Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 22

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 22

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 22: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 22. Anne kuwa a wannan lokacin Ido kawai ta…

3,315 words

Anne kuwa a wannan lokacin Ido kawai ta zubawa benazir tana kasa motsawa bare iyayin kukan itama.

*********A Kaantes ma a tsaye suka kwana kan ummensu Bilal data rikice gabaki Daya sbd zuciyarta Datake tsinkewa tana shiga tsoro da firgici akan 'danta.

Duka wayoyin Bilal din Basa shiga hakama ga ummen asthma ya tashi gabaki Daya kaman wadda ta jima tana jinya kiransa DD keyi Yana qarawa Amma Sam wayoyin Basa shiga.

Hakan yasaka dole DD a ranar ya kwana cikin KAANTES Bai tafi gidansa ba, Dad kaante ma hankalinsa yayi mummunan tashi shikuma dayaga baa samun Bilal din Kuma har tsakiyar dare har Asuba har safiya Bai dawoba Dan haka Suka Yanke shawarar Neman Ababa.

Zazzaune suke jigum jigum kaman gidan makoki a palon dd babba suna jiran dd babban ya kira Ababa Wanda shikuma aketa kira baya dauka.

Daga DD har dad kaante dashi Kansa dd babba harma ummensa zuwa lokacin hakurinsu yafara qarewa suna buqatan Jin komai gameda haihuwar da zuwan Bilal din dama Asibitin da suke.

Kokarin sake saka Kiran dd babba yayi daidai Nan wayar dad kaante tayi ringing cikin zaquwa ya daga Kiran ganin number sbd ko Bilal dinne Dan haka kawai wannan Karan suke Jin yanayi mara Dadi akan lamarin nasa.

A kunnensa ya Kara wayar tareda cewa hello da sallama.

Wani bayani aka fara Koro masa Daya sakasa yin shiru Yana kasa tanka kalma ko Daya sbd jinsa Daya fara daukewa kafin ganinsa.

Subucewa wayar hannunsa tayi yafara kokarin Kai hannunsa kirjinsa ya Dafe zuciyarsa Amma Bai karasa Kai hannunba ya Yanke jiki ya Fadi

Abbakar da DD sukai Kansa shi Kansa dd babba zuwa lokacin gab yake da samun attack Dan haka da sauri Abbakar ya dauki wayar dad kaante din ya miqawa Dd babba Amma ya girgiza masa alaman ya amsa wayar.

Cikin karfin hali da jarumta Abbakar ya gama sauraron bayanin da jamian tsaron suka gama jerowa ya kashe wayar zufa na tsinke masa sharkaf tareda tsananin tausayi da jimama harma da tashin hankali Amma Kuma ba dalilin boye zancen tinda dole aji,

Sauke Kansa yayi cikin raunin murya da tsananin bayyanarda damuwa yace

"Sir Bilal ne ya samu hadari motarsa ta Kone kurmus,Ansamu konanniyar gawarsa a m.....

Bai qarasa ba suka ji Wani irin Kukan Umme Daya saka kaantes din dauka tsit baka Jin motsin komai.

Mum Khadija ce matar qanin dad kaante dasuka iso gurin tare ta riqota jikinta na daukan rawa itama da mummunan labari tashin hankalin da babu wanda ya saka masa rana.

DD kuwa kasa gasgata Abinda aka fada din yayi sbd yanda jikinsa yake wata irin rawa idanuwansa dake farare masu tsananin kwarjini take sukai jajir ya fice palon da sauri ko gabansa baya Gani ya fito Ya nufi motarsa Naseer Dayake shigowa Yana hangosa ya taho da sauri ya Bude masa motar Bai tsaya cewa komai ba yace su nufi hanyar barin gari inda accident din ya afku.

Umme kuwa Wani irin Kuka takeyi Dayake tayarda tsikar jikin Masu jinta Dad kuwa tini Akai part dinsa dashi sbd likitocin da aka kirawo har biyu da zasu dubasa Dan take numfashinsa ya tsaya.

Dd babba ma zaune yake Amma duk ilahirin hannuwansa da kafafunsa rawa sukeyi, Zuciyarta tayi nauyi baya iya motsawa kowane lokaci attack zai iya samu Dan haka Shima take akai ciki dashi Dan jiran likita.

