Kenza eBookz

Yaro ma namiji ne cmplt 1 - Chapter 2

Yaro ma namiji ne cmplt 1 - Chapter 2

Yaro ma namiji ne cmplt 1 Chapter 2: Yaro ma namiji ne cmplt 1 Chapter 2. kintashi yayi cigaba da zamansa kaman ba dashi take ba abinda ta lura shine kuka…

4,491 words

kintashi yayi cigaba da zamansa kaman ba dashi take ba abinda ta lura shine kuka Abul yake hawaye ne sosai ke zuba daga idanunsa sai jikinta yayi sanyin tausasa murya tayi tace " Yahya bawai ina k'inka da Rukayya bane a'a kawai bana son tashin hankaline nasan halinka nafi kowa sanin nagartattun halayanka amma me zamu cewa mutane ko a cikin gidan nan wallahi sai Rukayya ta fuskanci matsala ballatana a waje wasu hujjoji muke dashi da zamu kare ta dashi ga matsala kaduba dakyau kaje kayi tunani kadawo karka fad'awa kowa fa"

hawaye ya share yace " Inna kafin na fad'a miki wallahi sai da nayi har istahara nayi kuma wallahi har yanzu ina jin son abu sosai don Allah ki taimaka min ki ceto rayuwata Didi ce kome na"

shiru tayi takasa magana tunda taga yana share kwalla tasan ba karamin son Rukayya yake ba toh ya zatayi da mutane .

Ashe duk hirar da suke akan kune Inna Kulu murmushin mugunta tayi tace" Saima(sunan Inna kenan) wallahi idan ina raye ba karan da zaizo wajen Rukayya sai na hanata jin dadin rayuwa kwafa tayi dole gobe naje wajen me buzun kura asake samata mugun bakin jini wanda dole ka gudu da kafarka yanzu gidan zani na zuga Uwarka ta hanaka "

🌹🌹🌹 kewayarsu takoma tafinciko wani kod'ad'in gelaita tafita sai gidansu Abul tashiga tasame Umma da baki donko cikakiyar sallama batayi ba " gaisuwar ma sama sama sukayi sabida gulma ya ciwu ta kaman har tana tauna harshenta sabida gulma sannu sukaita mata tace "hmm Hajiya Abeeda kina nan ga Abul khairi yana can ana tusa masa wanca ragowar maza don haka kiraba su inba haka ba toh za'a kwaso miki damuwa "

Umma da ta fahimci maganar Inna kulu murmushi tayi tace "Kulu kenan wace miki muna hana yaranmu farin cikinsu duk abinda suke so indai ba sa6awa shari'a ba toh muna Son kuma kina magana ne akan Rukayya toh Wallahi in akwai wacce tafi Rukayya shekaru kuma yace ita yake so wallahi zamu nema masa ita balle kuma Rukayya yarinyar da ba ruwanta zaki iya tafiya"

kunyane yakama mata cike da borin kunya tace " ba kome na gode sai anjima ku"

fita tayi ranta a bace tace "wallahi koda zanyi yawo tsirara sai na hana aure "

wata daga cikin bakin Umma tace " da alamun y'ar kishiyatar ce ko takawo gulmarta "

takaice ne ya kama Umma tace " ko d'aya wallahi y'ar wan mijintane fa take kishi da Uwar yarinyar yanzu tanayi da y'ar kuma " tsaki tayi .

D'aya matan tace "Allah yakyauta "

"Amin "suka ce,

🌹🌹🌹

fitar Inna kulu kuwa ranta ba karamin 6ace yayi ba kasa hakuri tayi tace " indai ina raye sai na hana wanna auren zaku gani gobe me buzun kura zamin maganinku "kwafa tayi.

