Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 24

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 24

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 24: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 24. “control your tongue, Bana son nanata magana kin sani, kuma bana…

4,480 words

“control your tongue, Bana son nanata magana kin sani, kuma bana son bata miki rai amman kina kokarin ganin sai na bata miki rai, kin riga kin karya yarinyar kin kuma juya mata baya dan haka babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan wani abun ne a tsakanina da ita ne ba da ke ba, lamarinta ya daina damunki kina damuna, ki bar ni na ji da ciwonki da kuma kuskuren da na aikata”

Tunda ya soma maganar hawaye yake sauko mata har ya gama ya juya ya fice daga dakin cikin bacin rai. Maganganun da yai mata suna ta maimaita kansu a cikin kunnenta, zata ita rantsuwa ta sake ra tsewa babu kaffara, cewar Aliyu be taba daka mata tsawa kamar haka ba, ko fada sukai ko suka samu tsabani sai dai ya kyaleta ya ki yi mata magana ya daina kulata amman ba fada kamar haka ba.

“A a ba zaka auri wata ba Aliyu ko bana da rai balle ina raye, ba zaka so wata ba”

Ya fada tana girgiza kai sai kuma ta saka hannunta ta watse duk abunda yake kan miron ta dauki stool din ta jefi ruwan mirror da shi a take ya watse ya fadi kasa tana ihu kamar wata mahaukaciya. Kuka tai sosai har sai da kanta ya soma ciwo kamar ance mata da gaske Aliyu son Ataa yake kuma aurenta zai yi, sai da idonta yai ja sosai sannan Aliyu ya shigo dakin ya daga daga kwancen da take ya rumgume matarsa tsantsan jikinsa.Wani lokacin yana dagawa Rahma kafa saboda ciwonta yasan abu kadan zai iya sanadin tashin ciwonta ko kuma ya saka ta cikin wani hali, idan ma ta yi kishi ai saboda shi tai kuma saboda tana son sa, sai dai hakan ba zai saka ya biye mata ba ta yarda cewar ita kadai zata zauna a gidansa ko a zuciyarsa duk kuwa da ba shi da muradin auren mace sama da daya. Kara fashewa tai da kuka tana jimkeshi da hannayenta. Sun dauki lokaci a haka kamin ya dagota ba tare da ya ce mata komai ba ya saketa ya shiga bandaki yai wanka tana zaune a gurim har ya fito ya shirya a gabanta ya saka agogon hannunsa da atm dinsa da wallet sannan ya kalleta.

“Ta so muje ki karya”

Kamar mai jira sai ta mike tsaye ta sauri ta bi bayansa domin shi tuni yayi gaba, kamar masu rigengen saukowa daga stairs din haka suka sauko, ita tana sauri ta cin masa su sauko tare shi kuma yana ta lafiya abunsa ba tare daya jira ta ba. Ya riga isa dinning sai yaja mata kujera ta zauna sannan ya shiga zuba mata abincin bayan ya gama shi ma ya zauna kusa da ita ya zauna yana ta lasa wayarsa kamar be san da zamanta a gurin ba.

“Ba zaka ci abincin ba?”

“Na ci”

Ya fada ba tare daya kalleta ba, ba dan kuma ya ci abincin ba. Sai da ta ci ta koshi sannan ya tashi ya koma sama sai ta bishi a ciki ko da ta shiga ta samu yana hada maganinta gurin daya, sannan ya shiga bathroom ya debo mata ruwan tab ya mika mata maganin ta karba ta sha. Sai ya sumbaci goshinta kamar yadda ya saba mata.

“Zan fita amman ba zan dade ba zan dawo yanzu”

Da kallo ta bishi har ya fice daga dakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tana jin tashi motarsa ta dauki wayarta ta kira mahaifiyarta tana kuka.ALIYU POV.

Ko da isa gidan Momy biyu ta kusa domin rana ta bude sosai wani gurin ma har an fara kiran sallah. Amina ce da Momy zaune a falon Amina na kwance Momy kuma na zaune suna cin apple. Daga kwance da Amina take ta mikawa Aliyu gaisuwa sai ya watsa mata harara.

“Ni za ki gaisar a kwance”

Saurin tashi tai zaune ta sake gaisheki sai kuma ya ji amsa mata ya kalli Momy yana mika mata gaisuwa.

