Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 22
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 22: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 22. Shine Kawai abunda ya fada min ba tare daya kalleni ba ya cigaba da…
4,347 words
Shine Kawai abunda ya fada min ba tare daya kalleni ba ya cigaba da tukinsa ni kuma na cigaba da rare masa kukana har muka isa arkilla, wata hanyar ya biyo inda manya gidaje na alfarma, bakin wani katon gate ya tsaya wanda saman gate din duk iccen fulawa ne da yai rassa ya sauko har gurin gate din. Da karfi zai saka a cire min kodar ya sakawa matarsa ni ya kyale ni shine kawai abunda zuciyarta take raya min. Da muka shiga harabar gidan sai na ga manyan motoci uku a fake kusa da ta farkon ya faka tashi motar ya bude ya fita ba tare da ya ce min komai ba. Nima na bude na fito na tsaya gurin motar ina hawaye gaba daya tsoro ya gama kamani dan a nawa tunanin wata kila ma tsafi yake. Da kai yai min alama da na wuce ciki ni kuma na lake kafadata ta alamar ba zanje din ba, gaba yai abunsa ya bar a gurin ina karewa gidan kallo ina hawaye, gidan be min kama da na yan yankan kai ba amman ba ni da tabbacin ba cutar da ni zai yi ba, gashi kuma ya saka an tafi da Nana waya sani ko sani abun za a mata. Karar bude kofar falon naji kamar yadda na ji lokacin da zai shiga, sai na hango wata farar mace ta fito daga falon ta doso inda nake tsoro ne ya kamani a zatona wani abun zata min sai ta kusan karasowa kusa da ni sai na ga ashe matar da na taba gani gidan Mama Fulani ce wacce ta ba ni cake, fuskarta da tausayi ta karaso inda nake ta kai hannunta ya rika fuskata sai na ga idonta da hawaye.
“Alhamdulillah Allah mun gode maka, sannu kinji”
Na gyada kai ina hawaye sai tasa hijabina ta goge min fuskar.
“Daina kuka kinji zo muje ciki”
“Ina nan ya kawo ni?”
“Ya kawo ki inda za ki samu gata ki samu jindadi a nuna miki kauna”
“Mamana tana asibiti ya saka an tafi da ita ban san abunda zai mata ba, bana kwanciyar hankali har sai naji halin da take ciki”
“Ba cutar da ita zai yi ba, shi ma ya dade yana nemanki da inda kike ni da shi, ban san cewa ke ce ba sai bayan da Fulani ta koreki, ki aminta da mu Wallahi ba za mu cutar da ke ba”
“Mahaifiyata fa?”
“Ita ba zai mata komai ba”
Matar ta fada tana hawaye sai ta rumgume ganin ina kuka. Shi kuma ya fito daga falon ya nufo inda muka na yi zaton ko wani abun zai fada min sai na ga ya bude motarsa ya shiga.
“Dan wajen Fulani komai ake ciki ka kira ni saboda hankalinta ya kwanta”
“Okay Momy”
Ya fada yana kallona daga cikin farin gilashi motar. Sannan taja hannuna ta nufi hanyar falon da ni, da muka shiga ciki sai sai yan matan nan da na gani idan Mama Fulani su Biyu Siyama da Husna da kuma wata wacce ban sani ba suka ce min
“Sannu”
Kai kawai na gyada musu na zauna a kujerar da matar ta zaunar da ni. Sannan ta zauna kusa da ni ta rike hannayena.
“Dan Allah ki daina kuka Wallahi raunana min zuciya kike idan kina kukan nan sai ki saka nima nai”
Sai kuma ta kalli Siyama tana share hawayenta ta ce.
“Shiga ciki ki hada mata ruwan wanka”
“Aa ba zan yi wanka ba, na fi son naje asibitin kusa da ita hankalina zai fi kwanciya”
“Za a kula da ita za a mata duk abunda take bukata idan ma kinje ba wani abun za ki mata ba, kuma ba cutar da ita zai yi ba taimakonta zai yi”
Kai na girgiza.
