Uwar y'an mata complete - Chapter 15
Uwar y'an mata complete Chapter 15: Uwar y'an mata complete Chapter 15. Yaran ya duba cikin farin ciki da walwala, ya rinƙa tambayar su ɗayan bayan ɗaya,…
4,311 words
Yaran ya duba cikin farin ciki da walwala, ya rinƙa tambayar su ɗayan bayan ɗaya, kowa ya faɗi burin ransa ko abinda suke so yay musu, da murna kowa ya faɗawa Daddy abinda yakeso har aka kawo kan Mamu, "MAMANA...MAMANA...MAMANA, Daddy ke faɗi har sau uku amma firrr idon ta na kan talabijin...Tsawa Hajiya Halima tayi mata ta ce"Ke Mamu ba dake ake magana ba, zaki amsa ko sai na sameki wurin na ɓaɓɓallaki?" nar nar tayi da ido tana turo baki ta ce"Na'am Daddy!"Murmushi yay don ya riga ya karanci rayuwar ƴarsa duka ko zaki baya musu sai da lallami ya ce"Ke me kike so ne?"Babu komi Daddy."kamar ya ba komai Mamana?Ki faɗan ko meye zan sai miki."Idonta ya kawo ƙwallah ta sunne kai, sai cika take kamar zata fashe ta ce"Daddy na gane Mommy bata so na,komi gidan nan nice kuma a hakan wai ace nice Hajiyar gidan, ai idan an yaba dani sai a daina yi min faɗa, a dinga jin tsorona kamar waccen masifaffiyar tsohuwar Hajiyar nan...A'ah Mamana tsaya nan kar ki ƙara faɗawa Hajiyata hakan kinsan idan taji ranki zai ɓaci!Murguɗa baki tayi ta ce"Daddy ai mun saba don ni idan tayi min bataci bulus ba wallah, don ko faɗuwar nan da tayi...Saudat ce ta rufewa mamu baki ta ce"Suda ko aku zancen ma kije garin mugun iyayi ki tona asiri...sai kuma tayi shiru, nan Mamu ta gano bakin zaran kallon Mommy da Daddy tayi wanda duk hankalin su na garesu sai dai basu fahimci komai ba, sun ɗauka yawan magana ne na irin Mamu, Daddy ya tashi tsaye ya ce"Mamana tunda baki son komi ni zanje in ƙwanta in huta har ya fara tafiya Mamu ta ce"Daddy! Tsayawa yay cak yana dubinta wani juya ido tayi sannan tayi murmushi ta ce"Nidai gida zaka sai min...Gida kuma Mamu? Hajiya Halima ta ce"Tana dariya."Daddy ya ce "Mamana me zakiyi da gida? Gyara zama tayi tare da buɗe ƙafafunta ta fara nuna musu da hannayenta tana zanawa ga kafet ɗin ta ce"Ka gani nan nice Mamu banda ƙoƙarin ALLAH ba na Boko, mallam ya zane ni amma ƙwaƙwalwata ta kasa buɗewa Daddy, Mallamin mu ya ce"Haka zan tabbata daƙiƙiya bana ganewa amma kuma ya ce min "ina da hikima wacce zata zamo jarina."To Daddy kaga tunda banda ƙoƙari da na gama makarantar ga aure zakuyi min, ni kuma kafin in yi auren nan ko...zan mallaki gidan kaina."Idan ka sai min gida zan sa masu haya, duk kuɗin da zasu biya zan sa Mommy ta ajiye min a act ɗinta idan nayi aure zan buɗe manyan shaguna irin naka, in kuma buɗe gidan ƙwalliya da gyaran jiki, ka ga ko banda zurfin ilimi ni Maryam Bello Babale ina da tarin dukiya, da wannan dukiya kuma zanyi amfani in taimaki marasa ƙarfi idan na taimake su da sannu zanyi ficen da wasu