Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 23

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 23

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 23: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 23. Ta fada tana bude front seat ta zauna shi kuma yai ma motar key…

4,433 words

Ta fada tana bude front seat ta zauna shi kuma yai ma motar key suka kama hanyar asibitin. A inda ake faka motoci ya faka motarsa sannan bude motar ya fito ya bude gidan baya ya dauki kwandon plate din da karamar kula Siyama kuma ta riko mayan kulolin guda biyu ta dora daya saman daya. Security din na ganin zubinsu ya san ba irin zubin mutanen da zai tarewa kofa ba ne, da kansa ma ya bude musu ward din Anas room suka shiga. Aliyu ne a gaba domin shi ya san inda dakin yake Siyama na biye da shi a baya har suka isa cikin dakin. Tura kofar kawai yai ya shiga ba tare da sallama ba, sai dai yana kokarin sakin fuskarsa duk da ba murmushi yake son yi ba. Zaune ya samu Ataa saman gadon da mahaifiyarta take kwance tana bachi, Doc Bukar kuma na zaune saman kujerar da ke fuskartar Ataa yana nuna mata abu a laptop dinsa, babu Hijab a jikinta sai dankwali gashin kanta a waje ta rike shi tana wasa da shi tana kallon video a laptop. Haka kawai sai Aliyu ya ji babu dadi samun su haka, baya son ganin Ataa da wani namijin a yanzu dan gani yake kyaunta zai iya jan hankalin wani namijin ya cutar da ita. Duk yadda yai kokarin sakin fuskarsa sai zuciyarsa tai masa ba dadi. Kusa da Doc Bukar Siyama ta aje kulolin hannunta sannan ta karbi na Aliyu ta aje kasa, da gangan Aliyu ya kasa cewa Doc Bukar komai sai kokarin danne bacin ransa yake.

“Aliyu ka shigo”

Doc Bukar ya tambaya yana rufe laptop din da murmushi a fuskarsa.

“Eh”

Mike tsaye Bukar yai yana fadin.

“Ka yi waya da Muhseen din?”

“Na yi”

Yadda Bukar yaji Aliyu na amsa masa magana da a take kuma babu sakewa ya san ransa ne a bace sai dai be yi zaton ganinsa da Ataa bacin ran nasa ba, a zatonta wani abun ne dabam yake damunsa.

“To ni zan wuce yar Fulani sai jango ko?”

“To sai da safe”

Ataa ta fada murya kasa kasa shi kuma ya juya ya fice yana murmushi. Duka duka yaushe aka Ataa ta zo asibiti da har zata sake da Doc Bukar haka shine abunda ya tsayawa Aliyu a rai.

“Ina Hijabin ki?”

Ya tambaya da kamar fada, har Siyama ta kalleshi.

“Gashi”

Ataa ta fada tana dauko shi daga gefen Nana ta maida saman jikinta. Har ya bude ba ki kamar ya sake cewa wani abu sai kuma yai shiru ya maida dubansa gurin Nana.

“Ya mai jiki”

Siyama ta tambaya.

“Alhamdulillah da sauki”

Ta fada tana kallon Aliyu da fuskarsa ke daure. Juyawa yai ya fice daga dakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Siyama tai saurin binta tana ma Ataa Allah kyauta. Rai a bace ya shiga motar yana ta mamakin yadda maza suke sakewa da mace da sun ga kyau su yi ta rawar jiki.

“Mtssssssss”

Yaja tsakin daya saka Siyama kallonsa kadan tai saurin kawar da kai, tana tunanin abunda tai ba daidai ba da har ya saka shi tsaki. Be shiga cikin gidan ba ya tsaya bakin gate ba tare da ya danna horn ba, Siyama na ganin hakan ta san baya son shiga ciki ne, sai ta bude motar ta fita shi kuma yai ribas ya juya, yana driving wayarsa tai ringing kallonta kawai yai ya dauke kai rabon da yaji ringing din waya indai ta shi ce har ya manta, dan shi baya son ringing sai dai ya bar waya a silent ko vibration. A bakin gate din gidansu Rahma ya faka motarsa sai a sannan ya kai hannu ya dauki wayar yana duba yadda Nasir da wata bakuwar number suka jera masa missing calls hudu ya saka wayar vibration sannan ya shiga text ya aikawa Rahma sako.

