Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt - Chapter 16
Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt Chapter 16: Yan'uwantaka ne ko soyayya cmplt Chapter 16. ******************* Kwanci tashi inji masu iya mgn sukace asaran…
4,046 words
******************* Kwanci tashi inji masu iya mgn sukace asaran me rai"ayau dai watan maryam da yusuf 5 da aure"cikin ikon ubangiji"kulawa da tattali da ladabi da biyayya"bbu wanda maryam bata masa"yusuf kuwa na k'ok'arin kyautata mata da bata farin ciki"ayanzun haka anraba auren fatima da muhsin tana gida"yyinda ansaka ranar auren nasiya da muhd"nan da wata 4 masu zuwa"baby boy na gidan faruq "wato Abdallah yayi wayo masha Allah.....ayau yakama Friday k'urarran lokacine"maryam tun 12 dama take tashi duk Friday"kuma yusuf yafad'a mata sai la'asar zai dawo gida"ta hau nafef ta tafi gida.....gaba d'aya yau jinta takeyi wata iri"ga tashin zuciya da kasala tanaji ga jiri"haka ta fito da nufin ta tafi bakin titi ta hau adaidaita"tana fitowa tadinga ganin juwa....luuuuuuuuu tayi zata fad'i"taji antarbota"tana d'ago kanta suka had'a ido da yusuf....✍️ 6/1/22, 20:15 - Ummi Tandama😇: ukuty nah lafiya ko bakyajin dad'i ne?"yafad'a Ahankali yana mannata da jikinsa"saurin toshe hancinta tayi" sbd jin k'amshin turarensa zai tayar mata da zuciya"kallonta kawai yusuf keyi yana son fahimtar meye dalilinta na toshe hancinta?"broth banason k'amshin turare....bata Ida mgn ba"amai yataho mata"k'okarin janye jikinta dg nasa tayi"amma saima yasake rik'eta yana cewa"baby bakya lafiya kika b'oyemun....gaba d'aya maryam ta wanke masa jiki da amai"amma shi ko a jikinsa"saima sannu yake mata yana duk'ar da kanta awajen"danda nan aka dinga kallonsu"wata sister khadija ta iso wajen tana cewa"subahanallahi sister maryam"bakyajin dadine?"d'auke kansa yusuf yayi yana jan hannun maryam"wacce ke d'agawa sister khadija kanta"gsky bara nayiwa dr salma mgn kuje ta dubaki"dg haka nurse d'in ta wuce"yusuf yad'auketa gaba d'aya"suka shige toilet d'in dake reception d'in...da kansa yawanke mata jikinta"fuskarta bbu walwala tace".broth kayi hak'uri nab'ata maka jiki dan....rufe mata baki yayi da tafin hannunsa yace".ta lafiyarki nakeyi sweet heart ba wani b'ata jiki ba"muje adubaki mutafi gida"ada nace sai 4:pm zandawo"kawai jikina yabani kamar ba normal kike ba"yafad'a yana kama hannunta suka fito"office d'in dr salma suka wuce"dama sister khadija ta sanar mata"suna shigowa dr tayiwa maryam sannu"suka zauna itada yusuf"dakejin kamar yamayar da ciwon a jikinsa.bayan tagaishe da yusuf"sannan ta fara mata tambayoyi"dg k'arshe tasaka taje toilet tayo fitsari"yusuf dai na zaune"aransa yana addu'ar Allah yasa cikin ne"bayan ta kawo fitsarin aka auna.....atake dr takama murmushi tace".sister maryam congratulations"Allah ya imganta"kina da jaririn juna biyu"zamu d'ibi jininki"sbd musan sati nawa ne?"bakin yusuf yakasa rufuwa"yana kallon maryam yaga yanayinta"saiyaga ta rufe fuskarta tana dariya"hannunta yakama yana murmushi yace". Alhmdllh! maman baby congrats!turo baki tayi"dr tayi murmushi tana zaro siring ta d'ibi jinin maryam"wacce tana jikin yusuf aka d'iba sbd batason allura....basubar asibitin ba"saida dr tagano cikin maryam sati4 ne cif"gaba d'aya yusuf wani irin farin ciki yakeji marar misaltuwa"babu kunya suna shiga mota yakira mama"ko gaisawa basuyiba yace".mama wlh uk'uty cikine da ita ayanzun muka dawo dg asibiti sun....fisge wayar maryam tayi takashe tana turo baki"kukan shagwab'a tasaka tana kwanciya ajikinsa"ukuty karfa kija mu fad'i pls"tobakai bane saika dinga fad'in inada juna biyu"laifine danna fad'awa su mama?"Eh mana"tunda zanji kunya ko?"amma ai dole su sani"hakane amma ai zasu gani ajikina basaika fad'a ba"kuma ni kunya zanji....atime d'in da cikin yashiga kinji kunyane sai gun fad'a