Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 24

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 24

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 24: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 24. Budurwar yarinya kyakyawa Anne tagani tsaye…

3,349 words

Budurwar yarinya kyakyawa Anne tagani tsaye a tsakar gidan hannunta riqe da babbar qatuwar leda tana kallan Annen itama cikin muryar me nutsuwa tace

"Sannu Ina wuni."

Kallanta Anne takeyi kafin ta Dan sauke kallanta ta amsa a sanyaye ta Dora da cewa

"Bari a kira hande.

Juyawa tayi zata nufi dakin hande Zeenah ta katseta da cewa

"Nan ne gidan su benazir????

Dakatawa Anne tayi tareda juyowa tana kallan Zeenah din kafin tayi Wani motsin Ababa da hande suka fito lokaci Daya Jin ana tambayar benazir Dan kuwa yanzu bazaiyi wasa ko barin kowance kuskure ba Dan haka ya fito yaga waye ke nemanta Kuma lafiya.

Kallo Daya Ababa yayi mata yaga kammanin zuriar kaantes take zuciyarsa tayi Wani tsalle ta dawo kirjinsa ya Dan saki fuska Yana cewa

"Barka da zuwa,daga Ina? Benazir kike nema?

Numfashi Zeenah ta sauke ahankali tareda kallan Ababan ta Dan gaidasa a jagarce kafin ya gaida hande itama tace

"Daga kaantes nake baby nazo Gani"

Wani farin ciki Mai girma ne ya rufe Ababa yace Mata ta qaraso ciki

"Bismillah Bismillah"

A palonsa aka sauketa ta zauna ahankali tareda ajiye ledarta hannunta tareda key din motanta da wayarya gefe tana Dan kallan yanayin palon.

Ababa da Kansa yaje ya kirawa benazir yace taje da kanta ta dauko babyn ta kawowa baquwar.

Jiki sanyaye benazir ta shigo palon da siririyan sallama ta qarasa Kai tsaye dakin Ababan dama suna shiga tinda sune masu gyarawa ta dauko babyn dake bacci hankali kwance ta fito da ita hannuwanta da zuciyarta na rawa sbd daga wannan lokacin dai ya tabbata itace tayi cikin Kuma ta haihu,tazama uwa ta zama mahaifiyar babynta har abada.

Rintse idanuwanta tayi ahankali tareda sauke numfashi da ajiyar zuciya Mai sanyi ta Bude idanuwanta daidai lokacin da ta iso gaban Zeenah wadda itama ta zubawa benazir din da babynta idanuwa tanajin hawaye na ciko idanuwanta da tsananin son babyn harma da benazir din da tausayinsu na rashin jigonsu Bilal.

Cikin nutsuwa benazir ta miqa mata babyn bayan sun gaisa kowannensu cikin sanyi.

Hannuwan Zeenah har rawa suke gurin karban Babyn tana amsarta ta rungumeta a hankali tsawon mintina biyu kafin ta Kwantar da ita cinyarta tana kallan fuskarta da babu Abinda ta baro na kamannin kaantes saima sake a girma zatafi yin kama dasu din.

Ahankali ta dago ta Kalli benazir da kanta ke qasa tana kasa kallan Zeenah sbd kunyar qaryat Datake dabaibaiye da ita.

Cikin kulawa Zeenah tace

"Yaya babyn lafiyanta kalau right? Kema duk Kuna lafiya Amma ko??

Gyada Kai benazir din tayi tana cewa

"Eh alhmdllh"

Ababa na ganin Hakan ya fita yana cewa hande ya biyosa sbd Ababa Zeenah din Daman ganin babyn da kyau.

Suna ficewa Zeenah ta Kalli babyn hawaye na gangaro mata na rashin dadyn yarinyar ahankali itama benazir nata hawayen suka gangaro na rashin tata yar uwar Amma ba Daman nuna ma tanada yar uwa sumayyah kaman yanda Ababa ya a fada har abada saidai tayi kukan kewanta cikin ranta badai a fili ba.

Ganin hawayen benazir yasa Zeenah kasa riqe kukanta cikin tausayin benazir datai rashin Bilal din itama sai ta ringa rarrashinta sbd kukan benazir da yayi karfi a hankali.

