Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 21
Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 21: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 21. Kukan dasuke Yi a kanta kaman ransu zai…
3,370 words
Kukan dasuke Yi a kanta kaman ransu zai fita yasa Ababa kasa riqe Kansa yaje jikinsa na rawa ko gabansa baya Gani ya dauko wayarsa ko ganin numbers daidai bayayi ya Nemo sunan Bilal ya saka kiransa.
Bilal dake zaune gaban ummensa Yana Jin zuciyarsa na tsinkewa Tin safiyar yau din sai yanajin Hakan damuwar yanda zai iya sanar da mahaifiyarsa da 'dan uwansa Abinda yake faruwa na qaruwar haihuwar da zai samu ta qaddara.
Ummensa da itama tata zuciyar ke tsinkewa tinda suka shigo kaantes kallan Bilal tayi tana sake Jin jikinta na mutuwa ta riqo hannunsa tana Kiran sunansa ahankali tace,
"Bilal....kafin tayi magana wayarsa tayi ringing Ya saka hannu cikin aljihunsa jiki a mace Shima ya Ciro wayar Yana dagowa yaga sunan Ababa take gabansa ya Fadi jikinsa ya sake mutuwa.
Kallan ummensa yayi yaga itama shi take Kallo jikinta a mace.
Wayar ya dauka tareda Dan janyewa daga gabanta.
Murya na rawa hankali tashe Ababa yace
"Kayi sauri kazo yanzu da gaggawa Sumayyah da Abinda yake cikinta na cikin mummunan hadari tin jiya take nakuda ba haihuwa har.....
Bai qarasa ba Bilal ya katsesa hankalinsa a matiqar tashe jikinsa na daukan rawa yace
"Meyasa ba'a kirani ba tin jiyan? An kaita Asibiti ne? Ganinan zuwa yanzu.
Kashe wayar yayi ya juyo ya nufi kofa zai fice Umme tayi saurin riqesa hannuwanta na rawa a tsorace tace
"Waye ne? Waye Kuma ba lafiya? Meyake faruwa ne? Ina zakaje?
Kasa amsawa yayi sbd hankalinsa Daya matiqar tashi Kasa magana yayi idanuwansa na sauyawa da tsoron Daya kasa nutsuwa dashi.
Sake jero masa tambayoyin Umme ke kokarin Yi Amma Bai gama ji ba yayi gaba Yana sake saka Kiran Ababan yaji a gida suke ko asibiti Amma yakasa samunsa sbd Ababan Yana can ya kira dd babba ganin Bilal baigama sauraronsa ba ya kashe wayar.
Dd babba dake zaune a palonsa na alfarma suna magana da DD da dad kaante Kiran Ababan ya shigo wayarsa yaqi dauka.
Bai gama dauke idonsa daga kan wayar ba Wani Kiran ya sake shigowa kaman bazai dauka ba Amma tinanin zai iya Kiran Bilal ya fada masa Kuma Bilal din zuwa zaiyi a samu matsala idan Wani ya gansa can Dan haka ya dauki wayar a natse ya daga Kiran.
Ababan Bai iya tsayawa ko sallama ba a rikice yace
"Alh babba 'yata mutuwa zatayi daga ita har Abinda yake cikin nata nakira Alh Bilal nafara magana ya kashe wayar,kunce idan haihuwa tazo a sanar ma...
Shima Bai qarasa ba dd babba ya katse Kiran hankalinsa na tashi ya miqe Dan tsayar da Bilal Dan kuwa matiqar Ababa ya kira Bilal to kuwa babu Abinda zai hanasa zuwa saidai komai ya faru Dan haka Bai tsaya Bata lokaci ba ya miqe da Kansa ya nufi kofa Yana saka Kiran wayar Bilal Wanda harya shiga mota.
Daga DD har dad kaante bayan dd babba suka biyo cikin mamakin meya daga masa hankali ya fice haka cikin sauri da bacin Rai. #MAMUH# #DD KAANTE #BENA #AMNAH #ZAFIN KAI #MAMUHGEE
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 36 Bilal Yana fitowa daga part din su Umme harabar gidan ya nufa Yana Ciro keys na motarsa duka hannuwansa na rawa,
Tashin hankalinsa da ficewa hayyacinsa akan Abinda yake tsoran Ababa zai iya Yi har sumayyah da Abinda yake cikinta su samu matsala duka Dan haka bazai taba tsayawaba anan tanacan tana fama tsakanin Rai da mutuwa.