A zauren tsakiya suka had'u da Abul ko kallo bata ishe shi ba wucewa yayi abinsa.

koda ya isa yasamu bakin zasu tafi wajensu yaje ya gaishisu suka ce toh " Abul yaushe zaka kawo mana sirikar mu munganta "

murmushi yayi yana shafa kai yace "very soon "

suka ce " Allah yasanya alkhairi ." "Amin " Umma tace,

bayan tafiyarsu ne Umma ta harare shi kafin tace " yayi kyau kasan al'adan gidan nan bama hana kowa ra'ayinsa shine kake boye min damuwarka har sai wasu sunzo sun fad'a min bazamu hanaka neman Rukayya ba amma ninafi kowa dacewar kafad'a min "

shiru yayi har suka isa falo tana zama yazo ya d'aura kansa a cinyarta yace " kiyi hakuri ina tsoran kobazaku yarda bane amma kuyi hakuri bazan sake ba" nan ya fad'a mata yanda sukayi da Inna murmushu tayi tace ba kome zansame ta.

🌹🌹🌹

Washe gari da sa safe Inna kulu tayi sanmakon tafi wudil wajen me buzun kura ta fad'a masa kome zane a kasa yayi yagoge har sau bakwai kafin yace " tabbas auren zayu kuma duk wanda yayi kokarin dakatarwa mutuwa zai sabida rabon dake tsakaninsu "

tace " nashiga uku yazamuyi bana son tayi aurene a rayuwar duniya"

yace " akwai mafita d'aya shin..........

Maman waleed ce [11:47AM, 12/18/2017] REAL ME DAMBU CE🥗: ☔☔☔☔☔☔ *YARO MA NAMIJI NE* 💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DAMBU CE*🥗

*Ayya wai ina kuka shige ne Auntyqueen mermue da sis Billy ladan sis Meelat ahk ina tanemanku*😔Duk inda kuke Allah yasa daku da alkhairi.

*Wato na lura kufin son Abul fa ita Rukky bata da Team sai shi bari naga Abul da Rukky waye yafi Fans saura ku nuna son kai*🤕 luv oll😍 idan kuka ba abul zuciya nikuma na zugata takawo wani guy....😜

1⃣3⃣🌹1⃣4⃣

" A kwai mafita d'aya shine bari na duba wani abu akansu" nanma zane yayi ya goge yasake ya goge wani irin zufane yake karyo masa kama wanda ake watsa masa ruwa kallonta yayi cike da karya yace " a gaskiya Yaro nan bakaramin son yarinyar yake ba gaahi har Uwarsa ta amince haka kuma suna tsaye akan wanna alamarin abinda ya dace shine akan yarinyar zamuyi aikin duk da itama bata wasa da ibada sai dai a duk lokacin da take cikin matsanancin bacin rai bata saurin ambato Allah da wuri don haka zamu tura mata wanda zaisa mata k'iyayyar yaron sosai a rainta yanda zata tsane shi amma shima ba wani dogun aikin zayi ba sabida duk rananar da ya kusanceta karfina maganir zai ragu don haka dole kikula kisan yanda zaki jata ajikinki har tasake dake sai ki hanata yarda da shi kinuna rashin fahimta yasa baki kula amma yanzu kome ya wuce."

shiru tayi tace " anya me buzun kura nasan halinta tuntana Yarinya nake k'inta zata yarda dani kuwa " tsawa ya buga mata yace " duk abinda kika ga dama kiyi 6ace min da gani kafin nasa a juya miki kanki baya ga wannan hayakine kinayi aljanin k'iyayyar zai baiyana aikin hayakin amma ku lura da lokacin da take cikin da 6acin rai kome kashinsa zaiyi amfani fita min da gani "

jikinta har wani rawa yake sabida tsoran wani banza.

🌹🌹🌹

Bayan ta gama labaran cikin harshin turanci karfin tara na safe d'akin rawotanni ta shiga tasami kawarta Zulfa'u sau d'aya ta kalleta sannan ta kauda kai tayi ta zauna shiru yabiyo baya Zulfa kasa hakuri tayi dole ta katse shiru tace "Rukky magana na gaskiya shine babu yanda za'ayi kisami miji a wata biyu kacal sabida baki san halinsa ba shima baisan naki ba ina ganin kiyi hakuri da Abul mana inda bake koshi wani cikinku yafad'a Abul bai kai talatin ba wallahi bawanda zai sani tunda har yafito ya fad'i miki yana sonki kawai ki amince sabida kinsan halinsa gaba da baya."

