Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 49
Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 49: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 49. Wannan bayanin da Akai tas a gaban DD…
3,358 words
Wannan bayanin da Akai tas a gaban DD lokacinda suke office din hukumar Zurich din sai alokacin yasan haqiqanin meyake faruwa,
Wato Wani ne ya saka masa mugayen qwayoyi, to Amma a Ina?
Idan tinaninsa yazo daidai a ranar tinda gari ya waye babu Abinda ya sakawa cikinsa hatta ruwa Bai Sha ba sbd damuwa da bacin ran labarin accident din Bena haka ya tashi ta biyo jirgi baici komaiba harya sauka, Daga airport office dinta ya fara tsayawa Kuma anan ma baici komaiba haka ya Isa highbridge baici komaiba Saida yayi ordern abinci Wanda ya Saba cin abincinsu Daman bawai yanzune yafara ci ba,
Bayan wannan abincin baici komaiba a ranar Kuma tabbas Yana gama cin abincin Nan yasamu Kansa a mawuyacin halin da babu Abinda yake tinawa sai azabar daya ringa Sha a jininsa Daya ringa quna Yana babbaka, Zuwan Bena shine yabasa Iko da Daman yaqar ciwon da azabar sbd sonta Mai tsananin gaske da baimasan akwaisa a ransa hakanba shine yafi garfin azabarsa ya iya dannewa.
Shiru yayi a bayan motar shida dd babba Wanda Shima tinanin yakeyi Yana Jin a jikinsa ko menene matar DD din Daya tanada alaga da wannan Lamarin.
Shi kuwa DD tinani ya ringayi tsakanin ordern abincinsa da kawo abincin babu Wanda yazo gidan bayan Safnah sai Bena daga baya. Bena ta fita Sam a zancen ya cireta sbd Koda ta iso Yana gap da rasa ransa ma gaba Daya
Dan haka koma menene a tsakanin zuwan Safnah da Wanda ya kawo abincin ne.
Batareda ya juyo ya Kalli dd babba ya Bude baki a natse yace
"'Me binciken da akeyi ya bayar? Ansan waye ne? Akwai Wanda zargi ya nuna? Menene ainihin dalilin Daya Hana Mummyn Amnah tahowa? Shiru dd babba yayi tareda sauke numfashi Shima Bai Kalli DD dinba yace
"Bayan matanka biyu a ranar babu Wanda yaje gidanka, Su Biyun ne kawai suka shiga a dai time din da ake zargin daga lokacin ne koma menene ya sameka."
Sai alokacin D ya juyo ya Dan Kalli dd babba da idanuwansa dasuka qara haske sosai ya Bude baki Kai tsaye yace
"Kai ne ka Bada Daman a Dorawa BENAZIR alaman tambaya akan wanna maganar kokuwa su masu binciken ne??
Shima dd babba sai alokacin ya juyo ya Kalli Dawood din da kwariininsa Shima ya cika masa Ido musamman da babu Annuri ko Daya a fuskarsa. Wani lalataccen murmushi dd babba yayi kafin ya dauke idanuwansa akan DD din yace
"Kanada huija ko shedan fiddata daga zargin kenan?
"Ko menene acikin abincin danaci a ranar ko ruwan danasha suke,
Dan haka a lokacinda aka tafi gidana a in in Dayake kan dining shine Abu na farko Daya kamata a dauka Dan aunawa."
"Kana tinanin baayi Hakan bane?
Babu abincin da aka Samu ko abinsha a dining ko kitchen koma duka dakunan gidan Dayake nuni da kasha Wani Abu ma kafin shigarka halin daka shiga.
