Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 1

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 1

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 1: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 1. Follow this link to join my WhatsApp group:…

4,447 words

*Z A K I*

By Khadeeja Candy

1️⃣

Carar Zakaran dake harabar gidan ne ya katse min dogon bachin da nake. A hankali na matsa fuskata dauke da murmushi domin ko kadan hakan be bata min rai ba, na daga hannuna a sama ina mika tare da kara watsakewa, kamar kullum yau ma bachin ya min dadi, ba dan gurin da nake kwanciyar ba, sai dan farinciki da kwanciyar hankali da natsuwa irin ta masu wadatar zuci data cika min zuciyata nake kwanciya da ita a kowane dare. Kamar wacce akai wa dole haka na bude manyan kuma lussasun idanuwana da suka rine suka sauya kala sakamakon dadewar da nai ina bachin. Akan farinciki na sauke idonuwana wato mahaifiyata wacce ke sanye da wani jan yade kodadden irin na talakawa kuma na gadonmu.

"Wainar ki ce take ci tun dazun aka aje miki"

Da yaren buzanci mahaifiyata take muna min kyanwar dake kusada ni tana cin waina.

Murmushi nai na kai hannuna na shafa kyanwar kana na shiga mata magana da yaren buranci.

"Kin cinye min waina ko?"

"Ataa yau ba za ki je baranki ba ne?"

Kanane ya tambaya, hakan yasa ni saurin tashi daga kwancen da nake, na fito daga cikin bunkar ina hamma ba tare dana rufe bakina ba, ba dan kuma ban san babu kyau ba, sai dan rashin kula da watsi da addini irin na mu na... Da hanzari na nufi wani dan guri da muka killace da kwano domin yin wanka ko kuma ba haya. Ba wanka nai ba domin wanka be dame ni ba duk kuwa da kasancewar na fi kowa tsabta a cikin gidan mu amman a hakan sai na kwana uku ban yi wanka ba. Fitsari kawai nai na fito da sauri na wanke fuskata da fassashiyar butarmu marar murfi, sai da na gama wanke fuskar sannan na nufi gurin da muke girki na dauki gawayin kara na saka a bakina na tauna na saka yatsana na wanke bakin na kuskure sannan na wanke kafafuwana na nufo bukkarmu da sauri tuna ban yi sallah ba yasa na dawo na dauki butar nai alwala na sake kowa bukkar wanda zan iya kiransa da dakinmu. Zanen dake daure a kirjina na cire na dauki riga da wando na wani shudin yadi mai kamar laile na saka na dauki hijab na saka nai sallah mai kamar asha ruwan tsuntsaye, wato da sauri domin cikin kannanen lokaci na yi na gama. Bakin dankwali na dauka na cire hijab din kaina na saka bakin dankwalin mai kama da karamin gyale na rufe kaina kamar yadda na saba ko kuma na ce muka saba.

Na kai hannu na dauko madubi tare da gawayin dana daka na kwaba tare da man shafi a guri daya, tsayawa nai kallon kaina a madubin ina murmushin daya kara bayyanar da kyauwona har dimple dina suka bayyana, sai faman lumshen manyan idanuwana nake ina budewa. Abu ne da ya ke bayyane, bana bukatar kowa ya kalleni ya fada min cewar ina da kyau, kyau na hali ko na halitta kyau na jiki ko na fuska, ni kaina idan na kalli madubi kyawona tsorata ni yake, idan ba a kirani balaraba ba to ba za a cireni a jinsin india ba indiyawan ma sai an tona, hakika ni kaina na san ina da kyau na wuce misali, kyan dake hana ni shakaf a cikin al'umma, gashin kaina kadai idan na sake ya sauko mutune har mamakin yadda nake da yawan da tsohon gashin dake saukona har mazaunaina suke. Ba sai na fada ba, duk wanda yasan jajayen buzaye yasan su da kyau da gashi sai dai a cikinsu ni din ma ta dabam ce a bangaren kyau. Man dake gabana na gawayi na dauka na shafa a fuskata a take farin fuskarta da kyau ya gushe na koma kamar ba ni ba, dogon hancina kawai zaka gani ka iya gane ni shima kuma sai idan ka sanni farin sani sosai. Sannan na mike tsaye na dauki kwagirin dana saba ratayawa a koguna (kwankwaso) idan zanje yawon bara na daura. Gurin da mahaifiyata take zaune naje ina mata sallama da yaren buzanci.