RAHMA POV.

“Kin ga ko Rahma ki daina damun kanki da lamarin namiji, namijin ma wanda zai iya mantawa da ke a take, domin yana jin zai iya zuwa ya dauko wata macen ke ya barki a nan”

Cewar Muneera tana wani yatsina fuska. Ikram ta girgiza mata kai.

“Wallahi karki dauki zugar Muneera Rahma, Aliyu yana son ki kuma yana kaunar domin ba ko wane namiji ne zai yarda ya auri mace mai ciwo irinki ba har ya nema miki lafiya, yanzu shekara takwas kuna kokarin shiga ta tara amman be taba nuna gazawarsa akai ba, sai ma nuna miki kauna da yake, Wallahi da wata ce ke kamata ma yai ki ce masa ya auro wata ku zauna tare domin shi babban tukuncin mace a gurin mijinta”

Muneera ta taba hannu tana dariya.

“Lallai Ikram ba ki da hankali, ke baki ganin yadda ya fara gajiya da ita? Wallahi da yana kaunar ba babu abunda zai saka ya ce ba za a cire kodar mai son siyarwa a dasa mata ba, kuma duk inda kodar ta kai sai nemota ya saka mata”

“Wacce ta kone yanzu waya saka mata ita ba shi ba, wai ya kike haka ne Muneera zawarcin nan fa ba dadi ne da shi ba, kin kuma sani dan gashi nan kina yi, akan me za ki rika zugata ta kashe auren ta bar mai son tsakani da Allah ta dawo tana nadama”

“Wallahi babu nadamar da zata yi, ko sakinta yai alheri ne dan zata iya auren wani ta haihu ta barshi shi da baya haihuwar yana rabon ido, ke ce dai baki san duniya ba tunda ba ki taba auren ba shiyasa kike wannan maganar, anyi karatu amman kamar wacce ba tai ba, ni wallahi na riga na san right dina namiji be isa ya juyani yadda yake so ba”

Muneera ce ke wannan maganar tana harar Ikram. Duk abunda suke Rahma bata ce koma, sai dai ta kasa daina hawayen da take saboda kishin da yake damunta.

“A tsakankanin kwanakin nan ina jin kamar na rabu da Aliyu, ko dan na samu haihu kuma na matsar da jikina daga nasa, dan ba zan yarda ya hana jiki da wata yar talakawa kuma ya hada da ni ba, amman sai na ji kamar ba zan iya ba, Saboda ina son Aliyu sosai ya saba min da wasu dabi'unsa da ko bachi bana jindadin yinsa ida yadda baya kusa da ni”

Tana rufe bakinta sako na shigowa yarta da number Aliyu Sweet bae kamar yadda tai saving number sa da dan emoji din heart a karshe. Sai da ta share hawayenta sannan ta bude sakon ta soma karantawa.

_Fito gani gurin gate muje gida_

_Na fi son zama a nan_

Ta mayar masa da amsa a take ya sake aiko mata da wani sakon.

_Na sani, a sokoto za mu zauna amman a gidanmu_

_Ka bar ni a nan kawai_

_Ba ke son kulawata ne Rahma? Ba kya son zama kusa da ni ne?_

_Ina so Aliyu ina so_

Ta mayar masa da amsa tana hawaye sai ya sake turo mata wani sakon.

_Then fito muje gidanmu I'm waiting for you_

“Wai yana bakin gate”

Ta fada tana kallon kanen nata Muneera tai karaf ta ce.

“Mi ya zo yi?”

“Wai na fito mu koma gida”

“Tashi kije, ki fadawa Daddy kawai da Momy sai ki bishi ku koma can idan ma kina son zaman a nan da safe sai ya rika kawo ki”

“Ta je fa kika ce tab hmmm”

Ikram ta kalli Muneera da tai maganar ta ce.

