Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 2
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 2: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 2. Washe gari ma haka na farka raina fes zuciyata kal kamar yadda na…
4,302 words
Washe gari ma haka na farka raina fes zuciyata kal kamar yadda na saba farka a ko wace safiya ta Allah duk kuwa da irin rashin da muke da shi. Sai dai yau ta sha banban, dan kekasa kasa nai na ki yarda na bi mahaifiyata da taga bana son zuwa sai ta kyaleni a bisa sharadin zan je inda na saba yi nai ba tare da ita ba. Bayan ta fita nima na shirya na shiga kangon gidan nan na dauki kayan aikina na kama hanyar Flyover din Alu. Ina isa na fara aikina na wanki mota a biyani, idan na hango manyan motoci na fi saurin zuwa na wanke musu domin sun fi baka kudi tsabanin na direbobi da wasu sai dai su wuce su barka ma ba tare da sun baka komai ba, wasu kuma su samma maka abunda ya samu. Wata fara mota mai bakin gilashi na zubawa mai na fesa mata ruwa ina gogewa kamin traffic ya sakesu, bayan na gama na dawo ta gaban gilashin motar ina jiran mai ita ya sauke gilashin ya bani wani abu, A hankali aka zuke gulashin motar sai fuskar mutumen nan na jiya da shekaranjiya ta bayyana, a maimaikon ya bani kudina sai ya miko naga an zuro min hannu.
“Ba ni wayar da kika sata?”
Hannun na mace ne haka zalika muryar ma ta mace ce, sa tsakanin ba ni wayar da kika sata da kallonsa fuskarka da nake sai na rasa wane yafi wani razanar da ni, duk kuwa da kasancewar ba ni yake kallo dan da alama ni din ma ban isashe shi kallo ba, traffic kawai yake jiran a sake ya ja motarsa...
____________________________
Yaushe Ataa ta saci waya kuma? Wanene wannan mutumen? Ya dandanon labarin yake a kwakwalwarku? Akwai suga kuwa? 😃
#Vote #Comment #Share #Zaki https://my.w.tt/GuQH5GZKb9
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
3️⃣
ALIYU POV.
Ana sakin traffic din yaja motarsa sukai gaba. Husna ta waiga tana hango Ataa wacce ta koma gafen titi tana hango motarsu tana jin kamar ta koma amman ba dama.
“Wannan ya zama na karshe i mean na last last time da sauke gilashin motata ki yi magana da wani saitin kunnena”
Ya fada ba tare da ya kalleta ba, tsif tai kamar babu ita a gurin, ta san halin Aliyu sarai dan haka bata sake yunkurin sake yin wata maganar ba har suka isa bakin gate din gidasu. Bata jiran ya ce ta fita ta shiga gida, tasan halinsa farin sani ba tana da wahala ya iya bude baki yai magana musamman a inda zai iya isarda sakonsa da ido. Bude motar tai ta fita shi kuma ya hau titi ya dauki hanyar gidansa. Horn daya yai aka bude mai gadin ya bude masa gate da sauri sanin cewar baya son jira, yayi minti biyar a cikin motar sannan ya fito yana rike da wayarsa ya nufi wata katuwar kofar mai ruwan zaiba. Door bell ya danna, Rahama ta bude masa kofa duk ta wani hade rai, kallonta yai from head to toe wani farin yadi ne a jikinta mai tsarin ja yadi ya fito da kyaunta da kuma dark skin dinta. Murmushi ya sakar mata kadan a maimakon ya fada mata cewar tayi kyau, sai ya ratsa gefenta ya shiga cikin falon kai tsaye sama ya haye ya shiga dakinsa dake cike da kamshin turare.
“Ni fa ba zan iya ba, na fada maka na gaji gaji”
Rahama ta fada bayan ta turo kofar dakinsa ta shigo, zuwa tai kusa da shi ta tana da yi masa mitar data saba.
