Kenza eBookz

Wata kishiya complete by sa'adat - Chapter 19

Wata kishiya complete by sa'adat - Chapter 19

Wata kishiya complete by sa'adat Chapter 19: Wata kishiya complete by sa'adat Chapter 19. Turo kofar dakin yayi ya shigo jikinsa har yana rawa ya kagara…

3,338 words

Turo kofar dakin yayi ya shigo jikinsa har yana rawa ya kagara yasata a idanuwansa, ko ze samu kwanciyar hankali,. Kamshin turarensa ya doki hancinta yayinda tayi saurin dago idanuwansa ta zuba masa su, ji taji zuciyarta tayi mummunar harbawa, taga shi ma itan ya zubowa ido, daga jiya zuwa yau har ta rame, amma fa yafita rama,. Ganinta yasashi nan da nan yaji tausanta ya kuma lullubesa,, a bangaren al-muqri'ah kuwa ganinsa seya tunasar da ita abinda ya faru tsakaninsu na duwawuknta da yayita matsa mata su, gashinan har yanzu ciwo ma suke ta mata, saurin kauda fuskarta tayi gefe, tanajin kmr yanzu abinda ya faru tsakaninsu ya faru. "Yarinyata..." Abdoljalal ya fadi ba kunya ba tsoron Allahn duwawuknta daya gama mammatsawa amma wai yanzu yake cewa wani yarinyata. Ta dago ta sake kallonsa , seta dauke idanuwanta, Abdoljalal ya bita da kallon kewarta da yayi, yayin da the more yake kallonta the more zuciyarsa ke tsananta bugu a knta. Karasowa yayi hadi da sosa keya danya fuskamci har yanzu fushi takeyi dashi. Ya zauna kusa da ita gefen bed din yana zama tayi zumbur ta mike, ta koma can bedside ta zauna, se kumbura fuska takeyi.. Abdoljalal de ya bita da ido. "Ya jikinki yarinyata..." Ya tambaya fuska cike da damuwa. Tajisa amma ta masa banza, ya kureta da ido kmr maye duk tabi ta zurma kmr tayi 100days tana ciwo., dawo da idanuwa sa yayi yabi dakin da kallo, har zuwa kan bed dinta, idanuwansa suka sauka a kan wayarta da hajiya saude ta bata sanda aka kawota.. Hannunsa har yana rawa ya kai ya dauki wayar, direct contact ya shiga yaga number guda biyu ne kawai, da number dinsa dana hajiya saude, ya shiga miss call yaga ba a taba kiran wayar bama, ya sauke ajiyar zuciya da har kishi ya motsa masa, yasha ko waya take tayi da maza, se Allah ya rufa mata asiri. Cewarsa. Dealing number dinsa daya gani a wayar yayi yaji akwai card, kiran na shiga ya kashe wayar yayi message ta yadda ze gane lambarta ce, kana ya ajiye wayar inda ya dauketa duk tana kallonsa, yana ajiye wayar ya dago ya zubo mata ido, tayi hanzarin dauke idonta a knsa, ya karasa ya taba jikinta, yaji wani irin zafi rau, jin ya taba mata jiki tayi hanzarin mikewa ta nufa toilet ta kulle yabi duwawuknta da kallo, mikewa yayi ya nufo toilet din danya fahimci ma kamar duk ta tsaneshi ne ne ynzu. Tsayawa yayi a kofar toilet din yayi juyin duniya ta fito suje asibiti amma taki fitowa, har wuraren 2:am yana nan yana dakin amma taki fitowa dole ya fice ya bar mata dakin, tanajin ya fice ta fito ta kulle dakin ta koma ta kwanta tanajin kanta na mata azabar ciwo, dukda tanajin haushinsa amma ganinsa ya haifar mata dajin sanyi a ranta....