cike da masifa ta kalle Zulfa tace " haba dai yaron danayi masa hidima tun yana karamin kice na yarda na amince da shi akan yana sona habawa wallahi da sake duk wani sirrina duk saiya bude har nayi rayuwar aure dashi kai kai mun kwanta gado d'aya sanna nakira shi da Uban Yarana tab badani ba wallahi gwara najira subani kowani irin mutum amma banda sa'ar Yaseer "

dariya Zulfa take kyalkyalewa har tana dukan tebirin tace " wayon cikina Rukky Alhassan zakiyi abin kunya ko na ga haka shiyasa duk lokacin da yazo nan jikinki har wani rawa yake sabida tsoransa amma ba damuwa wata rana kece zakiyi haukansonshi Narantsen da Allah sarki"

bata sake kulata Zulfa ba sabida ta lura zata kara mata wani ciwon kaine.

🌹🌹🌹 Da dare bayan dawowar Alhj Attahir suna hirar yake fad'a mata irin nasaran da suka samu xuwan Abul wajen sayard da motocin ba karamin riba suka samu ba fatan alkhairi Umma ta masa sannan tace " Alhj Abul fa aure yake nema a cikin unguwar nan"

shiru yayi da jin abin dariya can ya sa dariya yace" yaunshe ka haife shi da zayi tunanin aure ? kuma wacce yarinyan ce haka da ta6ata lokacinta akansa ?"

haushin maganar Umma taji tace " ba shikenan ba amma yakamata kasan halin da yake ciki shine gaskiya domin ko azumin da yake ai da yakare kanshi yake amma ba damuwa."

Murmushi yayi kafin yace " wallahi Abeeda ina son yayi nima nasan me yasa yake azumin amma wacece Yarinyar "

"Rukayya ce yar gidan Alhj Hassan ce daga ita yarinyar har mahaifiyar ta sunki yarda sabida suna gudun abindan mutane zasu ce " abinda umma tace kenan,

farin cikine ya kama shi yace" wa Adamu naso haka ashe Abul shine mijin toh gobe da asubahi zama Alhj Alhasan magana shikenan inyaso ita yarinyar kwaji da ita

🌹🌹🌹

Inna kiranan Sa'idu yayansu Rukaiyya tayi ta fad'a masa yanda sukayi da Abul yace zaizo su maganar bata waya bace.

gashi sauran kwana hud'u wahadin yacika duk ta d'imance kaman wacce akace wahadin mutuwar tace.

🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀

Mmn Waleed ce [8:22PM, 12/18/2017] REAL ME DAMBU CE🥗: ☔☔☔☔☔☔ *YARO MA NAMIJI NE 💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY_

*REAL ME DAMBU CE🥗*

_Y'AN UWANA MARUBUTA NAGODE ABISA ADDU'OIN DA FATAN ALKHAIRIN DA KUKE MIN INA ALFAHARI DAKU_

*Wanna shafin bana kowa bane nakune sadaukawar*

*_DAMA TA FANS_*

*_MISS _ MARRIAM NOVEL GROUP_*

*_NASIBI WRITER'S ROOM_*

*_MUMMY RABI_*

*_AUNTY BINTA BABANGIDA_*

*_MY RIGIMATION_*😜

*_MAMAN SADEEQ_* KALPANA💅

*_MOMIN NASRIN_*😍

*_MMN AMAL,MY SHEMA,ADDAN JELATA,MMN NOOR,MMN'AL'AMIN,NEENA,_* Da wanda basu ji sunan ba inayinsun sosai😍

Mmn meenat Allah yaba yarona lafiya🤧

*Deeja Waziri tare da Bie bie dee ina tayaku murna k'anmala buks dinku lafiya Allah yabaku ikon fara sabi lafiya*🤝🏼

