Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 27

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 27

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 27: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 27. Shigowar Umme ya saka Benazir sunkuyar da…

3,353 words

Shigowar Umme ya saka Benazir sunkuyar da kanta qasa cikin sanyin jiki tana sake rufe kanta da dankwalin kayanta tinda Zeenah bata Bata mayafi ba gashi ita batama San Ina aka Kai nata kayan ba bare ta dauko ciki.

Cikin nutsuwa da girmamawa ta Bude baki a hankali ta gaida Umme.

Amsawa ummen tayi cikin kulawa tana cewa

"Meya faru ne? Kin Bata madaran kuwa? Ko kun kwana cikin sanyi Mura ya shigeta ne??

Kasa magana benazir tayi sbd batasan me zata ce ba tinda itama batasan me Amnah din kewa Kuka ba.

Kallanta Umme tayi tace sake hada mata madaran ki kawo mugani.

Ficewa tayi dakin da Amnah tana jijjigawa cikin kulawa da kauna.

Rintse idanuwa Benazir tayi sbd kanta Dayake Neman daukan zafi.

Madaran ta hada ta tsaya dakin ta rasa ina zata dosa sbd Bata Saba wannan free rayuwan dasuke tinanin tayi a gidan ba.

Zeenah ce ta kalleta bayan ta saka doguwan riga mara nauyi tace

"Follow me." Gaba tayi tana latsa wayarta data kunna lokacin benazir ta biyota a baya kaman mara lafiya sbd rashin kuzari da sanyin jiki.

Wani mahaukacin palon Daya gama Jin komai na Jin Dadin da kake buqata a zaman duniya suka fito komai da koina yagama daukan sanyi da qamshin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Duk inda ta saka tafin kafarta sanyi ya shigeta sai ta rintse idanuwa ahankali tana qanqame madaran Amnah Dayake hannunta.

Dakin Umme Zeenah ta Isa da ita ta Bude suke shiga Benazir din ta tsaya daga kofa Zeenah kuwa gurin Ummen ta nufa tana Kiran sunan Amnah dake Kuka har lokacin.

Dagowa Umme tayi ta Kalli benazir din tace

"Qaraso kawo abata mugani idan ba Wani abin yake damunta."

Takowa tayi ahankali ta qaraso ta tsaya daga gefe ta miqawa Zeenah madaran Umme ta amsa tafara Bata cikin sa'a kuwa ta amsa tanasha da sauri.

Gama Bata Akai Umme ta gyara mata jikinta da kanta ta Kwantar da ita take tayi bacci tana sauke ajiyar zuciya ahankali.

Kusan dukkaninsu ajiyar zuciya suka saukar Suma kafin benazir ta silale ta fito ta Maida kanta dakin Zeenah ta zauna qasa a darare zuciyarta ba Dadi Dan batasan Tayaya zatai rayuwa a Nan dinba Kuma, Duk da alqawarin data daukanwa Anne na zata Kwantar da hankalinta tayi rayuwa me nutsuwa to Amma ta Ina? Tayaya?. #MAMUH# #DBENA #MARRIAGE #ROMANCE #BABY MAMAH

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 47 Neman Nisa takeyi cikin tinani da damuwa Akai knocking kofar kafin aka Bude aka shigo.

Masu aiki ne guda biyu suka shigo a tare kowannensu dauke da fararen trays masu kyau dauke da breakfast dinta.

Cikin girmamawa Mai tsananin gaske sukai qasa da kansu suka gaidata.

Shiru tayi Bata dago ba sbd batasan da ita suke ba Dan haka Bata dagoba itama kaman yanda Suma Basu dagoba suka sake gaidata wannan Karan suna Dan dagowa.

Zeenah ce data shigo ta amsa musu tana cewa su Daya a cikinsu yaje ya kawo mata lemon zata ci abinci dashi.

Dayar ce ta fara Jere abincin a gaban Benazir da sai alokacin ta Dan dago ta Gane tin farko da ita suke.

Sake gaidata sukai ta amsa tana Maida musu da gaisuwa itama a sanyaye.