“Aa ni ban yarda ba, wacan karon ma cewa aka yi taimakona za ayi ashe koda za a cire mata a bar mu da lalura, kuma mutanen da sukai wacan aikin sune a yanzu, a gabana ya kira wani likita ya aiko da mota aka tafi da ita ni kuma ya kawo ni nan, hankalina be kwanta ba, zai iya cirewa ya sake kasawa matarsa, dan girman Allah ku tauyasa min ba ni da kowa a duniyar nan sai Nana ban san kowa ba a cikin danginmu Wallahi idan ta mutu ban san inda zan je ba”
Ina rufe baki matar ya saka a kirjinta ta rumgume ta fashe da kuka sautin kukanta har ya fi nawa dagawa. Husna da bakuwar da ban san sunanta ba suma suka saka kukan dakin yai tsin ba ka jin komai sai sautin kukan mutane hudu, ni Matar, Husna da bakuwar ban da Siyama da ita hawaye kawai take. Mun dauki lokaci muna kuka duka aka rasa wanda zai bawa wani hakuri balle kuma har ya rarrashi, Siyama ce ya shiga daya daga cikin dakunan ta hada ruwan wankam sannan ta fito tana fadin.
“Momy ga su can na hada dakina”
“To”
Wacce aka kira da Momy ta amsa cikin muryar kuka, ni dai ina rumgume a kirjinta ina fitarda numfashi a hankali, na jidadin rumgumar da tai min rabon dana kwanta jikin Nana a haka har na manta amman yau wata uwar ta rumgume ni na yi kuka a jikin rigarta ba tare da ta nuna min kyama ba. Ko da yake ba a fuska da hali ake gane mugun mutum da na kwarai ba, domin da a fuska ne da Doc Asim be mana haka ba, daga nai daga jikinta ina jan majina sai ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
“Ta so mu shiga ciki ki yi wanka”
“Momy bari na kaita mana”
Bakuwar ta fada tana mikewa tsaye gaban tv dana tarar da su suna game ta nufo inda nake, wata kila ita ma yar gidan ce domin ta yi kama da Momyn sosai. Hannuna ta rika na tashi tsaye taja har cikin dakin dan madaidaici mai gado daya da yar karamar kujera da teburin karatu an kawata shi iya gwargwado.
“Nan za ki cire kayanki ko sai kin shiga ciki”
“Ciki zan cire”
Ta min murmushi.
“Ya sunanki hala?”
“Aisha”
“Ni kuma sunana Amina, jin ga a girme na girmeki dan haka ke kanwata ce”
Bance mata komai ba sai ta nuna min bandakin.
“Shiga ciki sai ki yi wankan bari na kawo miki wasu tufafin da za ki saka”
“To”
Na nufi bandakin cikin tsoro domin ni har yanzu zuciyata bata natsu da su ba, a dayan bangaren kuma na kasa aminta cewar Aliyu ba cutar da Nana zai yi ba. Ban wani dade gurin wankan ba na gama na dauki zanena na daura na fito tsoron gashina har gadon bayana. Ko da na fito Amina tana zaune rike da kayan tana jirana.
“Wow”
Ta fada tana kallona sai kuma ta aje kayan hannuna ta nufo bayana tana taba gashina.
“Ke da gaske gashinki ne? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kamar aljana ko dai kari kikai”
“Gashi na ne”
Na fada cikin rashin sakewa.
“Ki shafa mai ki saka rigar”
Ta fada tana fita daga dakin. Abaya ce yellow da under wears sai dan karami dankwali baki. Sai da na fara saka kayan ciki sannan na saka abayar na daura dankwalin a fito da tsorona sai na zauna kasa, gudun kar na zauna a saman gadon ya zama laifi komai ban shafa ba duk kuwa da tulin kayan kwaliyar da suke dakin tsoro nake ban sani ba ko suma kamar Maryam da Rukaiya suke. Kofar dakin aka turo sai ga Momy ta shigo dauke da plate da kofi.
