba kuma su yake kashewa kuɗi,ta ce"Gaskiya ne Uwar Daba wannan ma magana ce mai kyau."wani kallo tayi mata tare da kanne ido da cije gefen leɓanta ta ce"ko ke fa ƙawata? Ai maza zuma ne sai da wuta,ki tashi tsaye kawai ki tarawa ƴaƴanki idan ba haka ba,kisha mamaki kina zaune sai ai miki sakiyyar da ba ruwa."Inji Uwar Daba tana ƙoƙarin tafiya,haka ne kam daman ni da na saduda saboda gudun mummunan mutuwa da baƙar makoma...Haba Zilly ai yanzu kowa aikata abinda yake so yakeyi, zuwa gaba sai mu tuba ga Allah daman Ajanna fa ta rabo ce,sannan ALLAH mai yafiya ne,har ƙofar falon tayi mata rakiya tare da bata tabbacin da zarar sun dawo daga ummara zata nemi Uwar Daba sau suje ayi yadda ya dace,Uwar Daba taji daɗi sosai aranta,da Zillaziya ta amince da shawararta da haka suka rabu kowa na tunanin mafita ta gaba.
**************** A gefen Ammi komai ya dawo mata daidai don yanzu bata wata damuwa tunda Gwaggo ta wuce,su Nabeela da Aysha duk sun fara kararun jami'a Yaseera da Khadija suna batun ƙare sakandare yayin da Fatima ke aji huɗu,rayuwa tayi musu daɗi koyaushe Umma na kulawa da su tare da nuna musu ƙauna,hakan Ammi tana daraja Umma bata san inda take aza ƙaunarta ba,zaman lafiya da ƙwanciyar hankali ya ƙara wanzuwa a gidan sai san barka,kuma har yanzu Ammi tana karantarwa a Islamiyya ta ko'ina haske take gani a rayuwarta amma barazana ɗaya da take fuskanta wacce ta kunno kai a yanzu bazata wuce....
MORE COMMENTS MORE POST
ƳAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM(EWF)*
_Home of Brilliant writers forum_
LABARI
TSARAWA
RUBUTAWA
HAƘƘIN MALLAKA
'YAR MUTAN DIKKAWA😍
BABI NA 54/55
_Bismillahir Rahmanir Raheem._
Uwar Daba na fita gidan su Zillaziya bata zame ko'ina ba sai wurin Ƙamshi,kallo ɗaya Ƙamshi tayi mata ta fahimci tana cikin damuwa tace"Uwar Daba tamu ya haka?Naga kin zauna kinyi wani dirshim kamar marar lafiya,ga ruwa na kawo maki da abin motsa baki duk ba wanda kika taɓa,ki faɗa min meye matsalarki ina da tabbacin xa'a samu ganinta a gurina kota girma ko kuma ta tsiya."Numfashi ta sauƙe tare da dubin ƙawarta,ta ce "Ƙamshi ina da wata damuwa,amma fa wurin ƙadangarun bariki irin mu ba wata matsala bace,shin ko ke san ina son in auri mijin Zilly?"Wata dariya Ƙamshi tayi tace"Daman na san arina don idan ka ga ƙadangare na shinshinar takalmi ɗauka zaiyi,idan banda abin ki Uwar daba meye ciki don kin auri Bello Babale?To bari kiji ni ƙamshi zan shige gaba,don in ga na ƙamsashe burinki ya tabbata,ai hakan ake yayi uwar wa?Ta aiketa faɗa mana irin daular da take ciki,da irin damawar da takeyi a gidan aurenta,nima nan da kike ganina ƙwanaki naso nayi wuuuf da shi daga baya kuma na fasa don nafi son saurayi mai kuɗi."Ruwan sanyi Uwar daba ta kora a maƙogwaronta sannan ta ce"Bari kawai ƙamshi sai yanzu naji sanyi,don na zata bazaki goyan baya ba,zakice naci amanar ƙawance...Haba ai haka ake yayi Uwar daba wa zai ga arziki ya wuce wallahi kiyi ƙoƙari kawai yanzu ki samo lambarsa daga nan zancen zai soma,tafawa sukayi tare da bushewa da wata dariya ta shaƙiyanci,nan Uwar daba ta faɗi ma Ƙamshi yadda sukayi da Zillaziya,wata magana sukayiwa junansu ƙusƙus sukayi dariya sannan ƙamshi ta shirya suka fita unguwa.
