Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 23
Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 23: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 23. "Wace jaririyar zaku karbe? "Yar dake jikin…
3,367 words
"Wace jaririyar zaku karbe? "Yar dake jikin uwarta zaa rabasu kwana daya da haihuwa? Anyiwa "ya ta adalcin rabata da 'yarta acikin wannan halin Datake ciki na rasa mijin aurenta? Tayaya idan tayi aure Nan gaba zata kasa nunawa mijinta tana da wata 'yar a Nan? Wannan zancen ai bazai binnu a Hakan ba, Abar mana babyn Nima Ina kaunarta zan rungumi kaddara mu Reneta idan uwarta ta samu Muji zuwa gaba tayi aure taje da ita can sbd bazamu bar 'yar ta tashi babu Uba ba anan ne zaa San Yaya 'yar take Kuma waye ubanta Koda baya Raye, Idan mutane suka shegantamun jika kokuma shi Wanda uwarta zata aura wataran ya sheganta mini ita nayi muku alqawarin bazan bari ba zan dauki mataki Kuma zan kula sosai da wannan babyn Amma kuyi hakuri bazan iya bari ku qwace mana ita ba a rabata da uwarta bayan wahala da gwagwarmayar da uwarta Tasha daga renon cikin zuwa haihuwarsa.
Yana gama fadan maganganunsa ya musu gaisuwar Bilal tareda sallama ya fuske ya juya Yana share hawayensa alaman iya gaskiarsa yake fada a matsayin Uba Kuma kaka.
A zuciyarsa kuwa qyam yake sbd yasan madokarsu Kuma itace ya doka Dan haka gida zai komawarsa Yana zaune zasu sake nemansa da yardar Allah.
Yana ficewa hawayen Umme suka qara gudu ta miqe tana ganin jiri tabar palon zuciyarta na nauyi.
Dad kaante ma kallan dd babba yayi jikinsa na mutuwa da zantikan Ababa Amma Kuma koma mene Suma suna buqatan 'yar ai a matsayinsu na kakanninta dasuka rasa mahaifinta.
Dd babba kuwa Jin Ababan kawai yayi Dan kuwa maganar komaima Bata tasoba yarinya bazata taba zama a wajen kaantes ba.
DD ma ficewa yayi daga palon sbd a nasa bangaren Shima yasan maganar barin jinin Bilal dinsa a Wani wajen ma har ana lissafin zuwanta agolanci tin yanzu ai baima San Hakan ba.
Babyn tagama dawowa hannunsa saidai uwar babyn ta hakura.
Ababa kuwa Yana fita Zeenah ta fice da driver suna fitowa ta karbi key tace ya jirata a hanya zataje ta dawo.
Bayan Ababa Zeenah tabi tiryan tiryan har gidansa.
Saida ta Dan jima a gurin cikin mota ta tabbatarda gidan ne kafin ta juya motarta tabar gurin.
Driver ta dawo ta dauka suka koma gida Kai tsaye gurin umme ta nufa daki ta sanar mata da ta gano gidan maman Babyn Bilal din.
*****Ababa na Isa gida shigewa yayi ya zauna palonsa ya rufe kofa ya fara warware tinani da abubuwan dake cikin qwaqwalwansa Dan ya huta shi Kansa sbd Kansa ya gama daukan zafi ya dauko maganar da baisan inda zata Kaisa ba tsakanin Ababa da Nobaba.
Amma dai koma yayane a mutu ko ayi Rai babu Wanda ya haifi wannan babyn idanba benazir ba ko duniya ma bazai yarda ta saniba bare kaantes. Karatunta kuwa daga wannan lokacin babusa Dan kuwa haihuwa tahau kanta,
Su kuwa kaantes ba hawan jini suke fama dashi ba ko saukan jini ne bazai bayarda babyn ba matiqar bada uwar babyn zasu amsa ba.
Benazir da Anne a daki kuwa zaune suke shiru babu komai sai jaririyar dasuke lallabawa kaman Basa son ko motsata sbd so da kulawa.
A yanda rasuwar sumayyah tazo musu da har ita har babyn suka rasu da ba lallai su samu qarfin wannan tawakkalin ba Amma Suma kansu a yanzu sunsan Wani irin dangana ne da Basu taba tinanin zasu iya samu ba Allah ya Sako musu.