*Naki daban ne Aunty maijidda musa* Ana tare🤝🏼

🎁H.A.W.🎁

1⃣5⃣ 🌹1⃣6⃣

Bayan Inna ta gama waya da Sa'idu sai takira Yaseer wanda yake service a ondo ta fad'a masa ay shikan kai tsaye ya amince dariya yayi kafin yace " Inna wallahi billahi azim Abul khairi shi yafi dacewa da Didi sabida nasan halinsa ciki da waje banda Didi banta6a jin ya kira wata mace a gabana ba yankance shi in Allah zai bashi mace ya bashi mace kamila kama Didi kullum maganarsa kenan tun muna scndry har muka rabu ya tafi gana duk wani saurayin da yazo wajenta shi yake koransa lokacin da na tambayi shi meyasa yake koran mata Samaruka cemin yayi wallahi baisani ba amma da zarran ta ganta da wasu maza ranshi ke 6aci duk hutun da zai koma Inna wallahi sai yayi kuka sabida Didi Inna Abul nasonta son da wallahi baki bazaiya furutawa ba amma kitunani akan haka duk zuwansa tsarabanta yafi nakowa amma duk yanda kukayi shine mai kyau "

wani farin cikine ya rufe Inna tace "ba damuwa bari naji me Y'ayanku zaice ."

Da wannan sukayi sallama

dan haka yanke hukumcin fad'a ma Babansu da ya dawo ta fad'a masa shima dariya yayi yace " toh shi kuma wato sunna zai d'abaka ko Allah yasa mudace amma fa tayi mashi girma ina shi ina Uwar d'akinsa banda namiji toh Allah ya tabbatar "

"Amin" Inna tace,

🌹🌹🌹

"karfe biyu da rabi na dare mafarkin da yasaba akanta y'au ma shi yayi dole ya tashi yayi wanka ya d'auro alwala sannan ya tada sallah nafila raka'a biyu yayi sanna ya d'auki alqur'an yqfara karatu ya dade yana karatu kafin ya rufe ya fara kwararo addu'a akan Sahibarsa Allah ya dai daita al'amarinsu nanma ya dade kafi ya tashi ya kwanta.

Da asubahi ma saura kad'an ya makara sai da Abbansa ya tada shi bayan an idar da salla ne duk suka fito shikan gida ta tawo Abbansa ne ya tsaya da su Baban Rukayya bayansu gaisa ne da yake dukkansu Baban Rukayya da Kanensa Abban Abul yace " gani dai a gabanku amma narasa me zance muku bansa ya zaku d'auki abinda zan fad'a ba "

shiru yayi

Babansu Rukayya yasan kwanan zance amma yafi son yaji daga bakin Alhj Attahir

duk sun kagu da son jin meke tafe dashi Baba Yakubu ne yace " Alhj karka damu ka fad'a mana kawai "

ajiyar zuciya yayi kafin yace " daman Yahya ne yake niman izinin neman auren Rukayya "

duk mamaki ya rufe su Baba Hameed ne yayi karfin halin cewa " Alhj kansa me kace kuwa "

"ehh dagaske nake fa ba da wasa ba saidai ko baza ku bashine " yace,

Baba Tanimu yace " a'a ba haka bane kawai muna gudun magana ne amma tunda shine yake son mun bashi ita Allah ya tabbatar"

Baban Rukayya baice kome ba sai murmushi da yayi.

Baba Baseeru yace " Yayan baka ce kome ba sai fama murmushi kake "

dariya yayi kafin yace " me zance tunda shi Yahya duk Yan mata unguwar nan basuyi masa sai tsohuwar y'arku " sai kuma yarike baki alamun yayi kato6ara.

Dariya suka saka dukkansu 6ata rai Abban Abul yayi yace " bana son haka fa Alhj hassan y'artawa ce tsohuwa bakai ba takwara na fad'a maka "

dariya sukayi masa haka suka rabu cike da raha da farin ciki sai tattaunawa suke har suka shiga gida lokacin shida da arba'in da biyar dai dai itama tafito kenan tana da labarun karfe bakwai sai sauri take a dai dai zauren cikin gida suka had'u tsugunawa tayi kasa ta gaishe su , duk suka amsa Baba Hamisu yace " mamana muna sa idonki fa gobe inbaki samun ba toh munyi miki miji "

a razane ta d'ago kai sai kuma ta mayar kasa tace " bani da zabi sai naku "

Baba Tanimu yace " jeki Allah yayi miki albarka a dawo lafiya"

"amin " tace,

sukuma suka shiga gida kowa ya kama gabansa zuwa aiki.