Haka ya jera 1week yana ziryar dakin, wani lokaci ya sameshi a bude wani lokaci a kulle, tinda ta gane ma, yana zuwa take rufe dakinta, inyazo yayita juyin duniya ta bude amma taki budewa har yanzu fushi takeyi dashi ga zazzabi tana fama dashi, duk tabi tasashi a usumar rayuwa, sati daya be gantaba ji yakeyi kmr ze haukace, kansa ya dauki zafi yana tafiya yana layi, kmr mahaukaci haka yake jinsa a kwanakinnan, ko abincima ya dena ci. Ya shiga damuwa harya gaji da damuwa... Ko abincinma ta dena fitowa dafa masa, yasan duk sanadin matsa duwawune da yayi, gashi ansashi ababbar bala'i kwata-kwata ko bacci beyi, kwana yakeyi yana kwallar tashin hankali, be taba tabbatar da meye matsifar duniya ba se akan yarinyar nan, sam shi besanma tashin hankali ba se a knta. 10;pm yazo ya tsaya a bakin kofar dakin nata, yaci saarh yana taba handle din dakin nan take dakin ya bude, seda ya sauke ajiyar zuciya ya sako kai cikin daki da sauri kmr an jefosa, idanuwansa suka sauka a kan larai dake zaune gefen bed din ita kuma al-muqri'ah tana kwance ta lullube rub, har kanta da bargo, ganinsa a dakin yasa larai a mamaki, ta tsugunna ta gaidasa ya amsa, amma hankalinsa na kan al-muqri'ah, karasowa yayi, ya yaye mata bargon data lullube dashi, wani irin zafi da tiririn dake jikinta ya dokeshi,. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Ya hau salallami cikin tsananin tashin hankalin dabe taba shiga kwatan kwacinsa ba se yau,, ya zuba ma kyakyawar fuskarta ido, duk tabi ta karayin haske amma ta rame sosai, idanuwanta a kulle suke amma taji shigowarsa har zuwansa kanta duk tanaji bata bude idontaba. Jikinsa har yana rawa ya fice a dakin ya nufa side dinsa cikin gudu gudu, ya dakko car key dinsa, ya isa packing space da knsa ya dakko mota zuwa kofar dakin yarinyar, duk ma'aikatan gidan sun shiga mamakin ganin saraki da kansa yau yake driving, abinda wasu basu taba gani ba se yau, shi sam baya tukin mota sede a tukashi. Yana ajiye motar a saitin kofar dakin ya fito cikin tashin hankali, Da knshi ya tasheta zaune ya bata takalmi tasa, ba tare data masa musu ba, larai dake tsaye tana kallon munafunci da kwa-kwaf ganin gogan na niyar ya kamota yasata Saurin kamota cikin hanzari dantaji yana cewa asibiti zasuje. Laraice ta kamo masa ita har cikin motar, ta shigar da ita mazaunin gaba, duk jikinta yayi lagwa lagwa zazzabi ya karar mata da karfin jikinta. Abdoljalal ya shiga yaja motar suka fice a gidan. Nan larai ta tsaya bakin kofar dakin, tana mamakin wai Saraki ne yau da daukar me aiki a motarsa. "Tabbas da wata a kasa..." Larai ta fadi a bayyane hadi da rike haba, tin a fuskar gogan ta fuskanci abubuwa dayawa a kan yarinyar ammafa sede maganar nan bazata fito fili ba, wane mutum wane aikinsa.

Se hakuri da typing error ba editing.

Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card.

SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah)

Page15 Tirkashi! Nan fa Ma'aikatan gidan suka rikece da gulma ammafa gulma ta zuciya domin wannan magana bazata faso fili ba, kowa sede yasawa bakinsa linzami, laf ma'aikatan gidan na cike da alhini amma ga iya wada'da suka gani, ko labari kowa ya kasa bawa dan uwansa saboda kada kace kai nace, ammafa alhini be barsu ba, dan a tsawon shekarun aikinsu a gidan basu taba ganin saraki ya dauki me aiki ba a motarsa, sun kula asibiti ze kaita, domin tin bata da lafiya larai tazo ta shafa musu labarin bata da lafiyar, amma fa yanzu bataso tace dasu komi ba, sede tayi wucewarta ta koma bakin aikinta a zuciya kadai taketa juya lamarin amma harshenta baze iya tattauna maganar da kowa ba,. "Wace ni bakina kanin kafata..." Larai ta fadi a zuciyarta tana meci gaba da aikin gabanta.

