'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale - Chapter 5
'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale Chapter 5: 'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale Chapter 5. Garba da Hadi suka fusata sosai Suka mike…
4,416 words
Garba da Hadi suka fusata sosai Suka mike cikin zafin nama zasu fita Khalifa ya dakatar dasu da fad'in"Ina zakuje a wannan halin."? Garba Yace."Yallabai yarinyar nan yau sai tayi nadamar uwarta bata haifeta ba mu za tayiwa 'kazafi! banta'ba ganin butulu irinta ba, wallahi da ba don Yallabai yace tun farko a kyaleta da yanzu na zubar mata da hakora da tuni tana kwance tana jinyar kanta dan sai nayi mugun sa'ba mata kammani."! Khalifa yace."Ku dawo ku zauna ku samu nutsuwa." Suka koma suka zauna suna huci! yanda suka fusata niyyarsu subi Wasila gidan redion tana fitowa suci ubanta sai kuma aka katse musu hanzari.....Khalifa yaje ya zauna kusa dashi ya sanya hannu ya dafa kafad'arshi a hankali yace."Siyasa ce f........! katse shi yayi ta hanyar d'aga masa hannu Khalifa ya tsira masa ido ganin yanda duk ya wani burkice har yanzu yana digar da gumi kamar dakin babu Ac 'yan ya tsunsa biyu ya d'ora saman fatar le'bunansa ya tsurawa guri daya ido yana girgid'a kansa.
_Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/17, 10:05 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
_*Allah dan tsarkin mulkin ka, Allah dan 'karfin ikon ka, Allah da buwayar ka, Allah dan jin'kan ka, ka azurta wannan baiwa ta ka Hauwwa'u da sanyi idaniya👏🏻 Ya Allah munyi tawassali da Annabi Muhammadu SAW kayi mana dominsa Allah ka azurta Hauwwa da 'yaya masu albarka👏🏻 Allah ka yaye mana hijaban da suke lullube ka biya mana dukkanin bukatanmu na alkairi👏🏻*_ ~~~~~~~~~~~~~~~ *Free Pege13* Khalifa ya dafa kadarshi a karo na biyu yace."Duk abun fa ba na tashin hankali bane naga kamar ka dauki al'amarin da zafi tuntuni na fada maka dama siyasa ta gaji haka dole ne kafin mutum ya kai gaci yayi ta fuskantar kalubale iri-iri amma a zahirin gaskiya abunda su kayi basu kyauta ba ai abun ya shigo da cin zarafi kuma ni banga laifin yarinyar ba domin sanya ta sukayi su biya ta shiyasa na hana su Garba daukar mataki a kanta, ka kyalesu kawai kar ka tofa wata magana shiru ma magana ce, surutu kam da kace nace na jama'ar gari ka dauke kanka a kai idan sun gaji zasu bari amma kuma munanan kan bakanmu babu gudu babu ja da baya.....Ya dago jajayen idanunsa yana kallonshi yace."Wane irin mataki zan dauka kan yarinyar."? Khalifa yace."Kawai ka kyal....." Wasa ma kenan!!." yayi saurin katse shi ya cigaba da cewa"Wancan karon ta zage ni! kace in kyaleta wannan karon tayi min 'kazafi na zina abunda na tsana a rayuwa ta kace na kyaleta No! kai kanka kasan 'karya ne wallahi ba'a haka dani da farko na tausaya mata a matsayinta na 'ya mace kankanuwa yasa na rabu da ita na kuma bata damarta a siyance tayi abunda take so amma abun ya wuce gona da iri da gaske takeyi yarinyar kana maganar sata sukayi ko basu sata ba za tayi tunda bata kaunata yana da kyau in nuna mata asalin waye ni."!!