Numfashin takaici DD ya sauke sbd Abinda ya kamata ayi bashi akeyi dinba a nasa ganin Dan haka yace "Naci abinci a ranar Wanda nakeda tabbacin shine ya bamu wannan matsalan Dan haka zan kira securities na highbridge zasu turo footage na sake dubawa,
Idan har babu komai Dayake nuna naci abinci a gidan har shara idan an duba to tabbas fitar da abincin Akai Dan haka Wanda ya fitar da abincin shi kawai ake bugatan Gani asan inda zaa fara sauran binciken , " Wanna maganar tasa ta saka dd babba yin shiru Yana shiga nazari tabbas dole idan yaci abinci to meyasa zaa kawar da komai agi barin ko spoon Dayaci abincin dashi Kuma ko a sharar gidan babu inda aka zubar da komai da alama gidan aka bari dasu kenan gaba Daya.
Ajiyan zuciya ya sauke tareda kallan DD yace karya kira securities da Kansa tinda Bai gama warkewaba ya bari Ashir bello zai nemesu ya sake duba footage din dakyau ya duba Wanda ya fita da Wani Abu Dayake nuni da kayan abincin ne.
Hakan da dd babba yayi shikuma shine ya sake jefa zuciyarsa cikin zargin akwai abinda ba'a son ya sani shiyasa baa San ya shiga zancen bayan shine sosai a cikin zancen.
Shiru kawai yayiwa dd babba din har suka Isa gidansa aka saukesu su Kuma suka Isa masaukinsu.
Baibu waya a tareda shi sbd bashine ya kawo Kansa qasar ba kawosa Akai Dan haka da daddare har ya kwanta ya kira Naseer a wayar gidansa yace ya kawo masa waya ko iPad Yana son magana da Amnah. Hakan dayace ya saka Naseer fita ba jimawa ya kawo masa tasa iPad din Dan yayi amfani da ita.
A daidai wannan lokacin Amnah na tareda Nafisat tana gyara mata kanta cikin kulawa Kiran ya shigo.
Amnah na ganin numbers din na waje ta San daddynta ne da sauri ta tashi daga jikin Nafisat tana murna ta dauki wayar.
Kyakyawar fuskar daddynta ce ta bayyanar mata cikin tsananin farin ciki ta ambaci sunansa tana cewa "Daddy na ya warke Allah ya karbi addua na danakeyi kullum yehhhh"
Wani sanyi ne ya shiga zuciyarsa ya Dan lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta yace
"Angel din daddy nayi kewanki" Zaunawa tayi daga tsallan da take tana marairaice fuska tace
"Daddy nayi missing naku kaida mummy kullum bana iya bacci da daddare sbd mummy Bata Nan,
Nidai Dan Allah ku dawo,kace mummy na ta dawo....hawaye ne suka fara gangaro mata sbd a kwanakin ba garamin kewa da guncin rashin mahaifiyarta takeji ba dagyar take iya bacci kullum haka Nan take Jin wata irin kewan mamanta tana cinta kusan kullum da zazzabin dare take kwana haka Nafisat ke kulawa da ita Sosai kaman jininta.
Shiru yayi tareda zubawa Amnah din idanuwansa dasuka saka yarinyar sake tsinkewa da hawaye tana sake ambatar sunan mummynta jiki a sanyaye.
Wani Abu ya Dan hadiye daga maqoshinsa Daya tsaya kafin ya Dan diadaita Kansa batareda Abinda yake zuciyarsa ya sauka kan fuskarsa ba cikin nutsuwa da kulawa yace
"Angel,Ina mummynki taje ne??
Dagowa tayi ta kallesa tana sake tsiyayo hawaye tace
"Mummy ba tana gurinka ba inji su Umme da dad kaante hakama aunt Z tace mummy tazo gurinka itama batada lafiya zasu warke ku dawo tare"
Shiru yayi tsawon mintina yana shigar da zancen Kansa kafin ya sake kallanta da idanuwansa da zuwa lokacin sun fara sauyawa ya sake tausasa murya cikin nutsuwa yace
"Tinda ta taho gurina Kuma bakiyi waya da ita bane?
Girgiza Kai tayi tana cewa "kullum idan nakirata bana samu Kuma idan nace aunt Z ta bani mummy na muyi magana sai tacemun tana bacci kokuma tana sallah"
Shiru sukai dagashi har Amnah din tsawon mintina kafin ya dago ya kalleta yace ta miga Nafisat din waya taie ta dauko littafin karatunta na Arabic ta nuna masa.