Yana driving yana kallonta cike da tausayawa, yayinda hankalinsa kwata-kwata Be jikinsa, zuciyarsa na kanta, se rawar sanyi takeyi har zuwa lokacin. Karatun alqur'ani yasa a cikin motar, saboda duk zafin ciwo inde za asa karatun alqur'ani me girma a kusa dame ciwon insha Allahi ze samu sassaucin ubangiji. Da temakon Allah kawai ya isa wani dankareren private hospital wanda yafi kusa dashi, ko kusa be tinkari zuwa asibitin dr mus'ab ba saboda yaanada nisa.. Packing kawai yayi ya fito ,ya bude mazaunin datake, yana niyar daukanta cik ta sakko da knta, cikin dakiya ya kamo mata hannu, ta kwace hannunta, asibitinma dabadan ciwo ya addabetaba da bazata zoba wallahi kawai bata da choice ne. Kaf mutane suka zubowa Al-muqri'ah ido dukda tana cikin ciwo amma se kallonta akeyi saboda tsananin kyaunta Abdoljalal se hade girar sama data kasa yakeyi, bakin ciki ya cikasa,. A jere suke tafiya shida ita Abdoljalal se kallonta yakeyi, yanata wani kakkareta, dukda darene amma asibitin nada yalwar haske kai kace rana ce, hakan ne ya bawa masu kallonta damar kallonta. "Sannu Allah baki lafiya..." Ya fadi kmr zeyi kuka yayin da yakeji kamar ya ciro ciwon yasa a jikinsa, jinyarta tafi masa zafi a zuciya a kan tasa jinyar, da ana cirewa daya ciro ya hada da nasa ciwon.. Ba bata lokaci sukaga dr a asibitin, Abdoljalal yace dr mace suke bukatar gani, dole kuwa dr macen al-muqri'ah tagani, ba wani lalata lokaci aka mata gwaje-gwaje nan ana gano maleria ce, da ulcer. Nan take aka basu gado, aka shiga bata temakon gaggawa, aka mata allurori ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita akasa mata drib. Abdoljalal dake zaune kn kujera yana facing dinta, tausanta dukya rufesa, ansha gwagwarmaya da ita kafin ta tsaya aka mata allura besan matsoraciya bace se yau, da kyar ya riketa ta yadda aka mata allurorin, ance fararen mata basu da kwari, ita de kyakyau take tanada karfi danshi kansa dabadan yanada karfinfa da yau baze iya riketaba. Sosai ya kurewa kyakyawar fuskarta da ido, yayin da santa ke yawaita a birnin zuciyarsa, se numfashi take saukewa na rashin lafiya.... Har wuraren 12:2am yana zaune yana kallonta, kana daga bisani ya mike yaje ya kira wata nurse yace ta kular masa da ita, zeje ya dawo...." nurse Munirat tace toh sir..." se wani kwarkwasa take masa tana jujjuya rigiza rigiza din nonuwa kmr jarkoki, da uban duwawuka abin de ba tsari, kmr a kifeta da kwano, ko kallo bata isa Abdoljalal ba, shi besanma tanayi ba, a duniya mace daya ya taba gani yaji sha'awarta ta fitar hankali itace al-muqri'ah, kuma yasan itace last...

