Yarima suhail complete novel - Chapter 5
Yarima suhail complete novel Chapter 5: Yarima suhail complete novel Chapter 5. _sak'on gaisuwata agareku *Zaynav mtz fan's, Yarima suhail fan's 1&2, Ummun…
3,373 words
_sak'on gaisuwata agareku *Zaynav mtz fan's, Yarima suhail fan's 1&2, Ummun meenal fan's, hibbatullah fan's, janaf fan's, zauren sainah fan's, mummyn khalil fan's Aufana true fan's* da sauran groups d'in da ban samu nalissafoba😍👌 ina jin dad'in comments d'inku Allah yabar k'auna_
_*Wannan page d'in nakune my hafnan, Janaf, Aysha nd ummun meenal ina ji daku cikin zuciyana😍😘*_
page 7⃣
yarima sai dare sannan yabaro turakar su ummi yakoma part d'insu, saida yayi wanka yashirya sannan yafito dining yad'anci abinci bayan ya gama kallo yakunna yana yi, bud'e k'ofar akayi aka shigo bai ko d'ago kai ba domin ya san gimbiya ce.
gimbiya sumayya ganin bai kalletaba yasa tatako tazauna gefensa cike da isa tace daman nazo infad'a maka jibine fa zan tafi kuma kasan ba zan iya tafiya mai tsayi a motaba dan haka sai kabada kud'i ayomin Visa,
wani mugun kallo da yarima yawurga mata saida hantar cikinta takad'a, batare da ya janye idonsa a garetaba yace ni na'aikeki?
Gimbiya sumayya itama kallonsa take tace toh naga kai yafi dacewa da kasa ayankar min ticket tunda k'ark'ashinka nake.
yarima shuru yayi kamar ba zaice wani abuba sai chan kuma yace ke ban ta6a sanin bakida hankaliba sai yanzu baizama dole inyi miki hakanba kuma bana tunanin akwai Wanda ya isa yasani dole, dan haka tashi kifitar min daga d'aki tun kan in6ata miki rai.
gimbiya sumayya mik'ewa tayi saida takai bakin k'ofa sannan tajuyo takalli yarima suhail tace koma dai me kenan katabbatar zuwa gobe ka yimin abinda nakeso inkuma bahakaba zan fad'ama dada, tana gama fad'in haka taficce daga d"akin.
yarima suhail takaicine da bak'in ciki suka taru sukayi masa yawa tsaki yaja kawai ak'arshe ma yakashe kallon yatashi yashige bedroom d'insa cike da 6acin rai yakwanta, yanajin wani iri a zuciya ji yake an cucesa da aka za6a masa gimbiya sumayya a matsayin matarsa domin kwatakwata halinta baiyi masaba. ak'arshe wayarsa yajawo yakira d'aya daga cikin yaransa yace zuwa gobe a tabbatar anyi ma sumayya Visa.
Wanshe kare wajen k'arfe sha biyu da yarima yagama shirinsa fitowa yayi yanufi d'akin gimbiya sumayya inda yataddata a lokacin tafito daga wanka, a wulak'ance yakalleta sannan yawurga mata ticket yace ba dan halinki nasa akayi mikiba dan ganin damanane.
harararsa gimbiya tayi tace eh ahaka d'in dai saida nayi magana, yarima suhail murmushin mugunta yayi sannan yataka inda sumayya take, dak'arfi yajawota tafad'o jikinsa har saida tad'anyi 'yar k'ara sannan yace sumayya inaso kisani darajar iyayena kawai kikeci da badan hakaba wlh da sai kin gane kuskurenki.
gimbiya sumayya tace suhail kadad'e baka nuna min kuskurenaba kuma yadda kake tak'ama da sarautarnan nima ai jinintane, bamuda banbanci ni da kai, kuma idan ka cika d'an halak kata6ani kagani, kuma bari kaji jikina kagama samunsa tunda har kata6amin fuskata jiya yanzu daidai nake da kai.
yarima suhail d'auke ta yayi da mari yak'ara mata wani tare da wurgata saman gado yace banyi niyar kwanciya da ke ba ammah yau zan nuna miki na ciki d'an halakne ni, saman gadon yabita tare da fizge towel d'in da yake jikinta nan suka shiga kokawa ak'arshe yarima suhail yasakarmata nauyinsa.
mugunta yasa mata yadirjeta son ransa, gimbiya sumayya kuka kawai take, yarima saida yagaji dan kansa sannan yabarta,
kayansa yad'auka yasanya bai ko k'ara kallon inda sumayya take kwanceba tana ta ja masa Allah ya isa, fita yayi daga d'akin yakoma part d'insa yayi wanka yashirya sannan yaje fada yagaishe da sarki daga nan yafita yabar gidan.
