Kenza eBookz

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 51

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 - Chapter 51

Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 51: Zafin kai complete by mamuhgee wps office 1 Chapter 51. Hakanan Kansa na ciwo yayi sallar Asuba…

3,342 words

Hakanan Kansa na ciwo yayi sallar Asuba suna idarwa kusan dukkaninsu a tare suka jima masallacin Saida gari yayi haske kafin suka fito ko ciki Basu qarasa ba Kiran Sir Ashir bello ya shigo wayar dd babban dake hannun Abbakar Kuma shine ya dauka yaji sakon Sir Ashir din Wanda Shima Bai rintsaba ko kadan shi da yaransa kwana sukai Aiki da bincike tareda zuwa gidan DD na highbridge suka duba fingerprints na Safnah dake gidan wanda yazo daidai da Wanda yaje jikin ledan da DD yakai musu hakama same fingerprints ne dake jikin motan da Bena tayi accident da ita kwanakin baya da ake bincike Akai itama a boye da dd babab ya saka.

Shiru Abbakar yayi bayan kashe wayar Sir Ashir bello din Yana Rasa ta yanda zai isar da bayanin da Neman da Sir Ashir din ke musu.

Dukkaninsu musamman DD da idanuwansa sukafi na iyayen nasa kaifin kwarjini suka zuba masa suna jiran Abinda zai fada shikuwa so yeke iya dd babba zai isarwa sakon.

DD da ransa ya Baci ya hade fuska dakyau tareda kallan Abbakar cikin kamewa da Bata Rai yace

"Banajin akwai sauran Abinda ake boyewa Wanda bansaniba,idanma akwai zan sani ayau din,.ka fada me Sir Ashir bello din yace,Ina sauraronka."

Shiru Abbakar yayi kafin ya Kalli dd babba Wanda Shima yanzu sakon kawai yake buqatan sani shikuwa dad kaante kallan mamaki duka yake musu sbd baisan binciken me duk suke jiran sakamakonsa har haka cikin daga hankali ba.

Numfashi Abbakar ya sake Yana San kasa kallan DD yace

"Sir Ashir Yana buqatan ganinka acan sbd kace baka buqatan zuwansa Nan koyaushe kawo report sbd kada a ankarar da yan jarida Amma yace Yana buqatan zuwanka sbd sakamakonsa komai ya fita na qwayoyin da aka shayar da DD da Wanda aka shayar da kakarsu Bena harma da sakamakon binciken accident din Bena.....

Wani irin Kallo DD yayiwa dd babba cikin matsanancin mamaki da zuciyarsa dake daukan Wani nauyi da harbawa ba daidaiba sbd Bai taba sanin accident din Bena bana Allah bane akwai zargin da akeyi akan Hakan shine aka boye masa akwai Wanda ke bibiyab matarsa da Wani sharri, Meyasa zaa boye masa dan kuwa da tini zai fara Bata kariyar da ko Kansa bai sametaba.

Shi Kansa dad kaante mamakin ya shiga sosai Yafara rarraba idanuwa cikin firgicin meyake faruwa da familyn nasu wai.

Dd babba kuwa Kai tsaye Bai iya cewa kowa komaiba ya wuce gaba Abbakar na bayansa ya je ya dauko key din motarsa da sauri.

Shima DD Kai tsaye Naseer ya kira Wanda Shima ranar a cikin Kaantes ya kwana take ya fito cikin qananun guntayen kaya Shima ya tada motar DD din Suma suka rufawa dd babba baya Dad kaante na kasa tsayawa yayi Dan andena barinsa Baya tinda Shima babba ne a familyn ya dauko key da Kansa Bai tsaya Kiran driver dinsa ba yaja ya mara musu baya.

dd babba ne yafara Isa yau Yana fatan komai yazo karshe sbd zarginsa da hankalinsa Daya kasa kwanciya akan matar DD Dan haka baya cewa komai har suka Isa

Suma DD a cikin motarsa babu me iya magana sai nauyi da tafasan da zuciyarsa keyi akan Abinda zasu tarar na duk Wanda yakeda saka hannu akan accident din Bena, Bai damu da Wanda ya shayar dashi mugayen drugs dinba shi ayanzu wanda yake son hallaka matarsa yake son Gani.