“Aliyu na fada maka ni gaji, ga zafi sokoto ga wannan uban aikin fisabilillahi baka min adalci, baka tausayi na, tun farko sai da na fada maka ni ba zan iya zuwa na zauna ni kadai ba kace za a samu mafita gashi nan ka barni kullum sai sai wahala na ke ta yi”
Be dago ya kalleta ba, har ya gama cire agogon hannunsa ya bude maballan rigarsa sannan ya juyo ya rika kanta ya sumbanci goshinta ya saketa ya nufi bathroom. Ta saba inda fada ne zata yi ta gama be ce mata uffan ba wani lokacin ma har tambayar yake shikenan ko akwai wani? Magana tana masa wahala ainun kamar wanda aka idan yai maganar zata ragu .Haka rayuwarsa take tun yana karami indai ka girmeshi yai maka laifi sai dai kai ta nasa fada ka gaji ka bari ba zai ce uffan ba, idan kuma shi ne a sama da kai to baka isa ka daga kai ka kalleshi ba ma balle har kace zaka masa fada. Baya son yanayi, magana tana masa wahala ko da zo ki karba ne, baya jira sai dai a jira shi, yawan kallo yana bata masa rai ko da kuwa shi zai shafe sa a daya yana kallonka ne, baya son hayaniya and when ever he say no that's means no for sure. Duk wanda yake masa da shi a cikin familynsu tun daga dangin uwa har na uba babu wanda ya isa ya tsare Aliyu da kallo balle kuma har ya cilasta shi yin wani abu. Mommy ce kawai ta isa da shi sai Daddy bayan su babu mai kallon idonsa kai tsaye yai masa umarni da yi ko hani.
Wanka yai ya fito daure ya tawul fuskarsa kamar ko yaushe ma'ana babu far'a balle murmushi. Kamar be san da zaman Rahama a dakin ba haka yabi ta gabanta ya wuce zuwa gaban maduba yana shafe jikinsa da karamin tawul. Tsadadden man shafi mai kamshin gaske ya shafawa kansa sannan ya juyo ya nufi wani bangare na daki da aka ware aka zuba masa tufafinsa a ciki. Rahama ta biyoshi tana magana cikin bacin rai.
“Ni fa na fada maka na gaji”
Be ce uffan ba, kuma be bar mata wata alama da ke nuna cewar yaji abunda take fada ba, ba kuma dan be ji ba sai dan haka dabi'arsa. A gabanta ya kwance tawul din jikinsa ya shirya cikin wasu kananan kaya wadanda suka kara fitar da kyaunsa da kuma aibarsa fuskarsa sai annuri take kamar sabon ango. Wata yar karamar dorowa ya janyo ya dauko pen da memo aurensu yai rubutu a kai ya mika mata sannan ya fice daga gurin zuwa bedroom.
“Na yi Magana da Mommy tace za a samo aikin, amman tace ki daina wahala da yawa saboda ciwonki kuma Jawahir zata rika zuwa tana rika miki aikin gida”
Tana gama karantawa ta saki paper a nan, ta saba karanta abunda baya iya fada mata idan an maganar basa kusa, wani lokacin kuma sai ya zauna ha fada mata kamar ba shi ba. Yana gaban madubi yana fesa turare ya hangota ta fito sai ta jingina da kofar closet din tsa dayan hannunta ta rike kanta, da sauri ya aje turaren ya nufi inda take hankalinsa a tashe ya rikata ya dawo da ita jikinsa daga jikin kofar closet din.
“Kin cika yawan magana Dear, kuma kinsan matsalarki”
Ya fada yana kissing front head dinta.
“Na yi magana da Doc Asim yace za a samo very soon, idan an samu sai muje waje a dasa miki, i can't wait to see you alive healthy”
Ya rumgume tsantsan a kirjinsa yana shafa bayanta kamar ba shi ba.
ATAA POV.