“Kai komai na ka na zafi ne, shi gasar da mutun a kwance kuma laifi ne?”

“Yayanta ne ni fa Momy wannan ai rashin da a ne, je ki duba min abinci”

Ya karasa yana kallon Amina, da sauri ta tashi ta nufi dinning. Momy ta sake kallonsa ta ce.

“Ka je da safe ka duba mahaifiyar Ataa?”

“A a ba mu dade da tashi daga bachi ba”

“Kai da wa?”

“Rahma”

“Au iyayenta sun yarda sun baka ita? Ta dawo?”

“Daman ai ba hana min sukai ba, zuwan da sukai a nan ma da ban amince ba da ba zan barta ta zo ba”

“Amman dai kasan ya kamata ka je da safe ka gaisa da mahaifiyar yarinyar nan”

“Momy ban san rana yayi haka sosai ba yanzu zan je”

“Kara ka fara zuwa inyaso idan ka dawo sai ka ci abinci, Muhseen ya zo kuma ban san halin da ake ciki ba, ni bana son zuwa yanzu ina jiran Ramatu ne ta zo muje tare dan na fada mata cewar Daddynku yana da patient a asibiti ta zo ta rika kwanar mana da ita, ka ga ita ma Ataa sai ta samu tana dan hutawa kar dawainiyar tai mata yawa”

“Ramatu mai aikin Hajiya Baraka?”

“Eh kasan tana da kirki sosai, bana son dauko wani daga gidan dangina ne ko na Daddynku bana son maganar tai ta yawo ne, amman ka ga Hajiya Baraka aminiyatace ba kowa zata fadawa ba”

“Muhseen ya zo kik ce Momy?”

Ya tambaya yana kallon Amina wacce ta doso inda yake rike da plate din abinci.

“Eh nan ya fara sauko kamin ya wuce asibitin”

“Ina abincin da za a kai mata?”

“Gashi can a dinning”

Ya mikawa Amina keys dinsa hannunsa.

“Saka min abincin a mota”Hannu biyu ta saka ta karbi keys din ba dan tsoronsa na sai dan Momy ta koya musu haka karbar abu da hannu biyu tun suna kanana domin yana karawa mutum kima da daraja a idon mutane.

“Da ya so mi yace? ”

“Be ce komai ba, kawai dai yace ya dauka Ataa na nan”

Momy na fadin hakan Aliyu ya mike tsaye ya fice daga falon ba tare daya taba abincin ba. Cikin motar ya zauna har Amina ta gama saka masa abincin sannan ya yi ma motar key tun kamin ya danna horn mai gadin ya bude masa gate ya dauki hanyar Usmanu Danfodiyo University teaching hospital wato uduth a takaice. Tafiyar da zata dauke shi minti ashirin da biyar ko ashirin yai ta a cikin minti goma sha sha hudu, a gurin da aka tana dan aje motoci ya aje motarsa ya fito da abincin dake cikin kulolin da kwadon da aka zuba plates da spoon a ciki ya aje a gurin sannan ya rufe motar. Tunanin yadda zai dauke su yake dan baya jin zai iya maya biyu yaje ya dawo dan daukar abinci kawai. Wata budurwa ya kalla ta sha kwaliyar kanti tana tsaye jikin wata farar mota sai yauki take kamar miyar kubewa da alama wasu take jira.

“Ke zo nan”

Ya fada kai tsaye kamar wacce ta sani ko kuma daya daga cikin kanensa yana kallonta fuskarsa babu alamun wasa. Kallonsa budurwar tai daga sama zuwa kasa farar shadda ce a jikinsa ta yi mugun karbarsa kamar wani ango fuskarsa nata haske ga farinsa sai shining yake, ta kuma lura da makekeyar expensive car din da dake yake tsaye kusa da ita ta san tashi shi domin alamun naira sun nuna a jikinsa. Ta nuna kanta tana wani lauye baki kamar wata karuwa.“Ni....”

Be ce mata komai ba sai kallonta yake, ita bata jira yace ita din ko ba ita ba sai ta karaso kusa da shi tana wani rangwada kamar zata karye.