Khalifa ya sauke ajiyar zuciya yace."To yanzu kai me zakayi mata kake wannan maganar."? Kai tsaye yace."Auranta zanyi." Khalifa ya kalleshi da mamaki a fuskarsa....."Aure."!? yafada yana jimantawa....."Kwarai kuwa wannan ce hanyar da zanbi inci mutuncinta yanda raina ke so."Khalifa ya jinjina kai yana mamakin al'amarin yanzu duk tsayuwar ka da tsantseninka da bin diddiginka sai ka kare kan wannan yarinyar da bata da tarbiya." wani irin murmushi yayi kana ganinsa kasan na mugunta ne yace."Wai Khalifa ka mance waye Ahamdu ne? kai kana tunanin auran zanyi shine da manufa mai kyau! No! zan aureta ne kawai dan in nuna mata iyakarta." Khalifa yace."Sai nake ganin da ka sauya wata shawarar wannan ba tayi ba bana so ka auri yarinyar nan ka keta mata haddi sannan kuma ka saketa daga baya." Wani irin kallo yayi masa yace."Baka so na keta mata haddi ita ta keta nawa! kai kana tunanin wannan yarinya zaka sameta da wani Haddi a kanta tana daukar sunan budurwa ne kawai amma bata da maraba da bazawara so kar ka wani damu da wannan matakin da zan dauka zan aureta ne dan in cimma munufata a kanta harkar siyasa kuma babu gudu babu ja da baya da kaina zan dauketa in kaita tashar da taje ta gabatar da sharrin nata ta warware musu ku'lalliyar data 'kulla."
Khalifa yace."To ai shikkenan shawarar tayi ma'ana dan gaskiya nima yarinyar tayi mugun bani haushi na lura ta dauki lamarin da zafi kuma akwai kuruciya a tare da ita." Girgiza kai yayi yace."Koma meye a tare da ita ni zanyi maganinta sai 'kura ta lafa tukkuna zan sanya su Hadi suyi min bunkice a kanta dan na lura zaman kansu suke da mahaifiyarsu....duk inda iyayenta maza suke zan sanya a buncika min su."
Kira ya shigo wayarshi dake gefe guda a ajiye ya mika hannu ya dauka a nutse..."Hajiya Babba ce matar mahaifinsa ta farko Cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa babu walwala sosai yanda yaji muryarta a cunkushe yasan ta samu labarin abunda ke faruwa yace."Hajiya kunanan lafiya ko."? Ta amsa lafiya lau idan ka samu dama kazo gobe idan Allah ya kaimu zamuyi magana da kai." Yace."Shikkenan Hajiya Allah ya kaimu lafiya." Ta amsa da "ameen." Sallama sukayi ya kashe wayar yana kallon Khalifa yace."Zancan dai daya ne hajiya ta samu labari ko da yake ma'abociyar sauraran redio ce taji da kunnanta na riga nasan maganar da za tayi min kenan maganar aure wanda saboda maganar yasa na dauke kafata da zuwa gidanta duk zuwan da zanyi sai ta kawo min tallan mace wanda hakan ba ra'ayi na bane ni nafi so inga mace da kaina na aura ba sai an kawo min ba, magana dai duk ta 'kare gobe insha Allahu zan sanar mata da cewar na tsayar da matar da zan aura kalas."! Khalifa yace."Shikkenan kuma maganar Zainab ta tashi kenan dama kuma mune muke ta naci kana wulakanta mu." Yace."Khalifa ina jin kunyar Hafsa ne wallahi shiyasa ma zaka ga sau tari bana son zuwa gidanka saboda bana so ta dinga kallona da wata manufa tayi min alkairi na 'ki kar'ba, Zeey bata da makusa ta ko wanne bangare tayi kawai bana so in auri abunda baiyi min ba gudun shiga hakki ka basu hakuri da ita da kanwarta." Khalifa ya mike yana fadin"Ni zan wuce gida sai yadda ta yiwu mu bari gari yayi lafiya tukkuna sai muyi magana kan kazafin da akai mana." Ya mike yana fadin"Eh wannan ce shawara mai kyau.!!!!
To a ranar da al'amarin ya faru Wasila bata kwana a gidansu ba, domin mai girma gwamna najin irin 'baram'baramar da tayi sai kawai ya sanya security suzo su dauketa saboda yasan idan ta fito za'a iya ragargaza mata kai!! aikuwa hakan ce ta kasance da mabiya Ahamadu dan sun shirya tsaf sunyi dafifi a farkob titi suna jiran fitowar 'yar gaske da 'yan rakiyarta irinsu Camas! suyi musu tsirara su dake su...... da kyar Jami'an tsaro suka sha dasu Wasila ita kanta ta furgita da al'amarin.....Sai salati takeyi ganin yanda take hango jama'a da shar'ba! shar'ban makamai da bulalai! a hannunsu suna hayaniya da kiran sunanta wai duk ita suke nema wai!! tasan da sun ritsata kuma sai buzunta.
