Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 48

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 48

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 48: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 48. Ganin sumayyah ya saka Wani bangare na…

3,361 words

Ganin sumayyah ya saka Wani bangare na zuciyarta sanyaya ta zubawa sumayyahn idanuwanta itama sumayyah ta qaraso da sauri ta fada jikinta ta rungumeta tana Kiran sunanta a Karo na farko bayan shekaru.

"Anne, Anne" take furtawa dukkanin jikinta na mutuwa da Wani irin dacin zuciya ja rabuwarsu.

Ita kanta Anne hawayen takeyi tana Jin dumin 'yarta data Dade da yarda da ta tafi lahira ta barsu.

Sun jima a Hakan Bena bata motsa daga yanda take ba sbd Bata hayyacinta Sam.

Sumayyah ce ta sake Anne tayi kan Bena din itama ta rungumeta tana kiran sunata tsananin son 'yar uwarta na motsa mata gaba Daya.

Ahankali Bena ta Bude idanuwanta jikinta ba qwari kaman yanda zuciyarta take ba qwari ta kasa ko motsawa a yanda take sai hawaye sirara da suka gangaro mata,

A Karo na biyu na Wani matakin raywarsu zata sake danne qunci tabarwa zuciyarta ita kadai taci azabarta ita kadai batareda ta sanar musu ba Dan hanasu shiga damuwa da baqin cikin rayuwar dasuka samu me nutsuwa da kwanciyar hankali.

Babu magana dake tashi a dakin nasu bayan ajiyar zuciya da hawaye dake sauka a tsakaninsu.

Ahaka suka dauki tsawon lokaci su kadai har azahar sai alokacin suka ci abinci sukai wanka kowannensu yafito fes zuciyoyinsu cikeda nutsuwa da kwanciyar hankali Banda Bena da dauriya kawai takeyi Amma duk dauriyarta Basu Dade da gama cin abincin da sukaci ba zazzabi me qarfin gaske ya rufeta musamman kanta dake tsananin ciwonda takejin kaman zai tarwatse.

Rikicewan jikinta ya saka hankalinsu tashi Basu tsaya Kiran Wani likita ba dole Akai asibiti da ita sbd har Amai takeyi jikinta ya sake gabaki Daya.

Suna Isa asibiti aka Bata gado dukkaninsu kin komawa gida sukai suka zauna Asibitin zaman Jira zuciyoyinsu ba Dadi.

********** AUis special care Zurich.

Kwanansu biyi da Isa Saida suka gama samun nutsuwa da ganin komai ya shiga daidai inda ya kamata ya shiga na Neman lafiyan DD din tukuna suka samu Daman kunna wayoyinsu Dan samun Daman magana da Wainda suka baro Nigeria.

Dd babba ne ya fara samun labarin batan Bena daga bakin Abbakar Dan haka yayi shiru cikin matsanancin mamaki da tashin hankalin Daya sake tabbatar masa da tabbas akwai abinda yake faruwa wanda suke zargi tin farko.

Wani Dan zufa ya share da tissue me laushi Yana jefarwa sbd tinanin Abinda zai biyo bayan batan Nan nata idan DD ya farka, Ta bangare Daya ga familynsa Dama suna cikin rudanin Bena data kasance ba mahaifiyar data haifi Amnah ba, lafiyar DD kawai kowa ke Jira ayi magana dole kowa yasan menene asalin Abinda yake faruwa.

Labarin batan Bena kaante shi zai bawa duk Wanda yakeda hannu a batan nata Daman yin koma menene manufarsa na Hakan Dan haka take dd babba ya sanar da Abbakar kada kowa yasan Bena kaante ta Bata baa ganta ba, Ayi duk bincike da zaayi me tsananin gaske daga boye kada abari kowa ya San Bata Nan,Abar kowa da sanin ta biyosu Nan Zurich gurin jinyar mijinta.

Wanna umarnin na dd babba ya saka hankalin Umme sake tashi Amma Kuma hakanan ta daure take danne tashin hankalinta cikin mutane tana nuna Bena din na can tareda su DD a Zurich.