“Karki zuga ta akan abunda kika san gaskiyarsa, namijin da baya fushi idan yai be iya ba, duk yadda yake son ta idan tana masa irin haka zata nisanta sonta ne kawai a zuciyarsa”

Saukar da kafafunta Rahma tai daga saman gadon tunawa da Aliyu baya son jira duk kuwa da tasan ita yana daga mata kafa, sai dai idan yai fushi da ita itace zata shiga damuwa.

“Bari na fadawa Daddy da Mommyn sai na tafe”

“Wai da gaske tafiya za ki yi? Allah mai iko, ni kan kada Allah ya dora min son namiji haka”

Kallonta kawai Rahma tai ta ce

“Ba za ki gane ba ne, Ikram hada min magani na a jaka”

Ta dauki mayafinta ta dora a kafata ta fice daga dakin.

ALIYU POV.

Yana zaune cikin motar yana ta kallon wayarsa ko zata sake turo masa sako amman shiru, bata turo masa ba kuma baya son shiga ciki saboda iyayenta domin ya lura yanzu kamar basa son auren su. Sai dai yana daga musu kafa kuma yana dagawa Rahma kafa a duk abunda take saboda ya dauketa abokiyar rayuwa, a ganinsa idan mace bata jidadin a gidan aurenta ba to a ina zata je ta jidadin? And ya san mata karamar kwakwalwa ne da su shi tunaninsa da nata ba daya ba, shiyasa baya biye mata, idan kuma aka zo maganar mata yana raga mata sosai kuma yana daukarta da muhimmanci yana mata uzuri saboda ya san darajar ace wannan matarka ce, duk wani rashin kulawarsa da wulakanta mutane a waje ne ban da matarsa. Yana hakimce cikin motar Rahma ta bude gate ta fito tana takawa a hankali ta doso inda motarsa take, fita yai daga motar ya bude mata front seat tun kan ta karaso. Hugging dinta ya fara yi kamin ya sumbaci goshinta.

“Ya jikinki?”

“Da sauki”

Ya karbi jakarta hannunta ya saka a motar sannan ta shiga ya rufe kofar ya zagaya ya koma mazaunin direba ya hau titi.

MUHSEEN POV.

He wake up early saboda jirgin da zai bi na safe ne wanda zai tashi da misalin tara na safe. Gashi kuma akwai aikin da yake son yi a nan kamin ya wuce sokoto. Daga dawoalwarsa Dag masallacin da yai sallah asuba ya nufo part din Mama Fulani dan hadawa kansa ruwan Lipton, yana ta kallon Garejin da Ataa take yana murmushi ya san da tana nan da yanzu ta fito ta shiga aiki, bata wani dade sosai a gidan ba amman na saba da ita kamar wacce suka taso tare, zuwan nan ma saboda ganinta ne yasa yake son yaje saboda yayi missing dinta sosai. Be yi zaton zai samu Mama Fulani a kitchen ba, domin ba halinta ba ne fito tun asuba tai aiki.

“Mama ke ce a kitchen yanzu ni na dauka ma wata yar aikin aka samu”

Ya fada da mamaki karara a fuskarsa. Ita da murmushi ta kalleshi tana sanye da kayan bachi kana ganin fuskarta kasan tana cikin farinciki sosai.

“Ina dai a sake dauko mana wata yar aikin amman tsohuwa na ke so ba yarinya ba”

Dariya Muhseen yai ya nufi butar ruwan zafi ya dauko ya zuba mata ruwa yana fadin.

“Saboda mi?”

“Ai ka fi kowa sani”

“Wai tafiya za ki yi ne hala? Naga kina farinciki kuma kin shigo kitchen tun da safe”

“Aa Wallahi Abbah ku ne ya fada min jiya da dare bayan ya dawo aiki, kasan maganar kamfanin nan da ake son siyarwa”

“Eh wani abun ne”

“Wani abokin kasuwanci Abbah da ke can Agadaz ya ji, ya fadawa Babansa sai suka kira Abbah ku suka ce masa suna son za su iya kamfanin su sabunta shi a cigaba da yin komai a karkashin mahaifinku, shima yace shekaranjiya ya samu labarin kamar wasa sai jiya da rana aka jira da number Nijar sarkin ya fada masa jikansa zai zo ya kara duba kamfanin kuma su tattauna akan maganar yau”

“Wow amman am so happy for Abbah Wallahi”

“For us dai ai wannan dukan mu ne, domin ance mutumen ba shi da keta, sarkin Agadaz ne komai yaransa da jikoki yake wakiltawa su yi shi yana can sai idan wani abun babba ya taso yake zuwa”

“Au sarki ne ma amman wannan ya tara da yawa”

“Kai ance yana da dukiya sosai, shi da iyalansa, ance duk inda zai je da jirginsa ma yake yawo”

“Amman Mama irin wannan anya ma zai ci abincin kin san sun fi son abinci waje fa irin na turawa”

“Abbah kune ya ce a shirya masa dan yafi son abincin gargajiya, ai ba sarkin ne zai zo ba jikansa ne, da misalin goma za su iso shiyasa na soma aikin tun yanzu kamin su Maryam su farka su taya ni”

“Okay ni kuma da 9 zan je sokoto”

“Gurin me?”

“Ba na fada miki Aliyu ya kira ni ba akan rashin lafiyar matar nan mahaifiyar Ataa”

“Wai a ina ya ganta?”

“Oho ai tunda kince a sokoto take kuma yana can ga Momy ma a can nemanta ba zai musu wahala ba”

“Muhseen ku fita daga safgar yarinyar nan dan girman Allah, wai kamar ku za a ce kun tsaya kuna bata lokacinku akan wata kazamar yarinya yar matsiyata irin wannan? Haba dai idan ma kyauta ne yake dibarku ai sai ka koma gida Yola ka zabo kyawawan mata suna nan da yawa yayan manyan mutane amman ya yar talaka ba, dan akasan ba zan bari ka auri yar da ubanta baya iya amsa sunansa a garinsu”

Murmushi yai.

“Mama kenan, yanzu idan wata kaddara ta faru aka ce sai na auri Ataa yaya kenan?”

“Babu ma abunda zai faru, kuma ko ya faru ba zaka aureta ba, kai ni fa na tsani yarinyar nan ko sunanta bana son ji”

“Gashi kuma naga kamar dan ki sonta yake”

“Ai Aliyu ba irinka ba ne Wallahi, Aliyu ya fi karfin yar talaka yar talakan ma wacce tai aiki a gidansu, kawai dai yana kokarin ganin sun rabu lafiya ne kar su bata masa suna kasan talaka da sheri ga hassada”

Wannan karon dariya Muhseen yai domin shi a tashi fahimtar Aliyu ya fara son Ataa tun da har zai iya daga waya ya kira shi dan ayi ma mahaifiyarta aiki, mutumen da you can die in front of him ya wuce ya bar ma. Mama Fulani ta aje wukar hannunta ta fito daga kitchen ta nufi dakinsu Maryam. Wutar dakin ta fara kunnawa sannan ta shiga tashinta.

“Maryam ku tashi mana ku rika min aiki mu yi mu gama ku yi wanka ko shirya”

“Fita za mu yi?”

Maryam ta tambaya tana murza idonta.

“Ba ko dai za mu yi, kuma idan Allah ya min yadda na ke so ya kamu da son daya daga cikinku”

Ta fada tana fita daga dakin zuwa dakin Rukaiyah domin tashinta.

ATAA POV.