**************** Ammi ce da sauran ɗalibanta zaune suna karatu,bayan an kammala dukkan karatuttuka,sannan ta fara masu jawabi akan muhimmancin AZKHAR(Addu'oin safe da yamma na tsari) ta ce"Da yawan mata basu san meye Azkhar ba,wasu ma sun sani basuyi akan basu san muhimmancin da yake da shi ba,haka wasu suna yi amma ba koyaushe ba,to ya kamata hankalin mu ya dawo jikin mu,Annabi Muhammad(S.A.W) ya lizimci addu'oin safe da yamma haka sauran Annabawa da sahabai da manyan malamai maza da mata duk suna AZKHAR saboda muhimmancinsa da amfaninsa manzon rahma ya umurce mu da mu dinga karanta su,saboda mu samu tsari daga dukkan abin sharri,ƴan uwa idan muka riƙe su kodayaushe to mun huta don babu wani sihiri da zai iya kama mu,haka da yawan mata suna zuwa wurin bokaye wai a basu tsarin jiki...ƴar uwa da kiji gurin wani mallam ko boka gwara ki laƙanci azkhar zaki ga haske,da sauƙi da kuma ci gaba a rayuwarki,don haka don Allah mata a daina sakaci da addu'a domin mutanen duniya sun lalace,zaki ga baki damu da mutum amma kuma ke kin tsone masa ido,yau mutum bayada gadonki amma yana da kaf na rayuwarki komai naki sai ya sa miki ido,zaki ga baki ma mutum komai ba amma shi gani yake kin tare masa komai,zaki ga ansa ki abaki ke da ƴaƴanki wanda wani baki tamkar guba ne,aƙwai masu kandun baka da sauran su,amma idan kin riƙe azkhar kinayi kina yiwa ƴaƴanki wallahi kowa tama zai barki,saboda hakan nake ƙara kira da ku riƙe addu'oin Azkhar kuma ku koyawa yaranku su kuma ƙananun ku dinga yi kuna shafa masu."ga kaɗan daga cikin addu'oin...
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
A cikin littafin HISNUL MUSLIM 72/92
KO
CITADEL OF THE BELIEVER(Invocations from the qur'an and sunnah)
أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ. اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ لاَ تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلاَ نَوْمٌ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلاَ يُحِيطُونَ بِشَىْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلاَّ بِمَا شَاءَ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَلاَ يَؤُودُهُ حِفْظُهُمَا وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ
قُلْ هُوَ اللَّـهُ أَحَدٌ، اللَّـهُ الصَّمَدُ، لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ، وَلَمْ يَكُن لَّهُ كُفُوًا أَحَدٌ.
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ، مِن شَرِّ مَا خَلَقَ، وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ، وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ، وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ.
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ، مَلِكِ النَّاسِ، إِلَـٰهِ النَّاسِ، مِن شَرِّ الْوَسْوَاسِ الْخَنَّاسِ، الَّذِي يُوَسْوِسُ فِي صُدُورِ النَّاسِ، مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ.
أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ (اَمْسَيْنَا وَاَمْسَ) الْمُلْكُ لِلَّهِ وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، لَا إِلَهَ إِلَّّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِيْ هَذَا الْيَوْمِ (اللَّيْلَةِ) وَخَيْرَ مَا بَعْدَهُ، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ (اللَّيْلَةِ) وَشَرِّ مَا بَعْدَهُ، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ، وَسُوءِ الْكِبَرِ، رَبِّ أَعُوْذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِيْ النَّارِ وَعَذَابٍ فِيْ الْقَبْرِ
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِر لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ
اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ (اَمْسَيْتُ) أُشْهِدُكَ وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ، وَمَلَائِكَتَكَ وَجَمِيعَ خَلْقِكَ، أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ وَحْدَكَ لَا شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُكَ وَرَسُولُكَ
Wannan addu'ar kuma ta neman tsari ce,daga dukkan abubuwan ƙi...
أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لَا يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولَا فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وَذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ، وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فِيهَا، ومِنْ شَرِّ مَا ذَرَأَ فِي الأَرْضِ، ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طَارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بْخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ "A nan zan dakata, sai kuma wani zubin idan Allah (SWT) mai kowa,mai komai ya bamu ikon gudanarda al'amurran rayuwar mu Allah ya amince mana."Ammi ta ce tana mai gyara zaman farin gilashin idonta."
Ɗalibanta godiya suka dinga mata,a lokacin da wasu ke rufe littafan su da suka gama rubuta addu'ar,masu Hisnul muslim kuma suka saka alamomi gurin addu'oin daga nan shugabar ɗalibai tayi addu'a aka shafa kowa ya kama gabansa.
************* Hajiya Babba sai kaiwa takeyi tana dawowa cikin falon,dogon nazari tayi sannan tayi ajiyar zuciya,domin abubuwa da dama sun ƙulle mata,babban abinda ke damunta ba zai wuce irin haɗin kan da take gani tsakanin Uwar ƴan maata da Zillaziya,wanda abin yana baƙanta mata rai. Gashi duk wata hanya da zata bi don ganin ta raba zaman lafiyan su ta bi amma abin yaci tura,wani abin mamaki shi ne yanzu Zillaziya ta fanɗare har ma tana neman nuna mata ita ba koman kowa bace...Sallamar sa ta katse mata tunani"Amsawa tayi, lokacin da yake ƙoƙarin zama,suna musayar gaisuwa"Da ladabi ya ce"Hajiya daman na zo in faɗa miki ne,in shaa Allah gobe ko jibi zamu tashi zuwa ƙasar saudiya,kamar dai yadda muka ajiye magana a baya."kallon shi tayi kana ta gyara zaman ta ta ce"To ɗan Inna amma ya kamata ita Zillaziya ta ɗan zauna kaga su ABDUL basuyi wani ƙwarin da za'ayi tafiya da su ba...Hajiya naga da ita Inna Karima zamuje ina ga zata iya tayata riƙe ɗayan,inji Alhaji Bello. Hajiya Babba ta ce"Ya zancen Buzun ya dawo ko har yanzu bai amince da zuwan ba?A'ah ai ina ga ya dawo tare da shi zamu tafi,don tun ƙwanaki ita Zillaziya ke faɗan Baban ya dawo,ɓata rai tayi wanda a zahiri zaka fahimci abin bai mata daɗi ba,ta ce"Allah ya kyauta ya kai ku ya kuma dawo da ku lafiya,amma daga yanzu bana son ka ƙara yiwa matan ko dangin su wani kyauta ko wani alheri ba tare da sanina ba,amma har ta ina zaka biya mata ummarah har da wani kalan dangin uwarta da ubanta don kawai almubazzaranci ai wannan ɓata dukiya ne,addini garesu bare suyi karɓaɓɓiyar ibada,ita Karima har muka gama budurci aka aurar da ita bata gama haddace fatiha ba,jahila ce ta bugawa a jarida bata san komai ba sai tallar dawo da nono amma wai ita ka biyawa ummara har da basu kyautar gida,shi kuma Buzun meye amfanin gashi nan kamar fanko sai dogon wuya kamar maraƙar lema..."Haba!Hajiya don Allah ya wuce a daina tuna baya,nidai don Allah na biya musu domin nuna masa godiya akan kyautar da yayi min,amma in shaa ALLAH daga yanzu duk abinda zanyi zaki sani domin faranta ranki."yaƙe tayi sannan ta ce"ALLAH yay albarka ya ƙara arziki,ya mayar min da kai da tagwayena lafiya,don Allah a kula min dasu kaji ɗan Inna."To shi kenan Hajiyata, ni zan wuce shago,don zan kammala duk wasu shirye-shiryen da zan damƙawa yarana.Daga nan sukayi sallama ya wuce,ita kuma Hajiya sai masifa take akan abubuwan da ƊAN INNA keyi kai tsaye wani zubin batare da saninta ba.