masu ilimin basuyi ba akan hakan nakeson ka sai min gida Daddy."Ba Hajiya Halima da Daddy ba hatta Zillaziya tayi mutuwar zaune da jin kalaman Mamu masu cike da ɗinbim hikima ace kamar Mamu ƴar aji biyu a sakandare da wannan tunanin?"Tafa hannayensa Daddy keyi yana murmushi ya ce"Da kyau Mamana tabbas ke jinina ce kuma ba shige kikayi ba gado kin kayi, son dogaro da kai acikin jinina yake, shiyasa nabar aiki ofis na dawo kasuwanci, ALLAH muku akbarka ya cikawa kowa burin sa na alheri, maganar sai miki gida anyi an gama kin samu uwar masu gida." Tsaye ta tashi tana kuwwa ta dinga tiƙar rawa a gaban Daddy tana na gode, na gode Dady, Hajiya Halima murmushi tayi ta dubi Zillaziya da ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta ce"Antynsu kina ganin diramar uba da ƴa?"Uhumnnnn na gani ai tayi dabara inji Zillaziya tana ƙoƙarin ɗaukar Abdul Rahman dake wasa, ta ce"Alhajina don ALLAH ka taimaka ka ɗauko min Abdul Raheem ya yi bacci...Caraf Mamu ta ce"Haba Anty ko ki tayani murna kodai cikinki ya murɗa zaki bayi? Kuma wai Daddy ya ɗauko Abdul don salon gwaɗare bani ke kai miki su ba kullum wallahi Anty kiji tsoron ALLAH." Dariya Zillaziya ta wacce tafi kuka zafi don daman ance "Da wasa da yaro gara ƙwana da yunwa." don gashi Mamu ta faɗa mata magana cikin sigar wasa don dama tana canta wasa. Amma kannewa tayi ta ce"Mamu kenan ta wajena, ai kin san bana yiwa yara baƙin ciki, Allah ya cika miki burinki." daga haka ta saɓa Abdul ta wuce Alhaji ko ɗauko ɗayan yay yabi bayanta.
Suna fita Hajiya Halima ta dinga jawa Mamu kunne, akan ta daina yiwa manyan magana kowacce iri, buɗan bakin mamu cewa tayi"Aaaah Mommy nifa naga kamar taji takaici...ki rufe min baki marar kunya sai na saitaki hankalinki inji Hajiya Halima don ta lura Zillaziya bata ji daɗin abubuwan da suka faru ba. Tashi mamu tayi fuuuu ta wuce tana wani karkace kanta gefe wai anyi fushi(ooooh mamu ciwon kan uwar ƴan mata da fatan masu ƴaƴa Maryama ba haka suke fama ba?)
Har ɗakinta ya bita sannan ya ajiye Abdul addu'oi yay ya shafa musu, sannan ya ce"Maman Twins sai da safe, kanne idonta ɗaya tayi da sigar masifa ta ce"Haba Alhaji anya zaka shiga aljanna? Kai kan ka kasan ba ai min adalci ba, duk da yaran maza rabon mai yawa ne amma baka nemi suma ka basu nasu haƙƙi ba, kamar yadda ka ba uwar ƴan mata da yaranta, nifa mota kaɗai na tsira da ita, sannan su su Abdul ɗin basu da haƙƙi ne ki meye ? Bansani ba naga kowa kayiwa abin azo a gani banda mu, kuma don tsabar rashin son a zauna lafiya ita fa ta ce"komi bata so, addu ah take so da fatan shiga aljanna kayi mata shikenan amma zaka bata zunzurutun kuɗi har rabin miliyan, to gaskiya Hajiya Babba zan faɗawa don ta ƙwato mana haƙƙin mu."Daga nan tayi shiru tana jijjiga jiki tana yi masa kallon banza.