“Aa ya kika zauna kasa? Tashi ki zauna saman gadon mana”
“Nan din ma ya ishe ni”
“Aa tashi ki zauna ya za ki zauna kasa”
Saman gadon ta aje plate din da ke rufe sai ta mika min kofin hannunta ashe tea ne a ciki.
“Ki ci abinci kinji ki kwantar da hankalinki ki yarda da mu ba zamu taba cutar da ke ba, kuma mahaifiyarki zata samu lafiya ta warke In-Sha-Allah”
“Bana jin yunwa bana iya cin komai a yanzu”
Na fada ina aje kofin tea a kasa sai ta dafa ni ta zaunar da ni kusa da ita saman gadon.
“Na sani an miki zalinci kuma an miki rashin kyautawa, tabbas Dan wajen Fulani ya yi kuskura ban sani ba ko za ki yarda cewar ba da saninsa aka aikata miki hakan ba?”
“Idan ba da saninsa ba ya za ayi a sakawa matarsa? Kawai sun yi amfani da rashin ilmina ne suka saka na saka hannu a takardun da sunan taimakona za ayi ashe kodarta za a cire, saboda ya tambayi ne na ce masa ba ni da kowa sai yai amfani da wannan damar ya cire mata koda kuma ya saka a kulleni har kwana hudu gidan yan sanda, wai na bata masa suna”
Na karasa ina hawaye.
“Wallahi ba da wanin sanin sa akai miki haka ba, kudi aka bashi aka ce ya siyo ba mu san cewa zalinci zai yi ya cire kodar mahaifiyarki, kuma tun daga lokacin da abun ya faru muke ta neman ki da inda za mu ganki mu taimaka miki amman ba mu samu ganinki ba, ban san cewa ke ce kike aiki a gidan Fulani ba sai daga baya, shi kuma ya fada min cewar kin ki bashi hadin kai ne shiyasa be taimaka miki ba”
“Ina tsoron taimakon kowa ballanata na shi, Wallahi Aliyuna nan bashi da imani da tausayi kansa kawai ya sani”
Wasu yawu ta hade da karfi tai min murmushi.
“Ba ki fahimce shi bane, amman za ki sanshi nan gaba kadan”
Ban sake cewa komai ba bayan hawayena da na share ina murza yatsun hannuna na rasa yadda zan yi zuciyata ta aminta cewar ba cutar da nana Aliyu zai sake yi ba.
ALIYU POV.
Daga Arkilla ya koma uduth din, duk wani abu da ake ma patient kamin a shiga da shi ganin likita shi yai kama daga karba kati da kaiwa a bude file. Sannan ya kira Doc Bukar ya fada masa cewar ya kawo ta har an shiga da ita ciki, ba bata lokaci Doc Bukar ya iso asibitin sai da Aliyu yai masa bayanin cewar matsalar koda ce sannan ya shiga dakin da aka kaita ya soma bata taimakon gaggauwa shi da wani likitan. Bayan sun fito Doc Bukar ya saka wasu nurses din suka kaita akai mata hoto a aka debi jininta sannan ya canja mata daki aka kaita wani dakin na musamman.
“Aliyu ya akai aka bar matar nan haka? Ciwon nan yana kokarin cinye ta?”
Lokacin da suka jero suka fito daga emergency ne Bukar ke masa wannan tambayar.
“I can't tell yanzu fada min ba zata samu sauki ba?”
“Zata samu mana, amman dole sai mun jira Doc Muhseen ya zo shi kadai zai mata aikin nan tun da Doc Mustapha yana waje, daman sune likitocin da suka fi kwarewa wannan fannin”
“Ka kira shi?”
“No na yi request a kira shi dai, ai ba mu muke kira ba, kuma ko bayan nata ai zai zo ya duba wasu patients daman amman sai next week”
“Kana tunanin zata kai gobe?”
“Yes zata iya kaiwa next year ma a haka, daman yanzu jini da ruwa ne abunda ta fi bukata, to mun saka mata ruwa jinin kuma na saka a bincika idan kawai wanda yai daidai da nata ko kuma zai iya zama a jikinta”
“Ka gwada nawa mana idan zai yi”
Doc Bukar ya kalleshi.
