Kenza eBookz

'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale - Chapter 6

'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale - Chapter 6

'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale Chapter 6: 'yar bangar siyasa book1 by bintu umar abbale Chapter 6. Khalifa yace."Kwarai kuwa malam muma…

4,457 words

Khalifa yace."Kwarai kuwa malam muma abunda muka hango kenan ya sanya muka sa ayi mana bunkice akan asalin yarinyar sai kuma Allah ya takaita mana lokaci guda kazo gari ashe ma ba a kurkusa kuke ba." Malam yace." Mu 'yan karamar hukumar Garko ne Yahuza mahaifin yaran ciki daya muke dashi mu hudu iyayenmu suka haifa ni ne babba sai Habibu sai shi Yahuza sannan kanwarmu Kattime To shi kadai ne ya tsalle a cikin mu ya tawo nan yake sana'oinsa har Allah yasa ya samu sana'a ya siyi gida kana yayi aure ya hayayyafa yanzu shekaranshi Takwas da rasuwa bayan karamar jinyar da yayi wanda muma sai labarin mutuwarsa mukaji......Dalili kenan da ya sanya nazo da kaina na dauke yaran har da ita mahaifiyar tasu na tafi dasu can garin namu ko sati daya ba suyi ba suka gudo........Tiryan tiryan Malam ya zayyane musu rayuwar dasu Wasila suka dinga yi tun farkon mutuwar mahaifinsu da irin rashin kunyar da mahaifiyarsu ke sawa suyi musu da yanda shi kuma yayi zuciya ya zare hannunsa daga kansu....Sai wannan karon da yaga abun yayi tsamari ya sanya yace bari ya dauki mataki na karshe kan abunda sukeyi.

Ahamadu yace."Arrama yanzu idan ka tafi dasu can Garkon kana da wanda zaka bawa auransu ne."? Malam yace."Ba za'a rasa ba Alhaji kasan shi auran karkara ba'a tsawwala da yawa insha Allahu sati biyu ba zasuyi a gida ba zab daura musu aure."

Yace."To idan babu damuwa ni ina son abani auran babbar kuma bana so a ja dogon lokaci idan da hali wannan juma'ar mai kamawa nake so a daure aure."

Malam yace."Alhaji da dai 'karamar ka dauka dan sai naga kamar tafi babbar hankali hankalin ka zaifi kwanciya da ita karamar." Yace."Kar ka damu malam shi aure ni'ima gareshi watakila ta sanadiyar auran namu sai kaga tayi hankali fiye da tunani mai tunani idan da hali a amince mun in bada sadaki na yanzu." Malam yace."To to ai babu damuwa nima zanfi jin dadin hakan kaga sai in koma gida da karfin gwiwa ta kuma in sanar da 'yan uwa abunda ke faruwa."

Ahamadu yace."Kwarai naji dadin yanda ka yarda dani ka amince min auran yarinyar da wuri ba tare da kaga waliyai na ba insha Allahu ranar juma'a zamu zo tare da kanin mahaifina Wanda shi kadai ne ya rage min a halin yanzu kasancewar nima tun ban kai matsayin wannan shekarun ba mahaifina ya rasu na rayu tare da yan uwansa wannan kuma da kake gani a zaune kusa dani abokina ne sha'kikina tare mukayi karatu kuma muke harkokinmu a tare insha Allahu tare zamu zo dashi ranar juma'a."

Malam yace."To masha Allah Alhaji ai ni ganin farko da nayi maka naji hankalina ya kwanta da kai wallahi babu d'ar! zan baka auran Wasila koda banga Waliyinka ba nasan zaka rike mun ita da kyau da amana, babu abunda zance sai dai ince Allah ya saka da alkairi saboda ka gama min komai tunda har ka yarda zaka auri wannan yarinya." Ahamdu yace."Babu damuwa malam, ai an riga an zama daya kuma Allah dai ya kara girma." Mikew yayi ya nufi cikin gidan..........mintuna goma yayi a ciki ya fito hannunsa rike da wata doguwar takarda dake cike da kudi." Ya mikawa malam na fad'in"Wannan shine sadakin Wasila malam."

Malam ya kalli uban kudin da ya mika masa sai ya girgiza kai a nutse yace."Ashe baka so auran yayi albarka ba Alhaji Annabi Muhammdu SAW yace."Mafi albarkar aure shine karamin sadaki wannan da yayi yawa duk da ban lissafa na gani ba amma idona ya gane min kudi ne masu yawa, saboda haka dubu biyar kacal zaka biya sadakin wannan yarinya."

