Wata kishiya complete by sa'adat - Chapter 15
Wata kishiya complete by sa'adat Chapter 15: Wata kishiya complete by sa'adat Chapter 15. Jiki na rawa, ta dauki abincin data kawo masa na rana a kn…
1,268 words
Jiki na rawa, ta dauki abincin data kawo masa na rana a kn dinning, dan Tashin hankaki be batta ta dafa wani ba, ta nufa falonsa, direct ta nufa upstairs bata taba hayowa upstairs din nasa ba se yau, bin ko ina takeyi da ido, yayi kyau iya kyau amma tashin hankalin dake zuciyarta be bari ta fahimci kyaunba, tinda usman yace mata beda lafiya bata kara fahimtar jikinta ba har zuwa yanzu. Tsayawa tayi bayan ta gama hayowa saman, taga dakuma kusan hudu biyu na kallon biyu, daki na farko ta nufa nan zuciyarta ta sanar da ita yana ciki sbda a nan tafi jiyo kamshin turarensa. Knocking tayi a hnkli a bakin kofar dakin, cikin sanyin murya yace "Waye? Da bebanci tace masa "Ni ce..." Yayinda duk ta kosa tasata a ido. Jin maganarta tasashi saurin tashi zaune hadi da mata iso, yanajin wani kwari na ziyartarsa daga jiya zuwa yau duk yabi ya rame ainun kmr yayi ciwon 1week, ga ciwo nacinsa kuma yakishan maganin arziki se jiya dayaji wuta iya wuta shine usman ya kira usman ya bashi drink a frij yasha paracetamol. . Turo kofar dakin tayi ta shigo idanuwanta da nasa suka sarke da juna, nan take tausayinsa ya lullube zuciyarta, ta zubo masa ido kmr yadda shima ya zubo mata nasa sexy eyes din, yana mejin wani sanyi daya ganta, nan take 50% din ciwonsa tini duk ya ragu. Ganin yadda ya rame daga jiya zuwa yau yasata jin hawaye sun cika mata ido duk yabi ya chanza dagani yasha wahala,, cikin hanzari ta karaso ta ajiyr trea din a bedside, ta tsugunna ta gaidasa hadi da tambayarsa ya jiki..." Da sauki ya amsa...' idonsa na knta, tini ya hango taruwan kwallah a cikin idanuwan nata. "Tashi ki zauna gefen bed ki zuba min abinci inci.." Ya fadi da muryarsa a ta masu ciwo. Ba musu ta zauna Kn bed din , amma sede taki yadda ta kara kallonsa danta tabbatar inta matsa a kallonsa tana iya fashewa da kuka. Serving dinsa tayi da abinci mara nauyi (dafa dukan taliya wadda taji kayan lambu) da perper fishi din data dafa masa, ya amsa, ya ajiye a kan cinyoyinsa idanuwansa na knta, wallahi ganinta ba kamaramin haifar masa da karfi yayi a jikinsa ba, amma ya narke yace ''ki bani a baki...'' Dagowa tayi ta kallesa ta zaro ido,, dan ita seya koma mata kmr wani baby. ya kara marairaicewa dan gudun kada tace aah yace "Kinga fa banda lafiya tin jiya ban iya komi dan Allah knji yarinyata..." Se tausansa ya kara ratsata, sannan sunan daya kirata dashi na Yarinyata yayi tasiri a ranta. tasowa tayi ta matso kusa dashi ta zauna ta fara basa abinci a bakin, ya amshe, se bin fararen yatsunta yakeyi da ido, yanaji kmr ya kamosu ya hau tsotso, seda yaci abincin ya koshi duk tana bashi a baki yaci sosai, sbda rabonsa da abinci tin shekaran jiya, nan ya danji karfi ya fara zuwan masa, Dan tini yayi rabin warkewa da ganinta, sede fa akwai babbar jinya a zuciyarsa, wadda besan da ita ba. ta miko masa drink a hannunsa, yaki amsa yace shima sede ta bashi a baki, bashi tayi yasha ya koshi, ya koma ya jingina bayansa da fuskar gadon yana kallonta, jinsa yakeyi kmr wani baby yau,. Tashi tayi ta dauki trea din ta masa Allah ya kara sauki, sam beso ta tafi ba amma beda yadda zeyi dan haka yace "Ki kawomin furar rufaida a frij anjima zuwa 10:pm ..." Al-muqri'ah tace toh hadi da ficewa a dakin yabi bayanta da ido, dabadan dauriya ba wallahi da babu abinda ze hanashi rungumarta a dakinnan yau, dan wani abu ke jansa a kn yarinyar., tashi yayi ya dauro alwala domin zuwa lokacin anyi isha'i yayi sallar isha'in ya idar ya koma ya kwanta se kallon agogon dakin yakeyi, duk yabi ya kosa 10:pm tayi ya sake ganinta. 