Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 12

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 12

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 12: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 12. Washe gari suna fita cikin Saa Bilal ne…

3,281 words

Washe gari suna fita cikin Saa Bilal ne yazo daukansu ya dawo kenan dan haka ta ringa jera ajiyar zuciya daban daban har suka isa saidai bata iya masa wani zancen ba tinda ita kanta tasan bazai yiyu ace tana dauke da abinda Annen ta fada ba dan haka sai kawai sukai iya maganar da zasuyi ya tafi bayan yasa taci abinci sosai sbd ganinta dayayi duk ta rame tayi fayau kaman ya saceta yaje yayi jinyarta cikin kyakyawan guri mai nutsuwa da kwanciyar hankali tareda kulawa.

Har suka tashi sama sama take dan haka ta riga Benazir komawa gida tana isa gidan dole ta kamawa Anne aiki saidai ko rabi batayiba ta yanke jiki ta fadi Allah yasa Yauma hande bata gidan dan haka Anne cikin firgici ta zuba mata ruwa ta farfado sukai daki ta kwanta.

Koda Benazir ta dawo jikin nata yayi dan tsanani saidai tana bacci dan haka batayi dogon motsiba dan kar ta tadata ta fita suka cigaba da qarasa sauran aikin.

******Bayan kwana biyu sunata jinyarta a boye ba tare da sanin Hande ko Ababa ba, Tana cikin rashin kuzari ko kadan ga yawan Amai yanzu datakeyi babu wata wata Anne cikin tashin hankali da baa saka masa rana ba tace wlh ciki ne a jikin Sumayyahn.

Benazir kusan sumewa tayi da zancen ita sumayyar kuwa daman bata hayyacinta,

A zaune suka kwana dare cikin matsanancin tashin hankali da fargaba da jiran tabbatarwa, Daqyar sukaga gari ya waye cikin rashin sanya yau suka tattara sumayyar ta dan samu qwari suka fice makaranta sbd a can zasu samu tabbacin Zargin Annen. Kaman yanda Benazir ke addua Alh bilal dinne da kansa yazo daukansu ganin halinda Sumayyah take suka wuce kai tsaye asibiti sina zuwa aka kwantar da ita.

Tashin farko likita ta iso musu da sakon ciki ne a jikin Sumayyah na sati hudu.

Wuta ce ta dauke masa Benazir kuwa duhu idanuwanta sikai lokaci daya kuma qafafunta na kasa daukanta ta zube qasa tana kokarin samun ganinta ya dawo. Follow me on Arewabooks @Mamuhgee dan samun pages dasuka fi yawa. #MAMUH# #DD KAANTE #BENAZIR ABABA#LITTLE BENA#HOTHOT#LOVE#ROMANCE#ZAFIN KAI#BILLONAIRESromance#sumayyah Ababa.

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 09033181070 09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

ZAFIN KAI

19 Ganinta neman gagararta dawowa yayi sbd bata taba samun kanta a mafi tashin hankali irin na wannan daqiqun ba datake cikinsu a yanzu, Cikin haihuwa fa ake magana sumayyah take dauke dashi, Ta haifa 'da ko 'ya masu rai fa,Innalillahi wainna ilayhi rajiun, Qalu innalillahi wainna ilayhi rajiun, Ya ilahi meye haka kunnuwanta yau sukaji, Babbar kadaddariyar jarabawarsu ce yau ranarta ta tsaya, Tsikar jikinta ne gabaki daya suka tashi sbd tinaninta daya dade da tsayawa babu abinda take gani sai gawar kansu su uku ita da Annensu da sumayyar harma da cikin.