Tun daga lokacin basu k'ara had'a hanya da gimbiya sumayya ba baima san lokacin da tatafiba sai wajen dada yakeji,
hatta umman sumayya yanzu ko ya gaisheta bata amsawa dan haka shima yadaina gaisheta, ko da ace tana tare da abban sumayya toh abbah kawai yake gaishewa tsakaninsa da ita saidai tahararesa shikuma yanuna ko inkula.
__________________
awata anguwa mai suna yamza wata yarinyace take tafita a nutse kanta a k'asa yarinyar ba zata gasa shekara ashirinba wani gidane tashiga gidan da kagansa kasan bamasu hali bane saidai rufin asiri, da sallamarta tashiga, wata matace da nahango zaune tana wanke-wanke ciki-ciki ta amsa mata sallamar
cike da ladabi zarah tak'arasa inda matar take tare da tsugunnawa tace mama sannu da gida.
harara matar tawurgamata tace ke shine bakiyi min wanke-wankeba kika kama hanya kika fita daga gidan ko?
zarah cike da nutsuwa tace mama dan Allah kiyi hak'uri wlh ganinayi na makara islamiyya shiyasa.
rik'e baki mama tayi tace eh islamiyya fad'amin nida banyi islamiyarba, ke ga ustaziya ko? to wlh inbaki canza haliba haka zakizo kik'are cikin gida, kiduba kiga 'yan uwanki kullum sai sun fita sun samo mana 'yan kud'in da zamuyi hidima ammah ke kina nan jibge a cikin gida saidai aciyar dake ashayar da ke iyakarki kashi, toh wlh indai bakiyi dagaskeba sai kin rasa mashinshini domin wannan girman kan naki babu inda zai kaiki.
zarah shuru tayi batace komai ba domin idan da sabo ta saba da halin iyayen nata,
tsawa mama tadakamata tace watau ga mahaukaciya ina magana shine kikayi shuru kika kyaleni watakau ga mahaukaciya tana magana.
zarah cikin nutsuwa tace Allah yabaki hak'uri mama kawo wanke-wanken in k'arasa miki.
ummah d'auraye hannunta tayi tamik'e tace ai ko bakiceba daman ke zaki idashi tunda baki aikin komai sai karatu saikace alhuda-huda.
mama tana tashi zarah tacire hijab d'inta tarataye saman igiya sannan tazauna tacigaba da wanke-wanken.
tana cikin yi saiga yayarta tashigo babu ko sallama kallonta zarah tayi cike da takaicin ganin irin shigar da take jikinta kayan sun matseta gyalen da tayafa ko dashi k'ara babu, d'auke kanta tayi daga kallonta tacigaba da wanke-wanke tana addu'a cikin zuciyarta Allah yashirya su sugane gaskiya.
muryar yaya rauda ce tajiyo tana cewa zarah ina mamanmu take? batare da takalletaba tace tana cikin d'aki.
Rauda kira tashiga kwala ma mama daga inda take tsaye, mama datake d'aka dasauri tafito kallabinta a hannu tana washe baki tace a'ah 'yar albarka har kin dawo?
Rauda yamutsa fuska tayi tace eh ga wannan ledar da take hannunta tamik'a mata, ummah cike da farin ciki ta amsa tana cewa me muka samu yau?
malam yusuf ne yashigo gidan yana cewa a'a 'yar baba ai naga lokacin da aka safkeki kinga har da 'yan canji mutumin yabani gaskiya yana da kirki.