Bayan ya fito harabar asibitin ya shiga Motarsa yaja ya fice a asibitin, yana tafe yana mamakin wai yau shine Ya fita shi kadai ba tsaro, kuma da motarsa, shi da kansa yasan yana cikin hatsari amma fa se yanzu ya fahimci hakan, dazu be fahimta ba, saboda be cikin nutsuwa amma yanzu nutsuwa ta fara kusantoshi, adduarh yashigayi na neman kariyar ubangiji.... Direct babban kayataccen restaurant ya nufa ya siya abinci kala hudi, da farfesu kala biyar, akasa mishi a mota,,,, yaja motar ya karasa super market ya Shiga yayi mata siye-siyen abubuwa Da dama na makulashe,, ya koma bangaren kayayyakin sawa, ya siya mata abaya kusan kaloli asirin, se hijjabs masu kyau na kamfani, kala ashirin duma, da breziya danya kula kullum yawo takeyi ziryarta ba breziya, bata killace wadannan nonuwan shiyasa ya siyo kata bra danta dinga killacesu. Yase musu duk wani abu dazasu bukata. Bayan ya biya Aka kwashe masa kayayyakin akasa masa a mota, yayima wadanda suka kawo masa kayan motar ihsani kana yaja motar ya bar harabar mall din ya nufa asibitin duk yabi ya kosa ya isa yasata a idanuwansa ko zeji kuma jin dadih, hatta numfashinta datake saukewa ji yakeyi kamar a zuciyarsa take sauke numfashin, ta riga ta jima da zama jijiyoyi masu amfani a jikinsa. "Ina sanki...." Ya fadi yana driving amma ji yakeyi kmr yana gabanta, seda ya saki murmushin nishadi. Yana isa asibitin ya fito ya fara kwaso kayayyakin motar ya fiddosu waje, a guje securities din dake gadin asibitin suka iso suka kwashe kayan daya firfito dasu , ya musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da ita, suka shigo suka ajiye kayayyakin suma ya nusu ihsani, suka amsa suka masa godiya suka juya abinsu, daman basu shigo ba a bakin kofar dakin suka tsaya, shi ya karaso da kayan cikin dakin. Karasowa yayi bakin gadon idanuwansa na kanta, har zuwa wannan lokacin bacci takeyi sosai se sauke numfarfashi kawai takeyi na bacci. Munirat dake zaune kn kujerar dake fuskartar Al-muqri'ah , se kallon al-muqri'ah takeyi tana yabawa da halittar da Allah yama yarinyar. Tana ganin Abdoljalal ya dawo ta wani fara kwarkwasa, ta zubo masa ido tin shigowarsa. "Ya jikin nata bata farka ba kou?'' Abdoljalal ya tambayi munirat idanuwansa na kn al-muqri'ah. "A, bata farka ba sir ,,,jikin nata da sauki a hankali zata warware duka insha Allahu. ..." Munirat ta fadi tana ta wani sanabe. Abdoljalal ya mata godiya, ya sallameta ya bata kudade 30k ta amshe se godiya takeyi ta fita zuciyarta fal farin ciki nan ta kara fadawa san guy din, dan dagani yanada danshi a hannunsa, ita danshinne ke janta.