Suna isowa Kai tsaye suka fito daga shi har Naseer tare suka nufi ciki daidai lokacin da Sir Ashir da idanuwansa sukai Wani luhu luhu sbd rashin bacci da aiki tuquri na azaba dasukai acikin daren.

Miqawa dd babba report din yayi Wanda Kai tsaye DD ne ya fara saka hannu ya karba Dan ganin suna Neman Bata lokaci gurin bayani da boye boye.

Yana budewa yafara bin rubutun ahankali da reports din Yana karantawa.

Shiru yayi tsawon seconds Yana kokarin Dora zancen cikin Kansa a daidai.

Kallan Sir Ashir bello yayi fuskarsa a matiqar hade da yanayin wulaqanta yace

"Waye Safnah din?

Daga Sir Ashir har dd babba da Naseer kallansa suka dago sukai cikeda sanyin jiki da mamaki, Naseer ya kalla ganin alaman duk sun Santa da idanuwansa ya kafe Naseer Yana jiran amsa

Naseer ya Dan matso gefensa kadan cikin sanyin murya yace

"Second wife Dinka,'yar uncle Dinka Alh basheer bulama, Safnah basheer bulama"

Cikin Wani irin mummunan yanayi yace "kana nufin SSB??

Shiru Naseer yayi sbd bazai iya Basa wannan amsan kai tsayeba Dan kada suyi breaking zuciyarsa bayan tsananin baqin cikin da zai samu Kansa a ciki na Jin matarsa ce tayi wainnan ayyukan.

Kallansu yayi Daya bayan daya kafin ya tsaida kallansa kan dd babba Yana cewa

"Meye ne?? Kunyi shiru ne Kuna tausayin waye ne? Kuna kunya ko baqin cikin ace matatace tayi wannan aikin?? Like seriously?? Kallan Naseer yayi Kai tsaye yayi wurgi da takardun Yana juyawa yace

"Kira manyan hukumar yan drugs dake Lagos wainda case din nawa yake hannunsu wainda zasu miqata hukumar Zurich dake Neman inda qwayoyin suka fito sune zasu San abinyi da ita Amma kafin Nan muje naji meye hadin wancan mutumin da ita dataje gidansa ta bawa mahaifiyarsa qwayoyin hakama meyasa mahaifiyar tasa babu Abinda take kira sai sunansu su Biyun dole akwai Wani abin da basu saniba hakama idan Safnah ce ta batar da Bena da saka hannunsa tinda yayi niyar guduwa.

Kansa Wani tiriri yakeyi Yana daukan zafin gaske sbd yanzu ne ya tabbatarda Bena na cikin hadarin gaske Jin abubuwan dake faruwa.

Suna ficewa dd babba ya Kalli Sir Ashir ya sauke numfashi cikin nutsuwa yace

"Yanzu da akeda shedu da tabbacin itace zayi wannan ayyukan zaku iya kamota a shigar da case din hannun manyan hukuman yan drugs a fara tambaya da bincikenta yanda ya kamata ta hanyar da kuka Saba ji da irinsu.

Angama" sir Ashir ya fada sbd Daman Jira suke sosai dasu samu ta shiga hannunsu Dan kuwa wainnan qwayoyin ba qaramin zancen bane a gurinsu Dan yanzu akan Hakan shi wata hanyar samun Qarin girmansa tazo musamman manyan hukuman yan drugs da zata shigo ciki basuda Imani ba sani ba sabo Dan kuwa da tin farko hannunsu zancen ya shiga da babu Abinda zaa tsaya yiwa boye boye da tini Safnah anrufe bayaninta na Wani ake.

Dd babba na barin office din Shima Sir Ashir ya Bada umarnin a buga takarda a aika Lagos ta email yau a bugo musu stamp a dawo da ita su fitar ta tabbacin zaman samun qwayoyin dasuka Fi Muni a tareda Safnah din.

DD da Kansa yake tuqin motar Wanda ya saka Naseer yin shiru kawai Yana jiran su Isa Shima.