Rashin comments ke haifar da rashin post
ƳAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:45 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM(EWF)*
_Home of Brilliant writers forum_
LABARI
TSARAWA
RUBUTAWA
HAƘƘIN MALLAKA
'YAR MUTAN DIKKAWA😍
BABI NA 56/57
_Bismillahir Rahmanir Raheem._
*DON ALLAH MASU TAMBAYA TA, DAGA FARKO ZUWA INDA AKA TSAYA KUYI HAƘURI, HAR AI DOCUMENT SAI KU KARANTA SABODA NAYI NISA SOSAI.*
Hausa kance"Zara bata barin dame"a ƙwana tashi ba wuya a wurin ALLAH,don su Zillaziya har sun dawo,daga saudi arebiyaKarima ba'a magana don ƴan unguwar fagge sai shiga da fice ake,yanzu kam burin su ya ɗauki aniyar cika don daga ganin Karima har su Safara'u, za'a ga canjin rayuwa ya tabbata a garesu.
Dawowar su daga ƙasa mai tsalki ya haifar da farin ciki a zukatan su,saboda Zillaziya da Mommah duk wanda ya gansu zai ga jin daɗi da hutu tare da walwala a tattare da su,sunyi kyau ga shi sun saka hauren makkah,ƴan uwa da abokan arziki da HAJIYA suke kiransu.
Abdul Rahman da Abdul Raheem tubarkallah sun ƙara girma,gasu farare tubul-tubul da su tamkar ƴaƴan turawa,Alhaji Bello yana ji da ran hakan Hajiya Halima faɗan irin ƙaunar da yayyen su ƴan mata ke masu ma ɓata lokaci ne bare ma kankat Hajiya Babba,su Karima ba a baya ba,ta kowanne gefe jaruman tagwayen ƴan gatan gaske ne,da ke shan kula da tarairaya ta musamman.
************** A ƙwana a tashi ƙwanaki sai tafiya suke yayin da tsawon rayuwa ke ragewa,haka gwagwarmayar rayuwa ke ƙaruwa,ƙwance take a saman makeken gadon ta tana danna waya,murmushi ɗauke ga fuskarta wanda da gani za'a fahimci tana cikin jin daɗi,a gaban gilashin wayarta sunan "MANYAN MAATA"ya bayyana wanda ga alama chatting takeyi,saƙon Uwar Daba ya shigo inda take mata kirari kamar"Ƴar barayar haji Bello uwar ƴan biyu ikon Allah."Dariya Zillaziya tayi a fili sannan ta fara rubuta mata"na dai gode miki uwar daba ta mu."Ƙamshi ce ta turo"anayi ina jin daɗi."can sai ga ƴar caras ta rubutu "na gaida mulamullan mata kyauta."Zillaziya ta mayar mata da amsa''Ƴar caras ta manyan alhazai."Zilly amaryar Belko uwar ƴan maza ya yau?"emojis ɗin dariya Zillaziya ta tura mata "Uwar daba ta rubuto" Zilly ina Antynki?"Kamar jira ta ke tafara labarta masu duk abinda ke faruwa a gidan,nan wasu suka dinga tayasu murnar akan zaman lafiyar da ke wanzuwa atsakanin su,yayinda wasu ke zugata akan kar ta yarda da Hajiya Haleema,tare da bata mugwayen shawarwari. pc uwar daba ta biyo Zillaziya tana zugata tare da hure mata kunne, basu rabu ba har sai da Zillaziya tasa ranar da zasu tafi inda Uwar daba ta ce"zata rakata don abata taimakon da zata mallake Alhaji da ilahirin abinda ya mallaka." [11/9, 8:45 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM(EWF)*
_Home of Brilliant writers forum_
LABARI
TSARAWA
RUBUTAWA
HAƘƘIN MALLAKA
'YAR MUTAN DIKKAWA😍
*BABI NA 58/59*
_Bismillahir Rahmanir Raheem._
*ADVERT👇🏿*
*Assalamu Alaikum.*
*Shin kunji labarin shaharariyar matarnan datayi fice wurin gyarawa mata rayuwar aurensu, da kuma koyar dasu haɗin kayan mata a online ta sake dawowa da sabon salon ci gaba awurin mata kai harma da tsofaffi? Kintaɓa haihuwa nonuwanki suka zube? Wannan damarki ce💃🏻.
Kin taɓa haihuwa gabanki ya buɗe? Wannan damarki ce💃🏻💃🏻.
Kina matsalar bushewar gaba? Wannan damarki ce💃🏻.
