Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 8

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 8

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 8: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 8. Ita kuma tana komawa wata exam din tashiga…

3,341 words

Ita kuma tana komawa wata exam din tashiga tana cikine Ms aysha din tazo nemanta dan haka tana fitowa kai tsaye office dinta ta nufa.

Da farko qare mata kallo Ms aysha tayi tana mamakin meya hada Sir bilal da sumayyah din amma kuma data qure mata kallan sai taga kyakkyawa ce hutu da gyara ne kawai bata samuba,to kuma koma menene ba ruwanta abinda yake gabansu zasuyi.

Gurin zama ta nunawa Sumayyah din tana mata tambayoyi daya bayan daya.

A tsarge sumayyah din take amsawa har Ms ayshan ta ringa dan janta da fira sbd ta saki jikinta ganin duk a kame take da rashin sakewa.

Ms Aysha wayayyar babbar mace ce kuma mai saukin kai da fahimtar komai cikin sauri, Kai tsaye ta fahimci so da kaunar sumayyah mai tsanani a tareda Sir bilal gashi sumayyah din kuma kaman bagidajiya ce.

A ranar dai basuyi komaiba fira kawai Ms ayshan tayita janta dashi sbd tafison tafara sakewa da ita ta yanda zata fahimci matsalar karatun sumayyah din da kyau.

*_PHYDOORS FOOD AND MORE_*💯🔥

*_Ina masoya Abincin gayu dana gargajiya da Sea foods? Ga ingantattu kuma tsaftattun kayan Phydoors Sea foods and more da muka tabbatar da dadi, kyau, inganci da tsaftarsu tareda saukinsu._* *_Uwar gida, Amarya shin kun taba aikin Abinci da kayan Phydoors sea foods and more kuwa?_* *_Idan baki taba ba ina shawartarki da gwadawa sbd a take zaki gano bambamci da kuma damar Girki masu dadi da ingancin da suka wuce ki._*

_*Phydoors sea foods and more Suna tare daku a koina sbd suna aika kakansu koina a duk Inda kikeso cikin tsari da packaging mai kyau da kulawa hakama ga sauki da Ragusa,Akace siyan na gari maida kudi gida.*_

*_Phydoors food and more is a food branded based in abuja and offered national wide delivery of her items, available food stuffs are stone free crayfish , egusi, palm oil, plantain powder in kg, prawns 🍤 , fried kpomo, some from as low as 2k._* *_Contact her through this line 08062181151 or DM me let’s do paired order for minna and suleja. She’s based in abuja._* _*Or visit her instagram handle*_ @ _Phydoors_Food_

*********** A hanyarsu ta komawa gida Sumayyah ta fadawa Benazir komai tana tambayarta ya zatayi. Numfashi Benazir din ta sauke sbd ita kanta yanzu karatunta ya cake wahalarsa take sha sbd yanda kusan semister din taqare mata gurin attending lectures din sumayyah da kula da sumayyahn gashi daman yau gabaki daya da tinanin yanda zata taimkawa 'yar uwar tata ta wuni har acikin exams dinta tinanin takeyi shiyasa yauma duka jarabawan datayi sai duai itama.

To amma jin hakan yasata shiga nazari sbd Ms Aysha babbar mace ce da kusan makarantar kowa ya santa dan tanada kulawa da mutunta kanta dan haka idan har zata taimakawa Sumayyah karatun kuma acikin makaranta ha wani gurin daban ba to kaman duka an taimakesu ne sbd itama sanin sumayyah nada inda ake koyar da ita karatunta to itama zata samu nutsuwar yin nata karatun kada ayi haihuwar guzuma a tsakaninsu kowa da F.

Hankali kwance suka dawo gida saidai koda suka dawo Annensu ta kona kayan guga kaman yanda sumayyah tayi kwanaki, Bai daketa ba ita amma wani mahaukacin marin daya taba lafiyar kunnenta daya ya shimfida mata a fuska take kunnanta daya ya dauke sauti batajin komai har dashi har sika dawo.

Fuskarta dukkansu suka kalla lokacinda suka shigo tana zaune tsakar gidan tana tuqa tuwon yamma datayi a tsakar gida kan gawayi.

Gefen fuskarta a kumbure yake shatin hannuwansa duka biyar sun fito baro baro akan fuskar, Bakinta daga gefe ya kumbura shima yayi tsayi kaman anja ledar ruwa.

Karyewa zuciyoyinsu sukai da ganinta a hakan amma ba daman nunawa idan ba daki suka shigaba gashi hande na zaune tsakar gidan tana shan redionta hankali kwance.

Daki suka wuce bayan sun gaida Handen ta amsa Suna shiga suka tube abincin da sukazo dashi yau din jin sikai duk ya fice musu aka sbd ganin halinda Annensu take ciki.

Ajiye jakunkunansu dasuka gama yagewa da warwarewa tin na shekarar farkon da aka siya musu kuma ma na gwanjo ne.

Fitowa sikayi Benazir ta amshi aikin abincin kai tsaye taci gaba duk da ga magrib ana kokarin kira, Sumayyah kuwa tarin wanke wanken dayake jibge ta debo ruwa a drum ta zauna tafara gashi tsaban tsaftar Ababa baa wanke kayan cin abincinsa so daya sai anyi so biyu a dauraye kusan so uku sbd duk randa yaji qamshin omon wanke wanken a cup idan zaisha ruwa kokuma a plate idan zaici abinci to wanda yayi wanke wanken saiya gagara shan ruwa a ranar sbd mari ko harbi da qafa.

Anne kuwa tsintsiya ta dauka ta hau shara sbd ayyukan daman koda suka dawo duk sun hade mata gashi tin karin safe sai abincin da Ababa din ya rage da rana Yabata yunwa ke cin hanjinta amma sam bata nunawa 'yayanta ne kawai suke mata kallo daya su gane halinda take ciki.

Sai bayan magriba suka kammala ayyukan sikai alwala suka shige ciki bayan anbasu kasonsu na abinci a roba daya suda Annensu daman haka aka saba tin lokacin sunada yawansu bare yanzu da iya su uku ne kawai.

Sallah sukayi suna idarwa Benazir ta fito ta dora ruwan zafi a kofin silver sukai zafi sosai ta dawo daki dasu ta dauki dankwalinta wankakke ta ringa taba ruwan zafin dashi tana matsewa tana dan gasawa Annen fuskarta da bakinta harma da idonta daya dayayi kwanciyar jini aciki.

Bayan tagama mata Annen taji dan saukin radadin da gurin ke mata suka fidda abincinsu sukaci suka koshi sauran Apple Biyu da wani tsadaddan cookies Benazir tayi masa wani irin boyo a cikin kayansu sbd Annensu taci ta safe dan yau sunga alamar ta jigata da yunwa sosai da alama andena bata abincin rana itama sbd suma baa basu yanzu idan suka karya suka fice sai sun dawo da yamma abasu na dare.

Da zazzabi mai qarfi Annensu ta kwana ko tashi zaune bata iya yi sosai, Kallanta Benazir tayi taji bazata iya barinta ahakan ba kuma aikine zatayi bayan tafiyarsu har saita kusa sumewa kilan, Dan haka taqi tafiya ranar makaranta sbd exam daya ce da ita kuma sai 2 na rana dan haka bayan fitar Ababa sumayyah ce kawai ta tafi ita ta zauna tabawa Annen apple da cookies din taci daqyar tareda ruwan lipton din da aka basu matsayin karin safiyar. #MAMUH# #DD KAANTE #BILLONAIRESROMANCE #CONTRACT#LOVE#MARRIAGE#ZURICH

ZAFAFA BIYAR🔥

-ZAFIN KAI Mamuhgee

-TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma

-FURAR DANKO Billyn Abdul

-BAKON MUNAFIKI Miss xoxo

Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400

Pay at 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim

Send your Shedan biya Anan👇 09032345899

MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇 09033181070

Zafafa🫶🔥🔥

_Mamuhgee 14_ Bayan Annen tagama cinye abincin ta kwantar da ita bayan ta sake gasa mata fuskarta da bakinta ta fito tafara duka ayyukan gidan.

Bangaren dabbobinsa ta nufa tahau sharewa ga yawa gurin ga qazantar kashinsu da suka tattaka da abincinsu ruwa duk sun zubar a gurin haka suke share gurin kullum so biyu a wuni shiyasa kusan duka bayansu basada qwari wahala ta cinyesu.

Sai bayan karfe goma ta gamo da bangaren dabbobin tadawo tahau gyaran gidan, Daga dakin Ababan ta sharo da palonsa ta dawo na hande ta sharo ta sharo nasu ta share tsakar gidan ta tattara ta cika baron da suke cikawa da shara kullum akai babbar bola a zubar,ta ja baron taje bola ta zubar tadawo tayi diban ruwa a famfon dake bayan gidansu ta cika dukkanin drums na gidan kafin ta zauna tafara wanke wanke tana gamawa ta dora girkin rana bayanta na wani irin riqewa amma ba daman nunawa.

Wanka ta shiga sbd jin ana kiran sallah kenan karfe biyu takusa kenan. Tana fitowa wanka sallah tafara yi kafin ta sauke girkin ta kwashe a kulan da ake kwashewa ta tsaya ta kalli uban wankin shago da aka kawo gashi tanason guduwa taje exams dinta ko yayane tinda kudin abin hawansu na hannunta Sumayyah Sulaiman ne zai kaita.

Anne data tashi tayi sallah ne taga Benazir din nata wankin kayan zuciyarta ba dadi sai kawai ta qaraso ta amsa wankin tana nuna dauriya da cewan ta warke Benazir din taje makaranta.

Ta hakura da jarabawar ta yau dan haka tace Annen taje ta kwanta kawai amma Annen taqi ta takurata dole ta shirya ta fice da sauri zuwa makarantar.

Tana fita mashin ta hau cikin sauri suka ringa gudu ya ajeta ta ciro kudinsa hannunta na rawa ta miqa masa ta shige.

Koda ta isa hall din dazasuyi exam din har anfara badan Allah yariga ya qaddara sai tayi exam din ba da bazasu barta ta shiga ba dan kuwa daqyar aka bari ta shiga bayan anc cinye fiyeda rabin time din exams din amma dayake ta dage tayi karatunta tana shiga tafara rubatawa cikin saa.

Sumayyah batasan Benazir din ta shigo makarantar ba dan haka tana fitowa exam dinta karfe qarfe hudu sai kawai suka wuce gida da sulaiman.

Benazir hudu da rabi ta fara neman Sumayyah koina bata gantaba gashi kudin hannunta bazai kaita gidaba sbd cikin sauri ba canji ta barwa mai mashin daya kawota sadaka tinda tasan sunada me maidasu gida.

Duk inda take saka ran ganinta ta duba bata ganta ba dan haka taje ta duba inda Sulaiman ke jiransu taga bayanan ta tabbatarda sun wuce.

Numfashi ta sauke mai dumi jikinta na sanyi sbd tana hango nisan tafiyar da zatayi ra qafa kafin ta isa gida.

Fitowa tayi tafara tafiya da qafa kanta hanyarta bata iya tsayawa kallan mutane ko wasu guraren sbd kada ta qara batawa tafiyarta lokaci.

Tafiya takeyi ba tsayawa mai nisa ko rabi batayiba magriba tayi ta qarawa kanta sauri sbd Ababa idan ya rigata komawa gida Allah ne kawai zai fiddata.

Tafiya takeyi tana qara sauri hankalinta na qara tashi da duhun dare dakeyi. Qafafunta wani zugin gajiya suka fara ga bayanta kaman zai rabu da siririn qugunta amma ba sanya qara sauri takeyi.

Sumayyah a gidan tana isa ta tadda cewan Benazir din ta tafi makarantar itama Take hankalinta yayi mummunan tashi sbd sun dawo daban daban Allah yasa kada Hande ta fada kuma Allah yasa Benazir din ta riga Ababa dawowa.

Karban wankin da Anne bata gama bane har lokacin tayi amma hankalinta gabaki daya yana kan Benazir dake waje ga magrib tayi. Addua takeyi tana qarawa akan Benazir da dawowarta.

Bata iso gida ba sai bayan sallar ishai qafafunta daqyar suke daukanta ga maqoshinta ya bushe qam sbd tsoron abinda zata tadda gidan da azababbiyar gajiya.

A tsakar gidan ta tadda kowa a tsaye ana jiranta Anne da sumayyah data gama shan dukan wahala kan Dawowa bata jira Benazir din ba duk kamanninta sun sauya sbd marika suna rakube gefe tsaye kansu a qasa jikinsu na rawa da tsoron abinda zaiyiwa Benazir.

Hande ma na gefe zaune kan kujera tanata fada akan ita bataga amfanin karatun nan nasu ba sbd fandarewa zasuyi idan suna shiga mutane.

Ababan a tsaye yake yana Nazarin matakin da zai dauka, Qarasowa Benazir tayi ta tsaya tsakar gidan jikinta da zuciyarta a mace sbd tasan Hukuncinsa akanta yau ba gudu ba ja da baya dan haka tsaya kanta a qasa batareda tace komaiba.

Shiru gurin yayi bayan fadan Hande babu abinda yake tashi tsawon mintina kafin ya dago ya kalleta da idanuwansa da sukai jajir da bacin rai da masifa Cikin muryar kai tsaye yace

"Daga ina kike? Ina kika je? Me kika tsaya yi kike dawowa gida yanzu?

Bata dago kanta gabaki daya ba ta bude baki jiki a mace cikin nutsuwa tace

"Kudin abin hawan ne bai isaba da muka dawo daban daban sbd Anne ba lafiya shine ta rigani dawowa nikuma na dawo da qafa"

Kallan Sumayyah yayi tasake yin qasa da kanta zuciyarta na karyewa sbd tasan dukan Benazir din zaayi itama. Dawo da kallansa kan Benazir yayi yana maimaita kalman sun dawo daban daban din wato dan barnar kudin Abin hawa.

Hakuri Benazir ta bude baki ahankali zata basa ya saukar mata da wani lafiyayyan mari a fuska wanda yasa habo zuwar mata nan take amma takasa saka hannu ta tare jinin Ya sake sakar mata wani marin a dayan gefen take gudun jinin habon ya qara gudu kanta na qasa.

Qafa yasa zai harbeta Hande tace barta haka ai ko yanzu gashinan taga hukuncin hakan tinda ga jini nan nai mata gudu a hanci.

Bai saurari Handen ba sbd kafin dawowar tata jinin sa idan an auna yakai 200 da yan kai sbd tashin hanakali da masifar idan itama ba guduwar tayi ba dan wlh da saiya kusa kashe uwarta. Dukanta ya ringa yi takai ta qafa zuciyarsa na tafasa da bacin rai da baqin cikin tareda zazzabin dolen data sanyasa.

Hande ce ta qwaceta tabasa hakuri ya fice daga gidan ita kuma Benazir din sumayyah tayi saurin qarasowa ta kamota jikinta tana fashewa da kukan tausayinta dan take taji ta dena jij nata zugi da radadin sbd ganin dukan Benazir dinta.

*_PHYDOORS FOOD AND MORE_*💯🔥

*_Ina masoya Abincin gayu dana gargajiya da Sea foods? Ga ingantattu kuma tsaftattun kayan Phydoors Sea foods and more da muka tabbatar da dadi, kyau, inganci da tsaftarsu tareda saukinsu._* *_Uwar gida, Amarya shin kun taba aikin Abinci da kayan Phydoors sea foods and more kuwa?_* *_Idan baki taba ba ina shawartarki da gwadawa sbd a take zaki gano bambamci da kuma damar Girki masu dadi da ingancin da suka wuce ki._*

_*Phydoors sea foods and more Suna tare daku a koina sbd suna aika kakansu koina a duk Inda kikeso cikin tsari da packaging mai kyau da kulawa hakama ga sauki da Ragusa,Akace siyan na gari maida kudi gida.*_

*_Phydoors food and more is a food branded based in abuja and offered national wide delivery of her items, available food stuffs are stone free crayfish , egusi, palm oil, plantain powder in kg, prawns 🍤 , fried kpomo, some from as low as 2k._* *_Contact her through this line 08062181151 or DM me let’s do paired order for minna and suleja. She’s based in abuja._* _*Or visit her instagram handle*_ @ _Phydoors_Food_

Daki suka koma Kaman marayu suka zaune kowannensu jikinsa na radadi da zugi Benazir bata iya ko dago kai ta iya cewa kala ba sbd batasan me zata fada ba ko cewa.

Anne da kanta ta dafi ruwan zafi tazo ta zauna tana gasa musu fuskokinsu da jikinsu gabaki daya zuciyarta ba dadi, Ta rasa tayaya zata iya ceto ko kubutar da 'yayanta ga wannan masifar sbd ita kanta ta kasa guduwa ko tserawa wannan rayuwar,idanma tinanin guduwa ko tserewa daga rayuwar gidan Ababan ya fado ranta wani masifaffen tsoro da ciwon hauka takejin kaman zai kamata shiyasa bata iya guduwa batasan cewan aikine yayi akantaba ya kafeta ko namanta zai ringa yankawa bazata iya guduwaba sai ranar dayace ta tafi da kansa. A ranar ko abinci daqyar sukaci sukai salloli sika kwanta kowannensu zazzabi na rufesa mai qarfi.

Washe gari Benazir batada exam kuma Interval na kusan sati day take dashi dan haka Sumayyah ce kawai ta tafi itama sbd uban carry overs datake dasu ne hadi dana wannan samister din suka saka exams dinta yin yawa ba ranar da batayi.

Da zazzabi sosai a jikinta ta tafi makarantar jiki a mace ga tsoro sbd bata taba fita ita daya ba bayan jiyan da yau din sun saba komai tare sukeyi da qanwar tata Benazir. Koda ta isa a jujjuye tayi exam din farko ta fito tana fitowa ta yanke jiki ta fadi Allah yasa Ms Ayshah na kusa dan haka take aka dauketa ta kira sir Bilal ba bata lokaci yazo yakaita asibiti.

Acan ta wuni yau da babu Benazir daga ita sai shi shine yayi jinyar cikin kulawa sa ita sosai.

Sai yamma ta daga hankalinta kan komawa gida da kansa ya kaita bayan ta karbanwa su Benazir da Annenta maganin zazzabi acikin nata harma dana shafawa ciwo.

Data shigo gidan aiki sukeyi cikin matsanancin zazzabi dan haka tajasu daki suma suka sha aka shafa na shafawa Allah yasa sun gama aiki suna cin abinci take dukkaninsu bacci ya daukesu.

Washe gari ma koda ta isa maboyar dasuke hawa napep din sulaiman maimakon ra gansa Alh bilal din ta tadda da kansa dolenta tashiga basu wuce makaranta ba gurin likita suka fara zuwa ya dubata ya sake mata allurai sai daya sakata cin lafiyayyan breakfast da aka kawo ba bata lokaci daga Kaante Hotel and suites, Taci abincin cikin kunya da takurawarsa kafin yabata magani tasha tukuna ya kaita makaranta ya wuce.

Kafin su shiga exam Ms aysha ta dan qara mata bayanin handout din course dazasuyi exam dinsa. Bayan sun fito saida yayi magana da ita da wayar Ms aysha ya bata qwarin gwiwa da kalamai masu sanyi nutsuwa kafin tashiga wata jarabawar sai gashi kalamansa da dokinsa yasa ta dan tabuka abin arziki sai abin ya mata dadi.

