Kenza eBookz

Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt - Chapter 17

Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt - Chapter 17

Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt Chapter 17: Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt Chapter 17. Anutse yusuf yashigo parlourn"yana sanye da suit farare…

1,901 words

Anutse yusuf yashigo parlourn"yana sanye da suit farare k'al"sajensa yasha gyara"fuskarsa shimfid'e da tattausan murmushi"yanata zuba k'amshi"maryam tabishi da ido"sonsa da k'aunarsa na nunkuwa aranta"da tsantsar kishinsa.....sweet heart har kun gama shiryawa?"yafad'a yana kafe maryam da ido"jiyakeyi kamar ya mannata da jikinsa"mungama broth"sannu da zuwa"yauwa to kutashi muje ko?"yafad'a yana satar kallon mama dake kallon TV"mama sannu da gida"yauwa"dan Allah ku kulamun da yarinya"karku barta tana kuka yusuf"idan kunyi hak'uri da anyayeta zan maidota anan"Allah yasa ku haihu da yawa karku biyoni agun haihuwa"sosai maryam taji tausayin mama"karki damu mama"insha Allah zamu haihu da yawa"Allah yasa to"ayita hak'uri da halin zaman yau da kullum dan Allah"Allah yayimuku albarka yatsareku dg sharrin abink'i"ku kula da azkhar yusuf"dukda nasan bakwa wasa"addu'a takobin muminice"insha Allah mamanmu"cewar yusuf yana dariya"kuje gun ummanku da hjy kuyi masu sallama"dato suka amsa"ya amshi troley d'in maryam suka fito"bayan sun je gun umma da hjy"wacce ke kwance ,suka shige sabuwar motar Yusuf....bayan yabawa motar wuta yakalli maryam yace". uk'uty amaryar broth"harda zolaya ko?"eh mana"koke ba amaryar bace?"Eh mana"hmmm idan muka koma zakiga ba haka bane"broth ina zamuje wai?"gidanki mana"ai ba hanyar bane"okay sak'o zamu amsa ai"dato ta amsa tana kallon little"broth yarinyar nan dakai take kama"ai gara tabiyo dadynta uk'uty"kinga alamar nafiki bada himma ko?"yafad'a yana kashe mata ido"murmushi kawai tayi"aranta tana mamakin meye zasujeyi a anguwar malali?"horn yusuf yayi abakin get d'in wani katafaren had'add'an gida"wow masha Allah! tafad'a tana kallon gidan time d'in da aka bud'e get"parking yusuf yayi yana murmushi"sbd ganin alamar maryam na santin gidan"atare suka fito tana kallon haraban gidan"amamakinta taga sabuwar motar tata da yusuf yasiya mata"broth wai.....shiiit!muje kawai kedai"yafad'a yana rungumota jikinsa suka wuce interest d'in shiga gidan....a main parlou suka shigo"k'aton photo d'in maryam da yusuf yarik'e babyn suna dariya"shine akayi babba kamar suyi mgn aka lik'a jikin bango"kwantar da little dake bacci kan kujera maryam tayi,kafin ta yiwa yusuf kallon tambaya"yana murmushi ya rungumeta ta baya yace".wannan shine sabon gidanki my mero y'ar bak'a ta"da hanzari ta juyo tana ihun murna ta ruk'unk'umesa......sai kuka da hawaye"kuka kuma ukuty"yafad'a yana d'ago kanta dg jikinsa"taya bazanyi kukan farin ciki ba broth?"ka inganta rayuwata"ka d'aga darajata"ka nunawa duniya nima macece"inama ace haka sauran maza keyiwa matansu halacci"dan Allah broth duk rintsi karka rabu dani....yana kallonta ido cikin ido yace".ko wuya ko dad'i maryam yusuf yana tare dake har k'arshen numfashi"banida wani buri aduniya daya wuce mukasance tare har abada.fatana Allah yasa alkhairi azamammu, yabamu zuri'a d'ayyiba"Ameen yah Allah miji nagari"ina alfahari dakai broth"abaya inaga kamar baidace na aurekaba"ashe aurenkane babbar dacewa agareni"lumshe idanuwansa yyi yace".nima abaya nayi zaton uk'uty bazakimun biyayya ba"ashe ba haka bane"tun kafin aurenmu kike bani kulawa da gudun b'acin raina"har kawowa aurenmu"Allah yayimiki albarka yabarmu tare"Ameen yah Allah mijina! ina alfahari dakai....sosai suka dinga gayawa juna kalaman k'auna"ganin ankusa kiran magrib yusuf yajata ya nuna mata ko ina na gidan"sannan yatafi masjeed"maryam takira mama ta sanar mata.....sosai tayi mamaki tamusu addua da fatan alkhairi"sannan taje gun umma da hjy tasanar musu"sai gashi kafin dare duk dangi anji yusuf yayi sabon gida....

