Kenza eBookz

'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 16

'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 16

'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 16: 'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 16. Zaune take gaban mai martaba kanta a qasa Ibnateeyh yanzu kinsan in…

3,977 words

Zaune take gaban mai martaba kanta a qasa Ibnateeyh yanzu kinsan in lissafina dai dai ne to yau saura wata 1da satanni bikin nan ko fatan kina sane? Don haka za'a fara shirye-shiryen biki da komi sannan zanyi magana da mahaifin yaron Insha Allahu ni ina ji a jikina ya kusa dawowa ma don haka kema ki fara shiri inaso gaba ɗaya ki daina fita yanzu kinji ba "Insha Allahu Papa Allah taimaka" shine kawai abunda tace ganin kaman bata yanayi me daɗi sai Mai martaba ya sallameta Sannan ya aika da ɗan aike akan a faɗawa Abban Amjad yana nason ganinsa gobe in Allah ya kaimu

Umman Amjad ce zaune tayi tagumi tasa tuwo a gaba amma bata ko sa hanu ba shigowan Abba kenan daga wajan jin saqon qiran Sarki ya tarar da ita haka Girgiza kai yayi bece komi ba Zama yayi kusa da ita MARYAMA ki masa addu'a kinji Inshà Allah alkhaery ne ya riqe sa kinji Sai hawaye a idonta sharrrrr ta cire hannu a abincin ma kuka nason qwace mata Saurin share mata hawayen Abba yayi Kul Maryama na haneki da mawa ɗanki kuka kibar zubar masa da hawaye dan hawayen uwa masifa ne akan ɗan ta ba mutuwa yayi ba tafiya ce kuma Insha Allah yana hanyan dawowa kinji ko mutuwa yayi ma tsakaninki dashi addu'a dan shine soyayyan ki gare sa Adduah zamu masa yanzun ma kinji a haka ya lallaɓa ta da qyar ta yarda taci abinci Nan ya fada mata yacce suka yi da ɗan saqon mai martaba Sun kuyar da kai Umma tayi tace "Ni wallahi duk ji nayi ma da ban kawo shawaran ya shiga gasar nan ba tsakani da Allah na fara dana.." ta kasa qarisawa sakamakon kallon da Abba ya jefa mata Wai ke Maryam mai yake damunki ne kam? Ja kike dashi akan hukuncin da Allah yayi akan ɗan ki? Kinsan zaki zo duniya? Ko kinsan zaki samu yaron? Mai yasa dan Allah ya qaddara abu akan yaronki kikeson butulce wa Allah ta hanyan nuna baki karɓi wannan qaddaran ba? Lokacin samun damuwan mu yayi tabbas in dai bazaki gyara kalaman ki ba, ki godewa Allah dan bakisan iya alkhaeryhn da yake cikin wannan qaddara ba ki ɗauki kanki ki kwatanta a matsayin da Sarauniya take ciki na rashin lafiya shekaru da shekaru in kece zakice haka? Tom inaso ki kasance mai yiwa Allah godiya dan yaronki kaman yanda Allah ya baki kyautan sa tom haka yake kyauta ga al'umman Annabi SAW kisa albarka a komi da ya shafi Amjad in dai kinason ki shirya da mahaliccinki akan kyautan da ya maki "Kayi haquri Abban sa" shine abinda Umma ta faɗa tana share fuskan ta Abba yace "ba ni zaki bawa haquri ba ki nemi yafiyar Ubangiji tun da wuri" Astagfirullah ya Rabb Allah Alhamdulillahi Allah ka kare mun shi ka basa sa'an abinda yaje nema ka bamu ikon cinye ko wacce qaddara tamu Yauwa Abban sa nikam ya za'a yi da maganan shirin bikin ne tom kaga fa ya kamata ace iyanzu ankai kayan tambaya da sauran su ya rage kayan Aure da sadaki to su masu sarautane Mu kuma Alhamdulillahi Murmushi yayi ai tun ɗazu da wannan magana muke ai da yafi Amma da kikace Alhmdlh kin gama zance shi wannan kalman yafi komi yanxu dai in Allah ya kaimu zuwa goben naje naji qiran akan mene ko ya ya ake ciki inyaso in na dawo mu kuma sai musan ya za'a yi mai ya kamata ayi ba Musan ta ina zamu fara amma mudai Allah ya dawo mana da ɗanmu lafiya shine babba a wajan mu dasu duka Da "Ameen" Umma ta amsa ayyah jarumin Ummansa Ummanka na kewan ka nasan kaima duk inda kake kana kewata Fatam Allah ya tsare mun kai ya haɗaka da mutane na gari Allah dawar dakai gida lafiya ya nuna mana wannan biki Alfarman fiyayyen halitta SAW.