Rauda yamutse fuskarta tayi tace ammah ai abba nace kadaina tambayarsu kud'i inkana tambayarsu ai sai kaja surainani ,
abba yace 'yar baba bafa tambayarsu nakeba sune suke bani kuma kinga babu kyau maida hannun kyauta baya ko ba haka bane Zainabu? mama tace hakane malam, yanzu dai mik'o wani abu nan dan musamu daren nan muci mai d'an dad'i-dad'i.
abba yace toh naji yanzu dai menene cikin ledarnan?
mama duba ledar tayi tare da washe baki tace ashe kazace yau shagali zamuyi kenan.
Abba ma washe baki yayi yace gaskiya naji dad'i daman wannan bakin nawa yakwana biyu bai ci namaba, ammah dai 'yar baba Allah yaimiki albarka,
mama tace toh yanzu dai kakawo asiyo kayan miya muyi d'an pepper chicken, abbah dubu d'aya yamik'a mata yace gashi sai akasiyo har da buredi wanda zamu d'an dangwala romon ai haka zaifi ko?
mama tace eh malam, ai saima autarka tadawo muga ita mi zata kawo mana, ai ni yau naga amfanin haihuwar 'ya'ya mata daman malam ai nafad'a maka 'ya'ya mata dad'i garesu, malam yace hakane sannan yakai dubansa ga zarah da take tsugunne tana ta wanke-wanke, yamutsa fuska yayi yace Asma'u wlh d'iyar chan duk cikin 'ya'yana ita kad'aice batada k'ashin arzik'i wani ma lokacin ji nake anya jininace?
ummah tayi karaf tace a'ah malam wannan cin mutuncin da me yayi kama idan ba d'iyarka bace toh wanene ubanta? ko akwai wani mijin da na aura bayanka? ko kuma kana nufin ina bin mazan banza.
malam yace a"a zainabu nidai ina nufin kwata-kwata bata d'auko halinaba, kiduba kiga ko farin jinin samarin nan ita batadashi,
ummah tace ah toh yanzu naji bayani, ai malam kakalli wannan munafukar kawai bak'in ciki kawai take yi mana dan kar muci moriyarta kasan yanzu sai kahaifi d'a baka haifi halinsaba, wlh akwai samarin wulak'antasu kawai take tana korarsu sai wannan matsiyacin malamin nata da ta lik'e mawa me na k'asa yaci bare yaba nasama.
malam yace oh ni wlh daman nayi zaton haka ni wlh wannan sakaryar d'iyar bansan yaushe zata waye kamar 'yan uwantaba, Allah dai yashiryata.
mama tace Ameen dai
malam yace yanzu dai dafa mana kazar a d'ansa kayan yaji nasan zatafi dad'i haka bari ind'an fita.
ummah tace toh malam adawo lafiya.
zarah dai zaune take tana wanke-wankenta duk firar da iyayenta sukeyi akan kunnenta hawayene yacika mata ido tana jin wani abu ya tokare mata mak'oshi saboda takaicin halin iyayenta, cikin ranta addu'a take Allah yashirya mata iyayenta da 'yan uwanta sugane gaskiya.
bayan ta gama alwallah tad'aura sannan tad'auki hijab d'inta tashige d'akinsu, lokacin yaya rauda tana shafa da alamu daga wanka tafito.
zarah shimfid'a darduma tayi tad'auko alk'ur'aninta tana karantawa har aka tada sallar magrib sannan tatashi tayi sallah
ido tazuba ma rauda tana kallon yadda take sallah cikin sauri babu alamun nutsuwa atare da sallartata
ko da rauda tagama sallar zarah kallonta tayi cike da nutsuwa tace yaya rauda ya kamata idan kina sallah kidinga nutsuwa domin duk abinda zakije nema yana a hannun wanda kike gabansa a yanzu.
harararta Rauda tayi tace toh malama yimin wa'azi tunda kinfini sani, kinsan Allah zarah idan baki fita daga hancinaba sai na 6a66allaki a cikin gidan nan kuma da kike maganar sallah ai Allah da zuciyar mutum yake amfani, kuma idan ke kike raba ladar toh dan girman Allah kihanani 'yar bak'in ciki kawai. tana gama fad'in haka tatashi fuuuu taficce tabar d'akin tana ta mita.......