Yusuf be shigo cikin gidan ba sai bayan sallar isha'i"yana rik'e da manyan ledoji Ahannunsa yashigo cikin main parlou"maryam na zaune da kayan bacci ajikinta tana kallon wani indian firm"little nacan cikin gadonta tana bacci"da sauri maryam ta tashi tsaye ta nufesa tana murmushi ta russina tace".sannu da zuwa"yauwa baby nah"turo baki tayi tace".niba na girma ba"ah ah aguna bakya girma ,kullum ke yarinyace ai... yafad'a yana d'ago ta, yajanyota jikinsa"zama sukayi gefen kujera"yusuf na mamuk'e da ita"ko plate da cups yahanata tashi ta d'akko"acikin ledar sukaci naman da frash milk"sannan yana rik'e da hannun ta suka wuce kitchen ta kwashe komai ta kai..... uk'uty muje nayi wanka saimu kwanta ko?"dato ta amsa suka wuce d'akin sa"bayan ta had'a masa ruwan wankan yace".kar abar little ita kad'ai"idan nafito zan biyoki acan"dato ta amsa ta wuce d'akin ta"ita kanta abuk'ace take da mijin nata"sbd kayan da mama ta d'irka mata na sha dana tsumi"dukda tasan idan tazo hannun yusuf zata gaya musu....bata gama wannan tunanin ba little ta farka"zarota tayi dg cikin bed d'inta"ta zauna agefeb bed ta shayar da ita.bayan tagama bata ta azata asaman kafad'arta"tana jijjigata sbd tayi gyatsa....yusuf yashigo dg shi sai boxer kawai ajikinsa"tashi tayine?"yafad'a yana k'ok'arin zama gefen maryam ya kwanta ajikinta....wani yarrrrrr taji"Ahankali tace". Eh tama gama sha ai"kice anyi daidai kenan?"tunda tagama saita barwa dadynta fili yayi yadda yakeso"murmushi kawai maryam tayi tana shafa gashin k'irjinsa da hannunta guda"ukuty jeki kwantar da ita pls"dato ta amsa sbd dama tama koma baccin"tashi tsaye tayi taje ta kwantar da ita ta tofa mata addu'a"tana rufeta taji yusuf abayanta ya rungumeta"ya matseta ajikinsa yana maida numfashi"murya can k'asa yace". Imiss you ukuty"yafad'a yana janta saman bed"yafara k'ok'arin rabata da kayan jikinta"sosai yabata tausayi"sbd yadda yaketa rawar jiki"idanuwanta alumshe takasa hanashi"pls uk'uty kimun abinda zanji dad'i"yafad'a yana had'e bakinsu agu d'aya"shafa kansa tayi tana maida numfashi...hasken d'akin yusuf yarage.....kafin su Lula wata duniyar"Awannan dare maryam taga surkulle kala kala da sabbatu agun yusuf "tasha kalaman k'auna da soyayya"takumaji ajikinta bewar Allah"sunjima suna abu guda....koda Asuba yusuf saida yakoma second round"sannan sukayi wanka da sallah"suka koma baccin gajiya dabasuyi ba ajiya....