“Dauki kulolin nan ki biyo ni”

“Okay”

Ta fada yadda take pronouncing o din is like tana koyawa mutane karatu ne. Shi ya rika kwandon yai gaba ita kuma ta riko kulolin karama da babba ta bi bayansa zuciyarta na raya mata cewar ya kyasa da ita. Kai tsaye suka wuce ciki tana biye da shi har suka shiga dakin da mahaifiyar Ataa take. Inda taga ya aje kwandon ta karaso ta aje kulolin tana kallon Ataa wacce ke zaune saman gadon hawaye shar a fuskarta a zatonta ita ce bata da lafiyar.

“Sannu ya cikin”

Ta fada tana wani lankwasa harshe kamar wata bakanuwa. Hannu Aliyu ya saka aljihu ya ciro wallet dinsa ya zaro dubu uku har zai dora a saman gadon asibitin ya ce ta dauka sai kuma ganin Ataa yasa ya mika mata da hannunsa.

“Aa ka barsu kawai”

“Karba mana bana maida kudi”

Hannu ya kai ta karba.

“Thank you”

Ta furta tana juyawa ta koma tana ta sauraren ta ji Aliyu ya kirata ko ya biyo bayanta amman bata ji ba har ta fice. Ko be tambaya ba yasan an shiga tiyata ne da Mahaifiyar Ataa tunda Momy ta fada masa Muhseen ya zo kuma gashi be tarar da ita cikin dakin ba. Kallon Ataa dake zaune kan hospital bed din Aliyu yai with serious face ya ce.

“Mi akai miki kike kuka?”

Bata ce masa komai ba bayan turon karamin bakinta da tai ta saka hannayenta ta share hawayen fuskarta. Wata kila tsoron tiyatar da aka shiga da mahaifiyarta take ko kuma wani abun akai mata, or maybe Muhseen ya fada mata wata maganar ne marar dadi.“Ga abinci”

Dauke kai tai.

“Bana ci”

A tunaninsa ko tana tsoron kar ya saka mata wani abun ne ko kuma ya cutar da ita shiyasa ba zata ce. Kujerar da ke gefen gadon ya janyo ya zauna ya dauki plate din ya zuba jalop din da sannan ya bude dayar kular ya zuba farfesun kazar da ke cikin ya saka spoon ya soma ci, abinci yake ci amman idonsa akan Ataa ne har ya ci rabi ya mika mata sauran.

“Karbi ki ci”

“Na ce bana ci”

“Idan na ce ayi abu yi ake ba a musa min karbi ki ci na ce”

Kallonsa tai hawaye na mata zuba.

“Ai babu wanda ya isa ya cilasata kai yi Aliyu, sai dai ka cilasta wasu, babu wanda ya isa ya taba wani naka balle ya taba ka, yadda kaga dama haka kake haka kake juya kowa, ka taka kowa ka cilasta ka zalinci wanda ka ga dama saboda kana da kudi ni kuma kana gani na talaka”

“Ba ni na cirewa mahaifiyarki koda ba, lokacin da aka cire mata koda ina a gurin ne kin gan ni ne?”

Ya fada yana kokarin danna fushinsa. Sai ta girgiza kai

“Baka nan, amman kudinka suna nan, ikonka yana nan, isarka tana nan waya sani ko asibitin taka ce? Kai ma baka son talaka miyasa ka sakawa matarka kodar talaka? Karyar soyayya kake mata tunda baka iya daukar kodarka ka saka mata ba, ba tana da iyaye ba miyasa basu bata kodar su ba? Sai ta Nana matar da ita kadai ta rage min a duniya? Kokarin kare kanka kawai kake yi ai Muhseen ya fada taya za a sakawa matarka kodar da baka san mai ita ba? Duk wannan taimakon kana min ne saboda ka san ka zalince ni ka cutar da ni ni da mahaifiyata Aliyu kai azzalumi ne....”

Cikin wani irin fushi marar misatuwa ya jefar da plate din hannunsa ya mike tsaye yana huci kamar zai dake ta, sai kuma yai saurin kawarda fuskarsa daga barin kallon yana kokarin saita numfashinsa. Mikewa tai tsaye wanda hakan yai daidai da shigowar Doc Bukar dakin, tana kallonsa fuskarta da hawaye ta ce.