Ahamadu yace."Malam ka ka'rba don Allah ai ba wani kudi masu yawa ba dubu dari ne kacal kuma kasan dai yanda kudin mu suke basu sa wani daraja kar damu insha Allahu aure zaiyi albarka."

Malam yace."Shi dai ba zai kar'bi wannan zunzurutun kudin ba a matsayin sadakin Wasila ya fiso idan yayi mata aure ta zauna mutuwa ce zata raba.....Ahamadu da Malam suka dinga ta'kardama da jayayya shi ya dage sai ya 'karba shi kuma yace ba zai kar'bi dubu dari ba dubu biyar zai 'karba....Khalifa ne ya raba gardama ya ciro kudi daga jikinsa dubu goma ne ya irga dubu biyar ya mikawa Malam yace."Ga sadakin Wasila daga Ahamadu." Malam ya sanya hannu biyu ya kar'ba yana fadin"Ubangiji Allah ya tabbatar da alkairi Allah ya basu zuria mai albarka." Khalifa ya amsa da "ameen rabbi malam muna godiya da karamci."

Ahamdu yaji haushin abunda khalifa yayi masa amma bai nuna ba sai ya aje takardar kudin kan teble din gabansa dauki wayarshi ya kira Garba......Garba na zuwa yace maza ya fito da mota ta zuba kayan abinci komai da koma yazo ya dauki malam ya kaishi har Garko Garba ya wuce da sauri domin aiwatar da aikin da aka sa shi. Ahamadu yace."Malam yanzu Garba zai kai gida maganar su Wasila kuma da kaina zan sanya a kai maka su har inda kake daga gobe jibi insha Allahu." Yace."To Alhaji Allah ya saka da alkairi ya biya dukanin bukatu na alkairi."

Bayan tafiyar Malam mai allo Khalifa ya kalli Ahmadu yace."Na lura wannan dattijon na arziki ne wallahi sai duk naji jikina yayi sanyi musamman yanda naga ya tsaya kai da fata akan ba zai kar'bi wannan kudin da ka bashi a matsayin kudin sadaki na fahimci yana so auranku da yarinyar yayi albarka wanda kai ba haka abun yake ba a zuciyarka, dan Allah ka kar ka watsa wa mutumin 'kasa a ido ka rike yarinyar nan amana ko dan saboda karamcinsa kamar yanda ka fad'a masa watakila ta sanadiyar auran sai kaga tayi hankali duk abubuwan da suka faru a baya su wuce kamar ba'ayi ba."

Shiru yayi yana nazarin maganar khalifa din yace."Nima jikina yayi sanyi lokacin da naga mutumin sam! ban dauka zanga kamilin mutum daga bangaran yarinyar ba ashe ta fito daga tsatso mai kyau gaskiya wannan mutumin ba duniya ce a gabanshi ba ka duba ka gani kudi a wannan zamanin sam basu gabansa wasu iyayen da suke so in kaje neman auran 'yayansu ka sakar musu kudi a gurinsu hakan burgewa ce, shi kuma na lura albarka kawai yake nema."

Khalifa yace."Shine ai shawarar da nake baka rike masa yarinyar shine zai sanya ya tabbatar da cewa kai d'in mutumin kirki ne.""

Murmushi yayi yace.''Kai nifa ina nan kan bakana wallahi! sai naci uban yarinyar nan wallahi in keta ta kuma in saketa."