A daran mai girma governor yayi mata wanka ta 'yantu a siyance ta tashi daga 'yar banga ta koma cikkakiyar 'yar siyasa mai lasisi mai al'bashi kamar ma'aikaciya ya sanya mata miliyan hamsin a account dinta kana ya damka mata mukullin mota yar yayi ya bata dankareren gidansa dake tishama, gida na gani na fad'a cikin GRA babu abunda babu a ciki na more rayuwa........Mai girma governor yace ba zata koma gida ba tukkuna sai nan da sati biyu kura ta lafa tukkuna sai ta koma sabon gidanta tunda jama'ar gari basu sani ba hakan zaifi kwanciyar hankali itama sai taji wannan shawarar tayi mata saboda tana jin tsoro ta koma gida azo a kasheta da daddare sai ta kira Rashida a waya ta sanar mata da halin da ake ciki tace ta fadawa mahaifiyarsu ta kwanta da hankalinta duk wani alkairi da jin dadi na duniya sun samu." Da jin wannan magana da wasila tayi sai duk suka kwantar da hankalinsu ya tsumma a randa suka cigaba da rayuwarsu a hankali kwance.....Wasila da Camas! suka cigaba da zama a government house alhazawa nayi musu facaka da kudi Camas! sai tsikarar duniyarta takeyi da tsine babu abinda ya dameta Ita kuma Wasila sai kaf-kaf take da budurcinta duk 'kwakwar mai 'kwakwa dole ya hakura.
*** "Wai Bitan! Malam mai allo yasan abunda ke faruwa kuwa da zuriar d'an uwanshi Habibu wannan rayuwar dasu Uwani sukeyi ba rayuwa bace yarinya 'kankanuwa ta zama karuwar karfi da yaji gari ya dauka da maganar Wasila har wani kirari ake mata da *'Yar gaske!* yarinya karama ta fantsama kanta har siyasa yau ta zagi wancan gobe ta shiga redio ta zagi wancan tayi shigar banza ta fita a gari tana zubda mutunci ni ganauce ba jiyau ba sati uku da suka wuce na ganta tare da wani hamshakin mai kudi a mota yarinyar nan yi tayi kamar ma bata sanni ba ta dauke kanta."
Matar da aka kira da suna Bitan! ta gama gyara itacen dake cikin murhu ta karaso kan tabarmar da kanwarta ke zaune tace."Wallahi Kattime bamu san abunda ke faruwa ba kinga mu nan muna cikin karkara gashi sai muyi sati bamu kunna redio ba ballanta muji abunda ke faruwa a gari kune mutanan cikin gari kunfi mu sanin abunda ke faruwa amma bari malam din ya shigo sai ki fad'a masa abunda ke faruwa inyaso tin kafin abu yayi nisa yayiwa tufkar hanci." Haraja tace."Aikuwa ba zan tafi ba har sai naga shigowar malam gidanan na fad'a masa abunda yake faruwa dan wallahi ina jin tsoron yarinyar nan ta haifo d'a mara ido." Bitan! tace"Ai yamma tayi yanzu yanzu zakiga ya shigo kin san yamma nayi yake tashin al'majiransa su tafi bara sai kuma takwas na dare su sake zama." To kafin ma ta rufe bakinta sai gashi yayi sallama ya shigo cikin gidan.....Yana sanye da farin yadi babbar riga da 'yar ciki kanshi nan nad'e da koran rawani hannunsa rike da carbi fari tas! Bitan! tayi saurin mikewa tsaye tana masa barka da zuwa da sauri ta dauko masa buta wacce ke cike da ruwa ta mika masa asuwaki ya fita waje domin daura alwala lokacin sallahr magariba ya gabato dalili shine limamin babban massalacin dake 'karamar hukamar Garko.
_Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/17, 9:28 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*PEGE DIN NAKU NE* 👨👨👧 *MYSON, NAJIB SA'ID* Tare da kai da *LAWAN RANO* Nagode kwarai da kulawar ku akan wannan book din Allah ya 'kara kauna ya baku mata na gari👏🏻 ~~~~~~~~~~~~~~~~
*Free Pege14* To ganin Malam mai allo ya nufi masallaci yasa suma suka daura alwala domin gabatar da tasu sallahar kafin ya shigo gidan su tattauna abunda yake faruwa, suna zaune kan tabarma ya shigo bakinsa da sallama kamilin mutum ne wanda karatun al'kur'ani ya ratsa shi fari tas dashi kana ganinshi kaga bafulatani usul......Bitan! ta gyara masa tabarma ya zauna yana fad'in"Ashe bakuwa mukayi a gidan Hajara kece kike tafe."? Ta amsa da "Eh wallahi malam tun kusan azuhur nake gidanan Bitan tace min kana tsangaya tare da yan makaranta malam ya gida ya damuna dafatan duk mun same ku lafiya."? Ya aje carbin hannunsa a gefe ya amsa da fadin" Lafiya lau Haraja ya yara ya mai gidan naki."? Duk sunan lafiya kalau wallahi ai yace ma a gaishe ku da kyau."! To masha Allah muna amsawa amma dai za kiyi mana kwana biyu kafin ki koma." Murmushi tayi "A'a malam gobe nake sanya ran komawa dama muhimaniyar maganace ta taso wanda shi mai gidan nawa ne ma yace lallai nazo na shaida maka abunda ke da akwai." To Allah yasa alkairi Hajara ina sauranki." Malam mai allo ya gyara zamanshi yana fuskantar Hajara wacce ta soma warware masa abunda ke faruwa ga iyalin Dan uwanshi Yahuza mai rasuwa.........Ta kara da cewa"Malam yana da kyau ku sanya ido sosai kan wannan yarinyar domin a gaskiyar magana abun da takeyi ya soma wuce gona da iri watarana zata dauko muku abin kunya ko kuma taje ta zagi wani babban mutumin da zai daureku gabadaya yau da al'amarin ma a kanta zai tsaya da sauki wani abun idan ta dauko to ku da bakuji ba baku gani ba sai ta shafeku wannan shine dalilin da ya sanya nace to bari nazo na fada muku halin da ake ciki."
Malam mai allo yayi shiru yana jimanta al'amarin, to har yausha hakan ta faru basu sani basu sani ba ko da yake hakan zata iya kasancewa tunda bayan rasuwar Yahuza rigima suka dinga tafkawa da Uwani mahaifiyar yaran kan dole sai an raba gado an bata na yaranta shi kuma yace ko za'a raba gado to ba za'a bata na yara saboda ita mace ce su kuma yaran lokacin suna yara kananu za dai a siyar da gona a raba kudi kaso biyu shi ya dauki kashi daya sauran kuma ya zama magada wato Wasila da Rashida kenan in yaso ita sai a fitar da ita na tuminin takaba kamar yanda addini ya shara'anta.....Nan ma sai ta tada ballin masifa taje 'yan uwanta suka zugota tazo tana yiwa su malam rashin kunya wanda hakan ya janyo sukayi mata fatata fatata! sannan suka kwace su Wasila daga hannunta, kwana biyu da faruwan lamarin Wasila dake tana da wayo a lokacin ta kai kimanin shekaru goma sha biyu sai ta fakaici malam din ya tafi tsangaya ra rike hannun kanwarta suka gudu da malam ya dawo ya samu labari yace."Suje idan shine sai sun tako da kafafunsa sun neme shi, to hakance ta kasance koda su Wasila suka koma gaban mahaifiyarsu sai wahala tayi tsanani a garesu da kyar suke ci daya a rana Wasila itace yawon bin gidajen amare tana musu wanke wanke da raino da share share su bata kudi da abinci ita kuma Uwani itace aikin wankau da dakau da sauransu.....Wasila ta yanke shawarar tun karar wan mahaifin nasu domin su bashi hakuri suka shirya tsaf suka nufi Garin nasu Garko!! Malam ya dinga musu fad'a sosai yace."Duk tsiya dai nine mahaifinku tunda babu ubanku kuna bin shawarar mahaifiyarku kuna bijere ma dangin ubanku to ko auranku ake nema gurinmu zaku zo gwara ku nutsu kuyi hankali ku zauna tare damu zaman ku cikin wannan gida ku kadai bai dace ba saboda haka na yanke shawarar zan baku daki daga ku zauna har Allah yasa ku samu mijin aure ita kuma Uwani ta tafi gidansu itama bata wuce aure ba idan ta samu miji tayi aure....Da jin wannan magana ta malam mai allo sai su Wasila suka yanke sgawarar guduwa domin a ganinsu yanda suka saba da zaman birni zasu cutu a kauye....Washe gari Uwani ta tasa kan 'Yayanta da asuba suka gudu....Wannan abu da sukayi ya batawa malam mai allo rai tun daga lokacin ya dauke hannunsa daga kansu idan ma sauran 'yan uwa suka kawo masa maganarsu sai ya koresu yace kar wanda ya sake kawo masa maganar wadannan yaran marasa kunya suje duniya ce zata koya musu hankali.