Amnah ma Hakan Umme ta fada mata Dan haka yarinyar ta Maida hankali akan yiwa iyayenta adduar Allah yabawa daddynta lafiya ya dawo shi da mummy dinta su koma highbridge tare tinda tasan aranar da kafin ciwon daddynta mummy dinta a highbridge ta kwana.

Nafisat ma sosai ta dage gurin cigaba da kulawa da Amnah cikin so da kauna tana sake debe mata kewan iyayenta.

Ahakan cikin tashin hankali da matsanancin tsoro da tsaka me wuya familyn kaantes suke, Zargi da bincikensu ya qarfafa musamman Daya kasance ace lokaci Daya ansamu D a wannan halin hakama kawai a wayi gari babu Bena babu labarinta.

Abbakar da Kansa yaje gidan Ababa suka gaisa kaman yanda ya Saba ya Ciro kudi me yawa ya miqa masa.

Wani murmushi Ababa yasaki Yana kallan kudin yace

"Sakon dd babba ne ko na Benazir?"

Shima Abbakar murmushin yayi Yana cewa

"Sakon Bena ne sbd tafiyan gaggawa ya kamata zuwa can Zurich gu......

Bai qarasaba Ababa ya Dan sake wata dariyar takaici kafin yace

"Ita Bena din?akace batada lafiya Kuma shine harta warke zata iya tafiya."

Murmushi Abbakar ya sake sakewa yace

"Acan zaa dubata itama,gobe Inshallah zata wuce"

Shiru Ababa yayi zuwa lokacin sbd zuciyarsa data Dan fara shiga wasi wasi da shakka, Shin da gaske Abbakar yake Bena na kaantes gobe zata wuce Zurich din? Kokuwa dai fada kawai yakeyi? Idan Kuma da gaske ne Bena Bata wuce ba to ai ba kudi ya kamata a akawo masa ba da hukuma ya kamata yagani. Ta Wani bangaren Kuma yasan dd babba zai iya komai a sirrance har a kamasa sbd kada sunan kaantes ya lalace.

Tinani da lissafi yake Neman shiga Abbakar ya qare masa Kallo kafin ya Danyi gyaran murya sukai sallama ya miqa masa kudin ya wuce.

Yana barin gurin da mota Ababa ya saka kudin hannunsa aljihunsa Yana wucewa gaba batareda ya koma cikin gida ba Kai tsaye gidan Alh basheer bulama ya nufa.

Abbakar na barin kofar gidan Kai tsaye office din babban Jami'in da case din ke hannunsa ya nufa Yana Isa ya sanar dashi yanda sukai da Ababa.

Sallamarsa Sir Ashir bello yayi Yana Kiran wayar dd babba.

Bayan dd babba ya gama sauraransa Shima numfashi ya sauke ahankali yace,

"Saura matarsa da mahaifiyarta dasukaita kaida kawo a gidan ranar da abin ya faru, Suma a sirrance zaayi binciken banason Abinda zai jawo mana bacin suna da shiga headlines na labarin da ba ci gaba ko wata daukaka muka sake samu ba"

Haka a ranar da abin yafaru a footage na anguwan bayan anfito highbridge matar Dawood din bayan fitowanta sunga Wani me napep daya ringa binta a baya a hankali har suka bacewa anguwar gaba Daya Dan haka Shima a Yi kokarin tsananta bincike a gano napep dinsa a gano ko waye ko akwai abinda zasu Gane ta gurinsa sbd kusan duka shigowarta anguwar da fitarta sun duba dakyau sunga Yana bibiyarta daga nesa sosai Dan haka dole Shima akwai Wani Abinda yasa yake Hakan ko Kila tare suke.

Gyada Kai sir Ashir bello yayi Yana sake bawa dd babba tabbacin komai zai tafi yanda suke so zasu Gane komai a tsanake cikin sirri batareda sunyi alerting Wanda yake da hannun duk wannan abubuwan ba., Su anasu bangaren ma wanda miyagun qwayoyin jikin DD suka fito hannunsu suke da tsananin buqatan sani sbd hukuncinsu 40years ne gidan yari kawai.

*****Ababa hankalinsa na rabuwa biyu ya kusa Kaiwa gidansu momy Amma Kuma sai tinaninsa ya hanasa sbd idan ya fada musu zasu ankare da wuri so Dan haka idanma tarko ne aka hada masa su zasu iya kaucewa daga tarkon Dan haka ya fasa fada musu ya juyo ya dawo gida.

Yana isowa gida Bai fadawa hande komai ba ya shige daki yana sake shiga tinani da lissafi,

Babu ta yanda dd babba zaiga Bena da Anne tare ace besan Abinda ya faru Ba,Dan haka tabbas akwai abinda ake shiryawa a boye, Idan bazai Gane ko menene ba dole ya danawa su Safnah tarkon da sune zasu fada tarkon dd babba bashi ba Dan kuwa shi nasa laifin na canjan sumayyah da Bena ne Su kuwa hardana kisa a cikin nasu lefukan, Idan yaji tsit din yayi yawa dole yayi Abinda zaa San waye ya kashe hajiyar su Alh basheer bulama sai tashin hankalin ya karkata ya koma can yayi amfani da wannan Daman yasan nayi sbd yasan yanzu duk Ido da tsaro na Kansa, Allah dai ya Isa tsakaninsa da dd babba da zuriar kaantes gabaki Daya wlh. ##MAMUH#

_Masoya masu goyan bayanmu a da yaushe, masu san shek'e masge kwarkwatar idanunsu, da san kwakwale damuwarsu, da sanya bak'in cikin su facewa, su kwamaso sink'i-sink'in dariya, annashuwa da sassanyan murmushi kan fuskarsu, su antayawa ruhinsu salama, su sanbad'awa zuciyarsu yalwa, masu san farin ciki wajen karatun littattafan Hausa? to ku matsu kusa, dan nesa tazo kusa, ga shahararriya, hazik'a, fasihiyar, mai san kasancewar ku cikin annuri, wacce ta saba kawo muku nagartattun litttattafanta masu dad'i, wacce ta kware wajen rubuta dad'ad'an labaru tun daga kan wanda ya k'unshi nadama, kuku,tausayi, cin amana, da nagartacciyar soyayya mai yalwa mai sanya tsoho ko tsuhuwa su tuna da jiya samartakarsu da 'yan matancinsu ya motsa,_ _ta sake dawo muku da wani sabon salon littafinta mai k'unshe da abubuwan mamaki, al'ajabi, kala-kala, wa'azantar da ban tausayi gami da sanya zuciya tsinkewa, wanda zai nishad'antar daku, ya d'ebe muku kewa ya sanya masu hawan jini, sauka, masu ciwon zuciya darawa,_ _*BAK'AR SHUKA...2 shine sunan littafin, wanda *HAUWA A USMAN JIDDARH* tayi bajakulin fasaharta da basirarta wajen antayo muku dashi, *BAK'AR SHUKA...BOOK2*_ _zaku biyu naira d'ari hud'u (400) kacal domin samun labarin da karantashi akan 400 kacal da k'arin bayani sai ku tuntub'i wannan number 08037649871 ko ku tura ta 0153259310 Gt Bank Hauwa Auwal Usman_

*_Arewabooks@@Mamuhgee_*

85

Qarfe ukun Daren ranar aka samu nasarar yiwa DD allurar qarshe cikin guda ukun daya kamata ayi masa duk bayan kwana biyu ake daya sbd ba qaramin qarfin gaske qwayoyin sukaiwa jikinsaba hakama duk allura Daya kudinta ba qaramin firgici zaka shiga ba na jinsu Dan haka sai ranar su dd babba suka dawo hayyacinsu yanda ya kamata suna fatan farfadowansa kowane lokaci,

Ta bangare Daya Kuma suna cikin fargaba da tashin hankalin ta inda zaa fara masa bayanin uwar 'varsa ta Bata baa ganta ba tsawon kwanaki biyu. Zeenah gabaki Daya ta jeme a iya kwanakin biyu sbd tashin hankali da damuwa,

Ga batan Bena ga D a kwance ga Amnah can gida kullum kira takeyi tace a Bata mummynta suyi magana basuda mafita dai kame kame suke mata kullum sbd maganar ma yarinyar abari tasan ba'asan inda mummy dinta take ba Bata taso ba Dan kuwa zata iya shiga mugun halin da basusan ya zasuyi da ita ba.