Ummensa hankali tashe ta biyo bayansa tana son sanin meya faru sbd Bata taba ganin 'danta me sanyi da nutsuwa ba acikin wannan mummunan yanayin Dan haka ta biyosa tana Kiran sunansa hankali tashe Wanda yayi daidai da fitowar su dd babba Suma Yana Kiran Bilal din cikin karaji da babban sautin daya tabbatarwa dasu dad kaante ba lafiya ba akwai babban lamarin Dayake faruwa.
Bilal a Karo na farko rayuwarsa Daya take umarni da Kiran dd babba ya fada motarsa tareda tayarwa da Wani mugun ribas ya nufi gate ko Gani bayayi sosai.
Dd babba cikin tsananin bacin Rai da fushi ya daga murya yace securities kada su budewa Bilal din gate
Sunajin haka take suka Maida gate din suka rife gashi yariga ya kawo Dan haka motarsa ta daki gate din Amma Bai tsaya ba kokarin sake yin gaba yayi ribas yakeyi ya sake dukan gate din Amma kafin yayi Wani yunquri DD ya iso gefen motar ya Bude ya zare key din Yana kallansa da idanuwansa dasuke masa kallan mamaki Mai tsanani Yana Jin da akwai babban lamarin dake faruwa da 'dan uwan nasa.
Umme ta Riga dd babba isowa ga Bilal din hankalinta tashe hannuwanta na rawa ta fito dashi motar tana kallansa zatayi magana dd babba dashima ransa yagama mummunan Baci Yana zuwa ya dauke Bilal din da Wani lafiyayyan Marin Daya saka Bilal din dawowa hayyacinsa ya sauke Kansa hawaye masu dumi suna gangaro masa da tsananin damuwa da baqin cikin rashin darajarsa takai a saka masa hannu duk girman shekarunsa masu yawa.
Saukan Marin dd babba akan fuskar Bilal yasaka DD da Umme da dad kaante harma da securities shiga mummunan tashin hankali da tsoro.
Umme hannuwanta na rawa tana son kamo sa Amma bacin ran dd ya saka kowa kasa motsawa.
Kaman daga sama muryar DD Mai sanyi da nutsuwa a kame yace
"Me yake faruwa ne anan?" Akwai Abinda ya kamata mu sani ne?
Bilal ya kalla Wanda hawaye yakeyi sosai kaman karamin yaro Amma yakasa dago Kansa, Yau na Daya daga cikin ranakun da bazai taba mantawaba a matsayinsa na me amsa sunan kaantes.
DD Maida kallansa kan dd babba da ransa ya gama Baci yayi kafin suyi Wani yunquri Umme ta riqo hannun 'dan zasuyi ciki idanuwanta na cikowa da hawaye sosai itama.
A fusace dd ya Kalli Abbakar yace ya Bada umarni na doka Mai tsananin gaske kada a budewa Bilal gate ya fita gidan Bada izininsa ba
Da sauri Abbakar ya nufi gate Dan isar da sakon ga securities na gidan gabaki Daya.
Kiran Ababa ne ya sake shigowa wayar Bilal wannan Karan Umme ce ta karbe wayar tana kallan sunan me kira kafin tayi yunqurin dauka Bilal din ya amsa ya daga kafin ya iya Bude baki yayi magana Ababa Daya kusa haukacewa sbd tashin hankali kukan da benazir keyi cikin mafi girman tashin hankali kawai ya karawa Bilal din take ya tsaya cak tareda rintse idanuwansa dasukai jajir sbd masifaffen tashin hankali ya kashe wayar tareda juyowa kawai ya zube gaban dd babba Kansa a qasa cikin qunci da Wani irin 'daci Mai tsanani na zuciya muryarsa na danne halinda zuciyarsa ke ciki yace
"Nayi alqawarin bazan taba barin kowa ya Ganni a gurinsu ba Amma Dan Allah ka bani izinin zuwa nakaisu asibiti.