Zaunawa yayi inda munirat ta tashi, ya kara kureta da ido, numfashinta nata fita a hankali a hankali dagani yasan tana jin jiki,. Muaahhh!! Ya karasa ya manna mata kiss a kumatunta saboda ji yayi kawai wani abu na fusgarsa a zuciyarsa game da ita. Bata farkaba se 1:30am ,ta farka da salati a bakinta, ta bude idanuwanta a kansa, taga shima itan yake kallo, haka kawai taji wani abu na ratsata me wuyar misaltuwa, in har taganshi se zuciyarta ta amshi wani irin sako da batasan wanne neba. "Sannu ya jikin naki ?'' Ta amsa da "Dasauki..." Da bebanci,,, yayi mamakin yadda ta amsa wato de yaga alamar ta fara sakkowa, daga uban fushin da akeyi dashi. Tashi yayi ya nufa toilet ya dakko wata roba sabuwa dal domin komi na asibitin tsaf yake, ya dakko ruwa a cikin kayayykin daya siyo, ya bata ta kuskure bakinta, ta zuba a robar yaje ya zubar kana ya dawo ya dakko abinci ya bata taci kadan, danma yanata lallabata kmr kwai. ya dakko maganungunan dasuka bada sukace a bata inta farka taci abinci, ya bata maganin ta kauda kai, nan ma ya fahimci har maganin ma bataso kenan. Lallabata yayi da kyar ta amsa tasha, se binsa takeyi da ido, yanata dawainiya da ita, wani abu ta dingaji a game dashi a zuciyarta, saboda dawainiyar dayakeyi da ita se taji ma ya bata tausayin da batasan dalilinsaba. "Kin yafemin pls?'' Ya fadi hadi da marairaicewa yayinda yake zaune yana kallonta. Daga masa kai tayi alamar Eh.... Ajiyar zuciya ya sauke na zallar farin cikin ya fara shawo knta tinda harta yafe masa... 2:30am ta koma bacci, shikam gogan be rintsa ba, se aikin kallonta kawai yakeyi har asubahi yayi sallah, bayan drib dinta ya kare ya cire mata. Itama tashi tayi tana mejin karfi a jikinta, ba kamar jiya ba, ta kalleshi yana kn dadduma ta nufa toilet, Tana shiga toilet din ta ganshi tsaf tsaf da sababbin brush. brush din tayi, taga komi sabo ne na bukatuwar toilet din, ga ruwan zafi, dan haka wanka tayi ta maida kayan jikinta ta dauro alwala ta fito taga benan, a dakin, taga ya ajiye mata kaya a kn gadon asibitin ta duba taga abaya ce da hijjabi, dauka tayi tasa ba karamin amsarta kayan sukayi ba musammanma hijjabin ya matukar mata kyau, ya amsheta ainun kalar abayar maroon ce, se hijjabin milk color ne, ita knta kayan sun mata kyau, se godiya take masa a zuciya. Ta nufa dadduma tayi sallah ta taso ta zauna gefen bed din kenan,dr da nurses suka shigo har zuwa lokacin be dawo ba yaje gida ne dan yayi wanka ya dakko wayoyinsa, jiya rudu be barshi ya dakko wayoyin nasa ba, kuma yasan dole ne za a nemeshi a wayoyinnasa. Dr ta dubata sosai ta mayar mata da wani drib din da allurori a ciki dan tin jiya gogan yace kawai kar a sake mata allura a jiki sede a zuba mata a drip in zeyu dr tace bakomai, suna gama mata abinda zasu mata suka fice a dakin, sunata yabawa da kyaunta hatta dr seda ta yaba da kyaun nata.

Al-muqri'ah ta koma ta kwanta tanata Allah Allah ya dawo, dan tsoro ma takeji ya tafi ya barta ita kadai,. Dr din da nurses basu jima da fita ba ya dawo sanye da manyan kaya na Alfarma wadanda suka amshi launinin jikinsa ga kamshi yanata zubawa tako ina,. Dagowa tayi ta kalleshi shima itan yake kallo ba karamin tsananin kyau ta masa ba, hijjabin ya amsheta ainun,. Ita knta taga kyaunsa sosai, daman deshi me kyaune ta fahimci hakan tin ganinta dashi na farko. Karasowa yayi hannunsa rikeda ledoji ya ajiye yana fadin "Me kyauna knyi kyau sosai...." Murmushi ta sakar masa, hadi da masa godiya tace shima yayi kyau da bebanci... Abdoljalal ya karaso ya zauna cikin nishadi da farin ciki,, shima ya mata godiyar kyaun datace yayi.. Ya kalli hannunta yaga an maida mata wani drib din se yanzu ma ya lura saboda hankalinsa na kanta be kula ba sam "dr ya shigo ne?''Abdoljalal ya tambayeta. Al-muqri'ah ta amsa da "A..." Yace "Okay ya kikejin jikin dasauki!'' Ta daga masa kai alamar eh , yace "Allah ya kara sauki..." Ta amsa da amin, duk suka sakarwa junansu murmushi a lokaci guda. ... Wata iriyar kulawa yake bata ta musamman a zamansu a asibitin, hadi da tattali, da zallar kimar mutumcin SO, yabi ya maidata wata narkakkiya se narke masa takeyi,. satinsu daya aka sallamesu suka koma gida, ma'aikatan gidan duk suka zuba ido, gulma ajali in ba ayi ba a mutu, amma fa wannan gulmar sede gani kawai. seda duk suka gwale ido sukaga komi.... Har dakinta ya rakata ya kwashi kayayyakin daya siyo mata danya mata sabon shopping. ya kai kayayyakin dakinta da kanshi ya hanata daukar komi ma'aikatan gidan na kallo a kan idansu akayi komi, tantiri kam ai baki da jiki tini duk suka mutu, amma shifa yasawa ranshi kawai tausayintane yasa oga keyi mata hakan, danshi yanada tausayi shiyasa yake bata kulawar nan, amma fa dukda haka kulawar tayi yawa,... " tantiri ya fadi a zuciyarsa, amma fa har yanzu yana cikin kwad'ayin yarinyar, kuma shi inde miyaunsa ya tsinke tabbas seya maida yawu.