Muje zuwa fan's ✍️

ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️

💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 💦💦💦💦💦💦💦

𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

_______________________________________________________________

🅿️ 51&52

💋💋 امى بتولة💋

** 𝙈𝙖𝙝𝙖 𝙄𝙨 𝙖𝙣 𝙖𝙧𝙖𝙗𝙞𝙘 𝙣𝙖𝙢𝙚 𝙬𝙝𝙞𝙘𝙝 𝙢𝙚𝙖𝙣𝙨 𝙆𝙞𝙣𝙙𝙣𝙚𝙨𝙨𝙨 & 𝙗𝙚𝙣𝙚𝙫𝙤𝙡𝙚𝙣𝙩 Maha is a name for ur baby girl's **

Mahreen ce ta kalleta ganin ta shigo da gudu kuma tana waige sai tace "ke kuma daga ina Maha? Ke da waye wa kika stokano? Maha tace "sai jero mun tambayoyi kike Ina ruwanki" ta wuce banɗaki tayo alwala tazo tai Salla Da ta idar ta ninke darduma ta wuce tayi ɗakin Umma dan tana ga kaman zai iya biyo ta nan ɗin ma Ita dai Mahreen ido ta zuba mata bata kuma cewa komi ba har ta fice a ɗakin taɓe baki tayi ta tashi itama ta ɗauro alwala Assalamu'alaikum Ummata Amsawa Umma tayi shigo mana ɗiyar Umma kuma surkan Ummanta Turo baki tayi Umma kema xaki fara ko zan koma inda na fito Allah Murmushi Umma tayi zo ki faɗamun waya taɓamun ke Autan Umman ta Kan gadon Umma ta haye ta kwanta uhmn Umma nazo bacci a ɗakinki ne Anya ba laifi kikai wa soja ba kika gudo doter? Umma nidai bacci nazo yi banyi komi ba kuma ki tambayesa kiji Tom ayi lafiya Auntan umma Umma wayanta ta ɗauka ta qira layin Ameerah ya shiga har ya yanke ba'a ɗauka ba qara qira tayi haka ba'a ɗauka ba san da ta qira ana uku kamun aka ɗauka Ameerah na ɗauka tace "afuwan Ummana" Ina kika aje wayan kika je? Umma na mance wayan a ɗakine Tom yayi kyau ya kuke? muna lafiya Ummanmu Ya mijinki ya baqonku? Dukanmu lafiya lah Umma afuwan ban faɗa maki ba ai jiya ya tafi Umma da yanayin faɗa tace "Ameera ya tafi kuma ban gane ya tafi ba?" Umma yace abu zaije yi a bauchi tom tunda ya warke zai tafi Ameerah ashe niba uwarki bace da baxaki faɗamun ba ko Abbanku amma de ya maki kyau daga ke har mijin naki Umma Kashe wayanta tayi ranta a ɓace Ameerah ce ta qirata ɗauka tayi tace "Yanzu kuma me kika qira kicemun? Qasa tayi da murya kiyi haquri Ummata amma akwai phone number ensa a wajan Daddyn little Shikkenan naji yanzu ina ya tafi? kwashe duk yacce suka yi da yayanta amjad en tayi ta faɗa ma Umma Yanzu Ameerah rashin hankalinku da rashin tausayinku yakai haka dama mutum besan kowa ba tunda Allah ya haɗa ku ta sanadin hatsari ai seku temaka masa shima nan gaba sai kuga da ikon Allah ya temaka maku ko wa wani naku Baisan kowa a Bauchi ba so kuke yaje yai ta tangariri agarin bauchi ko? Nagode maku Ameera Umma kiyi haquri Allah nace ya bari muzo tare yace a'a time nasa kaɗan ne shikkenan yayi kyau Allah tsare sa ya basa sa'a Haquri Ameera ta qara bawa Umma Umma tace "Bakomi" sallama suka yi ta kashe wayan ta Numbern Abba ta nemo ta qira Ɗauka yayi "assalamualaikum hajiyata ya akayi ya gida" Yallaɓoi kasan me yaranka suka yi A'a sai kin faɗa maman yarana Kwashe yacce suka yi da Ameerah tayi ta faɗa masa Subhanallahi yanzu shi mijin nata biyewa shirmenta yayi? To shikenan Insha Allah zan qira mijin nata ya turoman numbern yaron in yaso sai na turawa Abdul ya kaisa gida ko ina fatan hakan yayi maki Hajiya ta Allah qara girma yallaɓoi hakan yayi sosai ma, Allah shirya mana su sukuma Allah barmun kai "Ameen hajiyata" Abba ya faɗa yana murmushi Ɗan hiransu suka yi na masoya Insha Allahu nima nan da kwan 2 zan dawo hajiyata dan nayi kewanki Amma mai za'a ajiyemun haka aka damu na dawo? "Kaima dai yallaɓoi ka sani dolema a tanadar maka abu mai daɗi koda kaman ruwan roba ne( faro)" Umma ta faɗa tana dariya haba dai hajiyata wannan kam kice nai zamana nasha anan kawai sai dai ko acemun yar buduwar matata ta ajeman kanta Zaka sani jin kunya yallaɓoi har da jikanne nake budurwa? a'a nikam a wajena matata ƴar shawal-shawal take kaman ƴar 18 years Dariya tayi yallaɓoi banda zugi fa kar kasa kai na ya fashe ba jini Dariya suka sa duka sukai ta hiransu gwanin sha'awa har suka yi sallama. Itama Umma hawan gadon tayi takwanta gefen Maha da ta jima da yin bacci...

