Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 13
Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 13: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 13. Ta bangaren Alh bilal kaante kuwa a cikin…
3,365 words
Ta bangaren Alh bilal kaante kuwa a cikin kwana biyun da baya ganinsu duk zuwan dayake yi kullum dan daukansu kaman zaiyi hauka a cikin kwanakin sbd gabaki daya shima ya shiga tashin hankali mai girma rashin ganinsu, Tsoron Ababa da abinda zai iya yi musu yasashi komawa kaman mai tabin hankali shima dayake mutum ne mai nutsuwa da kamun kai take aka gano yana cikin mummunan yanayi na damuwa da tashin hankali, Dad kaante da dd babba tini suka fahimci yana cikin mawuyacin hali sukaita tambayarsa ko lafiya amma sam zurfin cikinsa baya barinsa fada musu komai dan haka ran dad kaante ya baci ya kira Mahaifiyarsu Bilal din ya bata lokacin dawowarta idan ba haka ba damuwa zata kashe mata 'da a banza tana can gurin wancan da baya buqatan kowa tinda shine ya zabi zama baa cikin family dinsaba.
Dd babba kuwa ganin da gaske lamarin yayi yawa sai kawai ya tura bilal din wani aiki Kenya dole Bilal ya tafi bayan kusan har kwanciyar jinyar kwana biyu yayi sbd rashin sanin halinda su Sumayyah suke ciki, Yayi yawo anguwar yafi so hamsin a kwanakin amma babu alamarsu gashi yana gudun ya tinkari Ababan kai tsaye kila bai saniba tukuna kada ya janyo musu fitina wanda ya san da DD ne da tini zai tinkari Ababan duk abinda zai faru ya faru kowama ya dade bai saniba.
Ms aysha ce Aminiyarsa da zata iya masa komai ko baya nan dan haka ita ya sanarwa komai tareda rokonta taje ta dubo masa su tareda kular masa dasu.
Ranar daya wuce washe gari cikin saa sai ga Benazir tazo makarantar itama sbd Ababa yafara fahimtar ta dena zuwa hakama suna neman mafitan yanda zasuyi da cikin daga Bilal din tinda basuda kowa basuda gurin zuwa hakama bayyanar cikin dede yake da basusan ma me zasu ce ba.
Zuwan Benazir makarantar ya hana ms aysha zuwa gidansu ta zauna da Benazir din cikin kulawa ta tambayeta lafiyarsu da yanayin Sumayyar.
Shiru Benazir tayi takasa magana sbd kukan dayazo mata a hankali Ta sanar da ms aysha mafita suke nema basuda yanda zasuyi da rayuwarsu.
Kukan Benazir ya taba zuciyarta sosai kusan saida idanuwanta suka ciko da hawayen itama dan haka Cikin tausayi da baqin cikin qaddarar itama ta ringa rarrashinta tareda yanke shawarar zaa cire cikin kawai kokuma dole Alh Bilal ya fito fili a yi maganar aure tin kafin maganar cikin ta bayyana.
A gaban Benazir Ms aysha ta kira Bilal sukai magana sosai ta nuna masa damuwar dasu Benazir suke ciki.
Kai tsaye kasa amincewa yayi da cire cikin sbd hadarinsa da cutatarwa ga Sumayyah zatayi yawa.
Bai taba jin karfin soyayyar data danne tsananin tsoro da shakkar dd babba da dad kaante ba sai a yanzu dayake jin zai iya daukan hukuncinsu dana familyn kaantes gabaki daya akan sumayyah.
Kaman yanda Benazir da Anne suke neman mafitar lamarin Ms aysha da Alh Bilal din sun musu alqawarin yana dawowa zai nema auren Sumayyah batareda Ababa yasan da maganar cikin ba hakama duk dukiyar dayakeso yayi alqawarin basa dan ya basa auren sumayyah din.
Wannan alqawarin yasa Benazir daurewa ta tsaya makaranta bayan Ms aysha tayi mata alqawarin tsaya musu har qarshen rayuwarta insha Allah.