Rintse idanuwa dd babba yayi sbd dai anzo gabar da dole dadynsa da mahaifiyarsa da DD su San Abinda yake faruwa tinda hakan ta faru gabansu.
Kallansa dd babba yayi Kai tsaye yace baka buqatan zuwa zaa aika driver yakaisu Asibiti idan ta haihu anfasa Kai auren Wani wata satin Nan zaa daura auren qasar zaka bari gabaki Daya ba yanzu zaku dawo ba sai ranar danace.
Kallan dad kaante yayi cikin bacin Rai Mai tsananin gaske da Bai samu ya fidda ba tin ranarda maganar cikin ta bayyana sai yau din yace
"Yarinyar da zaa daura masa aure da ita ciki ne da ita Kuma nasa haihuwa zatayi a yau din, Ku sheda matiqar yabar cikin gidan Nan wlh karya dawo ya hada komai nasa daga can wata qasar zai tafi bazai taba dawowaba, Wannan shine umarnina.
Yana gama fadar Hakan ya bar gurin ransa a bace yabar su dad da Umme da mutuwar tsaye zuciyoyinsu na sanqarewa.
Dad kaante mamakin kusan illata masa numfashi yaso Yi Saida Abbakar ya kamasa da sauri sukai ciki baya ganin gabansa sosai sbd jininsa ya hau Nan take Yana buqatan likita da gaggawa Shima.
Umme ma kusan Yanke jikin tayi zata Fadi DD da Bilal din sukai saurin tarota a tare sukayo ciki da ita zuwa lokacin itama tafara ganin dishi dishi take jininta itama yake Neman hayewa Dayake tanada asthma take taso mata sbd numfashinta Daya tsaya cak na wucin gadi.
Rikicewa jikin ummen yayi kaman kiftawar Ido Dan haka hankalinsu ya tashi musamman Bilal Dayake ganin shine sila.
Likitan gaggawa aka kira Wanda yasaka familyn kaantes din ankara da tashin hankalin da ake ciki Abinda dd babba ya gudara sai gashi ya bayyana Amma a iya familyn.
Ummensu a cikin Abinda Bai gasa awa uku ba ta koma kalan tausayi Amma a hakan ta riqe hannun Bilal tana son Kuka Amma ta kasa tace ya fada mata gskia.
Sunkuyar da Kai yayi cikeda kunyarta data DD dake rungume da ita dayan gefen saidai Kuma bazai iya mata karya ba kokuma gyaran zance Dan haka cikin sanyin jiki da damuwa ya sanar dasu irin tsananin son dayakewa Yarinyar, Itace farin cikin Daya rasa tin tasowarsa, Kuma Bai taba Jin sonta ya sauyaba a ransa duk da Abinda ya faru tsakaninsu, Yana sonta tsakaninsa da Allah fiyeda yanda yake son komai nasa, Idan zaa barsa ya tafi yayi rayuwarsa da ita ya yarda aturasa kowace qasar ce abarsa da ita.
Maganganunsa suka Sanya Umme da DD yin shiru suna sauraronsa,
Bilal bamai hayaniya da son maganganu bane, Baka Gane Abinda yake ransa duk tsanani sbd ya iya binne komai cikin ransa Amma ayau Bilal Yana bayyanarda soyayyarsa ga macenda Allah ya qaddaro masa haduwa da ita, Wane irin so ne wannan Daya sanyashi yakejin zai iya zabarta yabar ahalinsa.
Umme kuwa Kuka ta fashe dashi a hankali tana girgiza tareda riqe hannunsa gam tace
"Karka tafi ka barni bazan iya rayuwa babu Kai ba, Karka zabi barina ka tafi, Kabi umarnin dd babba ka bari ta haihu a daura Muku auren zan karbeta hannu biyu nayi Maka alqawari Amma Dan Allah kada ka karya umarninsa a rabani dakai.
Shiru yayi batareda ya iya cewa komaiba sbd maganganun ummen kashe masa jiki suke Yi Dan ita da sumayyah sune mata biyu dayafi so fiyeda komai a rayuwarsa.
Yanda take rokonsa gata batada karfi ko kadan jikinta yasa DD janyota daga hannuwan Bilal data riqe Yana kokarin Kwantar mata da hankali sbd numfashinta ya far sake kokarin daukewa Yana fizgowa.
