Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 4

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 4

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 4: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 4. Sai magriba ta gama ayyukan dasuka saba yi su…

3,375 words

Sai magriba ta gama ayyukan dasuka saba yi su biyar harda Annensu a baya amma ayau ita daya ce tayi aikin dan haka koda ta gama ta dawo dakinsu tayi sallar magrib da ishai kwanciya tayi gefen sumayyah da har lokacin take kaman bata dawo hayyacinta ba.

Washe gari daqyar ta iya ayyukan gidan tasamu aka basu abincinsu ta kawo daki suka rufa su ukun suka cinye batareda ko wannensu ya koshi ba dan haka gurin wanke wanke wanda Ababan ya rage ta kawowa Annensu ta qarasa cinyewa ta koshi ita kuma sumayyah wanda Hande ta rage ta kawo mata itama ta qarasa koshi.

Washe gari ma haka itace tayi ayyukan gidan sbd har lokacin sumayyah bata gama dawowa daidaiba.

A cikin kwana biyu ta qarasa zabgewa sbd wahala da rashin bacci ga damuwa da tinanin da yayiwa rayuwarsu daurin minti.

*********A hankali sumayyah da Anne suka warke suka dawo daidai Annensu ta dawo saidai kaman batai haukar kwana biyu ba tadawo yanda take saidai kullum cikin fargabar kada ciwon ya sake tashi suke dan haka suketa kokarin hanata tina su Samirah da safnah suka dage suka maye mata gurbinsu batareda bata dama ko kankanuwa ba ta tinasu dan sai saukin haukan yazo mata da mantuwa mantuwa kwata kwata sai tana mantawa da basu biyun ne kawai yayanta ba sai can lokaci lokaci tace ina samirah?ina safnah?

Data fara maganarsu da sauri suke dubarar dasuka mantar da ita zancen sbd kada ciwonta ya tashi komai ya lalace musu.

A yanzu rayuwa tayi musu wani irin juyi zuwa mafi wahala da ukuba sbd wahalarsu tafi yawa a yanzu da suke iya su biyu kawai, Ababa a yanzu Annensu itace mukullun daya kama na juya rayuwarsu yanda yake so sbd yagama gane itace kawai abinda zai kama yace su fada wuta su fada batareda tinanin komaiba,

A yanzu daya dauki wannan tsarin sai haukarta dake hawa tana sauka tayi masa daidai, Ya zauna ya tsara sabon lale ga rayuwarsu gabaki daya ta hanyar miqasu ga auren jari ga wasu dilolin miyagun qwaya da masu safarar mutane da ya samu amma sam hadin bazaiyi ba saiya wadatar dasu da ilimin boko mai dan zurfi dan haka kai tsaye ya fidda kudi aka nemar musu gurbin karatun diploma wanda yafi wata yana lissafin kudin dazai kashe kafin yakai ga maida kudinsa yana jinjina maqudan dukiyar da zai samu daga manyan dealers din na qwayoyi da akace suna sakarwa matayensu da iyayen matansu.

Ita benazir kai tsaye Wani hamshaqin drugs dealer dake zaune a lagos da qasar Germany ana tallata masa hotonta yace ya amsa aurenta sbd dari bisa dari tayi masa dan haka ita take yafara yiwa Ababa barin kudi dan haka koda Ababan ya dawo dag lagos ita take aka sauya mata karatun da zatayi zuwa degree.

Cikin saa Tana rubuta jamb taci Admission dinta bai wani zama wahala ba sbd komai acikin saa ta rubuta taci.

Sumayyah ma kusan komai nata ya kammala itama Aminin Ababan Alhaji Sadau shine ya gabatar musu da komai aka jira lokacin fara karatun nasu.

A rayuwar quncin da suke ciki babu abinda ya sauya saima qaruwa sbd duk ya kallesu a yanzu tsagwaron dukiyarsa yake musu kallo dan kuwa kudin daya kashe a shigar dasu makaranta jin yake idan kudinsa basu dawoba ko qasar qetare sai yaje ya nemo masu siyan bayi sun siyesu an basa kudinsa.

