'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 15
'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 15: 'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 15. Mahreen ta fito wanka da mamaki taga har Maha ta gyaran ɗakin kuma…
4,417 words
Mahreen ta fito wanka da mamaki taga har Maha ta gyaran ɗakin kuma tsaff har qamshi yake Taɓe baki tayi dama haka kike kekam kaman me aljanu Batace ma Maha uffan ba ta wuce dan ta shirya ta fita ta gaida kakus Maha ma toilet en ta shiga sanda ta wankesa tass sannan tayi wanka itama ta fito Kusan a tare suka gama shirya wa Tabarakhallah Masha Allah kyau suka yi sosai kaman masu zuwa gasan kyau Abaya suka sa ita Mahreen ta saka peach ita kuma Maha ta saka maroon gashi dukansu farare Kar kuso kuga kyan da suka yi kyau har yana ɗiga. Fita suka yi a ɗakin sun samu hayra itama ta gama shirya komi har tayo wanka abunta, dukan su suka yi ɗakin Kakus dan gaishe ta sallama suka yi ta amsa tana ɗaurin ɗankwali juyowa tayi tana kallonsu tana murmushi Masha Allah kaga larabawan jikoki na Allah dai ya rayamun ku ya maku albarka Gaisawa suka yi duka tana qara sa musu albarka Hayra ce ta shigo tace "Amarya kizo mu karya" danqwalon hayra tayi dan fatarin kakarki amma ba niba uwaki ce Amarya ba ni ba dan jakan ubanki dama tare dani kike karyawa ko neman magana Maha da bata iya yin shiru tace "ke dai stohuwar nan ba'a maki gwaninta ko kaɗan" Takwara ke kuma ki fita a idona kamun na taso banson aikin masu tangaɗi da sanyin safiyar nan bazaki sani sinqin surutu kaman mai layiii ba Ita dai Mahreen murmusawa take, tashuwa suka yi suka fice duka suka bar kakus dake qoqarin fitowa itama Bayan duk sun fito sun zauna a dinning ɗin Maha ce ta kalli hayra tace "yanzu yaya hayra dan jaraban tsohuwan nan itama a dinning take cin abinci mutum na tafiya kaman me tete" Dariya suka sa duka na rabaki da surutun safe na kakus Maha, kinga dai ke takwaranta ko tom wallahi ba rage maki zata yi ba jaraban masifan ta na safe yafi na ko yaushe Maha tace "yo to ni ina ruwana tamun na mata kalass" Kakus ne ta iso wajan tace "ke hariratu ubanki Muhammadu ne mai jaraban masifa, ke kuma mai sunan aljanu ubanki kika rena dan jakar ubanki, tangaɗaɗɗun yara kawai masu sinqin reni". ja mata kujera hayra tayi ta zauna Tace "to ina su sojan mijina? Kai amma dai yaran nan baku da kirki harda ke indo da nake wa kallon mai hankali cikin carbi, yanzu dan sikitin sinqin rashin mutunci shine har za kusa abinci a gaba baku nemo ƴan uwanku ba sufa sune maza suke nemowa ku ba abinda kuka iya sai ci bari kuji tom inga ɗan kwal uban dazai ci abinci anan su soja basu zoba ingwada masa nawa tagaɗin yafi nasa" Maha ce ke qunquni, yauwa kin fara ai kenan da wannan zagin da bansan a ina kika koyo saba Kallonta kakus en tayi, juyar dakai tayi nide ba inda zani atou Hayra ce ta tashi taje sashensu ta qira ya Abdoul ta kuma dawowa ta qira ya habeeby Ta samu ya Abdoul ya gama shiryawa fitowa yayi yayo dinning ɗin, shima ya soja dinning en yayo Zaunawa ya Abdoul yayi a setin Mahreen wacce tunda yazo wajan ta sauqe kanta qasa dan dai yanzu kuma take jin kunyan sa Saving nasu Mahreen da kanta ta tashi tayi ta sawa kowa nasa Da tazo kan na ya Abdoul rasa mai zata sa masa tayi shi dai ya soja yana gani sai smilling yake kawai dan burgesa suke A haka dai tasa masa ferfesun kayan