Bilal kaante kuwa wutar data dauke jikinsa babu abinda yake zuwa kansa sai tausayin Sumayyah da abinda yake cikin wanda baisan me zai fada akansu ba yanzu, Kalmar cikin ta girgiza sa ne sbd abune da bai taba zuwa tinaninsa ba a wannan lokacin. Shi kansa a nasa bangaren wannan wani babban qalubalen ne da tashin hankali sbd tsakaninsa da iyayensa da danginsa wani abune da ko zasu rasa komai bazasu yarda da wannan zancenba sbd karma ya fita,dan gwara ya jewa dd babba da dad kaante da labarin sunyi asarar miliyoyin kudi masu yawan da hankali bazai dauka ba akan yaje musu da wannan labarin.

Daga shi har Benazir babu wanda yakeda nutsuwa ko tinanin kallan junansu kowannesu da nisan da yayi cikin nasa tashin hankalin da baa saka masa rana ba.

Kaman masu jiran sakon mutuwa haka suke babu me motsi,har lokacin Benazir na zube qasa zaune batada qarfin tasowa shima har lokacin yana tsaye,

Benazir tashin hankalinta yasa tini ta manta da yanayi sumayya tinaninta akan cikin yake har lokacin dan kuwa zancen ya kasa zaunuwa a ranta tayaya sumayyarsu zata samu ciki? Ina ta samesa? Da wa? Yaushe? Sam kanta ya kasa daukan zancen bare tasan yanda zuciyarta zata aje zancen.

Acikin zaman jiran da baifi na awa daya ba Idanuwanta sukai wani fadawa tareda yin jajir Daqyar take iya hadiye busashen yawu a makoshinta daga bakinta daya bushe qayau,

Bilal kaante kansa bakin nasa a bushen yake saidai yanayinsa yasa baa iya gane zallar damuwa da tashin hankalin dayake ciki.

Sumayyah batasan halinda take ciki da wanda suke ciki sai bayan awa hudu data share tana bacci sbd ruwan bacci dayake cikin ruwan da aka daura mata,

Tana farkawa Abinci mai lafiya da rashin nauyi Bilal yasa aka kawo mata, Benazir har lokacin bata dawo cikakken hayyacinta ba gabaki daya bata gane komai sosai dan haka tana gefe rakube tayi zugum batasan me take tinaniba ita kanta tadai san tana cikin mafi girman tashin hankalin rayuwarsu.

Shine da kansa ya bawa sumayyar abinci cikin kulawa da so mai tsanani yanajin inama da aure ne tsakaninsu wannan qaddarar qaruwar ta same su da sai ya nuna mata soyayyar da zata manta da quntatacciyar rayuwarsu ta baya, Yanzu gashi qaddara ta riga fata,waye zai fara tara da wannan maganar mai girma?

Sumayyah data dan samu kanta sai alokacin ta maida kallanta da hankalinta kan Benazir da zama abin tausayi cikin awanninsu a asibitin,

Magana takeson yi mata amma ganin gabaki daya Benazir na wani yanayi yasa ta kasa mata maganar ta dan dawo da kallanta kan Bilal da shima tin dazun ita yake kalla cikin tsananin tausayi da kulawa dan bayajin zai iya gangancin yimata abortion sbd tsoron abinda zai iya samunta kuma cikin ba laifinsa ne ba qaddara ce ta samar dashi wadda suma suke cikin nadama da neman yafiyar ubangiji tun ranar ra tsautsayin ya afka musu har yanzu kuma bazasu dena neman yafiyar Allah ba har qarshen rayuwarsu sbd shedan da kaddarar wannan samun ya afka musu.

Sabon zaman makokin da bana mutuwa ba suka dasa babu mai iya magana acikinsu kowa da tashin hankalin dayake tada zaman lafiyar zuciyarsa.

Benazir data rasa tinanin kamawa miqewa tayi jiri na neman dibanta tace gida zasu tafi kawai.

Kallanta Bilal yayi yana dago wayarsa da kira ya shigo yaga sunan dd babba ne kuma baa qin daga wayarsa idan ba babban dalili ba dan haka ya daga cikin tattaro nutsuwarsa datake kokarin barin jikinsa sbd komawan sumayyah gida da wannan cikin a yanxu babban hadari ne ga rayuwarta sbd komai ma zai iya faruwa idan Ababa ya sani.

dd babba dake babban lafiyayyan office dinsa na gida yanajin Bilal ya daga wayar kai tsaye yace yazo yanzu yanzu yana nemansa.