Zillaziya bana son tashin hankali...kai ka nemeshi da kuɗinka dole ai shi ta ce"tana tunzurar baki."To yanzu su Abdul ɗinne kike ganin banyiwa adalci ba ko har da ke?"Ba sai na faɗa ba, kowa ya gyara ko ya ɓata ya sani"Ko don kaga su basu girma ba, ai ni da a uwar su nasan abubuwan da suke so don basu da baki ne, shiyasa basu iya faɗi amma idan aka basu rabonsu nasan me zan saya musu sai shaida...Shi kenan, zan basu dubu ɗari biyu sai ki sai musu abinda suke so, daman ni abinda yasa ban sako su ba naga yarane basu san komi ba, sannan duk hidimarsu ina ba da kuɗi ana yi musu shiyasa, da kike zance aba kowa rabon sa karki manta ba mutuwa nayi ba, a ina zaki san rabon kowa, sannan ni kyautata muku ne nayi don ALLAH ya ƙara buɗa min bawai rabon gado na nikeyi ba, kina maganar na ba Sadiya kuɗi ai ba roƙona tayi ba, asali ma dukiyata kinga zahiri bata dameta ba kuma bata gabanta, addu ah ta nema nayi mata ko ke kika nema zan miki, akan nayi niyyar kyautar kuɗi ko abin kuɗi ga iyalina shiyasa na bata, sannan da kinyi haƙuri ke jure kin tsaya ke ga motar da zan saya miki to bazaki wani ƙorafi akan kuɗin da na bata ba, son motar zata ninka kuɗinta da yawa. Saboda haka bana son ƙananun maganganu karki sake Hajiya taji idan kuma har kika bari ta san da maganar wallahi zan fasa sayen motar, kuma nasan bazata tilasta ni akan na sai mikin ba don haka ''Idan kunne yaji gangar jiki ta tsira."Daga nan yay tafiyarsa ya barta nan tana hasala. Hawayen da ta hana idonta zubowa ne suka dinga tsiyayowa a hannunta da ta haɗe da ƙirji wani haushi takeji a ranta tunanin take ita da ALLAH ya albarka da jarumai tushen arziki har biyu, maimako ta ƙwashi kaso mafi tsoka mai yawa, amma wai ita ce da ƙalilan? Don duk abubuwan da ƴan matan suka faɗi zasu caji kuɗaɗe masu yawa awurin Alhaji, ƙwallah ta goge tayi ƙwafa wayarta ta ɗauka ta fara danna kiran gaggawa...
idan ba comment ba post
'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍
GA MASU BUƘATAR TALLACE TALLACEN HAJOJI MUNAYI AKAN FARASHI ME SAUƘI [11/9, 8:45 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM(EWF)*
_Home of Brilliant writers forum_
LABARI
TSARAWA
RUBUTAWA
HAƘƘIN MALLAKA
'YAR MUTAN DIKKAWA😍
*Assalamu Alaikum wa Rahmatullah*
*Maata Maata Maata iyayen gida,kar ku ga laifina mutane da yawa suna kirana me ɗiya mata 😂idan suna neman books ɗina ba komai MAATA abin martabawa ne,ina Maata ƴan kasuwa ina masu online business?ko zu ga dama ta samu Akwai wani tsarin tallah ta muku hajojinku da mukeyi ta hanyar sakawa a jikin shafukan lutattafan marubutan online na hausa.*
*Hajiyata Zamu tallata miki hajarki ta hanyoyi daban daban. Za'a tallata miki a whatsapp, Wattpad, Telegram da dai sauran wuraren da books ɗinmu suke zuwa kamar su okada da bakandamiya da dai sauransu da yardar ALLAH*💪🏻💪🏻
*Saka talla ajikin shafukan litattafanmu abune mai matuƙar janyo customers gaba ɗaya africa bama Nigeria ba, a wattpad kaɗai muna da fans sama da dubu biyar*🤝🏻🤝🏻
*Hanzarta ki kawo mana hajarki kowace iri ce domin samun dubannan mutane masu siyan kayan a nahiyar africa gaba ɗaya duk akan farashi mai sauƙi*💃🏻💃🏻💃🏻.