“Seriously?”
“Yes ina son rayuwar matar nan Bukar, ko me za ayi dai i need her alive”
“Then ka kira dan uwanka ka fada masa idan zai iya ya zo ya duba ta yau ma, idan yai mata aiki ina da tabbacin nan da two weeks zata koma normal”
Wani guntun numfashi Aliyu yaja ya sauke sannan ya kalli Doc Bukar din ya ce.
“Muje a gwada jinin”
Tare suka juya suka zuwa lap a can aka gwada jininsa da na Nana aka ga zai shiga sai ya kwanta aka cire gora uku a jikinsa aka sannan ya taso ya fito Doc Bukar ma bashi gangon madara.
“Ya jikin Rahma tana ta samun sauki dai ko?”
“Ka ji bata da lafiya ne?”
“Yes ba mahaifinta ya saka cigiya gurin likitoci cewar yana bukatar kodar siyarwa ba, sai dai samun koda yanzu ba abu ne mai sauki ba ba kowa ke iya siyarda wani bangare na jikinsa ba, kamar wannan maybe ita ta siyar muku da na farkon gashi yanzu sai an sake mata aiki”
Sai da Aliyu ya shaye madarar sannan ya jefar da gongon ya kalli Doc Bukar kamar zai yi magana sai kuma yai shiru dan yasan daya fadi gaskiya kara ma kawai yai shiru dan babu wanda zai yarda cewar ba da amincewar Doc Asim ya cire kodar ba.
“What is better now is ka kira Muhseen ka fada masa cewar kana da patient ya zo ya duba maka ita, na san zai yi ai”
“Zan kira”
Ya bashi amsa sannan ya rako shi har gurin motarsa ya shiga ya sannan Doc Bukar ya juya ya koma cikin asibiti Aliyu kuma ya amsa wayar da Rahma take masa.
“Aliyu ka shigo garin nan?”
“Eh”
“Amman ban sani ba”
“Shigowar dare nai, ya jikinki?”
“Aliyu yarinyar nan ka biyo ko?”
Yayi shiru be ce mata komai ba.
“Aliyu wai ba zaka fita harkar yarinyar nan ba? Shikenan daga yarinya ta zo tayi karya kai kuma ka zauna akai ka yarda cewar hakan din ne?”
“Babu ruwanki a cikin lamarin nan, ban nemi shawararki ba akaran kaina nake komai, and bana son yadda kike min magana kamar kina saka ni nai dole”
Ajiyar zuciya ta sauke daga can cikin wayar sannan ta dora da dalilin daya saka ta kirashi.
“Adamu mai gadi ya fada min wata ta zo zata siyar da kodarta kuma ka yi magana da ita ina take?”
“Ataa ce yarinyar da kike fada akanta, ta zo ta siyarda kodar dan kawai ta nema mahaifiyarta magani irin wannan yarinyar ce kike cewa kar a taimakawa? Haba Rahma”
Kashe wayar tai bata sake cewa komai ba, shi kuma ya sauke yana mai jin haushin abunda tai masa dan shi ba a kashe nasa waya sai dai shi ya kashe maka indai ba Momy ba ko Mama Fulani ko Abbah Daddy, sai ko Nasir shi ma kuma ba kullum ba. Sai ya tuka motar ya dauki hanyar gidansu Rahma dan zuwa ganinta and yana son yin wasu maganganun da ita, a dayan bangaren kuma yana jin kamar ya kira Muhseen yai masa magana, duk da yasan ba abune mai sauki a gareshi ba kiran Muhseen har yai requesting wani abu a gurinsa, he can't remember when last yai waya da shi, wani bangaren na zuciyarsa yana fada masa ya hakura kawai har sai next week idan Muhseen din ya zo, sai kuma yaji kamar ba zai iya kyale Nana a cikin wannan halin ba bayan sune silar shigarta halin kuma yana da yadda zai yi. Cikin wayarsa ya shiga ya nemo number Muhseen yana ta kallonta kamar ba zai kira ba, sai kuma sata zuciyar tace masa ya aika masa kawai da sako, wata kila kuma kiran ya fi dan zai fi daukar abun da muhimmanci, ba shi da wani zabi daya wuce kiran idan ma ya koma gida be san ta yadda Ataa zata dauki abun ba idan ya fada mata likitan da zai mata aiki sai next week zai zo wata kila ba zata yarda da shi ba. Ringing tai har ta katse Muhseen be dauka ba, bs karamin jihadi yai na sake kiransa tare da alkwarin idan har be daga ba ba zai sake kiransa ba, tana yin ringing daya Muhseen ya daga.