K'arfe 8:11 am kukan little ne yatashesu"maryam badan baccin ya ishetaba ta farka"yusuf yatashi yad'akko little"ta amsheta tana bata mama....bayan tagama bata suka koma wani baccin sai 9:30 am suka farka"atare sukayi wanka"bayan sun gama shiryawa gurin k'arfe 10"yafita"itakuma tayiwa little wanka"tafara gyara gidan, dukda beyi komai ba"gurin k'arfe 11 me gadi yayi sallama da kayan break fast"yasanar mata tun k'arfe 8:30 am mama ta aiko a kawo, atime d'in basu tashi ba"maryam ta amsa tamasa godiya"yusuf kuwa gida yaje yagaishe su, ya wuce office"bejimaba yadawo dama hutun sati 1 yad'auka sbd yakasance tare da family nasa...maryam na kitchen tana kallon dukiyar da yusuf yazuba mata yashigo cikin kitchen d'in"turo baki tayi ta kauda kanta"ukuty nah nayi laifine ko?"toba kaine kafita bansan ina kajeba?"sorry kinji baby nah"office naje na amso hutun 1 week sbd mushana ko?"dariya tayi tace".ka kyauta"muje kayi break fast"okay ina little"tana can d'aki tana wasa"muje na d'auketa mu gaisa"mama tace".anjima idan mai aikin tazo tagama abinda takeyi akaita da marece za'a maidota"amma abata mama tasha sosai...to shikenan Allah sarki mama"bari kawai"ai gara akaita komunfi shanawa da kyau"anty safeenah ma zasuzo anjima ganin gida"bazakiyi grikiba sai gobe nayi order d'in abinda za'a kawo da rana.dato maryam ta amsa suka wuce bed room d'in yad'akko little"sukadawo parlourn"yana mata wasa suna break fast"bayan sun idar maryam ta wuce kitchen ta wanke kayan"yusuf nata rirrigar little hartayi bacci"yakaita d'akin maryam ya kwantar da ita..zai fito maryam ta shigo"my big mero muje gasky abani kulawa"turo baki tayi cike da shagwab'a tace".bayan kulawar jiya har yauma?"eh mana ukuty nah"adinga tausayamun nasan kina k'ok'ari ki k'ara kinji"yafad'a yana d'aukarta gaba d'aya suka wuce master bed room d'in sa........

*Bayan shekara 5* Rayuwa ta lula"waran da dad'i,wataran akasin hakan"to hakane a family d'in Alh idris da Alh Aminu.....hjy tarasu shekara 3 dasuka wuce"mubarak da Ahmed sun sami aiki anyi aurensu.....fatima tasami wani babban mutum ta aura da matarsa ta mutu"yyinda yusuf yacanzawa su Abba gida....ayanzun haka badiya yaranta 2"ab'angaren lovers bird kuwa"maryam yaranta 3 yanzun"amma idan kaganta zaka d'auka ba ita ta haifesu ba"little nada 2yrs aka haifi khaleefa(Aminu)yanada 2 yrs aka haifi ihsan(habiba)ayanzun haka itada yusuf shekararsu 32 aduniya"amma idan ka kalli yusuf zaka zata yyi 40yrs"sbd kamalarsa da dattako"ga kuma manyan kud'ad'e daya kama"zama na tsantsar so da k'auna sukeyi da maryam"dukda wataran ana sab'awa"musammun akan matan dake nuna suna sonsa......