_Comments_ *nd* _Share_
_Sis Nerja'art✍🏻_ 👑👑👑
_*YARIMA SUHAIL*_
👑👑👑
_*Written By~Sis Nerja'art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®* *[onward together]* *{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }* THE PEN OF LOVE 😘 HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 🙂 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑 *JUST GIVE US FOLLOW....*✔
page 8⃣
tashi tayi fuuu tawuce tabar d'akin tana mita ita dai zarah bin rauda tayi da kallo cike da bak'in cikin halin 'yan gidansu a kullum addu'anta Allah yasa sugane gaskiya.
addu'a tayi sannan tatashi tacire hijab d'inta tafito takar6i kayan miyan da suke hannun mama tajajjaga mata sannan tatambayeta idan akwai abinda za'a, mama tace a'a, sannan tawuce takoma d'aki koda tayi sallar isha'i zama tayi tana ta bitar karatunta sai wajen k'arfe takwas sannan k'anwarta Aysha tadawo gida hannunta d'auke da leda tun daga zaure tafara kwalah ma mama kira
mama da take tsugunne tana hura huta jikinta yana 6ari tamik'e tana washe baki tace a'ah autata har kin dawo.
Aysha tana yatsine fuska tace eh wlh , mama kar6ar ledar hannun Aysha tayi tace me kuma muka samu?
Aysha kar6e ledarta tayi tace kai mamanmu ba fa wani abu bane d'inkinane nabiya na amso,
fara'ar da take d'auke a fuskar mama ce taragu tace kina nufin babu abinda kika kawo mana? kiduba kiga 'yar uwarki kaza takawo mana gata chan saman wuta ina mana ferfesu,
Aysha tace oh mama kedai kullum burinki abaki kud'i, jakkarta tabud'e tad'auko 2k tace gashinan kid'auki d'aya kiba abbah d'aya.
mama kar6a tayi tana washe baki tace kai 'yar albarka gaskiya naji dad'i ammah ba zan ba mahaifinkuba dan shima d'azun ya samu kud'i kar ma kikuskura kifad'a masa kin bamu kud'i, Aysha wucewa tayi tanufi d'akinsu tana cewa nidai mamanmu wannan tsakaninku da abbane,
zarah tana zaune saman darduma tana sauraren dukkan abinda suke tattaunawa,
Aysha ce tashigo d'akin tana cewa wash wlh na gaji, jafe jakkarta tayi bisa katifa takalli zarah tace yaya zarah kina nan kina ta bitar karatun?
zarah batare da takalletaba tace Aysha daga ina kike? meyasa kikeso kiga kinyi dare a waje a matsayinki na mace?
Aysha turo baki tayi tace ammah ai mama tasan da tafiyata, zarah aje littafin da yake hannunta tayi tare da tattara dukkan hankalinta ga k'anwarta tace Aysha wannan rayuwar da kika d'aukar ma kanki ba mai 6ullewa bace k'ara tun wuri kigyara tun kan lokaci yak'uremiki gudun kar kiyi nadamar da batada amfani.
mama ce da tazo wucewa tajiyota tana magana lek'owatayi d'akin takalli zarah taharareta tace toh sarkin 6akin ciki mekike ce mata? badai hure mata kunne kikeyi ba dai ko?
zarah kallon mama tayi tace a'a mama kawai ina bata shawarace d's zata fisheta.
salati mama tahau yi tace nashiga ukku ni Zainabu yau Allah yabani d'iya mai bak'in ciki da ni, yanzu 'yan kud'in da take kawo mana ne kike ma bak'in ciki? toh idan suka zauna gidan ubanwa zai dinga ciyar da mu? kinsan dai mahaifinku bai bada abinda zamu ci muk'oshi .
zarah cikin lallashi tace mama kiyi hak'uri ni ba haka nake nufiba, idan na 6ata miki rai kiyi hak'uri.
mama tace daman ai haka zakice munafuka kawai wlh da ace ba ni nahaifekiba da na ce ke ba jinina bace.
zarah dai shuru tayi tana sauraren maganganun mama har mama tagama fad'anta tafita tabar d'akin.
karatunma zarah kasa cigaba tayi saboda haushi nan ta tattare littafan tamaida su ajakkarta, sannan tahaye saman katifarsu takwanta.
