'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 14
'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 14: 'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 14. Cewa yayi "qanin ubanki ne zaki tashi ne ko sai nayi ball dake? wai…
4,003 words
Cewa yayi "qanin ubanki ne zaki tashi ne ko sai nayi ball dake? wai ke ina wasa dake ne kam da har zaki ɗauki wayana? Kin tashi kin ban wayana ne ko sai na harbe ki idiot kawai Jin muryan sa kuma tasan halin sa tashuwa tayi a hankali tana hawaye dan tabbas ta bugu Ɗauko wayan tayi ta basa tana Allah ya isa kuma sai Allah ya saka mun. Sarai yaji me tace amma sai ya basar heɗe ransa yayi yace "ke me kika ce? Tura baki tayi ni ba abinda nace Qwafa yayi ya duba wayan yaga chajin shi bai ko sauqa ba alaman bata yi komi dashi ba kawai neman magana ne, tsaki yaja "Ni na rasa mai yasa bansa security a wayan nan ba" da ya gama seta mata zama yai hanyan waje dan ya koma ɗakin sa. Bayahn fitowan Mahreen wajan zama ya abdoul ya nuna mata ya mata umurni da ta zauna dan samun su tattauna Bayani yake ta koro mata daki-daki na yacce yai kewansu sun jima basu zo Bauchi ba Sai da ya tabbatar ta sake dashi suna hiran kamun ya numfasa a yanayi na muhimmin magana ya dube ta yace "qanwata ki aramun duka hankalinki anan zamu yi magana mai muhimmanci kinji" kallon sa tayi da murmushi tace "yayana in da qarin hankalin ma duka na ara maka ina sauraranka" Nan ya kwashe duk abinda ke xuciyan sa abinda yake ji game da ita tun da ya ganta ya faɗa mata(hausawa suka ce abari ya huce shi ke kawo rabon wani). Qanwa ta ina sonki so kuma na gaske son Aure wanda in son samu ne ayi bikin nan cikin wata 1 kai yamun nisa ma irin dai week hakan nan Tun da ya Abdoul ya fara jawabi tayi qasa da kanta ta ɓoye fuska a hijab da ya kai aya ya buqaci da ta ɗago ta basa amsa taqi ganin ya masta ko takan wayan ta dake hannun sa bata bi ba tayi hanyan ɗaki har da ɗan gudun ta Dede tana shigowa ɗakin shi kuma Soja zai fice a ɗakin kenan suka kusa yin karo Ransa a ɓace amma ganin Mahreen tsayawa yayi ya dara yace "yarinya ta kamu kenan taga handsome yayana* Wucewa tayi tana rufe fuska bata ce komi ba.
Duk abunda ke faruwa kuwa Hajiya kakus ta fito ɗaukan abun gurza goronta data bari a palourn sai ta tarar da draman da ake yi Ganin duka jikokin nata na son junansu abun ba qaramin daɗi ya mata ba( a tunanin ta Soja ma hira yaje) haka taje ta kwanta da farinciki. Ya Abdoul ganin ta gudu sai abun ya burge sa ya kuma qara masa qaunan ta "tabbas inason mace mai kunya" abun da ya faɗa ya miqe yana murmushi Soja yace "yayana Allah kaimu musha biki" Ya Abdoul da farinciki Yace "Ameeñ our able army" Dariya soja ya kuma yi ya wuce wajan baccinsa, shima ya Abdoul fice wa yayi ya nufi nasa wajan baccin a sashin su, wanda yake dama da soja ne amma yace a sashen kakus zai kwana. Ya Abdoul ko da ya koma ɗakin sa haka ya kwanta yana ta juye-juye shi dai har ga Allah yake son qanwar tasa kuma bai qi a ɗaura masu aure ko yanzu ba. (haba malam abdu daga uhmn sai ehem ko a hand kake ne? Kunga inko a hand yake ya hwaɗan nice ourmman batoolerh mai wuqa da nama sai nasa a aura masa ita yanzu) ko ba haka ba FAN'S ?