“Ya akai?”
Aliyu yai shiru na wani lokaci ba tare da yace komai ba tana jin zafin tambayar da Muhseen yai masa. Har Muhseen zai kashe wayar sai Aliyu ya ce.
“Akwai wata patient mai matsalar koda, ina son ka duba ta gobe”
“Yaushe ka zama ogana ne da har zaka ba ni umarni?”
Aliyu yai shiru be ce komai ba sai dantsar hakora yake gumi na karyo masa a take. Can Muhseen ya ce
“Idan ma wani abun ne ai ba kai zaka fada ba, daga can asibitin za a turo min mail, sai idan alfarma kake nema then say it”
A fusace Aliyu ya katse kiran ya gwammace yai hakan da ya furta neman alfarma a gurin kowa balle kuma Muhseen da furta hakan zai ba shi damar ganin ramarsa. Bacin ransa ne ya saka yaji ba zai iya zuwa gurin Rahma a haka ba, can din ma yasan ba bacin rai zai kwaso domin ba fahimtarsa zata yi ba. Canja hanya yai ya dauki hanyar da zata sadashi da Arkilla phone dinsa a dayan hannunsa yana driving da dayan, sako ya shigo wayarsa ta saman screen din ya karanta abunda Muhseen ya turo masa.
_Ka fara bawa Ataa wayar zan yi magana da ita then zan zo gobe_
Wani murmushin haushi Aliyu ya buga wayar a front seat yana wani irin huce how on earth Muhseen zai saka masa doka wai sai ya bawa Ataa ya yi waya da ita sannan zai zo, har ya isa gida be daina jin zuciyarsa na tafasa ba. A harabar gidan ya samu Momy zaune tana gyara giďa daman ta kan zauna wani lokacin har ita da Daddy ko da yara, tana ganin yadda Aliyu ya fito mota tasan akwai bacin rai a tare da shi, kai tsaye inda take zaune ya nufo ya zauna kusa da ita.
“Wai ni Muhseen zai sakawa doka?”
“Miya faru?”
A nan ya labarta mata abunda ya faru sai Momy tai murmushi.
“To yanzu kiran waya ka bata su yi magana shine wani abu?”
Yayi shiru be ce komai ba. Momy ta dauki wayarta ta kira Siyama tace ta fito tare da Ataa su same ta harabar gidan, a tare suka fito Siyama da Ataa sai dai Ataa ta fi sauri gurin karasowa gurin domin a tunaninta wani abun ne.
“Miya faru? Ina Nana”
“Waya za ki yi da Muhseen yanzu, shi zai zo ya duba Maman ki gobe”
Momy ta fada tana kiran Muhseen din waya. Sai da suka gaisa sannan ta ce masa.
“Ga Ataa din”
“Momy ba a wayarki na ke son magana da ita ba, a wayar Aliyu”
“Naga kamar duka daya ne ai”
“Na sani Momy amman wayarsa na ke so please”
Katse kiran Momy tai ta kalli Aliyu.
“Da wayarka yake son magana da ita, ka kira shi yanzu nan ka bata”
Har ya bude baki zai yi magana sai Momy ta tari numfashinsa.
“Umarni ne ka kira shi ka bata wayar ta ce”
Ta fada da kamar fada tana kallonsa fuskarta babu alamun wasa.
