Yarima suhail complete novel - Chapter 4
Yarima suhail complete novel Chapter 4: Yarima suhail complete novel Chapter 4. gimbiya sumayya sai yatsina take tana ji suna k'ara mata girman kai,…
3,355 words
gimbiya sumayya sai yatsina take tana ji suna k'ara mata girman kai, baiwarta haule kawai tace tazo tarakata nan haule cikin sauri tataso tatake mata baya har sukaje 6angaren yarima nan ma dogarawa suka shiga gaisheta sannan suka bud'e mata k'ofa, kallon haule tayi fuskarta ba yabo tace zaki iya tafiya.
haule durk'usawa tayi k'asa tace toh ranki yadad'e atashi lafiya,
sumayya tana shiga ganin yarima baya parlour yasa dan haka tashiga bedroom tana bud'ewa yarima da yake tsaye yana sanya kaya da alama daga wanka yafito yakallota, kallo d'aya yayi mata yad'auke kai gimbiya sumayya cire alkyabtarta tayi ta aje gefe tare da takawa inda yarima yake tsaye tace my sweetheart ko intaimaka maka?
yarima bud'ar bakinsa sai cewa yayi a yau kuma? kedai kawai kifad'amin me kikeso?
gimbiya tace haba yarima daga nace zan taimaka maka shine harda tambayar me nakeso? kenan banda ikon yi maka komai sai idan ina buk'atar wani abu.
yarima a wulak'ance yace ai hakan halinki yake, kema kuma kinsan hakan kike, yana gama fad'in haka yazagayeta yawuce yaje yahaye gadonsa yakwanta.
gimbiya sumayya tsaye tayi tana mamakin halin yarima cikin ranta tace nasan ta yadda zan 6ullo maka, itama takawa tayi tanufi gadon tahau takwanta tare da rungume yarima tace sweetheart ni bana buk'atar komai sai kai mijina.
yarima murmushi yayi yace ashe anyi miki karatun ta nutsu gaskiya natayaki murna idan har dagaske kin gyaru.
cike da k'ulewa gimbiya tace haba yarima wai meyasa kakeson kaga ka cimun fuska wani fa lokacin har a gaban bayina da kuyangina kake yada min magana.
yarima shuru yayi baice mata komai ba, ganin haka yasa tad'ago kanta takallesa sai ganin idanuwansa a lumshe, shafa sajen fuskarsa tayi tare da yin murmushi tace my dear ba dai bacci zakayi ba,
yarima batare da ya bud'e idonsaba yace ya dai? gimbiya sumayya bakinta takai cikin nasa nan da nan yarima yacafke suka shiga faranta ma junansu.
saida yarima yadirjeta son ransa sannan yabarka atare sukayi wanka sannan suka kwanta tana rungume a jikinsa, yarima yana mamakin sauyawar da sumayya tayi ahaka bacci yayi awon gaba da su.
da asuba ko da sukayi sallah komawa sukayi bacci sai wajen k'arfe tara sannan suka farka a tare sukayi wanka sukayi breakfast bayan sun gama gimbiya jerawa sukayi da yarima suna tafiya inda dogarawa da kuyangi suka take musu baya har saida yarima yazo wajen motar da zai je wajen aiki da ita sannan sukayi sallama dasauri wani bawa yabud'e masa motar yashiga, saida sukaga tafiyarsa sannan gimbiya tajuya suka koma gida, cikin ranta tana ayyana yadda zata biyo ma yarima ya amince batare da tashin hankali ba.
ko da yarima yadawo wajen k'arfe biyu ita taje tataresa cikin shigarta ta alfarma tafito a sarauniyarta ta asali sannan tarakasa har d'akinsa shidai yarima kansa yad'aure sosai ganin wata irin kulawa da yake samu a wajen gimbiya wadda tun satin aurensu rabon da yasameta, ita tataimaka masa yayi wanka yashirya duk k'uiyarta ajeta tayi gefe tatattali mijinta
bayan kwana biyu yarima ne kwance da gimbiya manne da juna suna ta wasanninsu, gimbiya ganin yarima yana shirin nemanta yasa tadakatar dashi, yarima kallonta yake da mamaki idanuwansa duk sun canza kala, yarima dakyar yabud'e baki yace ya dai?