Zeenah dake Kuka sosai da mum Khadija harma da wasu daga masu aikin gidan suka kama Umme Akai ciki da ita, Bata taba saka ran mutuwar danta ce ta sanyashi fita yabar gida ba da bazata bari ya bar ko kofar part dinta ba, Irin Kukan datakeyi ne yasa mum Khadija fashewa da kukan tausayinta sbd kowa ya sheda soyayyar dakewa danta wadda ya kasa samu gurin kowa daga familynsa.

*****Koda DD ya Isa Shima Saida ambulance tazo ta daukesa daga gurin da hadarin ya faru sbd gawar Ta Kone kurmus ta yanda baa ganeta motarce kawai ake iya Ganewa itama sbd kafin konewar da alama ya daki Wani abin ne lambar motar ta fita harma da baya motar Shima ya balle ya fita.

Hakan yasa Akai saurin Ganewa aka kirasu sbd matsayinsu.

Rasuwar Bilal kaante a cikin Bata rufa awa biyu ba labarin ya bazu koina Aka fara kokarin saka lokacin janaiza, manyan mutane kuwa tini suka fara kira da Kuma fara Siyan tickets na zuwa gaisuwa da janaiza.

*****A lokacinda labarin rasuwar ya shiga kunnan Ababa a lokaci Daya shi da benazir wannan Karan suka Yanke jiki suka fadi sbd sani da tabbacin Data Basu na cewan Bilal ne ya dauke sumayyah.

Anne da zuciyarta ta qyame kyam a tsakanin Daren jiya zuwa safiyar itace ta zubawa benazir ruwa ta farfado itama tata zuciyar na qamewa tana tashi daga tsoka.

Ababa kuwa Yana farfadowa ya sake yanke jiki ya Fadi sbd ta tabbata sumayyah da Bilal sun mutu sun bar duniya. 38👇👇👇👇👇👇 ##MAMUH# #BENAZIR #ABABA #AMNAH #DD KAANTE #MARRIAGE/LOVE/ROMANCE

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 38 Benazir data kasa yadda da sumayyah ta tafi barsu rawa dukkanin jikinta rawa yakeyi ahankali tana kasa Jin hawaye ko Daya cikin idanuwanta, Bakinta da makoshinta Wani irin bushewa sukai tana kasa samun yawu ko kadan cikin bakin da moqoshinta.

Babyn dake jikinta ce ta motsa ahankali Hannuwanta dake rawa ahankali tasaka ta sake rungume 'yar tana sake Jin zuciyarsa, idanuwanta da bakinta na bushewa sbd su 'yar uwarsu,Rabin jikinsu suka rasa ita Kuma babyn uwa da ubanta ta rasa a lokaci Daya.

Ababa Da ake kokarin kwasa zuwa Asibiti Anne ta kalla da idanuwanta dasukai jajir Amma babu Wanda ya samu Kuka a cikinsu sbd basuda sauran Abinda suke ji a zuciyoyinsu dasuka sanqare,

Hande Kuka takeyi tana qarawa akan kada ta rasa 'danta, Mutane ta samo aka shigo aka dauki Ababan zuwa Asibiti cikin tashin hankalin kada a rasa shi.

A wannan lokacin ne Wani irin kukan da Bata San dashiba ya zuwar mata dukkanin jikinta na rawa da jijjjiga ganin ita tata 'yar kusan mutuwa tayi cikin tsananin wahala baa damu da akaisu asibiti ba har aka rasata gashi yanzu gawar ma sun rasa a lokacinda suke sakaran Bata mutu ba Kuma labarin hadarin ta da mutuwarta da Bilal yasake tsinka fatansu,

To su kuwa a yanzu meye suke da Wani buqata ko fata bayan mutuwar Suma su huta, Ga sabuwar Alhaki Allah ya sake jefo musu a cikin wannan lokacin da Suka gama sarewa gabaki Daya da duniyar da rayuwarma.

Benazir na Jin kukan Anne na shiga zuciyarta yana yankan Amma Bata iya matsawa saima sake rungume babynsu datayi tana Jin a yanzu da babu shigowa wannan babyn rayuwarsu da babu Abinda zai hanasu samun bugawar zuciya a ayau din su mutu su huta Amma duk motsin da babyn keyi jikinta Jin sumayyahnta takeyi a jikinta da zuciyarta Dan haka take sake qanqame babyn.

Kukan da Anne tayi Mai tsananin gaske Bai rage mata komai na nauyin da takejin zuciyarta tayi mata ba Dan haka ta share hawayenta ta miqe tsaye ta kama benazir din itama ta tayar da ita suka koma dakinsu.

Suna shiga Annen ta hau tattara dakin ta kwashe kayan da sumayyah ta haihu Akai ta fito dasu ta debo ruwa tahau aikin wankewa batareda ta furta kalma ko Daya ba.

Tana gamawa ta dawo dakin ta gyaran musu shi tas Har lokacin benazir na zaune rungume da 'yar Bata motsaba idanuwanta a bushe.

Anne ma da aikin fitan hayyaci takeyi tana gama gyara dakin ta fito ta share tsakar gidan ta gama ta Dora ruwan zafi suna tafasa ta juye tayo dakin dasu ta ajiye ta Kalli benazir tana miqa hannu zata karbi babyn tace

"Kawota a sake mata wanka"

Sai alokacin benazir ta dago da busashin idanuwanta ta Kalli Annen tsawon mintina Take a lokacin siraran hawayen tausayin mahaifiyarta suka gangaro mata sbd tasan baa cikakken hayyacinta take ba.

Hannu Daya ta saka ta share hawayen tareda daurewa ta dawo hayyacinta ta Kalli Annen ta girgiza mata Kai ahankali tana Ciro babyn daga jikinta ahankali tace

"Zan Yi mata Anne ki zauna ki huta"

Hakan data fada ya saka jikin Annen sanyi sbd tasan tsoron Bata yar takeyi sbd tinanin Bata hayyacinta kada ta jefata cikin ruwan zafi.

Dan haka Bata Musa ba ta juya ahankali ta koma gefe ta zauna tana kallan benazir zubawa benazir da babyn Ido.

Hannuwa na rawa da tsoron rashin iyawa Benazir tayi qarfin halin yiwa babyn wanka hannuwanta na tsananta rawa.

Bayan ta gama mata duk ta jiqa jikinta da gurin.

Ta miqawa Anne babyn Dan ta samu miqewa ta kwashe kayan wankan Anne ta girgiza mata Kai tareda cewa ta riqeta kawai bari ita ta kwashe kayan.

Kayan ta kwasa ta fitar ta dawo ta goge gurin tana gamawa ta karbi yar benazir ta sauya kayanta sbd kada sanyinsu ya damu babyn dake jikin nata Tana gama saka kayan ta fice tayo alwala sbd lokacin sallar azahar da yayi tini.

Tareda Anne sukai sallah babyn na tsakiyarsu shimfide.

Suna idar da sallah suka fara jerowa sumayyah addua zuciyoyin kowannensu na dakewa da qarfafa tawakkalinsu, Gawarta ma Basu saka ran Gani ba sbd zuwa lokacin sun sani an hadata da Bilal anrufe tinda danginsa sun San ita zai aura, Basuda masaniyar komai sai Ababa ya dawo yajiyo idan gawar zaa Basu kokuma an rufeta tini.

Babyn suka zubawa Ido dukkaninsu suna qarewa fuskarta Kallo zuciyar benazir na karban duk Wani feeling akan babyn.

Sai alokacin takejin 'yar cikin ranta sbd dama da sumayyahn na Raye da Bata Nan 'yar sumayyah 'yarta ce, Cikin ne kawai Bata dauka ba da haihuwarsa Amma kusan duk Wani wahala,Reno,farin cikinsa da baqin cikinsa Dede sukaisa da sumayyahn a yanzu Kuma ta tafi tabar mata 'yar bayan tazo duniya.

Anne kuwa miqewa tayi ta fito ta Dora musu abinci duk da tasan ba cinsa zasu iya ba Amma dole zasu rayu suci gaba da rayuwa sbd 'yar sumayyah data barmusu Dan haka komai a yanzu ba Dan kansu zasuyi ba sbd babyn zasuyi.