Rintse idanuwansa yayi cikin damuwarsa dake bayyana yana kallan su Benazir data miqar da sumayyah har sun kusa kofa yana jin kansa na sarawa da ya biyo bayansu ya bude musu mota yana kallan Benazir da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da sanyin jiki tareda kunyar kansa yace mata gobe da safe zasuyi magana idan ya taho daukansu amma ta kula da Sumayyan kafin goben.

Kai kawai ta iya gyada masa sbd bazata iya magana ba kuma bazata iya dagowa ta kallesaba.

A motar ma babu mai iya magana hankalinsa yayi mummunan tashi zuwansu gida da abinda zai iya biyowa kafin safiyar gashi dd babba na masa neman gaggawa wanda bai taba jin hankalinsa ya rabu biyu akan zuwan kiran dd babba ba sai yau din.

Yana ji yana gani dukkaninsu sukai shahadar rabuwa ya ajesu ya wuce yana sake jin fargaba na shigarsa na barinsu ya nufi gida.

Suna shiga gida suma kai tsaye dakinsu suka nufa sbd ba kowa tsakar gidan Annensu na bangaren dabbobinsa tana shara batasan dawowarsu ba,hande kuma tana daki tana baccin rana.

Kwantar da sumayyah tayi har lokacin bata ce mata komaiba sbd batasan me zata fada din ba sbd zuciyarta data kasa dawowa da bugawa daidai.

Zubewa tayi gefen sumayyar tareda rafka wani mummunan tagumi nauyin idanuwanta na qaruwa,

Sumayyah datake kallanta cikin nauyin idanuwan itama tashi tayi zaune tana kallan Benazir din da damuwa ta bude baki cikin taushin murya mara karfi tace

"Bena meya faru? Meyasa kike cikin yanayin nan? Wani abin ya faru ne?

Juyowa Benazir tayi da jajayen idanuwanta ta zubawa Sumayyahn sai alokacin taji hawaye na ciko idanuwanta.

Cikin mutuwar jiki da damuwa mai tsanani sumayyah ta dafa hannun Benazir din dake rawa muryarta na shiga tashin hankalin ganin hawayen dake ciko idanuwan Benazir tace

"Meya faru Bena? Dan Allah fadamun meya faru, Meya sameki?

Wani irin kuka mai ciwo da radadi ne ya kufcewa Benazir din mai qarfi da rshin sauti ta sunkuyar da kanta tana kasa magana.

Kukanta ya saka jikin Sumayyah daukan rawa sosai cikin tsoro da fargaba mai girma sbd duk abinda ya saka Benazir hawaye babba ne bare kuka mai qarfi irin haka.

Annensu data shigo dakin tayo alwalar sallar laasar zatayi tana ganinsu ta qaraso tana kallan Benazir datake kuka mai ciwo da radadin rai.

A tare cikin rudewa suka sake jefa mata tambayar abinda ya faru.

Annensu ta dago ta kalla tausayinta ya kamata saidai babu abinda zasu tare daga qaddarar da ubangiji ya doro musu saidai tasan wannan qaddarar mai nauyi ce garesu musamman Annensu da bazata iya daukan wata azabar ba da ciwon lamarin a matsayinta na uwa kuma mahaifiyar sumayyah.

"Menene Benazir ki fada mana,meya faru?"

Takardar da aka basu a asibitin ta cikin Sumayyah ta ciro daga cikik rigarta ta miqawa sumayyah sbd Anne bazata iya karantawaba, taja wani numfashi mai zafi da mutuwar jiki Muryarta a sanyaye ta bude baki tace

"Anne ciki ne kaman yanda kikai tinani......

Kasa qarasa bude takardar Sumayyah tayi ta tsaya cak tareda dagowa tana kallan Benazir datake hana kukanta dawowa tana kallan Annensu data dauke wuta.