Ana tashi makaranta ms aysha ce ta dauketa ranar da kanta ta kaita gida kuma cikin saa Ababa bayanan hakama hande tana baccin ranar data saba dan haka har cikin dakinsu dayasa ms ayshan zubda hawaye suka shiga ta duba sumayyah tareda yiwa Anne Alqawarin zata kula dasu Benazir kaman yayan data haifa a cikinta da yardar Allah.
Kudi ta basu amma tashin hankalin dasuka shiga ma na ganin kudin yasata maidawa jaka ba shiri sbd tsoron kudin. Tanaji tana gani ta tafi batareda bar musu komaiba sbd sunqi karban kudin.
Tana ficewa Hande ta tashi data fito ta ringa mitar qamshin tiraren manya take jin ya cika gidan koina.
Shi kansa Ababa daya dawo saida ya tsinci qamshin musamman dakinsu dan haka aka bincike kayansu tsaf baa ga komai ba dole aka hakura sedai saka idanun da akai akansu sosai sbd sam hande ta kasa yarda dasu a kwanakin.
Benazir dole ta koma makaranta kullum tana zuwa Sumayyah dai dole aka hakura saita warke tukuna.
Kullum idan taje sai tayi magana da Alh bilal din a waya yaji ya jikin Sumayyah ta fada masa da sauki ta wuce karatunta. #MAMUH# #BENA#DD#ZAFIN KAI#
ZAFAFA BIYAR🔥
-ZAFIN KAI Mamuhgee
-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma
-FURAR DANKO Billyn Abdul
-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo
Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400
Pay at 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim
Send your Shedan biya Anan👇 09032345899
MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇 09033181070
Yan Nijar kuma ga inda zaku biya👇👇👇
+22799643131
Zafafa🫶🔥🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 21 Taka tsantsan suka hau yi da duk wani abin da zai saka a fahimci halinda sike ciki komai qanqantar kuskure kiyayesa sukeyi, Sumayyar ita kanta dole ta ringa tilasta kanta tana nemo kuzari da qarfin hali tana fitowa wasu ayyukan sbd saka idon Hande akansu yayi yawa.
Benazir ma datake zuwa makaranta tini sukaiwa kansu fada komai na Alh bilal harma dana ms aysha sun dena karba duk tsananin yunwa da rashin lafiya sun dena karban abincinsa da maganin dasuke fitowa daga garesa duk da bak dawo din ba kawo musu akeyi makaranta amma sam Benazir ta dena karba.
Saida suka share sati kusan uku suna fama da jikin Sumayyahn kafin ta fara fita makaranta.
Annensu duk suka fita harsu dawo hankalinta baya jikinta sai taga dawowarsu sbd yanzu tsoron mutanen waje ma takeyi, Benazir yanzu takeji duk da tasan ita tanada kame kai da hankali fiyeda yayarta Sumayyah din duk da ba dubararka bace tsarewar Allah ce.
Ita kanta Sumayyah tinda ta dawo makarantar take cikin damuwa da tsarguwa tareda kunyar dagowa ta kalli mutane sbd kunyar abinda yake jikin nata ganin takeyi kaman zaa ganeta.
Dan haka rayuwar makarantar ta zamar mata kaman wani sabon qunci da damuwa dan kuwa gabaki daya a muzance take cikin mutane,
Mummunan hali ta samu kanta aciki wanda ya saka rayuwar makarantar da karatun ficewa kanta gaba daya, Tamkar mujiya haka ta koma acikin mutane, Tin tana daurewa har takasa damuwa da qunci yayi mata yawa dole ta dena shiga mutane kwata kwata sbd itama ciwonta dake neman dawowa.
Hankalin Benazir tashi yayi ya rabu biyu akan karatunta da kuma Sumayyah din musamman yanzu dayake tana daukeda lalurar juna biyu.
Daga ita har sumayyar karatun acikin kwanaki kalilan neman lalace musu yakeyi ga jikin Sumayyah din ciwo yau gobe lafiya tin suna iya controlling abin suna boyewa har hande tagane sumayyah dai dale akwai abinda yake damunta bayan malaria da sukace.
Ana cikin wannan matsuwar da tashin hankalin sukai exam wadda daga Benazir din har sumayyahn babu wanda ya iya karatu bare rubuta abin arziki.