Tana gamawa ta tilasta benazir suka zauna suna cusa abincin a dole Suna gamawa sukai sallar laasar Lokacin babyn tafara Kuka sosai tana Neman Nono.

Kukanta ya saka radadinsu dasuke dannewa Neman tsinkewa Amma Anne ta daure ta shiga dakin Ababa cikin kayan haihuwar Daya Tara ta samo ruwan zamzam suka taho suna cikin bawa yarinyar Aka dawo da Ababa a jeme ya zabge cikin wuni Daya.

Hande ma har lokacin kukan takeyi Akai Akai.

Gidan tsit ya dauka kowa na jimamin mutuwa da rashin da sukai gashi kaman yan kankan Kai baa ma San anyi mutuwa ba gidan bare a shigo musu gaisuwa tinda baa ga ana janaiza ba bare karban gaisuwa.

Ababa Dayake fama da Kansa Jin kukan babyn yayi yawa yasa jamilu yaronsa siyo madarar jarirai gwangwani uku da ruwan roba Katan Daya.

Ana kawowa aka bawa benazir batareda an sanar da ita yanda ake bayarwar ba.

Dayake babyn tafara galabaita Bata tsaya Bata lokaci ba itada Anne suka dafa ruwan zafi suka hada mata a fidar dake cikin kayan haihuwar da hande ta watso musu daki bayan dawowar tasu.

Ana sakawa jaririyar fidar farko kasa kamawa tayi dai daga baya Anne ta karba ta ringa diga mata madarar cikin baki tukuna ta Dan fara motsa bakinta madaran na shigewa.

Hawaye masu zafi ne suka gangarowa benazir lokacin da babyn ke Shan madaran tana motsawa ahankali batareda tasan Tayaya zasuyi rayuwa da babyn a haka ba.

A haka suka kwana zaune gidan babu Wanda ya iya kwantawa bare ya iya rintsawa sai hande kawai Amma Ababan ma a zaune ya kwana cikin ciwon zuciya Dayake Neman Kaisa lahira a kwana daya da wuni biyu.

Har safe zuciyarsa cikin mummunan hali take ciki Yana saka da warwara Dan kuwa yasan ya tabbatarda sumayyah akwai Abinda dai yake qasan bacewarta bat, Gawar da aka samu cikin motar Bilal kaante guda Daya ce bayan biyu ya kamata a gani idan Kuma drivernsa ne ya tuqosa gawa uku yakamata a gani Amma Daya aka samu wadda Suma jamian tsaron kaman wainda aka Basu San aikinsu ba baida tabbacin anduba gawar an tabbatarda ya waye.

Zafin da Kansa ya dauka ya sakasa kasa tantance komai bayan tabbatarda koma meyake qasan wannan lamarin Bai lalata komai nasa ba ya janyo masa lukutar masifar dazata Kaisa qasa.

Dan haka da safe bayana ya sake samun saukin dawowa hayyacinsa Ya Yanke Wani mummunan kudirinsa akan Abinda yayi Niya Dan haka Yana fitowa Abinda yafara shine sanar da benazir da Anne dake jiransa akan maganar sumayyahn cewa anriga anyi janaizarta tareda Bilal tin jiyan addua da fatan samun rahamar ubangiji kawai zaa ringa mata harma da Bilal din.

Daga Anne har benazir ga mamakinsa babu Wanda ya some masa kaman yanda ya tsammata,. Abinda Bai saniba sun riqa sun Riga zuciyoyinsu sun bushe sun saddakar sun karbi kaddarar mutuwar sumayyahn tin jiyan dan haka suna samun tabbacin daga bakinsa suka sake daukan taurin zuciya suka sawa kansu.

Ababa kuwa Daman Hakan yakeso Dan haka shiryawa yayi ya nufi KAANTES gurin gaisuwa da sanar dasu an haihu lafiya kalau.

*******A Kaantes ana cikin tsananin hali da qunci da baqin cikin rasuwar ta Bilal wadda kusan duka ta taba iyayensa da kakan nasa da basusan suna kaunarsa ba sai a yanzu da bayanan yabar musu duniyar Dan haka dukkaninsu babu Wanda yake zaune da qafafunsa a kwance suke ba lafiya hakanan ake daurewa ana karban gaisuwar daga manyan mutane da baqin dake zuwa na kusa Dana nesa.