Khalifa yace."Subahanallahi! wai me yasa kake hakane? ka sani kake takewa yanzu meye amfanin hakan da za kayi."? Sosa kanshi yayi yace."Ai kai dama ba za kaga amfani ba saboda ba kai akayi wa auran nan da zanyi zanyi shine da manufofi da dama kaga na farko zan tashi daga sunan Gwauro kamar yanda ta fad'a zata zame min garkuwata a siyance na biyu zan dawwamar da rayuwarta a cikin 'kunci da ba'kin ciki in takure ta guri guda in muzguna mata har sai ta durkusa gwiwa bibbiyu tana bani hakuri na uku kuma na taimake ta daga wannan yawace yawacen banzan da takeyi a gari tana zubda mutuncinta na killace ta a guri guda....Na hudu kuma auranta zai wanke ni daga zargin da tasa jama'ar gari suke min....Ita ta nufe ni da sharri ni na saka mata da alkairi kaga anan jama'ar suka ji labarin na aureta za tasha tofin ala tsine da zagi sannan ita da harkar Siyasa har abadah! na biyar bukatata ta biya na raba abokanan adawata da ita tunda yanxu kamar itace a matsayin yarinyar su wacce suke sanyawa nayi musu abu ba tare da shakkar kowa ba, nasan kafin su samu 'yar siyasa mai mutukar a'kida irinta za'a sha wuya, kasancewar siyasarmu ta yanzu ta zama sai a hankali duk inda mutum yasan zai samu nan zaije hakanan za kagansu yau su zagi wancan gobe su zagi wanannan sam basu da gwani mutum in dai zaka bashi na 'batarwa shikkenan magana ta kare, amma ita yarinyar ns fahimci ba wannan ke gabanta ta tsaya bangaransu su kadai shiyasa suka riketa hannu bibbiyu saboda sun lura abokiyar tafiya ce....Kuma kasan ba zasu ta'ba bari tayi aure ba zasuyi ta bata kudi tana shirme a gari rayuwarta ta lalace a banxa a wofi.''''' Khalifa yace."Kayi tunani me kyau gaskiya amma dai duk da haka don Allah ka sassauta mata idan ta shigo. Murmishi ya saki mai dauke da manufofi da dama ta'be bakinsa yayi yace."Kana 'bata bakin ka ne khalifa yanda yarinyar nan tasa ni 'bacin rai itama ranta sai ya 'baci."

_Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/18, 10:18 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free Pege16* Uwani ta fito daga kicin tana fad'in"Da alama dai mutumin nan ya gaji da tsayuwa ya tafi haba! jama'a wai babu dama aga Allah ya rufawa mutun asiri sai a dinga bakin ciki! kiga mutum da rigima haka kawai ka ni'ko gari gari ya gari kazo kace zaka dauke min 'yaya saboda munafurci nasan magulamata ne suka kai masa gulma shine shi kuma ya bazamo babbar riga yazo har gidana ya nuna min iko to ni babu wanda ya isa yace zaiyi min iko da 'yayana 'yan uwana ma ban d'agawa 'kafa ballanta wani saboda haka ke Rashida maza maza ki kira Wasila a waya kice tazo yau d'in nan ta dauke mu a mota mu bar nan tunda har wannan tsohon ya soma zuwa shikkenan kuma zai ta daga mana hankali gwara kawai a nemu mu a rasa a unguwar." Rashida tace"Ni wallahi tausayinsa nakeji gaskiya Uwani banji dadin abunda kikayi masa ba Kamar uba yake a gurinmu kin tozarta shi a unguwa." '' Ayyo kina so ki nuna min kinfi kaunarsa a kaina ni dana tsuguna na haifeki naci kashinki da fitsarin ki shine zaki butulce min shi me ya ta'ba tsinana miki a rayuwa." Rashida tace"Wallahi kafin babanmu ya mutu ya fada min lokacin da aka haifeni da ya rasa yanda zaiyi da hakika can kauye ya nufa gurin Malam mai allo din ya bashi katuwar tinkiya aka rada min suna da ita." Uwani tayi kasake tana kallon 'yar tata ashe kafin mijin nata ya mutu sai da ya fada musu abubuwan da suka faru a baya....."To ai hakika dama dole ce a wuyansu take idan basuyi ba ai sai a kira ki da shegiya gwara ma ki daina wannan magana dan bayan ya bada tinkiya anyi miki rad'in suna babu abunda ya kuma tsinana miki." Rashida tace."Gaskiya dai ki daina ci masa mutunci." Uwani ta fashe da kuka tana fadin"Sai ki zageni Rashida ki fito fili kawai ki zageni yau naga matsayina a gurin ki shiyasa ni Wasila tafi min ke sau dubu duk abunda tasan za tayi ta faranta min rai shi takeyi duk abunda nace tayi tana yi min babu musu ke kuwa fa sai dai ta nemo kudi kina daga kwance kice, to duk rashin mutuncin da kikeyi min sai na fada mata." Tana gama maganarta ta shige daki tana matse hawaye.....Wayarta ta dauka da Wasilan ta siya mata ta hau kiranta....Lokacin suna tare da mai girma governor suna meeting Wasila taga kiran amma bata dauka ba sai bayan sun fito daga dakin meeting din ta kira ta....Uwani na daga wayar ta fashe da kuka "Wasila maza ki zo gida Rashida na nan tana min rashin mutunci duka na ne kawai ba tayi saboda zuwan Malam mai allo."