10:pm dai-dai ta iso kofar dakin tayi knocking yace ta shigo dan yasan ita ce, hannunta rike da trea tashigo dakin, ya zubo mata ido a wannan karan kai kace yau yasaba ganinta gaidasa tayi hadi da masa ya jiki ya amsa cikin murnan ganinta,. ta ajiye trea din hannunta a bedside inda ta ajiye na dazu, ta zauna kasan dakin yace "aah banso ki zauna a kasa ki dawo kan bed dina ki zauna..." Ta taso ta dawo gefen bed din ta zauna, tana kallon gefe, kyar ya kurawa gefen face dinta ido, dai-dai saitin dimple dinta yaji kmr yasa mata harshe ya tsotsi gurin amma ya danne, ya rasa meke dibarsa a kn yarinyar, yake irin wadannan tunani tunanin dabe saba irinsu ba.. Da bebanci tace masa yasha furar..." Yace "aah baze sha ba ya koshi amma zesha anjima..." Daman badan yasha furar yace ta kawo masa ba, kawai dan yanaso yayita ganinta ne,, ya zaunar da ita yanata kallo har 12:am kana ya batta ta tafi badan yaso ba, da tunanin rashin lafiyar tasa ta kwana a ranta, tasan yanajin jiki, kawai danta fuskanci yanada dauriya ne ainun. Washe gari ma haka ta wuni tana ziryar dakinsa, tana basa abinci a baki yana ci kadan-kadan yau yakeci ba kamar jiya ba. Yauma da daddaren riketa yayi har daya na dare. Ta tashi zata tafi ya riko mata yatsun hannunta na dama.... Wani irin shocking me ratsa gangar jiki ne ya ziyarcesu a lokaci guda musammanma shi gogan,, duk seda jikinsu ya amshi bakon yanayi, ya kara rike hannun nata gam a cikin nasa wani irin laushin dadih na ratsashi be taba rike hannun mace me laushin nata ba, abinda yaji a jikinsa baze misaltuba,harshe baze iya kwatanta abinda yaji a rike hannun nata ba, amma fa yaji ni"ima ta ratsashi hadi da nutsuwa a lokaci guda. A bangaren al-muqri'ah seda ta sauke ajiyar zuciya so takeyi ta kwace hannunta a cikin nasa saboda abinda takeji a jikinta, bako ne bata taba jinsa ba se yau, shiyasa ta gaza rikewa, danma ta daure, zata iya rantsewa wani namiji be taba tabata ba se yau, Shine namiji na farko da hannunsa ya fara zuwa cikin hannunta, ba d'ana mijin daya taba kusanto jikinta seshi, shiyasa hatta da kwakwalwar knta seda ta amsa. Kokarin kwace hannunta a cikin nasa ta shigayi amma kash! Duk yadda taso ta kwace hannunta a cikin nasa ta gaza yin hakan, sbda rikon daya mata ba dan kadan bane. Idanuwanta ta zuba masa taga shima itan yake kallo nan take ta Fahimci idanuwansa duk sun bi sun kara narkewa, saboda wani irin abu dayakeji yana masa yawo a cikin kwaryar mararsa....sunfi karfin 10mnt a haka se kara matse mata hannu yakeyi a cikin nasa, ganin yanata matse mata hannu har ta d'an farajin zafi yasata sake kokrin kwace hannunta a cikin nasa a karo na biyu, wannan karanma gazawa tayi, rikon daya mata yafi na farko, dan hk ta hakura. Ajiyar zuciya ya sauke hadi da lumshe idanuwansa ya budesu a knta, yayinda idonsa da nata suka hade cikin na juna, nan taga idanuwan nasa sun kara narkewa fin dazu.. "Pls ki kwana a nan knga banda lafiya kar in mutu kafin safiya dan Allah ...." Yayi maganar cikin magiya hadi da kara narkewa dan gani yakeyi in ta bar dakin ze iya mutuwa kafin safiya, sbda tunaninta, ya tabbatar da in yana ganinta ciwon jikinsa zefi masa sauki..
*Wad'anda suka Biya VIP zasu jini da daddare insha Allahu.... Ranar friday da saturday bana posting pls*
Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card.
SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah)