Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 7
Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 7: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 7. Wani tsalle zuciyar Anne tayi kaman zata fado…
3,367 words
Wani tsalle zuciyar Anne tayi kaman zata fado sbd tsananin tsoro da firgita muryanta na rawa qasa qasa tace "Ina kuka samo? Menene wannan din? Meyasa kuka taho dashi gidan nan? Kusan kashemu Ababa zaiyi idan yaga wannan kayan ko Hande.
Sumayyah ce ta dauko doughnut hannunta na rawa sbd tsoro ta tura mata a baki itama murya na rawar tashin hankali tace
"Anne kiyi sauri kici zamu fada miki daga baya inda muka samu"
Laushinsa da qamshin mai dadi tareda azababbiyar yunwar cikin Annen yasata yagar rabinsa tafara ci take taji cikinta yana kukan yunwar ya samu abinci.
Hannu baka hannu qwarya takecin kayan musamman kazar me shegen dadi tana gamawa ta shanye orange drink din dasuka juye a leda suka dauro mata sbd bazasu iya shigowa da robar gidan ba.
Hamdala Annen tayi bayan da cikinta ya cika sosai Ta hada wani irin uban zuba sbd tana cin kowace irin loma cikin babban tashin hankali da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa, Yanda kasan barayi haka dukkanin idanuwansu suke a waje kowannensu na hada gumi suna kallonta ta koshi.
Sauran abinda ta rage Sumayyah taci ta bawa Benazir sauran itama ta cinye suka nade ledojin kowacce ta tura cikin rigarta dasu suka kwana ajiki dan abincin da aka basu ma dole suka turasa sbd kar a gane sunci wani abin.
Washe gari ba laifi jikin Sumayyah saidai akwai zazzabi data kuma tashi dashi sbd yanayin makwancinsu basuda kofa a dakinsu shiyasa kusan kullum ko lafiyansu kalau kusan da zazzabi suke tashi kowannensu sbd sanyi dan duk zafi su yanada wahala sujisa sosai sbd anguwar tasu kaman daji take ba mutane dan haka akwai sanyi sosai. #MAMUH# #BILLONAIREROMANCE #DD KAANTE #CONTRACT#HOTLOVE#ABABA#BENAZIR ABABA KAANTE.
ZAFAFA BIYAR🔥
-ZAFIN KAI Mamuhgee
-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma
-FURAR DANKO Billyn Abdul
-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo
Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400
Pay at 09033181070 09032345899
Zafafa🫶🔥🔥
_Mamuhgee 12_
*_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI JAMA’AR ZAFAFA BIYAR_*
*_KAMAN KO DA YAUSHE DA MUKE KAWO MUKU ABABEN AMFANI GANGARIYA KUMA DAKI BARI MASU AMINCI A KUDADE KALILAN_*
*_YAU MA MUN ZO MUKU DA TALLAN BABBAN SHAGON NAN DA KE KAWO MU KAYAYYAKI NA KASAR GERMANY!! KUNSAN DAI GERMANY SUNE AGABA A FANNIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA KARKO_*
*_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_*
*_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_*
*_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_*
*_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_*
*_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_*
*_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM:@Maabluxuryhome_* *_FACEBOOK:@maabluxuryhome_*
*_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_*
*_A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_*
*_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_*
*_08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_*
****** Sauran ruwan zafin lipton da Ababa yasha shayi aka basu babu bread haka suka shanye zallar ruwan zafin da ko sugar baijiba sukai shirin makaranta suka fice.
Suna fita yauma tafiya kadan sukai motar Bilal daya kwana dasu a ransa baida sukuni ta tsaida mashin dinsu a kunyace suka sauko sbd overload dinsu ba kyan gani itace a tsakiya sun matsu iya matsuwa suda mai mashin dayake jin tudun kirjinta wanda kusan hakan suke zuwa makarantar kullum babu ranar da har akai makaranta ba cikin baqin ciki da quncin yanda jikinsu ke manne dana mai mashin din ba.
Shi kansa Bilal dake cikin motarsa qarewa yanayinsu dana mai mashin dain yayi yaji wani irin abu ya tokare kirjinsa musamman yanda kowaccensu dazata sauko kusan daida jikinta dana mai acaban ya hadu.
Rufe idanuwansa yayi ahankali tareda dauke kai daga kallon gurin glass ya aka sauke drivernsa ya miqawa mai mashin din 2k yace ya wuce kawai.
Drivern da kansa ya fito ya bude musu bayan motar suka shiga sbd Sir bilal din yana seat din gaba.
Suna shiga aka bar anguwar dasu babu wanda ya iya magana acikinsu bayan gaisuwar da sukai masa cikin girmamawa da nutsuwarsu dake sake samar musu da gurbi a zuciyarsa.
Hanyar asibiti suka nufa kai tsaye Yau babu bata lokaci dubata akai aka canja dressing din qafar wanda suna kama hanyar gida suke ciresa su yar sbd kada a gani.
Ana gama dressing gurin aka bata magani tasha suka fito ya ajiyesu makaranta bayan yasa akawo musu abinci daga restaurant dinsu na Kaante hotel and suites. Suna fitowa first lectures dinsu aka kawo musu abincin har kofar hall dinsu sumayyah din sbd Sir bilal ya sanar dashi hall din dazai sameta tinda ba waya ne dasu ba.
Sumayyah ganin mutane dakuma tsoron jawa kai attention yasa ta karba da sauri tabar gabansa ta nufi gurin Benazir da itama tsoron ganin abincin yasata jan sumayyah suka bar cikin mutane.
Nesa da mutane suka boye suka zauna tareda zubawa ledojin ido hankalinsu tashe sbd zuwa lokacin har ga Allah taimakon ya ishesu tinda sumayyah din tasamu sauki ba laifi.
Har aka tashi basu ci abincin ba suka fito saiga driver yana jiransu a gate suka dauke kai suna shigewa mutane sbd kada ya gansu amma haka ya ringa binsu yana sanar dasu Sir bilal yace kada abari su hau mashin.
Benazir kaman zatai masa sujjada ta ringa rokonsa ya dena binsu shima kaman zai musu sujjadar ya ringa rokonsu akan umarnin mai gidansa ne.
Sumayyah datafi shiga tsoro tana kalle kalle tace su shiga kada wani yagani tinda ba tafiyar zaiyi ba.
Haka suka iso anguwarsu kaman zasuyi zawon kayan cikinsu sbd tsoro. Yana ajiyesu suka fito qafafu na rawa suka nufi hanyar gidansu suna waiwaye sbd ledan dake cikin hijabansu.
Yauma cikin saa Hande bata tsakar gida sukai saurin isa daki.
Na yau basu ci ba sbd yanada qamshi zaa iya jinsu dan haka suka boye cikin kayansu sai tsakar dare suka tashi yunwa na neman kashesu suka hau ci kaman wainda sukai shekaru ba abinci.
Suna gama ci ko ruwa kasa fitowa su sha sikai sbd fargaba dan haka a hakan suka kwana yauma ledojin a cikin jikinsu suka kwana dasu.
Anne da sukaiwa bayanin Abinda yake faruwa tsorone yafara shigarta sbd ranar ra zaa ganesu take tsoro dan kuwa ranar ruwan masifar fa zaayi a gidan hakama shi kansa mutumin dake taimaka musun Ababan ba barinsa zaiyiba da balainsa dan haka ta ringa musu nasiha da gargadin su kiyaye su nesanta kansu da abinda zai qarasa kashe musu dan kwanciyar hankalin dasuke samu wasu lokutan idan masifar Ababa da hande ta kwanta.
Tamkar wanda aka wajabtawa haka Alh bilal kaman yanda su suke fada yafara sauya rayuwarsu daga wahalalliyar azababbiyar yunwa, Kullum sai ankawo musu abinci a boye suke karba suna isa dashi gidan sunaci su da mahaifiyarsu wadda a yanxu ciwon yunwar daya gama cinye hanjinta yafara dan sakewa sbd a baya haka take kullum a mokade kaman ledar da aka jefa cikin tafasasshen ruwa.
Aduk sanda suke shigowa da cin abincin cikin masifaffen tashin hankali da firgici mai tsanani sike cinsa su gama dan kuwa sun sani na lahira sai yafisu jin dadi duk randa mummunan tsautsayi yasa kaddarar tonan asiri ya kamasu.
Shi kansa Alh bilal din daya sake fahimtar yanayin da suke ciki na ba qaramin taimakawa abincin ke musu ba daya fara fahimtar yunwar dake tareda sumayyah tafara sakinta kaman yanda likitan dake dubata yafada sai ya dage da ciyar dasu din a boye ta yanda shima nasa familyn basu san rayuwar daya jefa kansa ba.
A yanzu da ya zama kaman biyayyarsa shima kusan tilas ce garesu sbd kyautatawarsa garesu sai ya zama wani irin girma da darajarsa suke gani gashi shima din sai ya dena tinkararsu kai tsaye cikin mutane sbd fahimtar suka tsananin shiga firgici da tashin hankali idan yayi hakan dan haka haduwarsu sai ya zama a sirrance sukeyi.
Hawa Mashin din zuwansu makaranta daya tsana fiyeda komai sai ya siya musu napep kai tsaye sbd kaisu kawai da daukosu tinda basa son shiga motarsa koyaushe suka shiga cikin yanayi na mummuna suke dan haka wanda ya bawa napep din aikinsa kawai kaisu da dauko su.
Da farko tsoron hakan sukeji sosai sbd basu san yanda zasiyi da kudin mashin din da ake basu ba, Basu iya boye kudi ba sbd ko sun boye basu san me zasiyi dashi ba tinda basu taba sakawa ransu tinanin guduwa subar gida ba bare su ringa boye kudin gashi idanma sun gwada boyewan tinda suka fara zuwa makaranta akai akai Ababa ke sawa hande tana bincikesu da kayansu dan haka basu taba tinanin boye wani abin ba ko ba kudi ba Abincinmq dasuke shigowa dashi dan suna cinyewa ne a take dasun shigo dashi, dan haka kaman yanda Allah ya kawo musu mai taimakonsu a boye sai suma sike bawa wani tsoho makaho kudin a hanyarsu ta tafiya kullum sbd baida kowa shima yana cikin mawuyacin hali.
Tsohon daya gama wanyewa dasu kullum shima a duk lokacinda ya bude bakinsa Benazir yakewa addua sbd itace mai fitowa ta basa, Adduarsa kullum Allah yakaita matsayinda bata taba tinanin zuwaba tareda rayuwa mai Albarka da kwanciyar hankali tareda zuria dayyaba.
Exams dinsu aka fara dan haka hankalinsu ya rabu sbd kowa karatunsa yake kokarin maida hankali akai musamman Benazir sbd lectures da dama data ringa rasawa a lokutan sbd sumayyah da ciwon datayi bayan nan dan haka idan suka shigo makaranta sumayyah bata sake ganinta sbd Sosai karatunta ya samu ci baya shiyasa ta dage sosai kafin ta fadi Ababa ya kusa kashesu su dukan gwara a samu mai taimakawa wani acikinsu.
Sumayyah da kanta ya daure matiqa sbd exam din farko da suka fara babu abinda ta gane sunanta kawai ta rubuta sai questions din data maimaita masa a booklet bayan question daya babu abinda ta amsa said ta fito idanuwanta cike da hawayen tausayin kanta da yanda rayuwa zatai mata idan ta gama shekarun nan biyu duka a fail, Wane mataki Ababa zai dauka akanta? Siyar da ita zaiyi ga 'yan qwaya da gaske ko me?
Inda suke zama ta nufa ta zauna ahankali tana sauke kanta qasa dukkanin jikinta na mutuwa hakama tsoron dake mamaye zuciyarta na qara bayyanuwa a kan fuskarta.
Haka ta jima a gurin tana saqa da warwara cikin damuwa har lokaci yayi suka sake shiga wata exam din nan ma kusan biredi ne ke dukan fanke bata tsinano abin arziki ba dan haka wannan karon tashin hankalinta da tsoronta qaruwa yayi sbd azabar datasha wancan karon data fadi exams din a hannun Ababa.
Tana fitowa kasa riqe zuciyarta tayi taje maboyarsu ta zauna hawaye na tsiyayo mata ta saka fuskarta tafin hannuwanta tana sakin kuka mara sauti gashi bazata iya fadawa Benazir ba ta sakata damuwa nata karatun ya fita kanta, Bazata so hakan ba sbd ko yayane tanason Benazir ta samu kammala karatun da sakamako mai kyau.
Tana gurin zaune har yamma Benazir ta gama suka tafi gida a napep gurin komawarsu Benazir ta lura da yanayin Sumayyah din ta tambayeta exams dinta.
Kasa magana Sumayyah tayi sbd hawayen dasuka cika idanuwanta kafin tayi wata magana Benazir ta fahimci komai cikin damuwa da tausayin yar uwarta tayi shiru ta kasa cewa komai sbd itama tasan suna dagewa ne suyi karatun sbd azaba da hukuncin Ababa,ita kanta idan ta tina da azabar da zata biyo bayan faduwa jarabawar tashi hankalinta keyi bare Sumayyah data dandana azabar hukuncinsa na faduwan.
Shirun Benazir yasa hawayen sumayyah saukowa tana rufe fuskarta da hannuwanta sbd kukan dayake zuwar mata zuciya a karye.
Har suka isa gida kuka sumayyah din keyi itama Benazir kukan zucin takeyi jikinta a mace, Mai napep na jiyesu suka nufi hanyar gida sumayyah na goge hawayenta dan kada hande ta gani wani masifar ya biyo baya.
Sulaiman drivern napep dinsu na aje su wayarsa ya fidda ya nemo numbern Alh bilal ya saka kira sbd umarnin daya basa akan duk yaga matsala ko damuwarsu ya sanar masa.
Kai tsaye ya sanar masa suna cikin wata matsalar sbd Sumayyah nata kuka har suka isa.
Shiru Alh bilal din yayi sbd yana tareda Mahaifinsa a lokacin.
Dan numfashi ya sauke ahankali tareda bude baci yace
"Ok shikenan idan na samu time zan kira naji qarin bayani."
Kashe wayar yayi tareda ajiyewa gefensa yana qin kallon mahaifinsa sbd zai iya tambayarsa daga ina ne kiran.
Kallonsa Alhaji DAUDA KAANTE yayi sbd yasan Bilal din da zurfin ciki yanzu haka wata matsalar ce dan haka kai tsaye ya gyara zamansa kan lafiyayyar luxury couch din dayake kai cikin babban palonsa dake Kaante Mansion yace
"Da matsala ne?"
Dagowa Alh Bilal yayi ya kalli Dad Kaante yana basar da tinaninsa akan zancen kukan sumayyah yace
" ba komai bane wani yaron dana sa aka dauka aiki ne ya kira."
Basar da zancen Dad kaante yayi cikin manyanci irin na wanda tarin arziki yagama hudawa tako ina komai a hankali kwance ba sakawa hayaniya sai ciwon kai da 'dayan 'dansa yake sakar masa wanda idan ba DD kaante din ba babu wanda ya isa tayar masa da hankali ya sanyasa shiga tinani.
Kallan hoton DD din da shi kadaine hotonsa ya isa a maqala a palon Dad kaante din dana Oga kwata kwata wato kakansu shugaban family din gabaki daya wanda shine Asalin Kaante din wato Dalhat kante.
Shi kansa Alh bilal hoton DD din ya kalla kafin ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa yace
"Dad insha Allah zan gwada masa magana zai dawo ko zuwa qarshen watan nan ne"
Numfashi mai dumi Dad kaante din yakuma sakewa a karo na ba adadi sbd ya rasa tayaya DD yake iya sakar musu pressure, Tayaya zai dauke mahaifiyarsa da qanwarsa sama da watanni Shida suna gurinsa Zurich, Meyasa bazaiyi tinanin anan din yaya ake ji babu su din ba, Ina matsayin mijin Mahaifiyar tasa kuma mahaifinsa dana qanwar tasa daga zuwar masa ziyara ya riqesu, Sam baya duba bacin Raina dana DD babba akan hakan koyaushe mahaifiyarsa kawai ya sani. #MAMUH# #DD KAANTE#BILLONAIREROMANCE#Contrct #BENAZIR#MARRIAGE#LIFE
ZAFAFA BIYAR🔥
-ZAFIN KAI Mamuhgee
-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma
-FURAR DANKO Billyn Abdul
-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo
Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400
Pay at 09033181070 09032345899
Zafafa🫶🔥🔥
_Mamuhgee 13_ Hakuri Sir bilal ya sake bawa Dad kaante tareda tabbatar masa da zasu dawo qarshen watan da yardar Allah harma da DD din idan Allah ya dorasa akanshi.
Cikin 'yar damuwa Dad kaante din yayi sallam da Bilal ya fito yana fidda wayarsa dan kiran Sulaiman da hankalinsa yake kansa.
Motarsa ya nufa batareda ya nufi babban part dinsa ba dayake gefen mansion din iyayensa ba duk acikin guri daya. Yana shiga motar ya rufe ya saka kiran Sulaiman wanda shima yake zaune yana jiran kiran maigidan nasa dan sake kora masa bayani.
Kiran Sir bilal din na shigowa wayarsa ya dauka da sauri yana sake gaishesa kafin ya sake masa bayanin komai na abinda ya fahimta.
Shiru Sir bilal din yayi kafin ya kashe wayar yana tinanin menene zai saka sumayyah kuka da damuwa har a hanya?
Tada motarsa yayi yana kallon time sbd yanada meeting da baqin masu mahimmanci ga DD yana buqatan nutsuwa yayi magana dashi ta waya Dan haka ya daure ya wuce office idan Yaso washe gari da wuri zai sameta school yaganta.
Washe gari Koda ya isa suna cikin exams dan haka ya zauna cikin motarsa yana jiranta.
Tsawon mintina talatin da shida yayi yana jira sai gata ta fito ta nufa inda suke zama yau din ma bata cikin kuzari sbd zuwa lokacin tagama saddaqar da masifar da zata shiga ta Ababa.
Kokarin zama takeyi qamshin tirarensa ya shiga hancinta ta dago da sauri tana ganinsa tayi saurin maida kanta qasa tareda zamewa ta durqusa ta gaidasa cikin tsananin girmamawa.
Yanayinta yake sake karanta yanason magana da ita amma sanin hankalinta bazai taba kwanciya ba sai yace ta biyosa kawai.
Kaman baiwarsa haka tabi bayansa kanta a qasa cikin nutsuwa.
Motarsa ya bude mata tashiga shima ya zagaya ya shiga tareda rufe motar yaja suka bar makarantar saida sukai tafiya mai dan nisa zuciyarta na bugawa Qafafunta tini suka fara rawa saidai bata iya magana ba.
Inda babu mutane sosai yayi parking ba tareda ya kashe motarba sbd Ac ya juyo ya kalleta cikin nutsuwa ya sauke numfashi mai dumi tareda ajiyar zuciya kai tsaye yace
"Meyasa kiketa kuka yau sulaiman yace akwai matsalan dayake damunki, Ko zan iya sani idan ba damuwa.
Idanuwansa ya zuba mata yana jiran amsarta,
Shiru tayi bugun zuciyarta da rawar jikinta na bayyanuwa ga hannuwanta dake rawa.
Hannuwanta ya kalla yaga yanda suke rawa a hankali kafin ya maida idanuwansa kan fuskarta yana sake tabbatarda akwai matsalar dake damunta.
Maimaita tambayarsa yayi cikin kulawa nan ma kasa magana tayi ta girgiza masa kai kawai ahankali.
Ganin hakan yace
"Inaga zanje gidan da kaina naga Babanku sai naji ko wani ne a gidan ba lafiya"
Jin hakan yasa gabanta mummunan faduwa sbd duk yanda suka kai ga kamewa da kiyayewa tareda taka tsantsan koyaushe da zuwa gidansu yake musu barazana yana taimakonsu dan kuwa duk abubuwan dayake musu saiya basu tsoro ya firgitasu da cewan zashi gidansu gurin babansu suke yarda su karba taimkonsa.
Bude baki tayi cikin sanyin jiki da damuwa ta sanar dashi bata gane komai na karatun da sukeyi ne har jarabawar.
Shiru yayi yanason fahimtar zancen nata da kyau sbd jin zancen yayi kaman kai tsaye da yawa dan haka ya sake kallanta da kulawa yace "Karantarwar ne malaman basu iya ba basayin yanda zaku gane kokuwa?
Shiru tayi sbd muzantar datayi saidai kuma daman su din ba masu wata darajar da zasuce basu saba da muzantar ba dan haka a sanyaye tace "Aa nice bana ganewa,kaina baya gane komau" da wasu irin hawayen kunya da muzantar kai ta qarasa zancen.
Ya fahimci abinda take nufi dan haka jikinsa yayi sanyi da tausayinta dakuma nauyin zancen dan kuwa a familynsa marasa ilimi zaune a kansu basa karbuwa a Kaantes saukin abin suna dubawa hardana Addini ba iya bokon kawai suke so daga matayensu ba.
Ahankali ya sake kallanta yana sake jera mata tambayar yanayin yanda tayi last session dinta da yaya results din suke.
Batada zabi bayan fada masa gaskiar bataci komaiba a bayan duka wannan semister din ma courses din datake carry over dinsu yafi wainda zatayi a semister din yawa.
Wayarsa ya dauka ya saka kiran wata number ta wata lecturer mace wanda tana dauka kai tsaye ta hau gaishesa.
Cikin mutuntawa ya amsa yana tambayarta aiki da dama da student ta amsa da duk lafiya kalau, Cikin natsatsen turancinsa daya kama bakinsa kusanma fiyeda hausarsa sbd zamansu a qasashen turawa fiyeda nan din idan ba yanzu daya dawoba sbd su biyu ne 'yaya maza a familyn kuma idan ba shi din ba DD bazai taba dawowa dan karban ragamar kula da huldodin kaantes ba.
Bayani sosai yayi mata akan zata samar masa da wadda zata ringa yiwa Sumayyah karatu yanda zata gane.
Kai tsaye ta amsa masa da an gama insha Allah ita da kanta ma zata ringa dan budewa sumayyah din karatun da engausa sbd a yanda ta fahimta may be harda turancin yasa bata gane karatun dan haka zata ringa gwada yi mata bayanin karatun da mafi hausa kafin idan tagane sai akoma na turancin.
Godiya yayiwa Ms Ayshan ya kashe wayarsa bayan ta basa time din dazai ringa kai mata sumayyah din gidanta.
Sumayyah data dan fahimci wasu abubuwan dayake tattaunawa da Matar shiru kawai tayi sbd iya saninta hakan bamai taba yiyuwa bane zuwanta wani gurin ita daya, Me zata cewa Ababa,Anne da Benazir idan suka ji?
Bayani yakeson yi mata amma yana iya ganin tashin hankalinta afili akan zancen dan haka sai kawai ya dora hannuwansa akan steering motar yaja suka fara tafiya yana mata bayanin cewan zai sake magana da Ms ayshan ta ringa yi mata karatun a makaranta kawai ba sai gidanta ba.
Da haka ya maidata school ya tafi cikin sauri sbd yayi lattin meeting dinsa,