A jikin benazir babyn take kowane lokaci sbd ita yanzu so na tamkar itace ta tsuguna ta Haifa babyn takeji Wanda Daman ko sumayyah na Nan tasan zata mata wannan son,yanzu Abinda yasa yafi qarfi da tsanani sbd batada uwa batada Uba sai su kokuma tace sai ita tinda Anne Allah ne kawai yasan yaushe da yaushe ne take daidai bare ta nuna mata soyayyar kaka.
Saidai Abinda Bata saniba ba kaman yanda take Jin yar cikin tsakiyan ranta kaman sumayyah ce a hannunta haka Anne ke Jin 'yar itama cikin ranta kaman sumayyahnta ce ta dawo musu a matsayin jaririya Dan haka kallan 'yar kawai idan tayi sai taji zuciyarta na Neman narkewa ta fashe da kuka shiyasa take Dan dakatar da kanta tana barwa benazir sbd itace uwarta a yanzu da babu sumayyah Dan tanada tabbacin akanta benazir babu sadaukarwar da bazata iyaba a ciki gidan tinda Suma dasuke manyan tana musu tin baya.
Sai yamma Ababa ya fito bayan ya cire kayan dayaje dasu kaantes ya Sako wainda yafi sabawa da sakawa na yadika marasa nauyi su kuwa idan zasu uwar shadda yakesha harda babban Riga sbd nuna mutincin Kansa.
A tsakar gidan ya janyo kujerarsa ta roba ya zauna gefen hande da itama zamanta kenan tsakar gidan kan tabarma ta fito Tasha iska sbd Kuma ta kasa ta tsare Basa buqatan bako kowane iri ne Dan kadama a ankare da halinda suke ciki na haihuwar banza a gidan.
Ita yanzu fatanta tinda sumayyah ta rasu tabarwa su benazir 'yar so take Ababa ya samowa benazir koma waye ya daura mata aure dashi benazir ta tafi da 'yar can su qarata gidan auren a huta kada yarinya ta girma jamaa su rasa inda aka samota idan Kuma auren bazai yiyuba to gwara tin wuri ace Anne ta haihu ta yanda ko yar ta girma babu Wanda zai San shegu suka fara haihuwa a gidan Suma Dan daga wuyan dasukewa mutane ya fadi.
Shi dai Ababa duk tinanin hande nata ne kawai nasa tinanin da burin daban Kuma nasan shine magana tinda shine me Yanke yanda yakeso ayi.
Abinci yayi Kiran Anne ta fito ta kawo masa sbd Bai samu Daman cin abincin Rana ba Yana ciki Saida yagama lissafe.
Ajiye masa abincin tayi zata bar gurin ya Kalli kofar dakinsu yace
"Uwar me benazir takeyi a ciki da 'yar Amanata duk sai zafi da sauro ya cinyeta daki kaman dakin boka tsabar duhu da kaya."
Ahankali Anne ta Dan kallesa kafin ta Bude baki tace
"Idan anfito da ita waje akwai sanyi zai iya kamata"
Ajiye abincin Daya dauka zai fara ci yayi ya Kalli hande data matse fuska yace
"Wai hakane hande?"
A siqe handen tace
"Eh Amma Kuma ai da uwar datayi naqudar 'yar ce zaa ce kada ta fito dakin sanyi zai iya shigarta......
Katseta Ababa yayi Yana dire abincin hannunsa da qarfi yace
"To waye ne yace uwar datai naqudarta ta haifeta Bata gidan.?
Da sauri dukkaninsu suka miqe suna waiwaye hande cikin fargaba da tsoro Anne kuwa cikin mamaki da firgicin itama Hakama benazir take ta fito dakin rungume da babyn Yana raba idon son ganin sumayyah da Ababa ke maganar.
Kallan benazir data fito yayi yana sake fuska sbd lissafinsa da gabaki Daya yanzune zai hau daidai idan komai ya tabbata yace
"Kunga uwarta Nan wadda tayi cikin tayi naqudar Kuma ta haihu"
Page 40 👇👇👇👇👇 #MAMUH# #BENA #DD KAANTE #KAANTES #AMNAH KAANTE #SAFNAH #LOVE/ROMANCE
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 40 Dakatawa daga dube duben dasukeyi kowanne cikin tashin hankali da firgici suka dawo da kallansu a Kansa gabaki dayansu.