🌹🌹🌹

A wajen aikin ma dakyar tayi aiki domin bata da kuzari har tashi daga aikin me nape ya kawo ta tana sauka tabiya kud'i zata shiga ashe shima yana kan motarsa durowa yayi yasa kananun kaya sajinsa da y'ar gemun wanda suke had'i da juna sunsha gyara fuskansa tayi wani fass da shi cikin takun kasaita ya shiga zauren yayin da ita kuma take tafiya cikin nutsuwa har tashigo zauren kamshin turarensa ya shaka sai da ta lumshe idanun ta kafin ta bud'e akasan shima ita yake kallo yace " Preety barka da dawo nasan kin gaji da yanzu kina da miji ai dasai yayi miki wanka ya baki abincin da ya dafa da hannusa ko "ya d'aga mata gira.

Tsaki ta ja bata san lokacin da bakinta tace " d'an iska Yaro kawa....."😳

Mmn Waleed ce [11:09AM, 12/19/2017] REAL ME DAMBU CE🥗: ☔☔☔☔☔☔ *YARO MA NAMIJI NE* 💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DAMBU CE*🥗

*Ba danku ba da daga y'au wanna buk din ya koma tarihi amma kuka bani kwarin gwiwan rubutawa har nake tashi da niyyar rubutawa dan haka bani da Bakin muku godiya sai dai Fatan alkhairi a rayuwarku* kuncire min tsoro kunsamin jarumta ѕtαч ín вlєѕѕíng ѕíѕtєr'ѕ.

🎁H.A.W🎁

1⃣7⃣🌹1⃣8⃣

"Rintse idonsa yayi da danasani mata magana bai ta6a tunanin zata iya zaginsa ba don haka y'au sai ya ladabtar da ita akan laifinta.

harta bar zquren farko tashiga zaurem tsakiya yana biye da ita itama taji tsoro don sauri take sosai tashiga gida domin jikinta yana bata Abul baza kyaleta ba.

Suna shiga zauren cikin gida da yake yana da zurfi ga d'an duhu kafin ankara ya sha gabanta fuskansa d'auke da murmushin mugunta yace " nine d'an iska ko ? y'au zaki ga iskanci ya ganin idanunki "

jikintane ya fara rawa kaman wacce aka shekawa ruwan sanyin gashin garin ya d'au hadari har wani irin duhu yayi wanda yakarawa zauran duhu sosai.

Takowa yake ita kuma tana ja da bayan sai yarfe hannunta take ta raraba idanu kama kace kyasss ta zura a guje har takai jikin bango sai tsaya ta fara kokaran bashin hakuri had'a hannuwanta tayu alamun yayi hakuri ko takanta baiyi ba

hannunsa yasa ya dafa bangon d'aya hannun yana rike da phone dinsa mayar da phone din yayi aljuhun wandonsa kafin ya kama lips dinta da yatsan hannunsa

guda biyu ya d'anke su sosai yana murmushi mugunta yace Didina kenan dake a tunaninki sumbatarki zanyi koda wasa bazan fara ba amma wannan shine hukumcin laifinki don idan zamu kwana qnan bazan sake bakinki wanda bayi iya magana ba tunda ke haka Allah yayi harshinki muzuba waye zayi nasara ni da ke."

duka da yakushi yashata bana wasa na tun tanayi harta hakura hawaye nazuba shakaf fuskanta ya jike da ruwan hawaye yarfe hannunta take takuka amma ko ajikinsa.