"Anne, Anne, Anne" tafada hankali tashe tana taro Annen jikinta sbd yankewan da jikinta ne neman yi.

Tashi tayi hankali tashe koina jikinta na rawa ta taro Annen tana sake kiran sunanta cikin sabon tashin Hankali murya qasa qasa sbd ba daman daga muryar kada a jisu.

Sumayyah da itama tayi mutuwar zaune ta juyo ta kalla cikin tashin hankali tace kawo ruwa Anne zata siqe. Sumayyahn bata san me Benazir take fada ba sbd suman datayi a zaunen itama.

Tashi Benazir tayi da sauri ko gabanta bata gani tana kimfewa ta sake tashi da sauri ta fice ta debo ruwa tana zuwa ta zubawa Annensu kofin ruwan gabaki daya kafin ta sake fita qafafunta na hardewa ta debo wasu ta zubawa sumayyah ta wurgar da kofin tayi kan Annensu dake jan numfashi daqyar tana dafe kirjinta dake toshewa.

Cikin tashin hankali da tsoro mai tsanani Benazir take shafa mata bayanta tana karanto mata adduoi tana kiran sunanta a hankali.

Sumayyah data dawo hayyacinta kuwa wasu hawayen tashin hankalin da baa saka masa rana bane suka tsinke mata tana jin tsoron da bata taba jinsa ba a rayuwarta yana shigarta sbd tabbas lokacinta yayi.

A hankali Anne ta dawo daidai ta dago ta kalli Benazir da idanuwanta sukai jajir ta maida kallanta kan sumayyah take suka fashe da wani irin kuka mai tsananin ciwo da tashin hankali duka su ukun a lokaci daya.

Kuka sikeyi sosai mara sauti kowannensu na rasa abin fada tsawon lokaci mai tsayi kafin Benazir ta dago tana share fuskarta sbd jin motsin fitowar Hande tsakar gidan tana kwada kiran Annensu dan batasan suma sun dawo ba.

Kowannensu taqaita kukansa yayi suka share fuskokinsu babu wanda yace komai suka fito daya bayan daya fuskokinsu a qasa sbd yanda idanuwan kowannensu yayi jajir ya kumbura.

Kallansu Hande batayiba bare taga halinda sike ciki kai tsaye ruwan datasa a debo mata a bokiti Benazir ta debo mata takai mata bandaki ta fito sukai alwala sai alokacin suka samu damar yin sallolin dake kansu itama Annen me alwalar laasar saida ta sake wata.

Koda suka gama sallah jigum jigum sukayi har lokacin babu me magana sbd bude bakinsu ma a yanzu tsoro sukeji dan basusan ta inda zasu faro wannan maganar ba a cikin gidan da fitar maganar daidai take da tsayuwar alqiyamarsu.

Har akai sallar magriba aka fito babu wanda ya fita acikinsu da alwalar sukai sallar suka sake komawa zaune kowa yayi shiru yayi nisa a tinaninda babu komai acikinsa sai tashin hankali da tsoro tareda tinanin makomarsu a gurin Ababa.

Abincin dare da aka basu a ranar haka ya kwana bar safe babu wanda ya sake kallan inda yake sbd masifar da suke ciki.

Suna gama sallar asuba Anne ta kalli sumayyah da a daren guda ta zabge sbd tashin hankali.

Dukkaninsu babu wanda idanuwansa basu fada ba sukai jajir sbd duk kasancewar bacci barawo a ranar ya kasa sace su ynda suka ga rana haka suka dare.

"Waye yayi miki haka Sumayyah? Wane qaddara ce wannan sumayyah? Tsautsayin menene wannan? Meyasa sumayyah? Waye ne??

Tsit dakin ya dauka bayan numfashin dake fita a sarqe da damuwa mai tsanani babu abinda akeji a dakin.