washegari da sassafe ya tashi, bayan an kawo masa abun kari a gidan wannan mutumin karyawa yayi ya gode yace ze wuce Rakasa wannan bawan Allah yayi suka yi sallama yana qara masa godiya sosai Gaba ɗaya sai kuma ya rasa ta ina zai fara neman wannan bishiyan Tambaya zeyi ne ko yaya? a haka dai ya samu wani bawan Allah yayi tambaya jejiin garinnan babba kowa ce masa yake kawai ya shiga jejin dan ba nan kusa bane Ya shiga jeji-jeji sosai sunfi a qirga dan kwanansa ɗai-ɗai har 5 amma bai samu itacen nan ba.

Mahreen gaba ɗaya ita da ya Abdoul sun zama layla da majnoon qarfi da yaji Yayinda Maha da soja abun nasu de sai du'aee kullum kaman wuta da auduga haka suke Yau Abba zai dawo bayan kwana biyar da aka qara masu a aikin nasu Me aiki ta gyara gidan tsaff sa qamshi kawai ke tashi, kitchen kuma tare da su Mahreen da Maha aka yi komi Bayan sun gama sun kammala komi kowa ya wuce dan ya shirya Sunyi wanka duka Maha tawa little ma wanka duk sun shirya kowa yayi kyau Umma tayi ado cikin dogon rigan swissless blue black tasha sarqanta da kunnenta na gold karkuso kuga kyawun Umma kaman wata Amarya, sai ka ranste bata haifi soja da Ameera ba Futowa falo tayi ta zauna sai qamshi take Maha ce ta fito ɗakinsu tana isowa palorn tace "Rassss Ummata kyau haka ai sai kisanya Abba kasa haquri ya huta" Umma amma kinsan me saura abu 1 makeup kizo muje namiki Allah zaki ganki Amarya sak kawai Murmusawa tayi ta mata danqwalo, Yau kuma nice abokiyar wasan taki doter? Umma bafa haka nake nufi ba Suna cikin hiransu basu ko ki dirin motorn Abba ba sai sallaman sa tare da Soja da little Ayoyo Abbana da gudu Maha ta rungumesa Doter an girma ba'asan an girma ba zaki karya Abban naki ai Dariya tasa Abba inna karyaka dole a aikani aikin soja na karya soja Shafa kanta yayi Allah maki albarka uwata. Umma kuma zuba masu ido tayi kawai sai murmushi take Abbane da suka haɗa ido ya kashe mata ido guda 1 kauda kai Umma tayi tana dariya qasa-qasa Haurawa sama Abba yayi ya nufi ɗauki ganin haka sai Umma ta tashi tabi bayan sa "Su Umma miji" inji Maha tana dariya Buge mata baki Mahreen tayi wai ke iyayenki ma abokanan wasanki ne ba wanda kika bari Abba na isa ɗakin yana juyawa kallon qofa sai sallaman Umma, Buɗe hanu yayi da sauri Umma ta faɗa jikinsa suka rungume juna Hajiyata kinyi kyau na sayi wankan nan tabbas irin wannan haɗewa haka ina ma zan iya kallon kowa Murmushi tayi shikkenan yallayboi wanka ta biya kuɗin sabulu Umma taya Abba tayi yayi wanka Ya shirya suka fito suka yi qasa dan yaci abinci Abba ne yace "nifa a qasa zan zauna" Abincin suka kawo qasan da komi duk zaama suka yi Umma tayi saving mijinta Sunacin abinci suna fira