Gimbiya turo baki tayi cikin shagwa6a tace sweetheart Please wani taimako nakeso kayi min, yarima zuba mata ido yayi baice komai.
ganin haka yasa gimbiya sumayya yin murmushi tana wasa da gashin da yake kwance a k'irjinsa tace dan Allah so nake kabarni inje Abuja.
yarima da mamaki yake kallonta yace me zakiyi kuma a abuja? Sumayya d'ago kai tayi tana kallonsa tace so nake inje inga boutique d'in da muka bud'e kaga tunda aka bud'e banjeba kuma badad'i ace har tsawon wannan lokacin ban lek'aba,
yarima d'auke kai yayi tare da cewa ba zakije ba, gimbiya a firgice takallesa tace yarima meyasa? dan Allah kar kahana ni.
yarima suhail wani mugun kallo yawurga mata tare da cewa idan ke bakida hankali to ni ba mahaukaci bane, babu yadda za'ayi insaki matata tayi irin wannan tafiyar mai nisa kuma ya kike tunani mutane zasu d'aukeni? kawai akan kasuwanci?
gimbiya sumayya tashi tayi daga jikinsa cikin fushi tace wlh ban ta6a sanin kai butulu bane sai yau duk hallacin da nayi maka kwana biyu ammah baka ganiba? toh bari kaji akan *KUSUWANCI NA* zan iya yin komai dan haka muzuba mugani kuma tafiya tana nan daram ko da baka. ....
wani gigitaccen mari da yarima yad'auketa dashine yasa takasa k'arasa maganar, kallonsa take da mamaki saida 'yan cikinta sukaso sukad'a ganin yadda yake huci,
yarima dakyar ya iya bud'e baki yace ke har kin isa kidinga min shouting haka? ko dan kinga ina lalka6aki? toh bari kiji albarkacin iyayena kawai kikeci kuma babu inda zakije sannan daga yanzu kidinga ladafta maganarki idan kina a gaban *yarima suhail*, yana gama fad'in haka yad'auko rigarsa yasaka yaficce daga d'akin fuskarsa babu alamun annuri a tattare da shi ahaka yawuce yatafi part d'insa.
gimbiya tana ganin ya fita tafad'a saman gadon tacigaba da rizgar kuka takaicinta marin da yarima yayi mata tun da take iyayenta basu ta6a sa hannu suka daketaba sai yau wani yadaketa kuma wai miji.
tashi tayi tajanyo alkyabtarta tasaka tafito fuuuu dasauri kuyanginta suka mik'e zasu take mata baya cikin fushi gimbiya tadaka musu tsawa tace duk wacce takuskura tabiyoni abakin aikinta.
dasauri duk suka koma suka zauna domin sunsan abinda gimbiya tafad'a zata iya zartar da shi.
cikin sauri take tafiya kamar ta6a66a har ta isa 6angaren ummanta duk mutanen da suke gaisheta bata luraba saboda hankalinta baya a tare da ita tana cikin matsanancin bak'in ciki,
ummah da take zaune bayinta suna ta mata hidima saidai ganin gimbiya tayi kamar an jefota, a firgice ummah tatashi daga kishingid'en da take tace sumayya lafiya?
sumayya dasauri tazo tafad'a jikin ummah tare da fashewa da wani sabon kukan nan hankalin ummah ya ida tashi, cewa take sumayya kifad'a min abinda yake damunki mana,
ummah cikin 6acin rai takori ma'aitanta duk suka fita suka bar d'akin, sannan tad'ago kan sumayya cike da damuwa tace shalele wa yata6a min ke?