Kina fama da tusar gaba? Wannan damarki ce💃🏻.
Kinada kishiya amma kin kasa gane kanta? Wannan damar kice💃🏻💃🏻.
Mijinki yana ƙorafi akan kwanciyar aurenku? Wannan damarki ce💃🏻.
Kinada matsalar warin baki? Wannan damarki ce💃🏻💃🏻.
Gabanki yana wari batare sakinsan dalilin hakan ba? Wannan damarki ce💃🏻💃🏻.
Kinaso ki rage tumbi kiyi sisi? Wannan damarki ce💃🏻.
Kinaso ki ƙware a kirsa? Wannan damarki ce
Kinaso ki iya haɗa turarukan wuta da kuma na jiki kai harma dana mopping? Wannan damar ki ce💃🏻💃🏻.
Shin kinason kisan matakin dazaki gyara tarbiyan yaranki? Wannan damar takice gaba ɗayanta.
Kin iya girki? Kokinaso kinƙware ta kowane fanni? Wannan damar kice dazaki iya haɗa komai daya shafi rayuwarki idan har kika kasance tare da Billy galadanchi da kuɗi naira dubu biyu kacal💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Idan har kika biya kuɗinki badai mutum ba saidai Allah, hanzarta biya kuɗinki tanan👇🏻 0026971316 Gtbnk Balkisu musa galadanchi. Saiki tuntuɓi wannan lambar domin a rangaɗa ki a group inda zaki shana💃🏻💃🏻.
Whatsapp: 07084161619
Call: 08039424298.
Kada ku manta mata masu buƙatar special consultation zasu biya 3000 kacal domin maganin matsalaolinsu inshaa Allah🤝🏻🤝🏻 ******************* Cikin ikon ALLAH Sama'ila ya samu aiki, a ma'aikatar su Abbu ya fara aikinsa, cikin sa'a ganin hakan yasa Umma ta shige masa gaba, wurin nema masa mata mai suna "Safiyya" tana da kirki sosai aurenta ɗaya mijinta Khamis ya rasu bayan auran su da shekara ɗaya, Safiyya tana da kirki da addinin musulunci bugu da ƙari ga nasaba mai kyau, Safiyya Musa ƴar mutan zazzau ce, mahaifinta limamin jumma'ah ne gidan su na nan kusa ga gidan Umma duk layin su ɗaya. Hajiya Arziki taji daɗin zaɓen da Umma tayiwa Sama'ila sosai, shiyasa ita ma tayi a manna tare da sanya albarka tare da fatan alheri, Haɗuwar Saffiya da Isma'il haɗuwa ce wacce ta samu tubali daga iyaye shiyasa ba'a jima ba akai komai na aure, kamar yadda addinin islama ya tanada, ba'a jima ba aka gama komai iyaye suka taka rawar gani Amarya ta tare a gidan Hajiya Arziki inda suke da sashen su dabam.
Auren Sama'ila ya kawowa Hajiya Arziki sauyin rayuwa, domin tana jin daɗin zama da surukarta Safiyya, abin gwanin ban sha'awa komai Safiya ke yiwa Hajiyar su Sama'ila, da taimakon ƴar aikin Hajiya suke aiki don ana baiwa ma'aikatan gidan abinci da sauran bayin ALLAH da Hajiya ke cisuwa. Sama'ila kam "Kakarsa ta yanke saƙa." don a ganisa yanzu yay aure zaman lafiya suke shi da Amaryar sa Safiya, shiyasa ya mayarda hankalin sa sosai akan aikinsa har yana neman kafa jarin da zai samu gurbin kama sana'a a gefe kuma yana yiwa ƴan uwan sa magiya akan su nutsu su dawo, ga mahaifiyar su, ko da yaushe amsa ɗaya yake samu a wurin yayyen nasa ahi ne "Zasu dawo idan lokaci ya yi."
