Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 5

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 5

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 5: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 5. Bude baki tayi ahankali ta yiwa Benazir din…

3,242 words

Bude baki tayi ahankali ta yiwa Benazir din bayanin batan student id card dinta tareda kasa fada mata mutumin da yayi mata magana sbd tinowa da hakan kawai girgiza kayan cikinta da zuciyarta yake bare iya bude baki ta fadawa ko Benazir cewan wani namiji ya tsaidata.

Shiru Benazir tayi sbd itama batasan ta ina zara fara ba tunda ba muaamala sikeyi ba da mutane bare su tambaya qarin bayani.

Shiru sukayi sun jima a hakan batareda sanin abin yi ba,ganin hakan Sumayyah taji gabaki daya hankalinta ya qara tashi suka fito daga department din suka nufi gurin da babu mutane sosai suka zauna take Sumayyah ta fashe da kuka mara sauti tana jin yanda zasu sanar da Ababa hakan.

Shiru benazir tayi itama jikinta na mutuwa sbd tasan bawai tsallakewa zatayiba itama hadasu zaiyi ya musu hukunci daya. Kasa cewa Antyn tata sumayyah ta dena kuka tayi sbd batasan wane qwarin gwiwar zata bata ba dan haka sukai tsit sai kukan sumyayah da ita kadai ce take jin sautinsa.

Basu san zaune suke gefen wata lafiyayyar black beymack ba saida mai motar ya doso gurin kai tsaye idanuwansa akan Sumayyah wadda idanuwanta sukai jajir jikinta yai sanyi gaba daya.

Kallo daya Benazir tayi masa tayi qasa da kanta bugun zuciyarta na tsananta tareda wata irin fargaba mai tsanani wadda ta sanya numfashinta fita da sauri saidai tinda tayi qasa da kanta bata dago ba.

Shi kuwa sumayyah data qarasa rikicewa da ganinsa yake kalla mamakinta na sake kamasa sbd kai tsaye ya gane tsoron maza takeyi kokuma irin tarbiyar da aka bata ne daga gidansu.

Tsoro ya hana sumayyah dauke idanuwanta daga kansa hannuwanta dake qanqame da jakarta suna rawa.

Kasa shiga motarsa yayi sbd zuciyar kulawa da tausayi tareda sanyi da Allah yayi masa fiyeda kowa a familynsa ya juyo ahankali cikin nutsuwa ya dawo gabansu ya tsaya murya a kamale yacewa sumayyah

"Student id card din ki na gurina nayi kokarin baki a jiyan amma baki tsaya ba, Yau kuma ban fito da motan dana barsa ba a jiyan amma insha Allah gobe zan sake shigowa wani abin zan taho dashi ki jira ni anan around 4 haka lokacin na shigo sai na baki"

Daga sumayyah din har Benazir a tare suka dago suka kallesa suna masa wats irin godiyar data bayyanar da fadawar tashin hankalinsu.

Da mamaki ya zubawa Sumayyah idanuwansa masu haske yana cewa "Kina kuka ne sbd Batan card din ne?" "Are you for real? Share hawayenta ta hau yi tana sauke kanta qasa daga idanuwansa dasuka fara firgitata.

Kamanninta da Benazir yasashi fahimtar 'yar uwarta ce kuma kusan halinsu daya na rashin iya kallon mutune da alama itama tsoron mazan takeyi. Wani gajeran murmushi ya saki tareda bude motarsa ya fada ya tada tabar gurin yana kallansu ta mirror harya bace basu dago sun kalla inda yabi ba.

Ajiyar zuciya Sumayyah ta ringa saukewa a jere tana jin sanyi na mamaye zuciyarta data kusa bugawa da tsoro. Tashi sukai suka koma kowannensu ya nufi gurin da zaiyi lectures basu koma gida ba sai 6 saura. Suna isa sallar magrib kawai sikai sika fito aikin wanki saida suka gama aka basu abincinsu suka zauna sukaci tareda Annensu dake dan fama da zazzabi kwana biyun sbd yammacin dasuke kaiwa aikin na mata yawan dayafi karfinta.

Basa karatu gida ko sun dawo sbd basuda abin haskawa haka suke hakura duk yanda sukazo karatu musamman sumayyah datakeson Benazir din ta ringa dan wayar mata da kai akan wasu kalmomin.

Washe gari tinda suka wayi gari sike cikin faduwar gaba da fargaban yanda zasu tafi gurin wani namiji karban student id card din na Sumayyah, Sumayyah tafi Benazir din shiga tsoro da fargaba sbd itace tayi sakacin yar da card din hakama saninsu ne Ababa wasu lokutan yana sakawa ana bibiyarsu dan haka sike cikin fargaban.

Har sika isa makaranta babu mai walwala ko nutsuwar zuciya, Haka sika wuni ba sukunin rai har 4 din tayi sika isa inda yace din suka tsaya suna waige waige ciki fargaba. Sam hankalinsu bai kwanta ba da haduwar dan haka a matse suke kusan mintina ashirin kafin motarsa ta danno kai a gurin dan shi tini ya manta dasu din saida ya qaraso gurin ya gansu tsaye ya tina Allah yasa da motar yazo.

Yana parking tin bai fito ba ya ciro card din ya miqa musu ta window Hannu biyu sumayyah tasaka ta karba batareda ta dago ba cikin girmamawa mai tsanani sukai masa godiya kaman wanda yayi musu wata babbar kyauta.

Mamaki suka sake basa tareda birgesa musamman sumayyah wadda Sanyinta da rauninta dayake bayyane yafi basa tausayinta da burgewa.

Juyawa sukayi suka bace bat daga gurin qafafunsu na sarkewa.

Saida suka bacewa ganinsa kafin kowannensu ya saki boyayar ajiyar zuciya basu cewa juna kala ba suka tinkari hanyar ficewa daga makarantar zuwa gida.

Saida suka isa gida suka shiga dakinsu suka zauna kusa da Annensu hankalinsu ya kwanta daidai suka sake ajiyar zuciya a tare batareda sunyi yunqurin zantawa akan komaiba game da lamarin batan id card din gaba daya.

******kaddara zaace ko tsautsayi kokuma rabo? Haduwar sumayyah da Bilal kaante daga wannan lokacin sai ta zama kaman wainda ake turowa dan kuwa kusan babu ranar da zai shigo makarantar Allah bai qaddara haduwarsa da sumayyah ba wadda tsoro da firgicin datake shiga a duk lokacinda zata gansa yake sake qarfafa masa tinanin hulda da ita dan kuwa nutsuwarta da kamala tareda tarbiyarta a bayyane take, Rauninta kaman wani abin birgewa ya zama garesa dan kuwa hawayenta a kusa suke A kwai ranar daya tsayar da ita ga mamakinsa hawaye yaga suna gangaro mata sai hakan ya sake sakasa tinani da kwadayin son saninta a ransa. #MAMUH# #DD KAANTE#BENAZIR# #LOVE #MARRIAGE #ROMANCE# #BILAL KAANTE#SUMAYYAH#

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 09033181070 09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

_Arewabooks@Mamuhgee_ 9 Sumayyah tsananin tsoro da tashin hankalin yanda mutumin yake tinkararta kai tsaye lokuta da dama idan suka hadu a hanya yasa ciwon damuwa da tsoro mai tsanani suka shigeta, Ta fadawa Benazir ma ta kasa, tsoro da fargaba takeji dan haka daga karshe saita dena fitowa kwata kwata daga hall din lecture dinta idan tashiga, Wannan matakin data dauka yasa ta dauki lokaci mai tsayi bata sake haduwa dashi ba har tafara mantawa da lamarinsa gabaki daya ta koma tana fitowa kaman yanda ta saba.

Ta nasa bangaren Bilal kaante kasa mantawa yayi da ita musamman yanzu sbd ita din yake dan shigowa gurin prof duk da prof dinne ya kamata ya ringa zuwa yana samunsa sbd matsayi da karfin power tareda tarin Asalin dukiyar dasuke dashi Kaante Family harma da suna.

Rashin ganinta kwana biyu ya fahimci da kanta take boye kanta din sbd shi dan haka shima sai bai takurata ba a boye yafara bibiyarta yayi bincike akanta ya fahimci Mahaifinsu mai tsanani da zafin gaske ne hakama yanada tsaurin hukunci amma sam bai samu sanin irin halin da rayuwarsu take ciki ba a karkashin mahaifin nasu sbd wata rayuwa ce da babu wanda yasan asalin balai da ukubar dasuke ciki iya tsananinsa kawai aka sani sai Aikin wahalar dasuke yi musamman na wankin qattin mazan dasuke masa na shagon shagon wankin daya bude babba.

A qanqanin lokaci da gajeran bincikensa ya dan fahimci rayuwar tsanani suke ciki sbd ko a yanayin rayuwarsu zaka iya fahimtar basa rayuwar 'yanci da sakewa sai yanda akai da rayuwarsu.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan kwanaki yana yawo da tinanin rayuwarsu yana bibiyarta daga dai ya tabbatarda tausayinta ne tareda soyayyarta suke shigesa abinda bai taba faruwa dashiba soyayyar wata mace bayan ta mahaifiyarsu da qanwarsu qwalli daya dasuke uwa daya wadda itama DD ne ya saka masa kaunarta mai tsanani sbd yanda duk tsananin zafinsa daga Mammah sai Zeenah din yake ragawa a duniyarsa da babu kowa acikinta bayan kebe kansa daga yan uwa da familyn nasa.

Bilal Sumayyah ta shiga zuciyarsa cikin sanyi da nutsuwa, Yanajin sonta na qarfafa zuciyarsa saidai kuma damuwarsa ta yanda bazata samu karbuwa a familynsa Ba dan fitowarta daga ahalin da ba kowa ba kuma basuda abinda shi a nasa familyn ake kira Girma maana kalman nan ta kwarya tabi kwarya,

KAANTE family wani babba,sananne,attajiran family ne da ake kiransu da billionaires wasu kuma su ce musu the family of power. KAANTE's Sun kasance wasu irin sananni dasu hada,fame,wealth,power harma da lokaci da Allah ya basu sam an kasa samun wanda ya wucesu ko ya fisu, Idan akwai wanda zai iya tsayawa gaban KAANTEs din ya nuna musu isarsa da zafin kai a duniyarsu to DD KAANTE wato DAWOOD DAUDA KAANTE,wanda yake 'da kuma guguwar da ita kadai take girgiza familyn batareda sun iya yin komai ba akai haka shine kadai yake tsayawa gaban duk wanda zai kawowa familyn Hayaqi batareda batawa kai lokaci ba.

Tayaya zai iya gabatar da Sumayyah ga familynsa a matsayin wadda yake so da kaunar mallaka. Kusan shine babba a familyn dan haka sunada high hopes akansa na auro macen data dace da matsayinsu, 'Yar babban gida,wayayya 'yar boko mai zurfi ilimi da class kaman yanda duka sauran mazan familyn suke auro matayensu. Tayaya zai fara dan shi dai zuciyarsa tayi naam da sumayyah bayajin zai ja da baya saidai kuma fargabarsa bata gushe ba saima qaruwa datake yi.

*******Sumayyah data manta dashi sukaci gaba da rayuwarsu kaman mujiya acikin mutane suna sake maida hankali ga karatunsu ahankali ciwonta yafara dawowa sosai kaman qwaqwalwanta zai juye gabaki daya sbd yawon makarantarsu yanda yake cin kudin Ababa yasa Ababan ya tsananta musu azabarsu da wahalarsu sun koma yanzu so daya ake basu abinci hakama aikin wankin shagonsa harma da guga yanzu sune sukeyi ga aikin gida ga aikin sharewa da wankewar gurin dabbobinsa masu yawa da tsananin qazanta ga nasa wankin gana Hande ga girki da wanke wanke gashi komai qanqantar laifi duka suke sha sbd tsananin kiyayewarsu yasa ya dena samun dalilin dukan nasu kaman jakuna shiyasa yanzu komai qanqantar lefi yake sauke gajiyarsa akansu da duka.

Basa samun lokacin karatu ko kadan sai ya zama makarantar ma idan sunje yanzu kusan daqyar Benazir ke ganewa Sumayyah kuwa sam ta dena ganewa wasu lokutan ma magana takeyi ita daya ana lectures sai hakan yasa mutane suka fara ankara da kaman tana matsalar juyewar kai, Tin maganar na yawo iya tsakanin course mate dinta sai maganar ta fara yaduwa har gurin da baa zato Sai abin yafara zama kaman ana tsokanarta ana nunata akan tanada juyewar kai.

Tin tana daurewa tana nesanta kanta da mutane sosai har abin yafara yawa ko inda mutane suke bata iya zuwa sbd yanda ake mata kaman mai ciwon hauka sosai.

Tayi kuka,tayi kuka,tayi kuka amma babu wani sauki ko sassauci, A hankali karatun da makarantar suka fita randa da kanta gabaki daya musamman da mutane suka gano bata gane komai na karatun, Abin tsokana ta zama a gurin dalibai yan uwanta batada me tsaya mata kuma tunda taga matsalarta tasa rayuwar Benazir ta juye gabaki daya itama yanzu karatun nata yafara lalacewa tare suke zuwa can baya gurin da babu mutane suyi kukansu babu mai iya rarrashin wani su gama su dawo babu mai iya kallonsu da daraja saima aka saka musu wani sunan tozartawa MENTALS.

A gida babu daman su bari Ababa yaji abinda yake faruwa zai iya kusan kashesu dan haka kullum da Annensu suke zaunawa tsakar dare sukai kusan asuba suna kuka babu mai iya magana bare rarrashin wani idan sukai suka gama saisu kwanta wani lokacin kuma alwala suke yowa suyi nafila suyita kaiwa ubangiji kukansu, Rayuwar gidan tin shekarun dasuka gabata suka manta da cewan basu kadai bane 'yayan Annensu sbd Tini Sunayen su Safnah suka zama shafaffen tarihi a gidan shi kansa Ababa tini ya manta dasu daga rayuwarsa har mantawa yakeyi da ba iya su Benazir da sumayyah ne kadai aka haifa da sunansa ba.

*******Exams dinsu ta matso sosai dan haka hankalinsu su duka ya tashi musamman sumayyah data san Alqawarin Ababa na cewan saiya karya qafarta da hannunta idan ta sake faduwa jarabawa dan haka gabaki daya ta fice hayyacinta a kwanakin bata rintsawa kwana takeyi a zaune tana karatu amma babu kalma ko daya datake shiga kanta kaman an rufe qwaqwalwanta da kwado.

Benazir ajiye nata karatun tayi kullum na Sumayyah din sukeyi tana kokarin koya mata amma babu wani motsi ko daya, Data ga lokaci nata qurewa babu sauyi sai kawai takoma tana skipping lectures dinta tana shiga nasu sumayyah din dayake suna kama sosai sai lecturers din basa wani ganewa students din kawai ke ganewa sai suka ringa tsokanarta suna cin mutuncinta itama amma bata taba dago kai ta kallesu ba.

Sosai hankalin Benazir yasake tashi data gama fahimtar abinda take tsoro ne yake tabbata wato irin ciwon rasa hankalin Annensu sumayyah ta kamu dashi wanda tsananin depression ne yake haifar musu dashi yakaisu ga wannan lalurar.

Gabaki daya mutuwa jikin Benazir yayi ta rasa tata nutsuwar da tinani harma da kusan nata hankalin itama tafara rasawa sbd wannan babbar masiface da tashin hankalin da ita kadaice zai kashe dan kuwa daga sumayyah har Anne kusan kashesu ne bazaiyiba sbd azaba, Idan ya bar Annensu gidan duk da haukarta sbd ya ringa juya rayuwarsu yanda yakeso ita sumayyah bazai taba barinta gidansa ba sbd babu amfanin da zata masa,bazai tsaya komaiba zai rabasu da ita yakai bola ya yar babu ruwansa da hadarin hakan ga budurwar data girma sosai.

Wannan tinanin ya sanya rayuwar Benazir ga mummunan hadarin datake gab da rasa nata hankalin itama, Ita kanta yanxu dataga gaskiar lamarin sumayyah addua takeyi da fatan nata hankalin ya gushe Ababan ya tattara su su biyun da Annensu ya watsar bola indai zasu rayu a tare.

Gugar kayan dasuka wanke suna dawowa sukeyi sbd Ababan yace da safe masu kayan zasuje karba shago dan haka tinda suka dawo suke wankin basu gama ba sai bayan ishai dayake ana iska sosai kayan sun bushe da wuri karfe biyu da mintina arbain suka tashi suna goge kayan.

Sumayyah da bata gane komai yanzu sosai tana farawa tabar iron din kan kayan data fara gogewa tana dan bubbuga kanta da hannu tana kiran sunan kanta dana benazir din kaman me fira da wasu.

Hayaqin konewar kayan yasa Benazir data duqufa tana goge kayan da sauri sbd suje su kwanta tareda Annensu ta dago da sauri ta dauke iron din kan kayan tana kallon kayan jikinta da daukan rawa gabaki daya zuciyarta na neman dakatawa daga bugawa.

Kallon Sumayyah tayi da idanuwanta dasukai ja take sbd tashin hankali taga sumayyah din itama kayan take kalla jikinta na wani irin kyarma tana neman ficewa hayyacinta kanta na neman juyewa gabaki daya sbd tsananin firgici da tashin hankali mai tsanani.

Ganin tana fisga tana neman buga kanta da qasa Benazir tayi sauri ajiye iron din ta kamota ta rungume tana hanata bayyanarda matsalar tata dan kada tsautsayi yasa Ababa ya gane ko Hande.

Fisga Sumayyah keyi sosai tana kokarin kamo iron din daya kona kayan matsanancin tsoronta na bayyanuwa a fili duk da tana samun gushewar hankali lokuta da dama amma sam tsoron Ababa daya ginu cikin jini da zuciyarsu bai taba gushe mata.

Qaurin wutar kayan ya sanya Ababan dayake palonsa fitowa tsakar gidan idan suke gugar daman baiyi bacci ba sbd wani lissafi dayake yi kusan awanni ya kasa gamawa kusan dama duk ranar daya samu kudi masu dan kauri baya bacci har asuba.

Akan babbar rigar wata farar tsadaddiyar shadda idanuwansa suka Shaddar harta kone iron din ya fasa zanin qasanga harya kona tabarbar datake qasa itama ta cinye daidai shape din iron din gugar.

Benazir na ganinsa ta saki Sumayyah wadda rawar jikinta yai tsananin gaske suka gyara zamansu zuwa kan gwiwarsu kansu na yin qasa sosai babu wanda jikinsa baya rawa mai tsanani acikinsu.

Kayan ya sake kalla fuskarsa na dauke rahamarsa gabaki daya yace

"Uban waye yayi wannan aikin?"

Benazir ce ta dan dago ahankali batareda ta iya kallan fuskarsa ba sbd tsoronsu akansa bazai bar hakan ba ta bude baki zata basa hakuri bai bari ta gama bude bakinba yasa qafa ya shura bakin nata tayi baya ta fada bakinta na fashewa da jini tareda radadin azaba.

Sumayyah qamewa tayi dukkanin wutar jikinta na daukewa numfashinta yafara kokarin daukewa saidai kafin ta fice hayyacinta tafara jin saukan azaba ajikinta tin tana jin dukansa da wani radadi a jikinta har ta dena ji bata sake sanin inda kanta yake ba.

A tsakar gidan suka kwana har asuba Benazir na qarasa goge sauran tulin kayan zuciyarta na tsalle da radadin kallon 'yar uwarta a gefenta some babu daman bata taimako sbd yana zaune har ta gama.

Sanyin Asuba yasa Sumayyah farfadowa cikin tsananin azaba lokacin Benazir tagama har Ababan ya bar gurin da sauri ta ringa daukan kayan tana kaiwa palonsa tana gama kwashesu duka ta dawo da sauri ta kama Sumayyah din da hawaye ke gangarowa daga idanuwanta ahankali,

Miqar da ita tsaye tayi saidai azabar da Sumayyahn taji a tsakiyar tafin qafafunta yasata daka tawa tana rintse idanuwanta suna kasa kallon juna ita da Benazir din. #MAMUH# #DD KAANTE #BENAZIR ABABA #BILLONAIRE #ZAFIN KAI #KAANTEs #ROMANCE #LOVE #LIFE #NOVEL #SUMAYYAH #BILAL KAANTE

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 09033181070 09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

_Arewabooks@Mamuhgee_ 10

*_MAAB LUXURY HOME🔥💯_*

*_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI JAMA’AR ZAFAFA BIYAR_*

*_KAMAN KO DA YAUSHE DA MUKE KAWO MUKU ABABEN AMFANI GANGARIYA KUMA DAKI BARI MASU AMINCI A KUDADE KALILAN_*

*_YAU MA MUN ZO MUKU DA TALLAN BABBAN SHAGON NAN DA KE KAWO MU KAYAYYAKI NA KASAR GERMANY!! KUNSAN DAI GERMANY SUNE AGABA A FANNIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA KARKO_*

*_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_*

*_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_*

*_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_*

*_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_*

*_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_*

*_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM:@Maabluxuryhome_* *_FACEBOOK:@maabluxuryhome_*

*_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_*

*_A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_*

*_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_*

*_08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_*

********** Suna isa dakinsu suka tararda Annensu zaune tana hawaye masu dumi da ciwo sbd duk abinda yake faruwa tsakiyar gidan tana ji amma batada iko ko daman fitowa. Suna shigowa ta bisu da ita batareda ta motsa ba dan batasan me zatayi ba yanda zuciyarta ke radadi.

Zaunar da Sumayyah Benazir tayi tareda zubewa gefenta itama saida sukai shiru kukan Sumayyah kawai ke tashi tsawon lokaci kowa da damuwar datake yankar zuciyarsu. Kusan awa daya a hakan kafin Benazir da Anne suka fito sukai Alwala suka dawo daki kafin itama Sumayyah din ta fito cikin azabar tayi alwala ta koma dakin.

Sallah kawai sukai tareda addua suka fito fara aikinsu gadan gadan harda Sumayyah din sbd baa basu damar hutawa daga aikin ba koda ciwo kuwa.

Readers Also Read