Ana kawowa Zeenah Abinda tace suka fice ta zauna tana kallan benazir data kasa kallan kayan da aka Jere a gabanta qamshinsu na cika hancinta zuwa cikinta.

Chips ne da ketchup da scotch eggs se pepper soup na Kazan da aka cirewa qashi dakuma tea mara Madara me qamshi da zafi sosai.

Bata dauka ita aka kawowa wannan abincin ba saida Zeenah ta sakata cinsa tareda Tayata zuba komai cikin wasu irin plates da suka saka benazir din hankalinta na Neman tashi da wannan rayuwar data samu kanta aciki alhalin mahaifiyarta na can cikin zafaffiyar rayuwa.

Duk yanda Zeenah taso Benazir ta sake taci abincin Bata iya cinsa sosai ba sbd ba cimarta bane irin wannan abincin Dan haka sama sama taci komai taji ya isheta.

Tattara kayan Akai aka fice dasu Mai Aiki ta shigo ta sake gyara dakin ta Kuna humidifier ta fice.

Umme da Zeenah ma shiryawa sukai suka fice zuwa Asibiti dubo dd babba.

Ita kadai aka bari sai Amnah da masu aiki.

Da Rana ma haka masu aiki suka kawo mata abinci aka jera mata Daqyar ta iya cin kadan tace ta koshi suka dawo suka kwashe.

Kaman mara lafiya haka ta wuni a daki jigum tana renon Amnah duk a sanyaye ba kuzari.

Sai magrib suka dawo har lokacin tana daki zaune ba motsin kirki.

Shigewa sukai kowa yayi wanka suka Dan huta kafin suka fito cin abinci wannan Karan haka aka sakata fitowa zuwa dining Wanda har Akai aka gama Bata iya Sakin jiki ta zauna ko daidaiba bare iya cin abinci a cikinsu.

Dole aka maidata daki aka Kai mata Wani abincin acan Shima Bata iya ci ba saida Umme da kanta ta shigo tace taci.

Yau dinma hakuri Umme ta Bata akan su sake kwana dakin Zeenah kafin gobe.

Wanka sukai kaman yanda Zeenah ta sakata ta shirya ta shirya Amnah suka kwanta.

Yau ma kaman jiya sai kusan hudu ta samu bacci ya Dan dauketa.

Washe garin ranar tana daki masu aiki suka zo aka cire tsadaddin furnitures na dakin dake maqale Dana Zeenah da basuyi komaiba aka saka komai sabo a dakin tareda tsarin abubuwan dakin babys.

Me Aiki aka kawo ranar sabuwa wadda hidiman laluran benazir da Amnah ne kawai aikinta da haka ita aka saka ta Jere kayan lefen Benazir tsaf a closet hakama tarin kayan da aka siyawa Amnah duk ta Jere komai Duk da babu inda yakeda Wani Abu me suna datti ko qura a dakin Amma Saida Nafisat me aikin ta tsaftace koina ta wanke toilet din da a ranar Shima aka zuba mata toiletries da komai na buqatanta Dana Amnah.

Ac aka kunna tareda qamshin masu Dadi Zeenah ta kawota dakin ta fice sbd wayan da zatayi.

Tinda ta baro gidansu babu Abinda ta dago tayiwa kallan ko sakan uku bare kallan tsaf sai dakin.

Turkish Royal bed ne da set dinsa na komai tareda Wani mahaukacin Katan mirror Daya ci kusan Rabin bangon gefe Daya.

Komai na dakin Ashe ne da fari aka saka sai daukan Idon nuna kudin Dayake cikin siyansa, A gefen makeken gadon daga qurya gadon Amnah ne fari Mai kyau da tsadan gske Shima hakama da kayan qasan baby a jikinsa,.

Ko beddings dake shimfide a gadon fari ne hakama pillows Akai kusan guda 8 dasuka sakata sauke ajiyar zuciya ahankali jikinta na mutuwa sosai.