zakiji??"kinga suma zasu gane cewa"YARO MA NAMIJI NE(mai dambu)"yafad'a yana d'age gira"yacigaba da cewa"ayadda na lissafa shekaranmu d'aya kaki haihu"naso ace ma 9 month wlh zaki haihu....broth Allah yashiryamun kai"Ameen uk'uty nah"yanzun mu koma gida kici abinci saina gaisa da baby nah ko?"nidai ah ah broth"jiyafa ba kungaisaba?"ai jiya bansan dashiba"yawan yin abinfa ga mace me yaron ciki yana sakawa Ayi miscarriage"da gske kikeyi?"wlh kuwa"amma bawai ina nufin ba'a yiba"okay"to nidai sai mungaisa da baby nah"yanzun broth inaso naci d'ata pls bakina bbu dad'i"sai kuma zogale da rama zanci"dasu gawasa,da agwaluma..... uk'uty abubuwa 5 kika lissafa?"kuma da wuya asamu"ni wlh shinakeso naci. bbu ruwana kasamarmun ko inane"kuma yunwa nakeji"tafad'a tana sakin kuka na gsky"subahanallahi"aizan samo miki yanzun kinji?karkiyi kuka baby nah"shiru tayi batace komaiba"hanyar gurin masu siyar da fruit suka tsaya"bayan yayi parking yafito.....gawasa, agwaluma"zogale, kawai yasamu"bbu rama da d'ata"be sanar mata ba"sai kawai taga sunyi hanyar gidan mama"yauwa dan Allah muje can"aiba zama zamuyi ba"gun sarkin mita zamuje(hjy)nasan agunta zaki samu d'ata da rama"anan meye? tafad'a tana bud'a ledar"yauwa zanci broth"sai anwanke uk'uty"kibari muje gidan yanzun na wanke miki ko...ni wlh banaso sai munje"kabarni naci abuna mana"ganin da gske takeyi"yasaka yyi parking"fitowa yyi yabud'e boot d'in motar"yad'akko wasu swan"dama da ledar ya fito"wanke mata su tas yyi yamik'a mata"jikinta na kirma ta amsa tafara cin agwalumar"dama bakinta bbu dad'i"bayan yashigo yaja motar yanata kallonta"yanajin tausayinta da tuna kalaman abokinsa faruq"akqn shima idan sunsami ciki"yadda maryam zata fitinesa"gashi kuma yafaru"uk'uty bbu tayi?"umm kawai tafad'a bata koma mgn ba"shima shiru yayi,da haka suka iso gida"fitowa dg motar sukayi"kai tsaye sashen hjy suka wuce"tana zaune ,da shirinta na zuwa sallar juma'a ajikinta"tana dama fura ,ga dankalin hausa agefenta dafaffe cikin plate"zata kwad'a da k'uli k'uli... d'ago kanta tayi ta amsa sallamar su"ikon Allah kune da rana tsaka haka?"maryam naganin dankalin ranta yabiya"broth zanci dankalin"tafad'a tana nunawa da hannu"d'aure fuska hjy tayi tace".sai kace wata k'aramar yarinya?"yusuf beyi mgn ya yakai hannu zai d'auki dankalin"hjy ta wafce plate d'in"cikin zafin nama yarik'e hannunta yad'auki babban guda.... innalillahi"isuhu cutata kukazo kuyi ko me?"banza yusuf yamata yana mik'awa maryam dankalin"tayi d'aurin d'auka"tana cewa"sauran furan"wacce ubanki Aminu ya aikomun da ita ko?"haba hjy"kitausayawa baby nah"juna biyune da ita fa..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un"sannu marar ta ido"lallai kaci ka gyare"ai gara daka mata ciki"to nidai bana neman kowa"kabata dankali saiku k'ara gaba ko?"shiru yusuf yayi yashige bed room d'in hjy"ajiya kabani isuhu dazaka shigemun k'urya?"k'ilan saina kira habiba zaku fita"wace irin jarabace wannan?"kuna gidan ban hutaba"yanzun anmuku auren ma"bazaku barni ba"yaushe rabon danaje gidanku Allah natuba"duka sau d'aya ne kuka tab'a had'amun kayan arzik'i ko?"maryam nacin dankali tace". ba'a dai son mutum me mance alkhairi"banza hjy ta mata ta ajiye furan tabi bayan yusuf"da sauri maryam ta d'auki furan ta kafa kai tana sha.....hjy nata mita da zage zage"ta fito rik'e da rigar yusuf "wanda hannunsa ke d'auke da d'ata dayaje nema.....ai hjy naganin maryam na d'ad'd'akan furanta "ai saita cika yusuf ta nufeta....da sauri maryam ta ajiye kwanon da y'ar kad'an aciki"da hanzari tabar parlourn"wlh bazan yardaba dole Aminu da idris su zab'a koni ko ku agidan nan"tab'e baki yusuf yayi yace".haba matar kijira kiji" ubanme zakamun?"bece komaiba yajuya yafice dg parlourn"hjy ta d'auki dankali da sauran y'ar furan"ta yafa mayafi ta rufe k'ofar ta ta wuce sashen mama......