Tsananinsa akansu ya qaru fiyeda ko yaushe sbd wasu irin dokoki da tsananin daya dora musu akan ko kallon wani namijn sukai a waje wallahi saiya maidasu makafi dan babu wadda bai gama jingar aurentaba ga wainda zasu maida masa asararsa.

Maganar kula kowane irin namiji a waje ko makaranta ya tsayar dasu ya maimaita musu kusan fiyeda yanda yake maimaita musu qiyayyr dayake musu,

Daga qarshe yayi musu alqawarin binne uwarsu da rai duk ranar dayaji koya gan dayarsu tareda wani.

Hankalinsu tashi yayi da maganar dan kuwa sai tsoron karatun gabaki daya ya shigesu sukaji basa shaawa musamman daya shimfida sabuwar dokar duk wahala da aikin gidan akan uwarsu zai koma duk suna fita harsai sun dawo. #MAMUH# #LOVE #QADR #MARRIAGE #BILLONAIRES KAANTES# #BENAZIR ABABA #ROMANCE#

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 09033181070 09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

_Arewabooks@Mamuhgee 7_

Wani babban tashin hankali mafi tsoratarwa da Benazir ta shiga bayan wasu shekaru shine fara lura da sumayyah data fara samun ciwon qwaqwalwa kaman Annensu sbd lokuta da dama haka zata zauna tayi shiru ta qurawa guri daya ido tana magana a hankali kokuma ta ringa kuka a hankali tana kiran sunan Ababa dana samirah sbd Safnah haka kawai Allah ya cire musu ita cikin ransu sbd abinda tayi din kafin guduwarta wanda kuma guduwar naya ya sake tsanananta musu komai daga gurin Ababa din.

Azabar dasuke ciki da qunci yayi nasarar taba qwaqwalwanta kaman mahaifiyarsu, Wace qaddara mai girma ce wannan ta hau kanta? Tayaya zataji da wannan masifar? Ya zatayi da sumayyah din? Tayaya zata ringa boye wannan lamarin?sbd komai tsananin tsanani bazata iya bari Ababa ko hande su san da wannan sabuwar qaddarar ba sbd Ababa komai zai iya aikatawa akanta sbd ganin itama tamkar wata asarar ce zaiyi na dukiyar daya kashe akanta.

Zubewa tayi tsakiyar dakinsu ta fashe wani irin kuka mara sauti dayake yankan kirjinta sbd tausayin kanta danasu sumayyah da Annen, Inama itama zata haukace gabaki daya ta yanda zata dena jin radadi da kuncin dayake ranta ta manta komai.

Sumayyah dake zaune shiru tana magana ita daya a hankali ganin benazir din a hakan yasata tasowa ta dawo gurinta tana rungumota muryarta a hankali ba kuzari tace "Benazir kuka kikeyi nima na fara samun matsala ko? Karki damu nima mutuwa zanyi idan na mutu komai zaizo miki da sauki zaki iya samun damar dauke Anne ku tafiyarku ko bara kuyi zakuji dadi a gaba insha Allah... Girgiza kai Benazir tafara hawayenta na tsananta gudu bata iya cewa komai sbd matukar Sumayyah ko Anne a yanzu ta sake rasa daya itama nata lokacin na zaucewa tayi.

Hawaye ne suka gangarowa Sumayyah ta sake rungume Benazir din jikinta cikin rauni da mutuwar jiki tareda sarewa tace"

Benazir nima banason na haukace ko na mutu amma da alama kaddarata ta haukacewan kafin mutuwar a kusa take,

Kuka mai sauti Benazir ta kasa riqewa ta fashe dashi tana cusa kanta cikin tafin hannuwanta dukkanin zuciyarta na karyewa dan Allah ya sani a jininta da tsokan zuciyanta take jin Sumayyah, Itace qanwa sumayyah din ce yayarta amma a gareta kaman sumayyah din ce qanwa sbd jin takeyi alhakin kulawa dasu a ynzu duka a kanta yake.