Karshe dataga tana shirin illatata tureshi tayi amma yanda kukasan bishiyar rimi haka taji shi ta kid'ima ta gigice tarasa yanda zatayi dole ta had'a jikinta dana shi yayinda ta tura akanta a fad'id'in kirjinsa dole yasa yacire hannunsa wanda hakan yasa tasake kuka me cinrai jikinsane yayi sanyin domin yasa bekyauta ba kukanta yana dukan zuciyarsa dan haka ya cireta a jikinsa yace "kiyi hakuri haka bazai sake faruwa ba"

jakanta ya d'auka ita kuma tabi bayansa yana tafe yana ambaton Allah.

shigansu kenan wani mugun hayaki me shegen wari ya biyo iska tashiki kamshi amma abin mamaki shine Abul baiji ba sai ma ambaton Allah da yqke jin wanna warin yasa kanta yayi wani irin sarawa wanda sai da tace " wayo Allah na "

jirine yake nema kwashe ta yajuya da sauri ganin tana layi kaman wata y'ar maye yasa da gudu yaso tare tadaka masa tsawa tace" karka tabani na tsane ka bqna kauran ganinka kuma idan baka fita harkata zaka sha mamakina "

Baba Tanimu ne yafito ya ga dawa Rukayya take fad'a yana fitowa ya ga Abul yana kallonta kama wani dolo ranshi ya bace amma ya boye gani Baba tanimu.

Fad'a Baba tanimu yarufeta da shi sosai " yace" tunwuri ki kaman kanki domin baki da mijin da yafi Yahya mun bashi ke daga y'au karna sake jin magana me kama da haka shashasha kawai "

ihu ta saka ta zauna a wajen ta kuka tana cewa " wallahi bana sonsa gwara mutuwana akan na zauna dq shi wallahi kuka kashe kawai dana zauna da wannan d'an iskan Yaro "

tab da Rukayya tasan Kanen Babanta suna gidan dukkasu ta bata fad'i hakq ba abin yayiwa kowa zafi don duk suka fito suka ga yanda take birgima a kasa shi kuwa Abul mamakinta yake ji. Komawa suka sabon shiri akanta basu fito ba sai da bulala dukkansu shidan suka rufeta da duka bana wasa sabida ransu yayi mugun 6aci a tarihin gidan itace ta fara musu jayaya akan aure idan suka ce farine to farinne Abul gani irin dukan dasuke mata yasa yashiga ya rufera ya rungumeta itama sabida azaba buya yatai a jikinsa duk da tana jin kama ta ana watsa mata ruwan zafi.

Dole suka hakura suna ce mata "aure babu fashi kokiyi rai ko kimutu."

🌹🌹🌹

A d'akin Inna kulu murna take har tana rawq shigowan Baba tijjani yasa ta zauna yana huci.

koda Abul yakai Rukayya Inna ko kulata batayi ba tace" Yahya jeka Allah yayi maka albarka"

"amin" yace,

🌹🌹🌹 gani abinda Rukayya tayi yasa aka saka bikin da yake har ankawo sadaki Abul da kayan na gani ina so kuma haka hanata zuwa aikin gaba d'aya Babanta yace don tana aikin yasa take bijiru musu daga yau ba'aiki.....

*ABUL KHAIRI BASHI DA TEAM SAI RUKKY*

Inda kuna yinsa mun tani a kasa😜😎

Mmn waleed ce [6:36PM, 12/19/2017] REAL ME DAMBU CE🥗: ☔☔☔☔☔☔ *YARO MA NAMIJI NE* 💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DAMBU CE*🥗

*H.A.W*

1⃣9⃣🌹2⃣0⃣

Duk abinda Rukayya keyi Inna bata kulata ba kullum Abul yana zuwa idan yazo Inna takan basu waje sai ta dawo kin sukuma suna falon bakar magana Rukayya ke fad'a masa indan ta fara sunkuyar da kansa kasa yake har sai ta gama.

Yayi murmushi yafita yasawa ranshi duk abinda zatayi wallahi bazai kulata ba gashin akansa an hanata aikinta don yau da yazo suka gaisa da Inna rukayya tana waje tana wankin unders dinta kallon d'aya wa brzy din ya kauda kai hankalinsa ya mayar wajen Inna

yace " Inna nazo ne akan maganar aikinta da aka dakatar mata da zuwa shine inda hali ta koma zai rage mata damuwa"

murmushi Inna tayi kafin tace " me na damuwa Abul duk d'an da yake jin maganar iyayensa burinsa ya kyautata musu ko suke balle ita da tafi karfin mu tana neman mu kasheta hmmm Allah yayi maka albarka kawai."