Ahankali wata had'add'iyar mota tayi parking bakin get d'in wata tsadaddar makarantar yara"cike da aji aka turo k'ofar"santala santalan k'afafunsa ya zuro a waje yafito"Saida na kallesa da kyau nagane ashe yusuf ne"yak'ara haske da kyau,da k'iba"sbd hutu da jin dad'in rayuwa"yana sanye da wata giznah kalar sararin samaniya"y'ar ciki da malun malun"maryam ta fito cikin shiga ta alfarma"tayi k'iba da haske ,ta k'ara wayewa"tana sanye da wani arnan leshi..kallo d'aya zaki mata kiga hamshakiyar mace"sunata zuba k'amshi me dad'i"rufe motar sukayi"maryam na rik'e da wata yarinya da bazata wuce 8 month ba"yusuf na murmushi yace". uk'uty bani mama na na d'auketa (habiba)"yafad'a yana amsar yarinyar"maryam na kallonsa tace".broth ciki zamu shiga ne?"tafad'a tana kallon k'ofar get"Eh mana"dato ta amsa suka shige ciki.... y'an kalle kalle sukeyi"abayansu sukaji wata nacewa hall d'in makarantar zaku shigane?yusuf yajuyo ya kalli matar"tana tsaye da k'afarta guda alauye..... had'e fuska maryam tayi sbd ganin yusuf da matar suna kallon kallo"hjy kubra ce? yusuf kaine?"innalillahi wa inna ilaihir raju'un"tafad'a tana kallonsa"dan Allah yusuf kayafemun abinda namaka"kaga yadda nakoma"sanadin karaya?.....bbu komai ya wuce"atake maryam ta tuna da wacece hjy kubra"saidai kallo d'aya tamata ta tabbar da YAU DA GOBE tayi aiki akanta"shikansa yusuf jikinsa yayi sanyi"zasu wuce yace".acan hall d'in zamuje"gayacan Inda wa'annan suka fito"tafad'a tana nuna musu da hannu.ke meye kikeyi anan?"kanta ak'asa tace".nanny d'in yara ce ni ana biyana amakarantar"okay yafad'a sunayin gaba"yana godewa Allah daya masa ni'ima"yana tuna daya biyewa son zuciyar hjy kubra ta yaudaresa sbd kud'i"da yanzun ina zai kai kansa"ita kanta dubi yadda rayuwa ta maida ita.yatabbatar da cewa duk rintsi kaidai bawa ka rik'e ubangiji alamurranka ,ka tsaida gsky zai taimakeka....dama broth wannan itace hjy kubra?"itace ukuty"kinga yadda rayuwa ta mayar da ita ko?"saina tuna time d'in datake hjy kubrar ta"kuma ayanzun haka shi Alh ASHIRU NAIRA d'in (tsohon mijinta")shine governor d'in garin nan"gashi sbd son zuciya tayiwa kanta"Allah yakyauta kawai suka fad'a suna shiga assembly hall na makarantar su little"atime d'in da suka shiga anata kiran abubakar Ahmed isah"yazo ya amshi gift nasa" yazo ana biyu"ga kuma maryam yusuf datayi na d'aya da gift nata a hannunta.... little naganin mommyn ta da dadynta ta nufosu aguje tana dariya"daddy sai yanzun?"sai yanzun little muka fito"cewar yusuf suna zama kan kujerun da iyayan yara ke zaune....kamar ance yusuf yaduba gefensa...yaga Ahmed da rukayya zaune da yaronsu abubakar Ahmed"yana tsaye gabansu da gift nasa"da sauri yaron yanufo little yana.cewa maryam yusuf zoki gaisheda mommy nah da abbanah"da ido yusuf ke kallon yaron,yahango kamannin Ahmed afuskar yaron"daddy zanje gun abubakar Ahmed"d'an ajinmu danake gayamuku yanada kirki"maryam na kallonta tace".sai kindawo.....da ido yusuf yabi little"yanata kallon Ahmed namata tambayoyi"sai kuma yaga rukayya da Ahmed suntaso"saurin d'auke kansa yayi"Assalamu Alaikum!suka fad'a atare"yusuf ya amsa fuska asake"Ahmed yabashi hannu sukayi musabuha"yaja kujera yazauna agefensa"maryam bata yarda ta kallesaba tagaishesa ya amsa"lah abba kasan daddyn maryam yusuf?"nasanshi abubakar kuje mota gamu nan tafe.... rukayya na murmushi ta kalli maryam tace ".ikon Allah kenan!gashidai komai ya wuce har yara sun saka zamu k'ullah zumunci"kullum zancen Abubakar maryam yusuf"ashe y'arkuce?"aikuwa itace"itama tana yawan zancensa agida"masha Allah"Ayi hak'uri da abinda yafaru abaya"kodan sbd yaranmu"yusuf yace".bbu komai ai"suna anan zaune shima faruq da hafsat suka iso"sbd duk anan yaransu ke karatu....da haka taro yatashi lafiya"sosai yusuf ya yaba da k'ok'arin little,wacce ayanzun haka tana gun mama da zama ta amsheta tun yaye."saidai tana zuwa ta musu week end"kowa yashige mota yanufi gida....sai muce su yusuf asauka gida lafiya....

Tamat Bihamdilillahi!🙏

Duka duka anan nakawo k'arshen wannan book nawa me taken *y'an uwantaka ne ko soyayya* Kuskuran danayi aciki yah Allah kayafemun kabani ladan fadakarwa.

Nagode! nagode!! nagode k'warai ga jama'ar dasuka biya kud'in su sbd su karanta rubutuna"ina alfahari daku"sai mun had'e asabon book nawa nan bada jimawa ba me taken *nida dr sadeeq*

Wannan book d'in nakudine duk wacce takaranta bata biyani hakk'ina ba nabarta da Allah.......

Na sadaukar da wannan littafin agareki mahaifiyata! hjy Aysha Abdallahi yamel"Allah yak'ara miki lafiya da nisan kwana my momma nah🥰💖💞

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull