Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 16

Uwar y'an mata complete - Chapter 16

Uwar y'an mata complete Chapter 16: Uwar y'an mata complete Chapter 16. Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na safe, Sahura ta iso gidan na yayarta…

1,671 words

Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na safe, Sahura ta iso gidan na yayarta kamar dai yadda ta alƙawarta mata jiya da sukayi waya, mai aiki ta samu a tsakiyar falon tana faman goge-gogen kayan kallo, da kujeru, sallamar da Sahura tayi ne yasa mai aikin waigowa da ƙarfi, don tana mamakin rashin neman izinin da ba'ayi ba, ganin wadda ta shigo yasa ta ajiye tsumman ƙasa ta isa gareta tana gaisheta da girmamawa, kallon ta tayi a wulaƙance ta watsar sannan ta amsa tana cewa "Hajiya Babba fa?" jikinta na rawa yayin da fargabarta ta bayyana ta bata amsa "Hajiya na ɗaki ina ga kamar tana bacci." Tsaki Sahura tayi ta ce" Bacci fa kikace? Ai yanzu ba lokacin da zata ƙwanta tayi bacci bane, waɗancan karnuka sun saka Bello gaba, suna neman hayyaƙe abinda ya tara, tun mu ma bamu wawura ba." shiru mai aikin tayi tana sauraren ƙanwar ta uwar gijiyarta, "Ke je ki, kira min Yayata...Hajiya Sahura dokar Hajiya ce, ba'a tashin ta muddin bata fito ba, ke karki raina min hankali don ma ke samu nace kije? Sahura ta ce a fusace, wato" Hajiya ba ina miki musu ba, bata bani ƙa'idar shiga in ba da izininta ba." Fuuuuu Sahura ta wuce sai dai tama kasa gane ɗakin na Hajiya don babu wani mahalukin da ta yadda ko amuncewa ya shuga ɗakinta hatta Alhaji Bello bata barin ya shiga, kusan ɗakuna biyu tana buɗewa masu kyau da tsari amma ba shi ne ba, sai da ta isa ga ɗaki na uku, maimakon ta ƙonƙwasa sai kawai ta faɗa ɗakin, jin motsin mutum ya sandarar da Hajiya Babba dake zaune tsakiyar gado ƙatuwar aƙwati cike da kuɗi ƴan naira dubu a gabanta yayin da wasu tulin kuɗin ke gefe da alama ƙara jira su take a cikin a ƙwatin,maganar Sahura ta dawo da ita daga dogon suman zaune da tayi ta ce''Hajiya Babba me zan gani?Kuɗi ne kamar tsaba a gabanki muna nema?Yanzu ke ina zaki da dukiya?Ko kuma idan kin mutu dasu za'a tisa ki ƙabari...Ke fita daga ɗakin nan inji Hajiya Babba wacce gabanta sai dukan uku uku yake, tana ƙoƙarin zuge zip ɗin aƙwatin, sauran kuɗin da basu shiga ta tisa a jikarta, sannan ta sauko daga kan gadon tana masifa" Nace ki fita idona in rufe Sahura, wato eashin kunyar da kike ma sauran ya kawo kaina? In ba rainin wayo ba ya zaku shigo min ɗaki ba salllama bare neman izini, ko an faɗa maki ana shigowa ɗakina, ita wancan sakara bata sanar miki ba? ko ɗan inna baya shigowa ɗakin nan shi da a ɗana balle ke banzar bazara ki fita tun ranki bai ɓaci ba" inji Hajiya Babba tana nunawa Sahura hanya.

Ahaaayyyehhhh nanaye Allah wadaran naka ya lalace, inji Sahura. ɗibe mayafinta tayi ta ɗaure a ƙugu tare da ƙwashe siket ɗinta ta ce"Hajiya yau ko ni ko kuma ke a ɗakin ga don wallahi tunda nigga kuɗin can,"ta nuna aƙwatin kuɗi"to kuwa sai ke bani nawa rabo ai "isan ba'a ba hali ba, sai aba ido." kinganni ina da lalurar kuɗi har firijin ɗina da nake sana'a ya lalace, na kawo miki kukana kin ƙi saimim,nace ki faɗawa Bello kin ƙi faɗa masa, nace ni in faɗi mai ke hana saboda tsabar rowa to yanzu kin ga sai ayi mai dalili...Sahura kuɗi na ƙarfi ne kizo ki ƙwata inji Hajiya a zafafe ta katse maganar Sahura." To shi kenan zaki gane don zan faɗawa ƴan uwana su sani har ba ƙauye zan basu labarin irin dukiyar da kika tara, har baki san yadda zaki da ita ba, baki sauran dunge amma kina tara dukiya don dogon buri abinda ko mutuwa kikayi mu ne zamu ci gado, kuma wallahi daga nan tafiyata zanyi ba zan rikeki wurin mallam ba yanzu ke don bakida godiyar ALLAH mai wannan kuɗin har kike son a hana Bello sakema matan sa kuɗi? har kike tunanin ki ƙara mallake shi wato saiki tara fiye ma da wannan? mu ƴan uwanki muna nema bayan kujerar hajj da me muka tsira da dukiyar? tunda ko zakkah da ƙyar kike bari ya bamu sai ɗan turmin atamfa da yadukan sallah da wata shegiyar dubu hamsin to bazata saɓo ba dole mu ɗauki mataki akan ki, mu ma musamu mu tara namu rabo...Sahura don ALLAH ki tufa min asiri, ke san halin su Tanko da Mudi da harkar jifa, karki sa su jefeni akan abin duniya haka ƴan uwan mu na ƙauye kullum cikin jifana suke da ɗan inna don kawai ina tsaye akan rayuwar mu ne, ban zauna ba yanzu idan kin faɗa masu zasu tasamu gaba kiyi haƙuri ki tufa min asiri zan baki duk abinda kike so." inji Hajiya Babba muryarta na rawa don ta karaya da zantukan Sahura. Murmushi Sahura tayi ta ce"Karki damu ƴar uwanta abinda nakeso ki canja min kayan ɗaki, asa min sabbi hul na nunawa matan layi, sannan ki sai min firijin LG da kayan kallo ki bani jari kuma duk sauran ƙannanki ki taimakawa kowa har na ƙauye ƴan uwan mu ki musu sha tara na arziki idan kinyi hakan to ke tsira daga tonon silili."Haba Sahura idan nayi haka ai kuɗin sai su ƙare ke da kika sani dai in miki...sharaɗi na ne Hajiya har sauran da basu sani ba, sai sun shaida kuma karki kuskura kice Bello ne zaiyi ko ya baki kuɗin da zaki mana hidima, da naki nake so kiyi, gasu nan na gaban ki don banga abinda zaki dasu ba, wasu ƙwallah masu zafi ta goge da sanyin murya ta ce"ina tarasu ne don gudun ɓacin rana ko da mun rasa watarana idan na tanada zasuyi amfani Sahura"Ai babu wani amfani da zasu miki sai dai su amfani malamanki Hajiya, don ke "Indararo ce" saboda haka ki yarda da maganata ko kuma in fallasa ki..."Shi kenan zanyi yadda kikace Sahura inji Hajiya. Hannu Sahura ta miƙa mata ta ce"bani ƴar dubu ɗari nan in sha ruwa a hanya."inji Sahura tana wani ɓata rai, jiki na rawa Hajiya ta ƙirga ta bata, amsa tayi ta zuge jikka tasa sannan ta ce"ni zan koma don na tuba ba zan ƙara yawon neman magani ba, kema kiji tsoron ALLAH don ba kyau kuma halal ne Bello ya kashe ma matansa dukiya haka ƴaƴa mata da maza duk abin sone sai ki karatun ta nutsu ki cirewa rayuwar ki aikin ƙiyayyar Halima da kikewa inkiya da "UWAR ƳAN MAATA" har gida zanje na roƙeta gafara na wuce sai naga aiken motar kayana." daga nan Sahura ta wuce ranta fesss

Tana fita Hajiya Babba ta kife kai tana rusar kukaaa...