Sun jima a palon su kadai daga Kuka Zeenah ta gabatar mata da kanta tareda Bata tabbacin duka familynsu suna tsananin son babyn kaman yanda suke son Dan uwansu dasuka rasa Bilal.

Hotunan da zata Kaiwa Umme Zeenah ta dauki babyn kafin ta bawa benazir kayan data kawowa babyn kafin su karbeta ta dawo hannunsu.

Zeenah kaman kada ta tafi tabar babyn taji Amma haka ta daure ta tafi tana zuwa gida takaiwa ummensu hotunan wainda suka saka hankalin Umme sake tashi akan sai ankarba babyn Bilal din tadawo hannunsu kokuma kawai tabar kaantes din su koma gidan DD ta Reni jikarta acan.

Wannan Kalmar tata da tashin hankalin datai harma da hoton babyn yasaka dad kaante da ubangayya DD Jin buqatan dawowar 'yar hannunsu cikin gaggawa shi Kansa dd babban baisan Yana son 'yar ba Saida yaga hotonta abin tausayi kayan jikinta ma masu tsananin arha da rashin nauyi ne da zai saka sanyi shigarta ya illatata da wuri.

Washe gari Ababa Yanata Kai kawo tsakanin gida da waje Yana lissafin yaushe Kaantes zasu nemesa sai kwatsam ga Kiran Abbakar akan dd babba na nemansa.

Bai tsaya batawa Kansa lokaci ba ya nufi KAANTES din sbd zuwa lokacin ya matsu ayi me yiyiwa kafin DD kaante ya tattara ya koma inda ya fito lissafinsa ya Kuma watsewa a Karo na biyu.

Yana Isa kaantes Kai tsaye yanzu an tantancesa Yana zuwa ake barinsa shiga Dan haka shida Abbakar palon dd babba suka nufa Yana zaune Shima Yana jiransu.

Gaida dd babba yayi tareda dad kaante dake palon Shima kafin ya zauna a natse Dan Jin meye dalilin nemansa.

Numfashi dd babba ya sauke kafin ya dago ya Kalli Ababa cikin nuna manyanta yace

"Malam Ababa maganar jaririyar dake hannunku ce mun Yanke shawarar karbanta tin yanzu sbd a dauke muku nauyi dama duk Wani Barnar sunan da kuke gudu mu zamu ji da komai ba zaa San 'yarka ta taba haihuwa ba inshallah."

Numfashi Shima Ababa ya sauke Mai sauti kafin ya dago ya Kalli dd babba Bai tsaya kwana kwana ba Shima yace

"Ni yanzu na aminta na yarda sunan nawa Dana 'yata ya lalace kowa zai San ta haihu ba aure ya sani Amma bazan taba raba 'ya da uwa ba, Yarinyar Nan tazo duniya a ranar da mahaifinta yabar duniya sannan Kuma a rabata da mahaifiyarta? Harma da tinanin bazata San mahaifiyar tata har abada ba?? Daukan haqqin wannan marainiyar jaririyar 'yar zaiyi yawa,

Nayi alqawarin barinta tareda uwarta tinda ta rasa ubanta inshallah zuwa gaba uwarta zata samu mijin dazai aureta da 'yarta Dan Allah ya rufa musu asiri, Maganar asan waye mahaifinta har sunanku ya Baci nayi muku alqawarin bama zamu taba bari tasan waye mahaifinta bare danginsa har sunanku ya Baci Dan haka daga yau na hakura zan dauki bacin sunan Amma abarni da jikata zata samu gurin agolanci Mai kyau inshallah.

Da gaskiyarsa yake maganar Yana bayyanarda qunci da damuwarsa akan zancen Dan haka take gabaki Daya palon ya dauki tsit.

Dd babba da dad kaante shiru sukai sbd har ga Allah zancensa da ya shigesu yayi magana Mai maanar da zaa duba idan har zaa yiwa marainiyar jinjirar adalci batareda sun duba sunansu sun cutatar da itaba.

DD kuwa daya shigo alokacin maganar agolancin da Ababa yafada tafi sokan zuciyarsa, Idan har Yana Raye har abada 'yar Bilal bazata taba agolanci gidan kowa ba.

