Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 35
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 35: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 35. “Daman Daddyn su ne yace a fada miki kuma a nemi shawararki aji ta…
4,463 words
“Daman Daddyn su ne yace a fada miki kuma a nemi shawararki aji ta bakinki, wai yana son indai za ki amince sati na mai zuwa a daurawa Ataa aure da wanda take so ko waye ne, mun hanke wannan shawarar ne saboda hankalin kowa ya kwanta ita kanta hankalinta ya kwanta kin ga ko zuwa sallamar nan ba dadi ne ba, amman idan har aka mata auren dole kowa ya kama gabansa, kuma yi mata auren ba shi yake nufin hana ta karatunta ba no zata cigaba da karatunta a gidan mijin ko kuma a nan idan zai yarda”
“Sati daya?”
Nana ta nanata.
“Nima kaina naga kamar abun yayi wuri, sai dai saboda kwanciyar hankali kowa ake son ayi haka, ina son ki manta da duk abunda ya faru ki tambayi Ataa wanda take so idan a kusa ne sai neme shi idan kuma nesa ne sai a san ta yi tun wuri, idan kuma kina ganin watan yayi tsawo za ki iya fadar lokacin da kike son a saka, nan da wata daya biyu uku ko shekara ma ko fiye da haka”
“A a hukuncin da kuka yanke ya yi, waya sani ko zan kai gobe ma balle nan da wata daya ko shekara, fatar ko wace uwa ai yarta ta samu gurin zaman da ya dace da ita, Na gode sosai Hajiya”
“Karki jin kunya ko nauyin komai Wallahi duk wani abunda nai saboda Allah nai, dan haka karki taba kawo wani abu a ranki, ni da ke an zama yan'uwa kuma zan mata komai kamar yadda nai alkwari In-Sha-Allah, idan tarewar a nan kusa ne ko nesa duk daya ne a gurina”
“Allah ya saka da alheri”
Sosai Nana ta so tayi ma Momy maganar tashinta, sai kuma ta ji nauyi saboda girman Abunda Momy ta zo mata da shi, idan kuma tai mata maganar a yanzu wata kila ba zata fahimta ba, sai kawai ta zabi aje maganar a cikin har na wani lokaci.
ALIYU POV.
be Momy sun koma tare ba saboda yana jin zaman sokoto yana gundirarsa, abunda Rahma tai masa kadai ya isa ya saka shi jin baya son zama gidan da suka kasance suna rayuwa a ciki su biyu, ga kuma tunanin cewar Ataa ba zata zabe shi ba, so yana ganin kamar komawarsa sokoto karin bakinciki ne kawai a gurinsa bayan wanda na Mama Fulani take masa a nan. Domin Abbah ya fada mata matukar aka tambayi yarinya ta amsa musu da cewar tana sonsa za a daura masa aure da ita sati mai zuwa.
“Wallahi Aliyu ka ma ce ka fasa idan ba haka na zan yi wa yarinyar nan raashin mutunci, sai na sa ta raina kanta sai ta gwammace a haifo ta duniya ba, ba zan taba karbarta a matsayin suruka ba, na kuma zan taba son ta ba, kar kuma ta ce zata kira da wani sunan ko ta tako inda na ke, kuma idan aka daura auren nan sai na taka har sokoto na ciwa uwarta mutunci na ga wanda ya tsaya musu a garin sokoto, wai har da hada baki da Abbah kun ce sati daya ko? Saboda ayi saurin yin abun ai kana jin kasan yarinyar ba yar kowa bace kuma ba neman auren suke sun ga dan arziki, wai Aliyu baka ma kunyar ace yarinyar nan ce matar ka?”
Daga ita sai shi ne a dakinta take mishi wannan fada, sai ya shafa kansa ya ce.
“Ni kaina ban tsammaci haka ba Mama, amman ya za'ayi”
“Baka ma san abunda za'ayi ba kenan? Abunda za ayi kawai ka fasa auren yarinyar nan domin ko na aureta ba zan bari ku samu kwanciyar hankali ba, ga yan mata nan ai babban abunda za akayi ka bawa Rahma haushi a yanzu ka auro wanda ubanta ya fi uban Rahma arziki, amman ba yar bara a titi ba, bara fa Aliyu bara”
“To zan yi tunani Momy”
Shine kawai abunda ya fada mata ya tashi ya bar mata dakin saboda Maganganunta basa masa dadi, sam be son ya ji mai zagin Ataa a yanzu.