Ita kanta sumayyah kukan mai sauti ta sake tana yin qasa da kanta sbd sanin lalura zasu zamarwa Benazir itada Anne dan haka har cikin ranta take rokon Allah idan zata zamewa Benazir 'dinta da Annensu kaddara mai wahala da nauyi Allah ya dauki ranta ta huta.

Kaman Benazir tasan adduar da Sumayyah din keyi ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Sumayyah kafin ta kalli Annensu dake gefe tana kallonsu cikin tsananin kukan da itama take rokon Allah ya dauki ranta idan har 'yayanta zasu samu 'yancin guduwa daga ukubar mahaifinsu su samu kyakkyaqar rayuwa a waje.

Ahankali Benazir din ta bude baki muryarta a shaqe sbd kuka tace"

Insha Allah zamu rayu a tare mu sauyi a tare Idanma mutuwar itace hutu garemu duka Allah ya kawo mata ita gabaki daya mu tafi garesa mu huta.

Sunkuyar da kai sumayyah tayi tanajin kaman itace kaddarar Benazir a yanzu sbd halin datake neman sakata na dawainiya da ita.

Benazir ganin naz tashin hankalinta akan lalurar sumayyah din na neman qarasa taba qwaqwalwanta dan haka ta sakawa kanta juriya ta danne ta nuna mata ba komai bane babu abinda yake samunta lafiyanta kalau hakama qwaqwalwanta lafiyanta kalau.

Hakan yasa kaman yarinya qarama sumayyah din ta yarda ta sake suka koma rayuwar wahalarsu a tare harda Annensu sbd sun gano a yanzu hadin kansu da girman kaunar dasu kewa juna shine qarfinsu.

A duk kowace rana kafin fitan Ababa sai maimaita musu gargadinsa mai tsoratarwa akan kada ko a tsautsayi su kula kowane namiji a makaranta ko a hanya.

Wannan gargadin nasa kusan kullum yayi sa sai sunji hankalinsu ya tashi saidai daman babu wata niyar kula kowa a ransu bare dasuka tabbatarda maimaicin gargadinsa akan maganar na nufin komai mai muni zai iya faruwa idan makamancin hakan ta faru.

****wannan dalilin ne yasa suka kama kansu acikin dubban mutane fiyeda kowa a makaranta,

Sun fara zuwa makaranta tamkar mujiyoyi acikin mutane ahakan suke zuwa su dawo,

Basu taba qara mintina ko biyu ba da an tashi suke dawowa gida sbd aduk lokacin da suka saka qafa suka fita Azabar Annensu ke farawa dawowarsu da wuri shine samun saukin azabarta dan haka da an fito lectures basa bata lokaci da sauri suke dawowa.

Da haka Ababan ya riqe lokacin dawowarsu kan lokaci batareda magana ba idan sun dawo Annensu ta huta idan basu dawoba tana cikin wuya.

Da zasu fara karatu Hande yabawa kudi ta siyo musu atamfo masu saukin kudi kusan guda biyar biyar sai jallabiya masu saukin kudi suka kusan guda uku uku shikanan sai mayafai biyu da hijab biyu kowannensu sai takarma daddaya.

Ahaka suka fara karatun cikin taka tsantsan da tsoro da fargaba, Babu wani mutum daya dasuke hulda dashi a makarantar kaman yanda basa yarda ko bada fuskan ayi hulda dasu.

Sumayyah fara shigarta cikin mutane sai yake kokarin bayyanarda matsalarta ta cikin qwaqwalwanta a fili sbd a duk lokacinda ta shiga mutane sai take jin kanta na juyawa, Sam tunda suka fara karatun bata wani gane komai sam sbd mummunan sabon da Ababa yayi musu bata iya shiga mutane tafi son zaman gidan.

Benazir kuwa sosai ta maida hankali ta qwallafa rai a karatun sbd samun Abin tsira daga mahaifinsu da yardar Allah saidai kuma yanayin Sumayyah yafara hanata kwanciyar hankali a yanda ya kamata a karatun.

A duk lokacin suka fito suka zo makaranta hankalinta yakan rabu biyu ne akan sumayyah da karatun,

Tin tana boyewa cikin kama kai daga kowa har kusan anfara ankarewa da Sumayyah din na dan da tabin kai duk da ba laifi wani lokacin takan gane karatu harma da tambaya. Ahaka suka ringa lallabawa suna karatunsu cikin kame kai daga wulaqanci da tazarcin mutane dasuke samu.

A gida kuwa idan sun daga daga makaranta babu wani sauyi daga rayuwar dasuka saba saima qari dan yanzu ganin yakeyi dukiyarsa suke ce fiye da baya dan haka a yanzu har shagon sanaar wankau ya bude wadda idan ankawo sune suke yi saidai acan shagon ayi guga a hada a leda a bayar idan masu karba sunzo dan haka yanzu wahalar taketa sake qaruwar musu sbd wankin kayan maza wani Abu ne mai tsananin wahala garesu sbd nauyi musamman manyan riguna wanda sai sunyita wankinsu kusan so uku kafin su wanku sbd sunfi qarfin hannuwansu rigunan.

Basu taba nuna gajiya ko wahalarsu a fili ba sbd babu abinda hakan zai haifar sai qarin azabar dan haka suke rayuwarsu a hakan.

A makaranta akwai wainda da yawa suke shaawar mu'amalantarsu sbd kame kansu sai yake nuni da kaman tarbiyace da suke da ita amma rashin fuskarsu da kamewarsa tareda tsoron shiga mutane dasuke a fili yasa baa tinkararsu.

Yanayin fatarsu mai duhu da kyau ga kamanninsu dasuke kusan daya ga kyan jiki na mata mai kyau da daukan hankali da Allah yayi musu yasa aka dan fara Ankara dasu wanda da basa kame kansu da tini sunfara tara samari da abokai barkatai.

*****A haka lokaci ya gangara dasu har suka gama session daya kuma babu wani sauyi ko daya bayan na Ilimi da wayewar dasuke samu cikin mutane Hakama sumayyah ta fara sabawa tini da rayuwa cikin mutane kuma a hakan bawai ta warke ko samun saukine ba kwata kwata Benazir ce a gurin kulawa da ita sosai tana kaffa kaffa kada Ababa ko hande su gane gashi Annensu a yanzu rayuwar tafi yi mata tsanani dan harsu je su dawo tana kan qafafunta tana aiki bata hutaba ko na daqiqa daya.

Results dinsu na exams na sumayyah ko kadan baiyi kyau ba duk da bata fadi duka ba amma kusan fiyeda rabi duka ta fadi, Ababan bai wani damu ba sbd shidai iya ilimin yakeson su samu da turancin bawai cin jarabawa ba da sakamako mai kyau sam babu matsalarsa da wannan amma dik da hakan saida yayi mata dukan data kusan sati bata miqewa daidai harda Annensu da benazir ya hada duk da ita nata sakamakon yayi kyau matuka sbd babu course daya data fadi.

********Sun kammala hutunsu sun koma session na biyu wanda ita sumayyah ba dan rashin kyan sakamakon ta ba da session dinta na karshe ne tun karatun 2years ne.

Dawowarsu hutu yasa sumayyah takura qwaqwalwanta gane karatu sbd Azabar data ringa sha daga Ababa tin daga farkon hutun har qarshensa gashi harda Annensu da Benazir yake hadawa kaman jakuna haka yake binsu kullum ya musu duka ga fucewarsa.

*****Sumayyah yau tsaban azaba har yamma takai makaranta wata abokiyar karatunta da itama bata ganewa irinta suka kai sunata bita suna takura qwaqwalwanrsu har Allah yasa suka gane abinda suke son ganewa tabiyo hanyarta tabi ta department dinsu Benazir wadda tasan bazata taba tafiya ba bata jurata ba.

Sauri takeyi hankalinta a tashe sbd tasan Yau sai Ababa ya yanki naman jikinsu ya zubar a bola sbd kusan anfara kiran magrib.

"Excuse me,Aslm alkim" taji anfada daga bayanta kusan gab da ita A hankali ta dakata tareda juyowa zuciyarta na bugawa kaman zata fado sbd tsoro jin muryar namiji Abinda tafi tsoro a komai duniya yanzu shine wani namijin ya mata magana.

Wanda tagani ne yasata neman rasa numfashinta sbd tsananin tsoro da rudewa tareda firgici mai tsananin gaske. Rawa qafafunta suka dauka ta juya da sauri zata wuce batareda ko sallamarsa ta amsa ba dan tabbas batajin ma da ita yake.

Da kallon mamaki ya bita da Id card dinta a hannunsa yana dan yamutsa fuskar kalau take kuwa, Ta gabansa ta zubarda id card din bata saniba ya dauka ya miqa mata amma ta wucesa kaman wadda taga abin tsoro.

Isowar professor Abdallah gabansa fuska a matukar sake da zallar girmamawa yana cewa"

BILAL KAANTE you are highly welcome Sir.

Wani qayataccen murmushi ya saki tareda saka id card din aljihun wandon tsadaddiyar yadin dake jikinsa ya miqawa prof Abdallah din hannunnsa mai haske da taushin hutu yana cewa

"Thanks prof, Bazan dauki time dinka da yawa ba time ya shige sai gobe zan dawo muyi magana insha Allah Nazo ne sbd nayi maka alqwarin zuwa din yau din amma wanj aikin ne ya dan riqe ni."

"Ba komai zan jira ka goben idan kuma zan sameka a Kaante ne duk ba damuwa tinda nasan abubuwan nada yawa a gabanka"

"No karka damu insha Allah zan samar da time din nazo gaben"

Juyawa yayi prof din na biye dashi suna magana har zuwa ina wata lafiyayyar tsadaddiyar motarsa ta Lexus take black yana bude securityn motar prof yayi saurin bude masa yana ce masa

"A sauka lafiya Sir"

Ngd yafada a hankali cikin nutsuwarsa da Allah yayi masa ta rashin garaje ga komai.

Yana zama cikin motar ya prof ya rufe masa ya tada motar a hankali ya fice daga makarantar yana duba time na gold Agogon rolex dake hannunsa sai kuma a lokacin yaji Id card din dake aljihunsa ya saka hannunsa daya ha ciro tareda kallon fuskarta yana karanta sunan Dake rubuce a id card din SUMAYYAH ABABA.

Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiye card din gefensa a hankali yana maida hankalinsa kan tuqin dayake yi. #MAMUH# #BENAZIR ABABA #DD KAANTE# #BILAL KAANTE# #LOVE#MARRIAGE#ROMANCE# #HOTLOVE#LIFE#FAMILY#CHILDSLOVE#

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 09033181070 09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

_Arewabooks@Mamuhgee_ 8 Hankalinsu duka baa kwance ba suka isa gida saidai cikin saa har lokacin Ababa bai dawo gida ba Hande ce kawai taketa fadan sun samu sake sunyi dare babu wanda yayi magana acikinsu saida tagama yi musu tatas kafin suka hanzarta yin sallah suka fito suka karbarwa Annensu aikin da bata gamaba har lokacin.

Wani sabon wankin ne suka fara cikin dare basu gamaba sai guraren karfe tara na dare Daqyar sukai sallah sukaci dan abincin da aka basu suka kwanta kowannensu gababin jikinsa na ciwo.

Washe gari haka guraren 9 na safe suka isa makaranta. Sumayyah kai tsaye libry ta isa sbd acan zasuyi karatu da wadda sukai jiya, Tana isa zata shiga ta nema id card dinta ta rasa, Gefe ta koma ta zazzage jakarta tafara dubawa hankalinta na fara tashi sbd batasan ya zatayi ta samu wani ba komai Benazir ce take yi mata bata iya zuwa da kanta.