maryam nafitowa sashen mama ta wuce"sbd ruwa me sanyi takeso tasha"mama da mai aikinta na kitchen"acan maryam tasamesu"auta kece da rana haka?"yajikin naki?"eh mama ina wuni"lfy qlau"ke kad'ai ce?"tare da broth muke"tafad'a tana d'aukar ruwa a fridge"ashe tare da marar kunyar kike"muje parlourn muyi mgn"ina shi yusuf d'in?"maryam na dariya tace".yana gun hjy"Allah yasa ba mgn zaije yad'akko mun ba..... tafad'a suna fitowa dg kitchen d'in"yusuf shikuma yana shigowa"mama sannu da gida"yafad'a yana tsayawa dg bakin k'ofar"ukuty zomuje tun kafin tsohuwar nan ta iso nan"wato hjy bazaku dena jantaba ko?"basuyi mgn ba da sauri yusuf yaja hannun maryam suka fita....ko minti 3 basuyi da fitaba"hjy ta shigo bbu ko sallama"mama nata kallonta tana jiran jin meye zata fad'a"habiba ina idris?"yana kasuwa hjy"to kirashi awaya"itama jamilah nasaka ta kira Aminu"komai yakeyi ya aje yazo"lafiya daiko hjy?ina lafiya ?"habiba kun haifamun k'aya"yusuf da maryam sun gallabeni"to ai basu na haifaba"iyayensu na haifa.sbd haka wlh dole uwayansu su shiga tsakanina dasu"kar su koma zuwa min shashe"shi tantirin marar kunya"yazo shiga mai mata"yamun bincike acikin d'aki kamar yabani ajiya"yakwashemun d'ata da dankali yabawa maryam"itaga mai yaron ciki"sannan ita y'ar banza ta d'aukemun fura ta shanye"duba kiga y'ar wadda ta barmun"ta fad'a tana nuna ma mama kwanon"to wlh ko abiyani abuna konayi Allah ya isa"mama na b'oye dariyarta tace".kiyi hak'uri zanyiwa Alh bayani yanzun"zai kuma hukuntasu"zancen fura zanbada yanzun asiyo miki"dankali kuma inadashi zan dafa miki"anata za'a yi za'a yi"naje kuma naji shiru ko?"to kibada naje nasiyo abuna"dankali kuma idan nadawo sallar juma'a baki aiko dashiba zakiga monzon aike...mama batace komaiba ta jawo post nata ta zuge ta ciro 500"dukda tasan furan da nashanun basu wuce na 200"tasowa tayi tazo gabanta ta russina ta bata"hjy ta amsa tana cewa nidai me zance?"saidai Allah yashiryesu"kima k'yale idris d'in kawai"amma kimusu mgn karsu koma zuwa min shashe....dato mama ta amsa"hjy ta fita"mama tace".ai zaizo yusuf d'in yasameni wlh"tana k'ok'arin tashi umma tayi sallama"mama ta amsa tana murmushi"umma tace".mmn maryam hjy tazone?"yanzun ai tafita"oh yarrabi"Allah yashiryi yaran nan"suna ina?"yo ai sun gudu tunda sunsan basuda gsky"umma na dariya tace".aidai nabiyata kud'in furanta"mama ma na dariya tace".nima ai nabiya"ohni hjy da jikokinta"Allah dai yakyauta"itakuma Allah yaraba lfy"mama ta amsa da Ameen"umma ta fita.....