Ranar da suka gama exams wani babban tashin hankali ya samesu na rasuwar mijin Ms ayshansu wadda a ranar ta bar garin zuwa jos garin mijinta inda acan zaayi janaizarsa.
Wannan babban sabon tashin hankalin yasanya jikin Sumayyah rikicewa gabaki daya sbd ms aysha itace gata da mafitarsu dasuke gani itama ta tafi ta barsu.
A ranar sabon tashin hankalin kwanan zaune sukai duka su ukun babu wanda ya rintsa sbd a yanzu kam babu mafita sai wadda ubangiji zai sake aiko musu kokuwa dai qaddarar ce dai ahakan tazo musu.
Wannan karan kukan da Benazir tayi yafi na kowannensu tashin hankali da taba zuciya sbd itace take iya hango kowannensu ciwonsa dap yake da tashi wanda tasan suna juyewa shikenan ita kadai zaa bari da dawainiya da wannan quncin da radadin wanda daqyar itama wannan karan idan bata samu mental problem dinba, Ya zasuyi da cikin sumyayyah? Zatayi da babyn idan aka haifa? Me zata fadawa ababa? Me duniya zata fada akan babyn? Tayaya takeda tabbacin Alh bilal zai waiwayesu? Innalillahi wainna ilayhi rajiun.
Kuka tayi sosai wanda ya saka jikin Sumayyah da Anne sanyi dan kuwa sunsan ko a gurin azabar idan zasusha nata zai fi yawa sbd itace mai lafiyar da zatafisu jin radadi da ciwo tareda qunci mai yawa.
Sai dataji hawayenta har sun qafe idanuwanta ko buduwa basayi sosai ta dena kukan ta kallesu cikin tausayawa sbd a yanzu ta rungumi qaddarar cikin lafiyarsu da abinda zai samesu idan suka rasa hankalinsu take ji yana cin zuciyarta.
Tausayin tausayi akeyi tsakaninsu Su suna tausayinta ita kuma tana tausayinsu da babyn da zaa haifa wanda zai taso cikin uquba da masifar da uwarsu ta taso aciki suma suka taso aciki.
Abincin dare ta fito ta dora tana gamawa tayi sallah ta fito ta hau wankin hande.
Sai goma da mintina hamshin ta shigo dakin ta tadda Annensu zaune tayi shiru tareda nisa cikin tinani idanuwanta na kan sumayyah wadda baccin wahala da dole ya fizgeta.
Qarasowa tayi ta zauna gefen Anne tareda zamewa ta kwanta tana yiwa Annen saida safe cikin dasashiyar murya.
Har kusan asuba Annensu bata rintsa ba tana zaune cikin nisa a tinaninda batama san me take tinanawarba, Ita kanta Benazir har kusan asubar batai bacci ba sai daga baya ya dan dauketa bata jimawa akai kiran asuba ta farka ta fito.
Tare sukai sallar asuba dukkaninsu Suna gamawa Anne da Benazir suka fito Itama sumayyar daga baya biyosu tayi suka fara aikin gaba dayansu.
Sai 11 suka dan samu saukin aiki suka zauna suka ci abinci Ko tashi gurin basu yiba amai ya subucewa Sumayyah mai qarfi sbd cikinta daya kasa karban abincin da suka cin.
Amai takeyi mai qarfi da sauti wanda yasa dukkaninsu miqewa suna rarraba ido, Hande kuwa da sauri tayo dakin tana tambayarsu aman lafiya ne kuwa?
Shiru sukai tayita maganarta ta gaji ta tafi kafin Anne ta wuce da sumayyan dan tayata wanke jiki Benazir kuwa gyaran gurin tahau yi ta kwashe ta wanke gurin fes da omo me qamshin ta goge.
Acan koda Anne ta wanke jikin Sumayyahn zazzabi da ciwon ciki mai qarfi ya rufeta saida Benazir tazo suka kamata suka kai daki Take ta juye cikin ciwo mai tsanan koina nata jijjiga yakeyi.
Anne ta zauna da ita Benazir ta fita ta qarasa aikin tareda girkin rana tana gamawa suka zauna kan sumayyar wadda take cire rai da rayuwa.