Sai da na kalleshi da kyau sai na gano ba shi yake min maganar ba, wata ce mace ce mai kama da shi take maganar tare da ziro min hannunta mai kunshin lallen hausa wanda yai baki sosai a farin hannunta. Ba tsaya karbar kudin wankin motar ba domin gaba daya hankalina ya gama tashi sai na juya da sauri na koma can gefen titi na tsaya ina kallonsu, jira nake naga ko zai fito ya biyo ni amman sai naga be ko kalli inda nake ba, yarinyar ce kawai ki aiko min da sakon zagin da hannunta. Wutar traffic ta saki suka kama hanya shi da sauran mutanen da ke tsaye da motocinsu, sannan na soma tambayar kaina, wai wayar waya na sata? Yaushe nai satar? A ina nai satar? Na san muna da talauci da yunwa amman hakan be tana saka mu maida abun wani namu ba, yo ni ina ma naga wayar balle na dauka. Wata kila wata mai kama da ni ce tai satar to amman wayar waye aka sace a cikinsu? Ita ko shi? Idan tashi ce ai da shi zai yi magana ba ita ba, ita kuma ai ban tana ganinta ba balle har tace na mata sata ko dai shine yai min kazafi yace na masa satar? Koma dai mienene zan yi iya kokarin da zan yi na ga ban sake ganin wannan hadaddiyar fuskar tasa ba, wacce bata ko kallon mutane da kima balle har ta martabasu, yau kwana uku kenan kullum idan na hadu dashi sai wani abu marar kyau ya faru da ni, da farko fitsari nai kuma ya watsa min ruwan kazanta, na biyu kuma kuka nai har da wani jefar da rigar dana taba shi sai ka ce ni din ba mutum ba ce, wannan karon kuma an laka min satar wayar da ban san kalar ba. Har nai na gama na nufo hanyar gida babu abunda nake sai miti da surutun rashin alherin da yake tare da wacan mutumen iyakar alkawarin da na daukarwa kaina ba zan sake hadu da shi ba, da alama nan gaba cewa zai yi wani na kashe ko kuma ya takani da mota ya wuce. Yau kam ban dawo da wuri ba, domin a hanya magariba tai min, hango manyan motoci guda biyu a gidan da zan iya kiransa da hamu yasa ni hanzarin cira kafa na karasa ciki da sauri, Nana na samu risine a kasa tana rokon wani mutum kamar zata fasa kuka.
“Dan Allah ke yi hakuri Wallahi babu inda zai je, shiyasa ya laba nan shi da yaranshi”
Babban mutumen mai rigar arkin dake nuna isarsa da tarin dukiyarsa ta dakawa Nana tsawar da har sai da naji ciki raina.
“Babu ruwana da wannan, akan mi za ku zo ku bata min gida, ku san nawa na zuba na siye filin nan, an fara min gini sai kawai ku zo ki shige kuna lalata min guri”
A nan nima na zubar da kayana na shiga rokonsa kamar yadda Nana ta hade hannayenta tana rokonsa.
“Baba dan Allah kai hakuri Wallahi idan ka koreni daga nan ban san inda zamu je ba ba mu da kowa”
“Ba ku da kowa daga sama kuka fado? Daga ina kuka taso kuka dawo nan? Ku koma can ni bana son ganinku anan, ku bar min gida na fada muku idan na sake zuwa na tarar da ku a nan sai na wulakanta ku”
Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga, sauran mutane da suke tare da shi suka shiga dayar motar suka bi bayansa. Kallon mahaifiya dake kuka nai ina kwalla sai kuma na daga kai na kalli yar bukkarmu, miye laifin mu dan mun raba a wannan gidan tunda ba a ciki muka zauna ba, miye laifin bukkarmu mu dan kawai mun zauna a ciki.
“Yau ko mun shiga uku an koro mu can nan kuma an kore mu, yau ina za mu?”