MUHSEEN POV.
tun bayan da yai maganar da Nana a waya ya zuba ido yana sauraren abunda zai faru, yasan indai tana da hankali da tunani ba zata bari yarta ta zaba tsakanin shi da Aliyu ba, da ace Aliyu ya samu shi ya rasa kara dai su rasa gaba daya, domin shi be ga ta inda zai rika kallon Ataa a matsayin matar Aliyu ba, a cikin Familyn a yanzu haka yana ganin kamar abu ne mai wahala ya ce zai samu wacce ta yi mishi ta kwanta masa a rai kamar Ataa, shi da ya dade yana burin auren mace da abokansa zasu susuce idan sun ganta kuma mai jini a jika kamar Ataa yanzu kuma ace Aliyu ne madadinsa, har ga Allah ya hakura da aurenta amman baya son Aliyu ya aureta kara dai ace bata cikin familynsu gaba daya. Tun daga ranar da ya bawa Momy hakuri be sake yarda sun yi ido biyu da Aliyu ba, kwata kwata baya shigowa gidan a lokacin da ya san Aliyu na cikin gidan, idan ya shigo yana part dinsa sai Aliyu ya fita sannan zai fito, dukan abunda kunnuwanta suke son ji wanda Ataa zata zaba, idan shi ne zai yi farinciki sai dai ya cire rai saboda ya san ba zata zabe shi ba kamar yadda yake ganin cewar ba zata taba zabar Aliyu ba.
ATAA POV.
wasa wasa akwa kwashe kwana biyu har uku Aliyu be dawo ba, ban kuma ji Momy na zancen dawowarsa ba, sai dai bana wasa da zuwa makaranta na da lokaci yayi rashin fara bokon kuma sai ya fara damuna wanda na san da Aliyu na nan da yanzu ya saka ni ko ya samu wanda zai saka ni, domin ina ganin sha'awar yadda Siyama ta ke shiryawa ta tafi makaranta da safe har jin na ke kamar na bita. Ranar Alhamis ranar da Momy ta cika kwana hudu da dawowa daga Abuja, Daddyn ya dawo da rana ya aiko Momy da kanta ta kira ni ni da Nana, tun daga lokacin da na ji kiran sai gana ya soma faduwa domin ina jin cewar zai tambayi idan na yanke shawara ne. A part dinsa muka taru gaba dayanmu har Momy da ni da Nana da kuma Daddyn kansa. Ni da Nana muka zauna kasa Momy kuma tana zaune a kujera daya da Daddy, babu yadda ba tai ba Nana ta tashi ta zauna saman kujera amman Nana ta ki. Bayan Daddy yayi gyaran murya ya soma magana da Nana kamin ni.
“Hajiya tace ta tatauna da ke akan maganar auren Aisha, kuma kim fahimta ina fatar ba mu danne miki hakki ko tauye ki a wani abun ba”
“Babu ko kadan”
“Mashallah, Aisha kwana ki na kiraki tun Hajiya bata nan na fada miki kije ki yi shawara ki fadi min kuma ki fadi a gaban kowa cewa ga wanda kike so, saboda kar ya zamana mun tauye miki hakki ko saka ki abunda be kamata ba ko kuma ba ki tashi ba a yanzu, dan haka muna saurarenki karki ji nauyin baki ko kunyar fadar komai ni na baki dama, idan ma ba ki da wanda kike so a yanzu ko kuma kina ganin kamar abun ya yi kusa za a iya daga miki kafa har zuwa lokacin da kike so”
Kasa cewa komai nai kaina yai mugun nauyi har ya sauko min ciki ido, gaba daya falon ji nai yana juyawa gabana ya shiga faduwa.
“Aisha... Ke mike saurare”
Ya maimaita jin na yi shiru har na wani lokaci, yawun bakina na hade ina da motsa yatsuna a cikin hijab.
“Yana da wahala ta iya furtawa, ba al'adar mu bace furtawa ka tsaye ka ce ga wanda kake so”
Momy ta fada, sai Daddy ya ce.
“Muhseen kike so?”
Na girgiza masa kai alamar a'a.
“Akwai wani wanda kike so ne?”