Migawa Nafisat din iPad din hannunta tayi tareda migewa tabar dakin zuwa dakin mummy dinta da gudu Dan dauko littafinta.
Tana ficewa Bai tsaya komai ba Kai tsaye cikin kamewan murya yace ta fada masa ina Bena take.
Shiru Nafisat tayi gabanta na faduwa hakama tana kasa dagowa ta Kalli wayar sbd tsoro da kwarjininsa.
Cikin Dan daga murya ya qara maimaita tambayar bacin ransa Dayake controlling Yana Dan bayyanuwa. Rawa hannuwanta suka Dan fara Yi murya na rawa tace
"Bata Nan"
"Tana Ina??
"Bansaniba,Amma ance wa Amnah tana tareda ku"
Shiru yayi kawai daidai lokacin Amnah ta kawo littafinta ta ringa masa bayani yana sauraranta kawai da amsa mata Amma kwata kwata hankalinsa da nutsuwansa baya Akai.
Yana gama magana da Amnah Kai tsaye Ummensa ya kira Yana kiranta cikin murna tahau gaisawa dashi tana Jin Dadin iinsa kaman daga sama taji yace ta Basa Bena yanason magana da ita.
Murmushin qarfin hali tayi tana cewa
"Yanzu ta kwanta bacci sbd ilkin nata Bai gama warwareba kasan Kuma tana bugatan samun isashen hutu Dan haka kabari lokacinda take farke sai a kiraka.
Numfashi kawai ya sake tareda cewa shikenan ya kashe wayar.
Yana kashe wayar saukowa yayi daga gadonsa ya zira slippers ya fito da keys na motarsa Daya dake qasar Yana fita ya fada motar yaja ya fice batareda Naseer da Zeenah dake gidan ba sunsan futarsa.
Kai tsaye gurin dd babba ya nufa sbd baya bugatan Wani kwana kwana ko boye boye a sanar dashi Abinda yake faruwa bayason kayan ciwon Kai da haukan dasuke Neman manna masa Dan tini Kansa ya fara daukan zafi da nauyi.
Koda ya Isa yasan room numbers nasu Dan haka Kai tsaye na dd babba ya nufa Yana Isa ya tadda room service zata fito Dan haka dakin Yana Bude ne Kai tsaye ya shige tana taresa ko sauraranta beyiba ya wuce zuwa quryan bedroom din sbd babban daki ne na masu kudin gaske Wanda zakaji kaman kana gidanka ne a sake.
Daidai kofar bedroom din Yana Isa ya sakata cak Jin Abinda dd babban ke magana Akai cikin waya Dayake Yi da Sir Ashir bello babban Jami'in binciken sirri.
Bayanin Ababa da asalin komai Sir Ashir bello ya buqaci ji komai da komai sbd yanzu binciken ya shigo da mutane cikin zargi da yawa, Matar Dawood din Safnah da mahaifiyarta na ciki dumu dumu hakama Ababa da ake zargin batan Bena dashi Kuma idan har yanada saka hannu a batan Bena shi to tabbas akwai alaqan batanta da Abinda ya samu DD.
Hakama ta Wani bangaren dole itama Bena din da Naseer zasu shigo binciken sbd Bena kadai ce ta samesa tagansa a halinda ya shiga dalilin gwayoyin. Ajiyan zuciya dd babba yayi yafara yiwa sir Ashir bello bayanin komai Daya bayan Daya na asalin rayuwar dasu Bena da mahaifiyarsu suka taso ciki da asalin Rabin kwakwalwan da mahaiflyarsu da sumayyah wadda itace Asalin budurwar Bilal Kuma mahaiflyar Amnah tareda yanda kaddara ta samar da cikin da renansa da yanda Ababa yarinta musu barazana a fakaice cikin dubara har suka aminta da auren sumayyah tazo ta rasu a gun haihuwar yayi canjen sumayyah da Bena tareda boye musu cewan sumayyah Bilal ne yazo ya sace gawarta da haryanzu basusan inda gawar suke ba wand yakeda tabbacin Shima wannan zancen akwai abinda yake boye cikinsa Basu saniba.