Ababa miqewa yayi Bai Jira Mai zasu fada ba yace

"Insha Allah gobe zamu bar garin gabaki Daya zamu koma asalin mu acan kauye zamu samun kwanciyar hankali da rufin asirin renanta ba maganganu Dan haka idan Kuna buqatan ganinta ko so Daya ne zaku iya zuwa kafin mu wuce nagode sosai Allah ya saka muku da Alkhairi Yakuma ji qan Alh Bilal ya masa rahama.

kofa ya nufa Kai tsaye zuciyarsa na tsallen Allah yasa maganarsa ta Doki inda yakeso ta doka.

Dad kaante da Dawood ne suka Bude baki a tare suka ce

"Zamu karbeta har uwar idan tayi wayon shekaru biyu uwar ta dawo gida tayi auren......

Katsesu yayi ta hanyar juyowa ya katsesu da cewa

"Aa ni 'yata yanzu zan mata aure bazata zo renan shekaru biyu ba ta qarasa lalata sauran rayuwarta, Kuyi hakuri mu tafiyar mu ka.......

"ZAN DAURA MATA AURE DA QANIN BILAL IDAN HAR HAKAN ZAI SAKA KA BADA ITA DA BABYN"..

Kalmomin dd babba kenan dasuka saka Ababa dauke wuta Yana juyowa Wani haqayin farin ciki da firgita na fita daga Kansa da kunnuwansa.

Dad kaante kuwa ajiyar zuciya ya sauke Bai shirya sbd shock duk da kusan Shima Abinda ya shirya fada kenan. ##MAMUH# #DD KAANTE #BENAZIR #BABY AMNAH #MARRIAGE/LOVE/HOT HOT #ROMANCE #ZAFIN KAI/ZAFIN KAI

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 42 Ababa Suma ne kawai Bai yiba a inda ya tsaya cak lakacin da kalaman dd babba sukai dirar mikiya cikin kunnuwansa, Kasa gasgatawa da gasken Abinda yaji yasakashi juyowa ahankali idanuwansa a kafe kan dd babban ya tsaya Yana zaunar da zancen cikin Kansa da zuciyarsa tareda boye shock dinsa.

DD kuwa wuta ya dauke na wasu daqiqun da baisan meyema zaiyi tinani Akai? Wane qanin Bilal din ake maganar ya auri mahaifiyar 'yar Dan uwansa? A saninsa bayan shi akwai qannan dangi dasuke dashi Amma dai koyaushe akace qanin Bilal yasan shi ake nufi duk da a cikin familyn ne kawai ake kiransa qanin Bilal Shima daga mahaifiyarsu sai dad kaante Amma kusan babu kiransa qanin Bilal sbd ganin yafi Bilal din samun cigaban rayuwa ta bangaren dukiya da suna.

Muryar Ababa dake rawa Yana damqeta Dan Hana bayyanarda zalamarsa a natse Yana kallan dd babba yace

"Idan har aurenta zakuyi Banda matsala da Hakan a shirye nake Amma dai Reno ko zuwanta zaman Dan Wani lokacin ne ban yarda dashi kwata kwata sbd babu adalci ahakan."

Dd babba numfashi ya sauke Kansa na sarawa da hukuncin Daya Yanke din Amma Kuma basuda zabin Daya wuce Hakan a yanzu sbd suna buqatan karban babyn ta dawo hannunsu Kuma rabata da mahaifiyarta kaman yanda Ababa ya fada cutatarwa ne,

Dad kaante ya kalla Wanda Shima dd babban yake Kallo kafin suka Maida kallansu kan DD a tare Wanda shikuma Sam hankalinsa Bai tashi ba sbd baima dauka cewan dashi ake ba akan maganar kawai dai buqatansa 'daya Daya sani shine 'yar Bilal 'yarsa ce a yanzu halak malak da Bilal baya duniya, Idan akwai wainda ya Isa ya karbi babyn yayi Iko da to shine Dan haka zai karbi babyn kota halin Yaya sbd sanin dayayi babu inda dukiya Bata magana Kuma Bata Aiki.

Dago kyawawan idanuwansa dasuka Dan fada yayi yaga kalar kallan da dd babba da dad kaante suke masa hakama Ababa Shima kallansa yakeyi Yana Jin kaman ya janyosa ya daura masa aure da benazir a lokacin.