gimbiya share hawayen fuskarta tayi nan takwashe dukkan abinda yafaru tsakaninta da yarima tafad'a ma sultana sadiya
sultana sadiya ranta ya 6aci sosai musamman ma da taji wai ya mari sumayya, cikin 6acin rai taharzuk'a tamik'e dasauri sumayya tarik"ota tace ummah ina zakije? ummah tace sakarni inje inci mutuncinsa sai yafad'amin dalilin da yasa yamareki ko mu da muka haifeki hannunmu bai ta6a kaiwa ga fuskarkiba da sunan mari sai wani banza zai mareki.
sumayya tace ummana kibarsa kawai ai sai na rama marin da yayi min dan ba zai ta6a ta6aniba azauna lfy, nidai yanzu kisamo min mafita saboda ina da burin tafiyar nan cikin satin nan.
ummah komawa tayi tazauna tare da cewa ai dole ma ne kitafi dan haka taso muje wajen dada nasan yadda zan 6ullo ma lamarin
cike da jin dad'i sumayya tace nagode ummana wlh saisa nake k'ara sonki, murmushi sultana sadiya tayi tace ai dole inso duk abinda kikeso shalelena. nan suka tashi suka d'unguma turakar su dada. .........
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
page 6⃣
suna shiga a parlourn dada batanan saidai ma'aikatanta nan suka zube suka kwashi gaisuwa wajen gimbiya sumayya da sultana sadiya ammah ko kallon arzik'i basu samuba, gimbiya ce a wulak'ance tace dada bata nan ne?
jakadiya tace ranki yadad'e ta d'an shiga ciki ammah yanzu zata fito,
gimbiya kallon sultana sadiya tayi tace ummah muzauna kafin tafito. sultana sadiya bata musaba nan suka zauna suna jiranta.
bayan kamar minti biyar sai ga dada tafito dasauri duk suka mik'e tsaye hatta ummah da gimbiya saida suka mik'e nan kuyangi suka d'auka angaisheki sultana takawarki lafiya, daganan sukayi shuru domin sun san dada batason ana mata kirari.
nan tazo tazauna saman kujera, sultana sadiya da gimbiya nan suka duk'a suka gaisheta, fuskar dada d'auke da fara'a ta amsa sannan suka zauna saman kujera, dada ganinsu da tayi haka yasa tasan muhimmin abune yake tafe da su dan haka tasallami kuyanginta gaba d'ayansu.
maida kallonta tayi ga sultana sadiya tace daga ganinku akwai abinda yake tafe daku ina saurarenku,
sultana sadiya murmushi tayi takalli gimbiya da tazuba mata ido tana jiran taji abinda zatace, d'auke idonta tayi daga kallonta tamaida kan dada tace ranki yadad'e daman sumayya ce tazo tasameni da maganar da ban ji dad'intaba shine nace ai ke yafi dacewa muzo mufad'a mawa saboda daga sarki sai ke ne shuwagabanninmu.
dada dai zuba ido tayi tana kallonta chan sai tagyad'a kai tace ina saurarenku.
sultana sadiya tace daman sumayya ce tasamen akan ta yi ma yarima magana domin yataimaka yabarta taje tagano yanayin yadda business d'insu yake tafiya saboda tunda suka fara wata biyar kenan ammah bata samu talek'a ba abokiyar kasuwancintata ta matsa akan ko da sau d'ayane taje taga yanayin wajen kuma akwai wani signing da akeso tayi shine takeso ko kwana biyune tayi toh tunda tafad'a ma yarima haka nan yahauta da fad'a da cin mutunci a k'arshe ma har da marinta yayi, haka tazomin a firgice shine nace muzo wajenki saboda ke yafi cancanta kishiga lamarin nan.
dada kallon sumayya tayi da idanuwanta suka kumbura saboda kuka, haushine yakamata ganin irin cin mutuncin da yarima yayi ma jikarta, cikin fushi tace wannan bazai ta6a yuwuwaba domin bana son azalunci wani bare ma ace nawane yazalunci d'an uwansa tafiyace kuma da bazan aminceba saboda baidaceba amatsayinta namatar yarima guda ace tana yawo kuma tunda kika taso a nan gidan sarauta bakiga iyayenki suna haka ba kuma kinsan memartaba bazai ta6a amincewa da hakanba,
gambiya sumayya marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace dada dan Allah kitaimaka min,
dada tace toh shikenan ai tunda har yaci mutuncinki toh sai kintafi dan haka kiramin shi a waya.