Aysha wanka tayo tashirya akan idon zarah wani yakirata a waya tafita tabar gidan, 'yar nokianta ce da taji tana ruri yasa takai idanunta a wajen ganin wanda yake kiranta saka tayi murmushi har dimples d'inta suka lotsa cike da farin ciki tayi picking domin tasan ko bakomai Malam Bello zai d'ebe mata kewa sallamata tayi masa, shima cike da farin ciki ya amsa mata, bayan sun gaisa malam Bello yace gimbiya zarah ya gida?
murmushi zarah tayi tace wai gimbiya dan Allah kama daina kar kaja akamani
dariya malam Bello yayi yace ai gimbiyarce.
zarah tace hmm dan Allah kadaina.
malam Bello yace toh malama zarah ta gida da mutanen gida?
zarah tace Lafiya lou Alhmdllh. malam musa gyaran murya yayi yace zarah wlh ina sonki so nagaskiya dan Allah kitaimaka kirik'e min amanar kanki domin har ga Allah aurenki nake son yi, dama zaki bani dama da naturo an aje maganata inyaso daga baya idan nak'are karatuna sai muyi aure.
zarah murmushi tayi tace kar kadamu malam ba ma sai ka turoba insha Allahu banda miji sai kai domin ka cancanchi kakasance mijina inko kaga ban aurekaba toh wannan daga Allah ne,
malam Bello dogon numfashi yaja yace Allah yasa haka my zarah, wlh gani nake idan narasaki toh na rasa farin cikina domin kece kawai kika dace da rayuwata.
zarah cike da tausayinsa tace kar kadamu malam insha Allahu ma ba zaka ta6a rasaniba.
Bello cike da jin dad'i yace nagode sosai zarah, yanzu inzo mugaisa ko?
zarah kallon agogo tayi tace a'a malam yanzu dare yayi kadai bari sai gobe.
malam Bello yace toh malama zarah duk yadda kikeso ai haka za'ayi Allah yakaimu, murmushi zarah tayi tace toh malam ahuta lafiya sai Allah yakaimu.
malam bello yace au korata ma akeyi? zarah tace wane ni inkoreka kawai dai zanyi bacci ne, bello yace toh gimbiya atashi lafiya zarah tace Allah yasa, nan sukayi sallama sannan suka kashe wayoyin. zarah bin wayar tayi da kallo tana murmushi domin har cikin ranta tana jin malam bello ko da tasan mayuwacine iyayenta su amince da shi tunda baida kud'i ammah ta ci alwashin shikad'ai ne mutumin da zata iya aure saidai wani hukuncin daga ubangiji.....kiran da mama takeyi matane yakatseta daga tunanin da takeyi, dasauri tatashi tafita a tsakar gida tasamu mama da abba Zaune saman tabarma suna cin nama suna dangwala romon da bread, kusa da mama tatsugunna tace mama gani, mama fuskarta a d'aure tace ga naki nan su kuma tunda su suka kawo saisa nafitar masu da nasu yafi yawa,
kar6a zarah tayi tace nagode sannan tatashi takoma d'akinta ,
abbah binta yayi da kallo cike da takaici yace ni inma rasa abinda yarinyarnan take k'unshewa a d'aki kullum tana d'aki ko fitowa batayi tasha iska. ummah tana yagar nama tace ita dai tasani matsalarta.
zarah tana shiga d'akinsu zama tayi taci naman bayan ta gama tafiddo kwanon sannan tayi ma iyayen sallama takoma d'aki saida tayi wanka sannan takwanta.
duk yadda taso tayi bacci ammah takasa tunanin wulak'ancin da takesha wajen mutanene da halin iyayenta da gwagwarmayar da tasha ne yasa tafara hawaye kullum batada buri da yawuce taga iyayenta da 'yan uwanta sun canza hali musamman ma idan tatuna da lokacin da suna yara haka suka taso a sake iyayensu basa kwa6arsu
Malam musa da Zainab sune iyayensu su ukkune suka haifa, Rauda itace babba sai zarah da take bi mata sai 'yar autarsu Aysha ko da ba wani tserataiya bane irin sosai d'innan a tsakaninsu k'ara ma Rauda itace taba zarah shekara biyar, inda zarah kuma taba Aysha shekara biyu.