Irin kallan da suke masa ya sakasa Sakin Wani gajeran crazy numfashin murmushi cikin zuciyarsa Yana cewa

"Wane crazy tinanin ne yake cikin kan tsoffin Nan"

A fili kuwa Kai tsaye cikin hade fuskarsa daga mamakin tinanin Dayake gudana cikin kansu yace

"You gotta be kidding me, Ba Abinda nake tinani ba kuke nufi kenan ba right?

Kallan da dd babba ke masa ya tabbatar masa da Abinda suke tinani Dan haka shi bai iya boye boye ba baya Yi so tsayuwarsa ya gyara a natse ya Kalli Ababa dake masa kallan mukullin arzkinsa kafin ya dawo da kallansa kansu dd babba ya Bude baki a natse yace

"Babu raayi ko gurin auran mace biyu a rayuwana, Dayan is ok so bana buqatan Qarin kowanne macen bayan dayan Please kar ayi complicating things anan, Maida kallansa yayi akan Ababa dake jiran matsaya Bai masa kallan tsaf ba Kai tsaye yace

"Zan baka blank cheque lissafinka yafara daga naira milayan 100 zuwa sama ka rubuta nawa kakeso ka kawon 'yata da kanka yau"......

Wani jiri ne ya dibi Ababa ya zubar qasan palon gaban DD din batareda ya sani ba sbd kudin Daya fada shi Koda an auri yar tasa Bai taba lissafin zai samu kudin zasu Kai miliyan darin ba bare zuwa sama.

Zufa ne ya tsatsafo masa ta ko Ina ya karye Yana tsiyayo masa,

Kasa dagowa yayi ya Kalli kowa sbd yaqin dayakeyi da zuciyarsa da hankalinsa dake Neman gushewa akan Jin kudin, Rawa hannuwansa suka dauka yayi saurin zirasu cikin babbar rigarsa kada a gani asan gushewan hankalin Daya samu na 'dan lokacin.

Girgiza Kansa ya hau Yi Yana Hana kansa bayyanarda halinda yake ciki Amma idan har wannan kudin zai iya sakasa haka hakama Idan DD kaante zai iya bayarda wannan kudin kaman ba komai bane to idan ya auri yarsa yaya kenan? Abinda zai samu zai zama nin ba ninkin wannan??? Hummmnn ya sauke numfashi a boye tareda yaqar zuciyarsa ya dago ya Kalli dd babba da Suma duk suka rasa abin fada sbd Tim farko kowannensu yasan waye Dawood da raayinsa da kalan yanayin rayuwarsa, To Amma a yanzu dukkaninsu suna buqatan 'yar dake hannun Ababan Dan haka suna buqatan sacrificing wasu raayoyinsu Dan samun Abinda suke so da buqatan kaman yanda dd babba ya sauke nasa tsananin raayin.

Ganin kaman Basa hayyacin fahimtar Abinda yake fada ya juya yabar palon may be idan Basa ganinsa su kawo Wani tinanin na Abinda zai yiyu.

Yana ficewa Ababa ma Dayake ta yaqi da zuciyarsa gurin Hana kansa karban kudin Dawood kaante din ya fice zuwa gida Yana hada hanya zufa na sake jiqasa.

Bayan barin Dawood da Ababa palon dd babba Kai tsaye Kiran Umme yayi a waya wadda itama take matse da akirata din Jin zuwan Ababa kaantes taji ya aka Kai karshen magana Dan Bata hayyacinta matiqar ba gabanta taga 'yar Bilal dinta Kuma jikarta ta fari ta dawo ba.

Lokacin da tashigo palon Kallo Daya dd babba yayi mata ya dauke Kai sbd ganin yanda gabaki Daya ta fita hayyacinta sbd ciwon rashin 'danta, Kaman wadda take kwance jinyar watanni Takoma idanuwanta kuwa sun kasa hucewa daga munin kumburin da sukai na kukan data kasa denawa har yau din na rashin Bilal da tsananin buqatan 'yarsa ta dawo gunta.

Cikin nutsuwa da sanyin jiki dd babba ya Bata tabbacin 'yar zata dawo hannunsu Amma sai idan ta saka Dawood amincewa da auren mahaifiyar babyn wannan shine sharadin Mahaifin maman Babyn idan ba Hakan ba a gobe zai tafuyarsa Subar garin gabaki Daya.