Mahreen na shiga ɗaki ta samu Maha na sharar kwalla sai tace "menene ya sameki ko wani abun ya habeeby ya maki? Maha kaman zata rufe addan nata da duka tace "Idon matambayi ne ya sameni, ba habeeby ba habibu mutum sai son jin gulma" Kallonta Mahreen tayi tai murmushi ita dai tana farinciki bata da time na surutu da Maha "Allah shiryaki" shine abinda tace tayi kwanciyan ta tana ta murmushi ita dai tana ji kaman ta jita a jikin yayan nata. Mutumiyar kuwa Allah ya isa take jawa soja yafi cikin girgi.
Autan Umma yana komawa ɗaki kwanciya kawai yayi ko ta kan wayan bai bi ba ransa fess ya fara maganin renin yarinyar nan.....
Masha Allah jama'a sahiyar alkhaery
Mu dai mun riga mun tashi👯 sai kuma inda qarfi ya qare✍️
Muje zuwa Masoyan 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀 𝘿𝘼𝙂𝘼 𝙏𝘼𝙎𝙆𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙌𝘼𝙇𝘼𝙈𝙄𝙉 👇 𝙃𝘼𝙍𝙄𝙍𝘼𝙏𝙐𝙒𝘼 𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙏𝙊𝙊𝙍𝙇
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 45&46
💋💋 امى بتولة💋
Kasancewan yau Sunday ba aiki da sassafe Ameerah ya haɗa kayan karyawa suka shirya suka nufi asibiti. Isan su asibitin direct wajan abokin nasa ya nufa ita kuma Ameera tayi ɗakin da mara lafiyan nasu yake Da sallama ta shiga ɗakin ya amsa mata Wajan gadon taje ta zauna kamun ta gaida shi Yaya na fatan ka tashi lafiya ya qarfin jiki? Lafiya Alhmdlh jiki da sauqi sosai Masha Allah haka muke so yayana Allah qara afuwa Ya amsa da Ameen daga haka bai qara cewa komi ba Ganin haka itama bata ce uffan ba Suna zaune shiru Daddyn Little yayi sallama ya shigo Amsawa suka yi a tare ita da mara lafiyan Gaisawa suka yi da Daddyn Little ya masa ya jiki? Yace "da sauqi sosai" Ameerah ce tace "husby har ka karɓo mana Sallaman? A'a wiffey ban same shi ba kinsan yau Sunday ba lallai yazo da wuri ba ga kuma munyi sammako Tace "Tom shikkenan sai kazo nasa maku abun karyawa" Sauqa tayi ta shumfiɗa masu babban darduma ta jawo kondon kayan karin ta zuba masu peppe chicken da chip's sai soyayyen kwai ta haɗa masu tea kowa da cup na sa. Yayana ka sauqo ku karya ko Ba musu ya sauqo a gadon suka zauna tare shi da Daddyn Little kowa ya ɗau spoon Chips en yaci kaɗan sai kuma peppe chicken, a jiye cokali yayi ya ɗau cup na tea yana kurɓa Daddyn Little ne yaci abinci sosai da ya gama ya ɗau tea shima Suna gamawa ta masto ta tattara wajan sannan ta koma ta zauna Bayan wasu lokuta Daddyn Little barin danna wayansa yayi ya maida aljihu, miqewa yayi yace "ba na koma wajan likitan nan ko ya zo" Ameera ta amsa adawo lafiya to Office na likitan ya nufa cikin sa'a kuwa dai-dai isan sa qofan office ɗin lokacin likitan ke isowa shima, da murmushi suka kalli juna Daddyn Little yace "kai man wanne irin likita ne kai haka ka tsaya soyayya kabar mu a asibiti tun qiran asuban farko". Dariya ya saka wato dai freind sammako kuka yi gaskiya sannu da qoqari Nikam inacan manne da matata sai yanzu aka barni na fito "Ɗan iska Zaka ji dashi ai Nikam buɗe mana qofa mu shige" Daddyn Little ya faɗa yana dariya Tare suka shiga office ɗin da sallama, likita ya zauna a wajan zaman sa shi kuma ya nema wajan zama ya zauna Gaisawa suka yi suka ɗan taɓa hira kamun Daddyn Little yace "kaga frnd sallame ni nasan zaka je duba Patience's naka so kar na ɓata maka lokaci a sallamemu mukam. sallama ya rubuta masu sannan da sauran magungunan da ake buqata na game da qafan nasa