Kwarewa Maha tayi, da sauri kankowa ya motsa Soja ya miqa mata ruwa dan yafi kusa da kofin ruwan Amsa tayi tasha kamun taji normal sannu kowa kece mata Bayan sun kammala cin abincin Abba ya kalli Soja wai son yaushe ne zaku Cairo en ne ko turkey kace? Sosa kai yayi Abba nifa ba lalllai naje ba gaskiya Ko meyasa son? Abba kawai banson nisa da gida ne gaskiya Shikenan fyne Allah temaka. Tashuwa Abba yayi to kuyi hira lafiya ba naje na kwanta na huta gudnyt koh yaran kirki Bayansa Umma tabi ta tayasa rage kayan jikinsa Kwantawa Abba yayi, Umma zaunawa tayi a gefen gadon Kallonta yayi lafiya tawan ba kwanciya zamu yi ba ko dai akwai wani abun ne? Bakomi yallaɓoi Uhmn yauwa nace ka amshi numbern ne? A'a ban amsa ba kin san sai a hankali sungulloli sun man yawa To Allah ya temaka my yallaɓoi Yanxu ki qira mijin Ameeran ya turo bacci nakeji Tom yallaɓoi ɗaukan wayan tayi ta fice a ɗakin duka Qiran Daddyn little tayi suka gaisa shima ta balbalesa kamun suka shirya tace ya turo mata layin yaronta, Haquri ya bata a take ya tura mata layin. Ganin layin ba qaramin farin ciki tayi ba shiga kan layin tayi tai...............

Muje zuwa fan's ✍️

ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️

💋💋 امى بتولة💋

𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

💦💦💦💦💦💦💦

𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮

𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖

(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍

_______________________________________________________________

𝘿𝙪𝙠 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙩𝙖/𝙮𝙖 𝙨𝙖𝙪𝙮𝙖𝙢𝙪𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙮𝙖𝙛𝙚 𝙗𝙖 𝘿𝙪𝙠 𝙠𝙪𝙨𝙠𝙪𝙧𝙚𝙣 𝙙𝙖 𝙢𝙪𝙠𝙖𝙞 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙮𝙖𝙛𝙚𝙢𝙪 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙗𝙖𝙢𝙪 𝙞𝙠𝙤𝙣 𝙖𝙢𝙛𝙖𝙣𝙪𝙬𝙖 𝙙𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙗𝙖𝙧𝙞 𝙒𝙖𝙟𝙖𝙣 𝙠𝙪𝙨𝙠𝙪𝙧𝙚 A𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙠𝙖 𝙮𝙖𝙛𝙚 𝙢𝙖𝙣𝙖 𝙗𝙞𝙟𝙖𝙝𝙞 R𝙖𝙨𝙪𝙡𝙪𝙡𝙡𝙖𝙝𝙞 SAW ❤️