gimbiya sumayya da ummanta sunji dad'i sosai da jin zancen dada, dan haka sumayya takar6i wayar dada domin takira yarima.
yarima tunda yaje d'akinsa saman gadonsa yafad'a cike da jin haushin sumayya ammah baiyi mamakin hakanba domin daman chan yaba ma ransa da biyu take nuna masa kulawa sai idan tana neman wani abu daga garesa, a gefe guda kuma na zuciyarsa ya ji haushin marin da yayi mata domin shi a rayuwarsa ya tsani hakan.
wayarsace da tafara ringing kamar ba zai d'aukaba saida takusan tsinkewa sannan yad'auko ganin sunan dadane yasa yatashi zaune tare da yin picking d'in wayar yasa a kunnensa yayi sallama,
dada ko amsa masa sallamar batayiba cikin fad'a tace toh marar mutunci kazo kasameni ina jiranka yanzun nan kar kuma kakuskura ka6ata min lokaci domin idan bakazo cikin lokaciba ba kaiba hatta mahaifinka sai ransa ya 6aci, tana gama fad'in haka takashe wayar.
yarima haushine yakamasa jin rashin mutuncin da dada tayi masa kuma wai harda mahaifinsa tsaki yaja yace tabbas wannan nasan had'in sumayya ne lallai yarinyar nan batada mutunci, tashi yayi yashiga toilet yayi wanka cikin sauri yafito yashirya sannan yakama hanyar 6angarensu dada, hana dogarawa yayi surakasa shi kad'ai yatafi yana tafiyarsa ta k'asaita babu alamun fara'a tare da shi tsakaninsa da mutane saidai yad'aga musu hannu ko da daman halinsane hakan.
baidamu da gaisuwar da kuyangi sukeyi masaba yashiga d'akin da sallamarsa ko kallon inda su gimbiya suke baiyi ba yazauna cike da izza.
dada sakin baki tayi tana kallonsa, gaisheta yayi, bata amsa masaba tace me yahad'aka da matarka?
murmushi mai aji yarima yayi yace dada ko gaisuwar ma baza'a amsa min ba? dada tace bana buk'atarta karik'e abunka, nace me yahad'aka da sumayya,
yarima sai a lokaci yakalli sumayya da sultana Sadiya yayi murmushi yace ashe ummah ce barka da rana.
sultana sadiya kamar tad'aura hannu saman kai tafasa ihu saboda takaicin yadda yarima yayi mata, ganinta a matsayinta na uwar matarsa ammah baya ji zai iya gaisheta cikin girmamawa.
ganin yadda dada tatsaresa da ido yasa yace dada wani abu tace miki ya faru a tsakaninmu?
dada tace kai banason shashanci ashe bakada mutunci, dan rashin imani har ka iya d'aga hannu kamari matarka, toh bari kaji wannan yazama nafarko kuma na k'arshe sannan maganar tafiyar da tace zatayi inaso kasani dole kabarta tatafi dan bak'in ciki d'an abinda take samune yake tsone maka ido.
murmushi yarima yayi yana kallon kaka sannan daga baya yamaida kallonsa ga gimbiya da tatsaresa da ido yace toh kinji dai abinda dada tace sannan yamik'e tare da kallon dada yace toh dada nabarku lafiya.
dada nace nashiga ukku ni Asma'u yanzun suhail saboda Allah baka d'aukeni da daraja ba? ina maka magana zaka tashi?
yarima komawa yayi yazauna tare da cewa sorry dada ba haka bane kawai naga kin yanke hukunci saisa.
da mamaki dada take kallonsa tace kana nufin kai baka aminceba?