Tana gamawa Ms aysha tasata jiransa sbd yace a tsayar masa da ita din. Shine yazo ya dauketa bayan yaxo masu da abincin da aka saba kawo musu kullum daga Kaante H&S yau harda magani aka siya musu na zazzabi da qananun ciwuka haka.

Kafin sukai gidan dayake iya su biyu ne sosai yanzu yake bayyanar mata da soyayyarsa da kulawa sosai wanda yasata itama jin wani iri a duk lokacinda suke iya su biyun.

A gida kwana biyu da ake kawo musu magani sosai suke samun sauki dan Anne tini ta warware Benazir ce kawai takejin jiki a lokacin sbd ta daku sosai a ranar kuma ga azabar tafiyar qafan datayo sun kamata sosai shiyasa nata jikin sai ahankali.

Acikin kwana biyu da babu Benazir Sumayyah tafara samun shaquwa da sakewa da bilal da ms aysha dan kuwa sosai suke nuna mata wata irin kulawa da kauna, Ms Aysha qawar Bilal ce sosai tin primary sukai karatu tare dashi da ita da DD wanda ba wata tazara ce tsakaninsa da qanin nasa ba dan haka sukai karatu tare saidai DD tinda suka gama junior class a secondary yabar qasar Dd babba yakaisa Zurich gashican ya zama dan zurich su kuwa har secondary da jamia suna tare kafin yabar qasar daga baya yakoma spain gabaki daya qarin karatu amma basu yanke muaamala ba sbd kusan baida Abokin dayasan sun shaqu dashi kaman Ms ayshan, Mijinta ma sosai yake mutunci dashi kuma yana respecting alaqarsu sbd sun dade da komawa tamkar 'yan uwa, Bata taba haihuwa ba duk tsawon shekarunta da aure saidai bata cire rai ba tinda da sauran lokacinta yanzu ne aurenta yake cike 19 years dayi.

Sosai Ms aysha take jan sumayyah a jikinta da kulawa da kauna mai tsafta sbd ganin dagaske Bilal yake sonta so mai tsanani saidai haryanzu halinsa na gudun zuciya da tsoron batawa iyayensa rai yananan shiyasa yakasa bayyanarda soyayyarsa da alaqarsa da sumayyahn a fili dakuma qarin itama bayason sakata da matsala gidansu dik da haryanzu baisan taqamaimai rayuwar rashin yanci da azabar dasuke yiba a gidansu ya dauka dai normal tsoro ne na mahaifinsu sukeyi sbd yanada zafi da fada sosai. #MAMUH#

_Mamuhgee 15_ Akace Salati baya hana daukan rai hakama qaddara yashi ce ko an daunqulata bata dunquluwa,zuciyar Sumayyah batai shawara da ita ba acikin qanqanin lokaci ta saka bilal cikin kanta.

Har Benazir ta samu sauki kuma interval nata ya qare ta dawo suka ci gaba da exams bata fahimci 'yar kusanci da shaquwan da Sumayyah ta samu da Ms aysha da Sir bilal ba sbd hankalinta gabaki daya akan jarabawarta ya koma sbd babu tsayawa yanzu saita gama duka exams din.

Sumayyah kuwa itama ba dan laifi Ms aysha na iya kokarinta akanta ga bilal yanzu da duk ranarda baizo ya ganta ba a wayar Ms aysha yake magana da ita.

Tin tana jin nauyin ms ayshan sosai harta dan sake da ita sbd a rayuwarsu basu taba samun kulawa,kauna ko tattali da sakewa daga wani ba wannan ne karan farko datake samun hakan daga Bilal da ms ayshan.

Koda suka gama exams suka fara zaman hutu daga bilal din har sumayyah jin sukeyi ba dadi musamman shi din.

Readers Also Read