Sam bana jin dadin ganina Aliyu a yanzu, saboda jin kai da yake fama da shi ga uban nuna isa da yake yi kamar shi ya fi kowa a duniyar nan. Wato shi ba zai iya cewa ya jikin Nana ba, ba kuma zai iya shigowa da sallama ba, sai amsawa mutane magana tsaitsaye da gadara. Abincin daya kawo ma kin ci nai saboda shi ya riko dan haka ni ba zan ma ci abincin daya kawo ba. Sai kawai na zuba na rana da Momy ta kawo mana na sake cinsa sannan nai sallah isha'i na kwanta. Ba laifi yau na tashi raina da dan sakewa saboda Nana ta gane ni kuma ta samu bachi mai kyau da allura da Doc nan yai mata jiya domin har yanzu bata farka ba. Duk kuwa da zuciya ta bata aminta da shi sosai ba saboda gudun abunda ya faru ya sake faruwa, sai idan na tuna abunda Allah ua kaddarawa bawa babu mahani sai na kwantar da hankali domin ko dauke Nana nai ban san inda zan kaita ba daga nan, ba ni da kudin magani kuma ban san wanda zai taimaka mana ba, idan ban yarda da Aliyu ba ina kokarin yarda da Momy saboda yanayin da na gani a fuskarta kamar ba zata iya cutar da wani ba. Misalin takwas da wasu yan mituna Husna da Amina suka shigo suka kawo mana abun karyawa, ina cikin amsa ya mai jikin da suka min Nana ta farka wani abun mamaki sai ta tashi zaune da kanta sai dai fuskarta ta dan kumbura kadan, a nan suka shiga gaisheta suna mata ya jiki ta amsa musu da hausar ta da bata fitowa sosai, sannan suka min sallama suka tafi ba laifi sukan suna da son mutane babu nuna kyama ba kamar su Maryam da Rukaiya ba. Toilet na shiga na dauko karamin bokiti da ruwa a kofi na kawo na wanke ma Nana baki da kaina sannan na zuba tea din da Momy ta aiko mana na bata ta sha sannan na rika ta sauko daga kan gadon ta shiga bandakin da taimakona tai alwala muka fito ina rike da ita na saka mata hijabina tai sallah daga zaune.

Bayan ta gama ta koma saman gadon ta kwanta, wani likita ne ya shigo ya dubata ba wacan na jiya mai far'a da son mutane ba, wannan fukarsa a daure take, tsabanin wacan daya sake min fuska ya tambayi sunana da garinmu har ya dauko laptop dinsa ya nuna min rawar yan garinmu. Bayan fitar Doc din wata nurse ta shigo ta bata magani sannan ta fita sai a lokacin ni kuma na zuba abincin ina ci ina amsawa Nana tambayar da take min wai yaushe na dawo.

“Tun shekaranjiya, amman baki sani ba”

“Bana iya gane komai, na sha wahala sosai bayan tafiyarki Ataa babu mai kula da ni ga yunwa tun ina iya tashi har kai bana iyawa idan na tashi sai na fadi, na yi ta cewa Farida ta kira Maman Salma ta fada miki cewar ki dawo ki kula da ni kamin na mutu amman bata kira ba”

Da yaren buzanci take fada min wannan maganar, ban san lokacin da idona ya cika da hawaye ba na aje abincin da nake ci ina kallonta na ce.

“Ai yanzu ba zan sake tafiya na barki ba Nana”

“Bana son ki sake tafiya ki bar a nan, da ki je neman kudin maganina ki bar ni mutu a wulakance kara ki tsaya kusa da ni a haka na mutu a suturce, kar ki bari na zama ta farko a tsatson sarautar mu da za tai mutuwar wulakanci”

“Allah ya raba mu da mutuwar wulakanci Nana ba zan sake barinki ba In-Sha-Allah”

Na fada ina share mata hawayenta, sannan na zauna kusa da ita ina dauko mata labarin Abuja sai dai ban yarda na fada mata zancen korata kai ba, cewa nai dawowa nai na ban tsaya na karbi kudin aikina ba domin da sunan ganin gida na zo.

“Ki bar musu kudin can ba zaki koma ba, waya kawo ni asibiti?”

“Wata Hajiya ce ta taimaka mana”

Haka ta fada min ni kuma nai murmushi ina tuna Kamal ko ina yake a yanzu oho. Misalin sha biyu Muhseen ya shigo dakin da muke fuskarsa da murmushi kamar yadda ya saba, ina ganinsa dadi ya lullube ni na hau murna domin na san shi ne likitan da zai mata aikin kuma na san shi ba mugu ba ne kamar Doc Asim ko da yake ba a fuska abun yake ba.

“Pretty Pretty”

Ya fada yana min dariya sai nima nai masa murmushi.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa ya jikin Mamanmu?”

“Da sauki”

Ya karasa kusa da ita ya rika hannunta ya sumbace shi sannan yai mata sannu.

“Sannu Mamana Allah ya baki lafiya”

“Amin na gode”

Sannan ya nufi files din da suke nan yana dubawa sai ya fita da su, bayan wani lokaci ya sake lokowa ya kira ni, sai na tashi na fita na same shi tsaye jikin kofar.