“Wayar tana mota”
“Je ka dauko”
Tashi yai ya nufi motar ya bude ya dauko wayar ya dawo ya zauna sannan ya kira Muhseen ya mikawa Ataa wayar. Bata karba ba ta tsaya kallonsa sai ya daka mata tsawa.
“Ki karba mana...!”
A razane ta mika hannu biyu ta karba idonta na kokarin cika da hawaye ta kara wayar a kunne.
“Karka sake daka mata tsawa balle kuma ka ce zaka nuna nata dan yatsa, bata jidadi a wani gurin ba ba zaka zo nan ka hana ta ba, abunda kake yi ma kannenka da kowa ita ba zan daukar maka ba”
Momy ta fada tana nuna shi da yatsa cike da jin haushin yadda ya razana ta sannan ta mike tsaye ta dauki gyaďarta ta bar masa gurin, dafe kansa yai a gurin har yanzu gumin bacin rai ne yake sauko masa.
Gaisawa Ataa ta fara yi da Muhseen cikin sautin kuka sai ya ce.
“Mi aka miki kike kuka?”
“Ba a min komai ba”
“Zan zo na duba Mamanki gobe kina so?”
“Eh”
“To zan zo, ki kula da kan ki kinji? Idan na zo za mu yi magana da ke”
“To”
Daga haka ya kashe wayar, sai ta mikawa Aliyu wayarsa.
“Gashi”
Dagowa yai ya kalleta kamin ya kai hannu ya karbi wayar ya buga ta da kasa iya karfinsa a take wayar ta watse Ataa kuma tai ihu tai baya a zatonta wani abun zai mata.
*ZAKI
By Khadeeja Candy
30...
Daga gidansu Rahma gidansa ya dawo, sai ya tsaya a cikin mota ya kwantar da kujerar baya ya kwanta hannayensa rumgume a kirji. Gaba daya wunin yau be masa dadi ba, tun da yake a rayuwarsa be taba samun kansa ciki matsala irin wannan ba. Rahma a gafe ga Ataa and now Muhseen, sai a yanzu yake nadamar sanar da Momy abunda ya faru tsakaninsa da Muhseen da bata cilasta masa ya kira shi ba, da ransa be bace kamar haka ba. Ya dade a zaune cikin motar sannan ya bude ya fito ya shiga cikin gidan kai tsaye dakinsa ya wuce, ya kwanta be tashi ba sai kusan sallah magariba, tufafin jikinsa ya cire ya shiga bathroom yai wanka tare da alwala ya fito ya sake shiryawa cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da expensive perfume sannan ya fito ya sake shiga motar ya dauki hanyar gobirawa, a masallacin unguwar ya tsaya yai sallah kusa da wani mai siyardar nama, bayan ya gama ya shiga wani babban shago ya zabi waya mai tsada ya biya da ATM dinsa sannan ya fito ya shiga motarsa a cikin motar ya fiddo wayar ya kunna sannan ya soma driving da hannu daya. Har ya isa family house dinsu Arkilla, kusa da inda ya fasa wayar ya faka motarsa ya sauke gilashin motar yana kallon yadda wayar ta watse, da duhun magariba amman ko'ina haske ne kamar rana, ya dade yana kallon gurin sim dinsa da memory yake son cirewa ya saka a wannan wayar amman baya son taba wayar gaba daya ta fice a ransa. Fita yai daga motar ya nufi kofar falo ya shiga, Siyama kawai ya samu a ciki tana kallon rawar babban yaro a plasma tana koyon yadda suke, sai dai ganin Aliyu ya saka ta saurin zaunawa tare da canja channel din da take kallo zuwa wata dabam.
“Sannu da zuwa Ya Aliyu”
Sai da ya karewa falon kallo sannan ya ce.
“Ina Ataa da Husna?”
“Ataa tana asibiti Husna kuma sun fita ita da Anty Amina Momy ta aike su”
“Waya kai Ataa asibiti?”