************** Kamar mafi yawan lokuta ya kan ware wani lokaci na musamman domin zantawa da iyalan sa, haka ne ta faru a yau, bayan kowa ya gama idar da sallar ISHA, zaune yake kan kujera mai zaman mutum uku, sanye yake da jallabiya fara tas, carbi a hannunsa yana fuskantar talabijin, Hajiya Halima kuma ta sha ado da ƙwalliya kamar wacce zataje gasar nuna kyau, itama Arabian gown kore shar da hula tasa sai zuba ƙamshi take a gefen Alhaji Bello Babale, kasancewar yau ita ce da turakar mai gidan. Zillaziya ma tana gefe zaune duk da ba wani shiri tayi ba amma ba laifi ita ma tayi kyau, don dukkanin su sunyi jajur fatar su na sheƙi ga albarkar jiki da tasamu muhalli a jikinsu, yaran ko duk suna ƙasan kafet ɗin suna yiwa su Abdul wasa sai ƙyalƙyala dariya suke, Maganar Daddyn su ne ta natsar da hayaniyar su, tsit sukayi suna saurarensa jin ya ce"Yanzu kowa ya faɗi abinda yake so ya saya masa...Mamu ta katse maganar shi ta ce"Daddy nidai ba abinda nakeso irin ka zaga dani ƙasashen duniya in ci abincin kowanne ƙasa"Murmushi yay ya ce"Yanzu ke mamana bazaki rage wannan kauɗin ba, to ni ba daku nake ba, kijira tukun har iyayenki su gama faɗin nasa."Tuɓure bakinta tayi tare da dangware Abdul Raheem zaune ta koma daga gefe tayi tagumi tare da mayarda hankalinta kan kallo" Hajiya Halima ta ce"Oh! ni Sadiya ALLAH ya canja miki hali" Zillaziya dake danna wayarta komai batace ba don chat take da Uwar Daba. Alhaji ya ce"To bari in fara ta kanki uwargida rangida daman aƙwai alheran da suka shigo min a kasuwa, shi ne naga dacewar kuma ku shaida, yanzu ina son ki faɗan abu ɗaya da kike so ai miki? Wani waaar Hajiya Halima tayi da ido ta dube shi, tare da narke murya ta ce "Masha Allah Abban Zeenat ina tayaka murna, Allah ya ƙara ƙaro maka arxiki mai yawa da albarka...uhumnnn nidai in gani...shiru tayi na ƴan sakanni sannan ta ce"A gaskiya na ma rasa me zance,nidai a ganina duk abinda nake nema a duniya na samu kuma duk wani haƙƙi na kana ƙoƙaarin saukewa,don kai namijin duniya ne ka gama min komai, amma duk da hakan abu ɗaya ne nake so a halin yanzu bayan shi bana son komai sai gamawa da duniya lafiya." Ki faɗa min meye shi? In sha Allah zan ƙoƙari sama miki shi Mommy me kike so?" wani murmushi ta sauke akan ƙwayar idon sa ta ce"ina son ka ɗaga min ƙafar ka na shige Aljanna." Dariya yay wacce ta dawo da Zillaziya wurinsu don bata san me ake ba,hankalinta na kan waya, da ido ya kafe Hajiya Halima ita kuma ta wani sunne kai tana wasa da zoben gwal da ke sanye a yatsanta, ya ce" ALLAHU AKHBAAR, Mar'atussaliha kenan, Allah ya saka miki da alheri, ya saki a Aljanna." Ameen mijina Hajiya Halima ta ce"Tana murmushin jin daɗi." Zillaziya sake baki tayi tana kallon su, don abin yazo mata banbaraƙwai yadda ake zuba bariki a gaban idon yara duk da hankalin su na wurin kallo amma ita taji haushin hakan...Maganar sa ta dawo da ita hayyacinta inda yake faɗin "Maman Abdul ke fa me kike so...tun kan ya ƙarasa Zillaziya ta ce"Ina son ka sai min mota sabuwa dal sannan...Haba! Malama ki saurara, ai kowa abu ɗaya nace ya faɗi, ba laifi zan saya miki mota,duvan Hajiya Halima yay ya ce"ke kuma na roƙa miki aljanna duk da hakan zan baki kuɗi naira dubu ɗari biyar ki ƙara akan jarinki" wani zabura Zillaziya tayi ɓacin rai ya bayyana a zuciyarta nan take idon ta ya canja launi,wani tsabar kishi ya taso mata wanda ya kasa ɓoyuwa har ya bayyana, gyara zama tayi tana ƙoƙarin shanye ƙwallan da ya taru a ramin idonta.