“Kamal kike so?”
Momy ta tambaya sai na girgiza mata kai a nan din ma ina hade yawu.
“Kina da wani wanda kike so ne?”
Na kasa cewa komai ko matsin sai na kasa yi.
“Aliyu kike so?”
Daddy ya tambaya. A take wata irin kunya da ban taba sanin ina da ita ba, ta rufe kai kasa da kaina gabana sai faduwa yake idonuwana suka cika da kwalla. Tasowa nai na baro musu falon da sauri kafafuwa har hadewa suke kamar za su tarde ni na fadi. Da gudu na nufi Bq na fada saman katifa na fashe da kuka na rashin dalili.
ALIYU POV.
Yana zaune falon Momy Husna ta kira, sai ya ki ya daga kasacewar yana cin abinci ne, after few minutes Amina da kira shi nan ma be daga ba sai da ya gama cin abincin, yana kokarin bulbula zuwa ya sha Maryam ta zo da waya ta miko masa wai Amina tana son magana da shi. Ya dade yana kallon wayar sannan ya karba ya kara a kunnesa yana kai ruwan a bakinsa.
“Ya Albishirinka....”
Shiru yai ya kasa cewa goro jinin zuciyarsa na gudu da sauri ya rika shan ruwa har kana jin wucewarsu a makoshinsa.
“Ataa ta ce kai take so kai kai kai”
Mikewa yai tsaye da sauri sai sa ruwan da ke bakinsa suka tsarke shi a take ya fara tari a gurin. Ya sauke wayar ya kalla ya sake maida a kunnensa.
“Say it again....”
“Ataa tace kai ta ke so, kuma mamanta ta yarda a daura auren wannan week din”
Bude baki yai kamar zai yi magana sai kuma ya kasa, ya mikawa Maryam wayar ya shafa kansa ha zauna da sauri yana da mamaki, before yai sujada a gurin yana ma Allah godiya, then ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya nufi motarsa Nasir ya kira ya fara labarta masa abunda ya faru. Sai shafa kansa yake yana ganin kamar ba gaske ba, ko da ma tirsasata akai a gurinsa ba komai ba ne zai iya kula da ita. Ba shi da wanda zai taya shi murna a nan daga Mama Fulani har Muhseen and he don't want to celebrate it with Ammy saboda kar Mama Fulani ta ji haushi.
“Nasir za a samu jirgi yanzu?”
Ya tambaya with full farincikin a ransa da jikinsa da ruhinsa.
“I don't think so amman bari na kira na ji”
“Now pls”
Kamin Nasir ya kira ya fada masa cewar babu jirgin yau sai dai gobe har ya matsu. Haka nan kawai farinciki ya saka shi shiga mota ya zaga garin Abuja da kewaye sai murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin farinciki da jindadi. A gangan ya ki dawowa gida gurin Mama Fulani ranar dan baya son ta bata masa farinciki a yau. Da dare ya kira Momy baki har kunne ta kara tabbarta masa da hakan. Kasa kwana yai a daren saboda farinciki yana ta ganin Ataa a fuskarsa, kamin gari ya waye duk ya matsu. Tun 7 ya isa airport bayan jirginsu sai 10 zai tashi, a gurin Nasir ya same shi ya taya shi murna haka yai ta kira har ten sannan jirginsu ya tashi. Na dade ina kukan har na shigo ta same ni a dakin, hankalinta ya tashi sosai ganin kukan nawa ba na wasa ba ne.
“Lafiya Ataa?”
Tashi nai zaune Ni kaina ba zan iya fadar dalililin kukanawa ba, sai dai na kasa daina hawaye ina jin wani bakon yanayi na rabata har yanzu na kasa daina jin nauyin a kaina da kuma zuciyata ban taba sanin cewar haka ake ji ba ko kuwa dai ni na ji haka Saboda ban saba ba abun ya zamo min bakon al'amari?
“Ba kya son shi?”
Na kasa cewa komai.
“Karki cuci kanki Ataa idan ba ki son shi ki fada na san yadda ake idan aka gabatar maka da wanda baka so, karki cutar da kan ki”
“Ni ma ban san dalilin kukan ba, amman har ga bana jin wani kwankwanton ko tatamar zabar Aliyu da yai”
Har lokacin da na ke maganar hawaye be daina sauko min ba. Murmushi Nana tai ta kai hannunta ta share min hawayen fuskata.