Sunkuyar da kai Sumayyah tayi wasu hawayen na gudu kan fuskarta quncinta na tsananta tareda kunyar kanta dana mahaifiyarta da 'yar uwarta sbd wannan qaddarar masifarta ba iya kanta zata tsaya ba dukansu ukun ta tabbatarda sai sun mafi munin halin quncin rayuwa a gurin Ababa.

"Alh Bilal" tafada muryarta na yankewa sbd kuka mai qarfin dayazo mata. #MAMUH# #DD KAANTE# #LOVE#AMNAH KAANTE#BENAZIR#crazyinlove#

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim

Send your Shedan biya Anan👇 09032345899

MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇 09033181070

Zafafa🫶🔥🔥

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 20 Shiru dukkaninsu sikayi sbd daman sunsan bazai wuce Alh bilal dinba dan haka kowannensu ya sake shiru sbd basusan mafitar wannan qaddarar ba data rigayi fata.

Cikin rudewa da tashin hankali Annen batama san me dame take fada ba ta fara fada ciwonta na neman tashi sbd kanta da yayi nauyi neman juyewa yakeyi Benazir ta taso ta dawo gurinta da sauri tana kwantar mata da hankali sbd kar ciwon ya tashi komai ya lalace asan halinda suke ciki.

Har gari yayi haske suna daki suna fama da kansu ba sauki ko kadan dole Benazir ta fito ta hau aikin gidan gabaki daya ba maganar zuwa makaranta sbd tsoron fita takeyi ma tabarsu kada kafin ta dawo Ababa ya sani ta dawo ta tadda babu su ga kuma yanayin Annen daketa surutai cikin tashin hankali da fita hayyaci Sumayyah ma idanuwanta sunkai ko budewa basayi sosai sbd kumbura ga yanayinta na rashin lafiya.

Abincinsu na dare da basu ci ba haka suka zauna su ukun suka turasa cikinsu da sanyinsa harma ta sakewar daya fara yi sbd kada su fitar a san basu ci a fahimci suna cikin wani halin a gano.

Babu mai dadin rai ko nutsuwa a cikinsu haka kowa ya ringa diban abincin yana turawa bakinsa bame magana suna gamawa Benazir ta dauki kwanon ta fice taje tafara wanke wanke.

Annensu zaune take a dakin nasu ta kasa fitowa idanuwanta sunyi ciki ciki tsaban kuka da damuwa ta rafka tagumin da basusan yanzu kuma yanda rayuwa zatayi dasu ba.

Sumayyah kuwa ciwo ne yake cinta sosai amma tashin hankali da damuwa ya hanata nunawa itama tagumin ne ta rafka dukkaninsu kaman wainda ke jiran sakamakon mutuwa.

Benazir ma ayyukan gidan takeyi ba'a cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali ba kowannensu tinanin makomarsu yakeyi.

Sai bayan sallar Azahar ta kammala aikin tayi wanka da alwala tazo tayi sallah aka basu abincinsu data gama girkawa ta kawo ta ajiye musu dole sukai sallah suka zauna suka turawa cikinsu babu me jin dandanon komai a bakinsa cikinsu kowa 'dacin bakinsa yakeji musamman Sumayyah da nata ya hada dana ciwo da laulayi.

Tsit Hande taji gidan yayi suna daki babu me iya motsin kirki sbd damuwa da tinani dan haka ta fito tana qwala kiransu tana tambayar lafiya suke zaman daki kaman masu abin kunya.

Tsinkewa cikinsu yayi Anne ta kalli Benazir da itama ita ta kalla suka kalla sumayyah a tare kafin Anne ta bude baki cikin mutuwar jiki tace

"Ki zauna a dakin karki fito"

Gyada kai Sumayyah tayi tana rintse idanuwanta sbd kunyarsu dake cin zuciya da ganganr jikinta gashi ta kasa ko bude baki ta fada musu kaddara ce da shedan daya shigo ciki.

Anne da Benazir ne suka fito sbd kada hande ta tsananta maganar.