Baki sake hande tace nashiga uku yau ina Shirin ganin baqar Rana, Ciwon qwaqwalwa ka samu Ababan khairi?? Mutuwar sumayyahn ta taba ka hakane bansaniba? Benazir ce fa a gabanka, Gizo sumayyahn ke Yi Maka ne? Qalu innalillahi.
Anne da benazir kuwa tsayawa sukai cikin mamaki da fargaban maganar hande kodai gizo sumayyahn ke Yi masa sbd wahalan dasuka Sha a hannunsa.
Shiru yayi musu Saida hande tagama tsoki burutsun zancenta ta saurara taba kallansa da mamakin ganin hankalinsa kwance Bai shiga tashin hankali ba.
Tattaro duka nutsuwa da hankalinsa yayi ya fara kallansu Daya bayan Daya yaga su dinma dukkaninsu hankalinsu na akansa.
Akan benazir ya tsaida idanuwansa yafara da cewa
"Ke kina son 'yar hannunki kuwa?"
Shiru sukai hande na sake shiga mamaki hakama Anne dagowa tayi ta Dan kallesa ahankali sbd Jin tambayar abinda bama sai anyi tambayar ba sbd ansan amsar.
Shiru benazir tayi tana kasa ko motsawa bare iya magana Dan kuwa fadanma tana son babyn hannunta kaman ragewa Miya gishiri ne.
Tsuke fuska Ababa yayi Yana fara hasala a siqe yace
"Ba tambaya nayi bane?kuka tsaya mun kaman wasu gumaka."
Ahankali benazir ta gyada Kai batareda ta dago kan ba.
"Bakinki Zaki Bude ki ban amsa kan na tashi na fasa bakin ki a gurin"
Cikin sanyi Kai tsaye ta Bude baki a natse tace
"Eh Ina kaunarta sosai."
Wani zafaffen tsoki ya sake Yana Hana zuciyarsa fusatan da zata sanyashi tashi yayi mata dukan fita hayyaci sbd a ciki 'yayan hudun kaf Bai qaru da komai dasu itace last hope dinsa Kuma itace wadda zata kasance mukullin samunsa Dan haka yake sake tausan zuciyarsa Yana Hana kansa Dora hannu akanta.
Bayason rufa rufa ko batawa Kai lokaci har Wani lissafin ya kunce masa Dan haka ya sake hade fuska sosai yace
"Dukkaninsu ku Bude kunnuwanku da hankalinku harma da nutsuwarku ku saurari Abinda zan fada sbd magana ce da fitarta ko bayyanar gaskiyarta daidai yake da masifar da mutum bazai iya dauka ba.,
Hande ya kalla datake kallansa a matse da son Jin meyake faruwa da Ababan ne yace
"Ki nitsu hande kijini da kyau, Kema me ciwon qwaqwalwa ki nutsu ki Jini Kuma ki fahimceni dakyau Dan wlh kuna kaucewa magana zan dauki 'yar Nan nakai Tasha na ajiye Wani ya tsinta.
Daga yau benazir itace uwar data Reni cikin wannan yar takuma haifeta.
Anne ce kawai ta Dan kallesa sbd wannan ai maganar dazu ce ya maimaita.
"Idan nace itace ta Rena cikin Kuma ta Haifa Ina nufin babu Wanda zaisan munama da sumayyah anan gidan bare haihuwarta, Benazir ce kawai 'yata Kuma itace wadda ta Haifawa Bilal kaante 'ya gatanan a hannunta, Babu Wanda ya Isa yasan gaskiyar maganar Nan har sai ranar Danaso.
Wannan Karan harda benazir cikin masu kallansa Dan ita har lokacin Bata fahimci meye ainihin Abinda yake nufi ba.
Shiru sukai babu Wanda yace "toh" ko Wani abin sbd har lokacin dai ita hande kallan ya tabu take masa Anne kuwa Kai tsaye tasan meyake Shirin aikatawa da wannan maganar tasa.