Suna da kyau sosai kasancewar iyayensu fulanine na usuli, saidai zarah itace zaka kallah kaga sak mama, inda su Rauda da Aysha suke kama da abbansu saisa zarah tayi musu fintinkau wajen kyau dan ma Suna halin rashi.
sunyi karatu bakin gwalgwado dan dukansu daga secondary school suka tsaya da karatunsu babu wacce tacigaba duk suna gida Zaune, zarah ma ce tashiga makarantar koyan sana'a tayi Catrine (6angaren girki) sannan itace mai zuwa islamiyya ammah su rauda babu wacce take da lokacin zuwa islamiyya sharholiyarsu kawai sukeyi.
abun mamakinma a gaban iyayen nasu ake zuwa ad'aukesu ammah iyayensu ko da sau d'aya basu ta6a nuna 6acin ransuba domin basuda burin da yawuce akawo musu kud'i,
hatta abincin da zasu ci wani lokacin rauda da Aysha ne suke ciyar da su kasancewar Abbah baida tak'amaiman aikinyi daman ginine da kanikanci shima sai idan ya samu yakeyi.
ahakanma iyayensu sun tsani suga talakawa suna ra6ar 'ya'yansu, su ma kansu su rauda basa son talakawa 'yan uwansu saisa duk samarinsu masu kud'ine.
duk wanda zai nuna yana son zarah toh wulak'ancine sai yasha wajenta, mama tun tana fad'a har tagaji takyaleta, hantarace da wulak'anci babu wanda bata sha wajensu, ko kud'in wata na islamiyya sai tayi dagaske take samu wajen iyayenta inma basu bataba toh wajen k'anwarta ko yaya rauda take samu su ma sai tasha wulak'anci da gori suke bata.
kayan shafa ma sai sunga dama idan zasu siyo nasu suke had'awa da ita suna d'an siyo mata mai da powder da turare shima a wulak'ance ake bata.
duk aikin gida ita aka sakarmawa inba ka saniba ba zaka ta6a cewa zarah d'iyar gidan bace sai kad'auka *'YAR RIK'O* ce,
wa'azi nasiha babu wanda batayi ma 'yan gidan nasuba ammah sunbi son zuciyansu da na iyayensu.
zarah tun abin yana damunta ammah yanzu ya rage damunta
Malam bello malamin islamiyyarsu zarah ne yana da kirki sosai jininsu ya had'u da zarah saisa suke mutunci, daga baya yanuna yana sonta dakyar yasamu zarah ta amince masa suna soyayya, duk wasu littafan karatun zarah shi yake siya mata.
zarah tun tana nuna bata so ammah daga baya tahak'ura tana kar6a dan tasan iyayenta ba zasu ta6a siya mataba kuma babu inda zata samu kud'i tasiya, shima dan taga yana da hankali da nutsuwa kuma a yadda yake nunawa shi dan Allah yakeyi mata kuma yana so yasamu lada idan ta karanta.
Malam Bello karatu yake a university sannan yana tsare ma wani mutum shago da kud'in islamiyya da ake biyansa a nan yake samun d'an abinda zai rik'e kasancewar iyayensa suma ba masu hali bane sosai.
mama lokacin da tagano zarah tana soyayya da shi har kusan dukanta tayi tace me zatayi da wannan talakkan me nak'asa yaci bare yaba nasama ita dai zarah shuru tayi domin tasan abinda mama take nufi, ammah a ranta itadai bata da burin auren kowa sai malam bello dan shine kad'ai yake taimakonta.
bud'a k'ofar da akayine yadawo da ita daga kogon tunanin da ta lula, Aysha ce tashigo da leda a hannunta tana waya, zarah duba agogo tayi taga kusan k'arfe goma da rabi dan haka tajuya domin tayi bacci cike da takaicin maganganun da Aysha takeyi a waya batare a taji kunya ko nauyin Zarah ba.
ahaka Aysha tagama wayan itama takwanta har sukayi bacci yaya Rauda bata dawoba.
da asuba zarah har tayi sallah ammah Aysha bata tatashi ko da zarah tak'ara tadata cewa tayi dan Allah kikyaleni idan natashi zanyi nace miki.