yarima suhail shuru yayi kamar ba zaiyi maganaba saboda maganar da yakeyi ta gunduresa ga wani irin haushin sumayya da yakeji da kullum batada buri sai na had'asa da su dada, sai chan yace ammah dada kin yanke hukunci batare da kinji nawa uzurinba.
dada tace karik'e abunka domin babu abinda zaka fad'amin tunda ka gama zaluntar 'yar uwarka ni yanzu amincewarka nakeso
yarima cike da jin haushi yace na amince saboda ke dada, wani murmushin mugunta yayi yace ammah dai duk abinda yafaru ina gargad'inki da kiyi kuka da kanki sumayya.
sultana sadiya a fusace tace insha Allah ba abinda zai faru sai alkhairi bakinka da bak'in nufinka sukoma maka, sumayya tace wlh kau ummah .
yarima murmushi kawai yayi baice komaiba dada tace toh ka kyauta ammah yanzu sai kabata hak'urin marin da kayi mata kuyafe ma juna domin farin cikinku da zaman lafiya mukeso,
yarima wani irin kallo yayi ma dada domin yasan bayan mahaifiyarsa sai dada kawai yasan matan da zai iya ba hak'uri, duba time yayi sannan yace yanzu dai bari intafi saboda kaina ya fara ciwo.
ganin dada batace komaiba yasa yarima yamik'e tare da cewa na barki lafiya ranki yadad'e sannan yawuce cikin takunsa yabar d'akin.
gaba d'aya binsa sukayi da kallo cike da mamakin halin yarima, sultana sadiya ko k'arshen k'ulewa ta k'ule ta cika fam.
dada kallonta tamaido agaresu tace saidai hak'uri kunsan halin yarima suhail wani lokacin hatta ni kaina nuna min yake kamar ban isa da shi ba ammah dai Alhmdllh tunda ya amince kitafi ni nasan yadda zanyi da maimartaba sai kije kifara shiri kifitar da rana koma dai mi kenan zan fad'a miki ammah dan girman Allah kar kidad'e domin kinsan halin mijin nan naki.
Gimbiya sumayya cike da jin dad'i tace insha Allahu dada ba zan dad'eba baifi inyi 1wk ba, dada tace toh shikenan Allah yataimaka sukace Ameen, sannan sultana sadiya da Gimbiya suka k'ara duk'awa suka kwashi gaisuwa sannan sukayi mata sallama suka bar d'akin cike da jin dad'in nasarar da suka samu.
Yarima suhail ransa ya 6aci sosai kawai daman yana 6oyewane dan kar sugane halin da yake ciki yana fitowa direct 6angaren iyayensa yanufa a parlour yatarar da ummi kishingid'e ana mata tausa,
bayi da kuyangi suna ta yi mata hidima, suna ganinsa ko yazube yakwashi gaisuwa, yarima batare da ya tankaba yad'aga musu hannu cikin sauri kowa yatashi suka fita daga d'akin takawa yayi ya isa Saman kujerar da ummi take zaune zuba masa ido ummi tayi tana kallonsa, yarima zama yayi shima yana kallonta da idanuwansa da suka kad'a daga launin fari zuwa na ja saboda 6acin rai sannan yajanye fuskarsa daga kallonta, ummi tace suhail miyake faruwa ne? kafad'a min damuwarka.
yarima suhail saida yad'auki kusan minti biyu kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace ummi yanzu saboda Allah ina auren sumayya ammah ta d'aukeni kamar ba mijintaba ban isa in hanata abu ba sai ta had'ani da dada, kullum cikin kai k'arata take.
shuru yad'anyi nalokaci sannan yakalli mahaifiyar tasa da tazuba masa ido yace wai abun haushin har da mahaifiyarta take goyan mata baya toh ni cewa nayi bata min laifi? duk hak'urin da nake da ita bata gani duk abinda takemin wa nata6a samu nafad'a ma wa? kawai ina kyaletane albarkacin iyayenmu da zumuncin mu.
girgiza kai yayi cike da takaici yace ummi hak'uri ya k'are zan d'au k'wak'waran mataki akai.