maryam da yusuf nata dariyarsu suka shige mota abinsu"maryam tace".nasan had'uwarka dasu Abba bbu kyau broth"Hmmm!hjy fa kinsanta dason abin duniya"k'ilan kud'in furan ma kawai mama zatabata abar zancen"hakane kuma fa"nidai ai tunda kinci abinda ranki keso ai shikenan"Allah sarki broth d'ina"dukfa babyn kane yajawo haka"murmushi yayi yace".ko muje na siya miki furan?"ai yanzun masjeed za'a tafi"karnasaka kayi latti broth"okay yafad'a yana cigaba da driving nasa"broth!takira sunansa"na'am big baby"tana dariya tace".banason k'amshin turaren ka pls"to yaya za'a yi kenan?"kinga duk kayana k'amshin yazauna sosai"amma wane kikeso"idan munje zanduba nagani"ohni mai ciki"turo baki tayi tana harararsa"yana dariya yayi parking suka yafito"kasancewar yanzun sun ajiye me gadi"ciki suka wuce"maryam na rik'e da ledar kayan k'walamar....kayan jikin ta ta cire"sukayi wanka ahanzarce"yusuf ya shirya yatafi masjeed"ita kuwa anan tayi tata sallar"sannan ta zauna ta kwad'a zogale taci ta k'oshi"ta koma kitchen ta azawa yusuf indomie da serdine....tana zuba serdine d'in yashigo da ledar kwakwa da dabino"ta baya ya rungumeta"broth kadawo?"Eh ukuty yaya jikin?"da sauk'i"baki koma yin Aman ba ?"Eh banyiba"okay ga tsaraba"godiya nake sweet heart"meka rok'amana?"Allah yasaukeki lafiya ya inganta mana"sai kuma namana addu'ar samun zaman lafiya"toke wacce addu'a kika mana agida?"namana addu'ar Allah yabarmu tare"sannan yak'ara yalwata maka arzik'in ka"sai kuma karkamun kishiya"aikuwa namayi budurwa ayau....d'aure fuska tayi tana k'ok'arin k'wace jikinta dg nasa"yanata dariya yace".wasa fa nakeyi ukuty nah"inama zanga wata budurwa nida naje masjeed"hmmm!dama ai nasan tsokanata kakeyi"tafad'a tana juye indomie d'in acikin plate"tasaka fork suka fito parlourn.....maryam bataciba"kwakwa da dabino taci"yusuf ne kawai yaci yak'oshi yajata Master bed room d'in su suka fara aikin lada....
********************* Akwana atashi bbu wuya agun Allah"ansha bikin badiya da muhammad"su Ahmed sun kammala karatunsu sai jiran aiki"yyinda yusuf yasami k'arin girma agun aikinsa"arzik'i ya bunk'asa"ayanzun haka yusuf yabiyawa umma da mama hajji"yace".sai maryam ta haihu itadashi zasuje"yayinda hjy ank'ara tsufa"yau lafiya kobe bbu lafiya"mitarta sai abinda yayi gaba....gefe guda kuma maryam da yusuf suna rainon cikinsu sukeyi cikin so da aminci"gashi har cikin yashigo watan haihuwa ,yau ko gobe"komai da ake buk'ata na haihuwa an tanada"ayanzun haka yusuf yagina sabon gidansa"zai barwa su mubarak da Ahmed wanda suke ciki yanzun"so yakeyi da maryam ta haihu ranar suna su tare....komai yazuba sabo agidan"gida aljannar duniya a nassarawa.....
yau yakama week end"dama maryam ta d'auki hutun haihuwa tun last 2 month ma"tun daren jiya yusuf yamatsa mata da fitina"ita kuma takasa hanashi"tunda tasan yanada yawan buk'ata"shiyasa tun bata saba ba"hartazo ta saba da abin"balle mace me ciki abin son kowane namiji ce"tun 10 am ake abu d'aya har 1:pm"sannan yabarta sukayi wanka.ga bayanta da k'ugunta nata mata ciwo"bayan sun gama sallar azahar"tana kwance tace". broth dama yaune zankoma awo ko?"eh yaune"amma ai sai 4 ko?"Eh amma banajin dad'in jikin nawa"subahanallahi yafad'a yana nufarta"yakamata ta tashi da k'yar"ga uban cikin yayi girma yayo k'asa"ukuty meke miki ciwo?"kodai sbd abinda mukayine?"ah ah broth"badan ya yardaba yacanza kaya"ita kuma yataimaka mata ta saka doguwar riga suka nufi asibitin.....
Doctor tana gama aunata ta saka mata hannu"atake ta fahimci nak'unace"hartakai 3 cm"atake aka wuce da maryam labour room"kafin doctor ta fito tasami yusuf a reception tasanar masa"arikice yakira mama"yana k'okarin dannakai d'akin haihuwar dr ta dakatar dashi tace".yaje yakawo kayan haihuwa"becekomaiba yabaro asibitin....