DD kaante ma rashin lafiya ce a jikinsa sosai sbd Bilal Wani bangare ne na jikinsa da bayan iyayensa shine halittar dayafi tsananin so a duniya, Rashin Bilal lokaci Daya ya girgiza duniyarsa da Bata taba girgizuwa ba, Dan haka tin ranar da Bilal din Ya rasu Yana bangarensa Nan kaantes Yana fama da Kansa Shima Sai likitan dake zuwa dubasa kullum ko gurin karban gaisuwar baya iya fitowa.

Ababa Koda ya iso baisha wahalan shigowaba sbd Abbakar dake gate Dan haka Kai tsaye Akai masa iso ciki.

A palon dd babba ya zauna cikin jimami yafara yiwa dd babban gaisuwa kafin yayiwa dad kaante da sauran uncle din Bilal din dake gurin.

Amsa gaisuwar sukai kafin Shima ya zauna cikin yan karban gaisuwar Yana bayyanarda jimaminsa harda Kuka sosai Wanda yasaka dad kaante Ganewa da shine Mahaifin yarinyar da Bilal din su ke tsananin so harya rasa ransa akanta.

Ganin suna cikin jamaa ya Hana dd babba da dad kaante tambayan idan 'yar Ababan ta sauka lafiya ita.

Ababa da Kansa ya bayyanarda Yana son yiwa ummen Bilal gaisuwa babu musawa Abbakar yayi masa jagora zuwan babban palon dad kaante aka shiga aka kirawo ta.

Zata fito DD na shigawa palonta sanye cikin black Balmain jumpsuits kyakyawan fuskarsa fresh a kame kaman baa tabawa da hannu Duka masu masa gaisuwan Bilal din Daya shigo amsawa yayi a takaice cikin nutsuwa batareda ya tantance su waye da waye ba duk da harda mummyn Sbb amaryasa aciki.

Ganinsa yasaka Umme hadiye hawayenta tana kama hannunsa Daya miqa mata Dan kuwa yanzu shine sanyin idaniyarta.

Tare suka juya zuwa palon dad kaante suna shiga qamshinsa yafara ankarar da Ababa ba haj fatman bace kadai ta shigo Dan haka ya dago idanuwansa daidai tsayuwar DD a palon ya zubawa Ababa idanuwansa a Karo na farko Daya zubawa Wani idanuwansa Yana kallan tsaf.

Kwarjininsa yasa Ababa miqewa tsaye daga zaunen Dayake bakinsa na Tara masa yawun dazai hadiywa maqoshinsa Daya bushe sbd tabbatarda wannan shine DAWOOD KAANTE din da duniya tafi sani akan duka sauran 'yaya da jikokin gidan,Kuma qanin Alh Bilal.

Rawa hannuwansa suka dauka take baisan lokacinda yace

"Nine Mahaifin Benazir, Yarinyar da Alh Bilal zai aura kafin afkuwan wannan kaddarar ta rashinsa"......

Daga Umme har DD a tare suka sake sauke masa idanuwansu bakin Umme na rawa tace

"Ta haihu? Me ta..... Bata qarasa ba Ababan ya katseta da cewa

"Ta haihu lafiya ta samu 'ya mace Kuma duk suna lafiya uwar da 'yar."

Daidai Nan dd babba da dad kaante dakeson magana dashi din suka shigo Kuma a kunnesu zancen an haihun ya sauka.

Wani kukan da Umme batasan ko na menene ba ya kunce mata tana Jin bayan babyn a yanzu baby Abinda take buqatan a kawo mata tagani.

Ababa kuwa take ya Yanke shawarar benazir ce uwar yar Kuma babu Mai sanin ba ita din bace matiqar Yana Raye.

*Masu buqatan pages da Akai Nisa sosai suyi following Dina arewabooks at mamuhgee kokuma suyi joining VIP* 09033181070 09032345899 #MAMUH# #MARRIAGE #DD #BENA #AMNAH

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 39 Dd babba ne ya shigo dad kaante na bayansa suna kallan Ababan a tare sbd Jin Abinda ya fada zuciyoyinsu na karban sakon nasa da sanyi batareda sun ankare ba.