Koda suka Isa highbridge dokarsu da baa taba takawaba yau duka Saida DD ya takasu Wani mahaukacin horn yake musu jiki na rawa aka Bude masa da matsiyacin gudu ya shige Kai tsaye ya nufi gidansa ko parking daidai baiyiba ya tsayar da motar ya fito.

Naseer ne ya fito Shima da sauri ya rufe motar ya biyo bayansa suka qarasa ciki.

Hanyar kitchen suka nufa Kai tsaye tareda nufar store din da sauri Naseer yayi gaba ya Ciro key din inda ya ajiyesa ya Bude kofar tareda turawa ta Bude gabaki Daya.

Ababa dake zaune gabaki Daya karfinsa ya qare kaf babu sauran kuzari a jikinsa ko kadan sbd azabar kwana zaune dayayi Yana kirgan kudin da lisassafinsa gabaki Daya ya kunce,

Idanuwansa gabaki Daya sunyi luhu luhu sun fito sunyi jajir zagayen idanuwansa su Yi baqi sosai sbd azabar rashin rashin rintsasu da yayi ko kadan be rintsasu ba kudine yaketa Daman kirgawa ya kasa hada ko miliyan Ashirin tin dare har safiyar, Idanuwansa Basu taba haduwa da azaba irin ta yau din ba, Fankokin sunqi mutuwa sai daga kudin sukeyi koya hada ya aje, Yayi yayi ya kasa kashesu, Ya kasa hakura sbd taurin zuciya da naci da kwadayi da Neman mafitan dayakeyi. Babu iskan ventilation a dakin Wanda ya sake azabar dashi da numfashinsa sbd tsananin qamshin kudin Daya cika dakin babu inda window yake yasaka ko iskan fankar bayaji zufan jikinsa kusan ya qare Dan kuwa tin Daren yake tsiyayan zufa me yawa har safiya, Ruwan jikinsu sun qare daqyar yake iya daga hannunsa Yana cigaba da taba kudin Amma lissafin tini ya kunce masa babu Abinda yake so kawai a budesa ya fita iskan Allah ya dakesa ko baa basa ko sisi ba abarsa ya tafi sbd qamshin kudin kashesa zaiyi ya masa yawa aciki ya zamar masa cuta.

Kallansa sukai a wulaqance suna kallan idanuwansa da basa Gani sosai sbd kumburi da Jan dasukai,

Shi Kansa dagowa yayi ya kallesu dishi dishi yake ganinsu ko magana baiya iya Yi sbd azaban nauyin da Kansa yayi da azabar ciwo.

DD ne ya matso gabansa ya tsaya sai dayayi shiru ya hadiye tafasa da zafin da zuciyarsa keyi ya Bude baki Kai tsaye ya jefa masa tambayar waye ya Akai yasan Safnah bulama hartaje gidansa ta durawa mahaifiyarsa qwayoyi.

A yanda yake cikin matsananciyar azaba da wahala Yana Jin tambayar ya dago ya sake Bude idanuwansa dasukai masa zanen na Panda ya Kalli DD dakyar ya Bude baki yace

"Safnah ce ta Kori Bena da Annensu, Safnah ce ta biya kudin gaske me yawa suka bawa hande bana Nan hande ta Basu Anne da Annen sukai amfani suka Kori Bena ta tafi sun shiga duniya."

Naseer ne ya shigo dakin tareda cakumo Ababan ya fito dashi daga dakin ya jehosa harabar gidan inda zai samu iska ya Dan dawo daidai yayi bayani da kyau.

Sake maimaita Abinda ya fada yayi DD ya Kalli Naseer yace sakashi booth muje inda zeyi magana.

Ababa na Jin Hakan ya zare idanuwansa na Panda Yana cewa

"Safnah ce da haj Nuratu sukai komai yanada duka shedu da komai da zai bayar"

Naseer be sauraresa ba ya shaqosa wannan Karan idonsa biyu ya Bude Booth ya Jefasa ciki Ababa na Neman siqewa suka rufe Booth din suka shiga motar.

Kai tsaye office din Sir Ashir Suka nufa suna Isa aka Bude both Wani marar Imani cikin yaran Sir Ashir bello din ya saka hannu Daya ya Ciro Ababan Wanda tini yafara Neman somewa a Booth din sbd azabar zafi da rashin numfashi. ##MAMUH#

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 90 Idanuwan Ababa Basu gama budewa ba aka jefasa cikin Wani daki me masifaffen duhu da baka ganin komai se dai Kaji murya.

Zare idanuwansa ya fara Yana Neman ganin inda zaiga Dan haske komai qanqantarsa Amma babu cikin murya Mai tsananin bacin ran gaske DD ya sake jefa masa tambayar ya Akai yasan Safnah??

Rawar baki ya fara zaiyi magana yaji saukan Wani masifaffen Marin bayan hannun qato daya sakasa kifewa qasa kunnuwansa na dauke ji diff.

Rarrafawa ya fara Yana Neman inda zai dafa ya tashi aka sake jeho masa wata tambayar wadda kunnuwansa dasuke dauke ji Basu ji ba Dan haka ba amsa take aka sake kifa masa Wani Marin Daya dawo da jinsa take cikin gigicewa da murya me qarfin gaske yace

"yata ce nine na haifeta...

Shiru gurin ya dauka dukkaninsu shiru sukai musamman DD Daya kasa fahimtan me zancen ke nufi, Shi Kansa dd babba dake kan waya Yana Jin komai sbd yace Sir Ashir bello ya barsa Yana buqatan Jin komai.

Shaqosa officer din yayi cikin qarfi da rashin Imani yace

"Wacece yar taka?? Safnah bulama ake magana.

Shaqar data kusan raba Ababan da numfashinsa yasanyi shi kusan sakin fitsari Yana bubbuga hannun dake wuyansa sai Daya kusa mutuwa officer din ya sakesa lokacin Naseer ya shigo dakin sanyeda glasses din dake saka suna Gani cikin hudun ya kama Ababa ya daga sama tareda mannasa da bango a karon karshe ya sake tambayar gaskiyar Safnah da inda Bena take.

Yana Jin muryansa Naseer ya Bude bakinsa da muryarsa ta shaqe sbd wuyansa Dasha shaqa be dawo daidai ba yace

"Nine na haifi Safnah basheer bulama, Safnah da Benazir uwarsa Daya ubansu Daya wllahi, Nine na haifesu duka Kuma Annen Benazir ce ta haifesu duka, Su hudu ne, Sumayyah,sameerah, Bena da Safnah"

Kallan DD sukai dukkaninsu sbd zuwa lokacin kan kowa ya sake daurewa, Ababa yace shine ya haifi Safnah,to Kuma Safnah a matsayin 'yar basheer bulama aka Santa.

dd babba ne yayi shiru cikin zurfafa tinanin tabbas Anne ta sanar dashi yayanta hudu, Sumayyah, sameerah, Bena da Safnah.,

Safnah itace wadda ta gudu tabar gida, Safnah itace yar Anne Ababa yake nufi kenan? Safnah da Bena suna auren miji Daya kenan ko me??

Dukan wahala Naseer dake cikeda takaicinsa sukaiwa Ababa shida officer din Amma still Abu Daya yake fada cewan shine ya asalin uban Safnah ba bulama ba.

Ganin taurin ransa yayi yawa ya saka su Basa Daman kawo shedan dayace zai kawo akan Hakan.

Ta bangare Daya kuwa takardarsu suketa Jira cikin matsuwa ta dawo ta email dinsu sbd su kame Safnah wadda sunancan Suma cikin matsananciyar tashin hankalin rashin ganin Ababa da inda yake ga labarin gidansa Daya Kone kurmus ya sakasu sake shiga baqin ciki sbd sunso ne a kamasa da wainnan qwayoyin a gidansa.

Da motar office aka tafi da Ababa har shagon wankinsa inda ya boye jakar kayansa da komai Daya dauka na tafiya porthacort.

Ciro kayan yayi aka karba ana kokarin budewa yaga hankalinsu na Kai ya juya da matsanancin gudu zai tsare cikin rashin wasa da lamarin ba Bata lokaci aka harbe qarasa Daya wadda Bata karye dinba take ya zube a gurin Yana zunduma Wani mummunan ihun azabar daya sakasa somewa take jini na zuba sosai a qafar.

Kaman yankakken rago haka aka washesa aka saka mota Akai asibiti dashi.

Ana zuwa Asibiti bayan ana karbesa anyi ciki dashi bullet akwai aka buqaci Asibitin ta cire a nadesa hakanan a dawo musu dashi suka tafi aka barsa da jamian tsaro biyu suyi gadinsa.

A can office bayan an Bude komai na kayan Ababan anan aka samu duka Wani Abinda Daya saka DD kasa tsayuwa Saida Naseer yayi saurin tareda aka kawo masa kujera ya zauna ana qarawa AC din office din qarfi sbd Bai taba Gani ko Jin tashin hankali ba a ruyuwarsa irin wannan,

Shine duk acikin irin wannan abubuwan da Bai taba ji ba ko a labarai,bare drama ko film sbd bayama kallansu, Shine yake auren mata biyu dasuke uwa Daya Uba Daya.

Babban Abinda yake sake saka jikinsa daukan rawa da shiga matsanancin tashin hankali shine da mummunan qaddara ta sakasa Wani Abu ya shiga tsakaninsa da Safnah kafin Bena da Bena ana nufin ta haramta garesa kenan har abada??? Zai rabu da ita kenan bashi ba ita har abada?? Shikenan zata rabu dashi taje ta auri Wani namijin???.......Bai qarasa wannan mummunan tinanin ba zuciyarsa ta kasa dauka take numfashinsa ya fara daukewa Kansa na Neman tarwatsewa..

Da sauri akayo Kansa Amma kafin kowane motsi tini ya fice hayyacinsa sbd balain yayi masa yawa da masifa yake ya rasa numfashinsa dole aka kwashesa zuwa Asibiti.

Naseer ma dole yabarwa Abbakar harkar hukumar shikuma ya koma jinyar ubangidansa.

Kafin takardarsu ta dawo daga office Nan suka kira Alh basheer bulama Kai tsaye suka buqaci ganinsa batareda Yi masa Dan taqaitaccen bayanin Abinda yake faruwa.

Shima acan take jininsa yayi mummunan Hawan da dole saida akai gaggawar Nemo likita ya dubasa sbd Dakar zuciyarsa da abin yayi.

Hankalin iyalin Alh basheer din ba qaramin tashi yayiba da halin Daya shiga Kuma cikin rashin sa'a Koda Akai masa Kiran Yana tareda matarsa Daya da me aikinta tana jera musu abincin a dining Dan haka komai a kunnen me aikin akaisa.

Tana ganin halinda Alh basheer din ya shiga ta silale ta koma dakinsu na masu aiki ta shige toilet ta kunna famfon ruwa ta fidda waya ta Nemo numbern momy datake Aiki gidan sbd ita Dan kawai sbd ita, Tin jiya momyn ke kirana akan idan taga zuwan baqo gidan kowane iri ne gurin Alh basheer bulama ta sanar make dan ta tanadi wainda zasu kawar mata da Ababan Yana Isa batareda ya isar da Abinda yaje fada ba.

Ganin babu baqon dayazo sai Kuma ga wannan mugun sakon wayar ya saka shahida me aikin Kiran momy cikin bayani a natse Dalla dalla tayiwa momy bayanin Kiran da Kuma Abinda akace ankama 'yarsa ta bogi Safnah bulama dashi wato wasu qwayoyin.

Shiru momy tayi wadda sukafi kwanaki nawa Basu rintsaba sbd tashin hankali da baqin ciki me tsananin gaske tareda rashin sanin madafa.

Kashe wayar shahida momy tayi tana miqewa daga zaunen datake bakin gado shiru tafara kaida kawo hannuwanta na tsananin rawa kaman yanda zuciyarta ke harbawa da matsanancin tashin hankalin da baa saka masa raba ba.

Idan yanda Shahida ta fada ne ance Safnah bulama kawai ne ita baa ambaci sunanta ba Hakan na nufin baa San da itaba aciki ne kokum lissafin be zo kanta bane...

Ta faru ta qare musu kenan, Yau rana ta batar musu. Wace qaddararriyar masifar ce ta kaisu Sako Ababa a rayuwarsu suna komai a tsanake hankali kwance yanzu komai ya lalace,

Jinin Rai na kisan mutum nawa ne a hannunsu? Ita na hajiya Dana Rabi ne a hannunta saina Wanda ta taba yi a bayan aurenta da bulama ya mutu.,

Safnah kuwa jinin ran Wanda tafara kashewa na farko shine Wanda bayan barinta gida ya kamata yaso yimata fyade ta kashesa har lahira Wanda akan Hakan momyn ta hadu da ita ta taimaka mata suka boye gawar daganan suka zama uwa da 'ya, Sai Kuma jinin Hande da itace ta kasheta tinda itace ta dura mata qwayoyin a baki.

Idan har baa ambaci sunanta ba to tabbas nata asirin da sauransa Dan haka bazata sanar da Safnah ba silalewa zatayi ta gudu kafin Azo kamasu tabar Safnah a sameta ita Daya.

Sauran qwayoyin karshe dasuka rage musu ta dauko jikinta na tsananin rawa zata Bude ta zubasu a bakinta tashanye itama ta shiga mummunan halinda zaa dauka Safnah durata mata itama tayi Dan ta kasheta idan yaso kafin ta warke dai lokaci yaja case din ya mutu ita ta tsira.

Harta zuba a bakinta taji Bazata iyaba tayi saurin fito dashi tana gobe bakinta ta mayar dashi leda ta jefar tsakiyar dakin tana shiga Sabon tashin hankalin Neman mafita Dan haka gwara dai ta gudu inda zata tsira da rayuwarta.

Gurin drawer na aje kudinsu ta nufa ta Bude jikinta na wata irin rawa tahau diban kudi ta cika qatuwar handbag dinta babba ta dauki passport dinta ta saka tareda sauran id cards nata.

Tana fitowa Safnah dake dakin itama nata idanuwan kaman na Panda duk sun fito sunyi baki sbd tashin hankali da rashin rintsawa ta fito sukai Karo a palon.

Kallan juna sukai ta kalli momyn a tsanake itama momyn ita ta kalla tana boye tashin hankalinta ta kalleta tana Dan bayyanarda kulawa tace

"Bari naje na dawo yanzun Nan nayi Miki bayanin Wani abin mamakin kiji."

Gaba tayi tana Hana yanayinta bayyana.

Harta fice Safnah batace mata komaiba sai jakar hannunta data hango kudi masu tarin yawa aciki musamman daloli.

Mamaki ne ya kamata Dan haka ta Bude dakin momyn ta shiga ta nufi inda suke ajiye kudi taga babu komai se yan canja,

Passport din momyn ta duba Bata gansa ba nata kawai ta Gani Dan haka ta sake shiga matsanancin mamaki da tashin hankali.

Juyawa tayi zata fice ta hango ledan robar qwayoyin dasukai amfani dasu tsakiyar dakin take ta fahimci akwai babban Abinda yake faruwa.

Fitowa tayi da sauri daga Palo ta nufi harabar gidan har momyn ta kusa ficewa da kota ta tsayar da ita ta qarasa gurinta tayi qasa da glass Safnah tace

"Momy nesa ne zakije??

Cikin girgiza Kai tace "aa yanzu fa zan dawo,Dana dawo zakiji komai fa."

Jan motar tayi ta wuce Safnah ta bita da Kallo tana goge hannunta daga ledan qwayoyin data sakawa momyn bayan motarta batareda ta saniba.

Momyn na ficewa itama motarta ta dauka ta fito da sauri tabi bayan momyn.

Sun ficewa motacin jamiaan tsaro gudu uku suka iso gidan maigadi ne ya nuna musu motocin su Safnah dasuka fice yanzu Dan haka take suka bi bayansu Suma.

Hanyar barin gari momyn ta kaman tana kallan madubinta ta lura da motar Safnah dake binta Abaya.

Readers Also Read