Al-muqri'ah ta masa godiya, bayan ya gama kwaso kayayyakin suna zaune gefen bed shida ita, amma sunada dan tazara da juna, duk yadda ya kaiga jin sha'awarta har suka gama zaman asibitin ko tabata beyi ba, dukda yana azabtuwa amma haka nan yake jurewa da matsewa yake maida kwad'ayinsa, amma fa duwawu nashan kallo. Abdoljalal ya kureta da ido sam be gajiya da kallonta, har wata kiba tayi na kulawar daya dinga bata a asibitin tayi fresh wahalalhalun rayuwar dake tattare da ita suka fara gushewa tini zallar kyaunta harya fara bayyana, kasannan nata ya kara cika fam wato duwawukanta, sun kara bayyana, ta kara yin kyau da ita, takai mace ta riga ta kama kasa. Godiya ta masa na hidimar daya dingayi da ita a asibitin kanta na kasa. "Banasan kinamin godiya ai rance na baki zaki biyani nan bada jimawa ba....." Abdoljalal ya fadi yana wani karewa jikinta kallo kasa-kasa. Al-muqri'ah ta dago ta tsuresa da ido, jin yace wai zata biyashi... "Ni ai banda abinda zan biyaka..." Ta fadi hakan da bebanci. Abdoljalal yayi murmushi yace "Kinadashi mana ..." Al-muqri'ah tayi jim kana tace "ina yake?'' Da bebanci. Abdoljalal yace "in kika kara samun sauki zan nuna miki inda yake..." Al-muqri'ah tayi shiru hadi da shiga nazari tace " aah ya gaya mata yanzu..." Abdoljalal yaki yace "Me kikeci na bakinki na zuba,, in kika kara samun sauki zan nuna miki ai zaki biyani kou? Tinda kinada kayayyakin biya sama da kasa..., gana tsakiyama duk kinadashi. ....'' Al-muqri'ah da bata fahimci me yake nufi ba tace masa ehh zata biyashi..... Tashi Abdoljalal yayi da niyar barin dakin yace ta huta kuma karta ci gaba da dafa masa abinci ta bari se ta kara samun sauki..... Yace kuma ta dinga fesa maganin sauro na fesawar daya siyo... Al-muqri'ah tace toh ta kuma masa godiya, Abdoljalal yace "Zaki biya ai...." Al-muqri'ah ta daga masa kai alamar toh... Abdoljalal ya fice a dakin zuwa side dinsa samshi ko abinci beci dukya rame inyana ganinta sam bejin yunwa. A zamansu a asibitin al-muqri'ah ta fahimci Abdoljalal mutumin kirki ne kuma shakuwa ta kara shiga tsakaninsu me tsanani , ta faraji a zuciyarta zuwa yanzu ba abinda bazata iya ma Abban nata ba, danta faranta masa, kome ma zatayi masa tasan bazata biyashi ba, dawainiyar daya dingayi da ita a asibitin har kayanta ya dinga wanke mata abinda be tabayi ba, ko kayansa be taba wankewa ba tinda yazo dunita sede boxes kadai yake wankewa kansa, amma ita kullum data cire kaya ze wanke a zamansu a asibitin.. Al-muqri'ah ta kuma fadawa kogin soyayyar Abdoljalal ba tare data sani ba, amma ita knta ta afka kogin da yake ciki tsundum ya koyar da ita sanshi kuma tini ta dauka.

Readers Also Read