Tashi rukayya tayi daga waje takoma cikin inda tashiga d'akinta tana kuka kasa jurewa yayi ya bita har d'akin yana bata hakuri ko d'aga kanta batayi ba magana fara masa magana tace "

kimanin shekara guda kenan dq kashigo rayuwata karaba ni da masoyana karabani da iyaye Abul me nayi maka hakane me zafi da kake niman bayana eyye ?"

"kiyi hakuri "kawai yace mata kana yafita yayi alkawarin baza sake shigowa har sai dole ne zaisa yashigo.

🌹🌹🌹

Bikin na karatowa daga cikin wanda za'ayi bikin yaransu akwai,Baba hamidu yan mata uku ne,sai Baba tijjani yan mata biyu budurwa da bazawara kuma duk yaran Inna kulu ce, Baba hamisu guda d'aya ce,

Baba yakubu shi kuma duk maza ne zasu aure, sai Baban Rukayya ita d'aya ce,

don haka gyara suke samun daga Hajjo matan Baba baseer sai da akai ruwa rana da Rukayya kafin ta amince duk amare kansu na rawa amma banda rukayya.

Duk wani abinda yadace tayi taki yi karshe Hameeda da Zulfa sune akan kome duk amaran ankawo kayansu na Rukayya kawai ba'a kawo ba har anfara jefa mata magana Inna dai kota kula.

Y'auma kaman kullun tana zaune ta gyaran farcinta kira shigo wayarta tana dubawa ta ga nmb Hafiza yayar Abul da kama baza ta d'auka ba ganin irin kallon da Inna tamata yasa ta d'auka.

sai dasuka gaisa kafin hafiza tace " Didi don Allah kiyi hakuri mun had'a kaya saura abu biyu suka rage bamu san size dinki bane brzy dinki da shoe dinki"

shiru tayi tana satan kallon Inna kama zatayi kuka tace "shoe 37? brzy kuma 38 ne"

kashin wayar tayi ta fara guna guni tace " haka kawai an cuce ni an had'a ni da d'an is..." sai tayi shiru kallonta Inna tayi kafin tace "

ki godewa Allah da yabaki Yahya kuma bandan sonda Iyayenshi kemasa ba wallahi koda wasa babu wanda zaiso d'ansa yaro karamin d'anyan jini ya aure gusuma irinki wacce bata sanciwan kanta ba har shiyafiki hankalin kai Rukayya kiyi murabu lafiya in ba haka zanshiga jikinki wawiya kawa shashasha kawai,

🌹🌹🌹

gefe guda kuwa Inna kula bata bar Rukayya haka ba sai fa tasake komawa wajen me buzun kura ya bata maganin da zata ba Rukayya duk abinda tasata zata mata biyayya akai ba musu.

don haka yabata yace " kihad'a da wani kayanku na mata kibata tasha baki da matsala da ita sai yanda kikayi da y'ar banza tashi kitafi amma ki kiyayye rabo me karfi."

"tow boka me duniya nagode " tace masa,

🌹🌹🌹

cikin kuka tace " haba Inna yaron da na renishi kuma a ce shine mijina don Allah kufasa " tana kuka,

yanzu Inna ta daina jin haushin Rukayya saidai tana shakku akan al'amarinta tace " kina ja ikon Allah ne toh wallahi kukina so ko baki son magana yakare.

🌹🌹🌹 Umma da kanta takira Inna ta fad'a mata za'a kawo kayan Rukayya Inna tace " ba damuwa Hajiya yaushe don mushirya "

dariya Umma tayi tace "sai jibi za'a kawo Insha Allah "

da dare Baba na dawowa ta fad'a masa za'a kawo kaya jibi "

yace " Allah ya kaimu akwai me ko sau ankara"

tace " akwai saidai kud'in sallama masu kawo kayane wanda yake hannuna yakasa duba arba'ine "

yace " idan nakara sittin yayi ai ko"

" mungode Allah basu zaman lafiya" Inna tace "

Amin

🌹🌹🌹 Abul har gidan radio freedom yaji yanemin abata hutun karshe shekara kuma sun bata domun shekara hud'u tana aiku da su bata ta6a neman hutu sai akan auren.