"Na tafi Nana"

Haka nake kiranta da sunan dana tashi naji mutane na kiranta da shi duk kuwa da kasancewar ba shine aihanin sunanta na gaske ba.

"Allah ya tsare a samo da yawa"

Ta fada min tana dariya ni kuma na kada kai na fice ina murmushin domin bata san gaskiyar abun ba, a duk tsawon kwanakin da nai ina aikin. Sai da nai nisa da bukkarmu ta yadda babu wanda zai iya hango ni sannan na ra6a ta cikin kangon gidan da muke gaban bukkar mu wanda wani shahararren mai kudi yake ginawa na shiga ta gurin da aka fasa domin yin windows na fada cikin wani gurin da ban san me za ayi da shi ba, daki ko falo, na dauki kayan aikina na bi ta kofar gaba na fice, na saba ba tun yau ba, idan nai nisa da gidan mu da sunan zuwa bara kamar yadda mahaifiyata take saka ni sai na biyo ta window kangon gidan na dauki kayan wankin motana, na bi ta kofar fita na fito, har yau mahaifiyata bata ta6a sanin cewar ina wannan aikin ba, ni kuma ban ta6a ganganci fada mata ba, domin na san zata hana ni idan ta gano ba bara na ke ba, kamar yadda take son nai, ni kuma bana son barar domin tana ci min rai, kamar yadda take kankantar ni ga duk wanda na mikewa hannu na ce ya bani. Ya zame mana kamar al'adar yin bara a titi ko manyan gidaje ko ma'aikatu domin samun abunda zamu ci, wasun mu suna da shi wasunmu suna da rufin asirin da zasu iya rike kansu ba tare da sunyi bara ba, tsabanin mu da kullum sai mun yi bara muke samun abunda zamu ci. Na sha ganin irin wulakancin da ake ma mahaifiyata kala kala idan muje bara musamman akan titin manyan motoci wanda hakan yake bakanta min rai, sai dai ita ko a jikinta duk kuwa da irin kyamar da ake nuna mana. Wannan dalilin ne yasa na daukar mata alkawarin cewar zan rika yin bara da kaina ina kawo mata kudi ita ba sai taje ba, da wannan ta dogara ni kuma na sauya hanyar bara zuwa neman na kai, duk kuwa da kasancewar wasu na min dariya ganin kamar aikin be dace da ni ba, wai ace mace kamar ni ina tsayawa a inda motoci ke tsayawa saboda traffic ina wanke gilashin mota ana biyana, aikin da akasan maza ne suke yi. Nikam hakan be taba damuna ba, domin na san yafiye min bara kuma ina samun sosai fiye da baran ma, ganin ni macece yasa wasu mazan ba hansin suke ba ni ko ashirin ba, har dubu daya na kanyi dacen wani ya bani. Ba dan kuma an san ni din wacece ba, domin kullum fuskata shafe take da fantin gawayi wanda hakan kan jama min kyama a gurin wasu, sai dai ni yafi min kwanciyar hankali na boye kyauna na, gudun abunda zai iya biyowa baya, za a iya kawo min hari kamar yadda aka sha min lokacin da muke wacan gidan da ba a tashe mu ba, duk wanda ya kalle ni a aihinin yadda Allah ya hallicce ni ba za a min kallo daya a dauke ido ba, ba kuma za a ki fadar cewar ina da kyau mai jan hankali ba, mata ma sukan fada balle mazan da babu adadi. Ko a unguwar da muke zaune a yanzu wato Clapperto babu wanda ya san iya ainahin yadda fuskata take, domin kullum ina tare da bakin gawayi a fuskata, wanda hakan kan sa a kara kiranmu da kazamai, ganin irin gurin da muke zaune mai kama da juji, wani kangon fili ne kato wanda aka ware wani bangare na filin aka fara ginin gida kuma aka bari, lokacin da aka tayar da mu daga wacan kangon gidan da muke rabe sai muka dawo wannan muka zauna ba tare da tambayar izinin mai shi ba, muka kafa yar bukkarmu muka zauna a nan muke rayuwarmu ta yau da kullum.

Na saba tafiyar kasa, dan haka komai nisan guri ni baya damuna, ina tafe ina rare wakar mu ta buzanci wance mahaifiyarmu take yawan rarewa a gida, idan na dora alkalamina a ko wane kalar littafi zan cika shine da kalmar kaunar iyalina kamin na bayyana komai na rayuwata, ina son yan uwana kuma ina son yarena da al'adata fiye da komai a duniyar nan.

A sannu nake tafiyata har na iso babbar flyover din Alu inda na saba wanke motoci ana biyana, kamar kullum mutane suna ta kai kawo a gurin kama daga masu babura da masu napep da kuma masu motoci manya da kanana. A cikin a kusa na soma sana'ata idan naga babu motoci sai na koma inda muke zama ni da abokanin sana'ata yara maza mu zauna sai idan an sake hada motoci sai muje da gudu mu wanke wasu kuma suna siyar da popcorn wasu kuma pure water, wasu air freshener da turare dai sauransu.

Sai da yamma lis na nufo gida gani a gajiye amman ba zan iya cire kudi na hau abun hawa ba, a ganina idan na hau kudin zasu ragu, kamar yadda mahaifiyata ta koya tun a lokacin da muke bara. A hanya na siye pure water da gyada ina tafiya ina ci can ta tsallaken titi nake hangon wasu buzayen irina a jikin wata motar suna mika masa hannu ya basu, ni dai ban da kallonsu babu abunda na ke, ban ankara ba naji an watso min ruwan saman da akai kwana biyu da suka wuce, wadanda suke kwance a gefen titin sakamakon wucewar da wata motar tai da gudu kamar zata tashi sama. Wani bakin haushi naji domin ba kadan ruwan da motar ta taka suka bata min tufafi ba da kuma kayan aikina, dan brush da man wanke mota da kuma kyalena na gogewa idan na wanke.

Bance komai ba naja tsaki na cigaba da tafiyata, yo daman wa zance wa wani abu tunda ni kadai nake ta tafiya ta. A natse nake tafiya ta har na karyo kwanar dana saba bi idan zanzo gida, ina yanke hanya ne domin abun ya zo min da sauki, sai dai duk da haka ana kiran magariba na soma dosowa unguwarmu ta Clapperto road, a dai dai bakin gate din gidan dan Uti idanuwana sukai arba da kalar motar da wuce ta gabana dazun ta bata min tufafi, kuma wani abun dadi babu mutane a titi sai karar motocin dake kai da kawo.

Sai da naje gaban motar na leka gaba babu kowa a ciki, sannan na kara matsawa ina kara tabbatarwa idan ita dince ko aa, kalar dai daya ce sabuntar ma daya ce sai dai wannan anyi mata hoton ZAKI a jikin number motar kuma an rubuta mata ZAKI 001 da manyan haruffa tsabanin wacan da ban kula da number motar ba ma balle ma na san me aka rubuta. Komawa nai ta inda na fito ina ta kalle kalle har na hango wani katon dutse da be fi karfina ba, na dauko na zo na jefawa motar ta gurin gilashinta, a take ta fara kuka, ni kuma na ranta cikin na kare, ai daman dai burina na dauki fansa, ko ba shine ya bata min tufafi ba be dame ni ba dan dan'uwansa ne mai kudi sai suji yadda ake ji... Abunka da marar jiki nan da nan na karya kwana kwana ina ta sauri kamar an biyoni, tsoro ya saka na kasa mikewa kai tsaye na bi titi na isa gida, sai na shiga ta hanyar gidan taba (Gidan azaba) na bulla ta can kwantagora road na karyo ta wata hanyar, domin kawai wahala sannan na bullo da gidajen yan sanda da yake nan na biyo ta bayan gidan Alkali Abu dange wato gidansu Khadeeja Candy na fito titi Clapperto road na doshi gidanmu.

A inda na saba aje kayana na nufa na aje sannan na fito ina kirga kudin dake jakata, kamar ance na waigo ko da na juyo sai na hango wata halitta mai kyau da daukar hankali da kuma ban tsoro tana kallona. Mutum nake hange amman a siffa da fuskarsa, sai dai kwarjininsa da aibarsa kamar wani zaki. Nesa yake da ni amman fuskarsa zooming take min tana kawo min shi kusa kamar yana tsaye a gabana. Annuri ne shimfide a fuskarsa, sai dai ba irin na masu dariya da sakin fuska ba, irin wanda annurin ya zame masa jiki yake bayyana kansa a duk lokacin da mai shi ya kalleka, kwarjinsa ya cika min ido har kure ganina nake ganin kamar daga ni sai ainahin Zakin ne a jeji, wani abu mai zafi naji yana bin kafafunawa, ashe fitsari nake a tsaye ban sani ba, tsabar tsoro ya cika min ciki sai na fadi zaune a gurin na rufe idona kunya ce ta kamani budurwa kamar ni ace tai fitsari sai kuma naji ashe ba kunya ba ce tsoro ne.....

__________________

Who's ready for the next chapter?

#ZAKI #Vote #Share #Comment.

Thanks Share Pls🙏🏻 *Z A K I*

By Khadeeja Candy

2️⃣

Mafarin ko wace Rayuwa numfashi da jini ne, ne numfashin da nake fitarwa ne ya tabbatar da cewar a raye na ke. Sai dai bana iya tantance yadda nawa numfashin yake a yanzu, domin surkinsa da wani kalar iska ne mai dadi shaka. A take na bude idona sai na hango gurin da mutumen yake tsaye kamar anyi ruwa an dauke domin babu alamarsa balle shi din yayi batan dabo bat kamar be taba wanduwa a gurin ba. Wata kila yaji tsoron fuska ta ne dake da bakin gawayi ko kuma rufen idon da nai ya tsorta shi, shiya saka yai hanzarin barin gurin. Samun kaina nai da murmushin kaina saboda tsoron dana ji, na Lumashe ido ina shakar kamshin turare mai shiga har cikin kwakwalwa ya samawarda natsuwa ga marar ita ga mai ita kuma ya dada masa. Na risina na dauke kudina da suka zube ina dariyar kaina, domin sai a yanzu abunda nai yake bani dariya na fashe gilashin motar mutane saboda mai motar ya watsa min ruwan kazanta a jiki, wata kila ma ba shi yai ba. Lokacin dana hango mahaifiyata tana a gaban murhu sai farinciki da jindadi ya lullube ni, domin ba kasafai zaka zo ka tarar an dora girki a gidanmu ba, mun fi siyen garin kwaki mu jika ko muyi kwado (Datu) da kuli mu ci, idan wadatar tai mana yawa muna siyen kanzon tuwon dawa ko na shimkafa mu aje muna ci, hakan yasa na iya sarrafashi ta ko wace siga, idan nai jalof dinsa sam ba zaka ci ka dauka cewar kanzo ka ci ba har sai idan na fada. Ban saba shiga gidanmu da sallama ba, dan haka yin sallamar be dame ni ba sai kawai na karasa gurin mahaifiyata ya kai hannu na bude tukunyar dake kan wuta ina fadin.

“Nana me kike dafawa”

Ba shiri ya yada murfin sakamakon wani azababen zafi da naji a take yan yatsuna sukai ja, sai dai ganin taliya yasa ni manta zafin dana ji duk kuwa da irin halina na raki sai wani farincikin ya kara baibayeni har na hade yawu. Ina son taliya sosai musamman dafuwar masu kudi ba irin tamu ba da sai an sauke muke saka yaji da magi wani lokacin ka gishiri kawai za mu saka mu ci.

“Taliya ce nake dafawa”

Ta bani amsa itama fuskarta dauke da far'a.

“Ina kuka samu kudi?”

“Bayan fitarki Maman Maryam ta aiko mana da ita”

Na yi dariya ina saka hannuna a kwagirina dake kuguna na ciro duk kudin da nai na mika mata, ban san na rage ba balle har na cire wani abu ko da kuwa ina da bukatar siyen wani abu ne, har sai idan Nana ta dauka da kanta ta bani. Gaba daya kudin da nai a yau ba su wuce dari uku da yan canji ba, daman ba ko wace rana ce jumma'a ba.

“Wai Ataa ina kake zuwa baran ne? Kullum kudin da kake samowa be wuce wanda za si abinci da safe ba, da rana haka muke wuni babu komi a ciki inda ba Allah ya kawo mana wani abun ba”

Na yi shiru domin ban san me zan fada mata ba, tana da gaskiya a lokacin da take baran tana tara kudi mai yawa har ma ta siye wani abun ta aje, tsabanin yanzu dana hanata kuma ni bana iya kawo abun kwarai domin ni ba baran na ke ba.

“Nana kin san ni ban iya baran sosai ba, kuma bana son zuwa gurin manyan motoci ba”

“Ka gani Ataa ka cire wannan girman kan, ka raba kanka da girma kai ka ba dan kowa ba, idan za ka dage ka yi bara ka dage domin shi ne komai na mu”

Fada take min amman dariya nake, saboda yadda take kirana namiji kamar yadda take yi ma ko wace mace idan kuma namijin ne sai ta mayarda shi mace, domin ita har yanzu hausarta bata gama fita ba. Sai itama tai dariya domin ta san abunda nake yi ma dariya. Daga haka na samu na shashantar da maganar na tashi na dauki fassashiyar butar mu na zagaya a inda muka killace na wanke fitsari sannan na fito na saka sabulu na wanke fuskata mai bakin gawayi nai alwala na shiga bukkarmu. Ban samu kanena Lukman a bukkar ba hakan ya tabbatar min da cewar yana islamiya kenan. Iyakar kokarin da nai na canja tufafin jikina ne na saka wasu sannan na soma rama azahar kamin na dora da la'asar. Ba tozarci ba, ni kadaina ina shakkar sallah da muke a bukkarmu domin na taba ji a lokacin da nake zuwa makaranta ana cewa Allah baya karba sai mai tsarki sai dai ban iya banbancewa ba tsarki na fitsari da janaba ko kuwa tsarki irin wannan na tsabtace daki. Babu wanda zai iya zama dakin mu yai minti biyar a ciki saboda zarnin fitsarin Lukma da kuma na kayan daudar da suke bukkarmu ga tarin kwanoni marasa marafe da kuma tarin gwangwayen da Nana take tarawa wai idan suka kai buhu uku zata siyar. Ina sallamewa kunnuwana suka sato min muryar Lukma dake fadin.

“Nana kin dawo gurin baran?”

Juyo nai da sauri ina kallonsu daga inda nake zaune, daga ita har kanena basu san ina yi ba.

“Nana bara kike zuwa?”

“Ataa idan be je bara ba, da me zan dafa taliyar nan?”

Daga can gaban murhun ta amsa min kai tsaye. Wani abu na ji ya tsaya a kirji wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da mahaifiyata taje bara.