Rai a 'bace! ta kashe wayar ta nemi numbar Rashidar.....Rashida ta daga wayar tana zumbura baki "Wallahi Rashida ki shiga hankalin ki! dan Kutumar ubanki me malam mai allon ya tsinana miki da har kikewa mahaifiyarki rashin kunya har kin manta irin wahalar da tasha akanmu ashe dama kika bawa malam din yaci mata mutunci kamar yanda ya saba to wallahi sai ranki yayi mugun 'baci! kan hakan." ''Aunty Wasila ki saurara kiji abunda yake faruwa." Rashida ce ke ta magana amma taki sauraranta sai zaginta take cikin jin haushi ta kashe wayar....Wasila ta tsaya tana mamaki! lallai Rashida bata da mutunci ta gama wahala da ita amma ta kashe mata waya....Mahaifiyar tasu ta kira tace"Kinga Uwani na soma zargin yarinyar nan wallahi harda hadin bakinta gurin zuwan Mai allo gidanan dan haka hankalina ba zai kwanta ba komai dare zan shigo unguwar in daukeku ku zauna cikin shiri." Uwani tace"Nima dama shawarar dana yanke kenan dan tunda malam din yazo nasan sauran ma suna tafe haka kawai su rusa mana rayuwa waye zai koma kauye ya zauna? sai dai duk abunda zasuyi suyi." Duk dai magana ta kare ku zauna cikin shiri." Uwani tace "To shikkenan sai kinzo." kashe wayar tayi ta iske inda Camas take zaune tana kallonta.

Har kusan karfe goma da rabi na dare Garba na layin su Wasila cikin matasa yayi basaja so yake yaga ta inda Wasila zata 'bullo, shiru asalima tunda ya zauna ko kare bai gani ba a bakin kofar gidan nasu.....Yananan zaune mutane suka fara raguwa saboda dare kowa na tafiya gida shima sai ya yanke shawarar tafiya dama a Mashin yazo roba roba ya sanya mukuli zai kunna kenan ya hango tawowarsu Wasila jikinta sai walwali ya keyi kasancewar material din dake jikinta mai kyalline wani bala'in kamshin turare ya bakunci hancinsa lokacin data giftashi ta suka shige ita da Camas! wace ta nufi gidansu ita kuma ta hau buga kofar gidan......Matasan dake kusa dashi ne suka fara magana kasa kasa..."Shegiya karuwa kawai ina su Mado nanan da sunci ubanta ta gama guje gujen ta dawo karuwar banza da wofi! ai sai munci ubanta wallahi." Zaginta sukeyi suna kwashe mata albarka garba na jinsu bai ce komai ba yana nan zaune yaga sun fito ita da sauran mutanan gidan.....Gidan suka kulle suka wuce simi simi kamar munafuka...nan yaji matasan dake kusa dashi na fad'in"Ai babu matsiyaciyar uwa sama sa wannan matar duk itace ta sanya ta take wannan rashin mutuncin dazu fa wan mahaifinsu ne yazo suka rufe masa kofa ai wallahi mun kusa tashin su daga unguwar nan." "Kai kasan me zamuyi ma yanzu."? girgiza kai yayi yace." Kone gidan zamuyi dan uwarsu in sun dawo su kwana a waje." Kai wannan shawara tayi kyau abokina." Tafawa sukayi suka mike tare.....Garba ganin sun bar gurin sai shima ya hau mashin dinsa yabi bayan su Wasila can ya hangosu tsallaken titi inda tayi parking din motarta suka shiga a take ya bi bayansu amma yanda yake binsu a hankali ba zasu dauka su yake bi ba.

Dake unguwar masu hannu da shuni ce ko ina haske babu duhu da tarin kazanta daga can bakin titi Garba ya tsaya ya kafe mashin dinsa a hankali yabi bayan motar inda yaga ta nufi wani estete wanda manya manya mutane ke zaune a ciki Garba yayi mamaki sosai babu shakka yarinyar samu kudi ganin motar ta tsaya a bakin gate din wani tangamemen gida ginin zamani, yana kallo mai gadi ya bude gate din ta shigar da motar ciki, sai ya juya da sauri ganin sucurity na nufowa inda yake, da sauri ya tashi mashin dinsa ya bar gurin a guje......A daran ya shaidawa Ahamdu unguwar da Wasila take sam baiyi mamaki ba saboda yasan zasu iya yi mata abunda yafi haka, kudi ne gasu nan a banzace ayi abunda ya dace an'kiyi ana watsar dasu a banza a wofi jirgin sama ma zasu iya siya mata mutukar bukatarsu zata biya.