Shine abunda mahaifiyata take fada ya yaren buzanci tana kuka. Zuciyata ta sosu sosai tana da gaskiya domin idan har kuma bar nan ban san wani guri da zamu iya rabawa ba, domin ba mu san wani gurin da zamu iya zuwa mu nemi taimakon gurin zama ba. Daga ni har Nana haka muka wuni cikin damuwa da rashin walwala har garin Allah ya waye, da safe Nana ta aika Lukman ya siyo mana waina ni da shi ita kuma ta gagara cin komai. Sai dai hakan be hanata fita bara ba, ni ce dai ban je ba, daman yau bana jin fitar saboda abunda ya faru jiya na laka min sata da kuma zancen barin gurin da muka raba, sai duk haka yasa ni jin kamar ma bani da lafiya, sai dai yau na samu yin sallah biyu a cikin lokaci tun a gida na wuni kuma bana aikin komai, wato azahar da la'asar ban da Asuba da da nai bayan rana ta gama bayyana.
Can da yamma Nana ta dawo har da biredinta a hannu, Lukman na bayanta da gorar ruwansa rataye a wuyansa. Biredin kawai muka ci muka sha ruwa sannan ya dauko kudin da ta zo da su da sauran kudin da suke rage mana idan mun siye abinci gaba daya kudin ba su wuce dubu uku da yan kai ba.
“Wadannan kudi ba zasu iya mu kama haya ba, ni ban san yadda za mu yi ba”
Magana take ina karantar tashin hankalin dake zuciyarta har yake bayyana kansa a fuskarta, ni dai na yi shiru ina ta tunanin sama mana mafita.
“Nana ko mu nemi gadi wani gida? Ta yadda zamu samu gurin zama”
“Wa zai ba mace gadi? Idan mu mun samu ni ina zan iya tare barawo?”
“Ai dan mu samu gurin zama ne”
“Hakan ba zai yi ba, sai dai na bincika wani gurin ko Allah zai sa mu samu”
Tun daga ranar kullum Nana cikin neman gurin da zamu koma mu raba take amman ba mu samu ba, yawancin inda muke samu duka filaye ne mu kuma muna tsoron zama a fili sai dai a kangon gidan da aka fara aka bari ko kuma ba a karasa ba ko ya kuma ginin daya soma zubewa. A kullum da fargabar zuwan Alhajin muke kwana mu tashi muna ta zuba ido ko zai zo amman shiru be sake zuwa ba har aka kwashe kwana kusan goma shabiyar, hakan yasa muka koma muna rayuwarmu ta yau da gobe cikin kwanciyar hankali. Musamman ni da ban sake saka wannan bakin mutumen a idona na ba. Yau ma da gari muka karya duk kuwa da kasancewar bana sonsa amman babu yadda na iya dole na ci ko babu dadi, bayan mun gama sha ne na tashi nai alwalar isha'i na kabbatar sallah. Ina cikin sallah na ji ihun Nana waccw ta kewa a bandaki kasa karasa sallar nai jin ihun yayi yawa na dauki fitilar hannu dake dakin na fito waje da sauri ni da Lukman muka nufi kewan ina Haskawa sai na hango katon maciji ya nade gurin daya yana ta zuro mana kansa, Nana kuma ta fadi gefe daya tana ta murje murje da alama cizonta yai ko kuma sara, Lukman ya saka kara ni kuma na saki fitilar a firgice na ruga izuwa titi cikin hudun hangon gidan ina neman masu taimaka mana, daman na san ba za a rasa irin wadannan abubuwan ba a guri kamar wannan, musamman da dare ba hudu yake zageyemu har sai idan mun kunna kara ko fita ko kuma hasken farin wata, wutar nepa kan sai dai mu hangota a manyan gidaje. Da ihu da karaji na isa titin gawon nama ina ta neman wadanda zasu taimaka mana, mazan da suke zama a gurin titi suka yo kaina da sauri ni kuma na shiga gaba ina gudu suna gudu har muka dawo cikin kangon gidan dake cike da hudu, masu wayoyi suka kunna wayarsu suka haske bandakin sai Nana aka gani babu macijin babu labarinsa, motsin kirki ma bata iya yi da sauri wani yace a bashi kyale sai ya daure inda yake zaton macijin ya tsareta wato kafar data rike.