Juyawa Bilal yayi yabar dakin sbd baya iya kallan idanuwan ummen tasa Dan damuwa da rashin sanin mafita da zabi.
Kai tsaye Bai saduda ba sbd yanajin sumayyah na tsananin buqatansa ayanzu Dan haka ya sake komawa sashen dd babba Dan rokonsa.
jiki ba qwari yana hada hanya ya Isa kofar palon zai shiga ya tadda kofar Bude Bata qararasa rufewa ba kunnuwansa suka Jiyo masa Abinda ya sanyashi Jin Wani mummunan jiri daukansa.
"Aje da mota akaisu asibiti tana haihuwa da ita da babyn da iyayenta a kaisu inda bazasu sake waiwayo Nan din ba, Abasu dukiyar da zata hanasu sake tinanin sunyi zama anan ma bare sanin sunan kaantes, Duka wannan bayan Angama da matsalar Mahaifin nata ta yanda baisan meyake ba bare ya Hana barinsu garin."
Abbakar ne yake wannan wayar a palon dd babba shikuma ddn bayama Palon.
Wannan umarni ne da dd babba Wanda yasaka ayi Bada sanin Bilal ba ta yanda zai nemeta ya rasa Kuma a satin yakeda niyar daura masa aure da 'yar babban gidan da yayi Niya.
Jin wannan mummunan zancen yasa Bilal kusan somewa a gurin Saida ya share mintina Bai iya motsawa ba sbd tashin hankali da firgici.
Tsoro ne ya kamasa na Abinda zaa iya Yi din Dan haka qafafunsa na rawa baya Gani ya nufi motarsa wannan Karan cikin saarsa Yana ta-da motar ana Bude gate motar DD da Naseer ya tuqo zata shigo gidan Bai tsaya jiran komai ba yayi gate Dina guje ya fice bayan motarsa data DD din sunyi kusan kaura har Saida goshinsa ya bugu ya Dan fashe Amma Bai tsayaba yahau titi a guje.
Daga securities har Abbakar da Naseer da sauran jamaan gidan dasuka fito a rikice Basu tadda ko kurar motarsa ba ya bace bat.
****** Bayan sallar magrib ne lokacin Kuma a daidai wannan lokacin sumayyah tayi haihuwar da baa so ta yagata.
Daga babyn har uwar babu me motsi a cikinsu sbd galabaituw mai tsanani da azaba.
A hannun benazir yar ta fado Dan haka jikinta na rawa ta rungume 'yar maqoshinta na bushewa tareda idanuwanta dake qafewa ganin sumayyah Bata motsaba bare numfasawa.
Anne ma hannuwanta rawa sukeyi idanuwanta na Neman dauke Gani sbd ganin sumayyah kwance idanuwanta a rufe ba alaman Rai a tareda ita ta Yanke cibiyar mahaifar ta fado ko ta kan komai Basu bi ba itada benazir a tare hannuwansu suka Isa jikin sumayyahn suka kira sunanta a tare kowannensu muryarsa na yankewa.
Ababa dayaji shiru sake fadowa dakin yayi Yana Jin tsoro da tashin hankali Shima ya Kalli sumayyahn yaganta kwance babu alamar Rai a tareda ita take yaji jiri ya debesa ya dafa bango Daidai Nan babyn ta saki Wani irin kukan jarirai Mai karfin gaske tana motsawa da karfi cikin jikin benazir Datake a dunkule.
Kukan babyn yasaka Ababa kallan benazir da sauri muryarsa na yankewa da tsinkewa yace
"Ta haihu kafin ta rasu ne?"
Wannan Kalmar tasa ta saka Benazir da Anne tsayar da hannuwansu daga kokarin sake taba sumayyahn dasuke hannuwan Anne suka fara Wani irin rawa suna jijjigawa numfashinta na Neman tsayawa.
Benazir kuwa ganinta da jinta ne ya dauke take saidai taji Ababa Yana cire 'yar daga jikinta Amma Bata ganinsa Bata jinsa hakama Bata iya motsa ko Dan yatsanta.
Hande dake dakinta tana sallar ishai ya Kaiwa 'yar harya tuntube Dan tayi mata wanka.
Yana fitowa dakin hande dawowa yayi gurinsu benazir din zaiyi magana yaga gabaki dayansu Suma kaman sun mutu daga inda kowannensu yake zaune Gabansa yayi mummunan faduwa Dan haka ya fito dakin da sauri Dan dauko fitilarsa ta Mai tsananin haske sbd duhun dakin yayi yawa.
Yana fitowa Anne ta miqe tsaye ta fito dakin batasan Ina take jefa qafa ba ta nufi waje. #MAMUH# #ZAFIN KAI #BENAZIR ABABA #KAANTES *_Arewabooks@Mamuhgee_* 37 Ababa na dawowa dakin ya haska fitila yaga benazir zaune ta sankare da alama Bata hayyacinta ta zaunce ne a take da rasuwar sumayyahn.
Dayan gefen ya haska baiga Annensu ba, Kokarin haska dakin yafara koina babu alaman Annen Yana kokarin juyowa yaga kaman sumayyah ta motsa Amma Dayake tashin hankalinsa a yanzu kada Annen tabi hanya yasa ya fice dakin da sauri Yana kwala Kiran sunanta a rikice.
Hande da jaririyar ta isheta da kuka Jin ihun Ababan Yana Kiran Anne yasata fitowa daga daki a rikice rungume da 'yar acikin zanin uwarta.
Hankali tashe ya sanar da hande Annensu ta bi daji a Daren,
Hande cikin firgici tace
"Mun shiga uku da wannan qaddara, Daga mutuwa sai hauka ga Kuma jinjirar 'ya anbarni da ita a hannu wayyo Allah mun shiga uku.
Dakin su Annen ta fada ta fizgo Benazir dake riqe gam da hannun sumayyah suna fitowa tsakar gidan ta dungura mata 'yar tana fasa kukan sun shiga uku sun lalace 'danta ya hada iri da Anne me jinin Kaddara baqa iri iri.
Qanqame 'yar benazir tayi kaman sumayyahnta ce ta qanqame Ahankali take dawowa hayyacinta tafara Jin sama sama hande da Ababa na ihun Anne tabi daji haukanta ya tashi.
Fizgo tinaninta da hankalinta tayi da qyar tareda shiga girmamammen tashin hankali da masifar rayuwa.
Daqyar taji qafafuwanta a jikinta ta iya motsawa tafara jefa kafa koina ta samu ba nutsuwa ta nufi hanyar bangaren dabbobi Ababan dataga shi da hande sun nufa suna Kiran sunan Annen cikin mamakin ganinta zaune cikin dabbobi tana Kuka kaman ranta zai fita.
Benazir na hango Annen ta qaraso da tsananin gudu ta fada jikinta da babyn a hannu suka fasa Wani tsimamman kukan Daya taba zuciyar hande a Karo na farko.
Kuka sukeyi sosai hande da Ababa na kansu hande na fadan baa yiwa Mamaci Kuka,
Shi kuwa Ababa kokarin Ciro 'yar daga tsakiyarsu yakeyi kada a kashe masa ita Ta Daya bangaren baya hayyacinsa Shima kwata kwata sbd rasuwar sumayyahn Neman juyar masa da Kai takeyi,
Kakkarwa jikinsa yakeyi Yana hada gumi Mai tsananin yawa.
Rikosa hande tayi tana kokarin zaunar dashi sukaji motsi can cikin gidan da sauri hande ta sakesa Dan dubowa tana shigowa tsakar gidan bataga kowa ba.
Faduwa gabanta yayi ta waiwaya ta Kalli dakin su benazir saidai bazata iya leqawa ba tayi Ido biyu da gawa Dan haka take tsoro ya Dan shigeta ta juya zata koma Ababa ya iso Yana Neman zubewa qasa sbd jiri da bushewar yawun tashin hankali.
Dakin ta sake kalla tace masa
"A dakin Nan fa Akai motsin dazu fa, Kodai Bata rasu bane sumayy....Bata qarasa ba Ababa yayi Wani irin zabura ya fada dakin sbd tinawa da dazu kaman yaga motsawanta saidai Yana fadawa ya haska Kansa ya juye take sbd ganin wayam babu sumayyah a dakin koma me Rai koma gawarta.