“Na fada Aliyu ka kashe ni daman mutuwa ta fi rayuwa a yanzu, ka riga ka gama da ni tun da kasa aka cire mahaifiya koda dan zalinci ka sadawa ita ta rayu mu sai mu mutu, ga mahaifiyata can ana mata aiki Muhseen ya fada min zata iya mantawa da komai ciki har da ni har da ni Aliyu, idan kuma bata rayuwa ni ce a cikin matsala saboda zalincin da kuka mana kai da wannan likitan, har abada ba zan yafe muku ba kuma Allah ba zai bar ku ba....”

Ta fada kanta a sama tana kallonsa hawaye ke mata zuba sosai har wani dauke numfashi take kamar zata shude... Jawur idon Aliyu sukai yana kallon Ataa take rabe masa uku ba ko biyu babu ko kyafta ido. Doc Bukar ne ya matsa kusa da su yana Kallon Aliyu sai kuma ya kalli Ataa.

“Zauna”

Ya fada sannan ya kalli Aliyu.

“Da za ka fita na wani lokaci”

Sai a lokacin Aliyu ya kalli Doc Bukar ya sake kallon Ataa sai kuma ya nufi kofa ya fice cikin wani irin bacin rai marar misaltuwa.Ba zai iya fadar lokaci da ya kawo gurin motarsa ba wata kila ma taku biyu yai ko uku ko kuma dari ko dubu shi dai kawai ya samu kansa tsaye jikin motarsa ba tare da ya san ya iso ba saboda tsananin bacin rai da zafin kalaman Ataa, wani irin gudu jinin zuciyarsa ke yana da tabbacin da za a bude kirjinsa a yanzu wata kila da hayaki za a gani yana tashi. Ita kadai ta kai haka duk duniyar nan ta fada masa magana irin wannan mai zafi da daci kuma ya kyaleta ita kadai ce mutum ta farko da ta taba taba martabarsa da duk wani abun daya takama da shi tana a talakarta ta fada masa magana son ranta. Bude motarsa yai ya shiga ciki ya zauna for like 40 minutes sannan yai mata keys ya fita daga harabar gurin. Driving kawai yake ba dan yasan inda zai je ba, gida gurin Rahma ko kuwa gurin Momy? Ko gurin wasu abokansa ko yan'uwa? Kalamanta na ta maimaita kansu a kwakwalwarsa tun yana jin zai iya jurewa har ya kai ga runtse ido yana damke sitiyarin motar, sam ya manta cewar tuki yake kuma babban titi yake na gawon nama, har sai da yaji ya bugi wata motar wata motar kuma ta bugu bayan tasa, da sauri ya bude ido yana kiran mafi kyawun sunan a cikin sunayen Ubangiji wato Ya Rahamanin Rahim. Saurin tsayarda motar yai motar da ke gabansa tai gaba shi kuma ya faka tashi gefe ya fito ya nufi mai motar.

“Malam lafiya kake kuwa?”

Mutumen ya tambaya.

“I'm sorry ina cikin matsala ne”

Aliyu ya fada sannan ya bude wallet dinsa ya ciro sababbin kudi da zasu kai 50k ya mikawa mutumen.

“Ga wannan”

Mutumen ya kalli kudin kamar ya karba sai kuma ya dan tsaya jan aji.

“Ai ba kudi ba... ”

“Idan zaka karba ka karba kawai ba zan tsaya magana da kai ba na fada maka ina da matsala”

Hannun mutumen ya kai ya karbi kudin yana dan nuna kamar be so ba. Aliyu ya juyo ya bude motarsa ya shiga mutane sai kallonsa suke yai mata key ya sake hawa titin yana ta tasbihi saboda samun fin karfin fushinsa. Wani guri ya samu can kusa da ga ďan k'ane hotel ya faka motarsa ya fito yana shakar iskar gurin. Har yanzu ya kasa daina jin kalaman Ataa a kunensa sai dai wannan karon a maimaikon ransa ya bace kamar dazun sai tausayinta ya soma rabar zuciyarsa fiye da da, yarinyar da ke tsoronsa da masu kudi tun da har ta iya bude baki ta fada masa magana irin wannan tabbas tana cikin damuwa da bakinciki, ya sani ko Ataa zata fahimcin ba nan kusa ba kuma ba a yanzu ba. Yanzu ma laifin ba nata bane na Muhseen ne, for what zai fada mata cewar mahaifiyarta zata manta da ita? For what zai mata karyar cewar da hadin kan Aliyu aka cire mata koda? Komawa yai cikin motar a fusace ya dauki hanyar gidansu Momy.