“Ku nemo Napep? A kaita asibiti”
Daya daga cikinsu ya fada ni da Lukam babu abunda muke sai kuka ni ina rike da ita Lukman kuma yana tsaye bayana, a gurin wasu samarin ke kallo domin yau babu wannan bakin gentleman n a fuskata mai hana kowa ganin ainahin kyawo na. Ban san wanda ya kira Napep din ba nadai ga an shigo da ita har gurin Bukkarmu samarin suka rikata suka sakata ciki ni Lukman na shiga gaba ni kuma na zauna baya tare da ita ina hawaye kamar ba gobe. Ko wane motsi nata jinsa nake cikin kashina ji nake kamar ciwon a jikina yake, mahaifiyata ita ce duniyata, na gwada kokarina akan tsagaita kukana sai na gano ashe ni ba ba Jaruma ba ce a gafen dauri. Wata asibitin kudi mai zaman kanta Mai Napep din ya kaimu a lokacin da muka isa emergency sai suka karbe mu da gaggawa aka wuce da ita ciki Mai Napep ya juya yai tafiyarsa ni da Lukman sai muka yi tsaye waje. Har sai da Nurse din ta dawo kirana ta dauki sunan Nana ta bukaci naje wani guri na karbo kati sai na tuna da babu sisi a tare da ni, adole na bar Lukman a gurin na fita na hau achaba na je na dauko kudinta gaba daya na dawo naje na biya kudin katin sai kuma aka ce likita na son ganina. Da sauri na nufi inda Nurse din ta nuna na tura kofar office din na shiga hankalina a tashe fuskata duk hawaye ya bata ta, hannuna rike da yar jakar da Nana take zuwa da ita bara wacce kudin suke ciki.
“Nurse tace kana son ganina”
“Ke ce wa?”
Likitan ya tambayata yana min wani kallo daga sama zuwa kasa, duk wanda ya kalli sutura baya bukatar na fada masa cewar ba mu da shi, tufafin da nake saye da su kawai sun isa su isarda sakon talaucin da muke tare da shi.
“Mamata na kawo wacce maciji ya tsara”
“ina Babanku?”
“Babanmu ya rasu”
“To ina yan'uwanku da ke zan yi Magana”
“Ko minene likita ka Fada min mamata bata da kowa a nan sai ni, duka yan'uwan mu suna nijar”
Na Fada idona na sake cika da kwalla. Kallo yai sai ya sake kallona sannan yace.
“Okay wannan allurar za ki siyo naira dubu ashirin da daya za ki kashe”
Ya Fada yana mika min wata farar takarda. Ina karba na juya jiki ba kwari zan fice sai na ji ya ce.
“Kina da kudin ne? Idan ba ki kawo maganin nan da wasu hours ba Mamaki zata iya mutuwa”
Juyowa nai idona na zubar da kwalla ma girgiza masa kai dan bana ko iya magana.
“Babu?”
Na gyada masa kai.
“Bude baki kiyi magana wannan asibiti na ce zan iya taimaka miki idan baki da su”
“Wallahi ba ni da su ban san inda zan samo ba, bara mu muke kamin mu saye abincin”
Shiru yai kamar mai nazari, sannan ya kalleni ya ce.
“Shikenan zan mata allurar kuma zan ya mata tiyata na cire dafin macijin”
Da sauri na risina kasa ina masa godiya wani irin jindadi ya rufe jin za a ceci mahaifiyata sai dai ban taba jin inda akai wa wani tiyata aka cire dafin maciji ba sai dai allura.
“Taso muje ki saka hannu a file”
Da sauri na mike tsaye ina share hawayena, yana gaba ina binsa har muka shiga wani daki mai cike da nurse da yawa ya dauko wata takardar ya miko tare da nuna min inda zan saka hannu. Hannunsa ya dora saman nawa yana yimin sigh din yadda zan hi daidai, ina daho kaina nai arba da wata nurse tana girgiza min kai alamar kai, sai dai ban gane abunda take nufi ba na tausayi ne ko kuwa na kar nai yi ne oho ni dai fatana a ceto mahaifiyata.... https://my.w.tt/GuQH5GZKb9
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
4️⃣
Misalin goma aka shigo da ita tiyata amman basu fito ba sai karfe uku da wani abu na dare. Anyi mata tiyata cikin nasarar Allah da iyawarsa, saidai a halin da naga mahaifiyata sai na kara matso da maraicin mu kusa ni da Lukman. A wani dakin mai kyau aka ajeta kamar matar wani babban mutum ko kuma wata hajiya, a jikinta an manna mata wasu na'urori har a hancinta a wani abu mai kamar kwanfuwuta nake kallon tafiyar numfashinta, sai dai tana kwance a gurin kamar gawa jikinta babu tufafi sai wani zanen asibiti da aka saka a lulluba mata. Ina tare da ita har asuba ban runtsa ba, gani nake kamar zata iya farkowa ta bukuci wani abun ko da yake babu komai a tare da ni wanda zata iya ci ko ta sha, lukman ne kawai ke ta bachinsa hankalinsa kwance. Misalin takwas da rabi likitan ya shigo cikin shiga ta kananan kaya da rigar likitoci a samansu fuskarsa a sake yana ta min murmushi kamar mun saba.
“Ina kwana?”
Na gaisheshi cikin girmamawa. Sai ya amsa min kamar be gane ni ba, ba kuma kallon rashin ganewar bane, wata kila sai a yau ne yake tantance irin hallittar da Allah yai ta kyau mai daukar hankalin mace balle kuma namiji.
“Miye sunanki?”
“Aisha amman ana kirana Ataa”
“A nan kuka kwana?”
Ya tambaya yana kara tantance kyawun surar jikina.
“Eh”
“Ayyah ban sani ba ai da na kawo muku abun shimfida ko kina da shi”
Na girgiza kai alamar aa a cikin yanayin dake nuna dukan hankalina da damuwata tana gurin mahaifiyata ne.
“Da gaske baki da kowa a nan Nigeria? Ku yan nijar ba naga akwai wadanda suke da yan'uwa a nan ba?”
“Ni ba mu da su, ba a mu da kowa a nan”
Na fada masa cike da gundira da tambayoyinsa. Sai naga yayi murmushi kamar wanda jin hakan yai masa dadi, sai ya saka hannunsa aljihu ya nufi mahaifiyata yana dubata.
“Ki samo riga ki saka mata da zanen da zai iya rufe kafafunta, na bada a siyo mata maganin dubu dari da bakwai manyan magunguna ne masu tsada yadda mahaifiyarki za tai saurin jin sauki kuma an mata allurar bayan na mata sai nai mata operation na cire mata dafin macijin”
Wani irin dadi ne ya lullube ni sai na rasa ta inda zan fara masa godiya, hawayen farinciki suka cika ido har naji kamar na dauke shi na hade, a rayuwata ta duniya tunda Nana ta haife ni ban taba karo ko ganin mutum mai tausayi da jinkan masarasa irinmu ba kamar wannan likitan.
“Na gode Allah ya biyaka ya saka mata da alheri, Allah ya daukaka asibitinku Ya saka maka da aljanna ka taimaki rayuwata sosai ba zan taba manta ka ba”
Murmushi yai yasa hannunsa aljihu ya ciro kudin da za su kai dubu goma ya miko min.
“Ga wannan, ki je ki siya abinci ki yi duk abunda kike bukata, kuma idan mahaifiyarki ta farka ki kirani karki bata komai”
Wannan karon addu'ar gamawa da duniya nai masa, domin a tunani ita kan aljannah da duniyar duka ya sameta, domin mutum mai taimako mai share hawayen masara shi Allah yai masa alkawarin aljanna kamar yadda Annabi yace shi da mai taimakon maraya kafada da kafada za su shiga aljanna da shi. Babu abunda nake hangowa sai matarsa tabbas tayi dacen miji domin samun miji mai taimakawa al'umma har su yi masa addu'a ta yi babban dace. Bayan ya fice ne na kama hannun Lukman muka fita zuwa gida, sai dai abunda na tarar a gidan sai yafi tada hankalina fiye da ciwon mahaifiyata. Yar bukkarmu ce aka hankade can gefe aka cire kwannon da maihaifiyata ta saka domin zagaya yin fitsari ko ba haya, kayan abincinmu da tufafinmu an watsar da su can gefe gaba daya an watsar da komai. Tsaye nai ina kallon yadda kayan idona cike da kwalla, ba komai yasa ake mana haka ba sai rashin, rashi kuma na kudi saboda talaucin da yake tare da mu da kuma rashin kowa a kusa da mu. Lallai muhalli babban abu ne, da ace haya muke ko mallakinmu ne da wani be isa ya wulakanta haka ba saboda kawai mun raba a gidansa dan mu zauna.
“Ataa waya maka mana?”
Lukman ya tambaya yana bata fuska kamar zai yi kuka, ban da jansa jikina na rumgume babu abunda nai domin ina jin idan har na bude baki nai masa magana kuke kawai zai fito domin shine cike a zuciyata. Waiga nai banga kowa ba, da alama ba aikin yau ba ne idan kuma har yau akai shi tabbas tun da farar safiya aka zo aka mana haka aka tafi. Bani da wani zafi daya wuce na share hawayena na shiga hada tarkacen mu ni da Lukman babu inda zan kaisu gashi ni kuma ban iya hada bukkar ba balle na sake yin wata, Nana ce ta iya hadawa ita kuma tana asibiti, ance zuciyata tana ga mai kudi idan aka masa abu sau daya ba za akara ba, domin zai dauki mataki wanda bashi da shi kuwa sai ayi ta maimata masa kuma ya shanye yai hakuri saboda bashi da shi, ganin babu inda zan kai kayan yasa na hada komai na je can cikin wani daki da yake a kangon gidan da ba a karasa ba na saka su ni da Lukman sannan na fito waje na samo duwatsu na hada murhu na dauki jaran bukkarmu na saka na aiki Lukaman ya siyo mana ashana da taliya da cefanen dafa taliyar. Ni kuma na wanke tukunyar da mike girki da ita sannan na gyara tarugu da albasa na nufi gidansu kawata Farida dan na jajjaga, da nai sallama mahaifiyarta na ji taki ta amsa min a zatonta rokin wani abun na zo kasancewar wani lokacin idan ba mu da ashana ko gishiri tana aikawa tace ta sammata, har take yawan cewa wai mun cika roko, ni ko a ganina duk wanda zai mika maka hannu yace ka bashi tabbatas oa fishi kuma dan kana da shi ne ake zuwa nema a gareka amman mutane da yawa ba su fahimci hakan ba. Sai da na karasa har bakin kofarta ina sallamar sannan ta amsa min na gaisheta ta amsa ciki ciki.
“Dan Allah turminku za ara min zan jajjaga tarugu ne”
A tsaye ta bar ni a gurin na kusan minti biyar tana ta kallon arewa 24 a karamin tv ta sannan ta dago ta kalleni.
“Gashi can gidan kin gama ki dauraye”