ciki da tosted-bread da soyayyen qwai a gefe da kuma ruwan zafi Kallon gaban Abdoul kakus tayi ta kalli gabanta daga soyayyan kwai da bread se ruwan shayi Ajiye cokalin hannun ta tayi ta saka Salati Sai duk suka ɗago suna kallonta shi dai soja ya fahimci nufin ta tun da ya kalli kallon da take wa plate ɗin gaban ya Abdoul dan haka mai zai yi inba dariya ba harda kama ciki Itako Maha duk da kyawun da taga ya mata yana dariya hakan bai hana ta aika masa da harara ba tace a ranta "kaga Soja mugu bai san me akayi wa salatin ba yakama dariya dan baqin hali da nema mana surutu" Kakus ce tace "oh Ni Mairama daso yanzu ke indo dan ɗiban albarka da kuma rashin storon Allah sunan ki kaman na mayun daa Kiga abunda kika sawa abdu kiga abunda kika samun nida gidan yarana da kuɗin yarana fa aka sayi komi amma dae Allah ya kyauta don haka ban isa ba bazaki samun bushashshen biredi kaman kunnen zomo ba da wannan abu kaman wainar kashin shanu sannan ki cikawa Abdu kwano ba tun da bana uwarsa ba Nima samun ferfesun atou Mai zasu yi a wajan in ba dariya ba dukan su kowa ta basa dariya dan duk sun ɗauka wani abun ne ya faru ganin irin salatin da ta rafka Ya abdoul ne yace "haba amaryata kishi kike dani tom juyo muci tare" Ɗan qwal uba banson yaudara kayi kaɗan nayi kishi da kai Ni dai tunda ba uwarka ce ta saya ba yaronane ɗan albarka ya sayo to maza azubamun banson tangaɗanci Hayra ce dan ta kashe surutun ta tashi ta sawa kakus kaman na abdoul en har da chip's da suke ci suma Ai kuwa tana loma ɗaya da ferfesun ta kurma ihu ta tufar Yanzu dai ke ja'irar ƴar nan kasheni zaki yi wato ki huta wannan barkonon kike aikaman nasa a ƴan hanji na da nake maleji dasu to ta Allah ba taki ba Ai nasan wannan yar albarkan sona take shiyasa bata saka mun ba Maha ce ta turo baki ke dai takwara kin cika surutu abincin ma bazaki barmu muci a nuste ba dan Allah Bafa kyau surutu anacin abinci so kike muci tare da sheɗan halan Subhanallahi cubulle bakinki ya sari ɗanyen kashi Allah tsaremu haɗa hanya da sheɗan A'uzubillah bismillahi Yo kunga na koresa ai ba naci abinci na nayi shiru Allah zubo maki albarka cubulle. Shi dai ya Abdoul duk abun da ake bayama jin su gaba ɗaya idonsa na kan Mahreen Ita kuwa sai sunne kai take Kakus ce tace "jarababben kallo dai ba kyau sai ya sanya mutum tangaɗi gwanda a nistu aci abinci yafi lada ko ƴar mutane ta sarara" ta faɗa tana hararan ya Abdoul Murmushi yayi bai ce komi ba sanin sarai dashi take Wayan Mahreen ne yayi qara alaman saqo ya shigo taga ya habeeby ta gani ya turo mata text *qanwata ki barmun yaya haka ya karya mana karki zautasa da yawa kinji stohuwa ta fara banbami kar takai mana mazga* Ɗagowa tayi suka haɗa ido da ya soja en dariya ya mata sai ta harare sa a wasa ta tura baki ta kau da kai da kallon kowa tana karyawanta ita ma Sannan ya Abdoul ya ɗan nistu yana cin abinda ta zuba masa cikin nistuwa Bayahn sun kammala kowa yayi hamdala Main palourn suka koma dukan su Hayra ce da Mahreen suka tattare wajan, bayan sun kai kitchen suka haɗa wanke wanken suna yi Mahreen ta fita tabar hayra a kitchen ɗin zata ɗaura sanwa.
Gimbiya Mehwish itace bata koma cikin gidan ba sai yamma liss Direct ɗakinta ta wuce tana shiga tai jefi da abun fuskan ta takwanta a gadonta tana faɗin "washhh Ammaa ta na gaji da tunanin ba nayi bacci yanzu kam before magrib....