bayani ya masa yacce za'a sha da na shafawa duka sannan ya kamata ya kai sati a gida kamun ace ya fara fita sai dai yana da kyau ya dinga mosta qafan yana ɗan takawa dan zai fi saurin warke wa ko bai cika sati cif ba Daddyn little yace "bakomi doctor Insha Allah za'a kiyaye fitansa yanzun fatan mu dai Allah sa ya warke da wurin Musabaha suka yi ya kuma yiwa abokin nasa godiya yai masa sallama ya fice a office ɗin Wucewa pharmacy dake cikin asibitin yayi dan ya sayo maganin da aka rubuta a hanya ya haɗu da Abba ya shigo qara duba marar lafiya kamun ya wuce don jiya bai samu komawa ba. Tare suka je pharmacyn aka basu maganin duka da suka je wajan cashier Abbane ya biyan kuɗin duka yace Daddyn Little ya bari Suna gama biya suka koma ciki wajan su Ameerah Gaishe da Abba yayi suna tafiyan sannan ya masa godiya Allah qara arziqi Abba l Ameera ganin Abba sai taji daɗi sunkuyawa tayi ta gaida Abban nata ya amsa da fara'a yace "sannunku da qoqari mamana" Gaisawa suka yi da mara lafiyan Ya masa ya jiki? amsawa yayi da sauqi Alhaji
Umma ya qira bayan sun gaisa sai ya bawa Ameerah wayan Karɓa tayi ta gaisa da Umman, tambayanta mai jiki tayi tace "da sauqi sosai har an sallamemu" Umma tace ta basa wayan su gaisa miqa masa tayi "yaya na ga Umma ku gaisa" Amsan wayan yayi ya kara a kunnen sa, lumshe ido yayi bayan Jin sallaman Umman Ameera Bai san meyasa ba jin muryan wannan baiwar Allahn na rage masa kewan Umman sa. Gaisawa suka yi tace masa "yanzu ya jikin naka yaro na? ya amsa da sauqi Alhamdulillahi Addu'oee tai masa sosai wanda yasa shi Jin daɗi fin tunani gaba ɗaya sai yake jin kamar Ummansa ce. "Ameen ya Hayyu ya Qayyum Nagode sosai Umma Allah saka da alheri" Suka yi sallama ya miqawa Ameerah wayan Sallama itama suka yi tace" ga shinan Umma ba na miqa masa" Daddyn Little ta miqawa wayan tayi amsa yayi suka gaisa da surkar tasa yace "Umma bakomi Allah qara girma mungode sosai" Ya miqawa Abba wayan bayan sunyi sallama Abba kara wayan yayi a kunne ya fita a ɗakin.
Ameera tattara komi da suka zo dashi asibitin tayi Daddyn Little na taya ta yana kwashewa ya kai masu motor Bayan sun kai komai motor Taimaka wa mara lafiyan yayi yana ɗingisawa har suka isa in da motorn nasu yake Parke, suna isa yabuɗe masa murfin back seat ya shiga ya zauna. Sallama suka yi da Abba, escorts nasa suka tada motor sae filin jirgin dake garin Abuja Gaba Ameerah ta shiga Daddyn Little ya shige mazaunin driver ya jasu sai gida Hira suke sama-sama a motorn suna sako sa shi kuwa yayi nisa a tunaninsa baya amsawa hiran nasu ma (dama shiba ma'abocin surutu bane). Driving yake a hankali Juyowa yayi ya tambayesa bro akwai abunda kake buqata mu tsaya mu saya kamun mu wuce gida? Girgiza kai kawai yayi bai ce komi ba Ameerah ce tace "husby ka tsaya musai koda fruits ne to" Tsayawa suka yi suka saya da yawa kaman masu sari, aka sa masu a boot en motorn suka biya suka qarisa gida Suna isa mai gadi ya buɗe masu qofan yana ranka ya daɗe sannunku da dawowa amsa masa yayi Parking space ya isa yai parking motorn Ɗakin da suka shirya already don shi a balconyn gidan Daddyn little ya temaka masa ya kaisa har ɗakin Ɗakine madedeci mai ɗauke da duk wani abunda mutum zai buqata a ɗaki Gado,walldrop,resting chair,mirrow, bathroom dis and that ETC. Komai na ɗakin blue color ne A bakin gadon dake ɗakin suka zauna duka yace masa "sannu bro, sannan ya ɗaura da basa haquri