🅿️ 53&54

💋💋 امى بتولة💋

Abdoul ne zaune a ɗaya daga kujerun dake palourn kakar tasu, kujera me zaman mutum ɗaya 1 yana danna wayan sa. Hayrace tazo tawuce sa tana "Babban yaya sannu da zama halan yau kazo gadin kakus ne?" Ke dai bari kawai boɗɗi Kakus hukuma ce sai da rarrashi, tace "tom nide nayi kitchen yaya kamun ta fito ta balbaleni ban gama girki ba rana tayi Dariya yayi yace "keda kakus kam sai Allah kullum faɗa amma bata iya kwana bata ganki ba wataqil in mun aurar dake tare mijin ze aureku" Caraf sai a kunnen Amarya wacce ke fitowa yanzu daga ɗaki tace "Yo inba sinqin shishishigi shigilitu da sa ido irin naka ba ina ruwan ka tsakanina da baiwar Allah, Allah ne ya haɗa jininmu atou kuma qarshe ko mutuwa tare zai ɗauke mu bare miji da daman wannan dolen sa ne in dai ba'a tangaɗe aka haife sa ba ba mai raba mu" wucewa kitchen Hayrat tayi ba tace qala ba sanin halin kakar tata, ai kuwa dai bata stira ba dan kakus bin bayanta tayi da harara tace "kinanan a wajan kaman tangaɗaɗɗen budurwan kaza, ai da karma kije kiyi girkin yo ai ni dole ma na biki gidan miji kar kije kimana abun kunya tunda de baza kiyi abuba sai ance kiyi dan tsabar layiii" da ta gama ɓaɓatun zama tayi a kujera me ɗaukan mutum 2 tana bismillahi ni jikan mutum 4, Abdoul ne ya kalleta sannu da fitowa uwargida ta bayan ke babu wata sai dai amarya ya qarisa yana dariya Da har ta washe baki sai kuma ta stuke bakin kallonsa tayi tace "Yau ɗan nan har yaudaran yakai haka a gabana kake faɗan sai de amarya? Tom jeka na yafe maka ka kawo badon halinka ba ɗan kwal uba" Murmushi yayi shiyasa nake yinki amarya uwargida, gaisheta yayi ta amsa tana tambayansa ya aiki ya kishiyanta? Murmushi yayi ai maganan kishiyan naki ma shi ya kawoni Hajiya Kakus tamu، Yauwa dai ango ai ni nafison haka kuyi aure tun da raina inga yaranku Allah raya ku ya baku zuri'a mai albarka, nifa so nake kan na mutu naga har da tattaɓa kunne na kaga ƴar albarka takwarata matar auwalu har cikin na biyu gare ta kaga da yardan Allah in ta haifi mace kan na mutu zan aurar da yarinyan, Murmushi Abdoul yayi yana jin shirmen kakan tasu bai ce komi ba shi dai . Yauwa to wacece kishiyar tawa ma tukunna insan wacece ta shirya kishi da mairama daso, Murmushi yayi yace "wata baiwar Allah ce nutsaststiya kyakkyawa ga hankali ga ilimi ga tarbiya ga asali ga ga ga........." Me amarya zata yi in ba dariya ba Abdu lafiyan ka ko dai duk ta tangaɗar da kai ne ta zautar mun da ango tun yanzu ta mallakemun kai, murmushi yayi haba de ai ni dake mutu ka raba, Tom irin wannan lissafowan haka ko kunya na baka ji ba yo ma ai ka rage dan ganin idona kar nayi kishi nace a'a ko, Murmushi yayi ai kema kinsan kin fita komi amarya uwargida kuma duk a wajanki ta gado su, washe baki tayi Allah maku albarka jikokina Allah sanya alkhaeri, da Ameen ya amsa yace "Kakus ba kowa bace face... Maganan hayra ne ya tsaida shi tace "ya Abdoul yi sauri ka faɗa na matsu naji wacece akewa yabo ba kunyan kakus Allah yasa dai wacce nake tsammani ne" Danqwalan ta kakus tayi to ƴar kwal uba haɗasu kasa rabasu bazaki shiga tsakanin mu ba kuma baza'a faɗa ba tafi ki bamu waje gulmammiya kawai, taɓe baki hayra tayi tace "in tayi tsami za muji" ta wuce abinta Yace yauwa kakus AISHA ce fa MAHREEN Guɗa Kakus tayi tare da kabbara tace "ALHAMDULILLAHI Allah nagode maka ni mairo, amma naji daɗin wannan batu Allah maku albarka Abdu, a Yauwa kaga ina ma wayana ne laluɓosa tayi ta miqa wa Abdoul tace "gashi dannamin layin ita uwar tasu tunda ta balaga ta balage garin su ba abinda ake koya masu sai tangaɗi bata neman albarkan uwarta to ni uwarta zan nemi albarkanta ƴar jakar uba kawai" Qiramun ita in bazata zo ba ni zan iya zuwa har qasan masu layiin inba ma tsabar tangaɗe wa ba asawa gari sunan mutum wai fa sunan uwata sunan garin nasu tom dai bazai hanani qira ba, qasan kulu masu tangaɗaɗɗiyar hali suna koyawa yaran mutane fitsara da rena iyayensu wannan baqin halin har ina ni Mairo ɗan nan qiramun ita da wuri Karɓa yayi haba kakus surka tace fa kibar zaginta nikam Au ashe surkar ka ce? tom ban sani ba hanani faɗan abunda nayi niyan faɗa dan kwal ubanka jai'ri kawai ina ruwanka ni da ɗiyata inma me nace wani ya haifarman ita ba dai nice na haifi abata, shekara nawa ban sata ido ba ba dole abun ya dameni ba tunda zuciyata ni ba irin na ƴan kasar su bane, ita fa kaɗai gareni ɗiya mace, tom don haka karka shiga tsakanina da ƴata yar albarka Murmushi yayi dama abunda ya sashi saka baki kenan ta dena mita gashi hartasawa ummeyhn tasu albarka Numbern Ummeyh ya dubo ya qira, yana shiga aka kashe aka qira. Miqawa kakus wayan yayi Kinga ma ta kashe ta qiraki gashi kuyi magana to Yanzu dan tsabar ka renani baka ganin girma na ni uwar ubanka shine bazaka ɗaukan mun qiran ba na ɗauka da kaina dan jakar uwaka bazan ɗauka ba to Ɗauka yayi da sauri gudun kar qiran ya yanke "Assalamu Alaiki gwaggo" Amsawa tayi ah ah yaron gwaggo sai yau ake jinku kenan nasan yau ma albarkacin uwata aka qiran ko? Sunkuyar da kai yayi yana sosa qeya ayi haquri Ummeyh abubuwan ne sai a hankali, Ummeyh taace "Bakomi yaron Gwaggo" gaisawa suka yi yace mata "ga kakus" ya miqawa amarya wayan Amsa wayan Amarya tayi bayan ta karkata ɗaurin kwalinta Sallama Ummeyh tayi kakus tace "bazan amsaba dan gidanku wato de Jamila kin girmi neman albarkan uwaki sede ni na nemoki bazaki iya zuwa ki ganni ba bare gaisuwa kema kinbisu kun taru kun tangaɗe kunzama tangaɗaɗɗu masu layi to yayi kyau ni Mairo bazan maki baki b Allah shiryaki y maki albarka, amma nasan wannan balaraben mijin naki baze hanaki zuwa ba dan hankali garesa ga sanin girman iyaye tunda dai yaron nan habu har yamun takwara, Ammade Allah ya shirya mun ku wallahi. Ummeyh najin ta bata ce komi ba har ta gama magana sanin halin mahaifiyar tata "Kiyi haquri Gwaggo Insha Allahu bazan wuce kwana 2 ba zaki ganni" Ummeyh ta faɗa cikin ladabi Yauwa dai yar albarka ko kefa ni shiyasa nake sa maki albarka kullum ko baki nema ba dan kinfi sauran jin maganata Allah de ya maki albarka ya rabaki da tangaɗewa har abada Ta amsa da Ameen suka yi dan hira sama-sama can suka yi sallama kashe wayan tayi ta aje, qwalawa hayra qira tayi "Harirtu qawar kakus kawo man ruwa nasha ƴar albarka bakina sai zikiri yake duk sun bi sun sani surutu kaman kanari" Hayran ta shigo da sallama ta miqo mata ruwan ta karɓa tasha, Abdoul ne ya murmusa yace "yanzufa kika koreta gashi da kanki kin qirata" hararan sa kawai Amarya tayi bata ce masa komi ba. Abinci hayra ta shirya masu suka wuce dinnig kowa ta zuba masa, cin abincin suke bame cewa komi Sede kakus da bakinta baya shiru kana ganin bakin kasan akwai abunda yake son cewa..

Bayan ya turo mata layin ɗauka tayi ta qira amma sede be shiga ba ta gwada yakai sau uku 3 amma baya shiga akashe take ji, hankalinta ne ya tashi sosai dan haka kawai take jin kaman ba lafiya ba, dafe kai tayi tana ambaton sunan Allah "Ubangiji yasa ba wani abun ta sameka ba yarona" sai kuma tunanin ɗan ta yafaɗo mata rai nan take hawaye ya cika idonta jin kaman mostin mutum ya sanya ta saurin sharewa ta seta kanta, Mahreen ce ta shigo palourn zuwa wajanta tayi da sauri tana cewa "Ummanmu lafiya? Mai ya faru?" Murmushi tayi bayan ta ɗago kai tace "lafiya lau doter kawai na qira wani layine auntynku Ameera suka turomun sai de bai shiga ba" Mahreen tace "to amma Umma tagumi ba kyau ki dena kinji Insha Allah lafiya lau layin kuma zai shifa kibari anjuma ko gobe ki gwada inyaso in bai shigaba sai ki qirasu ki faɗa masu ko zasu qira maki layin ko Umma" Shikkenan doter ina Auntan Ummeyh fa? Tana can ɗaki da waya banmasan me take ba, Umma tace "to je ki qiramun ita" tashuwa Mahreen tayi tana to Ummanmu Wucewa Mahreen tayi ɗaki dan qiran Maha, Umma Qiran aminiyar ta ne ya shigo wayanta ta ɗauka suna gaisawa da alama magana me muhimmanci suke yi. Mahreen bayan ta shiga ɗakin ta samu Maha akwance tana danna waya, fisge wayan tayi tace "wai me kikeyi ne awaya kam maha?" Turo baki Maha tayi tace "ni don Allah ki bani kar ki batar dani inda nake abu ya ɗauko daɗi" Kallon fuskan wayan tayi ta kalli Maha mene wannan kuma? littafi ne? Maha tace "eh novel ne wallahi Adda kuma me shegen daɗi" Kallonta tayi tace "ooh kekam da novel bansan waya koya maki karantawan ba ma ni Indo" Allah kema Adda Mahreen in kin fara karanta littafinnan ba zakiso ki tsayaba ga abun tausayi ga darasi aciki ga daɗi kuma ayya barin ma maisunana ta cikin ɗayan littafin abun tausayi bakiga Yacce mamanta take treating nata ba, Kallon Maha tayi tace "to yanzu dai faɗamun sunan littafin dai ko" Guda biyu 2 ne aka turomun masu shegen daɗi kekam ma ba'a gama labarin ba tukun ɗayan dai sunansa JAHILCI KO AL'ADA ɗayan kuma something maita ne ko me na mance amma Adda kinji daɗin littafin nan kuwa wallahi ya burgeni, murmushi Mahreen tayi ai kuwa zan karanta nima ba na samu zama

( KUMA FAN'S KARKU SAKE A BAKU LABARI DOMIN KUWA DA ƊUMIN SA YAZO JAHILCI KO AL'ADA? VERY SOON ZA'A SAKE MAKU SHI 𝙊𝙪𝙧𝙢𝙢𝙖𝙝𝙣 𝙗𝙖𝙩𝙤𝙤𝙡𝙚𝙧𝙝🔥 𝙛𝙤𝙧 𝙡𝙞𝙛𝙚 )

Tom yanzu tashi muje Umma ce tace na qiraki, tare suka fice a ɗakin sukai palourn wajan Umma..

Readers Also Read