**ZAKI

By Khadeeja Candy

32...

Abinci kusan kala hudu Mama Fulani ta shirya ma bakon da zaizo, ko da tara tai gaba dayansu sun shirya Maryam da Rukaiya sukai wanka Baby ce kawai ta wuce scul. Amman shiru bako be iso har goma da rabi. Sai misalin sha daya Abbah ya kira yace mata bakon ya sauko Nigeria gashi nan ma zai taro shi a airport.

A sannan ne Mama Fulani ta saka su maryam suka kwashi kulolin abincin suka jera part din Abbah, ita kuma ta kunn turaren wuta irin mai kamshin nan sosai na larabawa ta kara kunna dayan ac sannan ya dawo part dinta, a daki ta samu su Maryam da Rukaiya sai kara gyara fuskarsu suke suna fesa turare. Wani dadi ne ya lullube ta ganin duka yayan nata sun fito fes gwanin sha'awa. Suna jin tsayawar mota sukai hanzari yafa gyalensu suka jiyo bayan Mama Fulani dake cikin wata shadda yar mali ta sha paint work gwanin sha'awa. Mota biyu ce ta Abbah da kuma wata mai tsada da suka shigo, ta kamfaninsu da ke nan Abuja. Suna fitowa daga motar Mama Fulani na fitowa ita da su Maryam suna musu marhabun bakin Mama Fulani har kunne, a maimakon mutum daya sai suka ga samari biyu dayan sanye da kananan kaya dayan kuma sanye da farar shadda ya nada bakin rawani a kansa kamar wani balarabe.

“Lale marhabun Lale lale marhabun da manyan baki”

Mama Fulani ta fada tana kokarin sauka daga balcony din ta nufi inda suke, sai duk suka saki murmushi suna kallonta.

“Sannu da zuwa”

Maryam ta fada kamin Rukaiyah ta dora da nata. Dayan ne ya amsa yayinda yadan kuma yake ta kallonsu yana murmushi kamar baya jin abunda suke fada. Abbah ne yai gaba zuwa part dinsa yana musu iso sai suka bishi a baya, bayan sun shiga ciki sun huta ne Abbah ya shigo part din Mama Fulani ya kira dan taje su gaisa da su, sannan ya shiga bangaren Ammy ya same ta falonta zaune ita da yaranta suna kallon wani film da ake hassaka a mbc Bollywood.Ganin Abbah yasa Batula da Zainab tashi zaune suna murna domin ba su san da shigowarsa ba sai ganinsa a falon.

“Sannu da zuwa”

Ammy ta fada tana dariya, sai ya zauna kusa da ita yana kallonta.

“Yauwa Hajiyar gida, ban fada miki za'ayi ba ki ba?”

“Na sani na fada min, amman naga ai Hajiya Fulani ce zata shirya komai ko?”

“Ko dai zata shirya ai ya kamata ku gyara ku fito ku tarbesu, na fa sha fada miki cewar bana son yawan kebe kanki da kike yi”

“Bana son yawa shiga Safgar Hajiya Fulani ne, bana son nai mata abunda zai zo ya zame mana matsala ko ka zo kana mim fada”

Be sake ce mata komai ba ya kalli yaransa.

“Batula ku tashi kuje ku gaisa da baki”

Gaba dayansu suka tashi suka Batula ta tashi ta shiga dakinta ta dauko mayafi Zainab kan haka ta fita ita Humaira daman abaya ce a jikinta da dankwali, Abbah ya biyo bayansu yana jerowa da Ammy Inteesar kuma na rike da hannunsa suka nufi part din. Ko da suka shiga Mama Fulani na zaune saman kujera tana watsar hakora Rukaiya da Maryam kuma na zaune a kujera daya ko wacce na duba wayar hannunta ala ala kowa waccensu take daya daga cikinsu ya ce yana sonta. Ganin Abbah tare da Ammy ya mugun batawa Mama Fulani rai, domin ita kwata kwata bata son yana kula Ammy da yayanta, sai dai kawai ya ji da ita da yayanta. Abbah ya zauna yana nunawa bakin nasa iyalansa sannan ya juyo yana fadawa Mama Fulani.