Karfe 5 na Asuba daidai DD ya budewa idanuwansa dasukai nauyi ahankali batareda ya motsaba sbd jikinsa da yayi Wani irin nauyi na kwanciyar kwanaki,

Ahankali cikin kasala da rashin kuzari ya sauke sanyayyan numfashi ahankali tareda lumshe idanuwansa va sake budesu anankali

Abu na farko Daya fara zuwar masa Akai shine sunan Bena Wanda shi kansa baisan wane hali zuciyarsa take ciki ba a yanzu kanta dama shi Kansa.

Dakin Dayake ya juya Kansa ahankali ya kalla ya mayarda idanuwansa kan sauran kayan monitoring heartbeat dinsa da sauransu ya tabbatarda a Asibiti yake Kuma tabbas Bata Nigeria bane musamman duba da blue kayan patients din dake jikinsa.

Babu kowa a dakin Dan haka ya sake rufe idanuwansa Yana sauke numfashi ahankali ahankali a Jere Yana son fara calming numfashinsa kafin yafara kokarin tashi zaune tini alerm na dakin ya fara qara me sauti daidai misali na Kiran nurse zuwa ga dakin.

Yana tashi zaune ana Bude kofan Dakin nurse ce ta shigo sai Naseer a bayanta da sauri suka shigo Naseer na wuce nurse din ya Riga Isa ga DD din Yana Jin Wani farin cikin ganinsa zaune.

Bai tsaya komaiba Yana Isa ya rungumesa sbd da Bai tashi yau dinba shikenan baa San ranar tashinsa ba har shekara zai iyayi a kwancen Amma Allah ya amsa adduar su ya tashi.

D baida Wani qarfi ko Dadin zuciya Dan haka idanuwansa ya mayar kawai ya lumshe yana kasa motsawa daga zaunen har nurse ta duddubasa taje ya kirawo likita har guda biyu da Wani nurse Daya namiji aka taru aka dubasa dakyau aka sake diban jininsa Akai gurin awo dashi Dan duba idan sauran drugs din dake jinin nasa allurar ta qarasa qona su.

Barka da tashi likitocin sukai masa cikin kulawa da farin ciki kafin suka fice daga dakin suna sake tattauna maganar ciwon nasa Suna ficewa ya Bude idanuwansa dake rufe ya Dan Kalli Naseer dake cikeda farin ciki sai kokarin Kiran su dd babba yakeyi a waya.

Magana yaso Yi Amma bayason ko Bude bakinsa nauyin komai na jikinsa yakeji Dan haka ya Dan ziro gafafunsa qasa ahankali Amma yakasa miqewa tsaye sbd sunyi nauyin da bazai iya tafiya da Kansaba Kai tsaye a yanzu daga tashinsa.

Yana Nan zaune Naseer ya kira su dd babba ya sanar musu take kowannensu yahau sujjada Yana godewa Allah sbd su kadai suka Dan mummunan tashin hankali da fargaban dasuke ciki akan wannan halin Dayake.

Bayan ya gama waya dasu Naseer din dawowa yayi ya sake kallansa cikin kasa boye farin cikinsa yace "zan shirya Maka toilet yanzu ka Dan gasa jikinka kanl sake kafin zuwansu dad kaante"

Yana fadan Hakan ya nufi bathroom din da sauri ya shige kaman bana asibiti ba kaman a hotel Dan haka komai tsaf yanda DD din ke bugatan toilet hakama kullum sai anwanke an sake tsaftace komai na toilet din duk da babu me shiga Amma sbd suna jiran farfadowansa kowane lokaci shiyasa koyaushe ake cikin Shirin duk Abinda zai buqata bayan tashin nasa.

Fitowa yayi da Kansa ya kama DD din Wanda baya iya tafiya haka Suka lallaba ya shiga toilet din dashi yakaisa har bakin bathtub Daya hada ruwan dumi sosai ya kawo masa komai Dazai bugata ya Jere masa harda sabbin towels guda biyu dasu toothpaste da toothbrush na wainda yasan asalin dasu DD ke amfani.

Zare rigar patient din dake jikinsa yayi ahankali tareda sakinta qasa tareda short din Dayake jikinsa ya shige bathtub din ahankali tareda kwantawa Yana rufe idanuwansa.