akan abunda ya faru tsautsayi ne ya yafe sa". Murmushi kawai yayi bai ce komi ba dama Daddyn Little yayi tsammanin haka Mutumin bai fiye magana ba sai dai wani lokacin gwanda in Ameerah ce yakan amsa mata jefi-jefi Bayan taga wucewan su itama cikin gidan tayi mai gadi ne ya jido kayakin dake motorn duka ya biyota dashi sallama yayi ya jiye masu komi a palourn. Tana shiga ɗaki ta wuce direct dan ta watsa ruwa ganin yanayin garin ana zafi Bayan Daddyn Little ya masa sallama wucewa yayi cikin palourn nasu ganin bata nan ya wuce ɗaki dai dai ya samu Ameera ta gama shirin shiga wanka tana tsaye ɗaure da towel sai kawai taji an rungumeta ta baya Ajiyan zuciya ya sauqe ya lumshe ido yace "wiffeyh wankan zaki shiga ki qyaleni bayan kinsan na gaji ba iyayi da kaina zanyi ba" ya faɗa da alaman shagwaɓa. murmushi tayi kai mutumin nan kai fa yanzu ka wuce wanka da yaron ka kuma ga wani ajiyan a ciki kaga ai sai dai awa yaran ka badai a maka ba Sa hanu yayi zai kunce towel en au wato nine ma mutumi bama za kice husbyn ba ko Bige hanunsa tayi kai fa ka tsufa yanzu Baban Little kutt nine na tsufa a guje tayi banɗakin tana addu'an shiga toilet murmushi yayi! Allah ya barmun ke Ameerah ta Allah sa na rigaki mutuwa dan bana jin zan iya zama da kowacce mace bayan ke Allah maki albarka Shima banɗakin ya shiga, wankan suka yi tare suka fito fuskansu da murmushi daga gani kasan qaunan junansu suke sosai basa fatan abunda zai rabasu in ba mutuwa ba. Shirya junansu suka yi, suka faɗa gado tare Ameera tace "washhh baban su little na gaji" bakinta ya kaiwa cafka in baki daina ceman babansu ba sai na cire maki baki yarinya Kissing junansu suka fara Janye bakinta tayi tana murmushi kwantar da kanta tayi a qirjinsa tace "Husby yanzu ya za'a yi da bawan Allahn nan? sa hanunsa yayi yana shafa kanta nima kaina abunda nake tunani kenan wiffey ban san ko zai yarda ya zauna damu har ya samu lafiya sosai ba, gashi bai son magana bare muji ko zai faɗa mana ko kaɗan ne dangane dashi. Amma kasan me husby ni wallahi sai fuskansa kemun ɗan yanayi da na Abba Dariya Daddyn Little yasa amma dai wiffey bakisan kama ba to kina ga mutum kaman balarabe kice yana kama da Abba shikkenan kinga anyi 1-1 kema kin zama tsohuwan idonki bai gani har gwanda na amaryata akan ke Hararan sa tayi a wasa ni dai ka dai na haɗani da wancan stohuwan da ta gama zamanin ta Hiransu suka cigaba dayi a haka har bacci mai daɗi ya ɗauke su . A nasa ɓangaren ma haka ya lallaɓa ya shiga bayi yayi abunda zai yi ya fito ya kwanta dan ya huta wa zaman asibitin da yayi na kwanaki. Abba sun isa airport inda suka shige jirgi suka kama hanyahn KD
Jirginsu ya isa lafiya, suka samu dakarun sojoji da motoci suna jiran isowan su dama Shiga Motor suka yi shi da sojojin da aka qaro masa dan staron sa(escort) suka yi gida Tun kan Motorn nasu ya iso qofan gida aka wangale masu gate sakamakon qaran jiniyan da ya sanar da sojojin dake cikin gidan dawowan mai gidan Umma da Little ke mata daru wai shi sai dai akaisa wajan auntyn sa Maha, tana jin qaran motocin tace "yauwa Angon gilani oya miqe ga can aboki ya dawo kaje kace masa ya kaika" ta shuwa Little yayi yai hanyan waje Umma ganin ya fita murmushi tayi tace "kaje can ku qarata da abokin naka dan anma yarona takwara da kai dai a kama a haɗani da aikin renon ka" miqewa tayi ta shige ɗaki dan qara gyara jikin ta kamun mijin nata ya shigo.