*Domin ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan lambar.*
Whatsapp 07084161619 Call 08039424298
*Sai kunzo*💪🏻
*BABI NA 63/65*
*SADAUKARWA NEH GA MAHAIFIYATAA*
*GODIYA GA ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI TARE DA AYARIN MASOYANA MASU ƘAUNAR RUBUTU NA*
*JINIJINA GA ƳAN UWANA MARUBUTA INA GODIYA GA EXQUISITE WRITERS FORUM ALLAH YA ƘARA HAZAƘA AMEEN.*
_Bismillahir Rahmanir Raheem._
Zuwan da Uwar Daba da Zillaziya sukayi gidan mallam, ya haifar da canje-canjen rayuwar mutane da dama daga ciki kuwa har da Alhaji Bello Babale, don kuwa soyayya suke ba kama hannun yaro, Uwar Daba tayi nasarar samun hankalin Alhaji ta hanyar kira da tura saƙo, wannan yasa tayi saurin samun sa gashi kuma duk ƙulli da aka basuwa da sunan Zillaziya ashe na Uwar daba ne don ita zai ma aiki, Zillaziya ta kasance ƴar rakiya a cikin tafiyar. A gefen Hajiya Babba abubuwa da dama sun wargaje mata domin duk abinda tayiwa Sahura alƙawari sai da ta cika, duk da hakan Sahura ta mayarda ita saniyar tatsa don kullum cikin karɓar kuɗinta ta ke idan kuma ta musa mata sai ta ce"Zata tona asiri" wannan yasa Hajiya Babba ta rame, tunanin duniya yay mata yawa, ta ga ƙanwarta na ƙoƙarin taga bayan abinda ta daɗe tana tarawa.
********Karima ta samu labarin duk abubuwan da uwar daba tayi ma Zillaziya abin yay mata zafi, amma ta dangana laifin wurin Zillaziya, don da bataje tana yawon fallasa sirrinta ga ƙawaye ba da bata shiga halin damuwa amma duk da hakan ta sha alwashin sai ta ɗauki mataki akai, Safara'u ta samu malamin islamiyar su wanda ya nace akan yana sonta duk kowa na aibata, halayen Karima amma ya wanke Safara'u don ya ce"Wannan halin uwarta ne ba na uwa ba, don haka ba zai yankewa wani hukunci akan laifin wani ba, sai dai suma yana musu fatan shiriya." da taimakon Mallam Kabeer aka samo garin su Buzu a ƙasar niger har ya yi tattaki ya nemo auran Safara'u a wurin Buzu don tunda ya dawo daba Ummara ya koma, da bada baki da w'azi da komi Buzu ya biyo mallam sai dai wannan karon harda matarsa buzuwa da yaran sa biyar mata wanda suka haifa da matarsa suka zo,hankalin Karima ya tashi dawowar su Buzu da Salima don cewa tayi"Sai dai su zauna tsohon gidan su, don nan gidan ƴarta ne, amma Buzu tsaye yay a wannan karon ya jajirce ya ce"Sai dai ita tabar gidan don surukinsa ya sayi gida ba uban Karima ba, ba abinda zai hana matar sa da ɗiyansa zama a gidan, a haka Karima ta haƙura amma babu walaƙanci da zagin da batayiwa Salima, nan aka ware musu ɗakunan su suna rayuwarsu har abinci Buzu ke kawowa suna dafawa ita kuma Karima baki yabi da cin daɗi kuɗi da komai Zillaziya ke mata ita da su Tasi, zaman gidan ya fara da masifa da faɗa ba dare ba rana ita Karima ta zagi Salima da Hausa su kuma su zageta tas da buzanci, Safara'u da Tasi Allah ya sanya musu ƙaunar ƴan uwan su haka suma suma son su Safah da Tasi amma masifar Karima ta hana su zaman lafiya, duk ita Salima ba ruwanda kuma tana da kauda kai ga al amurran Karima, Zillaziya ma tana gasa su don idan ta zo yuni a gidan ba ruwanta da su komai daga ita sai ƴan uwanta in banda zagi da harara ba abinda ke haɗata da Salima ko su Airah,Nu'aimah,Faɗima,Suhaila,da kuma Su'adah kyawawa ne farare tatas kamar larabawa gashi har gadon baya gasu da jiki mai kyau dukkanin su sun zama ƴammata duk da kyaunsu har yanzu babu wacce ta kama ƙafar Salima acikin su.