Haka suka wuni da ita a daki cikin damuwa da mutuwar jiki Haka kuma suka kwana da ita.
Washe gari ma haka suka kima wuni da ita jikin ba dadi sam sai addua ba wanda ya kulasu Hande ma ido ta kawo ta saka musu sbd tasan ko zasu mutu Ababa bazai saka kudinsa yakaita asibiti ba dan haka ba ruwanta tinda ba lafiyar zata basu ba bazata iya yawon sanni ba.
********acikin sati biyu sumayyah gabaki daya ta koma kaman mai ciwon qanjamau sbd rama da rashin kuzari, Ciwonta yaqi sauki sam kullum haka suke fama da ita,
Benazir da Anne ma kaman masu qanjamau din suma dan itace take ciwon amma ramar da zabgewar dukansu ne sukai babu me dubuwa acikinsu banbancinsu da ita kawai ita cikin ne yake ajikinta amma duk damuwa da kuncin daidai yake a zikatansu.
Har lokacin babu labarin ms aysha hakama ba na Alh bilal, A kullum yanzu sallamar ababa da tarinsa tashin hankalin na fits hayyaci yake sakasu sbd sunsan yau da gobe bata barin komai.
Babban sabon tashin hankalin dasuka shiga shine fara bullowar cikin, Ciki dai ya bullo bazai boyu ba, Fitowa tsakar gida yanzu kam ya gagari sumayyah indai da rana tsaka ne sbd kada hande tagani ta sanar da ababa.
Idan sun lissafa daidai watan cikin uku kenan ake magana.
Ajiyar zuciya tareda numfashi mai zafi Anne ta sake tana kallan sumayyah da benazir ke cirewa farce sbd tsayi da sukayi da wata tsohuwar rezarsu da suka siyo kwanaki a hanyar makaranta.
Sanyi jikin Annen ya sake dauka suma sanyi jikinsu yayi ganin irin kallan da Anne ke musu cikin sarewa da sadaqarwa.
Ajiye rezar hannunta benazir tayi tana dafa hannun sumayyah daya dauki rawa ganin Annensu datake sake tsinkar dasu.
A hankali anne ta bude baki cikin sanyi tace
"Ya zamuyi da cikin nan na sumayyah daya fara bayyana?" Kunsan cewan daga wannan watan cikin nan bazai taba boyuwaba, Tayaya zaa hana hande da Ababa ganinsa,innalillahi wainna ilayhi rajiun" tafada cikin fidda rai daba dukkanin sauki.
Sunyi kukan har hawayensu ya dena fita dan haka idanuwansu sukai jajir Benazir ta dago ta kalli Anne zatayi magana idanuwanta ya sauka kan hande dake gefen dakinsu tsaye tayi mutuwar tsaye tsaban tashin hankali da firgicin abinda kunnuwanta suka jiyo mata "Ciki a jikin sumayyah kuma"?
Miqewa tsaye dukkaninsu sukayi cikin firgici da tashin hankali mai girma suna kallan handen.
Sai data share mintina kusan shifa a qame kafin ta iya motsawa ta rufe idanuwanta ta bude ta sake taba kirjinta taji zuciyarta na bugawa daidai bata sume ba,
Tsikar jikinta je suka miqe gabaki daya sbd tsoro dan kuwa ita kanta tsoron maganar shigarta tayi tinanin idan ababa kawai yaji zancen.
Babu wanda ya motsa acikinsu tsaban tashin hankali da tsoron yau ranar da suke tsoro tazo.
Qafafuwan hande na rawa ta qaraso cikin dakin tana kallan sumayyah da cikinta yake bayyane dan qarami a jikinta Bakinta ya dauki rawa da yankewar kalma tace
"Cikin haihuwa a jikin sumayyah, Ciki dai ciki dai na 'dan mutum,Qalu innalillahi wainna ilayhi rajiun, Benazir,Benazir yanzu daman cikin mutum ne ajikin sumayyah kuke boyo? Meya kaiku? Wace qaddarar ce wannan? Uban waye yayi mata cikin? A in? Aljanun hauka ne suka shigeku duk ku dukan ko me? Cabdijam,babbar magana,attt.
Babu wanda ya iya magana acikinsu sbd dai rana ta riga ta baci ba gyara.
Janyo sumayyah hande tayi da qarfi tana qara kallanta cikin kunya da baqin ciki da takaici tareda mamakinsu.
Numfashi ga koma saukewa sbd bata da bakin magana lamarin ya shallake tinaninta.
Fitowa tayi dakin a rikice ta zube tsakar gida tana sake sauke numfashi a jere sbd ita kanta kwatanta tashin hankalin da zaayi a gidan kawai tayar mata da tsikan jiki yakeyi.
Duk bayan sakanni sai ta sauke numfashi mai zafi tana kallan kofar dakin nasu dasuka kasa fitowa kaman yanda kowannensu wuta ta dauke masa babu me iya magana.
Kaman masu jiran sakamako haka suka kasa ko zaunawa dukkaninsu suna a tsaye har akai magrib sukai sallah babu wanda zuciyarsa ke harbawa daidai har handen itama ranar tana idar da Sallah ta fito tsakar gidan ta dasa kejera ta zauna jiran dawowar ababa. #MAMUH# #MARRIAGE# #LOVE#HOT#LITTLE BENAZIR AMNAH KAANTE#DD KAANTE#ZAFIN KAI
ZAFAFA BIYAR🔥
-ZAFIN KAI Mamuhgee
-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma
-FURAR DANKO Billyn Abdul
-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo
Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400
Pay at 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim
Send your Shedan biya Anan👇 09032345899
MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇 09033181070
Yan Nijar kuma ga inda zaku biya👇👇👇
+22799643131
Zafafa🫶🔥🔥
22
*_Arewabooks@Mamuhgee22_*
Dagowa Anne tayi ta kalli Benazir da sumayyah tsawon mintina tana rasa tinanin kamawa kafin ta tsaida tinaninta akan Sumayyah dake dauke da juna biyun zatafisu zama cikin hadari idan suka fara cin dukan azaba.
Benazir ma tinaninta akan Sumayyah dake dauke da cikin yake sbd tsoron hadarin da zata iya shiga idan Ababa ya kasa controlling kansa.
Suna nan zaune akai sallar ishai suka miqe sukayi ba jira sbd basu sani ba ko idan ababa ya dawo zasu samu lafiya ko kuzarin yi din.
Hande ma miqewa tayi ta shiga dakinta tayo sallar
Tana gamawa ta sake fitowa ta zauna tana hadiye wani yawun tsinkewa sbd itama tasan tau balain sai Allah idan ba har akanta zaa dora laifinba tinda itace ya barwa saka musu ido akan kowane motsinsu ta sanar dashi halin dasuke ciki
Amma ace har sumayyah tayi gogewar sani wani namijin har yayi mata ciki bata fahimta ba kuma da alama ba fyade akai mata ba da bazasu boye ba kuma da tini Ababan ya qaddamarwa wanda yayi fyaden ko dan uban waye gashi ciki yanzu ya dauko hanyar girma suna gida daya basuda labari,
Ababa kafin tashin masifarsa mamaki ma kawai ya isa ya kashe masa jiki shi kansa.
Qarfe tara saura mintina shida Ababa ya turo kofar gidan ya shigo yana amsa waya hannunsa riqe da ledar lemu daya siyo zai sha.
Ganin hande zaune tsakar gidan tana kallansa tana masa barka da dawowa yasashi taqaita wayar yayi sallama ya kashe yana saka wayar aljihunsa yana amsa barkan datake masa yana gaidata itama.
Satar kallan dakinsu Benazir tayi tana jin shakkar fada masa itama sedai kuma dole ya sani dan idan bata fada ba ciki dai baya boyuwa
Ranar daya gansa da kansa idan ya qara girma kilan wuta zai cinnawa gidan ya kona su duka.
Shima dakin nasu ya kalla tareda bude baki ya daga murya ya kira sunan Sumayyah.
Lokaci daya a tare gabaki dayansu har Hande kansu yayi mummunan sarawa tareda bugawar zuciyar data kusa sakawa hande hearts attack sbd bata saba da wannan tashin hankalin tsoro da fargabar ba.