yusuf be jima da tafiya ba mama ta iso...✍️ 6/1/22, 20:16 - Ummi Tandama😇: yusuf be jima da tafiya ba mama ta iso asibitin"atime d'in komai yarikice wa maryam"nurses 3 da doctors mata 2 ne akanta"salati kawai da kiran sunan broth kawai takeyi.....cikin ikon Allah baby girl ta fad'o duniya"ta tantsara kuka har mama dake tsaye tajiyo"Alhmdllh! ta fad'a tana d'aga hannunta sama"hakan yayi daidai da shigowar yusuf"gaba d'aya yayi wani wuri wuri dashi"mama lafiya kike murna"bayan ukuty na nak'uda?"mama na murmushi tace".nayi laifi kenan yusuf?"to kwantar da hankalinka ta sauka"kai Alhmdllh! yafad'a yana sakin tsalle kamar wani k'aramin yaro"mama ta amshi kayan hannunsa ta k'wank'wasa k'ofar"mama to yaya jikinta kuma me aka samu??"nimafa bansaniba yusuf"kukan dai babyn naji"yusuf na k'ok'arin mgn aka bud'e k'ofar"doctor yaya jikin matata?"yafad'a cikin damuwa"Alhmdllh ta sauka lafiya"tasami baby girl"yanzun zamu shiryasu itada babyn akawosu d'akin hutu...dato mama ta amsa"yusuf na murmushi yace". Alhmdllh!yazaro wayarsa dg aljihun jeans d'insa yafara kiran dangi da y'an uwa da abokansa yana shaida musu uk'uty tashi ta sauka lafiya.mama kuwa girgiza kanta tayi tana kiran Abba ta sanar masa"sannan takira umma da anty safeenah....gaba d'aya yusuf maryam kawai yakeson gani"babyn aka fito da ita"mama ta tashi da sauri ta amsheta"masha Allah tafad'a"sbd ganin yarinyar nakama da yusuf sosai"yusuf kuwa bemabi takan babyn maryam kawai yake tambaya"aka nuna masa d'akin datake"da hanzari yanufi can"maryam.na kwance and'aura mata drip"sbd ta ji dad'in jikinta"baby sannu kinji?"yafad'a yana kama hannun ta guda"murmushi tamasa tace".broth haihuwa da wahala wlh"dan Allah karkoma yimun wani ciki"yana murmushi yace".baby lallai kinji jiki"shiyasa nifa ko babyn banganiba ke kawai nakeso nagani"sannu kinji"Allah yayi miki albarka"Ameen ta fad'a Ahankali"bbu dai Inda ke miki ciwo ko?"Eh saidai gajiya da yunwa"okay"bara naje nasiyo miki mutuniyar taki(kaza) dasu maltina ko?"Eh broth"tashi ki jingina uk'uty"yafad'a yana kama ta"ta tashi zaune"hakan yayi daidai da shigowar mama"da babyn ahannunta"turo baki maryam tayi tace".mama shine kika fara d'aukarta bakizo kinga jikina ba....haba auta aike angama yayinki"kukan shagwab'a maryam tasaka"mama na murmushi ta mik'awa yusuf babyn"ta matso tanayiwa maryam yaya jiki?"yusuf na murmushi yanata kallon babyn"yamata addu'a yatofa mata"ukuty kinga ashe da dadynta take kama badakeba ko?"nidama banaso ta biyoni"yana dariya ya aza mata ita kan cinyarta yace".gatanan sunanta MARYAM!namata hud'u ba da sunanki" sbd irin SON danake miki..bejira amsartaba yafice da sauri"mama na murmushi tace".to mudai da maryam zamu kirata"maryam dai na murmushi tana kallon babyn tana yabawa da kyawunta......aranta tana k'arfafa irin soyayyar da yusuf ke mata" kankace me?"jama'a suka fara tururuwar zuwa"badiya ma da nata cikin itama tazo"sai hafsat d'in faruq"su fatima dasu anty safeenah da matan kawu haruna"dangidai mak'il"yyinda Angon jego bakinsa be rufuwa"agaban kowa yakebawa maryam kulawa"sai bayan sallar la'asar"mama tayiwa babyn wanka"maryam kuwa k'anwar ummanta tamata"sai gurin k'arfe 6pm aka basu sallama suka hau shirin tafiya gida"suna a mota mama tace".yusuf gida fa zamuje"cikin fad'uwar gaba yace".dan Allah mama kubarta gidanta"ad'auki me kulawa da ita zan biya.abinda kike zato bazai faruba"nibanaso taje wankan gidan nan"nidai broth inaso wlh"cewar maryam"atake yusuf yahad'e rai"mama tace".to bbu gidankun dazamuje, acan gida zata koma guna"yusuf be koma mgn ba"yyi hanyar gidan mama"maryam kuwa sai taji babu dad'i sbd ada da fara'a arsa yake.yanzun yawani b'ata fuska.....