“Ina fatar mijinki ne na har abada, kuma ina fatar zabin Aliyu ya zame miki alheri a rayuwarki, rayuwar da na ke miki fatan samu ina fatar ita ce a yanzu take rabarki, kuma fatar wannan zabin da kika yi ba zai raba kan iyalan gidan nan ba”
A cikin raina na amsa da amin sannan na kwantar da kaina jikinta. Na kara fashewa da kukan, sai da nai mai isata na samu natsuwar ruhi da zuciya sannan na tashi na shirya na wuce makarantar islamiya, yau a inda na zauna jiya na zauna kusa da wata budurwa mai far'a wacce na zauna da ita jiya, sosai na maida hankalina gurin karatu amman na kasa karanta komai sai tunanin abunda ya faru nake har aka kusa ta shi.
“Yau ba za ki biya ba?”
Na dago daga tunanin da nake na kalleta.
“Zan biya”
“Na ga an kusa tashi ne, ban ma san sunanki ba”
“Sunana Aisha”
“Okay ni kuma sunana Asma'u”
“Kai ashe ke mamana ce”
“Ina da sunan Mama kenan?”
“Eh sunan Mamana ne”
“Eyee daga yau Mama zaki rika ce min”
Na yi murmushi tare da tashi na nufi gurin da malamin yake zaune ana biyawa, na biya harufan da na iya ya kara min wani na taso na dawo inda na ke ma zauna sai yarinyar ta ba ni yasin kanzo wai ko ina so, rai na biya dan haka na karba ina lasawa na ji yaji kamar zan hauka ce da sauri na mika mata ragowar ina fiddo halshena waje ,sai ta saka min dariya ita da wata yarinya da ke gefenta.
“Aisha Aliyu ta so ana kiranki”
Malamin nan da Aliyu ya danka ni hannunsa ranar ne ya shigo yana fadin hakan, ni kuma ban kula ba domin ban dauka da ni yake ba duk kuwa da kasancewar ni yake kallo kuma na san gurin saka sunan form din daya tambayi ni Aisha Umar na fada masa.
“Aisha Aliyu”
Ya maimaita yana kallona sai na nuna kaina.
“Ni...?”
“Eh ta so ana kiranki”
Na tashi ina ta tandar baki saboda yajin na fito na biyo bayan malamin sai ya juyo ya ce min.
“Dauko littafanki?”
Ba musu na juya na je na dauko na biho bayansa, ina ta mamakin dalilin kirana Aisha Aliyu da yai.
“Kije waje ana jiranki”
Na nufi gate din cike da tunanin mai kiran nawa a wannan lokacin da ba a tashi a makaranta ba. Ina fitowa ya hango Aliyu jikin motarsa sanye da kakanan kaya yana kallon inda na ke tsaye da alama daman ni yake jiran na karaso, wani irin tattausan murmushi da ban taba sanin yana tare da shi ba ya rika aiko min yana min wani irin kallo mai wuyar fassara, yayi masifar kyau saboda Murmushin ya kawata fuskarsa har sai da ya saka gaba faduwa, kasa karasawa nai a na tsaya a gurin gate din ina kallonsa sai ya gyara tsayuwarsa ya rumgume hannayensa a kirji yana ta kallona kamar zai cinye ni, daga bisani ya dago daga jikin motar ya daso inda na ke, kamin ya karaso nai kasa da kaina kunyarsa ta rufe kamshin turarensa kuma ya zagaye ni siffar zatinsa ta hana ni sukuni. Hannu ya miko min na san be saba taba ni ba dan haka na mika masa littafan hannuna sai yai gaba ya bar a gurin, sai da ya isa gurun motar ya bude front ya juyo ya kalleni sannan na fara takawa da sauri gudun kar wani ya fito ya hango mu daga dalibai ko malaman makarantar. Ina isa na shiga na zauna sai ya rufe motar ya bude gidan baya ya saka littafan nawa ya zagayo mazaunin direba ya shiga yai mata keys muka hau babban titin unguwar, na yi zaton ko gida zai maida sai na ga mun wuce hanyar gida sai tafiya yake da ni, ni ko sai tandar baki na ke saboda yajin da na ke ji tun ina yi a hankali har sautin ya fara fitowa, da sauri ya maido da hankalinsa gurina kamar ba tukin mota yake ba ko kuma na ce ba a kan titi mike ba.