“Pretty ya kin yi missing dina?”

Na yi kasa da kaina shi kuma sai kallon kirjina yake da fuskata kasancewar babu Hijab a jiki.

“Wani abun nake son na tambaye ki, miyasa kika bari Mahaifiyarki ta siyar da kodarta?”

A take fuska ta canja.

“Ba siyar tai ba, likitan nan ne ya cuce mu ya cire mata”

“To gaskiya ya cutar da ku, domin aikin nan da za a mata akwai yiyuwar bayan aikin ta iya manta wani bangare na rayuwarta ko ma gaba daya zuwa wani lokaci saboda abun ya taba kwalkwalwarta”

“Wani abun zai sake samunta kuma?”

Na tambaya hankali a tashe.

“No zata samu lafiya amman akwai yiyiwar hakan ya faru shiyasa na fada miki haka tun yanzu, gaskiya likitan nan da Aliyu sun cutar da ku, ko da yake Aliyu ya ce siya yai amman gaya zaka siye abu kamar wannan koda fa guda ace baka mai shi ba kuma har ka yarda kai amfani da ita”

Hawaye ne ya fara sauko min sai ya miko min wata takardar da pen ya ce na saka hannu.

“Ki kwantar da hankalinki wannan na dan lokaci ne amman zata samu lafiya, saka mim hannu zan mata tiyata”

“Muhseen na baka amanar mahaifiyata dan Allah karka cutar da ita”

Na fada bayan an saka hannun a inda ya nuna min na mika masa. Sai ya kai dayan hannunsa ya shafa kaina tare da yanjo tsoron dake bayana ya dawo da shi gaba.

“Ba zan mata komai ba, ba kowa ne kamar Aliyu ba, bari naje na saka kayan theater amman ki min alkawari ba za ki yi kuka ba?”

Na gyada kai ina hawaye.

“Good girl”

Ya fada sannan ya wuce ni kuma na resina a gurin ina kuka. Wasu nurses ne suka zo da kujera suka dora Nana akai suka fito da ita daga dakin ni kuma nai saurin share hawayena gudun kar na sakata a damuwa.

#Team Muhseen #Team Aliyu #Kamal #Team Rahma #Ataa

Wane Team ya fi yawa?.🤔 Ni dai Ina Team Rahma kishi gaskiya ne 🙄😏

*ZAKI

By Khadeeja Candy

31...

Kiran sallah asuba ne ya farkar da shi daga bachinsa da yake, kasancewar karar loudspeaker masallacin ta shigo sosai har cikin dakinsu saboda daukewar wutar nepa da akai misalin uku da rabi na dare. Sake maida idon yai ya lumshe ya saka hannuna na dama ya murza saman fatar idon sannan ya sake budewa ya kalli Rahma dake kwance kirjinsa tana sharar bachinta a hankali. Dagata ya fara yi daga jikinsa sannan na sauko da kafafunsa kasa ya zauna bakin gadon ya dafe kansa ya farka da Ataa a ransa kamar yadda mafarkinsa ma ita ce a ciki, ajiyar zuciya ya sauke sau biyu sannan ya unkura ya tashi jikinsa ba tufafi ya shiga bandaki, wanka ya fara yi kamin alwala sannan ya dauro tawul ya fito ya nufi wardrobe ya dauko karamin jean ya saka ya dora Jallabiya a sama sannan ya dauko kasa ya nufi masallaci. Bayan ya sauke farilla da addu'o'i ya dawo gida yana tafe a hanya yana tasbihi da hannunsa har ya iso, yana kokarin hawa stairs mai gadinsa ya kunna sola gidan ya gaske gaba daya, dakinsa ya shiga ya zauna bakin gadon tare da kai hannunsa yana tashin Rahma a hankali.“Dear tashi ki yi sallah”