𝘽𝘼𝙔𝘼𝙉 𝙎𝘼𝙏𝙄 𝙂𝙐𝘿𝘼 1
Rayuwa nata tafiya yayin da bawan Allahn da Daddyn Little ya buge satin sa ɗaya 1 ciff da sallama yau da ya kama Lahadi qafa kuma Alhmdlh sai dai ɗan abunda baza'a rasa ba Ameerah da Daddyn Little sun gwada tambayan sa da mamakinsu kuma ya amsa masu tambayan "Yace masu shi bauchi yake son zuwa" sai dai apart from haka bai faɗa musu komi ba dangane dashj sun haqura tun da ya yarda zai zauna har satin ya cika A ɗan satin da yayi a gidan sosai suka shaqu da Ameerah in da take ta roqonsa karya tafi ya zauna dasu inyayi sai suje Bauchin tare suma akwai family house nasu a can In ta faɗi haka baya cewa komi sai dai yayi murmushi kawai Shi dai shirinsa yake zai tafi dan a lissafin sa bai wuce wata 2 bane yanzu ya ragemasa Gashi be isaba bare yace ya samo abun da yazo nema.
Umma ce zaune a palour tare da Abba da angonta Little tana masa karatu Abba kuma na karanta jarida Wayanta dake gefen Abba ya ɗau qara Umma tace "yallaɓoi a taimaka a miqamun" Murmushi Abba yayi bai ce komi ba yasa hannu ya ɗauka ya miqa mata karɓa tayi ta amsa qiran Tana sallama tace "Mijin mata huɗu 4" Ummeyh tasa dariya kaji wani batu yanzu in ba wan da ya sani ba ai sai ya ɗauka haka ne alhalin zance ne bayan kinbi kin mallake ni gaki ke kaɗai a wannan qaton gida kin hanani qara amre Murmushi Umma tayi jin abinda Ummeyh tace Haba Gwaggo yara dan dai baku samu bane nasan da kun jima da yin huɗun hiran su suka cigaba dayi cikin barkwanci da raha Ummeyh ce tace "Umman yara guess what? Umma tace Gwaggon su amun da yaren da zan fi ganewa Tom albishir tace "goro fari tass, ina jinki ya akayi" Insha Allah jibi iwar haka ina Nigeria muna tare dan Allah da gaske kice Gwaggon su? Sosaima da gaske in Allah ya yarda Da farin ciki Umma tace shikkenan bauchi yayi qira dama nayi kewan Amarya ko naje na ganta nima Kede bari kawai Umman yara Insha Allah sena zo zamu je Allah kawoki lafiya mijin mata huɗu 4 Sallama suka yi tace a gaida mun yaya na Insha Allah yayanki zai ji gaisuwa Kaste qiran Ummeyh tayi. Umma ta kalli Little to nan da kwana huɗu 4 zan kai ka wajan auntyn ka Maha sai kabar damu na ko angon gilani Tura baki yayi nifa gilani ai anci ba'a cona an faca binta apoki na anbi muje mu ciga jilgi Jan kunnensa tayi duk girman rashin jinka zaka fama sai munje sai dae ko ka zauna kai ɗaya a gidan dan har da abokin zamu tafi Kukan sakalci ya saka Abba dake sauraran su yana murmushi Miqowa Little hannu yayi oya come on abokee bar grannynka ba zata shiga jirginmu ba kuma ita za'a bari a gida Tashuwa yayi ya fasa karatun ya tafi wajan kakan nasa ya zauna yanawa Umma gwalo wai bazata hau jirginsu ba ita zata zauna a gida Umma ta murmusa tace "ranka ya daɗe boɗɗinka na gaidaka wai insha Allahu nan da kwana biyu tana hanya" Abba yace "Allah kaimu Allah ya kawo ta lafiya Da Ameen Umma ta amsa Ta tashi ta haura sama ta barsu a palourn.