suna isowa gidan bema fitoba yatsaya acikin motar kowa yafita"mama na b'oye dariyarta tace" yusuf kaje yanzun ka kamata kayanta dana babyn wad'anda ke gida"dato ya amsa bece komaiba"mama na goye da babyn tayi gaba"maryam kuwa k'in tafiya tayi"bayan kowa yafita ta matsa gefen sa"yana k'ok'arin rufe murfin tayi saurin rik'e wa"fuskarsa ad'aure yace".malama kinbani ajiyane?"haba broth!saika yi fushi dan Allah?bansaniba"kikoma Inda kikeson zama"dama ai takuraki nakeyi ko?"to bama kwana 40 ba" idan kin tashi kiyi shekara 40"yana fad'in hakan yazuro hannunsa da nufin yaturata"tayi saurin rik'e masa hannu ,ta zura yatsun sa guda 2 abakinta tana tsotsa. cikin salon datasan yake manta wace duniyar yake...sai gashi da kansa yajanyota asaman cinyarsa yarufe motar"bakinsa danata yahad'e yana shafa kirjinta da sassan jikinta"ita kuma tana biye masa.....gaba d'aya nishin yusuf kawai akeji acikin motar....saurin rik'e masa hannu maryam tayi tana janye jikinta"idanuwanta alumshe tace".bana iya jure fushinka my prince"tuba nakeyi"kuma kasan agidanmu bazamu sakeba"amma anan zan fakaici idon mutane nazo d'akin ka nada mu shana kokuwa?"hakane ukuty nah"amma banji dad'i bane sbd ban fahimcekiba"zamuyi waya sweet heart"kar mama ta lura ban biyosuba"okay miye kike buk'ata bayan kayan sawarku??bbu komai"kaje kayo wanka kadawo kayi dinner ina jiranka"to shikenan my mero na"ki shafamun kan little mero"dariya tayi tana fita dg motar"ta tsaya tana d'aga masa hannu"tana juyowa suka had'a ido da mama da anty safeenah"rufe fuskarta maryam tayi tana murmushi"mama ta girgiza kanta suka juya"akunyace maryam ta wuce ciki"kai tsaye d'akinta nada ta nufa"acan tasami anty safeenah na shara"ancanza bed sheet"ga babyn kan bed tanata bacci"sannu laila"shi majnun d'in yatafi ko?"maryàm na dariya tace".kai anty"fushi fa yayi"shine na tsaya na rarrashesa"kin kyauta sosai"ni fad'a ma nayi akan zuwanki nan"tunda bayaso"nikaina sai yanzun naji dama ad'azun nace banason zuwa"wlh bazan iya bacci batare da yaya yusuf ba.....da sauri mama ta koma baya" sbd kunnanta dayaji abinda yafi k'arfin ta"aranta tace".shiyasa nace kidawo gida ja ira"da jegon yaje ya haike miki"anty safeenah kuwa batayi mamakiba sbd ita shaida ce akan yadda yusuf keson maryam....kitchen anty ta wuce"suka had'u itada mama da mai aiki"suka aza girki"farfesun kan rago da kunun jego,aka yi"sai tuwon dawa miyar kub'ewa, aka dafa man shanu....sai anata kiran isha'i suka idar da komai"maryam kuwa mik'ewa saman bed tayi"tana shafa kan babyn"gaba d'aya kewar mijintace aranta"wayarta ta zaro dg hand bag nata ta kirashi vedio call...yusuf na d'aure da towel iya k'ugunsa zai shiga bath room yayi wanka"yana tuna dukda cikinta yatsufa amma kullum atare sukeyin wankansu...kiranta ne yakatse masa tunani"murmushi yayi yace". Allah sarki my mero"kina raina"k'ilan nima ina ranki"yafad'a yana d'aga giran"broth wanka zakayi?"Eh babyn nah tunda kinmun wayo ko?"bafa haka bane"ni wlh yanzunma kewarkace ta dameni nakiraka"nima ke nake tunani"kukan shagwab'a tasaka tana wani narke murya tace".kasan bazan iya bacci batare dakai ba ko?"nima haka ukuty"gsky d'akina nada zankomo sai kundawo nadawo"Toba su mubarak naciki ba?"hakane suna ciki"amma ai akwai d'akin bak'i ko?"hakane "acan zan kwana my mero"tana y'ar dariya tace"kar akira magrib kashiga wankan"sai anjiman idan kadawo ko?"dato ya amsa yana huro mata kiss"tana dariya takashe wayar....cike da farin ciki yyi wankan yafito yatafi masjeed"bayan yadawo duk abinda yasan maryam zata buk'ata saida yad'aukar mata shi ita da babyn"yana ayyanawa aransa zai kwashe kayan sawarta da duk abinda zata buk'ata"yamayar asabon gidansu"idan tayi 40 saisu koma" tunda yanzun bbu halin su koma ranar suna.....da wannan tunanin ya nufi gun sabuwar motarsa yasaka komai"get man yabud'e masa get yafita....