Shiru yayi cikin ruwan tsawon lokaci seda ya ji jikinsa ya Dan sake sake sbd ruwan zafin dake ratsasa sosai suka sakar masa da jiki tsawon lokaci kafin ya fito cikin ruwan duk acikin sanyi ya dauki brush ya tsaya yayi brush tareda wanke bakinsa da mouth wash kafin ya koma qarqashin shower ya sakarwa Kansa ruwan zafin sai alokacin ya sake sauke ajiyan zuciya.

Yanda ruwan yake sauka jikinsa ahankali ya sakashi ahankali ya fara dawo da tinanin halinda suka samu kansu a ciki kafin shigarsa wannan halin da baisan meya samesa ba har lokacin.,

Bai iya Tino wahalar dayasha ba kafin kasancewa da Bena a yanzu iya nutsuwa da yanayin duniyar da suka kasance a tare yake Jin feelings din da dumin numfashinsu Daya ringa fita Yana sauka a lokacin harma da Wani girmamammen lamari Daya risketa aciki Wanda ya sakasa sallama mata duniyarsa gabaki Daya sune yake tinawa suna dawo masa acikin Kansa,

Bai taba kusantan kowace mace ba Dan haka baisan ya ake nufin Virgin ta kasanceba Amma dai a iya abinda yaji Yakuma tarar Bena din ta sake komawa Virgin bayan haihuwan ne? kokuma bata Haifa Amnah da kanta ba? Idanma Cs Akai mata to ya akayi Bai taba Jin dinki a Mararta ba sbd yasha shafa Mararta tin kafin su zama Abu daya yanzu din.

Meyake faruwa ne? Shine baisan komaiba akan wainnan abubuwan kenan kokuwa dai akwai abinda ya kamata y sani dinne Bai saniba?

Wainnan tinanin sune suka cika Kansa kafin na tashin hankalin da mamaki suka biyo baya sbd sai alokacin yake tinanin meya samesa ya shiga halinda ya shiga, Idan ya Tina daidai mutuwa yaji yakusa yi da mummunan desire da zai kira da dark desire ma sbd a lokacin da Bena batazo ba zai iya afkawa duk macen Daya samu Wanda zai iya kashe Kansa idan Hakan ba a faru bayan ya dawo hayyacinsa sbd tsananin gyanqyaminsa da raayinsa na macen Dayake so ne har cikin zuciyarsa da ruhinsa kawai zai iya kwanciya da ita shiyasa bazai taba iya kwanciya da dayan matarsaba sbd zai cutatar da ita matigar ya kwana da ita babu digon sonta cikin ransa, Yabarta ne idan yaga bazai iya adalci ba zai sallameta taje da budurcinta ta samu Wanda yake sonta har Zuciya.

Ya jima sosai Yana San jikinsa ya Dan samu karfi kafin ya gama ya fito daureda towel a qugu ya ratayo dayan a wuyansa Yana tafiya ahankali fatarsa ta sake haske sbd kwanciyar dayayi kwana biyu yayi fayau kaman mace me sabon shigan juna Biyu.

Ko Daya fito tini Naseer ya ajiye masa kaya da underwear sabbi na sunspel masu tsada.

Jikinsa ya goge a hankali da sauran rashin kuzarinsa ya gama ya saka underwears din da saka short wando me Dan tsayi kadan da black rugbay shirt sai alokacin yayi salloli Yana gamawa yayi adduoinsa Yana tashi ko gadonsa Bai qarasaba su dd babba suka shigo dakin kowannensu a tsanake cikin jallabiya

Dan lokacin 7 harta wuce.

Dd babba ne ya fara ware hannu cikin farin ciki me tsananin gaske ya rungumesa tareda Dan bubbuga bayansa Yana kiransa da "my champ" Shima dad kaante cikin farin cikin ya Dan rungumesa Yana Jin zuciyarsa na sanyi sbd Daya rasa DD Shima kaman yanda ya rasa Bilal da shikenan baisan ya rayuwarsa zata kasanceba.