Uwani da Rashida suka gigice ganin ubangidan da Allah ya mallakawa Wasila suka dinga shige da fice a gidan suna ta'be ta'ben abubuwa Uwani dai kusan zautuwa tayi saboda ta masifar rudewar da tayi taga uwar daula da duniyar da 'yarta ta cikinta ta samu.....Wasila tace "Ko wanne ya dauki daki daya ya ishe shi bukatar rayuwarsa Uwani kinga Abunda Allah yayi mana ko? da kina cewa muje muyi karuwanci shine zamuyi kudi da gaggawa to wannan sana'a da nakeyi mutukar ta karbe ka nan take zakayi arziki yanzu ina da kudi cikin account dina da ban san a dadin su ba kullum 'yan fadar mai girma governor tura min kudi suke bamu da matsalar komai a halin yanzu Allah ya yaye mana kuncin talauci ba tare da mun aikata sa'bo ba.

Uwani tace" Sai yanzu kuma na gane abunda kike nufi Wasila wallahi ni a daukata yanzu babu abunda ke saurin kawo kudi da gaggawa kamar karuwanci ashe akwai sana'ar da tafi wannan to Allah nagode maka da bai sa kun dauki gurguwar shawarar da nake baku ba."

To a ranar dai da kyar su Uwani sukayi bacci dan Wasila dakinta ta shige tayi wanka tayi kwanciyarta bacci mai dadi ya dauketa........A furgice! ta bude idonta tana salati! ta sanya hannu ta kunna fitilar gefan dago tana bin dakin da kallo kamar me neman wani abu....Kafafunta ta zuro kasa suka sauka kan kafet, ta jima a haka kafin ta mike ta nufi toilet fitsari kawai tayi ta dawo ta kwanta ta rufe jikinta da bargo amma banda fuskarta ta kasa kashe fitilar dakin tayi domin gani take kamar zai iya mamayarta kamar yanda ya mamaye ta cikin mafarkinta na yanzu, Tun da take a duniya ba ta'ba ta'ba mafarki wani d'a namiji ba sai yau! shin wai wannan mafarkin me yake nufi ne? meye ala'karta da wannan guy? ita dai tasan ba'kar gaba ce tsakaninsu to mai zai sanya yazo mata a mafarki yana mata murmushi saboda kuma tsabar wuce gona da iri har ya rungumeta yana tatta'ba mata sassan jikinta....Tayi sauri ta sanya hannunta a ramin cibiyarta sai taji tamkar hannunsa ne a gurin a lokacin da yake shafa mata cikin mafarkinta, jin tsigar jikinta ns tashi ya sanya tayi gaggawar cire hannunta daga gurin.....Rufin dakin ta tsurawa ido, itafa wannan mafarkin ya bata tsoro har yanzu tana hango fuskarsa da tattausan murmushi, shin wai abunda tayi masa bai dame shi bane da har zai zo yana mata murmushi, ita ta dauka zasu kulla gaba ne ita dashi wacce tafi ta da tsanani!!!!!!! Juyawa tayi ta rungume pillow tana lumshe ido....."Subahanallahi." Hannunsa taji a jikinsa ta mike a zabure! tana dube dube a dakin........Yau satin ta daya a gidanan amma bata ta'ba shiga tsoro da farga ba irin na yau! mikewa tayi ta zura hijab! ta bude dakin ta futa....Dakin da su Uwani suke nan ta nufa, gani take kamar in ta zauna a dakin ita kadai mafarkinta zai iya tabbata.....Duk suna tare dake bed din babbane su Rashida da Uwani anji Ac sai bacci akeyi, ta samu ta ra'be gefensu ta kwanta had'e da takure jikinta guri guda.......Ta jima a haka kafin bacci ya dauketa.