Hawaye masu dumi ne suka gangarowa ummen sbd lalata rayuwar 'danta da ake magana a maimaikon 'yar Dan uwansa da suke buqata su dukan,

Auren Sbb dole ne garesa Badan raayinsa ko buqatan Hakan yake ba Amma ya amince sbd ita Dayake son farantawa Amma tasani Wanda bayason hada ko muhalli da kowa har iyayensa ansamu ya aminta zaiyi aure yanzu tin baayi ba ana sake kawo masa Qarin mace ta biyu.,

Yaya Dawood zaiyi da auren mace biyu lokaci Daya? Tako wane saqo anshiga haqqin rayuwarsa, Amma Kuma Tayaya suna Kallo zasu rabu da 'yar Bilal ta tafi tabarsu kaman yanda Bilal ya tafi yabarsu da gibi me girman gaske a zukatansu.

A Karo na biyu zata sake zama uwa Mai son Kai ga Dawood Dan kuwa zata sake shiga rayuwarsa da Qarin wata macen.

Hannu takai ahankali ta share hawayenta tareda jinjina Kai tana Bada tabbacin zata gwada shawo Kansa akan maganar auren.

Miqewa tayi ta fito Kai tsaye part din Bilal da DD din yake ta nufa zuciyarta na karyewa.

Tana Isa a Palo ta taddasa zaune Yana amsa wayar Naseer a hankali Wanda ya kira akan yazo daukansa yau zai koma gidansa.

Jin qarshen wayarsa na tafuyarsa dazaiyi yasaka ummensa kasa riqe hawayenta suka gangaro tayi saurin sharewa da hannunta.

Zaunawa tayi gefensa tareda kasa juyowa ta kallesa sbd kunyar rokon da zata yimasa a Karo na biyu.

Idanuwansa ya dago ahankali ya zuba mata ya karance yanayinta tsaf tsawon mintina kafin ya Dan dauke idanuwansa Yana ajiye wayarsa dake hannunsa gefensa ya kalleta cikin nutsuwa yace

"Umme idan kikace nayi auren Nan Hakan na nufin Zaki janye wancan maganar auren na farko, Na baki zabin duk Wanda acikinsu kikeso ki zaba Daya zan aura kowace a cikinsu".

Yana fadan Hakan yayi mata shiru sbd babu Abinda zai qara Akai, Maganar zasuyita Janta ne har sai waninsu ya samu ciwon Daya shigesa na damuwa da maimaicin Abu Daya Wanda Sam Hakan baya cikin Abinda yake buqata a rayuwarsa.

Shiru ummen tayi tana kallansa da idanuwanta dasukai laushi sbd a cikin Biyun yanzu babu Wanda zata iya zaba tabar Wani.

Ajiyar zuciya tayi ahankali sbd da Bilal dinta na Nan da duk bazasu shiga wannan tsaka me wuyan ba daga ita har Dawood da zaa aurawa mata biyu duka badan Yana sonsu ba.

Miqewa tayi ta fito Bata iya zabar ko Dayaba a zancen ta koma part dinta tana shiga tinani da damuwan Tayaya ma zata iya kallan Dan uwanta da hajiyarsu ta fada musu Dawood bazai auri Sbb ba wata zai aura?

Wannan maganar kadai zata iya shiga tsakaninta da Dan uwanta da hajiyarsu komai ya lalace a zumincinsu.

Dad kaante ma da Kansa yaje yayo magana sosai da Dawood din Amma Sam raayinsa ya kasa sauyuwa Saida dd babba ya rokesa a matsayin shine zaiwa alfarmar Benazir, Idan ummensa ta rokesa ta zabar masa Sbb shikuma ya rokesa ya zabar masa benazir Dan haka Suka sakasa a tsakiya sbd sune mafi soyuwa a ransa su Biyun sai babyn da ayanzu tin batazo hannunsa ba yake jinta cikin ransa ta maye gurbin da Dan uwansa yabar masa.

Tinda dd babba yake babu Abinda suka taba ganin ya kwantarwa Kai sai wannan buqatan tasa ta auren Benazir wadda ta saka kusan sauran yayansa sanin halinda ake ciki.