Zeenah data shigo daga baya da gudu ta garaso ta fada jikinsa tareda rungumesa Shima rungumeta yayi ahankali Yana Dan Jin sassaucin nauyin zuciyarsa dake azabtiwa da rashin ganin wadda yakamata ya fara Gani farko farko.

Hawaye Zeenah ta ringa yi Wanda ya sakasa Bude bakinsa dole yayi mata magana da cewan

"Meyesa kike Kuka?

Kin dauka zan mutu ne?

Wa zan barwa 'yata da.. . Shiru yayi tareda kasa qarasawa Yana dagowa ya Kalli su dad kaante Kai tsaye dd babba ya kalla Yace

"Bata zo bane? Lafiyanta kalau right??

Zeenah na Jin Hakan ta dakata da hawayenta tana zamewa daga jikinsa tana Satan kallan dd babba dayace kar Wanda ya sanar masa halinda ake ciki.

Dd babba fuskewa yayi cikin basar da zancen da kulawa yace 'tama kasan batajin dadi so tana Nigera sai ta warke sosai zata iya zuwa daga baya kokuma idan mun koma shikenan."

Yanda yayi maganar yasaka DD Kai tsaye Shima ba Wani shakka ko Wani Abu kunya yace

"Sosai ne batada lafiya??

Nayi forcing kaina sosai ne akanta har haka? Did I really f... cikin Wani irin Jin nauyi dad kaante ya katsesa da cewa

"Rashin lafiya ne kawai Kuma ta warware inshallah."

Naseer ma Kansa qasa yayi sbd nauyin maganar DD din Wanda Sam shi bai ji Wani komaiba sbd yasan tabbas ya nuna mata qarfi tinda Bai dauka zai sameta a yanda ya sameta din ba,and baitaba dauka haka ake samun Kai acikin wannan rayuwarba shiyasa ya kasa controlling Kansa Dan haka idan har shine ya sakata a wannan halin Yana bugatan komawa Nigeria cikin ganganin lokaci sbd yaga yanayin jikin nata kada tanacan tana Jin jiki sosai Bai saniba.

Dd Babba Kuwa bai damuba da zancen dinba sbd yasan shi Dan Kai tsaye Daman musamman ga wadda yake Jin yanxu bazai iya controlling Kansa akan Yanda yakeji a zuciyarsa ba shikuma Daman Hakan shine fatansa.

Yanayin yanda DD yayi shiru ne Kauai ya saka dd babba Dan shiga nazari sbd idan Basu nuna masa taji sauki da gaske ba ba lallai ya zauna anan din dasuke son ya zauna ba har su fara zuwa su samu mafitan nema Bena din da qaske sbd dole zasu masa dubara abarsa Nan su koma su kadai. Shima DD din a natse cikin sanyi ya karanci yanayinsu Daya bayan Daya Amma Bai kawo tinanin komai a ransa ba bayan na sosai ya nunawa matarsa qarfin Daya illatata may be.

Kowanne fuskewa yayi suka danne suna sake bayyanarda farin cikin tashinsa Dan haka tini suma yan Nigeria aka sanar dasu suka samu farin cikin farfadowansa Kuma ana sake shiga fargaban bayyanarda maganar batan Bena.

Shi Kansa bai sake nuna damuwa ko Wani yanayi ba gameda maganar Bena din saima ya Dan ringa daurewa Yana nuna jarumtar qarfin jikin Dayake samu.

Har yamma suna Asibitin anata nuna masa kulawa kaman zasu hadiyesa shi dai Bai Wani sake sosai ba sbd zuciyarsa data kasa samun cikakkiyar nutsuwa, Hakanan yakejin Sam hankalinsa ba kwantawa zaiyiba matigar ba Bena din yaji ba.

Washe gari ahaka suka sake wuni results dinsa sun fito babu sauran drugs din a jininsa Amma sun Basu takardar Asibiti data hukuma Datake bayyanarda bashine yasha da Kansa ba Basa Akai Bada saninsa ba Dan haka hukuman gasar ta Bada takardarta akan idan sun koma gida Nigeria Akai binciken gano komai zasu shiga cikin zancen Wanda zaa kama da qwayoyin. ##MAMUH#

* Arewabooks@Mamuhgee_*

86

Readers Also Read