Kudin Daya ringa bawa Ababa da yanda yaketa bincike da Neman hanyar karbe mahaifiyar Bena daga hannunsa duk ya hada ya fadawa sir Ashir bello din Yana dorawa da cewa
"Ina zarginsa da batan Bena kaman yanda nake zargin matar Dawood da saka hannu a kan duka lamarin biyu sbd kishinta hakama Ina zargin akwai Wanda yasan me suke aikatawa idan ma suna aikawatan sbd yanda duk Abinda muke Gani akwai me bibiyab safnah din.
Idan akwai abinda DD ya taba ji a rayuwarsa Wanda ya buga zuciyarsa Nan take yaji Yana Neman kamuwa da heart attack to wannan abubuwan Dayake ji ne a yanzu a bakin dd babba Wanda idan a gurin Wani yajisu bazai taba yarda da Hakan na faruwa a duniya ba. ##MAMUH#
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 87 Kansa kasa yarda yayi da Abinda yaji Dan haka ko ganin gabansa bayayi ya juyo yabar dakin ya fito jiri na juya Kansa sosai ya sauko qasa kaman Wanda yake cikin maye haka ya Isa motarsa ya shiga ya zauna zufa na feso masa Tako ina yanajinsa a wata duniyar ta daban,
Kansa ba zafi yakeyi ba wuta yakeci sosai da sosai, Bena dinsa ce ake fadan ta taso a wannan rayuwar dayakejinta kaman duniyar wasu dabbobin ce ake fada?
Bena dince ta taso tana wankin wasu qattin Maza? Bena dinsa ce ake maganar da yanzu tana hannun yan drugs? Bena dinsa ce ake maganar ta taso cikin yunwa da wahala irin wannan da ko karensa bazai iya bari ya Rabi irin wannan wahalar ba bare ace Macen datayi nasarar da Saar shiga inda babu wata mace a duniya data shigar masa wannan gurbin, Bena dinsa ce ake fadan ba ita bace asalin macen da 'dan uwansa ya so ba,ya muaamalantu da ita suka samu ciki ya haifi Amnah ba....
Bilal da sumayyah ana nufin tare suka Kone a motan Bilal? Idan haka ne meyasa gawa Daya aka Gani? Hakan na nufin dayansu na Raye? Waye cikinsu a Raye?
Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Wannan mutumin daya haifi su Bena mutum ne kuwa kokuwa wani dabban ne Allah yayi da suffan mutane?
Antaba Kaisa Asibiti antabbatar da lafiyansa kuwa?sbd wasu mutanen ana zaune dasu ne kawai batareda ansan mahaukata bane masu asalin Abinda ake kira hauka.
Wata rawa jikinsa keyi sosai zufansa na qaruwa sbd Wani mummunan zazzabin tashin hankalin Abinda Bai taba ji ba ko tsammata a rayuwar ba Daya rufar masa a take.
Hannuwansa na rawa ta tayarda motar Yaja Yana fitowa daga parking lot din gurin Yana daukan iPad din Naseer dake hannunsa ya nema Naseer din Kai tsaye ya sanar dashi ya Siya masa ticket din komawa Nigeria yau din Nan komai tsakan dare.
Naseer na samun sakon ya miqe daga kwancen Dayake cikin mamaki da tsoro da fargaban ko DD din yaji maganar Bena ne.
Fitowa yayi yaje har bedroom dinsa ya dubo yaga baya gidan ya fita yaje ya duba motarsa ma Bata gidan take yasan yasan komai na maganar rashin sanin inda Bena din take Dan haka baida zabi bayan cika umarnin DD din.
Take yayi contacting Wanda zai Siya musu ticket da komai take sukai sa'a akawai jirgin dazai tashi zuwa Nigeria cikin Daren Dan haka dole ya hau hada musu kayansu ba tareda ko Zeenah ta saniba sbd tayi bacci na gajiya da rashin nutsuwar zuciya dasuke ciki musamman ita da kullum Kuka takeyi sbd shakuwa da kaunar dake tsakaninta da Bena ga tsananin tausayinta da kaunarta data qaru a ransu me tsananin gaske bayan da dd babba ya fada musu komai gameda raywarsu Bena din wadda hatta Umme data ji sai data kwana tana Kuka itada Zeenah,dad kaante kuwa Jin yakeyi da shine yasan da Hakan tini da bazai iya bin komai a hankali dinba kama Ababan zaayi a batar dashi gabaki Daya Annen Kuka ai insha Allah aikin zai karye ko baya Nan.
Koda DD ya iso gidan Yana shigowa bedroom dinsa kawai ya nufa ya a sauya kayansa daga na bacci Daya fita dasu baa cikin nutsuwa ba zuwa Riga da wando marasa tsayi ya saka facemask da Fcap ya fito Kai tsaye ya fito tini Naseer ya saka kayansu a mota Dazata kaisu airport suka wuce.
Har lokacin cikin Wani irin mummunan hali yake sbd zazzabin dabai taba shiga bane a jikinsa hakama zuciyarsa Wani irin wuta take ci dashi tana qarawa jikinsa zafi da zufa.
Maganar ma rashin ganin Bena ganganci ne ake fada bayan ansan yanda tayi rayuwa hannun mutumin dayake amsa sunan ya haifesu Dan haka shine na farkon zargi ma akan batanta, Fatansa dai yanzu yafara zuwa ya tsaya gabansa suyi magana ta billions tinda itace yarin dayafi Ganewa akan komai.
Idan kudine matsalansa to zai nuna masa kudinsa ko uwarsa ce calculator saiyayi batan lissafin da zai Basa shikuma Abinda yakeso daga garesa na Ina Bena take.
Hakama zai ninka masa ninkin su ya siyar masa da yancin Annen Bena ko nawa ne ya fada zai Basa daganan zai aikasa inda yakamata ace tini an Dade da aikasa sbd Bai yarda shi din me hankali bane.
Suna Isa airport ko awa Daya Basu rufa ba jirginsu ya daga zuwa Nigeria.
Dagawansu baifi da awa Daya ba Zeenah ta ankara da cewan ita kadaice a gidan take tahau Neman wayar Naseer Bata samu sai ga sakonsa Daya tura mata tin kafin su tashi ya shigo a lokacin na cewan D ya sakasu komawa Nigeria a Daren.
Tana ganin sakon hankalinta yayi mummunan tashi gigice ta kira dad dinsu ta fada masa.
Shima tashi hankalins yayi sbd yasan zafin kan DD bazai bari a tsaya ana komai a nuku nuku a boye ba sbd kada sunan family ya lalace akan Benan Nan ya fahimci yafison kowama ya sani sunan Kaantes ya dade Bai Baci ba.
Da Kansa ya fito dakinsa zuwa dakin dd babba ya sanar dashi halinda ake ciki.
Shiru dd babba yayi Shima baiso Hakan ba dan haka yace suma ba amfanin zamansu a nema musu jirgi gobe su koma.
Dad kaante na ficewa wayarsa ya daga ya kira Abbakar ya sanar dashi a sake budewa Ababa wuta harma dasu Safnah din asake Bude musu wuta ta yanda Wanda yakeda hannu acikin batan Bena zai iya yin Abinda zaa ganesa da wuri kafin DD ya iso zafin abin zai iya baci sosai.
Yana gama waya da Abbakar baccin dake idanuwansa ya kaurace gabaki Daya sbd baisan me Dame DD ya saniba a cikin Daren dazai iya barin qasar a take.
Umme ma hankalinsu tashi yayi data samu labarin abinda yake faruwa na tahowar DD Dan haka ta kasa samun nutsuwa kwata kwata.
************ Ababa a Karo na biyu Abbakar ya sake kawo masa kudi tareda buqatan son gaisawa da Anne wai Bena zatayi magana da ita a waya.
Shiru yayi wannan Karan qin karban kudin yayi ya Dan dake ya koma cikin gida ya jima kadan ya fito ya Kalli Abbakar yace batajin dadi bazata iya fitowa ba ta kira ni zuwa anjima zan hadata da Annen.
Hakan Daya fada ya saka Abbakar cewa shikenan sukai sallama ya miqa masa kudin dayazo dasu baiyi Niya ba Amma sbd kada a Gane komai saiya amsa kudin kawai Yana washe bakin qarfin hali sbd lamarin yafara isarsa.
Abbakar na wucewa yakoma cikin gida Yana hada zufan tashin hankali da tsoro sbd ya tabbatarda akwai abinda yake faruwa,
Wai shi wace qaddarar ce ma ta Kaisa hadewa dasu Safnah?
A baya duk barnarsa dayake abarsa cikin rufin asiri da lumana, Tafiyar Bena zir na Neman janyo masa masifu kala kala Dan haka wlh bazai yarda su jefasa masifar datafi wadda yake ciki ba ta sanin gaskiyarsa da kaantes sukai akane haihuwar Amnah.
Hande data ga Yana hada zufa ransa bace Yana Neman recorder dinsa da yayiwa mummunan boye wadda duk Abinda su haj Nuratu bulama da Safnah suka tattauna dashi akan abubuwan dasuke buqata.
Hakama abinda Basu saniba a ranar da suka Basa kudin Nan Bai baro gidan ba Saida ya qyalla Ido akan me aikinsu Rabi Daya ga yanda suke maganar komai a gabanta bayan takawo masa kayan Sha Hakan ya tabbatarda masa da tasan dukkanin sirrinsu.
Ranar Daya tabbatarda Basa gida saidaya koma ya samu ganin Rabin Kallo Daya yayi mata maganin Dayake mata dashi ya kamata take ya bayyanar mata da buqatansa ta zai raba duk Abinda ya samu da ita Amma ta sanar dashi duka motsinsu sbd ya tabbatarda zasu iya munafurtansa.
Rabi data San halinsu ciki da waje Kuma taga yanda suke tsoran shedancin Ababa dayafi nasu take ta amince da buqatansa sbd ganin Suma sun yarfada da nasa balain yafi nasu Dan haka Rabi tasan sai tafi zama safe idan tana tareda Ababa Dan haka cikin qanqanin lokaci yagama sanin sirrinsu a gurin Rabi hatta video din yanda suka kashe hajiyar Alh basheer bulama tana dashi duka suna hannunsa.
Bayan ya samu video dinne ma yayi baqin cikin shiga lamarinsu sbd yasan zasu iya Shafa masa kashin kaji Dan haka kafin ta lalace masa tasu zai lalata ya samu Daman silalewa kafin adawo Kansa.
Kayan Daya dauka dauka ya fitane yasaka hande binsa tana Kiran sunansa Amma Sam Bai tsayaba ya fice hande ta tsaya kallan iKon Allah tana tsinewa Anne da zuriarta sbd sun zautar masa da 'da, Sauran duk sun tafi ynzu wannan data dawo zata haukatar mata dashi.
Bayan fitarsa wayarsa ya fidda tareda Kiran Rabi yace ta shirya ta gudu ta koma gidan kaantes sbd Tona asirin su Safnah zaiyi porthacort zashi da sassafiyar washe gari daga can bazai dawoba.
Tana Jin Hakan tace maganar kudin dasukai zasu raba Kuma fa?
Cikin masifa da takaici yace " au baki gode na barki ba zan zareki acikin su shine kike maganar kudi bayan kinsan kema ba fita zakiyiba idan zancen ya fita, Abinda yasa na barki ki koma Kaantes ki nuna barazanar kasheki sukeyi kika gudo sbd so neke Suma ki ringa sanar Dani halinda ake ciki har na samu na gudu tukuna,idan ha haka ha ai kema inada shedan dake suke kulla komai har kisan dake Akai tinda kingani kikai shiru harda video kinada Amma kikai shiru."