Uwar Daba ta canjawa mahaifiyarta Baba gida, kasancewar ita kaɗai ce a wurin Baba shiyasa suke cin duniyar su da tsinke, tana samun kuɗi sosai a wurin Alhaji kuma da zarar ta ce masa "Bani" danƙamata kuɗi yake, a hankali ta dinga yi ƙasa da al'amuransa, babban burinta ta tara dukiya mai yawa sannan ta aure shi tana da abin kanta, duk kayan da yake sayarwa a shagunan sa tayi nasarar amsar su tana business, cikin ɗan lokaci Uwar Daba Collection yay fice don ko ina tana tura kayanta, tayi kuɗi na ban mamaki ƙamshi ce babbaar ƙawarta abokiyar cin moahe, kuma ita ce ke baibaya tana faɗawa Zillaziya komai da ke faruwa, Hajiya Haleema ta fara ganin canjin rayuwa a gidan domin komai ƙasa yakeyi gashi yanzu duk basu gane kan mai gidan addu'oin neman tsari take awurin Allah don a tunaninta wata jarrabawa ce ta same shi ta kariyar arziki, Zillaziya kam ta kusa hauka babu inda bata shiga ba ita da Karima amma Uwar Daba ta wuce sanin su, wannan ne ya haifar da danasani da nadama ta zahiri ga Zillaziya, kullum cikin kuka take da danasanin shiga group ɗin su Uwar Daba nadama take na fallasa sirrinta a media, iznah take gani na yarda da ƙawaye, a gefe kuma tana ganin har gobe aƙwai ƙawayen ƙwarai don ga Hajiya Haleema da Lababatu nan zumuncin su ya ɗaure har ƴaƴa da jikoki don Allah ya bata rabon haihuwar twins maza uku ita ma.
*BAYAN SHEKARA ASHIRIN*
Abubuwa da dama sun faru na rayuwa, wasu na farin ciki, wasun kuma na baƙin ciki, aƙwai na tsoro, firgici da takaici daga cikin su har da na samun Kariyar arziki Alhaji Bello wanda ya samu sanadin Uwar daba da irin asarorin da yay akanta a taƙaice sai da tayi masa damfara na makudan kuɗi tasa yaci bashin banki na biliyan goma, wanda akan hakan yay sanadin kamuwa da cutar hawan jini don sai da ya biya bashin, inda akarshe ta gujeshi ita ma dai bayan wasu shekaru, gobara ta tashi da agidanta cikin dare,nan ita da uwarta da komai suka nata suka ƙone, haka Hajiya Babba tsufa ya kama ga ciwon suga ya addabeta, ita ma tuni Sahura ta cinye komai nata, gashi Ɗan Inna ya samu kariyar arziki komai sun rasa, su Sahura yanzu suke taimakonta hatta gidajen nasu da manya motoci da duk ƙadarorin da suka tara an sayar Alhajin ya biya bashi, yanzu a ƙaramin gida suke zaune har Hajiya.
Hajiya Halima ta shiga tashin hankali, amma kuma da ta yarda da ƙaddara sai ta samu sarari, ga yayyenta maza duk sun ƙara samun tufin asiri suna taimaka mata sosai akan karatun su Mamu inda ma Allah ya agaza mata kafin abubuwan su ƙara lalacewa yaranta na gama karatu take sa ai musu aure har sai da akayi auren biyar a cikin su wato Dr. Zeenat, Brr.Khaleesat Engr. Bilkeesu O.c Hajaru, da kuma Saudat(Malamar jami'a ). wanda dukan su suna zaune a gidan mazajen su kuma kowaccen su tana aiki shiyasa suke ɗauke da lalurar ciwon Alhaji Bello da Hajiya Babba har ma kula da gidan duka. Mamu da Salma ne shekarar ƙarshe a jami'a inda Sareena da Saheeda ke karatun a makarantar koyon kiwon lafiya. Idan da tashin hankali a wurin Hajiya Haleema ba zai wuce Maryam ba don bata jin magana gata da ƙawayen banza kuma sam bata jin kunyar kowa bare tsoro, rayuwar mamu rayuwa ce wanda kowacce uwa ayau take fuskanta, duk da halinta ne tsiwa, amma sanadin ƙawayen banza ne rayuwarta ta lalace, Mamu ibada bata dameta ba, kullum cikin janyowa Hajiya Halima faɗa da tashin hankali take, akan Mamu hawan jini ya kama Hajiya Haleema, Mamu bata bin maza amma yawan mu'amala maza da ƙawayen banza da take yasa ake masu ɗauka ɗaya a makaranta da unguwa, kai tsaye idan har za'ayi wa Mamu fassara daidai da halinta to kai tsaye za'a kirata da ƴar iska amma kuma sanin halin mutum sai Allah, Hajiya Haleema bata burin da ya wuce ta ga Mamu ta tsayar da wanda take so acikin burguzun samarinta, wannan zai sa hankalinta da na Alhaji Bello ya ƙwanta. Saboda Mamu batajin maganar kowa yayyenta na iya ƙoƙarin su akanta amma ina tayi nisan da bata jin kira sai dai addu'a.