Inna kulu ta had'a maganinta da tsimi ta bawa kowa marar magani tatura aka kira mata Rukayya ta bata tace " na ba y'an uwanki nasu maza sha ina gani dan naji ance baki shan magani "

sai addu'a take Allah yasa tasha ay kuwa ta d'auki goran faro da tsimin kecikin ta kwankwad'a sosai Inna kula tace " jeki kullun kisha fa "

Rukayya tace " to na gode "

🌹🌹🌹

y'au za'a kawo kayan tun safe su Inna da Hajjo da Babbar y'ar Hajjo itama sa'ar Rukayya ce da matan Sa'idu da Hameeda suke aikin abinci da wasu abubuwa sai karfe biyu da rabi aka fara shigo da akwatina har goma sha biyu ganin wanna kayan yasa Inna kulu zaman yan bori🤣

Maman Waleed ce🤝🏼 [7:29AM, 12/20/2017] REAL ME DAMBU CE🥗: ☔☔☔☔☔☔ *YARO MA NAMIJI NE* 💦💦💦💦💦💦

_🌹LOVE STORY🌹_

*REAL ME DQMBU CE*🥗

*Masu min magana ta Pc ko ta group kuka ga ban kula ba don Allah kuyi hakuri ba wulakanci bane ko girman kai wallahi duk ba halina bane kumin uziri kuna da yawwa wallahi kuma bana ganin sakonku da wuri har sai nasake shiga group din kuyi hakuri*

_Wannan shafin nakune Hikima Asso Writer's Ina alfahar da ku nagode Allah ya had'e kanmu_

*Hikima Asso Writer's*

2⃣0⃣🌹2⃣1⃣

Ganin yanda aketa shigo da kayan yasa Inna kulu gigiciwa har takasa boye halinta cike da karfin hali tace "

duk wannan kayan na Rukayya ne akwati takwas da kite "

Goggo Haule Babbar yayarsu Baban Rukayya tazo itama karban kayan ita ta rangad'a gud'a sosaii sai kuma tasaka kuka tace "ashe zanga wannan ranar kai mahakurci mawadaci Allah na gode kai masha Allah Allah ya albarkaci su da zuri'a d'ayyiba Allah yasa auren mutu karaba Allah kabashi Ikon riketa da Amana itakuma kabata ikon masa biyayya "

kowa nawajen amin yake cewa amma banda Inna kulu addu'a take allah ya aikon gobara ya kona kayan

_kunji wata sabowa kuma_

bud'e kayan aka shiga yi duk wanda yaga kayan sai jikinsa yayi sanyin sabida yawansu har akwatin baya rufuwa duk cikin kayan babu wanda yaba kowa dariya sai akwatin hijabai sabida babu gyale ko d'aya Hameeda ta kalle Hafiza tace " ya haka banga gyale ba sai hijabai matar limance "

dariya matar Adamu tayi tace " wallahi shi yahana dakyar nasaka wanca sabida ranar bud'ankai shima baisan da shi bane "

y'an uwansu Umma ne da Abba dariya sukayi suka ce " toh ay shi ustaz ne baya hidimar gyale sai hijab "

wata kawar Umma ta 6ata rqi cikin wasa tace " d'an nawa kukewa ba'a zaku sha mamaki domin ustaz yafi kowa iya kula da matansa "

dukkansh dariya suka saka addu'a sukayi kafin suka mike da niyyar tafiya.

Hajjo da y'arta Rukayya da Hameeda kwaso musu kayan tarbansu sukayi tayi sannan Goggo haule ta d'auki kud'an tukwice ta basu naira dubu d'ari da talatin karin talatin din goggo taba da ashirin hajjo tabada goma godiya sosai gidajen biyi suke tayiwa juna sabida karamcin da aka musu.

sai da suka tafiya aka sake dawowa kan kayan inda akq shiga dubawa sosai turamen atanfa had'i da less da akwatinsu daban shadda y'ar asalin senegal da kamfala duk a waje guda aka had'a su material da lafaya suma waje guda dogayen riguna wajensu daban

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull