Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 6

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 6

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 6: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 6. Sai guraren 9 suka gama wanda suka iya suka…

3,366 words

Sai guraren 9 suka gama wanda suka iya suka shirya Hande ta basu abincin karyawan da Ababa ya rage sukaci suka fice zuwa makaranta lokacin kusan Benazir harta rasa lecture dinta na 8 to 10 suna isa ta shiga ta 10 to 12 Sumayyah kuwa kasa shiga lectures tayi sbd wani irin azabababban zazzabi mai qarfin gaske daya rufeta, Qafarta wani irin radadi da zogin azaba take mata sbd iron din da Ababan ya wurgeta dashi ya kona tafin qafarta sosai ba daman ta nuna azabar datake ciki a haka tayi aiki kafin su fito gashi zuwa lokacin kafar gabaki daya ta cabe daqyar ta iso makarantar ta nunawa Benazir babu wata matsala ne da qafar sbd ta samu ta shiga lectures nata da yanzu bata samun attending yanda ya kamata amma kam tana cikin mawuyacin hali.

A hankali ta daddafa ta kebe kanta cikin mawuyacin hali ta isa inda suka saba kebe kansu ta zauna jikinta na tsananin rawa ko numfashi daqyar take ja, Dan dago kafar tayi a hankali ta leqa inda konuwar take. Sanyayyan Numfashi ta sake jikinta na sake daukan rawar zafin zazzafi Qafar tini tafara yan ruwa masu maiqo sbd sosai iron din ya shigeta.

Jajir idanuwanta sikayi tana kasa fidda koda hawaye ta samu sassaucin radadin datake ciki cikinta da fili.

Zamewa tayi ta kwanta yashe a gurin azabarta na qaruwa idanuwanta na qanqancewa, Tsawon lokaci ta dauka ahakan kuma kowace daqiqa tana wucewa ne tareda qaruwar azabarta.

Sama sama take jiyo hayaniya da maganganun mutane masu wucewa, Tashi takeson yi ko zata iya kai kanta gurin Benazir sbd ciwon yafara fin karfinta yasha ruwa ne caba caba gurin aikinsu na safe hakama duk ta takesa ya cabar da qafar gabaki daya ya zabure da ciwo baji ba gani.

Daqyar idanuwanta dasuke kanne suka budu tana sake kokarin tashi sedai hakan sam yakasa samuwa Na idanuwanta dake rufewa ahankali tana neman somewa sbd tsanani da zafin azaba.

********Bayan Awa bakwai A hankali ta bude idanuwanta da sukai mata wani irin nauyi sbd baccin wahala da jan azabar dasukai har lokacin basu washe ba. Akan Benazir dake gefenta idanuwanta suka fara sauka wadda itama nata idanuwan suke jajir sbd tsananin tashin hankali biyu dayake dabaibaiye da ita, Na ganin yar uwarta a wannan halin dakuma na zaman dasukeyi a tsadaddiyar private asibitin wanda shi kansa sbd gudun asan halin da yake ciki ya sanyashj kawosu wata asibitin ba KAANTE SPECIALIST, Babban tsoro da mafi tashin hankalinta shine sikai magrib Sumayyah din bata farka ba dan kuwa ko a bayanta ne zata goyata su isa gida kafin magrib din matuqar bata farka ba.

Ganin budewan idanuwan Sumayyah a kanta ya sanyata sake ajiyar zuciya masu karfi a jejjere tareda rintse idanuwanta da sukai jajir Allah ne kawai yasan a tsananin halin data share wainnan awannin tana jiran farfadowar Sumayyah din,

A rayuwarsu bata taba tinanin zasu samu kansu a hali irin wannan ba na zuwa wani gurin neman lafiya kuma a qarqashin kulawan wani namiji wanda ko a tsautsayi Ababa yaji ko ya gano hakan tabbas Allah ne kawai zai ceto su daga mummunan qanin kisar da zaiyi musu.

Daga ita har sumayyah ba da izini ko saninsu Bilal kaante ya dauko sumayyah din ba ya kawo asibiti Seda ya kawota asibitin bayan ya tsinceta a halin datake ciki a some har saida aka gama yimata komai kafin ma ya koma makarantar ya nema Benazir ya sanar mata suka taho asibitin tare wanda wannan shine karon ta na farko shiga mota.

Rayuwarsu basa fita kaman yanda aka sani, Sunyi rayuwar karatun primary da na secondary har sukayi suka gama a qafa suke zuwa su dawo a qafa, Tunda suka gama basa fita koina kullum suna gida a kulle kaman kayan sata, Yanzu da suke jamia bai taba basu abinda zasu hau mota ba kullum a mashin suke zuwa kuma overload sukeyi shiyasa ko daya nada lecture daya dayan nada fiyeda hakan dole suke jiran juna komai dadewan da dayan zaiyi kuwa sbd Ababa bai taba yarda suna dawowa daban daban sbd kudin abin hawan.

Sumayyah data juyar da idanuwanta da qyar suka sauka kan Bilal Kaante dake tsaye bayan Benazir yana kallonta cike da kulawa da damuwa harma da mamakin halin daya sameta,

Ganinsa yasa hankalin sumayyah dawowa jikinta da sauri ta yunqura ta tashi zaune tana kallon Benazir jikinta na daukan rawa ita kanta Benazir datake cikin halin tashin hankali har lokacin matse take dasu bar asibitin da Bilal din su koma gida da gaggawa.

Saukowa gadon Sumayyah tafara a rikice tana cewa Benazir su tafi gida kada Ababa ya rigasu komawa gidan duk da Hande ko sunr rigasa komawa saita fada masa amma sassauci zai samu idan sun rigasa komawa din. Benazir da sauri ta miqe tsaye tana kamata ba bata lokaci suka fara kokarin guduwa hankulansu a tashe sbd sam babu wanda yake cikin nutsuwarsa bare wani tinanin da ba nakomawa gida ba yanzu yanzu.

Cikeda mamaki Bilal ya matso ya dakatar dasu yana cewa

"Meye hakan kuke kokarin yi? Tayaya zata iya taka qafafun nata ta isa gida musamman wannan rawar jikin da kukeyi tana taka qafar zata qarasa tadawa kanta wani matsalan.

Daga Benazir har sumayyahn babu wanda ya iya dagowa ya kallesa sai shiru da sukayi dan dai bazasu iya tsayawar ba hakama bazasu iya qalesa su tafiyarsu ba sbd taimakon da yayiwa Sumayyah din ta saidai itama kila su rasata.

Benazir ce daqyar ta iya bude baki cikin girmamawa sosai kanta a qasa ta basa hakuri tareda masa godiya sosai akan abinda ya musu din.

Kallon Sumayyah datake tsiyayar zufan wahala da azabar tsayuwar datayi akan qafafunta yaji zuciyarsa bazata iya dauka ba dan haka kai tsaye ya kai hannunwan ya maidata zaune kan gadon tareda durqusawa ya kamo qafar ya duba yana jin tsakan jikansa na tashi sbd yanda gurin ya sake cabewa take da yar tsayuwar datayi to bare tace zata taka zuwa gida.

Cikin fada ya kalli Benazir data sake daukan rawar jiki zuciyarta na bugawa kaman zata faso kirjinta ganin yakai hannunsa kan sumayyah wadda itama kusan kanta ya kusa juyewa sbd tsoro da firgicin jin hannun wani namiji a jikinta take tafara kokarin rasa numfashi sbd tino Fuskan Ababa idan ya san hakan.

Benazir din da Bilal sukai kanta suna girgizata Sake jij hannunsa jikinta yasata qarasa gigicewa tana neman rasa hankalinta Benazir da sauri ta janye hannun Sumayyah din daga hannunsa tana kasa kallonsa ta miqe tana ce masa gida kawai zasu tafi.

Kama sumayyahn tayi wadda ta ringa taka qafafunta cikin azabar datake jin gwara ita da wadda Ababa zaiyi musu idan yarigasu isa gida.

Bilal mamakinsa qaruwa yayi tareda wani irin tausayinsu da soyayyar Sumayyah din mai qarfi na sake mamaye zuciya da jininsa dan kuwa duk takun ta daya har cikin tsakiyan zuciyarsa yake jin radadinta.

Suna fitowa harabar asibitin bai tsaya komaiba ya qaraso gurinsu ya kama sumayyah din ya isa da ita motarsa ya bude ya sakata a seat din gaba ya rufe ya kalli Benazir datai mutuwar tsaye kai tsaye ya nuna mata bayan motar fuska a daure yace ta shiga.

Daga inda take tsaye bata motsa ba sbd wannan wani abun ne da bazai taba yiyuwa ba gashi kai sumayyah cikin motarsa ya gama firgita duk wata qarfin zuciya datake dashi. Ganin bata motsaba itama ya dawo inda take ya kamota ya bude bayan motar ya sakata sbd shi rayuwarsu da sukayi a turai yasa bai tsaya tinanin komaiba ya kama sumayyah dan daukanta a matsayin matarsa insha Allah, Ita kuma Benazir ya janyota ne sbd yariga ya sakata matsayin daya da Aleeyah kanwarsa.

Yana shiga motar bai tsaya sauraran tsananin tashin hankalin dasuke cikiba ya tada motar ya fice daga asibitin.

Tinda ya tinkari hanyar gidansu kowaccensu ta rasa motsi sbd sunsan yau Alkiyamarsu ta tsaya.

Wani babban chemist ya tsaya ya siya magani masu yawa da aka rubuto ya qaraso har hanyar dajin gidansu yayi parkin daga nesa dayake duhun magrib ya fara suka fito ya miqa musu ledan maganin A tare suka girgiza kai suna cewa bazasu iya tafiya dashi gidan ba.

Sumayyah ya zubawa kyawawan idanuwansa yana kwatanta radadin datake ciki sai kawai ya bude motar ya fito yana cewa" muje na kai maganin da kaina"

Suna jin hakan sumayyah ta fashe da wani irin wahalallan kuka ita kanta Benazir hawaye tafara batareda ta sani ba take suka zube qasa suna rokonsa kaman bayin da zaa cirewa kai.

Kallansu yayi ransa na suya sbd zuwa lokacin baya kaunar ganinsu a irin hakan.

Kallon Benazir daya fahimci itace qanwa amma itace ke fadan yanda sumayyah din zatayi yace

"Idan har bakwason naje da kaina gidan to sai kunyi alqawarin yarda da kullum zan kaiku asibiti aduba ciwon ana dressing harta warke idan ba haka ba zata iya rasa qafarta gabaki daya. Idan kun yarda shikenan idan ba hakan ba a ynxu zan biku har gidan nayi bayanin yanayin ciwon nata.

Babu wani tinani ko nazari Benazir ta gyada masa kai ta amince sbd yabar gurin kada mummunan kaddara tasa wani ya gansu kokuma muguwar kaddara tasa ya bisu gidan.

"Kin tabbatar?" Yafada yana kallon Benazir din wadda tini suka fara tafiya hankali tashe ta sake gyado masa kai suna jefa qafafunsu cikin sauri hankali tashe.

Wani irin sanyayyan Numfashi ya sauke tareda komawa cikin mota ya zauna yana kallonsu ta mirror har saida suka shige kwanar gidansu.

Tayaya 'yaya mata daya kamata su zama zinariyar kowane Ahali ace suna cikin irin wannan tsoron mai muni? Meyesa iyayensu ke musu tsanani haka wanda ya ciresu daga lafiyayyun mutane sbd tamkar Mujiya suke acikin mutane. Tada motarsa yayi yabar gurin yana sake jinsu acikin ransa fiyema da baya dan kuwa a yanzu bayajin zai iya janyewa daga kaunarsa ga Sumayyah. #MAMUH# #DD KAANTE #KAANTEs #BENAZIR #BILAL KAANTE #ABABA #HOT LOVE #BILLONAIRES #CONTRACT#MARRIAGE#LIFE#ROMANCE

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 09033181070 09032345899

Zafafa🫶🔥🔥

_Mamuhgee 11_

*_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI JAMA’AR ZAFAFA BIYAR_*

*_KAMAN KO DA YAUSHE DA MUKE KAWO MUKU ABABEN AMFANI GANGARIYA KUMA DAKI BARI MASU AMINCI A KUDADE KALILAN_*

*_YAU MA MUN ZO MUKU DA TALLAN BABBAN SHAGON NAN DA KE KAWO MU KAYAYYAKI NA KASAR GERMANY!! KUNSAN DAI GERMANY SUNE AGABA A FANNIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA KARKO_*

*_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_*

*_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_*

*_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_*

*_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_*

*_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_*

*_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM:@Maabluxuryhome_* *_FACEBOOK:@maabluxuryhome_*

*_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_*

*_A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_*

*_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_*

*_08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_*

************ Suna shiga gida Hande dake tsakar gida zaune tana jiran dawowarsu tahau fada da masifa sosai tana hadasu da kalmomi marasa dadi iri iri amma babu wanda ya dago kai acikinsu kansu na qasa harta gama fadan tace su matsa mata daga ka tukuna suka bar gurin suka isa dakinsu jakunkunan hannunsu kawai sika aje suka fito sikai Alwala suka koma suka hau sallolin dake kansu tin daga azahar sbd a asibitin Benazir bata samu ko motsawa ba ita kuma Sumayyah batama san ina kanta yake ba.

Suna gama sallah Annensu ta kalli Sumayyah dake sallah tana hawayen azaba tayi mata sannu tareda kamo qafar ta duba ta tofa mata addua cikeda jin qai da tausayawa 'yar tata datake jinsu su biyun a zuciyarta fiyeda yanda take jin kanta.

Benazir da Annensu ne suka fito suka hau wankin kayan shago da aka kawo Sumayyah kuma tana daki kwance tana fama da azabar ciwon ga yunwa a cikinsu kaman bazasu iya jan numfashi daidai ba.

Sai bayan ishai suka gama kuma har lokacin Ababa bai dawoba dan haka Hande na basu abincinsu suka koma daki suka zauna suka cinye sukasha ruwa suka kwanta.

Saar da suka samu a ranar Ababa koda ya dawo Hande tayi bacci bata samu sanar dashi sunyi lattin dawowa gida ba, Qarfe hudu na asuba suka tashi suna gama sallah Benazir ta fito tafara goge kayan da sukai wankin da daddare Gari na fara haske Sumayyah ta fito ta fara gugar itama sbd kada Ababa ya fito yaga ita batayi, Akwai zazzabi da rashin qarfin jiki sosai a tareda da ita amma hakanan ta daure sika qarasa gugan tareda Benazir suna kammalawa sukai wanka tareda shirin makaranta Hande ta basu sauran taliyar da aka dafa musu da safen suka karya, Banda sumayyah wadda ko ruwa takasa sha sbd qarfin zazzabin dake cinta haka suka lallaba suka fice har lokacin Ababa bai tashi ba.

Suna fitowa gurin hawa mashin dinsu baqar lexus na parking gabansu babu bata lokaci suka shiga sbd Sumayyah dake gap da zubewa qasa Aikuwa suna shiga motar ta some dan haka hankali tashe suka isa asibiti dan kuwa daga Benazir din har Bilal babu wanda yake tina komai bayan samuwar sumayyar da rayuwarta daga halinda take ciki.

Kaman wancan karon take aka kwantar da ita nurse da likita suka fara abinda ya kamata akanta Bilal din da Benazir suna waje babu mai iya magana a cikinsu sbd Benazir datake neman zauncewa da tashin hankali.

Haka sukai zaman jira bayan an barsu a dakin su kadai suna tsimayin farfadowarta.

Guraren qarfe goma numfashinta ya dawo daidai alaman bacci mai qarfi ya dauketa daga wahalar, Kallan Benazir Sir Bilal yayi yace mata zai tafi office yanada masu jiransa zai dawo ba jimawa.

Gyada masa kai kawai ta iya yi harya fice bata iya motsawa ba.

Zaman jira ta dasa har bayan azahar ta samu tayi alwala a toilet din Amenity room din dasuke ta futo tayi sallah tana idarwa Sumayyah din na farkawa ta taimaka mata zuwa toilet tayo fitsari da Alwala tazo a zaune tayi sallah tana idarwa Akai knocking kofar dakin tareda turowa aka shigo.

Kallon wanda ya shigo sukayi dukkaninsu a tare harda Sumayyah dake cikin mutuwar jiki.

Kallansu yayi shima cikin yar girmamawa yace Sir bilal ne ya aikosa ya kawo musu sako, Ajiye ledojin hannunsa yayi gaban Benazir yana juyawa bayan yayi musu fatan samun sauki ya fice daga dakin tareda rufo kofar.

Kaman bazasu taba ledojin ba tsawon mintina kafin Benazir ta bude ta duba taga take aways ne masu dauke da sunan tsadaddan restaurant din KAANTEs Hotels & Suites. Wasu irin tsadaddun Deserts ne da crispy chicken sai chicken biryani da kuma salad sai drinks marasa sanyi sosai da ruwa katan daya.

Wani tsinkakken yawu ya wuce maqogwaransu su duka biyun sbd wani irin kamshi da basu saba ji ba dayake shiga hancinsu.

Kallon juna sikai kowannen hanjinsa na fidda wani sautin kukan yunwar datake tauye dasu.

Babu wanda yayi magana a cikinsu abincin sike sake kalla Sumayyah na jin kaman zatayi amai sbd yunwa da matsuwa taci abincin, Ita kanta Benazir yawunta sun kasa tsayawa sai tsinkewa sikeyi suna wucewa maqogaranta. Sun jima suna shawarwari da zuciya da hanjinsu kafin daga karshe dai suka afkawa abincin da bismillah suka cinye komai tas sbd Nama wani abu ne da a iya shekarunsu bazasu iya fadan so nawa suka taba cinsa ba,layya Ababa bayayi,baya siyo nama gidansa baya yanka,idan kaga yaci nama iya wanda zaici ne shi kadai sai Hande dayake bawa dan haka a rayuwarsu dai bakinsu bai wani san dandanon namaba dan haka yau din suka ci kaman ba gobe. Suna gamawa Nurse ta shigo ta bawa Sumayyah magani tareda wasu allurai take sumayyah din takoma bacci.

Ita kanta Benazir din sbd hutu da Cimar da basu saba ba take bacci ya dan dauketa daga kujerar datake zaune.

Basu farkaba sai bayan laasar da sauri Benazir ta tashi ta fada toilet din dakin ta wanko fuskarta tareda Alwala ta fito ta kama Sumayyah tayo Alwala itama suka fito babu bata lokaci sikar sallar laasar suna idarwa sika fara tinanin tafiya gida sbd ba laifi sosai Sumayyah din ta samu sassauci daga mummunan azabar datake ciki,

Babban abinda yasa duk ha'darin hakan Benazir ta yarda suka zo asibitin shine tinawa takeyi da hadda qonuwar wuta ne yayi sanadin Rasuwar Samirah, Idan ta tina hakan jin takeyi zauncewa zatayi daga ita har Annensu idan wani abu mai kama da hakan ya samu Sumayyah sbd a yanzu da suka debo shekaru iya su tini sika manta da komai da kowa bayan junansu,

Wata irin kauna ce mai tsananin gaske da qarfi take sukewa junansu, Tin shekarun baya da suke tareda sauran yan uwansu daman Kaunar Benazir a ran sumayyah daban ce hakama ita kanta Benazir din sumayyah daban take a ranta bayan Annensu,sai samirah da itama suke ji da ita sbd tana kaunar yan uwanta sosai da zuciya daya,Safnah ce zasu ce basu tabbatarda tasu kaunarba a ranta amma a nasu ran itama suna kaunarta har cikin zuciyarsu amma daga ranar datayi amfani da Annensu ga gudu suka rufeta daga zuciyoyinsu dan bazasu iya ciretaba jininsu ce kuma suna sonta gaskia.

Kokarin barin dakin sukeyi Nurse ta shigo ta hanasu tareda sanar dasu sai Sir Kaante ya dawo umarninsa ne. Babu yanda basuyiba su tafi aka qi barinsu haka suka zauna suna jiransa har Sumayyah ta sake komawa bacci sbd akwai abinda yake sakata baccin tsakanin allurar da aka saka mata a drip nata kokuma maganin da aka bata.

Benazir zuwa lokacin hankalinta ya dawo jikinta gabaji daya bata cikin nutsuwa tsoro da bugawar zuciyarta gabaki daya sun zaburo,ko wane iskar numfashin datake shaqa tafe yake da zallar tsoro da fargaba.

Wani abincin aka kuma kawo musu wannan karon snacks ne,Samosas manya masu kyan gani sai doughnuts masu girma da taushin gaske sai cup cakes da wata kalar crispy chicken din, Ladar daya kuwa drinks ne sai Apples.

Numfashi ta sauke sbd wannan karon kam Asarar kayan zaayi dan bazasu iya cinyewa ba haka bazasu iya zuwa gida dashi ba.

Sumayyah data farka kadan taci sbd maganinta akwai me saka cin abinci sbd ganowa da akai akwai yunwa tareda uta sun dauka itace batason cin abinci basusan samun abincin ne batayiba taci ta koshi.

Benazir kasa cin komai tayi sbd fargaban zuwa gida da abubuwan gashi a yanayin ciwon sumayyah da maganinta tana buqatan abinci.

Tana cikin shawarwari akazo tafiya dasu gida ba Bilal din bane aiki ya riqesa suna ganin hakan suka saka ya ajiyesu makaranta daga can suka hau mashin suka koma gida.

Cikin tsoro da fargaba mai tsanani suka shiga gidan Hande na dakinta Annensu ce kawai tsakar gidan tana aikin wankin kayan Hande dasu zannuwan gadon Ababa. Suna ture ture sbd rawar jiki da tsoro suka fada dakinsu cikik rawar jiki Benazir ta fidda ledan kayan ta tura cikin kayansu na sakawa dake daure a gefe Sai alokacin ta saki ajiyan zuciya gabanta na tsananta faduwa tinda ba cinyewa akai ba har lokacin suna cikin hadari mai girma.

Sumayyah da zuciyarta da jikinta suka kasa dena rawa itama kallon Benazir tayi murya a sarke tace

"Bena ki shigo da Anne tin Ababa be dawoba a cinye kayan nan mu saka ledojin a bra tsoro nakeji sosai wlh, Idan tsautsayi da kadda yasa Ababa yaga ledan nan sai rasuwar samirah tafi tamu sauki da rahama.

Ita kanta Benazir bata cikin kwanciyar hankali idan ba kawar da komai akai ba tunda mummunan kaddara tasasu shigowa gidan da kayan sbd Annensu sukeso itama yau taciwa cikinta abinda zai koshi tinda abune da basu taba ba arayuwarsu ci a koshi.

Sallar magrib sukayi suna idarwa suka fito Benazir ta kamawa Anne wankin suka qarasa ba bata lokaci suna gama shanya suka shigo daki.

Benazir ce ta zauna setin kofa tana hango mai tahowa suka fidda kayan tareda budewa Anne suka ce tayi sauri taci ta koshi.

Readers Also Read