DD kuwa Dan rintse idanuwansa yayi Shima a hankali sakon na sanyaya zuciyarsa duka batareda sun saniba Dan kowa tashin hankali yasa sun manta da akwai jinin da Bilal ya bari duniya,

Sun cire Rai daga samun Abinda zai dawwamar musu da kaunarsa da soyayyar da suka kasa nuna masa sai gashi Allah ya dawo musu da jinin Bilal tsatsonsa.

Daga dd babba har dad kaante suna zaunawa kallan Ababa Dayake star kallansu Daya bayan Daya sukai Dd babba na sake sauke ajiyar zuciya a Karo na babu adadi sbd Bayajin Dadi sosai tin lokacinda rasuwar Bilal din ta riskesu babu me isashiyar lafiya a gidan.

Ahankali dd babba ya Bude baki yace

"Abinda aka samu din lafiya take itama?"

Gyada Kai Ababa yayi cikin zumudinsa Dayake boyewa Yace

"Lafiyarta kalau daga ita har uwar"

Umme ce ta Bude baki cikin hawaye masu sanyi ta zube gaban dd babba cikin bayyanarda quncin ranta da qanqantar da kai tace

"Babba Dan Allah a kawo min Babyn Bilal ni ta kowace hanyar aka sameta Ina sonta a hakan, Ina buqatan ta a hakan, Zan reneta a hakan,Dan Allah kabada Daman a kawo min ita sbd ita kadai ce jinin Bilal dazata maye mana gurbin Daya bar mana....kukane yaci karfin Mai qaramin sauti da cin zuciya.

Dad kaante ma kallan dd babba yayi cikin rashin qwarin gwiwa Dana jikinsa da ba lafiyar Shima yace

"Ta hanyar dawo da ita Nan zamu ingatanta rayuwarta yanda ya dace harma da Hana kowa sanin matsayin nata tinda da Yana Rayen a yanda kayi alqawari ranar sunanta ranar daurawa iyayenta aure."

Shiru dd babba yayi Yana sauraronsu Wanda ko Basu roqa din ba a yanzu da Bilal baya duniyar bazasu banzatar da jininsa Daya qwal Daya bari ba a duniyar sbd jininsu ce Kuma itace a yanzu zata maye gurbinsa a zuciyar mutane da yawa a familyn.

Ababa zufane ya fara tsatsafo masa cikin rigarsa Yana kallan bakin dd babba yaji Abinda zai fada akan roqon iyayen Bilal din.

DD ne ya katse musu zancen Kai tsaye a natse da cewa

"Akwai buqatan Wani tinani ne Daman akan dawowan babyn hannun mu?" Muna buqatan sai muyi nazari ne akan Hakan? Kai tsaye daga lokacinda ya fado duniya ita din ta zama kaantes, Akwai dalilin barinta Wani gurin ne daga lokacin da ta amsa sunan?

Shiru iyayensa sukai sbd shi Daya ne Daman yake fadan maganarsa a tsaye gaban dd babba ba acikin raini ko rashin daa ba Amma shi Sam baya kwana kwanar magana ko inane kuwa yinta yakeyi Kai tsaye ta gaskia da gaskiarsa.

Ababa kuwa Jin ana nanata maganar karban baby dai,baby dai baby dai sai kawai ya Dan gyara Yana kallan DD Da kyakyawan fuskarsa yake a kame duk da idanuwansa sun Dan fada a kwana dayan.

Dd babba cikin sanyi ya Bude baki cikin Yana kallan Ababa yace

"Kaji dai ko malam Ababa? A kawo mana yarinyar zamu karbeta tinda dai a yanzu mutuwa ta shiga tsakani Allah beyi zamu cimma manufar hada iyayenta aure ba.

Hummmmmnnn" Ababa ya sauke Wani boyayyan numfashi Yana Jin Kansa na daukan zafi Amma dai ya daure yana daidaita Kansa.

Dagowa yayi idanuwansa taf da hawayen da baisan lokacinda ya janyosu take ba.

Cikin rawar muryar sautin kukan Dayake daurewa ya kallesu su dukan yace

Readers Also Read