Carpet da table dasu stools harma da sauran kayan dakin kusan tsoro suka Bata saidai batada mafita ko tudun dafawa a wannan rayuwar data tsinci kanta aciki Dan haka ta Tako ahankali ta Kwantar da Amnah ta nufi inda take tinanin toilet ne ta shiga Nan Wani firgicin Yakuma cikata ta ringa saukar da hawaye masu zafin tonowa da Annenta tinanin anan ake nufin zatayi rayuwa Annenta na can cikin halin qaqanikayi.

Sosai tayi Kuka jikinta na sake mutuwa kafin tayo alwala ta fito ta tayarda sallah.

Tana idarwa taga har lokacin Amnah na bacci Dan haka ta koma toilet tayo wanka sbd tinanin al'adar da Dokan gidan ne wanka kafin kwanciya musamman ganin wannan gadan tasan bama zai yiyu ta hau musu gadon ba.

Tana fitowa ta dauko kaya inda Zeenah tace mata ta ringa daukowa ta saka doguwar Rigar jallabiya sbd a kwana Biyun datai dakin Zeenah cikin mawuyacin hali tayi su sbd kayan datake Bata tana sakawa Riga da wando.

Tana gama shiryawa Zeenah ta shigo ta zauna tana Tayata bawa Amnah data farka Madara.

Bayan sun gama Zeenah anan ta kwanta Saida Amnah tayi bacci kafin ta fice musu bayan ta nunawa benazir inda zata Kuna wutar dakin da kashewa kokuma rage hasken.

Zeenah ce ta sakata Hawa gadon kafin ta fice Dan haka tinda ta hau take shiru kaman wadda tayi bacci Amma zuciyarta cike take da tinanin inda ta samu kanta a yanzu.

Baby Amnah kaman tasan sunyi dakin kansu ranar bacci tayi sosai har safe ko madaran Bata farka ta Sha ba.

Suna yin sallar Asuba benazir ta gyara gadan ta sauko da Amnah suka zauna kan tattausan carpet din dake gefen gadon suna gyangyadi.

A gurin bacci ya sake dauketa sai kusan karfe Tara Nafisat ta shigo tafara kokarin gyara dakin ita Kuma benazir tayi toilet da Amnah Dan Yi mata wanka.

Yau ma a jiqe suka gama wankan ta kawota daki ta Kwantar Takoma itama tayo ta fito suka shirya suka zauna jiran tsammani kaman kullum.

Breakfast din na yau a dining aka kirawota a dosane tayisa cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.

Suna gamawa ta silale Takoma daki sukuma suka sake ficewa zuwa Asibiti sbd dd babba da zaa wuce dashi Zurich yaga likitan DD.

Dayake tafiyan tareda Dawood din harma da dad kaante zaayi sai Basu Wani tsaya Bata time ba cikin kwanaki 10 aka gama komai suka wuce Kuma tin ranar da aka tafi da dd babba asibiti Dawood Bai dawo kaantes ba sbd kullum a Asibiti yake haduwa da ummensa harma da dad kaante.

******Bayan tafiyarsu dd babba Umme ta samu nutsuwan dawo da hankalinta da kulawanta kan benazir data fara sabo da zaman daki da rayuwar kadaici data sake samun rayuwarta aciki duk da Zeenah na iya kokarinta gurin ganin tana debe mata kewa da Bata kulawa tareda nuna mata wasu abubuwan.

Wata sabuwar meyiwa Amnah wanka aka dauko dattijuwa wadda ita Kuma aikinta kawai na yiwa Amnah wanka ne sbd mura data fara shigarta na ruwan wanka da kullum saita shaqa sbd benazir Bata iya mata wanka toilet.

A jiki Umme tafara Jan benazir sbd lura da akwai tsoron mutane da rashin sabo da mutane sosai a tattare da Bena din,

Mum Khadija ma da bata cika son mutane ba tana 'dan kaunar Bena din sbd fahimtar zatayi biyayya makan baiwa ita Kuma Daman tanasan Wanda zai Basu girma da biyayya ya nuna su dinne a sama.

Zaman daki da qarfi da yaji Umme da Zeenah suke Hana Bena kullum indai zasu fito sai ankirata ta fito.

A dosane take zama cikinsu Bata iya magana idan ba tambayarta ummen tayiba ko Zeenah.