*** Cikin Shiri ya fito daga bedroom dinshi, Garba da Hadi na zaune a katafaran palon nashi suna ganin fitowarshi suka mike a tare gaisuwa suka mika amsa yana mika musu hannu sukayi musabaha da juna Ahamadu bashi da girman kai da d'agawa........Yana mutumta dan adam!! Garba ya isa inda yake yana gyara masa babbar rigarshi da yake yau shigar manya kaya yayi dakarkiyar galila ce a jikinshi green color wuyan babbar rigar anyi masa aiki na manya mutune wanda mafi aka sari masu sarauta keyi, yana gyara links dinshi Garba ya miko mishi hula zanna bukar 'yar gasken ya d'ora saman kanshi a sai ya sake wankuwa da kyau gyaran fuskarshi yayi dai-dai da tsarin askin dake kanshi saisaye yake yi bai fiye tara suma ba amma baya kwal kwabo ana masa saidaye ne agyara masa fuskarsa dai-dai da zamani....Duk wanda ya kalleshi sai ya sake kallo babu wanda zaice ya kai matakin shekurun da yake kai a yanzu.....tare suka futa dasu Garba mutukar ba nisa zaiyi ba baya tafiya da securities su Garba kadai yake dauka su raka shi, Garba ya bude masa bayan mota ya shiga ya zauna Hadi ya zauna kusa dashi ya mayar da murfin motar ya rufe.....Da sauri Garba ya zauna maxaunin direba tun kafin su iso bakin gate din mai gadi ya bude gate din.....Securities din dake zaune a bakin gate suka dinga daga masa hannu da fadin "A sauka lafiya Allah ya tsare a dawo lafiya." Shima hannunsa ya daga musu yana amsawa da "ameen." Har suka futa daga gidan......Sai da suka hau kwalta tukkuna Garba ya tambayi inda suka nufa, ya shaida masa inda zai suje gidan Hajiya Babba dake Zooroad. Garba ya dauki hanya kamar yanda aka umarce shi.

_Muje Zuwa_ *BINTA UMAR ABBALE* [7/19, 10:35 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!* 🌺 romantic love story🌺 *NA:* *BINTA UMAR ABBALE 🍒* *🌍Manazarta Writes asso* _'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_ ~~~~~~~~ *NA KUDI NE.......!* _Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free Pege17* Hajiya Babbah na xaune a palonta tare da wasu 'yan mata guda biyu Suhairat da Salimat 'Yayan mutun d'aya ne wato Hajiya Maryam wacce ta kasance 'kanwa ga Hajiya Babbah! kasancewar Allah bai bata haihuwa ba har mijinta ya rasu.mutane ke ta nani'ka mata 'yayansu mussaman 'yan uwanta waccan ta turo 'yarta gobe waccan ma ta turo 'yayanta jibi duk dan ganin daular dake tattare da gidan....Suhairat ce mai nacin zuwa gidan saboda kawai tayi katari da Ahamdu mutumin da ta kwallafa ranta a kanshi take masifar sonsa shi kuma bai san tana yi ba sai tayi zuwa goma gidan ba ganshi ba dan bai fiye zuwa da safe ko da yamma ba sai dare yake zuwa gaisheta, to yau dai sunji dadi jin Hajiya tace sunyiwa waya dashi yace zai shigo da wuri Suhairat ta sake gyara fuskarsa ta fesa turare ta 'kame! a kan mujera Salimat kuwa sai dariya takeyi mata tana fad'in"Allah yasa dai ya kyasa dan na lura kinyi masifar matowa a kan mutumin nan." Suhairat tace"Ke dai bari 'yar uwa ni wallahi da zai aureni da gudu zan yarda ina masifar sonsa komai nashi yana burgeni mutum kamili ga nutsuwa kamshin turaransa ma abin alfahari ne." Salimat ta dinga 'kyalkyala dariya tana tsokanar yar uwar tata......Cikin nutsuwa da kamala ya shigo palon bakinsa dauke da sallama. Dukaninsu suka mike tsaye suna masa barka da zuwa, kamshin turaransa ne ya cika musu hanci Suhairat sai murmushi takeyi tana gyara masa gurin zama....Ya zaune a nutse yana fadin" Suhairat kune yau gidan? ina Hajiyata." Wani fari tayi da ido tace"Wallahi kuwa Mune yau a gidan Hajiya na daki bari na kirata." Ta juya tana tafiya cikin wata iriyar siga.....Oho bai san tanayi ba dan idanunsa na kasan kafet, Tare suka fito da Hajiya babbah tana masa barka da zuwa ya amsa yana tambayar ta gida.....Suhairat ta dauko mishi lemo da ruwa ta tsiyaya masa ta mika mishi.....Ba tare da ya kar'ba yace."Bana jin zansha komai yanzu nagode Suhairat." Jiki a sanyaye ta ajiye cup din ta nemi guri ta zauna kusa da Hajiya......Yace."Ina ta son zuwa Allah bai nufa abubuwa sunyi yawa hajiya a gafarce ni." Tace."Ai babu komai Ahamdu dole ne ayi muku uziri saboda yanayin harkar taku ta jama'a bayan nan kuma nasan akwai hidimomi da yawa Allah dai ya taimaka." Ya amsa da "ameen." Palon yayi shiru Yana so yayi mata maganar dake tafe dashi amma zaman su Suhairat a gurin ya hanashi shi mutum ne mai sirri yafi son komai nashi a cikin tsari dan ya lura da yarinyar kanta rawa yake yasan dai zancen gizo baya wuce na koki ga yanayin yanda take masa kwarkwarsa za tace itama sonsa takeyi.