Daker ta motsa saboda bachin dake cikin idonta domin jiya bata samu bachi da wuri ba daga ita har Aliyu da nuna mata yadda yai maramarinta a tsakanin kwanakin nan. Sai ya tabbarar ta farka sannan ya dauki qur'anensa ya sauko downstairs ya zauna a saman kujera ya bude yana karantawa. Yayi one hour ya a karatun sannan ya hau ya maida qur'anen a nan ya samu Rahma ta koma bachi sanye da Hijab din da tai sallah, Bedsheet yaja ya lulluba mata saman jiki sannan ya sauko ya shiga kitchen, daman idan suna sokoto shi yake shi ke hada musu breakfast ba kamar Abuja ba da mai aiki yake musu. Ruwan Lipton ya fara dorawa sannan ya fasa kwai ya ya kada ya je ya firaye dankalin ya zuba mai ya soma soyawa, da kansa ya share kitchen din bayan gama komai ya zuba a abun zuba shara sannan ya dauko kayan ya kawo dinning. Ya kunna tv ya zauna a gurin yana kallon news baya son ya tashi Rahma a yanzu domin yasan bata saba farkawa da 9 ba sai 10 balle yanzu da yasan ciwon nata yafi na da yafi son ta huta iya hutawa har bachi ya gintse ta. Yana zaune a falon har 11 Rahma bata farka ba, tana can tana bachin dadi shi kuma yana zaune yana labartawa Nasir abunda ya faru a waya.“Aliyu idan ka nuna Muhseen damuwarka idan yai maka abu, domin idan ya lura kana jin haushi zai yi ta jindadi ne yana ta bata maka rai wanda hakan zai kara bata zumuncinku ne kawai”

“Muhseen kanena ne Nasir idan be min biyaya ba kar ya sammaci samun damata da har zai raina ni”

“Muhseen kanenka ne, amman babu wanda zai san da hakan sai idan ka fada domin babu wanda zai kalleshi ya ce kanenka ne, kai kuma kana son nuna masa kai ne sama da shi, yes haka ne amman ba ko da yaushe babba yake zama yace dole sai shi a bi shi, wani lokacin kai ua kamata ace ka bi dan a zauna lafiya”

“O ni zan bi Muhseen din? Nasir kamar baka san da Aliyu kake magana ba?”

“Na sani ma, naga ba kullum take jumma'a ba”

“Amman kullum rana ce”

Aliyu na fadar hakan ya aje wayar a hannun cushion ya tashi ya hau sama domin duba Rahma, a zaune ya same ta saman gado tana danna wayarta dayan hannunta na saman kanta tana tsifar gashinta. Kusa da ita ya zauna ya sumbace kumatunta.

“Good morning ya jikinki?”

“Da sauki”

Ta fada ba tare da ta kalleshi ba.

“Baki sha maganinki na safe ba, bana son tashinki saboda na san kin gaji sosai”

Ya fada yana janye hannunta daga saman kanta.

“Ki daina tsifar nan karki gajiyar da kanki idan mun ci abinci zan kai ki saloon a gyara miki kai”

Sauka tai daga kan gadon.

“Bana son fita ko'ina yau na fadawa Mommy ta aiko da mai mata kitso ta zo ta min”

Bandaki ta nufa ta barshi a gurin zaune. Bayan ta gama abunda zata yi ta fito sannan shi ma ya shiga ya wanke bakinsa ya fito sai ya same ta gaban madubi zaune tana kallon kanta hawaye na sauko mata.

“Wani abun ne kuma?”Juyowa tai ta kalleshi.

“Yanzu Aliyu idan na mutu ba zaka wuce wata daya ba zaka mantani ko?”

Kallonta yake ba tare da yace mata komai ba.

“Idan na tuna ba saboda ni ka zo garin nan ba sai na ji kamar na hadiye zuciya na mutu, ban taba kawowa a raina cewar zaka taba son wata mace ba, watan ma kazama yar aikin gidanka kuma yar bara a titi”

“Taso muje mu ci abinci”

Shine abunda ya fada yana juyawa.

“Ba ka son ayi maganarta ko? Saboda ta fini kyau ta karbu a zuciyarka, saboda kana sonta wata kila ma ka kosa na mutu ka aureta....!”

“Rahma....!”

Ya kira sunanta a tsawace da duka muryarsa, ba ita kadai ba har kujear da take zaune a kai sai ta girgiza.

Readers Also Read