“Amman Nana na fada miki zan rika yi ba”

“Ba inda kake zuwa kake zuwa (Nake) kai wani guri kake tafiya dabam”

Na turo baki baki ina bata fuska. Har tai girkin ta gama ni fushi nake ta yi dan taje bara sai dai hakan be hana ni cin taliyarba, sai dai ni sai da naje na siyo man kuli na zuba sama da yaji sannan abun ka da mai kwadayi baki baya son ba dadi. Washe gari ma kamar ko wace rana sai da haske rana ya leko bukkarmu sannan na farka daga bachi, a maimakon na tashi sai na kara dunkulewa cikin wani tsohon zanen gado wanda rabinsa ya gama yagewa (Barkewa). Bana jin yau zan tafi aikin dana saba zuwa da sunan bara, inda har zan je nai abunda zai kare mutumcin mahaifiyata ita kuma ta zaga baya idona taje bara banga amfanin zuwan nawa ba. Dan haka ban fito daga bukkarmu ba sai kusan tara da rabi duk da kasancewar babu agogo a bukkar balle na iya ganewa sai dai a yadda na auna tara tayi ko ma ta dan gota. A lokacin ne na dauki butarmu na zagaya can nesa da bukkarmu a wani fili da aka ware ban san me za ayi da shi ba, a nan na saba yin ba haya ta a duk lokacin da bukatar hakan ta kamani, domin a wacan gurin da muka zagaye da kwano da sunan bandaki idan mukai ba haya a ciki sai mun kwashe mun kai can nesa mu zubar a kullum ni kuwa zubarwa ne yake bata min rai, na zabi nai nesa da bukkarmu nayi bahayar a inda aka tana da domin yin wani abu.

Bayan na gama na dawo na saka kasa na wanke hannuna sannan na saka sabulu, sai kuma na dora da alwala sannan na shigo dakin nai sallah asuba. Da yaren buzanci mahaifiyata ta fada min cewar na dauki waina mai kuli na ci na tashi muje bara.

“Ni bana son zuwa bara Nana”

“Sai ka je, gaba daya zamu je”

Haka na turo baki na bata fuska sosai kamar zanyi kuka, amman hakan be saka ta kyaleni ba, har sai da na ci wainar ina ta fushi daya kasa boye kyawon fuskata, har sai ta na dauki bakin gawayi da mai na shafe fuskata da shi sai gani na fito wata mummuna kamar ba ni ba.

“Kin fi son ki shafa bakin gawayi kullum a fuskarki kamar wata dodo”

Mahaifiyata ta fada da yaren buzanci, daman can tafi kowa tsarguwa da shafa gawayin da nake domin yafi min kwanciyar hankali da lamana. Ko ba komai hakan hana sa ana min kallon kazama wanda ba karamin kariya yake min ba, na san da ace yan iskan mazan da suke unguwar za su ga ainahin yadda fuskata take wata kila da ace cikinsu wani ya keta min haddi....

Cikin rashin maida hankali na saka tufafin jiya masu kama da farin lela na yafa bakin gyale kamar yadda yawancin buzaye suke yi, mahaifiyata kuma ta yafa fari wanda ya gama dafewa ya canja kala saboda tsufa da kuma lalacewa. Lukman ya dauka yar robar ruwansa da kuma ta bara kamar yadda ya saba Nana kuma ta dauki ghana must go dinta ni kuma na daura jakata (kwajiri) a kuguna sannan na dauko wani tsohon gidan sauro ya rufe a saman bukkarmu a daidai inda kofar dakinmu kana na dauko wano (Langalanga) na rufa a gurin kofar kamar yadda muka saba idan za mu fita unguwa. Nana na gaba ita da Lukman suna firarsu abun shawa'a ni kuma ina baya ina kallonsu har muka isa gaban manyan shagunan da suke gawon nama inda manyan motocin masu kudi suke tsayawa siyen abu. Kamar yadda muka saba a can baya lokacin da muke baran ni nakan tafi gurin wata motar dabam Nana kuma ta tafi gurin wata dabam ita da Lukman idan mun fita tare da shi, idan kuma gida muka bar shi to ni da ita a tare zamu rika bin motoci ko kuma mutanen dake shiga cikin shagunan. Ba ma magana sai dai mu muka hannu mu marairaice fuska kamar za mu kuka ta yadda mai ba mu zai dauka ba mu da sama balle kasa ya taimaka mana. Haka muka wuni a gurin muna ta mikawa mutane hannunmu idan ya fito daga mota ko zai shiga wani shago har muka tara da dan yawa, duk abunda mahaifiyata ta siya sai ta aiko Lukman ya kawo min na ci. A haka muke har yamma tai daf da zamu tafi gida na hango wata motar a fake da sauri na nufi motar a zatona akwai mutane ciki sai da na isa sai naga babu kowa a ciki sai dai gilashin motar a sauke yake. Ina juyowa sai naji na bugu mutum, da sauri na dago kai sama ina kallon wanda na buga din, dogo ne mai faffadan kirji mai tsananin fari ga kwarjini da haifa, duniyar kamshinsa ta tunatar da ni cewar shine dai mutumen dana fasawa mota a yanzu ma ji nai na zama wata yar tsuntsuwa, yana ta kallona da fuskarsa mai dauke da walwala kuma ba walwalar ba, ba kuma ra a kira shi da rashin walwala ba, amana dai ba yabo ba fallasa a bayyana yake kana kallonsa kasan abu ne mai hawayin ya dabbata Sunnar murmushi a addininsa. Kwalla nake saboda ainahim zatin fuskarsa da nake kallo, ba hawayen kyawonsa ne ba, ba kuma na rashin far'ar fuskarsa ne ba, na tsoro ne irin wacan tsoron daya kamani jiya a lokacin dana hangoshi tsaye yana kallona, banbancin wacan karon da wannan a jiya fitsari nai yau kuma kwalla ne a idona na tsoro da fargabar abunda zai min. Lokaci daya naji an fisgoni wanda hakan ya bani damar sauke numfashin da ban san ina rike da shi ba sai a yanzu.

“Yana son ya shiga motarsa kin tare nasa hanya Ataa”

Nana ta fada tana rike da hannuna, ji nai na dawo duniyar mutane mai cike da hancin iska. Da hanzari mutumen yai saurin cire jacket din jikinsa ya bar t-shirt saboda na dan shafe shi kadan lokacin da mahaifiyata ta janyo ji domin na bar jikin motarsa, cike da kyankyami ya bude boot ya saka jacket din ya rufe ya dawo mazaunin gaba ya zauna yana goge hannunsa da tissue paper saboda ya rika rigar dana shafi gefenta kadan. Sai a yanzu na gane, wato duk tsayin da yake yana kallona na jiran na bashi guri ya shiga motarsa ne, amman ba zai iya yi min magana ba, wata kila maganar wahala take masa ko kuma yana kyamar furta kalmar kauce na shiga motata ga mace iri na ne.... Ni dai da kallo na bi motar sai a yanzu na lura da number motar ita ma ZAKI ne rubuce a jikinta, sai dai wannan motar ba irin wacan bace ko a kala balle a kama.

“Miya saki kuka?”

Na na ta tambaya da yaren buzanci tana nuna hawayen fuskarta. Sai na saka hannu na share na bata amsa da hausa ina turo baki kamar wata shagwa6a66iya.

“Tsoro na ji”

Dariya tai Lukma ma yai min dariya ni kuma na kara turo bakin kamar zan cireshi gaba daya... Sai da aka fara kiran sallah sannan muka dawo gida, a yau ma yar kullum ce sai da na wanke fuskata sannan na rama sallar da ake bina kana nai sauran, Mahaifiyata akam ba a magana domin sallah bata dame ta bayan sallah asuba bana jin tana wata Sallah sai idan ta kama. Lukman Nana ta aika ya siyo mana gari da sugar muka jika muka sha, ni kuma na roki Nana naira hansin a kudin dana samo ta bani na siyama kyanwata kifi na bata, tana ci ina shafata ina murmushi ina sonta sosai domin Allah ya saka min son kyanwa musamman wannan da muka sabu wani lokacin har fita nake da ita idan zan je wani gurin.

Chapter notes and social links

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JA5Ut6Au0j3DAjud3Ih37Q

Readers Also Read