******************** Sosai ta ɗauki hanya sai gudu take shararawa akan titin cike da ƙwarewa take tuƙin, tafiya take akai-akai tana duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta, bata ɗauki wani tsawon lokaci ba ta ƙaraso ƙofar gidan. Injin motar ta kashe sannan ta fito, sanye take da jallabiya kalar gold da mayafi, farin gilashi ne manne a fuskarta, hannunta riƙe da jika da takalmi masu tsini da wata irin rangwaɗa ta shiga ɗan madaidaicin gida ginin laka amma daga ciki an ɗan gyara shi, da sallama ta shiga inda ta sami wata dattijuwa tsakiyar gida tana shara, da fara'a ta amsa mata sallama tana faɗin" lale marhaba da Zullaƙaziya, ya gida?" Lafiya law Babaa." Ta ce"yaya ƴan tawaye an zama samari ko?" Eh Baba suna gaida ke inji Zillaziya. Uwar Daba ce ta fito cikin wata irin shiga ta mutunci sai ƙamshi ke tashi cingam take tauna ta manna baƙin gilashi ɗan ƙaramin mayafi riƙe a hannunta, ta ce"Hajiya Zillaziya ta gidan Alhaji Bello Babale murmushi tayi ta ce "Ya kike ?"lafiya law Zilly muje ko...Jikarta ta buɗe ta ƙirgo dubu biyar inda Babaa take tana fama busa wuta, ta nufa ta ce"Babaa ga wannan a sai goro...jikinta har rawa yake ta amsa ta ce"Na gode uwar ƴan biyu Allah yay albarka ya ƙara arziki ya raya miki yaranki ya baiwa ƴan baya damshinki.'" Ameen Zillaziya ta ce tana ƙoƙarin wucewa, Uwar daba ta dubi Babaa kana tayi mata inkiya da ido ta ce"Sai mun dawo."To Allah ya kiyaye ya baku nasara" inji Babaa.

Tafiya suka ɗiba mai nisa suna taɗi ita da uwar daba, wacce ke nunawa Zillaziya hanya har suka iso ƙofar gidan malamin, Uwar Daba ta shige gaba Zillaziya na baya har suka shiga zauren sosai suka tattauna da mallam sannan suka fito, har sun shiga mota uwar daba ta ce"ina zuwa Zilly na manta ƙamshi ta bani saƙo wurin malam" jim kaɗan bayan shigarta sai ta fito tana rufe jikarta motar ta shiga sannan suka kama hanya...

**************** Ammi ta gama shirinta tsaf na zuwa makaranta, tana rufe ƙofar gidan sai kuma wayarta ta ɗauki ƙara, murza mukulan tayi sannan ta cire, ta kaɗa jika tare da ɗauko wayarta ta ƙara a kunne "Assalamu Alaikum, Umma ina ƙwana...''Lafiya law ya gida?" Alhamdulillah Umma"inji Ammi.

Umma ta ce"Daman garin ɗan wake na gani ina son in say muku, ko aƙwai sauran wanda na aiko maki abari har ta ƙara ƙawowa?" murmushi tayi tamkar Umman na gabanta ta sanda kai tare da rage sautin muryarta ta ce"Umma ai wannan tuni ya ƙare ina batun na faɗa miki, kinsan mutanenki da son ɗan wake, don ma su Nabeela basa nan..."To ba damuwa bari a saye."Inji Umma tana dariya ta kashe wayar. Ammi sauke numfashi tayi tare da danna wayar a ƙirjinta"Alhamdulillah" ta faɗi a fili sannan ta wuce motar ta shiga inda mai gadi ya wangale mata get yana a dawo lafiya mu'uminatun mumina uwar alheri." Titin ta hau sosai ganin ta ɗan makara yasa ta dinga sharara gudu don bata son ɗalibanta na jiranta, agogon wayar ta duba wanda yay sanadiyar kaucewar ganinta batayi aune ba sai ji tayi sitarin motar ta ya kufce katuwar motar daf ɗin da ke gabanta ta buga kimis a gefen damanta da hagu napep ne "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!" shi ne kalmar da Ammi ke iya faɗi yayin da ta koma bugun wata mota....

'YAR MUTAN DIKKAWA CE

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull