'yar sarki ce by uwar batoolerh - Chapter 2
'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 2: 'yar sarki ce by uwar batoolerh Chapter 2. Cikin babban birnin kaduna Anguwan GRA anguwa ne dake ɗauke da manyan…
4,467 words
Cikin babban birnin kaduna Anguwan GRA anguwa ne dake ɗauke da manyan ginunnuka manyan gidaje sannan anguwane da ba cikowan mutane sede ɗai ɗai ku ,sekuma masu tsaron gidaje. Bangare guda kuwa wani babba gidane nagani nafada na hanga wanda yafi ko wannen ɗaukan hankalina, sojojine kewaye da gidan tundaga waje har cikin gidan. Gidane babba sosai wanda haraban gidan ke cikeda manyan motoci iri iri daga mabanbanta company's!!! Sojojine kota Ina a gidan da Alama de gidan Wani babba ne kuma me kuɗi. Batanan gidan wani qaramin yaro nagani kyakkyawa dabaxe wuce shekara 3 aduniya ba yana wasa da ball Yana gudu yana dariya har cikin babban palourn gidan. Wowww shine abunda nafurta ganin irin haduwa da tsaruwan wannan palour Palour ne babba me ɗaukeda manyan kujeru blue colour qirar Italian royel chair's Fadin tsari da haɗuwan gidan nan ɓata bakine Yaron ne de yayi sama Yana Hawa steps en Dan zuwa ɗaki. Wani ɗaki naji alamun mosti aciki. leqawa nai Dan ganin menene Wata dattijuwace na hanga zaune kan sallaya da Alama ta idar da sallah ne ganin hannuwan ta sama tana adduah
Faɗi take::: YA Allah ka bayyana mun shi inyana Raye ,inkuma baya Raye Allah nayafe masa Allah kasadashi d annabin rahama Addu'oee takeyi tana hawaye ,( nide danake gefe Ina cikide mamaki dakuma al'ajabi).
Ganin wannan yaron yafaɗo mata a jiki Shafa addu'an tayi ,tace angon! ya akayi? Da maganan sa kaman gwaranci(gwamanti) magana be nuna sosai ba yace'' gilani cayi danca( granny shayi zansha). Ɗagasa tayi tace tom mijin gilani.tashi muje Koh,cire hijab en jikin ta tayi nannade sa. Ɗaukansa tayi sukayi palour me aikinsu ta qwalawa qira ,tazo ta stugunna hajiya gani,yauwa indo ahadawa little tea ko musamman yaɗagoni wai zesha shayi, ranki ya daɗe banda rigiman wannan miji naki ai da seyaxo yafaɗamun kawai ba seya tasoki ba,ai in beyi haka ba indo be yi rigiman ba kede jeki kawo mana kawai، tace tom hajiya ta tashi ta tafi Dan kawo masa tea en, hira suke da wannan yaron yanamata gwalantinsa da maganansa dabai nuna sosai ba.
Da sallama ta qaraso palour miqawa Hajiya cup tayi ranki yadaɗe ga shayin me gidan naki, murmushi tayi ta amsa yauwa indo Allah biya angode, bakomi ranki yadaɗe tafaɗa tana miqewa tayi hanyan kitchen. Miqa masa shayin Hajiya tayi ta zuba masa ido tana Kallon yaron dake shan shayinsa hankali kwance murmushi tayi idonta akansa, da alama de ta faɗa duniyahn tunani, seda yaron yasa mata cup na tea en abaki kamun tadawo daga duniyan tunanin datake, cewa yake kica cii gilani murmusa wa tayi tana kauda fuska Yana kan tura cup en fuskanta akan setasha , dayaga taqi seya saka mata kuka!!!! Dede da sallaman Wani dattijo yashigo palourn sanye da kayahn sojoji a jikinsa.
Amsa sallaman tayi tana masa sannu da dawowa!! yayinda yaron kuwa yana ganin wannan dattijo yasauqa yaje wajansa da gudu Yana kuka, ɗagasa yayi waye ya taɓamun aboki yasamun shi kuka na harbesa? Yaron yace afoki gilani ce nafata cayi na taca taqi ca yafaɗa yana nuna masa cup en hanunsa Wannan dattijon murmusa wa yayi yace to nibani Nasha aboki tunda ita taqi sha batasan akwai daɗi ba Koh? Daga kai yaron yayi ya sa masa cup en tea en a baki kurba dattijon yayi yana girgiza kai yace kai shayin aboki bade daɗi ba daɗi yawuce grannyn ka kuma kar ka tsammata ko, dariya yaron yasaka yana eh afoki an anmata ba kuma. Sauqe yaron yayi yaqaraso gefen matar tasa yazauna yana Hajiya ta Barka da gida, Sansanyar murmushi tamasa, tashuwa tayi takawo masa ruwa yasha tace sannu da hanya baban Yara. Murmushi yamata sannu da zaman gida Maman Yara
Sauqe kanta tayi qasa tana wasa da zoben hanunta idonta atake yakawo kwallah!!! Kallonta yayi Hajiya ta lafiya ko kukane tarban da za'a mun ban ko hutaba? Kukan kuwa tasaka tana yallaɓoi ya labarin yarona tafaɗa idonta na zubar da kwallah Kallonta yayi bece komiba Kuka wannan dattijuwan da aqallah takai shekara 48 tafashe dashi Kallonta alhajin yayi yace.........
muje zuwaaaaaa masoyaaa ✍️
Dan jin menene take wa kuka? Me take nufi da yaronta?. Sannan kuma addu'an me take nufi?
Duk wannan amsoshi zamu samesu ne inmuncigaba da bibiyar wannan labari namu me suna ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
Allahummah salli ala sayyiduna Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama
💦💦💦💦💦💦
YAR SARKI CEE
🌹🌹🌹🌹🌹
𝗦𝘁𝗼𝗿𝘆 𝗔𝗻𝗱 𝗪𝗿𝗶𝘁𝘁𝗲𝗻 𝗕𝘆 𝗛𝗮𝗿𝗶𝗿𝗮 𝘀𝗮𝗹𝗶𝗵𝘂 𝗶𝘀𝗮𝗵 (ourmman batoorlerh 🔥)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
__________________________________________________________
🅿️ 13&14
💋💋 امى بتولة💋
Hajiyata ,nazaci kinɗauki wannan amatsayin qaddaranmu Yau shekara 30 Amma kusan kullum se kinyi maganan ɗanki ɗanki Nimafa yaro nane , haryau banjin akwai yaron da nakewa sonda nake masa ,Amma a hakan nima na haqura kema kisa haquri kinji muta addu'a kuma mu miqa lamarinmu ga ubangiji Kaman yacce muke adduah kullum in Yana Raye ko a inane Kuma inda rabon haɗuwanmu dashi kamun Rai yayi halinsa Allah yhadamu Inkuma ba rabon haduwanmu Allah masa albarka yakaresa Ako ina ,inkuma baya Raye Allah jiqansa mude munyafesa yafaɗa da sigan rarrashi. Kwantar da kanta wannan dattijuwan tayi a kafaɗan sojan mijinta Yana lallashinta.
Little ne yazo shima Yana hawaye yanacewa gilani cidena kuka Nima danyi inbaci denaba Ɗaukansa tayi ta rungume sa tana share nata hawayen nata murmushi tayi nadena mijin gilani ta sumbaci goshinsa kwantawa yayi ajikin kakar tasa ba jimawa bacci yaɗaukesa. Kallon mijin nata tayi ,baban Yara Allah yaronnan kallon yarona nake masa sosai komi nasa kaman na yarona Murmushi Alhajin yayi Hajiya ta rigima yafaɗa ya miqewa. Ɗauki mijinki muje ki kwantar dashi nikuma atayani shiryawa, ko de miqosa naɗaukesa kar ya wahalar mun da mata murmushi tayi tace yallaɓoi kai de kahuta murmushi yayi Allah maki albarka Hajiyata Tace Ameen yallaboi suka tashi sukayi sama ...
𝗚𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘀𝘂 A𝗺𝗷𝗮𝗱
Bayahn yatashi bacci yayi salla𝗵 yataya ummansa ayyuka 𝗦𝘂𝗻𝗸𝗮𝗿𝘆𝗮 hansti yayi. Abbansa zefita kasuwa yace Abbana tsaya mufita tare, yace tom ɗan Abbansa na tsaya ,dukda dama a staye nake Dariya Ummansa tayi, jarumin Umma yakamata amun surka fa adena barina ni ɗaya a gida nima. Bayahn yaja dokinsa yace tom Ummana angama, murmushi tayi tace tom Allah tsaremunku duka adawo lafiya addu'a ta musu sosai Sannan suka fita, abba ke tambayansa yaushe zaka dawo? yace Abba insha allahu bazan wuce kwana biyu ba, yace kakula sosai fa da jejin nan Allah Kuma yakareka yatsare mana kai , yace Ameen abbana mesona Jan kunnensa yayi wato dan ba Ummanka shine Wani abbana mesona da tana nan kuwa ba za'a cemun haka ba nasani!! Murmushi yayi yana Abba ai seka cireman kunne, inna cire maka kunne kam kace ummahn ka zata kai ni qara ai, murmushi yayi Allah barmun ku Abba na da Ameen Abban nasa ya amsa sukayi sallama da abban nasa. Yayinda shi yayi hanyan jeji, abbansa kuwa yayi hanyan tafiya kasuwa ,Wanda ke cikin masarautan Tafiya yake anuste ,tafiya irin ta jarumai ( ba na mata maza ba) Sanda ya isa bakin qofan fita garin masu gadin yauma saida suka gaidasa, amsa masu yayi ataqaice kaman koda yaushe yawuce. Bayahn fitarsa a masarautan ne yahau dokinsa yayi hanyan jejin.
Wannan kenan....
******* GIMBIYAA MEHWISH
Bayahn tabar wajan iyayen nata ɗakinta takoma, zagaye dakin take tayi tarasa meke mata dadi Ahaka de har tagama Shirin bacci takwanta Safiyar alkhairy uwar dakina MEHWISH
( Deejerhn mu MEHWISH na gaidaki)
**** Tafiya yake akan dokinsa sosai yayi nisa a wannan jejin Bishiyan dayake nema yagani tsayawa yayi a wajan Yana ciran ganyen dakuma sassakensa bayan yagama yacigaba da tafiya dan dubo ɗayan mahaɗin har lokaci yatafi besamu ba. Sosai yadudduba ɗayan mahadin maganin amma besamu bishiyan ba haryanzu Gashi lokaci yaqure masa dare yafara yi wannan yaja dole ya kwana ko fin kwana ma a jejin, A gefe ɗaya na zuciyarsa kuwa Ummansa yake tunani bayaso ko kaɗan yayi kewanta ko yawuni be ganta ba bare kwana( Allah tsaremun ke a ko ina Umma ta)
**A masauratahn kuwa sosai ake shirye shirye ba kama hanun yaro......
Yayinda Nima ourmman batoorlerh nake qara Shiri danbawa idona abinci
Sunan littafin 𝘆𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗰𝗲 Daga taskar 𝗨𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 ✍️
𝗧𝗮𝗸𝘂 𝗮 𝗸𝗼𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘂𝘀𝗵𝗲
*duk abunda yake ba Dede ba Allah kayafemu masu karantawa da me 𝗿𝘂𝗯𝘂𝘁𝗮𝘄𝗮 𝗱𝘂𝗸𝗮🥹 Allah kaimana rahama alfarman rasulullahi sallallahu alaihi wasallam ♥️
𝗔𝗹𝗹𝗮𝗵 𝗸𝗮 𝗱𝗮𝗳𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗶𝘀𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗾𝗼𝗻 𝗱𝗮𝗻𝗮 𝗱𝗮𝘂𝗸𝗼 𝗻𝗮𝗸𝗲𝘀𝗼𝗻 𝗶𝘀𝗮𝗿𝘄𝗮 𝘁𝗮 𝘄𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗶 𝗯𝗶𝗷𝗮𝗵𝗶 𝗿𝗮𝘀𝘂𝗹𝘂𝗹𝗹𝗮𝗵𝗶 𝘀𝗮𝗹𝗹𝗮𝗹𝗹𝗮𝗵𝘂 𝗮𝗹𝗮𝗶𝗵𝗶 𝘄𝗮𝘀𝗮𝗹𝗹𝗮𝗺
ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚 💦💦💦💦💦💦💦💦
𝗬𝗔𝗥 𝗦𝗔𝗥𝗞𝗜 𝗖𝗘𝗘
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 𝗗𝗮𝗴𝗮 𝗮𝗹𝗾𝗮𝗹𝗮𝗺𝗶𝗻 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗮𝗸𝗼𝗱𝗮 𝘆𝗮𝘂𝘀𝗵𝗲
( Uwar batoorl )✍️
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
______________________________________________________________
🅿️ 15&16
💋💋 امى بتولة💋
🄽🄸🄶🄴🅁🄸🄰
Garin Kaduna anguwan GRA qarfe 10:40am nasafe acan yamun. As usual addu'a yauma na sameta zaune kan sallaya takeyi da alama de abun yana damun ta sosai dan hawaye ne a fuskan ta shaɓe shaɓe.
( Allah maji roqon bawansa ne, komi yadameka aduniya , kama allah da manzonsa ka kama adduah insha allahu, allah xe sassauta maka komi).
Bayahn ta idar da addu'an tashafa hawayen fuskanta ta share ta tashi ta naɗe abun sallahn da hijab nata tafito ta ajiye a Waldrop, ta fito tayo qasa palour dan jiran dawowan mijinta da suka fita tareda jikan nata. Zaune take a main palourn nasu tana kallon labarai a tv dake maqale a bangon palourn duka hankalinta na kan labaran, sallaman da akayi yasata juyawa murmushi ne shimfiɗe a fuskan ta tana amsa musu maraba da baban yara da angon granny, zama sukayi alhajin yace yauwa Hajiya maman yara, ganin tashin yau matan nasa damuwan da sauqi fuskan ta asake hakan yamasa daɗi hira suke suna kallon tare, little ne yasauqa yaje wajan tv yaɗauko remote, Hajiya ce tace angon granny miqo karka shiga wani wajan takowa yayi yakawo mata yana un gilani aci ci canja mun doyi doyi an gani ( cartoons), amsa Hajiya tayi tom rigimammen miji kawo insaka maka masu fitina kaman kai sauya tasha tayi aikuwa ta stallen sa ya nemi waje ya zauna yana kallon cartoons en, Alhaji na kallon su yana murmushi.
Bayan wasu awanni Zaune suke a palourn nasu alhajin na aiki a system yayinda Hajiya da little ke karatu Me aiki ce tayi sallama a palourn stugunnawa tayi tagaida alhajin amsawa yayi da fuskansa ba yabo ba fallasa, qasa da kanta tayi hajiya akawo abincin nan ne ko abari a dinning? Ah ah indo kawo nan kekam, amsawa tayi ta tashi takoma dinning area ta kwaso abincin takawo masu nan palourn en, data gama kawowa tajuya takoma. Hajiyan ce da kanta ta tashi tayi saving nasu.
( dukda stufanta bata bari me aiki tamata komi na miji wonderful haka akeson mace, bakaman wasu matan namu ba hatta shinfiɗan miji se an masu Allah kyauta)
Suka zauna cin abincin daren Bayahn sun kammala hajiya da kanta tahaɗe komi me aikin ta qwalawa qira tazo tadaga kwanukan tayi kitchen dasu.
Little yace gilani kallonsa tayi tace na'am angon granny ,gilani namaki addu'a da nabi apoki na macallaci ai!!! Ta kallesa, tom kanari mijin granny faɗamun mekace a addu'an naka? Washe haqora yayi yace gilani, nace allah anca addu'an da gilani na taceyi kuyyum!!! Murmushi tayi tace ameen ya hayyu ya qayyum tana lumshe ido(yaro qarami da halin manya) Allah maka albarka mijin granny Yace ameen gilani nah.
Kashe kayan kallon hajiyan tayi ta taya mijin nata haɗa kayan aikin nasa, suka haurawa sama sukayi dan bacci ganin dare yayi.
Adduah granny tamasa ta kwantar dashi sleep tight ko angon gilani Kwanciya suma sukayi itada mijinnata. Nace safiyar alkhaeryh kakanun little ...
🅆🄰🅂🄷🄴 🄶🄰🅁🄸
washe gari da safe bayahn sun karya alhajin nata yashirya dan fita rakasa sukayi itada little har yashiga motor suna masa adawo lafiya driver yaja motor suka fita kamun suka komo cikin palourn itada angon nata. barin little en tayi yana wasan sa tayi daki dan tayi bacci har ya kwanta taji qaran wayanta alaman qira yashigo ɗauka tayi da murmushi ganin wacce ke qiran nata Assalamu alaiki ummana antashi lafiya Fuskanta da murmushi ta amsa sallaman tace lafiya ya gida ya jikinnaki? Tace dasauqi!!! ummana ya mijinki da rikici? Tace ah bawani rikici inma yanayi keya gado muna lafiya lau duka!!! Tace umma danzo anjuma nida daddyn little Tace tom allah kawoku lafiya kigaida sa,tom zeji umma. Sukayi sallama ta ajiye wayan nata ta kwanta...
*** Bayan ta farka alwala ta ɗauro tayi walha tayi addu'oeen ta kaman kullum, bayan ta idar palour ya yiwo. """'Little dake wasan shi taqiran bayan taɗauko takaddun arabic nasa, suka kama karatu.
Bayan sun kammala karatun tace to mijin granny jekaima kayi bacci kahuta ko kamun momynka tazo maqe kafaɗa yayi yace gilani an bi momy ba a wajanci da apoki an jauna Tace ai dama ba tafiya dakai za tayiba kaikam je ka kwanta abinka koh Anan palourn ya kwanta baccin kamun zuwan su momyn nasa.
🅀🄰🅃🄰🅁
***** washe gari ma hakan yafaru sosai 𝙖𝙢𝙟𝙖𝙙 𝚢𝚊 𝚔𝚎𝚠𝚊𝚢𝚎 𝚓𝚎𝚓𝚒𝚗 𝚊𝚖𝚖𝚊 𝚋𝚊𝚒𝚜𝚊𝚖𝚞 𝚍𝚊𝚢𝚊𝚑𝚗 𝚖𝚊𝚑𝚊𝚍𝚒𝚗 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚋𝚊 gashi ya kwana yayi nisan tafiya sosai. Tafiya yake a wannan jejin yana kan duba maganin hango wani bawan Allah yayi besan daga ina ba kawai shide ya gansa amma bega inda ya ɓullo ba stohone kutub a durqushe yake tafiya. Stohon ne ya tsaida shi yace yaro naga kaman abu kake nema Koh? gaidasa yayi yace eh baba, me kake nema haka yarona? faɗa masa sunan bishiyan yayi, wannan stohon yace tom yarona xantemaka maka da wanda yake wajena dan naga tabbas kasha wahala Amma ba'ah samun wannan bishiyahn anan kusa Se a qasar 𝙉𝙞𝙜𝙚𝙧𝙞𝙖, 𝚈𝚊𝚌𝚎 𝚜𝚑ikkenan 𝚋𝚊𝚋𝚊 𝚗𝚊𝚐𝚘𝚍𝚎 miqa masa yayi a qulle a stumma yace Tom gashi yarona, 𝚊𝚖𝚜𝚊 yayi yamasa godiya sosai 𝚜𝚞𝚔𝚊𝚢𝚒 𝚜𝚊𝚕𝚕𝚊𝚖𝚊 𝚍𝚊 𝚠𝚊𝚗𝚗𝚊𝚗 𝚜𝚝𝚘𝚑𝚘𝚗. Yajuya da farin ciki yana tafiya a kan dokin nasa , sosai dokin nasa ke gudu, yayi kewan umman sa kwana 2 ake nema begantaba ya qagu yasamu yakoma yau komi dare yaganta...
🄼🄰🅂🄰🅁🄰🅄🅃🄰
* 𝙜𝙞𝙢𝙗𝙞𝙮𝙖 𝙢𝙚𝙝𝙬𝙞𝙨𝙝 Wajan mahaifiyarta take , tana zaune tasata gaba, wannan bluen qwayan idon nata kwallah ne cike a cikinsu Jikin mahaifiyar tatace yatashi gaba ɗaya tarasa meke mata daɗi arayuwa!!! Dama haka ciwon yake mata Inya tashi bata iya ko mosti bare magana komi se anmata Sede ido kawai in yayi dama dama ne takan iya magana harta zauna da kanta Amma dukda haka komi mata akeyi sakamakon qafanta dabata iya takawa dashi, tsawon shekara 15 tun bayahn data haifi gimbiya bata sake lafiya ba tun abun na kaman wasa har yazamo se a hankali Data samu wani ciki tayi bari( misscariage) , shikkenan ciwon nan yasameta bata iya komi yazama very serious Sosai aka nema mata magani na gida dana asibiti amma inah haryanzu basu daceba Kullum cikin gayyatar masu magani akeyi Amma abu ɗaya akece masu shine suyi haquri basusan maganin ciwon nata ba, basusan ina zasu samosa ba, dan iya binciken su babu aqasar dasuke(inji bokaye da wasu malaman) Ance za'ah bawa duk wanda yabata magani tawarke kyauta amma dukda haka babu, aka maidashi kaman gasa wanda yaci ze samu matsayi a masarautan koma waye amma dukda haka ba'ah daceba kowa ya gwada amma bai ganin maganin cutan!!! Amma akwai wani malami ɗaya daya taɓa ce masu insha allahu, allah zeturo wani bawan allah kuma sanadin sa zata warke sucigaba da addu'a kawai dakuma haquri shi cuta jarabtace ta ubangiji. Har kullum gimbiya da mahaifinta mai martaba, addu'ar suke allah yakawo wannan bawan allahn lafiya sannan cikin gaggawa!! , Tana zaune tabuga tagumi kawai tana kallon ammaah en nata, tarasa meke mata dadi aduniya ,, ga abunda mai martaba yace mata na zuwan yaran sarakunan se qara matsowa yake!! Kwanaki kawai yarage sannan ga jikin ammaaahn ta Ita batajin zata iya aure tabar mahaifiyarta a wannan ciwon, dukda muradin mahaifiyar tatace tayi auren!! Sosai take tunani ,fuska cikide damuwa dakuma rauni!!! Ganin lokacin sallah yayi, adduah ta tofawa mahaifiyar tata Allah baki lfyh ammaah nah tafaɗa idonta da hawayen da har ya gangaro!!! Tashuwa tayi dan ta ɗauro alwala tayi sallah tunda lokaci yayi....
🄳🄰🄹🄸
*****𝙖𝙢𝙟𝙖𝙙 Sosai yake gudu da dokin nasa ga kuma dare yayi Amma ba alaman ko storo tattare dashi ummansa kawai yake tunawa so yake yaganta yau. Se can dare ya iso garin nasu(𝚖𝚊𝚜𝚊𝚛𝚊𝚞𝚝𝚊𝚗 𝚜𝚞) , yawuce gida !!! Umman sa ce da abbansa suka bude masa qofa yashiga dashi da dokinnasa Ummansa nata masa sannu, Taburma ta shimfiɗa masa, takawo masa ruwa yasha
Ruwan wanka tahadamasa yayi, yaci abinci Bayahn yagama komi suna zaune da iyayennasa, kwantar da kansa yayi a cinyahn ummansa Ummana nayi kewanki, tace nima haka jarumin ummah Abbane yakallesa tom nikumafa? Murmushi yayi idonsa kulle abba nayi kewanka amma kaɗan na ummana yafi yawa Ranqwashi yakai masa umman nasa ta tare masa ah ah zaka qarawa yarona gajiya Ja'irin yaro kawai faɗin abban nasa!!
Hira sukayi kaɗan ba sosaiba sakamakon ganin tilon ɗan nasu yadawo dare dare sannan a gajiye yake kwana 2 baya gida. Suka rakasa ɗakinsa ( as usual) aka masa addu'a yakwanta suka masa seda safe suka ja masa qofa. Sede me!!! bayahn fitan su umman nasa sosai tunanin wannan tsohon ya tsaya masa arai Yajuya haka yajuya haka da qyar de barawon bacci ya sacesa Semuce safiyar khairi 𝙖𝙢𝙟𝙖𝙙 𝙟𝙖𝙧𝙪𝙢𝙞𝙣 𝙪𝙢𝙢𝙖𝙣𝙨𝙖....
NIGERIA
***** Little yatashi bacci har Hajiya ta shirya sa suna zaune falo dashi suna karatu. Sallama sukaji, Da gudu yatashi yaje yai hugging nasu duka Momy da daddy ayoyooo Ɗaukansa daddyn nasa yayi, suka iso palourn suka zauna. Sannu da zuwa hajiya tamasu , momyn little en direct wajan mahaifiyarta taje ta rungumeta tana maqalqale ta kaman yarinya umma Allah nayi kewanki Hajiya cewa tayi nikam tashimun ajiki karki karyani tafaɗa tana qwalawa mai aikin tasu qira tayi, akan sunyi baqi takawo masu ruwa!!! Kallonta yarinyan tayi, yanzu ummata mune baqin? muda gidanmu Daddyn little enma yace, yauwa faɗawa umma de mukam ƴan gida ne ba baqi ba Cewa tayi tashimun ajiki, nide ku baqine atoh kugama kubarman gida Zumɓuro baki tayi umma daga xuwa se korinmu!!! Stugunnawa yayi harqasa daddyn little en yagaida umman tasu murmushi tayi ɗan albarka muna lafiya ya hanya? Yace alhmdlh umma Tace tom masha allah sannunku yaran kirki Allah maku albarka da Ameen suka amsa duka!! Yace umma ya fitinannen mijinki? Murmushi tayi ah ah kunga bamuso ni mijina ba fitinanne ba daga zuwanku ko Ƴar tata ma gaidata tayi ta amsa tana samusu albarka, dakuma tambayahn ya jikin nata tace dasauqi umma,Masha allah haka akeso Allah qara sauqi Daddyn little enne yace umma bara muyi tsokana Kallon yaronsa dake hanun nasa tun zuwansa yayi Little zamu koma gida koh? Aikuwa saurin dira yayi daga jikin daddyn nasa, zaka ɗauka wani abune ya cijesa Jikin hajiya yakoma yana turo baki Gilani kinji daddy ko, ni anjeba da gilani da apoki anjauna!! Dariya dukansu ukun sukayi dan daman sunsan kwanan xancen in de little ne, a duniya shida grannyn sa ko ita ta haifesa albarka. Tashuwa daddyn little yayi yanawa umma se anjuma xedawo sutafi
Raka mijinta tayi hanunta riqeda na litte Kallonsa tayi tace haba heartcode na kwana mana Kallonta yayi yana kashe mata ido 1 Inkin kwana kibarni dawa Zumɓuro bk tayi, shikkenan adawo lafiya Tafiya suke da ɗanta yana mata gwalanti( hira) Bayahn sun koma ciki hajiya ce azaune tana kallo Zama 𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖𝙝 tayi da ɗan nata Hira suke da ummanta inda take faɗa mata Qanin nasu yakusa dawowa insha allah Adduah tayi tana allah dawo dashi lafiya!!! Amma cikin zuciyahnta , babban yayanta da dama bata sansaba ya faɗo mata rai shi takeson gani🥹sosai takejin soyayyan yayannata.. Hira suke da umman nata na tsakanin ɗah da uwa
## 𝙢𝙖𝙨𝙖𝙧𝙖𝙪𝙩𝙖
Hidima ake babu wasa yau saura kwana 5 ayi taron Yayinda angama shirya komi zuwansu kawai ake jira
****bayahn sunkarya da iyayen nasa Maganin yakawo yace abba ga maganin yarinyan da kamun maganan tan Murmushi yayi yana shafa kansa allah maka albarka dan abbah Yace ameen abba na
Sallama abba yamusu akan ze miqawa abokin nasa baban yarinyan maganin zewuce kasuwa, amma ya akayi kasamu maganin nan cikin sauqi? yaron Abba
murmushi yayi abbana karka damu kaide akai masu maganin insha allahu za'ah dace, to Allah yasa amjad. yace masa insha allahu ze biyosa kasuwan inya gama taya ummansa aiki, dan baze je daji ba Yace shikkenan azo lafiya yaron ummah dama bekamata ka koma ba kahuta tukun!! Daga ciki ɗaki umma tayi magana ah ah ni ɗ𝚊𝚗𝚊𝚑 ba yaro bane jarumine Abbane yayi murmishi da yajiyota yace tom umman jarumi. Adawo lfyh suka masa...
*** Koda fitan Abba gidan abokin nasa yafara bi yabasu maganin yakuma masu bayani Sannan yakama hanyahn kasuwa...
Muje zuwa..... ƳAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl Justice Hareeyh🕊️
💋💋 امى بتولة💋
𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:- 08146292652 𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮. 09161720046 𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi😁!!!
# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩 # 𝙇𝙞𝙠𝙚 & # 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
💦💦💦💦💦💦💦 𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣
𝘽𝙮
𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖
(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl✍🔥)
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍
_______________________________________________________________
🅿️ 17&18
💋💋 امى بتولة💋
Bayan tafiyan Abban nasa kasuwa taya Umman tasa ayyukan gidan yayi duka suka yi tare suka gama tare komi da komi. Bayan sun kammala lokaci ya ja banɗaki yayi dan ya watsa ruwa yashirya ya bi Abban nasa kasuwa. wanka yayo yaje yashirya yafito a ɗakin nasa yana '' Ummana Sena dawo fitowa tayi a bayi tana tom jarumin Umma!! Addu'ar a dawo lafiya, kariya dakuma starewan ubangiji ta masa Sannan tace yakula. (nace sekace mace kodayake wai maza ma ana masu fyaɗe) Sallama yayi wa Umman tasa yafice a gidan yawuce kasuwa, cikin shigarsa ta burgewa dakuma salon tafiyarsa me sanya mutum kasa ɗauke ido a kansa, don shiɗin namijine jarumine amma in yana tafiya zaka ranste ba tafiya yake ba Kasancewar a nuste yake komi nasa dukda kasancewan sa jarumin.
A hanya kuwa duk wanda ya ɗaga masa gaisuwa sede ya ɗaga hannu ko ya girgiza kai alamun amsawa (ashe wannan da iyayensa kadai yake zuba) Miskili ne na bugawa a jarida ( miskili kafi mahaukaci ban haushi) Ahaka harya isa kasuwan wajen sana'ar tasu Abban nasa maganin gargajiya yake saidawa ( inda yagado shiga jeji kenan).
🄽🄸🄶🄴🅁🄸🄰
Sosai sukasha hira da Umma har yamma yayi, Daddyn Little ne yazo dan ya ɗauketa su koma, bankwana suke da Ummansu. Umman tasu tace'" wai nikam kuna zuwa gaida Amarya kuwa? ( kakarsu take nufi haka suke qiran ta Amarya) Daddyn Little yace " Umma ba sosaiba" Tom nide ba ruwana kunsan surutun stohuwar nan, inkunje kwafama dama kunfi kusa. ""Amma de kudinga zuwa gaida ta yafi!! Sukace Insha Allahu Umma a gaida Abba in yadawo!! in Sojanmu yadawo zamu zo kunce jaka faɗin Daddyn Little" Umma tace ah ah kuyi zamanku karkuzo kudamar mun yaro, kunga ɗan auta kubarsa yahuta. Dariyah dukan su sukayi, Umma kece fa kika sakalta shi, Amma babba dashi ace masa Auta!!! "Tace nasakalta en ina ruwanku yarona jinjiri dashi, kutashi ma kubarman gida, Da raha da dariya haka sukayi sallama Little se ɗaga masu hannu yake ko a jikinsa kaman ba iyayensa ke tafiyaba!!!( ɗan daɗi kaka bah, kunfasan kaka akwai dadii wanda suke raye allah qara masu lafiya yabamu daman kyautata masu 𝚠𝚊𝚍𝚊𝚗𝚍𝚊 suka rigamu gidan gaskiya allah masu rahama ameen) Suka kama hanyan birnin tarayyah ( 🅐🅑🅤🅙🅐 🅖🅐🅡🅘🅝🅢🅤 🅑🅐🅛🅐🅔🅔 ). wajan ciranin su yar lukuta ta ɗan daura Manoma iyayen sarholiya. Flight sukabi, suka kama hanyan komawa gidansu.
🄰🄱🅄🄹🄰 Bayahn komawan su gida, watsa ruwa sukayi sannan suka ci abinci Zaune Daddyn Little en yake kanta a jikinsa suna fira, cewa yayi " 𝙢𝙚𝙚𝙧𝙖𝙝 𝙩𝙚𝙧𝙝 yaushe zamu je gaida amarya ta? Turo baki tayi ni nagaji heartcode a bari sena haihu tukunna!!! Zaro ido yayi yana dariya, wato kina so kakus taban saki 1500 shine zakice har se kin haihu!!! don abar maki miji ke kaɗai tom anqi wayon zanje wajan amaryata atoh inyaso ke kizauna har se kin haihu kije nan da...... Hararansa tayi a wasa tana turo baki tom waya gaya maka ina kishi da stohuwan nan? Inna huta de se muje tare heartcode yace tom a huta lafiya, kishiyar kakus. (Haka suke zaman auran su lafiya lafiya!! cikin yarda dakuma soyayyahn junansu, wasa da dariya bawa kowa girmansa, dakuma zamowa abu ɗaya, ɗan uwan wannan na wannan ne!!! "Masha allahu nice couples"" ( Dama haka akeson ma'aurata sukasance cikin girma juna da fara'a wa juna!! ba irin matan mu ayau ba, am so sorryh to said koda da laifin maxan na matahn yafi taka muhimmiyar rawa inde a wannan zamani ne! Imagine wata tana zagin mijinta!! Tsakani da allah ko qaninki kika zaga ai yafara jin haushinki kuma zedena ganin girmanki bare kuma uwa uba mijinki uban ƴaƴan ki, kinaso ace iyayenki basumaki tarbiya bane? Ko menene?? Alhalin alhaqinsu zaki ɗauka laifinkine,su iyaye sun horar damu dede gwargwado: Gaskiya mugyara, hadisi ne guda na Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam Allah ya la'anci me xagin iyayensa Kuma inka zagi nawani naka kazaga! Ashe don girman miji ance da akwai wanda za'awa sujjada bayan Allahu Subhanahu Wataalah mijine. Bafa annabiba! Ba iyayena! Ba yayuba! Akace miji Dan Allah mugyara dan Allah dakuma tarbiyahn yaranmu Allah datar damu duniya da lahira Ameen)
💋💋 امى بتولة💋
🅀🅄🄱🄰🄸🅂🄷
* sosai yammata duk wacce tazo wucewa take samasa ido Wanda shikuma wannan sa idon ba abunda yatsana kaman shi. Staki yakera jerawa ahaka harsuka kammala haɗa kayahnsu ganin lokacin tashi yayi suka kamo hanyahn gida shida Abbansa. Suna tafiya suna hira, Abban sane ya kallesa yace jarumin ummansa kyakkyawa!! kaga ƴammata se kallonka suke, kasan me? Kayi haquri kawai ka zabi ɗaya inda dama ma kawai ka zaɓi hudu 4 kamana surkunaye alokaci ɗaya ummanka ma zata so hakan Abban yafaɗa yana murmushi!!! Haɗe rai yayi dan yasan sarai stokanan sa Abban nasa yakeyi, nifa kaga Abba banso kozanyi ma ba yanzu ba kuma bada waɗan nan mayun ba suna ganin mutum ido kaman zasu cinyesa yafaɗa yana qara haɗe fuska kaman matan suna gabansa (yana kallonsu)... A haka suna tafiyansu suna hiransu cikeda raha har suka isa gida.