Kallansu tayi taga duk sun jeme a dare daya kaman wainda sukai kwanan zaune, Fuskar Benazir ta kalla taga yanda ta sauya kwata kwata da alamar bata rintsa ba kuma harda alaman kuka bayan rashin baccin.

Kan Anne ta maida kallanta taga itama fuskarta tayi jajir ta kumbura, Shiru tayi tana nazarinsu sbd da alamar akwai abinda ya samesu dan duk wuya duk tsanani su biyun nan basu cika kuka ba sbd Anne ta dade da samun rashin lafiyar rashin kuka sbd shekarun data debo a rayuwar gidan zuciyarta ta mace bata iya kukan hakama Benazir sbd taurin rai da juriya ba qaramin tashin hankali da masifa ke sakata kuka ba amma yau gashi da alama kukan suka kwana yi..

"Kodai sumayyah ta mutu ne tsakar dare?" Tayi tambayar kai tsaye tana kallan hanyar kofar dakinsu da mamaki.

Anne wani numfashi mai sanyi ta sauke zuciyarta na sosuwa da abinda Handen ta fada tayi qasa da kanta tana kasa cewa komai. Benazir ma numfashin mara sauti mai dumi ta sauke tana girgizawa handen kai tace

"Tana nan lafiya ce batada tin jiyan"

"Shine kuka kwana kuna kuka ko me? Ta sake jefa musu tambayar tana kallan Benazir da idanuwanta ke sake yin qasa.

Shirunsu yasata rufesu da fadan batasan dabiar koke koke a cikin gidan da ba mutuwa akai musu ba.

Fada ta ringa yi sosai sai data gaji ta dena tace su wuce ga wankin shagon Ababa can an kawo.

Wucewa sukai inda manyan kullin kayan wankin masu yawa suke suka warware suka ringa kwashe kayan zuwa inda suke wankin.

Benazir ce ta fara debo ruwa masu yawa ta tara musu Suna fara wankin Anne ta sunkuyar da kanta qasa wani irin kuka mai sauti na subuce mata mai tafe da tsananin ciwo da quncin da zuciyarta take ciki.

Benazir radadin sautin kukan mahaifiyar tata ya sata kasa wanke kayan dake hannunta tayi qasa da kai itama wasu hawaye na tsinke mata, Me zasuyi? Meye mafitar halinda suke ciki? Ya Allah ka dubi maraicinsu" shine abinda zuciyarta kawai ta iya fada sbd sunsani sun tabbatar mawuyacin hali ne suke ciki mai nauyi.

Saida sukai kuka sosai kafin suka hakura suka fara wankin babu mai magana har suka wuni sunayi sai gab da magriba suka gama sbd abincin dare da Benazir ta dora tanayi tana tashi.

Daki suka shige bayan sunyi Alwala abincin dare kawai sukaci sukai ishai da akai suka lafe dakin babu wanda ya sake fitowa saida Ababa ya dawo Benazir ce ta fita taje takai masa abinci da ruwa ta dawo dakin suka cigaba da zaman damuwa.

Washe gari ma hakan ce ta kasance babu wanda ya fita makaranta cikinsu haka suka wuni cikin mummunan yanayi na damuwa.

*****kusan kwanaki hudu sika share a hakan cikin zallan damuwa da qunci tareda tsoro da firgici mai tsanani, Sumayyah na daki jikin nata sai tsanani yake qarawa amma basa barinta fitowa sai idan zata je bandaki kokuma idan Ababa ya dawo sbd kada ya saka musu idon zargin wani sai ta daure ta fito dan kawai ya gansu yasan suna nan kalau ba matsala,

Hande data ankara da yanayinsu gabaki daya ya sauya a kwanakin sai ta saka musu ido sosai ga Benazir data dena zuwa makaranta sbd tsoron kada ta fita a ganosu tinda daga Anne har sumayyah idan bata nan zasu iya firgicewa suyi abinda zai bayyanarda halinda suke ciki.

Readers Also Read