Ɗaukan wayansa yayi dan ya duba wani number, bayan ya duba kaman wanda akace masa ya shiga gelleryn sa me zai gani Maha ta goge masa photos na wayan sa duka Kaɗan ya rage yayi kuka dan har da sani contract da aka basu na aikin da za'a tura su turkey ta gogen photos ɗin ransa yayi mugun ɓaci ya rasa mai zai ma yarinyar nan ya huce Har jikinsa na rawa yama rasa mene zeyi yayi maganin yarinyr nan Qara kallon wayan yayi, tsaki yaja ya jefa wayan kan sofan dake ɗakin yana huci "Tabbas sai na zane ki yau Maha ba tausayinki Indae kince ke rashin ji ke ɗawainiya dake ba mu zuba" yana gama faɗan haka tashuwa yayi ya fice a ɗakin. Yana fitowa Kakus ya samu hayra na mata kitso suna zaune a palourn Ina su Mahreen suke amaryata? Ooh me amarya wani salon sinqin yaudara ne kuma yau ɗan kwal uba ba dai ka bani ajiyan su ba Tom suna cikin gida itada Maha Baice ko qala b ya juya yana ayyana irin hukuncin da zai mata........
Muje zuwa✍️
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦
𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 49&50
💋💋 امى بتولة💋
Ransa a ɓace dan haka bai bi bayansu sashen baba qarami ba Motor yaja ya fice abinsa a gidan gaba ɗaya yace "Insha Allah ko ba yau ba zamu gauraya ne dake Maha ᴋᴇʀᴇ ɴᴀ ʏᴀᴡᴏ ᴢᴀʙᴏ ɴᴀ ʏᴀᴡᴏ Insha Allah wataran za'a haɗu". Cikin ƴan kwanakin nan sosai soyayya yai qarfi tsakanin Mahreen da ya Abdoul nata Kakus tafi kowa farinciki dan abun ya mata daɗi Hayra kuwa ta koma cewa Mahreen matar yaya duk da in ta faɗa Mahreen cewa take bata son stokana ta cigaba da ce mata sister itakam
Maha ce hakimce akan kujera tsohuwa na zaune a kujeran dake kallon na Maha fuskan ta a haɗe Maha tace "Takwara wai me aka maki ne kika haɗe rai haka? Nikam gaskiya ma Amarya na gaji da garinnan gaba ɗaya tunda mutum yazo daga masifanki sai masifanki ba yawo ba wani dan fita shashu shiru kawai kaman mutum yazo gidan mutuwa Tafa hannu Kakus tayi ta rafko Salati kai kace mutuwa aka yi danqwalo ta miqawa Maha don ubanki uwaki ce Amarya ba ni ba masifa kuma nayi ni da baki na a gidan yarona kika zo kika sameni ba gidan ubanki ba bare ki gaya mun magana tangaɗaɗɗiya kawai tom ki gaji da garin nan har ki mutu in kinyi wasa sai na cewa ubanki abarki anan inga yacce zaki yi, wato ma dan lalacewa irin na Jamila gidan shisha ne ko shishu take barinku kuje oh Ni mairo naga rayuwan tangaɗi anan Insha Allahu Jamila zata zo ta sameni Caɓ ni dai komawa gidanmu zanyi abuna Sannan ki zage ta ai ƴarki ce ba wanda ya haifa maki ita kunfi kusa atou ni me nawa Yanzu dae cubulle dan baki da ta ido uwar taki kike cewa haka Allah ya shirya mana zuri'a, yanzu Shekara nawa ban ganku ba dudu yau kwanan ku nawa da zuwa inaji baku yi kwana biyu ba kice zaki tafi Zaro ido Maha tayi tace "yo kin tsufa ba dole kice haka ba to bari kiji takwara munfi sati a garin nan mun kusa kwana goma ma inaga" Kakus ta taɓe baki tace "to koma dai shekara ne ai cubulle mutum bazai guji nasa ba ni da nakeso abar mun ke tunda ke cubulle nace kinga hankalin mu zefi zama ɗaya abunmu ba mai jin tsakaninmu inasonki kina sona Tura baki Maha tayi tana magana qasa-qasa Mahreen ce ta shugo da sallama tare da ya Abdoul suna murmushi dukan su Kakus ce tace "tom tattabaru gidan soyayya sannunku da zuwa damunmu muna hiranmu na soyayya ni da cubulle ta". Dariya ya Abdoul ya saka wato dai yau shiri ake tsakanin kakus da cubun ta "Shikkenan Hajiya Kakus in zuwan namu bai maki ba sai mu koma inda muka fito" inji Mahreen Harara kakus ta mata sannu rasae wato kin qwacen miji ɗan cafanen da yakeman da ɗan goron da yake sayan mun kike son hanasa ko wai ku koma to ba in da zaku koma kaga zoka zauna angon amarya komi dozin nayi hiran da kai Dariya suka sa dukansu wajan ban da Maha da murmushi kawai tayi "Nikam ina habibu ne yayi? inji kakus Ya habeeby ya futa ai kakus inaji yaje wajan abokanan sa anan barrack na garinnan Ooh abunka da sojoji ba iyayen kalan dangi Kai da kake soja a kaduna me ya haɗaka da sojojin bauchi? habibu shishishigi shigilitu Sai sannan Maha tayi dariya tace "Allah dai ya maki albarka takwaras daɗi na dake baki qyale kowa ba wato dai kalan dangi yaje yi". Kallon ta Kakus tayi ta girgiza kai "cubulle ba dai iya dariyan mugun ta ba to wallahi yazo ya jiki ba ruwa na in yana lakaɗa maki duka ba ruwan mairo" ta faɗa tana karyan goron ta Ya taɓa ni ya gani hayya sai kuma tayi qwafa Hiran su suka cigaba da yi.
1 MONTH LETTER (bayan wata ɗaya)
a haka rayuwa ke ta tafiya da daɗi babu daɗi har yau gashi watan shi guda cur a garin Abuja, yau ne kuma yake lissafi da shirin barin Abuja ko da su Ameerah basu so ba domin zaman ya isa haka lokaci na tafiya
Sanda ya gama shiryawa tsaff be ɗau kaya Ko ɗaya ba banda na jikin sa tunda baizo da kaya ba anan ya same su, fitowa yayi yaja qofan ɗakin ya nufin cikin gidan nasu A palourn ya tsaya yayi sallama, amsa masa Ameerah tayi kamun nan ya qarisa shiga da ta masa izini Kallonsa tayi tare da zaro ido yayana mai nake gani? Ba dai kaceman ka shirya ba yayana sai kuma idonta ya kawo hawaye Murmushi ya mata bece komi ba waje ya samu ya zauna Daddyn Little ne shima ya fito ashirye ganin sa sai yayi murmushi yace "bros har ka gama ka fito ne? Ɗaga masa kai kawai yayi yana murmushi Gashi har xaka koma baka faɗa mana komi akan ka ba bro ko wataran Allah zai qara haɗamu ko wani zumunci haka kaga ai zamu iya kai maka ziyara Insha Allahu ko wiffey Murmusawa yayi ba qin faɗa maku nayi ba faɗan ne bance akwai amfani ba dan ina da nisa sosai Nima dalili ne ya kawo ni sai Allah ya qaddara haɗuwanmu Ameera da idonta ke cike da hawaye tayi caraɓ tace "yayana nisanka doesn't matter, yacce dalili ya kawo ka sai kaga mu kuma sanadi ya kaimu in Allah ya hukunta hakan" Kai de ka bamu address da kwatance kawai bros Shikkenan karku damu Yanzu dai banson ɓata lokaci tun da kunce akwai nisa bauchi da garin nan amma ba na faɗa maku ko kaɗan ne daga labarin inda na fito So tunda ga waya we will be communicating Insha Allahu nan ya basu ɗan taqaitaccen labarin daga in da ya fito mamakine ya rufe su duka Ameera ce tace "Yayana yanzu daga Qatar dana sani kake dan Allah? Kazo Nigeria kawai dan neman magani lallai sannu da qoqari yayana" Tom ai gwanda daka faɗa mana Ranan ai nace maka akwai family house namu a Bauchi sannan ina ji kakus na yawan cewa kakanmu malami ne yakan bada magani Kaga da ka bari munje can en may be ma ta gane maganin da kake nema basai kasha wahala ba, kaga mu qara ko da wata ɗaya ne kamun yasamu leave s wajan aiki sai muje dan bamu jima da dawowa ba wannan hatsarin ya faru Murmushi yayi shi dai bece komi ba Qanwata Kinga ba yanzu zaku shiga bauchi ba sannan ni ina da qidayayyen lokacin da ya kamata ace na koma Kwanaki sun tafi sosai zan shiga bauchi in yaso ko daga baya zamu haɗu daku in kun samu shigowa kamun na koma in Allah yasa na dace kuma na samu na tafi sai dai Allah haɗa mu da alkairi Sannan ina addu'an Allah ya sauqeki lafiya ya albarkaci duk abinda zaki haifa Idon Ameera cike da kwalla ta shafa cikin ta da ya fara fitowa tace "Ameen ya Rabbi yaya AMJAD" Murmushi Amjad yayi mata Haka kaman karsu rabu suka yi sallama Ameerah har da yar kwallanta suka baro ta a gida dan Daddyn Little ne ya kaisa har motor pack ya sashi a Motorn Bauchi ya biya kuɗin motorn sannan ya basa wasu a hanunsa duk da ya nuna a'a Jakan da tun ran da ya buge sa ya ajiye yaje motor ya ɗauko ya miqa masa bros ga jakan kayan ka nan sannan ya buɗe yasa masa kuɗin a ciki sun riga sunyi exchange na number. Sanda motornsu ya tashi kamun Daddyn Little ya ja nasa Motorn yabar tashan ya wuce wajan aiki Amjad na zaune cikin Motorn suna tafiya shiru yayi dan ya fara jin kewan mutane masu halaccinnan dan baya tunanin azamanin da muke ciki ana samun mutane haka Wasuma in sun buge mutum guduwa suke kamun ataru a kansu "Allah ka datar damu, su kuma Allah saka masu da mafificin alkhaeryh".
Mahreen, Maha da kuma Soja sun dawo gida bayan satan nin da suka yi a bauchi, suka dawo cike da kewan mutan Bauchi da surutun kakar tasu Umma taji daɗin ganin yaranta sosai sosai Inda gefe ɗaya kuma da Umman da su Mahreen en duka ido suka zuba ganin ikon Allah yaushe Ummeyh kuma zata iso kullum ina hanya na kusa zuwa amma shiru Mahreen ce in ta tashi qorafinta sai ta tura baki, tace "wa yasan ko jiddahn ya koma bangon duniya ne". Tsakanin Maha da Little kuwa soyayyace ba kaɗan ba In ka gansu sai ka ranste itace uwarsa yacce yake maqale mata Mahreen ke kwance a ɗakinsu tana aikin da ya same ta na waya wayanne a maqale a kunnenta sai narkewa take "nide ya Abdoul ka dena bana so Ta ɗayan ɓangaren ne naji ya Abdoul yace "nifa da gaske nake ba wasa ba zanwa su baba magana am eager to see you as my wife, I seriously need you by my side, Ina kallon wannan kyawawan idanuwanki masu tafiyar da tunanin mai kallonsu" Lumshe idon tayi Yace "and 1 thing kinsan me? Tace "uhm uhmn yayana ban sani ba sai ka faɗa" nifa in baki daina cemun yaya ba duk randa na kama bakinki hmmn Turo bakin tayi kaman yana gabanta nide uhmn Dariya yayi kaɗan kede kinji kunya ko tom shikkenan in zaki aje kunya agefe ki aje inba haka ba nifa baza'a qwareni ba bari kiji. I love you Queen Muahhh! blowing mata kiss yayi ta wayan saurin cire wayan tayi a kunnenta ta kashe tana murmushi ita dai ta rasa ya Abdoul wani iri ne ko kaɗan bai jin kunyan ta komi yaga dama faɗa mata yake Rumgume fillow tayi inasonkaaa sosai nima yayana. Maha ce zaune a palourn tana kallo Litlle ya futo daga ɗakin soja yana bubbuga qafa yana anci boi na anci boi na (Aunty ball na) Kallon sa tayi babyna ball naka a ina? Nuna mata ɗakin soja yayi a akin unkui Tace mass "Ina uncle en Kuma tom? Fara buga qafa yayi unkui ayanan boi na aunci Dafe kai tayi ba yacce ta iya haka ta tashi ɗaukansa tayi suka shiga ɗakin Wow ɗakin tuzurun soja kenan komi na dakin white colour ne ɗakin ya haɗu iya haɗuwa ga tafkeken