Zillaziya tafi kowa dana sani don sanadinta komai ya faru, tasha kuka da ƙunci haka ta sha tofin Allah tsine a wurin Hajiya Babba a lokacin da take fallasa kanta da kanta a gidan, Alhaji Bello ma yayi Allah wadai da halinta da kuma kokawa mata irinta masu fallasa sirransu ga mutanen da basu da tabbas akan su, Allah ya azurta Zillaziya da ƴaƴa Baƙwai dukan su Maza acikin su kuma Abdulrahma Abdurrahim Abdul malik da Abdul jabbar ne suka gama sakandare yayinda Abdul Basi da Abdul Hafeez ke sakandare, Zillaziya bata samu ƴah macce ba sai a ƴan shekarun baya ta haifi Karima(Ummi) taji daɗin haihuwar Ummi wacce a yanzu take da shekara huɗu, tana ji Ummi don abaya tasha gwagwarmaya da Alhaji akan kuɗin da yake kashewa ƴan mata musamman ko ga sallah komi sai an saya musu amma ita mazan daga hula takalma madubi sai agogo ake saya musu gayan tufafi, matan ko har kuɗin lalle da kitso kayan ƙwalliya, da sauran abubuwa wanda ba zasu lissafu ba, wannan tasha haɗata da kowa a gidan don yana baƙanta mata, amma samun Ummi yasa itama ta fara tutiya da macce don ana bata kuɗi duk da ba kamar yadda akayiwa yayyenta a baya bane, amma dai yafi babu.
A cikin ƴaƴan Zillaziya maza aƙwai nagari biyar aƙwai kuma maraji biyu don yadda Abdul malik ya ƙware a sata ko ɓera albarka haka shi kuma Abdul Hafeez tun yana firamare aji shidda ya haɗu da abokan banza suka koya masa shan taba haka manyansu na aikin su har ya saba da shan miyagun ƙwayoyi, yaran biyu sun addabi Zillaziya,Hajiya,da Alhaji don kullum cikin ɗauko musu magana suke ga Mamu cikon ta huɗun su. Zillaziya ta mallaki baƙinciki yaran nan biyu don hat nunata ake ana faɗin"Ga uwar mugun ɓarawo" sunan da kowa ke kiran Abdul da shi wannan yasa ta shiga tashin hankali mai yawa, sunyi kukan dare da rana tun Karima na tayata neman taimako har ita ma komai ya ƙare mata gashi yanzu batada ƙafa, watarana ta fito wurin wani malamin ƙauye ta faɗi da mashin ta ƙarye, tun sannan take zaune tana jinya Safara'u ce ke taimakonta wacce akayi aurenta da ƴan uwanta Suhaila da Airah har sun hayayyafa, Karima ta koma goro ko abin saye sai dai Hajiya Salima ta mayarta da alheri a maimakon sharri don yanzu gidan nata ne ita da yaranta duk sun auri hamshaƙan masu kuɗi kuma aunyi karatu sun waye, kowacce tana da katafaren gida da mota wasu na aiki wasu kuma kasuwanci, tuni suka ka ƙara kai Salima da Buzu makkah aka canja musu gida suka gyare ɗakin Hajiya Salima da Karima tsaf, sun taimaki Tasi yayi aure yana sana'a kuma sun kai Safara'u da shi Tasi'u makkah ko Karima don bata da ƙafa ne da a yanda rayuwarsu take zasu biya mata, Hajiya Salima sai san barka haka yaranta sun ƙara kyau da cika sun zama Hajiyoyi har Zillaziya suna taimakawa tare da tallafawa a wurin karatun su Abdul.