*Wannan kenan*
Malam mai allo ya kalli Hajara yana girgiza kansa yace."Hakika naji dadi da kukayi gaggawa zuwa ku sanar dani wannan al'amari dake faruwa, wannan rashin tarbiyar ne yasa tuntuni na hana Yahuza tafiya maraya da zama saboda nasan tilas a haifi da mara ido a lokacin ya rufe ido yaki sauraran kowa shi dai kawai ya tafi burni ya nemi kudi karin abun kuma ya hadu da mata mara kamun kai ya aure ai asalin lalacewar yaran daga mahaifiyarsu ne da ta basu tarbiya da duk haka bata faruwa ba mu kanmu Uwani bata ganin girmanmu ballanta tana nuna musu muhimancimu a gurinmu, amma babu komai insha Allahu gobe tare zamu tafi kome za'ayi kafata kafar yaran nan dan bazan bari su lalace ba ace muna kallo nan zan kawo su duk in aurar dasu kowa ya huta."
Hajara tace"Wannan shawara taka itace abun dubawa Allah ya tabbatar mana da alkairi." suka amsa da "ameen" gaba d'ayansu.
To kamar dai yanda malam mai allo ya fad'a hakane ya kasance da wurwuri yayi sallama da 'yan uwa ya fad'a musu abunda ke faruwa suma suka bada goyon bayan kan hukumcin da ya yanke, kana suka hadawa Haraja sha tara ta arziki suka bita da godiya da fatan sauka gida lafiya.
Uwani da Rashida kadai ne a gidan sunci kwalliya har sun gaji kamar wanda zasuje gidan buki ga cefane nan kayan miya da nama cikin takarda za'ayi miya gida sai kamshi yake yi....Amina na kwance a tabarma tana danna katuwar waya Uwani na kicin tana aiki Malam mai allo yayi sallama a kofar gidan.....Gaba d'ayansu sai da gabansu ya fadi! Uwani ta fito daga kicin da ludayi a hannunta tana fad'in"Ke Rashida muryar wa nakeji kamar ta wannan masifaffan tsohon."! Rashida tace"Wallahi nima irib muryarshi naj......Kafin ta karasa muryarsa ta sake karad'e gidan "Salamu alaikum."!! Uwani ta amsa da karfi tana fad'in" Waye wai yake rangwada mana sallama kamar munci bashi."
Malam mai allo ya girgiza kansa jin muryar Uwani radau! yasan zata aika tunda dama ba kunya gareta ba......"Nine malam mai allo na Garko."! Yafada yana dafe kyauran kofar gidan.
"Ayyo koda naji wannan sallama haka to ana zuwa." Uwani tafada tana jan karamin tsaki." Ta kalli Hajara "Ai sai ki tashi kije kece tilas dinsa ni kuwa yace zai min wannan wa'azin sai dai mu kwashi 'yan kallo ni dashi a unguwar nan."