“Wannan Sunansa Amir saboda yana da sunan Mai Martaba da shi shiyasa ake ce masa Amir baya jin hausa sai faransanci da buzanci sai kuma English wanda shi gama duniya ne a yanzu, wannan kuma Sunansa Usman shi yana jin hausar”

Da turansanci Maryam ta shiga gaishe da Amir din da idonsa ke kan Zainab, ya amsa mata ita da Batula sai ya sake kallon Zainab wannan karon sai da suka hada ido. Da yaren faransanci Zainab ta gaishe shi sai ya amsa mata yana dariya tare da tambayarta wai ashe tana jin faransanci, sai tai dariya ta soma fada masa cewar ta yi karatu ne faransa ita da Batula, bakinciki kamar ya kashe Mama Fulani domin shi ma dayan ta lura Humaira yake kallo yana ta murmushi gashi ba ma wata kwaliya sukai kamar na yayanta ba.Bayan sun gama gaisawa ne sun fice Abbah ya kira wani daga kamfanin ya zo suka soma nuna masu yadda abubuwan suke, ba dan ba su sani ba sa dan kara tabbatar musu da komai a agabansu. Daga bisani suka fito domin zuwa ganin cikin Kamfanin, a lokacin ne Ammy da yaranta ita da Mama Fulani suka fito gaba dayansu suna musu sallama domin daga can ba za su koma ba zasu dawo nan ba. Usman ne ya ciro kudi mai yawa ua bawa Inteesar ya ce su raba, sannan ya ciro wasu ya bawa Ammy da Mama Fulani, Amir kan sai da ya shiga mota a side din da yasan Abbah ya ba zai hango su ya sauke gilashin motar yacs ta Zainab ta zagoyo cikin yaren faransanci sannan ya rufee glass din. Zagayowa tai kamar yadda ya bukata sai ya mata sallama sannan ya mika mata katinsa da kudi mai yawa wai su raba. Godiya tai masa sannan ta matsa baya dayan ya shiga mota Abbah yaje ya shiga tashi suka bar gidan.

“Kawo kudin nan?”

Mama Fulani ta fada rai a bace sam bata jidadin yadda ya kira Zainab ba.

“Batula karbi ki bata”

Ta fada tana mikawa Batula kudin kamin Batul ta karba suka fadi kasa bata tsaya komai ba ta juya zata tafi sai da Ammy ta daka mata tsawa.

“Zainab dawo ki dauki kudin nan ki bata”

Juyo tai ya dawo ta duka har kasa ta dauko su ta karaso gurin Mama Fulani ta mika mata. Wani bakin haushi Mama Fulani ta ji ganin kati a hannunn Zainab tasan bata shi yai.

“Wato rashin kunya za ki min ko? To bari ubanki ya dawo sai wani kadadi take jikinta na rawa wai ita ta ga maza”

Uffan Zainab bata ce mata ba, saboda Ammy na tsaye a gurin kuma ko ba komai tasan Mama Fulani matar mahaifinta ce be dace tai mata rashin kunya ba. Fisgar kudin Mama Fulani tai har kumbarta na yagar hannunn Zainab.

“Fitsararriyar yarinya marar tarbiya”

“Zainab tana da tarbiya Hajiya Fulani domin uba daya ya tarbiyantar da su”

Cewar Ammy cike da jin zafin yadda Mama Fulani take ma yarta tana jan hannun Inteesar su nufi part dinta, daman tuni Mama Fulani ta karbe kudin hannun Inteesar.

“To ai daman na san ke kike koya musu yadda za su min rashin kunya da rashin kamun kai an ga maza sai karkadi ake ba ko kunya”

Mama Fulani ta fada cikin daga sauti tana bin bayan Ammy da yayanta da harara. Kamin su juya su koma ciki Maryam uwar masifa bakinciki ya hana ta cewa komai domin ita kan ta kyasa da ganin Amir din.Sai da suka zauna a falo sannan Mama Fulani ta kallesu.