Ahankali mura Mai qarfi ta shigeta ita da Amnah sbd sanyi da wankan Datake musu so biyu kullum tinda tazo sbd tsoron shafawa Wani Abu ko gidan datti ganin masu gidan da gidan kaman saika wanke hannu zaka taba su.

Boye zazzabinta Mai tsananin karfi tayi ta danne Bata bari ansaniba tinda haka Suka Saba gida, Na Amnah ne yakasa dannuwa sbd rigimar Datakeyi ba sassauci.,

Ta Dena baccin dare sbd ciwon Amnah ga nata ciwon ga rigimar Amnah ga kadaici ga damuwar mahaifiyarta sai kawai tafara Neman zauncewa ciwo ya Kwantar da ita gadan gadan harda Kuma Qarin sauyin cima da muhalli.

Hankali tashe aka kirawo likita har gida yazo ya dubata aka duba Amnah itama.

Wannan ciwon da sukai ya saka jikinta yin sanyi sbd kauna me tsananin dataga Umme nayi mata itada Amnah sai Hakan ya taba zuciyarta akan yaudarar ummen takeyi a matsayin wadda Bilal dinta ke tsananin so.

Wannan tinanin ya sanyayar da zuciyarta daga bushewan da tayi batajin kowane feeling a gidan da mutanen gidan.

Idan zatayiwa Umme adalci Bata cancanta wannan yaudarar da ake mata ba Amma Kuma itama Batada zabi sbd ba itace ta zabarwa kanta wannan rayuwar ba.

A haka dole ta fara sakewa dasu Dan faranta ran Umme Dan Zeenah dasuke nuna mata asalin kauna da kulawa.

Da farko kokarin cin cimar da duk aka Bata tafara tareda daurewa tana cin abincin taredasu a dining kowane lokaci.

Hakama takan daure da kanta ta fito Koda dakin Zeenah ne taje,

Kullum da safe da kanta take zuwa dakin Umme ya gaisheta ta dena Jira sai an Aiko kiranta ta fito.

Hakan data fara ba qaramin faranta ran Umme yafara ba Dan haka suka sake dagewa sosai gurin kulawa da benazir din.

*****dd babba ya samu sauki sosai Amma Dawood ya hanasa dawowa sai ya huta daga tashe tashen hankalin da akaita samu a baya Dan haka sukai zamansu sbd shi Dawood din yanada abubuwan da zaiyi a qasar Kuma ahakan yaqi barin ko so Daya Safnah ta gansa Kuma data kira yace Bai aminta ta samesa ba ta zauna inda take zai nemeta da Kansa.

Wata daya suka share harda sati uku kafin suka fara Shirin dawowa shi dad kaante Daman tini ya dawowarsa yabarsu acan.

*****Acikin wannan watan da satikan rayuwar Benazir a Kaantes ta fara amsa Wani sunan da matsayi na sauyi data fara samu,

Dukiya gaskia ce,hakama rayuwar hutu da daula gaskia ce,

Benazir ta fara samun sauyi na rayuwa Dana fata, Skin dinta brown ne lafiyayye tin asali, Su ba maabota yawo bane kullum sune kulle cikin kejin gidansu ahakan suka taso suka girma,

Fara jamiar su kullum jikinsu a rufe yake sbd rashin sitarar arzki da Horan da suka samu Dan haka fatarta na fara samun hutun kaantes da tsadaddiyar luxury rayuwar da ake Bata yasaka sauyinta fara bayyana a kankanin lokacin.

Cikowar jiki Kuma Daman ita din bamai jikin qiba bace Dan haka bata sauya ba tanan siririyarta Saidai murmurewan data samu.

Umme ta Siya mata waya itada Annenta aka aika mata driver yakai mata Dan haka tana magana da ita idan Ababa Yana gida ya Bata wayar tayi tagama a miqo masa ya aje.

Shima shirun da yayi ya daga qafa ne sbd sanin dd babba da Dawood din Basa qasar shiyasa yayi shiru sai sun dawo an nitsa yafara sanin matsayarsa.