Gyaran mirya yayi a nutse yace."Hajiya muhimiyar magana ce take tafe dani dan daga nan ma idan na tashi can gidan Kawu Almu zan nufa." Hajiya Babba tace "To babu laifi Ahamadu Allah dai yasa maganar dake tafe da kai irin wacce take bakina ce da nayi mutukar jin dadi." Murmushi ya saki wanda yasa Suhairat shagala gurin kallonsa Yace."Yana da kyau yaran nan su dan bamu guri." Hajiya ta kalli su Suhairat da suka kasa kunne suna so suji maganar ko kunya babu tace."Suhairat ku shiga ciki mana." Simi simi suka mike sam basu so hakan ba mussaman Suhairat tafi so ya fadin maganar a gabanta da jikinta na bata wani abu.

"Hajiya na samu matar aure insha Allahu ranar juma'a ta jibi za'a daura aure." Maganar data fito daga bakinsa kenan.....Fuskarta da yalwataccan murmushi tace"Alhamdullihi Ahamdu baka ta'ba zuwa da labarin da yayi min dadi kamar wannan ba masha Allahu to amma kuma al'amarin baiyi sauri ba kuwa ko bazawara ce ne."? Ya girgiza kai "Budurwace Hajiya." Tace."To to masha Allah amma kuma abun yazo min bagatatan banyi shirin komai ba ko da yake dama haka aure yake dashi da mutuwa ba'a shirya musu in lokaci yayi sai anyi, shin yarinyar 'yar wace unguwa ce kuma." Yace." Yar wata karamar hukama ce a wannan jahar sunan garin nasu Garko amma anan tayi rayuwarta Unguwar dorayi daurin auran dai Can Garko zamuje ayi." Tace."To Ubangiji Allah yasa za'ayi damu ya tabbatar mana da alkairi." Ya amsa da "ameen Hajiyata, ni zan wuce can gidan Kawu Almu babu wani abu da kike bukata ko."? Tace." Alhamdullahi Ahamdu bana bukatar komai ka wadatani da duk abun bukata kafin wani ya kare kasa an kawo wani babu abunda zance sai da nace Allah ya saka maka da alkairi ya jikan iyayenka." Yace."ameen Hajiyata Ubangiji Allah ya barmin ke na dinga ganinki ina jin dadi." Tayi dariya da fadin"Wace ni Ahamdu ai mutuwa rigar kowa ce zan mutu kaima zaka mutu." Ya mike yana kallon a gogon dake daure a hannunsa yace."Duk da haka dai Hajjah ina fatan kiyi rayuwa mai tsayi a duniya tace."To Allah yasa Ahamdu Allah yayi maka albarka ya baka 'yaya masu albarka." ya amsa da ameen yana mata sallama har bakin kofa ta rakoshi tana sanya masa albarka

Suhairat dake la'be bakin kofa ta silale 'kasan daki ta fashe da kuka "Shikkenan na mutu ni suhairat shikkenan karyata ta kare zaiyi aure ina zaune duk na kori masu sona saboda dashi bai san inayi ba na shiga uku na lalace." Kuka take sosai Salimat na bata hakuri Hajjah ta shigo dakin.

Tace"Ke suhairat lafiya kike wannan kukan." Rungumeta tayi tana shashsheka take fada mata tsayin shekarun da tayi tana jiran Ahamdu amma yanzu yazo yace zai auri wata.

Readers Also Read