Gimbiya wajan Ammaan ta taje dan yanzukam jikinta Alhmdlh abunda har yanzu bata iya yi shine dai ta taka da qafafuwanta har waje kuma abunka da ciwo in ya kwan biyu ma sai a hankali bare ciwon da ya ɗibi shekaru suna aiki da rubutu da kuma magun gunan da Abba ke turo masu kullum Sosai mutunci ya shiga tsakanin Mai martaba da kuma Abban 𝘼𝙈𝙅𝘼𝘿.
Hira suke da Ammaan ta amma gaba ɗaya tunaninta baya wajan Ammaan nata sosai take jin wani iri da kuma yawan kallon fuskansa a idanuwanta Ajiyan zuciya ta sauqe, Ammaan ta dake kula da duk yanayin da take ciki murmusawa kawai tayi dan daga ganin ɗiyar tata tasan matsalar ta Kallonta tayi tace "tashi kije ki huta ko ibnateeyh" Tura baki tayi tace "Ammaa a'a ni ban gaji da hira dake ba kuma ni banajin bacci To ni kuma na gaji da hiran bacci nake son yi Qara tura baki tayi idonta ko ya kawo kwallah Ammaan ni ɗin? murmushi tayi tashi kije kiyi tunanin surkina da kyau amma adinga masa addu'a Jin abinda mahaifiyar ta tace sai ta rufe fuskanta da hanunta ta tashi da gudu tabar ɗakin tana dariya ya akayi Ammaan ta taramfo ta Ganin ta fita da gudu har da rufe fuska sai abun ya bawa Sarauniya Dariya Murmusawa kawai tayi tana Allah maki albarka ibnateeyh Allah nuna mana wannan rana alfarman Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam Ko da t fita a wajan mahaifiyar ta maimakon ta wuce ɗakinta sai ta stinci kan ta da son zuwa garden tuna ranan da suka yi sallama sai ta nufi wajan kaman zata same shi zaune yana jiran ta Kuyangunta ne da suka biyota suka yi saurin mata shumfiɗa Suna tambayanta Allah yaja kwanan Gimbiya mai za'a kawo maki ranki shidaɗe? Fuskanta a rufe kaman ko yaushe idonta ma a lumshe bata ko mosta ba bare tace uffan Suna ganin haka sunsan me take nufi abunda yaban mamaki banga an shiga ciki ba a nan garden ɗin naga an taho mata da fruits ayanke kuma da alama a fridge aka cirosu, kayan itatuwan like kankana, abarba, ayaba, cucumber and apple etc. Fav fruit nata ta ɗauka kankana yanka 1 ta kai bakinta, mai ta tuna sai ta fasa ta ɗau Apple ta tauna a hankali Lumshe ido tayi jin daɗin Apple ɗin ya ratsa mata har kai she dont know why sosai take jin son ganin wannan kyakkyawan saurayin ko Apple ɗin ma dan ta tuna fav fruit nasa ne Shiyasa taci sai kuma taji daɗin sa daban yau....