******Qarfe uku na yamma jirginsu ya sauka Abbakar ne yaje daukosu Shikuma DD Naseer ne yaje ya daukosa daga airport gidansa Kai tsaye ya wuce saiya huta zaizo kaantes din.

Yana Isa wanka yayi yayi sallah baya buqatan cin komai sai ya huta tukuna Dan haka kwantawa yayi baccin yamma sai 5 da Rabi ya tashi yasake Yin wanka ya fito Kai tsaye yayi kaantes.

Koda ya Isa zaayi sallan magrib Dan haka tareda dd babba suka shiga sallar suna gamawa ya fito Abbakar na biye dashi Yana sake masa barka da dawowa suka nufo ciko.

Sashen ummensa ya nufa Kai tsaye Shima Abbakar ya koma.

Zaune suke a Palo dukkaninsu daga ummen har Zeenah da benazir dake gefen Zeenah suna bawa Amnah Madara a tare yauma rigimar takeyi.

Qamshinsa yayiwa palon dip Dan haka a tare Umme da Zeenah suka dago kallan kofar daidai shigowansa Sanye da black Balmain three quarter jean da hoodie sweatshirt hasken qafafunsa dake bayyane na daukan idanuwansu kaman koyaushe fatarsa kaman ta sabon baby sbd hutu da luxury rayuwar daya taso aciki yake aciki. #MAMUH# #DBENA #HOT LOVE #CRAZY IN LOVE #ROMANCE

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 48 Kukan Baby Amnah ne ya sakasa Dora fararen idanuwansa a gurinsu Zeenah din ya saukar dasu kan Amnah dake jikin benazir tana sake Kai madarar bakinta fuskarta a sanyaye da rashin sanin me zatayi Amnah ta Dena rigiman sbd rigiman Amnah daga rikitar da ita yakeyi Sam Bata San Abinda zai saka Amnah din Kuka.

Qarasowa yayi cikin palon har lokacin idanuwansa akan Amnah batareda ya Kalli wadda ke riqe da Amnah din ba.

Umme kuwa nata idanuwan akan dagayen fararen lafiyayyun qafafuwansa dake bayyane sike duk da tasan sune best kayan dayafi sakawa idan Yana gida Sam baya wahalarda Kansa da kaya masu nauyi ko takura.

Zaunawa yayi gefen ummen a hankali cikin nutsuwarsa ya gaidata batareda wainda ke palon sunji maganarsa sbd rashin daga muryan.

Zeenah dake kokarin gaidasa ne cikin farin cikin ganinsa maganarsa ta katseta kaman daga sama Benazir taji magana daga bayanta cikin sautin kamewa da nutsuwar murya.

"Baby Amnah ce??"

Benazir da maganar ta daketa Kai tsaye sbd Bata lura da shigowar kowa ba hannuwanta rawa suka fara ahankali batareda ta juyoba Dan Bata ma gane meya fada ba sbd nutsuwan muryan.

Zeenah ce ta daga baby Amnah din tana goge mata baki da lallaunsa pink baby hanky ta taso ta nufosa tana cewa

"Sannu da dawowa Yaya DD."

Babyn yake kalla harta iso gabansa tana sake cewa

"Baby Amnah ga daddy ya dawo ki Dena rigiman haka."

Sai alokacin ya juyo ya Kalli ummensa da idanuwansa dasukai Wani Dan shigewa da alaman "da gaske Amnah ce wanna?"

Murmush Mai yalwa Umme ta saki tana karban Amnah din daga hannun Zeenah tana sake goge mata Dan qaramin bakinta na mahaifinta data dauko Zak da Zak ta gyada masa Kai tana cewa

"Eh Amnah ce,gatanan duk ta ruda mummynta sbd rigimanta."

Numfashi ya sauke a hankali mara sauti Yana kallanta daga hannun ummen Yana son daukanta Amma Bai San ya zai daukota ba sbd shi ba maabocin daukan Yara bane, Bayama daukan Yara Sam Amma Kuma wannan tasa ce Yana Jin buqatan daukanta kaman yanda kowane Uba yake daukan 'dansa idan an Haifa masa.