maryam kuwa"wanka aka komayi mata,sannan aka zubo mata komai"amma bataciba"har babyn ta farka"bayan an bata ruwa da zamzam"ta wanke maman tayi addu'a ta fara shayar da ita"sai matse k'afafuwanta takeyi tana yarfe hannu sbd zafi"anty safeenah daketa shirin tafiya gidanta tace".sannu zaki saba nan gaba"amma ayanzun zakiji da zafi"tafad'a tana kallon kulolin abincin"wai bazaki ci abincin ba maryam?sai broth yazo anty" yana hanya"duk yau beci abinciba wlh"yayi nan yayi can"maryam kanki lafiya?sannu y'ar dad'i miji"cewar mama dake shigowa d'akin"dukda ak'asan ranta taji dad'in yadda maryam ke kulawa da yusuf"nidai mama Allah sai broth yazo zamuci.....kafin mama tayi mgn yusuf yashigo da sallama ad'akin"yana rik'e da ledoji"mubarak da Ahmed na d'auke da kayan su maryam"bayan sungaishe da kowa suka fita"yaya yusuf sannu da zuwa"yauwa sweet heart" ya jikin?"da sauk'i"mama sannu da gida"yauwa"to ga yusuf yadawo maryam"amma nasa abincin yana can parlourn"kece zakici komai anan"dato maryam ta amsa kawai"yusuf na murmushi ya amshi babyn dg gun maryam"mama ta juya ta fita"anty ta musu sallama ta fita itama ,sbd taje gidanta"ukuty k'in cin abinci kikayi dole saida ni??"Eh mana"Allah sarki my mero y'ar baiwa"Allah yabarmu tare"ina alfahari dake"nima haka"tafad'a tana murmushi"yamatso gefenta ya kamo hannunta ta dawo saman jikinsa"murya can k'asa yace".kin bata abincinta tasha"??yafad'a yana shafa kirjinta"Eh"amma wlh da zafi ni banaso"tafad'a cikin shagwab'a"zai dena uk'uty nah"karki barmun y'ata da yunwa kinjiko?"da ita dani wakafi so?"murmushi yayi yaja hancinta yace".kina kishi da itane?"nidai kafad'a mun"matseta ajikinsa yayi yace".kafin nasameta wana fara samu?"ni mana"to kece nafiso......dariya tayi ta sauka ajikinsa"tana jan hannun sa suka zauna a tsakkiyar carpet"atare sukaci abincin"dama yusuf nada son tuwo"kunun ne kawai kebe shaba"har naman atare sukaci"ga kuma wanima gasashshe na rago daya siyo mata"bayan d'azun ma yasiya mata kaji dasu maltina da drinks"toilet d'in dake cikin d'akin yashiga ya wanke hannu yafito"ukuty banyi isha'i bafa"zanje nayi sai mu had'u ta online"yanzun sai kiji ance bamuda kunya ko?"inama aljarabatu?"(hjy) yafad'a yana dariya"itama maryam na dariya tace".ai tunda kaji babu motsinta jikinne nata yatashi"to mudai idan lokaci yayi gara kawai ta ware"maryam na dariya tace".wlh broth karka bari su abba sujika"to ai gsky nafad'a"taso kiji wata mgn uk'uty nah"bbu musu ta taso"zanje gidanmu na kwanta "saimu had'u ta online"amma kona kwana anan bbu amfani. tunda batare dake zamu kwana ba"hakane broth"Allah yatsare hanya,ka kulamun da kanka pls"insha Allah"kimuku addua idan zaku kwanta bacci"to broth"rungume ta yyi ya manna mata kis agoshi yafita...sosai suka raba dare aranar suna chats....
************************
haka aka cigaba da zaman jego"maryam da baby nasamun kulawa agun mama da yusuf da sauran jama'a "badiya dasu fatima kullum suna agidan"hjy kuma ba kullum take lekowaba sbd bbu lafiyar kirki.....gefe guda kuma yusuf da maryam nashanawarsu hankali kwance su faki idon jama'a"gashi har yau take suna"me jego da little maryam sunyi cikar kwana 7"shar dasu"yusuf yayiwa maryam kayan barka nagani nafad'a itada babyn"harda key d'in sabuwar motarta"har kukan farin ciki maryam tayi"ya yankamata raguna manya 3"shagali bbu kama hannun yaro"tunda safe shigar farko iri daya suka saka brown d'in shadda giznah"aka mata make up"dandanan gida yafara d'aukar harami"sunso Ayi DJ"yusuf ya hana"acewarsa albarka yake nemama y'arsa"anci ansha"me jego da baby sunsami gifts"sai shiga maryam ke canzawa"kad'an kad'an yusuf yaratso jama'a yazo gunda kawai yaganta"itakuma ta biye masa cike da so da k'auna"sbd ayanzun maryam ko agaban waye nunawa yusuf so da k'auna takeyi bbu shakka.....da haka taro yatashi lafiya"sai muce Allah yacida y'an baya.....