“Kuka tai yi shine Momy ta saka Anty Amina ta kaita”
“Je waje ki dauko min sims dina da Memory”
Shine abunda ya fada sannan ya nufi dakin mahaifiyarsa, zaune ya samu Momy gaban madubi tana cire gulagulan hannunta, a gafen gadonta ya zauna yana cirewa wayar murfi, bata ce masa komai ba har Siyama ta shigo ta kawo masa sims din da memory ya karba ya saka a wayar sannan ya kunna.
“Ga abincin dare can zaka je ka kaiwa Ataa asibiti”
Momy ta fada bayan Siyama ta fice daga dakin.
“Momy ba za a bawa Siyama ko Amina ta kai ba?”
“Kai na ga dama, ka ce kana son taimakawa yarinya amman kana kokarin bata kanka a gurinta, wata rayuwa kake daukarwa kanka wace zata kara saka yarinyar ta tsane ka kuma ta yarda cewar da hadin bakinka aka cutar da ita, fasa waya a gabanta daka mata tsawa, ko zare mata ido ba ba zai kara maka komai a gurinta ba sai tsana”
“Ba saboda ita na fasa waya ba”
Ya bata amsa yayinda yake kunna wayar.
“Saboda Muhseen ko? Kana jin cewar ka ragu saboda ka kira Muhseen ka bata sun yi waya right? Shi bata waya suyi magana wani laifi ko abun jin zafi”
“Momy Muhseen kanena ne, be kamata yai min haka ba”
“Shikenan dan yana kanenka ba zai iya cewa ka kaiwa wani yai waya da shi ba? Wannan wane irin jin kai ne da kai haka?”
Yayi shiru be ce komai domin yana tunanin duk abunda zai fadawa Momy ba fahimta za tai ba, Mama Fulani ce kawai take fahimtarsa har ta goya masa baya, kuma bata taba masa magana akan wannan ba.
“Zaka je ko na tashi naje da kaina”
Dagowa yai daga kallon wayar da yake ya kalli Momy wacce ta daure fuska.
“Zanje Momy amman kamar kina fushi da ni, kuma kin san ina damuwa idan ke da Mama kuka fushi da ni”
“Bana jindadin yadda zamantakewar ku da Muhseen yake sam, ita ma kanta na san ba dadi take ji ba, tana kyale ku ne kawai saboda babu yadda za tai”
“Momy matsalar ba daga ni ba ne daga Muhseen ne ya cika son shiga rayuwata ne kawai”
“Ka gani ba, wannan halin na ka shi yake bashi haushi yake ba kowa ma haushi, kai baka taba yarda cewar ka yi laifi ba, baka tana yarda ace kaine mai laifi sai jin kai da son wulakanta kowa, babu abunda ka rage a halin Fulani kuma Wallahi wannan dabi'un ba su da ce da kai ba”
“Momy kawai kina son ganin laifina ne ki bawa Muhseen gaskiya bayan shi ne yake abunda be da ce”
“Na sani wani lokacin yana yin abunda be dace ba, amman ka fi zurfafa sama da shi, and dole na bawa Muhseen gaskiya na kare shi kamar yadda nahaifiyarsa take maka, ba zan taba yarda ka ce zaka ciwa danta mutunci ba ko ka wulakanta shi ba, ku rika abu kamar ba yan'uwan juna ba, kana ikirarin kai babba ne amman baka iya kawar da kai daga ganin wani abun ka ka kyale?”
Kansa ya mayar gurin wyar yana ta taba ba dan kuma yana bukatar tabawarba sai dan be san abunda zai cewa Momy ba, har tai fadanta ta gama ta fice daga dakin be ce gama be sake cewa komai ba. Bayan ajiyar zuciya daya sauke ya fito daga dakin ya nufi dinning inda Momy take hada kulolin abinci da kwadon da saka plate a ciki da spoon ta mika masa.
“Idan ka je kuma ka daka mata tsawa idan bata karba ba”
Murmushi yai ya karba ya nufi kofa Siyama kuma ta dauki ragowar kulolin ta saka masa a mota har ta juya zata koma ya kirata.
“Shigo muje idan munje can za ki rika kayan”
“To”