Dariya Umme ke masa da Zeenah lokacinda Umme ke kokarin Dora masa Amnah a hannuwansa Dayake Jin kaman zaa Dora masa farin cikin rayuwarsa ne kaf.

Ita kanta Amnah din kaman tasan gurin waye zata je dan haka tayi shiru idanuwanta a Bude.

Lokacin da Umme ta gama Dora masa ita ta janye hannuwanta suka barsa da ita ajiyan zuciya ya sake saukewa a Karo na biyu yanajin tsaftatacciyar kaunarta me qarfi da sanyi na sake kama zuciyansa,.

Yanzu shine uban wannan kyakyawan babyn ta hannunsa, Daman haka feeling na zama Uba yake da sanyin nutsuwa?

Meyafi wannan kyakyawan babyn ta hannunsa a rayuwarsa yanzu??

Dagota yayi ahankali ya Karanto mata addua a natse cikin qaramin sautin da babu Wanda yaji tukuna ya miqe tsaye da ita a kafadansa ya fice zuwa palon dad kaante yana tafiya kaman bayason jijjigata hakama Bai Wani iya riqeta sosai ba sbd Bai iya dinba.

Yana fita Benazir data kasa motsi bare juyowa ta miqe tsaye a hankali cikin nutsuwa ta dauki kayan madarar tayi kitchen ta miqawa Nafisat Dan da tsaftacesu ita Kuma ta nufi daki hannuwanta na rawa bugun zuciyarta Datake ta riqewa sbd bugawan Dayake da qarfi Yana qaruwa.

Bedroom dinta ta nufa ta shige tareda qarasawa kan sofa ta zauna ahankali tana damqe hannuwanta dake Dan rawa.

Babu Wani tinanin Dayake ranta bayan na firgicin data shiga duk da tanada dauriya da nutsuwan danne firgicinta.

Zaunawa tayi a dakin shiru Bata fita ba tanata daidaita kanta Daga tsoro da fargaban data shiga har tsawon lokaci kafin ta tashi ta fada toilet tayo alwala ta tayarda sallar ishai tayi ta gama.

Tana tashi daga dadduman sallah mayarwa tayi ta nufi toilet Dan Yin wanka.

Tana shiga Bata Wani jima ba ta fito ta shafa Mai sama sama tayi duk Abinda zatayi ta saka doguwan Slianche free gown black da fari kadan a ciko har qasa tana kokarin daukan wayanta tagani ko zata samu magana da Anne Nafisat ta shigo ta sanar da ita lokacin dinner yayi.

Sauke numfashi Mai dumi tayi ahankali tareda ajiye wayar Jikinta na mutuwa kafin ta miqe ta fito.

Tana fitowa Zeenah na fitowa daga nata bedroom din sanye cikin Riga da wandon Fendi masu Dan kauri ta shaqi qamshin Benazir din Mai sanyi Dayake Dan tashi jikinta tace

"Muci abinci muje mu duba dd babba tareda masa barka da dawowa."

Gyada Kai benazir din tayi tana qarawa da cewa to.

Suna doso dining din Yana sake shigowa palon a Karo na biyu rungume da Amnah datai bacci a jikinsa.

Da nutsuwa yace

"Zeenah karbeta I think ta gaji or may be she's hungry or something tana son farkawa kaman."

Benazir data kasa gaba ko baya ta tsaya bayan Zeenah kanta a sunkuye shikuwa Yana bawa Zeenah Amnah ya nufi dining gurin ummensa.

Qarasawan da Benazir bataiba kenan ta juya dauketa Amnah Takoma daki batareda itama ta iya Koda tsautsayi daga Kai ta kallesa ba kaman yanda shi bai ma yi noticing nata ba.

A daki taci abincinta bayan tagama shirya Amnah tayi bacci sai tabarwa Nafisat ita suka fita zuwa sashen dd babba.

Dan mayafin Dayake kanta yasakata kakkame jikinta sbd gabaki Daya babu mayafin kirki a kayan da aka Siya mata Tin daga kan na lefe har Wanda aka sake sissiya mata bayan auren.

Da sallama suka shigo Zeenah ce a gaba sai Benazir din bayanta kaman yau aka kawota gidan.

Readers Also Read