Muje zuwaa✍️
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀 𝘿𝘼𝙂𝘼 𝙏𝘼𝙎𝙆𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙌𝘼𝙇𝘼𝙈𝙄𝙉 👇 𝙃𝘼𝙍𝙄𝙍𝘼𝙏𝙐𝙒𝘼 𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙏𝙊𝙊𝙍𝙇
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
𝗪𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝘀𝗵𝗮𝗳𝗶 𝘀𝗮𝗱𝗮𝘂𝗸𝗮𝗿𝘄𝗮 𝗴𝗮𝗿𝗲𝗸𝗶 𝗺𝗮𝗹𝗮𝗺𝗮 𝘁𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗺𝗮𝘀𝗼𝘆𝗶𝘆𝗮 𝘁𝗮 𝗾𝗮𝘄𝗮 𝘁𝗮 𝗴𝗮𝗿𝗶 𝘕𝘈𝘕𝘈 𝘔𝘈𝘙𝘠𝘈𝘔𝘈 𝗵𝗮𝗯𝗶𝗯𝘁𝘆 𝗮𝗺 𝗞𝗶𝘆𝗶 𝘆𝗮𝗰𝗰𝗲 𝗸𝗶𝗸𝗲 𝘀𝗼 𝗱𝗮𝘀𝗵𝗶 𝗾𝗮𝘄𝗮𝗿 𝗮𝗺𝗮𝗻𝗮 𝗼𝗻𝗲 𝗹𝗼𝘃𝗲 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹
𝙶𝚊𝚒𝚜𝚞𝚠𝚊 𝚐𝚊𝚖𝚒 𝚍𝚊 𝚏𝚊𝚝𝚊𝚗 𝚊𝚕𝚔𝚊𝚒𝚛𝚒 𝚊 𝚐𝚊𝚛𝚎𝚔𝚞 𝚖𝚊𝚜𝚘𝚢𝚊 𝚕𝚒𝚝𝚝𝚊𝚏𝚒𝚗 𝚈𝙰𝚁 𝚂𝙰𝚁𝙺𝙸 𝙲𝙴𝙴 𝚊𝚔𝚘 𝚒𝚗𝚊 𝚔𝚞𝚔𝚎 𝚊 𝚏𝚊𝚍𝚒𝚗 𝚍𝚞𝚗𝚒𝚢𝚊𝚛 𝚗𝚊𝚗 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚝𝚊𝚔𝚞 𝚊𝚔𝚘 𝚍𝚊 𝚢𝚊𝚞𝚜𝚑𝚎 𝚄𝚆𝙰𝚁 𝙱𝙰𝚃𝙾𝙾𝚁𝙻
𝙶𝚘𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚖𝚊𝚛𝚊 𝚊𝚍𝚊𝚍𝚒 𝙲𝙴𝙾 𝙻𝙰𝙵𝙰𝚉𝙸 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝚁𝚂 𝙰𝚂𝚂𝙾𝙲𝙸𝙰𝚃𝙸𝙾𝙽 (𝙰𝙱𝚄𝙱𝙰𝙺𝙰𝚁 𝚂𝙰𝙳𝙴𝙴𝚀) 𝙳𝙰 𝙳𝙰𝚄𝙺𝙰𝙲𝙸𝙽 𝚈𝙰 𝚄𝚆𝙰 𝙽𝙰 𝙼𝙴𝙼𝙱𝙾𝙱𝙸𝙽 𝚆𝙰𝙽𝙽𝙰𝙽 𝙺𝚄𝙽𝙶𝙸𝚈𝙰 𝙼𝙰𝙸 𝙰𝙻𝙱𝙰𝚁𝙺𝙰.
***
🅿️ 47&48
💋💋 امى بتولة💋
Asuban farko Mahreen ta tashi ta gabatar da nafilan ta sannan ta tashi Maha Ana qiran sallah suka bi masallaci tare da Maha, bayan sun idar da salla kowa azkar nasa yayi da lazumin safe suna shafa addu'a Mahreen ta miqe ta fice a ɗakin, Maha kuwa komawa kan gado tayi ta gyara kwanciya dan har yanzu buguwan da tayi jiya yana damun ta Ko da Mahreen ta fita Gyaran palourn ta soma ta gyara dinning Sanda ta tabbatar ta gyara ko ina tass ta kunna burner da ta gani sannan ta wuce kitchen ta ɗaura ruwan abun kari Wanke wanke ta haɗa na ƴan stiraran kwanukan da ba'a wanke su jiya ba dan ta wanke sai ga hayra ta shigo kitchen en da sallama Amsawa Mahreen tayi suka gaisa hayra tace "sister irin wannan aiki haka da sanyin asuba gaskiya duk wanda ya aure ki ya huta na taya sa murna, ni fa duk jaraban tsohuwar nan da sanyin asuban nan ba fita zan ba atou" Murmushi Mahreen tayi kai de sissy Me a cikin aikin asuban yafa fi daɗi gaskiya nikam ma banjin sanyinn da kuke faɗa a nan Ji nake ma garinsu Umma yafi nan sanyi Haka dai kika ce sister amma bauchi yafi kaduna sanyi ina ma za'a haɗa chaɓɓ ( to to kuzo ku raba mana musu yan kd da bauchi ina ne yafi sanyi) Karɓan wanke wanken hayra tayi amma da qyar Mahreen ta bar mata sai ta koma kan girkin A haka suka cigaba da aikinsu suna yi suna hira su bibbiyun su har suka kammala komi Mahreen tace "tom sissy ni dai ba naje na duba wancan malalaciyar ko ta tashi ko kuma baccin ta koma, Na barki da aikin jerawa a dinning afuwan". Caɓ sister jerawa shine aiki? Ai aikin kam ya qare dan kin riga da kin gama yau delicious naki zamu ci Murmushi tayi ta fice a kitchen ɗin ta nufi ɗakin su tana shiga da sallama kallon ta takai kan gado kaman yacce tayi tsammani