gadon da zai ɗauki mutum 4, tunda suka shiga sashin take qare ma palourn nasa kallo har suka shiga cikin ɗakin gaba ɗaya kaman ba'a Nigeria part nasa yake ba bare ace maka a cikin gidan Abba ka yarda dan ya haɗu iya haɗuwa san da ta gama santin sa dan bata taɓa shiga ba kamun ta wuce yin abinda ya kawo ta Suna shiga ɗakin ya sauqe sa shi kuma ya nuna mata qasan gado wai yana ciki ball ɗin Sunkuyawa tayi dan ta ɗauko masa har ta miqa hannu sai taji motsin an buɗe qofan bayi Innalillahi wa inna ilaihirraji'un shine abinda ta furta a zuciyanta dan tabbas tasan yau ta gama yawo little ya jaza mata dama wasan ɓoyel ɓoyel suke da marar kirkin nan yanzu gashi ta kawo kanta har ɗakin sa daɗin ya kashe ta ya ɓoye wuqan ko ya dakata har tayi laushi ba wanda ya sani bare ta karɓe ta tama rasa yacce zata yi shi ko gogan naku ya fito wanka zuciyansa ɗaya 1 little ne kawai a ɗakin daga shi sai guntun towel white wanda be kai guiwansa ba faffaɗan qirjin sa a buɗe da kwantattun gashin da ruwa ya jiqa su(abinka da soja) Wajan mirror ya wuce bai ko kalli Little dake tsaye gefen gado kaman mai jiran abu ba, yana share jikinsa kaman ance ya kalli can ai kuwa karaf ta cikin mirrow idonsu ya haɗe Saurin rufe ido tayi tana duk addu'an da yazo mata a zuciyanta shi kuwa haɗe fuska yayi daga baya kuma yayi murmushin mugunta Tana nan wajan qasan gadon idonta a rufe a storace take sanda har ta qarisa futowa daga qasan gadon wajen qofa ta nufa da rarrafe wai dan kar ya ganta bata kai ga isa ba taji an riqeta Juyowa tayi zata kwala ihu Hanu yasa ya buge mata bakin Dama wa yasa ki shigomun ɗaki? renin daki kamun har yakai haka ko Bata ce ko qala ba ganin dai tana hannu idanuwan ga a rufe dan storo har jikin ta na rawa Sake ta yayi yana faɗin "qaramar mara kunya fice mun a ɗaki kamun nayi ball dake ta yacce ko qashinki baza'a iya ɗaurawa ba idiot kawai" Ai kuwa kaman jira take ya sake ta tana hamdala ta fita tana haqi da sauqe ajiyan zuciya yacce ya habeebu ya fusatan nan in yakaiman bugu 1 ai bani ba labarina amma Little ya jamun kwandon bala'ee Hararan hanyan ɗakin sa tayi ta shige dakinsu da gudu tana ga kaman zai biyo ta Little da ya samu Ball nasa dama palourn ya gudu yana yi dan inyayi a ɗakin unkui zai zana sa Bayan fitan ta murmushi yayi yaci gaba da abun da yake yi hankalin da kwance ko bai dake ta ba dai yasan ta storita
Motorn su tafiya yake shi kuma da yake zaune a gaban motorn ya zubawa hanya ido, idon shi nakan hanyanne amma tunaninsa gaba daya yana gida Ummansa kawai yake misalta irin yanayin da take ciki gashi baisan taya za'a yi yayi magana dasu ba duk sunqi riqe waya daga ita har Abba 1 month basu yi magana ba bata kallesa ba sai yanzu ma yake jin haushin rashin riqe wayan da Umma da Abba suka yi Shima kuma dama bawani damunsa wayan yayi ba shi yasa bai matsa masu ba dan bai tava kawowa zai yi irin wannan tafiyan har haka ya jima beji Umman sa ba Tafiya suke tun da hansti har har sune basu isa bauchi ba sai can tsakiyan dare dan ma Allah ya taimake su driven bai yi zagaye ba kuma an gyara hanya Sun shigo gari ga dare yayi gashi besan kowa ba Gaba ɗaya ya rasa ya zeyi haka de wani bawan Allahn da suka zauna tare dashi a motorn suka wuce gidan sa suka kwana kamun da safe ya nemi abunda ya kawosa bauchi.