DD kuwa daya gama fahimtar babu Abinda zai sauya tinanin su dd babban daga maganar auren dole ya amince sbd yasan auren sbd 'yar dasuke buqatan karba zaayisa hakama bayajin zai iya kallan matar da Bilal yagama mallaka a matsayin tasa matar, Bama zai iya saka kalman aurenta cikin Kansa ba sbd Dan uwansa musamman da haihuwa a tsakaninsu.

A cikin Daren zancen yarda da auren isarwa Ababa, Da farko kasa yarda yayi da Abinda dad kaante ya kirasa ya sanar masa akan zuwansu Neman auren 'yarsa gobe Saida ya kashe wayar ya sake dubawa yaga tabbas sunan dad kaante ne suka gama magana a lokacin.

Sakin wayar yayi tareda zubewa qasa da sauri yayiwa ubangiji sujjada ya taso ya fito zufa na tsinke masa ya tsaya tsakar gidan ya kwada sunan benazir wadda ke daki zaune tana bawa baby Madara.

Jin Kiran Ababa ya sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta sanyi da faduwar gaba ta miqe ta fito kanta a qasa ta tsaya gabansa daga nesa kadan rungume da babyn.

Anne ma dake dake rakube zaune fitowa tayi gabanta na faduwan ta tsaya gefen benazir.

Hande ma da sauri ta fito tana tsoron idan ba mutuwa benazir din tayiba itama yake wannan ihun Dan kuwa benazir na mutuwa wannan Karan zaucewa Ababan zaiyi.

Tinda aka haifesu shekaru masu yawa benazir Bata taba ganin murmushin Ababa akansu ba Dan haka daidai lokacinda ya kalleta ya saki murmushin baya tayi ahankali qafafunta na Neman sarewa da tsananin tsoro da fargaba tana sauke Kanta qasa.

"Benazir kin cika mun burina na shekarun Dana debo Ina wahala daku,.

Kallan yarinyar hannunta yayi yaji zuciyarsa na sake sanyaya da farin cikin ganin wannan ranar Yace

"Sunan benazir sunan sa'a ta ne a yanzu Dan haka itama na saka mata BENAZIR sbd idan Kuka je Tako ina sa'a tayita fasomin ba kakkautawa, Aurenki zaa taho nema gobe a satin Nan zaa daura Miki aure.

Anne data ji saukan zancen har cikin zuciyarta ta rintse idanuwanta a hankali tana tilasatawa zuciyarta karban zancen da sanyin farin cikin dole.

Follow me at mamuhgee Arewabooks ko VIP for more pages 09033181070 #MAMUH# #BENAZIR #DD KAANTE #HOT HOT #MARRIAGE #LIFE #DEEP

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 43 Benazir Bata iya dagowa ta kallesa ko Annenta ba sake Yin baya tayi ahankali ta dafa bango idanuwanta na kasa taro ruwan hawaye sbd takai matakin da ko kukan yanzu Bata iyawa Amma dai zancen har lokacin jinsa takeyi kaman almara,

Rabata zaayi da Annenta, Ya Anne zatayi rayuwa babu kowannensu, Sameerah ta rasu, Safnah ta tafiyarta, sumayyah ta rasu Ita Kuma yanzu gashi zata tafi tabar Annen da sunan aure,

Bata tausayin kanta sbd babu inda bazata iya rayuwa ba komai tsanani da wahala da rashin kauna hakama batada sauran Jin feelings a zuciyarta dama rayuwarta gabaki Daya da zata ji komai na duk abinda zata tarar a rayuwar da mahaifinta ya Saidata Akai.

Ababa cikin farin cikin dabai taba Jin irinsa ba ya tinkaro Benazir ya karbi babyn hannunta Yana mata wasa baki a washe Yana saka mata albarka harma da rungumeta Yana Jin kaunarta Mai tsanani wadda yake ganin kaman ta kudin dazaiyi ne sanadinta.

Hande ma farin cikin me tsanani na Jin zasu rabu da 'yar ta washe baki tana cewa

"Barkanmu da arziki daga qarshe dai zamu samu mu aurar da Daya daga cikin haihuwar Anne da babu Wanda aka amfana dashi."

Readers Also Read