Benazir ta Maida idanuwanta ahankali ta kalla sbd idan har ta fahimci inda Ababa yake Shirin dosa da zancensa itama lokacin rabuwarsu ne yazo zata tafi ta barta shikenan, Amma a bangarenta idan har zai cusawa dangin Bilal benazir a matsayin sumayyah su amsheta da 'yarta to zuciyarta zata yarda da wannan shawarar Dari bisa dari sbd benazir taje ta samu rayuwa Mai kyau ta fita daga wannan rayuwar da saidai su mutu a wahala tinda duka 'yayanta sun mutu a wahalar sun barta.
Da wannan tinanin Anne Bata tsaya nazarin komaiba itace ta fara dagowa ahankali tace
"Na amince da Hakan".
Wata dariyar Jin dadi ya sake mara sauti Yana kallan Annen da mamaki yace
"Na buga a daidai notin hankalinki ya dawo kenan?.
Sake dariyar yayi Yana cigaba da cewa
"Kuma yaushe aka baki zabin da kike maganar kin amince? Magana ce nayi da Wanda ya amince da Wanda Bai amince ba da Wanda ya fahimta da Wanda Bai fahimta ba duka a banza sbd magana ta zaunu babu Wanda ya Isa a cikinku ya dagata, Ke benazir ki sakawa kanki da qwaqwalwanki kece uwa kece mahaifiyar 'yarki gatanan, Ni bansan wata sumayyah ba anan gidan bare haihuwarta.
Hande ya kalla Yana cewa
"Hande ko ke kinsani ne? Kinsan sumayyah a gidan Nan me haihuwa?
Baki sake hande tace
"Sumayyah a Nan gidan Kuma? Labarin ya shude ai Kuma, Allah dai ya Daya Miki 'yarki benazir.
Wata dariyar farin ciki ya sake Yana Maida kallansa kan Anne da jikinta gabaki yayi sanyi ya mace yace
"Kin sake fahimtar komai yanzu da kyau ko?."
Ahankali ta gyada Kai tana rintse idanuwanta dake radadin zafin Kuka Amma bayama iya zuwan.
Benazir data fara fahimtar inda aka dosa hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ahankali ta zube qasa tana sake riqe 'yar da kyau idanuwanta na sauyawa zuwa jajir itama tana kasa Kuka ko hawaye sbd tashin hankalin da Bata taba tsammani ba.
"Ki shirya kowane lokaci idan muka gama maganar manya daura Miki aure zanyi a satin Nan sbd bazan yarda a Rena yarinyar Nan ba a waje mutane su ringa sheganta min 'yar jika ba"
Kalmar aure Daya fada ya saka Benazir qarasa zubewa qasa tana Neman fita hayyacinta hannuwanta na rawa sosai hakama duka jikinta.
Anne ce ta durqusa ta riqota tana karban babyn dake Neman subucewa daga hannunta tana hadasu ta rungumo jikinta idanuwanta na qanqancewa Amma ba kukan.
Ababa daidai lokacin hade fuskarsa yayi sosai ransa na Dan shiga Baci yace
"Wannan maganar tawa yankan wuqa ce nayi nagama ki sakawa kanki qarfin halin Hawa matsayin uwar 'yar idan ba haka ba kuskure Daya kikayi akan wannan maganar wallahi tallahi dauke 'yar zanyi har abada bazaku sake ganinta ba zaku rasata kaman yanda Kuka rasa uwarta."
Rarrafowa benazir tayi koina jikinta na rawa zata zube gabansa tayi roqo Anne ta riqeta hannuwanta itama suna rawa duka zuciyoyinsu kaman zasu Fashe a tare da babban tashin hankalin dayake Neman dimauta benazir, Tayaya zatayi aure tabar Anne a wannan masifar ita kadai, Tayaya Anne zatayi rayuwa babu ko dayansu a cikin su hudun, Annensu barin ta a gidan a hannun Ababa da hande gwara Susan hankalinta ya gushe Koda an cutatar da ita bazata ji komaiba.
Miqewa Ababa yayi tsaye yabar gurin batareda ya sake bi ta kansu ba ya fice gidan.