Hande data biyo bayansa tana ganin babu gawar ta saki Wani gigitaccen salatin dayafi kama da ihun Daya saka Anne da benazir tasowa suka fado dakin gigice tinanin sumayyah ta tashi.
Ganin ba sumayyahn yasa benazir rarraba Ido a dakin tana Neman sake zaucewa.
Anne kuwa fadawa tayi inda sumayyahn take kwance tana lalubawa ko idonta ne Basa ganin gawan Sumayyah hannuwanta suji mata.
Sabon tashin hankalin da Basu saka masa rana bane suka samu kansu a ciki na rashin ganin sumayyah ace ta bace bat idan da Rai idan gawar.
Ababa da Kansa ya gama juyewa tsaf lokacin barin kayan gidan yafara yana Neman haukacewa ya dauko bindigarsa ya fito idanuwansa jajir baya ganin ko gabansa ya fita yafara duba zagayen da kewayan gidan da anguwar ko zai San wane balain da masifar ne ya samu Kansa,
Shin guduwa sumayyah tayi itama kokuwa sace gawarta Akai? To waye yasan da ita da halinda ake ciki da har zai shigo gidan ya sace gawarta.
Benazir da Anne kuwa zuwa lokacin Kuka ma Wani gata da arziki ne dayafi karfinsu, Kukan sukeson Yi Amma babu hawayen idanuwan sun bushe bayan kukan babyn Dayake cika gidan babu me iya ko motsi sbd girma da tashin hankalin lamarin.
A inda benazir take zaune cikin duhun dakin rungume da babyn da har lokacin Bata samu an mata wanka ba, Qamshin da hancinta ya shaqar mata ne ya sakata miqewa a zabure tana tabbatarda Alh Bilal ya shigo gidan.
Fitowa tayi daga dakin Anne ma ta biyota kaman zariya suka fara ware idanuwa a tsakar gidan cikin duhu Amma Basu ga kowa ko komai ba Dan haka Suka koma bakin kofar dakin suka rakube suna jiran dawowar Ababa da Koda gawar sumayyahn ne.
Shiru shiru babu Ababa babu labarin dawowarsa Yana can yabi hanya Baya hayyacinsa gurin Neman sumayyah ko gawarta, Tin yana yawon dubawa cikin anguwar harya fice anguwar Bai saniba kaman tsohon mahaukaci haka yakoma acikin tsakar Daren.
Hande dataji jaririyar ta kasa Dena Kuka Kuma makotan kusa zasu iya Jin kukan su San da haihuwar dole ta fito ta karbi yar ta shiga dakinta da ita acan tayo mata wanka ta saka mata kayan da Ababa ya siyo na haihuwar ta fito ta miqawa benazir ita ta sake komawa dakinta sbd sanyi illa zai mata da tsufanta.
Benazir da Anne kuwa suna tsakar gidan Basu motsaba ko Nan da can suna jiran dawowar Ababa zuciyoyinsu na Wani irin tsallan tashin hankali mara misali.
Babyn a cikin hijabi benazir ta sakata ta dunkule sbd sanyi tin tana Kuka har ta Dena tayi shiru tana baccinta da jarirai.
A rayuwarsu Basu taba shiga tashin hankali irin Daren ba, Yanda suka ga Rana haka sukaga Daren gurin Jiran tsammanin tashin hankali,
Kiran Asuba Akai aka gama har Akai sallah aka fito babu labarin Ababa Suma babu alaman zasu motsa har gari yayi haske tukuna Benazir taja Anne da babyn a dayan hannunta sukaje sukai sallah suka sake fitowa babu me iya ko tsayuwa a cikinsu sbd fargaba da tashin hankalin.
Karfe 6 na safe Ababa ya shigo gidan ko Gani bayayi Yana kawowa tsakar gidan ya yanke jiki ya Fadi.
Hande da gudu tayi Kansa tana fashewa da kuka
Benazir da Bata gansa da sumayyah ba itama sarewa qafafunta sukai ta zube a gurin durqushe tana Neman Kuka ya taho mata ko zata samu sassaucin Abinda take ji a cikin kirjinta.