Jiki a sanyaye Rashida ta mike ta dauki yalolon mayafinta dake kan igiya ta yafa, duk rashin kunyarsu suna shakkar malam mai allo dan baya musu da sauki.........Tana fitowa ta durkusa tana gaisheshi bai amsa ba sai kare mata kallo yake ganin irin dinki dake jikinta atamfa ce duk an kacalcalata saman nonowanta duk a waje......Girgiza kansa yayi yace"Rashida kece kika dawo kamar ba d'iyan musulmai ba wannan shigar ta jikinki ta sabawa sharia meye abun burgewa anan.? to babu komai duk magana ta kare kiyi maza ki kirawo min daya marakunyar yanzu yanzu zan tasa ku a gaba mu wuce garko saboda na samu labarin ashararanci da kukeyi a gari mahaifiyarku na daure muku gindi kuna yiwa manya mutane rashin kunya wai Wasila ce take siyasa tana gogayya da maza saboda kasa ta rufe idon ubanku shiyasa annabi yace ka zabawa 'yayanka mace tagari duk dan gudun faruwar irin wannan, mu ba'a son ranmu dan uwanmu ya auri mahaifiyarku ba saboda sam bata da tarbiya gashi kuma kun dauko irin nata halin to kome zakuyi sai da kuyi amma tilas ku koma can Garko da zama idan Allah ya kawo muku miji kuyi aur......"Babu wanda ya isa ya rabani da 'yayana wallahi akan wannan sai in maka mutum a kotu."!!!!Uwani ce ke fadar wannan maganar ashe tana la'be tana jinsu......"Haka kawai zaka zo har gida kana zagina malam ka rike mutuncinka da girman ka ada can ma ban yarda ba ballanta yanzu da nasan ina da 'kumbar susa a hannuna dan haka ni banga wanda ya isa ya rabani da 'yayana ba."
Malam mai allo yace."Uwani rashin kunya za kiyi min."? Wannan ba rashin kunya bace gaskiya ce, sai da yarana suka girma suka zama mutane inacin ganiyarsu sannan za'a lalla'bo kawai saboda an samu labarin mun faso gari ace ga zance ga magana kafad'i idan kana bukatae wani abu yanzu yanzu sai na kira Wasila tayi maka hasafi ba wai kace zaka tafar min da 'yaya kauye ba."
Malam mai allo 'kwalla ta taru a kwarmin idonsa yace."Baku da kudin da zaku bani Uwani kuma kinyi min abunda yafi haka dan kin zageni a yanzu ba wani abun bane ni dai na gama yanke hukunci ke Rashida idan na isa daku maza jeki had'o kayanku muka kama hanya mu tafi.".
Rashida ta mike ta shiga cikin gidan tana kuka wayarta ta dauka ta kira Wasila ta fada mata abunda ke faruwa.....Wasila tace''Kome zaiyi kar ku sake ku bishi ku kyaleshi a soro idan ya gaji da tsayuwa ya gaji ya tafi masifaffan tsoho kawai." Uwani kuwa taja tunga ta tare bakin kofa ta rantse babu inda zai tafar mata da 'yaya......Suka dinga tafka rigima da Malam mai allo Uwani ta dinga yi masa rashin kunya kamar ba wan mijinta ba har hankulan mutane ya fara dawowa kansu mutane suka fara taruwa a'lamarin yayi wa malam ciwo a ranshi sai ya fito waje ya tsaya yana tsumayin fitowar Rashida ganin ya fita daga gidan sau kawai Uwani ta rufe kofar gidan ta zura sakata ta koma ciki tana surutai "Idan ka kaji da tsayuwa ka tafi tsoho mai nacin tsiya kawai..........Garba dake can gefe suna magana da wani mutumi ya nuna masa malam mai allo dake bin kofar gidan da kallo yana mamakin rashin kirkin Uwani wato shi suka rufewa kofa, sai ya sanya gefan babbar rigarsa yana goge gumin saman goshinsa.....Garba ya karaso inda yake hannu ya mika masa suka gaisa yace." Aramma idan ba zaka damu ba ina so mu tattauna wata magana da kai." Malam mai allo dake neman wanda zai rarrashe shi kan abunda su Uwani sukayi masa yace."Babu komai yaro ina sauraranka." Garba yace."Muje mota arrama." Malam mai allo baiyi shakkun bin Garba ba saboda lokaci guda yaji ya aminta dashi suka nufi inda yayi parking din motar a tare.
_Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/18, 2:01 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*PEGE 'DIN YAU NAKI NE* *Real Eshaa🌺* Marubuciyar book d'in. *NAGA RAYUWA* Fatan alkairi har karshen rayuwa aysha Allah ya kawo miji nagari wanda zai rike min ke tsakani da Allah👏🏻 ~~~~~~~
*Free Pege15* Cikin nutsuwa Garba yace."Aramma alamu sun nuna kamar kana da ala'ka da masu wancan gidan, dan Allah idan babu damuwa ina so in san wani abu dangane da wata yarinya a gidan mai suna Wasila." Malam mai allo yace."Ni a matsayin mahaifi nake a gurin Wasila da kanwarta Rashida Yahuza mahaifin yaran kanina ne ciki daya muka fito kuma mu 'yan asalin garin garko ne Yahuza yazo kano neman kudi tun yana saurayi sai ya sai gida yayi aure tare da wannan matar wacce ta kasance a matsayin mahaifiyar su Wasila da Rashida......Garba ya katse shi ta hanyar fadin"Alhamdullhi dama abunda nake so naji kenan ashe faduwa tazo dai-dai da zama malam idan babu damuwa zamuje can gidan ubangidana wanda shine ya sanya ni nayi masa bunkice akan asalin iyayen yarinyar to kuma sai nayi katarin had'uwa da kai, kar kadamu arrama idan mun isa sai kayi masa cikakken bayani akan yarinyar." Malam yace."Yaro ina fata dai ba laifi yarinyar tayi ba domin nima abunda ya taso ni kenan saboda na samu labarin cewar tana cin mutuncin manyan mutane a gari tana fakaicewa da siyasa wannan shine dalilin zuwa na garin." Garba yace."Kar ka damu arrama alheri ne insha Allahu muje koma meye zakaji daga bakin mai gidana." Malam yayi shiru yana nazari yana tsoro kar daga zuwan sa ya shiga masifar yarinyar nan tasa a daure shi baiji ba bai gani ba....Girgiza kai yayi yace."Babu damuwa samari muje kawai Allah yasa alheri ne." Garba ya kunna motar yaja suka futa daga cikin unguwar.
Suna tare da Khalifa a harbar gidanshi suna hutawa motar su Garba ta shigo cikin gidan.....Can parking spece ya nufa yayi parking din motar ya fito ya budewa malam mota yana fitowa Idanun Ahamdu suka sauka a kanshi A fuzge yaga suna kama da yarinyar babu tamtama wani nata ne amma babu shakka Garba ya iya aiki bai dauka futa ta farko za'a samu nasara ba to amma yanda yaga kamilin mutum sai yasha jinin jikinsa anya wannan kudi zasu rud'ashi ko dai ya sauya wata hanyar ne dan baiga alamar zalama ta kudi a idon dattijon ba......A nutse ya mike yana masa barka da zuwa dake suna zaune a wata rumfa wacce aka kewaye ta da wasu kujeru masu kyau tsakiyar kujerun katon teble ne da lemuka akai kana ganin gurin kasan na hutawa ne....Malam mai allo ya zauna nutse suka gaisa cikin girmama juna......Garba yace."Yallabai Allah ya takaita mana wahala ina zuwa unguwar nayi katari da wannan bawan Allahn shine yake shaida min shi din shine mahaifin Wasila shima zuwanshi kenan garin to anan na nemi alfarma a gurinshi kan yazo kana son magana dashi."
Cikin girmamawa Ahamadu yace."Alhamdullahi naji dadi da hakan ta faru dama ni nafi so nayi magana baki da baki da mahaifin yarinyar dan haka Garba kana iya tafiya babu damuwa." Garba ya bar gurin yana godiya....Ahamadu ya sake mikewa Malam hannu suka sake gaisawa Yace."Malam kan maganar wannan yarinya ne Wasila.'' Malam mai allo ya kalli Ahamadu ganin nutsuwa da kuma a kamala a tattare dashi ya sanya hankalinsa ya kwanta yace."Alhaji ina fatan dai yarinyar nan ba wani laifi tayi muku ba dan wallahi dukkanin abunda takeyi bamu sani ba tunda bama tare dasu labarin abunda takeyi ne ya iskemu hakan ya sanya hankalinmu tashi, muka yanke shawarar zuwa domun mu tattara su mu koma can inda muke da zama dama kuma zamansu hakan bai dace ba a matsayinsu na 'yaya mata komeye zai iya faruwa da rayuwarsu.