Hande ma miqewar tayi sbd itama lamarin yamata daidai gwara benazir tayita tafiya da 'yar sudai Abar musu gidan da ita kafin a ankara da haihuwar.
Daki hande ta shige tabarsu tsakar gidan sai alokacin Benazir ta fashe da Wani irin Kuka Mai tsananin ciwo da radadin zuciya tana qanqame Annenta.
Annen daurewa takeyi tana Hana kukanta fasuwa sbd ta sadaqar gwara benazir da 'yarta su tafi inda rayuwarsu zata inganta Dan haka dole ta danne tsananin qunci da ciwon rabuwa da benazir din Datake ji ta nuna jarumta Dan nunawa benazir zata iya zama ita daya a tsakanin Ababa da hande.
Irin Kukan da benazir keyi a tsakar gidan jikinta na jijjjiga duk Wani baqin ciki,qunci damuwa da tashin hankalin data jima tana boyewa suna bayyana sbd Bata taba kawo tinanin aure ko tafiya ta rabu da Annenta ba kaman yanda bazata iya rabuwa da 'yar sumayyah ba har abadan da Ababan ya furta.
Rarrashinta Anne keyi da hannuwanta batareda ta iya Bude baki ta furta kalma ko Daya ba Dan tana Bude baki kukan Datake riqewa ne zai fashe mata ta sake daga hankalin benazir.
Sai da suka jima a gurin benazir na kukan daya kasa raqe mata nauyin Abinda takeji danne a kirjinta,
Kamata Anne tayi suka miqe ko tsayuwa Bata iya Yi a ahankali suka koma dakinsu suka shige ta zube qasa tana fatan kanta ya juye itama ko zata samu sassaucin ko yayane taji sauki.
Zaunawa Anne tayi gefenta tareda dora mata babyn a jikinta tana Bude baki cikin qarfin hali da dauriya murya a sanyaye tace
"Karkiyi Kukan baqin cikin Hakan kokuma tinanin bazaki iya Hakan ba,. Zaki iya benazir, Zaki iya, Kiyi Hakan sbd ni sbd 'yar uwarki Kuma sbd 'yarki, Kije benazir ki samu ingantacciyar rayuwa na yafe, Na yafe Miki ki tafi kinji bena, Ke kadaice sanyin idaniyata da zuciyata a yanzu, Kije ki samu rayuwar da kowannenmu ya kasa samu Dan Allah, Kiyi Hakan sbd ni da 'yarki., Kafin zuwanku duniya ni kadaice a cikinsu Ababan Kuma na rayu wahala Bata kashe ni ba Kuma Dan Kun tafi dukkaninku zan rayu inshallah sai ranar da Allah yayi kwana na a duniya zai qare..
Maganganun Anne suka sake rusa zuciyan benazir ta fasa Wani sabon kukan Daya saka jikin Anne sake mutuwa da sanyi Amma bazata nuna rauni da qunci Mai tsananin dake dabaibaiye da ita a lokacin zata daure koma yayane.
Kuka babyn dake jikin benazir tafara ahankali tana motsawa.
Anne ce tayi saurin karbanta tana jijjigawa sbd ta Dena kallo da sauraren benazir data kusa karya mata dakewa da qarfin halinta.
Ita kanta benazir Bata iya dagowa ta Kalli Annen sbd tasan daurewa ce da jarumtan dole Annen keyi Amma Kuma ko suyi jarumta ko kada suyi bazasu iya kaucewa tabbatar maganar Ababa ba har dai a yanzu da batada zabi sai na bin Abinda yace tinda ko guduwa bazata iyayi tabar Annenta ba ga Kuma 'yar da batajin zata iya rabuwa ma da ita Koda Ababa zai ringa yanka Naman jikinta.
Masu buqatan pages din da sukai Nisa join VIP ko arewabooks 09033181070 ##MAMUH# #AMNAH KAANTE #BENA #DD #ABABA #SAFNAH #HOTROMANCE
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 41 Shiru dakin ya dauka bayan lokacin da benazir ta dauka tana kukan da bazata iya sanin ko yaushe tsawon rayuwarta tayi irinsa ba sbd duk masifa da tashin hankali Bata cika Kuka ba kukan ta Dade da qafewa saidai tayi hawaye ko mara sauti Amma a yau din har Kukan shekaru Sha sha dake cikin zuciyarta tayi zuciyarta ta rage mata nauyi.