Su kuwa acan daki take jini ya tsinkewa Sumayyah mummunan bugawar da zuciyarta tayi tareda sarawar kai mai qarfi.
Benazir da Anne ma kusan kowannensu daqyar ya samu yawun hadiyewa sbd makoshinsu daya bushe take qam hakama yawun sun kafe basu ma ankara da jinin daya fara zubowa sumayyah ba wadda itama bata tsars lura da jinin ba sbd zuciyarta data tsinke.
Cikin mamakin rashin amsawarta da fitowarta ya juyo ya kalli Hande wadda ta kasa kallansa tana dan dauke kanta zuciyarta na sake shiga wasi wasin fada masa.
Kallan kofar dakin yayi yana matse fuska ya sake qwala kiran sunan sumayyar.
Daqyar da wani irin mummunan yanayi ta iya bude baki ta amsa kiran nasa tareda miqewa tsaye qafafunta na rawa ta nufi kofar
Sai alokacin su Benazir sukaga jini a kayanta da sauri Anne ta miqe tayi gaba Benazir ta tsaya bayanta suka sakata tsakiya sbd dare ne duk da akwai wutar nepa amma idan suka dan kakkare ba lallai yaga cikin ba harma da jinin sbd ba hijab jikinta tinda basu saba zama da hijab cikin gidanba sbd basuda sitira da yawa shiyasa suke lallaba wainda sike da.
Yanda suka jero masa kaman kashin awaki yasashi tsayawa da kyau yana kallansu cikin sake tsuke fuska da mamakin sabon salon nasu na samun guri.
Sun zuwa suka tsaya gabansa dukkansu kansu a qasa
Anne ce kawai ta dan kallesa tayi masa sannu da zuwa cikin girmamawa kafin suma cikin girmamawa mai tsanani sukai masa barka da dawowa.
Ledar hannunsa ya miqawa sumayyah yana cewa
"Ki gyaro lemu ne ki kawomin banason manyan yanka kuma kin sani......Maganarsa yankewa tayi ganin yanda hannuwanta ke tsananin rawa gurin karban ledar.
Janye ledar yayi yana kallan hannuwanta dasuka sake rikicewa da tsananta rawa,
Fuskarta ya maida kallansa fuskarsa na sauyawa da mamaki yaga fuskarta na hada wani irin gumi da kasa motsa idanuwanta dan kada su dago.
Kan Anne ya maida idanuwanta yana kallanta itama zufan take cikinsa sharkaf hakama hannuwanta rawa sukeyi harma da qafafunta.
Juyar da kallan yayi kan Benazir datake a kame batai gumin ba amma yanda kirjinta ke bugawa yana iya gani da kuma yanda takasa dogowar itama.
Wani numfashi mai zafi ya sauke bayan ya gama karance yanayinsu duka
Ya dawo da kallansa kan hande zaiyi magana yaga itama a jiqe take da zufan yau itama takasa dagowa ta kallesa da kyau.
Sake kallan kowa yayi acikinsu daya bayan daya
Gurin yayi tsit ko sautin numfashinsu baka ji
gyara tsayuwa yayi a hankali,
"Meyake faruwa zaa fadamun yanzu nan"...sukaji saukar muryarsa kai tsaye.
Idanuwansa akan Hande suke sbd daga bakinta yake buqatan ji menene dayasa take hada zufa itama.
Kallansa hande tayi kafin ta kalli sumayyah data riga ta saddaqar su dikan ma sun saddaqar din.
Maimaita tambayarsa yayi hakurinsa na qarewa sbd tini kansa ya fara daukan zafi.
Wani nannauyan numfashi hande ta sauke tareda kallan sumayyah a karo na farko dataji tausayinsu ya dan saukan mata a rai sbd tasan suma duk yanda akai mummunan kaddarar samunsu tayi bada son ransu sbd yanda suke tsoro da kiyaye dokokin Ababa bazasu taba irin wannan aikin da ganganba.
Muryarta ba qarfi da kuzari ta bude baki tace
"Ciki ne a jikin sumayyah gashinan harya fito".
Shiru gurin ya sake dauka wanda wannan karan har dashi Ababan ya dauke wutar ba zata sbd saukan zancen kaman tsawa me qarfi haka ya jisa.