Sultana Bilkisu cike da tausayin d'an nata take kallonsa domin tasan halin d'an nata ko da za'a cutar da shi ba ya ta6a damuwa saidai idan an kaisa k'arshe shine zakaga 6acin ransa.
tashi ummi tayi daga kishingid'en da take tarik'o hannun d'an nata tace suhail kacigaba da hak'urin da nasanka da shi insha Allahu komai zai zo k'arshe, wani lokacin dakanta zata daina.
yarima suhail murmushi yayi wanda iyakarsa baki sannan yace ummi har wane lokacin kuma? kiduba kiga tsawon dad'ewarmu ammah kullum halinta k'ara canzasa take ni wlh da ace ina da wadda nakeso da aure zan k'ara domin sumayya da ita da babu, banbancinsu kad'an ne.
ummi zaro ido tayi tace karufa mana asiri yarima wane irin aure? dukafa yanzu aurenku baifi shekara d'aya ba.
murmushin takaici yarima yayi yace ummi ba zaku ta6a fahimtataba.
ummi tace indai baso kake a zargemuba.
yarima suhail jingine kansa yayi a kan kujera tare da lumshe idonsa yana jin wani iri a ransa.
sultana bilkisu kallon d'an nata take cike da tausayi ganin tunda yayi auren nan yabi ya rame tabbas tasan akwai abinda yake damunsa dandai miskilancinsa ya zame masa yana da zurfin ciki sosai. itama jan bakinta tayi tayi shuru domin tasan d'an nata baya da son hayaniya.
A ranar yarima bai fitaba d'akin ummi yawuni ak'arshema bedroom d'in ummi yakoma yasha baccinsa, ummi hana kowa tayi yashiga.
Gimbiya sumayya suna komawa turakar sultana sadiya kallon ummantata tayi cike da farin ciki tace wlh ummi kin gama min komai, tabbas nayi sa'ar uwa mai son farin cikina.
Sultana murmushi tayi tace ai wlh akanki ba na jin zan iya ragama kowa, wannan mijin naki na tsanesa dandai babu yarda zanyi ne, gimbiya zaro ido tayi tace ummah mijin nawa kika tsana?
sultana Sadiya tace eh man saboda ni naci burin in haifi Wanda zai gaji memartaba ammah ban haifaba saisa tunda aka haifesa naji bana sonsa.
dariya gimbiya tayi tace toh ai yanzu sai kikwantar da hankalinki tunda ni yake aure kuma duk wanda zai gaji masarautarnan ni zan haifa masa.
Sultana tace hakane ammah ai har yanzu naga bawani bayani wlh hankalina tashi yake ganin kunyi shekara da'ya har da d'oriya baki haihuba.
gimbiya tace haba ummah wa yake ta haihuwa yanzu sai mun gama cin zamaninmu sannan zan haihu
sultana sadiya sakin baki tayi tana kallonta da mamaki tace sumayya ban ta6a sanin ke sakara bace sai a yanzu keda kike auren yarima ai kyau ace kinyi saurin haihuwa ko da ace biyune kibari kiyi in yaso daga baya sai ki tsayar da haihuwar sai lokacin da kikeso.
Gimbiya sumayya cikin fushi tace gaskiya ummah ni nagama tsara yadda nakeso rayuwata tatafi kuma na tabbata yarima bazai ta6a k'ara aure ba domin su dada ba zasu ta6a amincewa da hakan ba.
sultana sadiya tace kima daina wannan maganar wlh ko ni ba zan ta6a bari yayi miki kishiba, nidai burina kijanye wannan plan d'in naki kihaifar mana baby,
gimbiya mik'ewa tayi tsaye tana gyara alkyabtarta tace ummah bari inje dai infara shirin tafiyarnan da zanyi saboda jibi nakeso inyita nabarki lafiya.
Sultana Sadiya bin d'iyartata tayi da kallo domin tasan dandai ajanye maganar haihuwarne shiyasa tace zata tafi, murmushi tayi tare da girgiza kai tace sumayya kenan Allah yasa kifahimci abinda nake nufi. .....
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ ?👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