Tashi tayi ta fito daga daki jiki ba qwari ta nufi toilet tayo fitsari tayi alwala ta dawo dakin, Sallah tafara Yi ta magrib kafin ta fito ta Dora ruwan zafi ta dawo daki ta hadawa baby Madara ta karbeta daga hannun Anne datayi shiru tana bin benazir din da Kallo duk inda ta motsa tinda tasan itama rabuwarsu tazo din.
Bude fuskan babyn benazir tayi ta zuba mata idanuwanta dake kumbure tana kallanta soyayyar uwar data tsuguna ta Haifa 'da na shigarta akan yarinyar, Ko Ababa ya fada ko kada ya fada soyayyar datakewa babyn na irin Wanda tasan sumayyahn ma zatai mata ne.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda gyarata jikinta tafara Bata madaran ahankali tana Dan rufe Idanuwanta sbd kanta dake tsakanin ciwon da kaman zai sauka daga jikinta.
Shiru dakin ya sake dauka babu me magana har tagama bawa babyn ta koshi ta miqe ta bawa Anne ita ta tsaftace mata fidan da cup din data hada Madarar ta kaisu inda take adanawa ta ajiye.
Sauran ruwan ta debo ta shigo daki dasu a babban roba Anne ta kama mata tayi mata wanka suka sake shiryata tsaf tini Takoma bacci Dan haka Anne ta goyata ita Kuma benazir jiki ba qwari ta fito tattara gidan da kitchen kafin su shige.
Har ta gama komai ta shigo musu da abincinsu hande Bata fito ba hakama Ababa Bai dawo ba Dan haka Suka shigewarsu.
Da daddare bayan benazir ta kwanta duqunqune da babyn ciki abin rufa sbd sauro da sanyi tayi shiru tareda shiga tinani Mai zurfi jikinta na mutuwa daga kwancen datake.,
Anne data kasa bacci Jin shiru benazir tayi bacci Ta tashi zaune ahankali zuciyarta na karyewa kukan Datake ta riqewa tin lokacin ya subuce mata Mai tsananin ciwo da quncin zuciya ahankali ta fasa shi cikin qanqanin sauti kada ta tada benazir wadda idonta biyu tana jin saukan sautin kukan Annen hawaye masu dumi suka gangaro gefen idonta batareda ta motsa ba sbd Daman ta sani qunce ne Mai tsanani a ran Annen ta danne Dan kawai tana son fiddata wannan gidan zuwa Wani gidan.
Anne da batasan benazir na jinta ba Kuka sosai Tasha Mai ban tausayi tsawon lokaci kafin ta rarrashi zuciyarta ta kwanta bayan benazir din hawayenta na cigaba da gangara gefen idanuwanta daga kwance,
Benazir dake tsiyayan hawaye daga kwancen itama rintse idanuwanta tayi tana fatan wannan ya zama shine alkhairi ga rayuwarsu su ukun ita da babynta da Annenta.
Washe gari daga Annen har benazir din kasa kallan juna sukai sbd kowannensu fuskarsa da idanuwansa a kumbure suke sbd kukan dasuka kwana Yi mara sauti.
Ta bangare Daya Kuma kowannensu ya dauki dangana da qarfin zuciya ya sake sakawa Kansa Dan haka ayyukan gabansu sukahau Yi Wanda kusan wannan Karan Anne ce tafi Benazir din Aiki sbd babyn da benazir keta dawainiya da ita gashi yau din tanata Kuka daqyar benazir ta samu tayi bacci ta Kwantar da ita taje tayo wanka tana dawowa ta shirya tana Shirin goyata Ababa yace Akai masa ita.
A dakinsa da komai na hutawa yake yasa aka Kwantar da ita kan gadonsa Takoma bacci abinta hankali kwance.
Aiki benazir tazo ta karbanwa Anne suka gama kan lokaci suna shiga daki Akai sallama gidan Wanda ya saka Anne fitowa tana amsa sallaman sbd hande na daki ba lallai ta fito ba.