“Ku kuma kun wani cika hoda kamar aljanu ai dole ba za su ga yadda ainahin kyauku yake ba”

“Ba wani rashin ganin kyau wannan kwaliyar da ke maida mummuna mai kyau ma, kawai dai bakij asirin Ammy ne ba banza take ba rinsu ba, tun da dai ba kyau suka fi mu ba”

Cewar Maryam tana wani bata fuska tana cin magani. Rukaiya ta tsire baki.

“Haka fa ranar muka fita da Inteesar wani ya zo yana ta daukar mata kaya sai rawar kai yake, ga ni ni babban amman Wallahi ta Inteesar kawai yake har da wani cewa Antynmu za ki ba ni wannan? Sai da na ce masa Abbah mu fada yake idan yaga ma muna magana da maza sannan ya kama kansa”

“Waya sani ko asiri tai muku ma? Ni fa abun nan har mamaki yake ba ni da tsoro ga kunan Masha-Allah da ku amman ace babu wanda zai zo ya taya, idan an zo ba za a koma ba, sai wani jikon ke Maryam Kamal din nan ke kawai yake zuwa gurinki shima sai can ba a rasa ba yanzu kuma yana ganin wannan shegiyar yarinyar Ataa ya koma kanta har ta kai mu ga tsabani”

Maryam ta kalli Mama Fulani da ke zancen ta ce.

“Nima fa abun yana bani mamaki Wallahi, kin ga zata iya mana mu aki mu ita a so yayanta, ba ki ganin yadda Abbah yake rawar jiki da ita?”

“Ai ku ba ku san komai ba, ni nan na san komai lokacin da aka kawota tana amarya a gidan nan sai kun ga yadda Abbah ku yake rawar kai da ita, ina tunanin tun can gidansu aka shirya mata ko minene sai da na tashi tsaye sannan na samu yancina a gidan nan, amman barta ko yanzu ai ba zan zura muku ido ba, shekara nawa da kare makaranta kunan babu mai shinshini, amman ita ko jiya na ga Batula tana tadi da wani”

Mama Fulani na fadin haka Maryam ta tashi ta nufi upstairs cikin wani irin haushi abunda ya faru.ATAA POV.

Zaunawa nai kamar yadda Doc Bukar ya bukata shi kuma ya fice daga dakin. Fita Doc Bukar yai a dakin be dade ba ya dawo dauke da gorar ruwa da tissue ya miko min, karba nai na share magina da hawayena sannan ya bude gorar ya dauki kofi ya zuba ruwan mai sanyi ya ba ni, da na sha sai na ji wani sanyi a raina har an samu sauke ajiyar zuciya.

“A karo?”

Na girgiza masa kai alamar a a sai ya karbi kofin ya aje ya zauna a kujerar da Aliyu ya tashi yana kallona.

“Za mu iya magana?”

Na kalleshi tare da gyada masa kai ima ta shisshikar kuka.

“Siyarda kodar mahaifiyarki kika yi wa Aliyu ko?”

“A a cirewa yai da karfi shi da wani likita, cin amanata yai ya zalince ni”

“Kamar ya ba da saninki ba?”

A nan na labarta masa abunda ya faru tun daga kan saran macijin har kawowa yanzu. Tausayina ne ya bayyana a fuskarsa karara wayarsa na ringing ya ki ya daga sai kallon yadda na ke hawaye yake.

“Na san Doc Asim kwararen likita ne mai zaman kansa, kuma likita da zai iya komai saboda kudi, wata kila ya yaudare ki ne ya cire kodar ya siyar musu”

“Taya mutum zai siye koda be san mai ita ba? Taya?”

Na tambaya cikin kuka, sai dan risino kusa da ni yana kallona.

“Ba lallai ne sai Aliyu ya san da hakan ba, kuma ina tunanin idan Aliyu ya sani ba zai karyata ya ce miki be sani ba, domin na san Aliyu tun ba mu san kanmu ba, he's my childhood friend mun dade a tare, da ya sani zai amsa miki ya sani ko da kashe shi za'ayi, Aliyu mutum ne kai fi daya, idan yace maka yes go yes din ne ko dai ka yarda ko karka yarda”

“Wata kila ya yi hakan ne dan ya kare kansa”

Readers Also Read