Agajiye maryam tayi wanka ta kwanta itada babyn"koda yusuf yazo yamusu saida safe yasamu sunyi bacci"addu'a yamusu yafita....
Washe gari da safe"normal maryam ta farka"bayan sun yi wanka itada babyn ta goyata"ta zauna zatayi break fast"gaba d'aya mijintane aranta"wayarta ta d'auka da nufin takirashi"taji sallamarsa"fuskarta asake ta d'ago kanta tana murmushi ta amsa"broth yanzunfa kai zankira ka shigo"ai nazo jiya da dare kunyi bacci uk'uty"sainaji kamar nima na kwanta agefenku"to ina tsoron mama"murmushi tayi tace".hakane broth"ina kwana?"lafiya qlau my nuri"yagajiyar jiya"Alhmdllh"ina little?bacci takeyi"okay yafad'a yana zama gefenta atare sukayi break fast"bayan sun idar yace". uk'uty office zanje"b'ata fuska maryam tayi tace".yaka mata broth ka zauna ka huta"idan da nazauna za'a barni daku saina zauna.amma kinsan yanzun mama ta shigo"kuma Kinga rabona da office 2 days fa"hakane kuma"yauwa my mero"saimunyi waya ki kulamun da kanku"insha Allah Allah yatsare"banda kallon y'an mata"dariya yyi yaja hancinta yace".kishin yamotsa kenan?"turo baki tayi tace".laifine?"ah ah aisai d'an gata ake kishi ko uk'uty?"hakane"tafad'a tana k'ok'arin biyoshi"murya can k'asa yace".jinin zaikai kwana nawa ya d'auke?"bazan iya ganewa ba broth"kasan jinin haihuwa ba kamar na al'ada bane"to nidai gsky yyi maza yad'auke nagaji da jira uk'uty kitausayamun pls"idan yad'auke zan maka mgn"kuma dai dukda ina jinin broth bana gudunka ko?"nasani uk'uti nah kinamun duk abinda zansamu nutsuwa da farin ciki"Allah yayimiki albarka yabarmu tare"Ameen tafad'a cikin jin dad'in kalaman sa.....har main parlour tarakosa"kamar karsu rabu...
*Kwana 40 da suka wuce* 6/1/22, 20:35 - Ummi Tandama😇: *Kwana 40 da suka wuce*
Alhmdllh yau da gobe akwana atashi har maryam sunyi 40 days"bayan mama tasha fama dasu"sbd irin rashin kunyar dasuke tsulawa agidan"ak'agare mama take sugama wanka su koma gidansu"yusuf anan yake break fast, lunch,dinner,sai 11:pm yake barin gidan kullum" har zuwa yau da maryam tayi 40 daidai......sosai mama ta gyara y'ar tata"kodan rawan kan dataga yusuf nayi"dilka ta sati 1 aka mata"ajiya akamata kitso"yau kuma lalle"gaba d'aya maryam batasan sabon gida zasu komaba"yusuf naso yayi surprise d'in ta"koda mama tace".anty safeenah zasuje amata share share"sai cewa yayi yamata da kansa ai....gaba d'aya yau maryam da yusuf suna cikin farin ciki"bama kamar yusuf"jinsa yakeyi asaman gajimare"tamkar wani ango...lolx"k'arfe 5 daidai da wasu mintina"maryam tagama shirinta"cikin d'inkin doguwar rigar ta atamfa super holland"anmata kwalliya da stones masu tsada"ga make up na zamani anzo anmata agida"tamkar amarya tayi"dama mama tace".da marece zasu koma"kuma ansamarwa maryam me aiki"sannan yusuf yace".bbu zancen takoma aiki gsky"ta zauna gida ta kula mishi da y'a dashi kansa... feshe jikinta da turaruka tayi",ta yafa mayafinta"little na hannun mama tagama shiryata"dama kayansu tun safe yusuf yatafi dasu"d'an abinda ba'a rasabane"kawai tasaka acikin k'aramin trolley"to maryam goyata zakiyi ko?"nidai mama ahannu zan d'auketa karta b'atamun kwalliya"hmmm!aidai marliyya(me aiki)gobe zatazo tafara goyonta"ke kuma saiku k'arata keda yusuf d'in"da anyayeta zan amsota"dakin kyauta mama"murmushi kawai maman tayi"ta mik'awa maryam babyn"ta amsa ta zauna ta zuge zif tana bata mama.....