*********** Yaran ne ke ta faman ƙiriniya a tsakiyar falon suna wasa, a gefe wata kyakyawar dattijuwa ce ke ta faman baribari tana tuntsura dariya, Daga madafa ta fito tana dariya ta ce"Saddiq...Siddiƙa, Fahad, Aslam ku zo nan, da gudunsu sukaje inda take ta ce"kuna son idan Anty Fatima ta dawo aiki in sa ta zuba ku mota a mayarda kowa gidan su ko? Tuɓure baki Saddiƙa tayi ta ce"A'ah Mama. Sadiƙ ya ce "Mama kiyi haƙuri mun daina rigerigen, Fahad ya ce"Muje inda Umma.''Dariya Ammi tayi ta ce"Ƴannema da karku bari yanzu inyi samtunku gidajen ku, komawa tayi ta ci gaba da aikinta bata jima ba ta dawo tana gaida Umma tare da ajiye mata abinci, yaran ko a faranti ta zuba musu bismillah sukayi sannan suka fara cin abincin duk da kuciryar su amma sanin halin Ammi yasa basuyi magana ba sai da suka gama sukayi hamdala.
Da ɗan jimawa Abbu ya ƙara ƙera gida inda ya mayarda Umma gidan, saboda ƙaunar da ke tsakaninta da Ammi ko shekara basuyu ba aka aurar da Nabeela,Aysha da kuma Yaseera inda daga baya akayi na Khadija wanda dukan sun yi karatu suna aiki har sun hayayyafa ƴaƴan su ne yanzu suke rayuwa a gidan, Fatima ma ta gama karatu tana aiki da zarar miji ya fito sai zancen aure. Umma, Abbu , da Ammi sun ƙara samun hutu da ƙwanciyar hankali ga iyali sai tunbatsa sukeyi haka shekaru sunja jiki ya fara nauyi duk da haka har yanzu Ammi na tare da ɗalibanta tana ci gaba da karantarwarta suna rayuwar su a cikin jin daɗi da walwala.
*************** Alhaji Sama'ila ya zamo zakaran gwaji acikin ƴaƴan Hajiya Arziki don arzikinsa ya bunƙasa wanda a yanzu duk yafi yayyen sa kuɗi, kullum cikin samun buɗi yake sanadin addu'a da farin cikin uwa, duk da tuni yayyensa suka dawo kano amma yanzu sunyi ritaya komai ya ƙare sai ɗan abinda ba'a rasa ba, kuma tuni Hajiya Arziki ta yafe musu, amma har gobe a zuciyarta babu kamar Samaila da Safiya da kuma ƴaƴan su maza da mata shidda, ta ko'ina Hajiya Arziki ta duba jikokinta ne wanda hakan ke sata farinciki. A yanzu dai rayuwa ta miƙe mata komai ta samu ƴaƴanya maza duk sum dawo haka jikokinta na tare da ita haka Alhaji Sama'ila ya tsaya mata ga komai na rayuwarta da ta sauran ƴan uwansa da dangi sai san barka.
************** *BAYAN SHEKARA UKU*
Alhaji Bello Babale ne zaune a cikin iyalan sa tare da duk ƴaƴan sa maza da mata da jikokinsa, kasancewar dukkansu sun zo yawon sallah tare da ƴaƴansu, kallo ɗaya zakayiwa falon da jama'ar da ke cikinsa zaka fahimci kuɗi da daula tare da jin daɗi ya samu muhalli, don ba ƙarya gidan ya haɗu kamar wata masarauta haka Hajiya Babba na gefe tana jan carbi sai fatan alheri takewa Uqar ƴan mata tana sawa Ƴan matan wanda suka zamo iyaye a yanzu albarka, domin tuni tayi nadama da danasani akan abubuwan da ta aikata a baya, don gashi yanzu matan ne ɗauke da fidan, matan ne suka zamu zakaru kuma matan ne suka ɓanɓara musu gida, matan ke ciyarda da sannan da arzikin matan kowa ke tutiya agidan daga mazan har uwar tasu da ita kanta Hajiyar bare uwar gayya mai gayya uwar tafiya wato UWAR ƳAN MAATA duk da suna ƙwatantawa amma MOMMY ce sarauniya kuma wacce tafi kowa daula a gidan.
A yanzu babu kowa gabanta don anyiwa su Mamu aure tuni tayi hankali har tanada ƴaƴanta biyu kuma har su Salma da Sareena dukan su sunyi karatu suna aiki, tuni su Zeenat aka zama hamsaƙan mata ƴan kasuwa har shagunan Alhaji Bello sun maida kaya inda ƙannan su maza ke kula da komai, Mamu burinta ya cika tayi karatun da bata aza zata iya ba, don ta gane shi karatu sa kaine kuma dagiya yake so, gashi tana kasuwanci ta buɗe shaguna ita ma haka tana wuraren ƙwalliya da sauran su sai san barka, hankali ya shige ta ta nutsu ta daina halayen ta kamar ba'ayi, A halin yanzu cike da wajen nigeria ba wanda bai san sunan familyn Bello Babbale ba sanadin tsohon ɗan kasuwa ne kuma ƴaƴan sa mata ma manya ne, hakan ya ƙara ɗaga tutar gidan da zuriyar duka, Zillaziya ta saduda tabi uwar ƴan mata ita da yaranta domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki haka sun riga sunyi gaba na baya kuwa sai biyar sahu.
_TAMAT BI HAMDILLAH_
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚Allah ya yafemana kuskuren mu ya bamu ladan daidain mu Ameen sai kutareni a sabon littafina mai durmuyarda zukatan masoya coming🔜in shaa ALLAH.
ABIN LURA A CIKIN LITTAFIN UWAR ƳAN MAATA SU NE;
A DAINA ZAƁEN JINSI A WURIN HAIHUWA A DINGA ROƘON ALLAH ƳAƳA NA GARI
MU SANI DA ƊA NAMIJI DA MACE DUK ƳAƳANE KUMA KOWA YANA IƳA ƊAUKAR GIDA
HAKA KARATUN ƳAH MACCE ABU NE MAI KYAU HAKA SANA'A JIGON RAYUWA CE
ABBU NAMIJI NE YA RIƘE UMMA HAKA SU ISMAIL MAZA NE SUN RIƘE HAJIYA ARZIKI ƳAƳAN BUZU MAATA NE SUN RIƘE GIDA HAKA SU ZEENAT DUK MAATA AƘWAI MAZAN AMMA SUNE SUKA RIƘE GIDAN
NEMAN MAGANI SHIRKAH NE KUNGA IZINA GA UWAR DABA KARIMA DA HAJIYA BABBAH
AƘWAI ABUBUWAN DUBAWA DA DAMA ACIKIN LABARIN WANDA IDAN NACE IN FAYYACE SU BA ZAN IYA BA AMMA DON ALLAH A ƊAUKI ABUBUWA MASU KYAU A KUMA YI WATSI DA MARAS KYAU MU SANI ƳAƳA MAZA DA MATA DUKA RAHAMA NE ALLAH YASA MU DACE DA NAGARI AMEEN.
ƳAR MUTAN DIKKAWAR KU CE😍 [11/9, 8:45 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM(EWF)*
_Home of Brilliant writers forum_
LABARI
TSARAWA
RUBUTAWA
HAƘƘIN MALLAKA
'YAR MUTAN DIKKAWA😍
BABI NA 60/62
_Bismillahir Rahmanir Raheem._