Dubawa takeyi da gaske tana bin pages damuwarta na bayyanuwa duk da tanada tabbacin yana jakar bata fiddasa ba. Duk abinda yake jakar tayi masa daddaya amma bata gansa ba, Tattara kayanta tayi ta maida jakar ta nufi gurin Benazir cikin dan sauri da damuwa,tsoronta da tashin hankalinta shine ace sai ka biya kudi zaa maka wani, Ina zata samu kudin?Ababa idan suka fada masa saiya kusan rabata da duniya kafin ya bada kudin,ya Allah yasa ta gansa kokuma baa biyan kudi ake bada wani.

A yau dinma tashin hankalinta bai bari tana tantance inda take saka kafafunta ba kanta a qasa har ta isa department dinsu Benazir din.

Kiris ya rage tayi karo da wanda yake tahowa yana amsa waya cikin nutsuwa da sanyin hali Da sauri ya dago hannuwansa yayi saurin tareta sbd kada jikinsu ya hadu.

A firgice ta dago tana ja da baya cikin qarfin gaske sai gata a qasa Bata damuba ta miqe da sauri kanta na yin qasa a sanyaye ta basa hakuri tana sake sauke kai kaman wadda take gaban Ababa.

Cikin dan mamaki ya kalleta yana tabbatarda itace mai student id card din hannunsa, Juyawa tayi zata wuce batareda ta dago ta kallesa ba zuwa lokacin jikinta rawa yakeyi sosai dan gabaki daya Azabar Ababa kawai take jin har tafara sauka jikinta.

"Hey Miss" yafada da muryarsa mai kamala yana taba Aljihun tsadaddun qananun kayan givenchy dake jikinsa baiji card din ba ya dan rintse ido a hankali yana tino yana cikin motar daya shigo makarantar jiya da ita. Ba damuwan komai a ransa ya ambaci sunanta kai tsaye daya tina shine a jikin katin ganin tana sake sauri kaman mai tsoron mutane a bayyane sai kawai ya qyaleta ya wuce yana duba time din agogonsa sbd ba lokaci zai bata ba a school din zaiyi magana ne kawai da prof ya wuce gurin aikinsa.

Yana wucewa Sumayyah data labe daga gefen wasu students ta futo tana kallon inda yabi da ido tsoronta na qaruwa sbd ta tina fuskarsa shine ta gani jiyan ya tsaidata. Meyake so a gurinta? Baiyi kama da student ba sbd shekarunsa da jikinsa tareda maturity dinsa sun bayyanarda hakan, Kyawunsa da kwarjininsa tsoro ya bata matuqa tareda firgitata,babban tashin hankalinta kada ya sake tsayar da ita wani yagani tsautsayi yasa Ababa ya sani Alkiyamarta ta tsaya.

Benazir data qaraso gurinta tana dafata daga baya saida sumayyar takusa shaqewa sbd tsoro da tashin firgita,tana waiwayowa taga Benazir ce wasu hawayen mutuwat jiki suka ciko idanuwanta ta sauke tana kokarin hanasu saukowa.

Benazir data ga hakan hankalinta ya tashi cikin mamaki qasa qasa sbd kar ajisu tace"

Me yafaru? Ababa yazo nan ne? Wani abu yafaru ne?

Kasa magana sumayyah tayi ta silale ta zube zaune kan gurin zama tana kokarin daidaita numfashinta dayake futa da sauri na tashin hankali biyu datake ciki na batan student id card dinta dakuma mutumin daya tsayar da ita wadda sunfi kaunar hadarin mashin da wani namiji ya tsaidasu. Shafa bayanta Benazir ta ringa yi ahankali ta cikin hijab dinta tana cewa

"Ki kwantar da hankalinki kada ki bari yanayinki ya sauya asan halinda muke ciki kaman yanda Ababa yafada mana."

A hankali ta ringa sauke numfashi tana kokarin daidaito nutsuwarta har tsowon mintina kafin ta dan dawo daidai ta dago idanuwanta da har sunyi jajir ta kalli Benazir dake jiran bayaninta cikin fargaban idan ba wani abin ne ya sameta ba.

Readers Also Read