kuwa hakan ta tarar a kwance ta samu Maha tayi ɗaɗɗaya tana sharar baccinta kaman bata yi na dare ba Girgiza kai kawai tayi tace "dede dake ai sai yaya habeeby ɗin Allah Ubangiji yasa ya Aure ki ko zai saita mana ke" Har zata shige bayi sai ta tuna yanxu ba safiya bane a jiddah qaramin wayanta ta jawo tayi dialing layin Ummeyn ta Yana ringing ɗaya Ummeyh ta ɗauka tana "Assalamu'alaiki beenty" Amsa Sallaman tayi "wa'alaikissalam Na'am Ummeyh na antashi lafiya? Lafiya Alhmdlh ƴar Ummeyh ya ummata? Uhmn Ummanki ki ko rigima Ummeyh daga gani ma halin tsohuwar nan Maha ta ɗauko wallahi Eyye Ummeyh kama haɓa tayi kaman ƴar tata na gaban ta nace gidanku Mahreen dan dai kin renani ki dubi idona kice uwata rigima mun fara wasan reni ko? Uhmn ni dai bance ba Ummeyh, ya Abeeyh? Igiyan ajiyansa da kika ban ya tsinke ya gudu, Ki fita idona Mahreen uwata ba sa'an wasan ku ba Turo baki tayi Allah ya baki haquri Ummeyh In ya bani haqurin ki qwace da kanki a wajan Ayya dai Ummeyh na kiyi haquri Allah baki haquri Ameen to ke kuma Allah ya maki albarka Mahreen ɗin Ummeyh da Abbeyh Murmushi tayi tace "Ummeyh yaushe zakizo? Muna missing naki" Very soon beenty Insha Allah Yanzu dai ina Auta? banji mostinta ba Gata nan kwance kaman kayan wanki Ummeyh tana bacci, Allah ba ɗiyarkin nan bata ji ko kaɗan Ummeyh ni so nake ma wataran ya soja ya taimaka ya jibge ta ko zata nistu shi kuma baya dukanta kaman me storon ya ko me ta masa sai dai surutu Ummeyh murmushi tayi tace "duka wannan dogon bayanin akan ƴar jinjirata Autan Abbeyh tom ta Allah ba taki ba za kiji dashi ne ba mai taɓa mun jinjira bawa Auta ta waya nikam naji muryan ta Daka mata mari a acinya Mahreen tayi "tom sarkin masu baccin safe tashi Ummeyh na magana" ta faɗa tana miqa mata wayan. Hararan Mahreen tayi ta amshi waya sai kuma ta fashe da kuka ni dai Ummeyh ko kizo mu koma ko na biyo ki tunda nazo ya habeebu duka na yake haka yaya Mahreen ma duk se cin zalina suke ba mai sona sai Umma da Abba da ya Abdoul da yarona Murmushi Ummeyh tayi tom ai naga masu sonki sun fi masu dukanki yawa kiyi haquri uwata ta kaina duk wanda ya qara taɓa ki sai ki haɗa shi da Umman ki ko ki faɗawa takwaranki kinji Insha Allah very soon nima zan zo nan da week in Allah yaso ya yarda in dai har ayyuka suka yi dama-dama kinji Tom Ummeyh naji Yauwá to share hawayenki Auntan Ummeyh turo baki tayi ni dama kuka na ba hawaye Dariya duka suka yi ita da Ummeyhn nata to Allah ya shiryaki uwata Maza a tashi aje a gaida Ummata nasan ko gaisuwa ba kiyi ba Uhmn kawai tace suka yi sallama ta bawa Mahreen wayarta Sallama suka yi itama ta katse call en, ajiye wayan tayi ta shige bathroom Maha tashi tayi ta gyara ɗakin tsaff kaman ba i taba ta kunna turaren wuta.