“Kin ji ciwo ne?”
Na kasa magana.
“Ko yaji kika ci?”
Na gyada masa kai alamar eh, sai ya faka motarsa gefen titi ya fita daga motar ya tsallaka titi ya shiga wani shagon be dade ba ya fito rike da leda ya dawo cikin motar, da kansa ya bude ledar ya fiddo gorar ruwan mai sanyi ya bude ta ya miko min.
“Na goge”
Na fada ina kokarin karbar ruwan, sai ya saka min murmushi as respond ya kai ruwan a bakina na sha ka dan na rike sauran.
“Sun ishe ki?”
Ya tambaya yana ta kallona kamar mai kula da yadda na ke shan ruwa, sai na gyada masa kai hannunsa ya kai ya karbi ruwan ya tashi motar da hannunaa daya dayan hannun kuma yana kurba ruwan. Yawo ya rika yi da ni a cikin garin sokoto wasu unguwannin na sansu wasu kuma ban sani ba, ni dai ban tambaye shi inda za muje ba nawa idone kawai. Sai da muka yi nisa sosai sannan ya faka motarsa gefen titi ya kwantar da kujerarsa ya juyo da fuskarsa gafena yana kallona, na yi zaton wani abun zai yi ko ya ce sai na ji shiru be ce min komai sai idonsa da ya tsare da su, mi kuma na kasa daga kaina na kallin gefen da yake ma balle kuma na iya hadu ido da shi.
“Ki yi hakurina da kallona, yau ji na ke kamar na hade ki ji na ke kamar na bude miki zuciyata ki shige na rufe, ji na ke kamar a cikin jinina aka halittoki, komai ya zo min a babin da ban yi zato ba, ban san wace karmar zan fada da zata gamsar da ke irin kaunar ki da na ji a raina ba”
Ji nai kaina yayi mugun girma, ban tana jin kunyar Aliyu kamar na yau ba, ban taba jin wani kalami mai girma daga bakinsa kamar wannan ba, bayan wacan furucin da yai min yau ma ya kara min wani wanda ke dora wacan a babin da zai tabbatar da wacan zancen na farko, a wacan karon na yi zaton yana rokona ne saboda kare Momy da son cika mata burinta, sai dai kalaman da yai min a yanzu da irin shaukin da yake ya sauya tunani na.
“Kar a tashi makaranta.....”
Na fada numfashi na fita daker kamar wacce aka taushewa zuciya.
“Na fadawa Malamin ku gida zan kai ki fita za ku yi da Momy”
“Amman yanzu an kusa tashi ai....”
Na furta still numfashin nawa na gargada, sai ya sake dauko ruwan da ke tsakanin ni da shi ya bude robar ruwan ya miko min.
“Sha”
Na karba da sauri na kai robar ruwan a bakina ina ta sha kamar ba zan daina ba har sai da na soma tsarkewa sai yai saurin rike robar ya ciro tissue ya mikon.
“Sannu”
Na karba na goge ruwan da suka zuba jikin hijab dina sannan ta zuke gulashin motar na wurgar da shi waje, gaba daya na tsawwala ina ta jin motar ta mana kada kuma kunyarsa ta rufe duk na bi na rude. Shi kanshi ya lura da hakan, sai ya gyara kujerar ya soma toka motar muka hau titi. Kadan kadan yake tukin har muka isa gida, a bakin gate din ya faka motarsa, ya bude motar ya fita ya zagoyo gefena ya bude min motar
“Babyna fito ki shiga gida”
Na san ma'anar Baby yana nufin jaririya mace, wato yana nufin ni jaririyarsa ce kenan. Na fito daga motar kaina a kasa sai da ya rufe motar sannan ya bude gidan baya ya dauko min tittafaina ya mika min sai da na mika hannuna an karba sai yaki saki
“Thank you so much Love, kin cece ni na zan tana manta wannan alfarmar ba, kin cancanci komai daga gareni I love you so much”
Har zan sakar masa littafan sai yai saurin sakar min ya tsaya yana kallona har na shige cikin gidan. Ban taba dawowa a irin wannan lokacin ba ana ciran sallah magariba, idan ma Nana ta tambaye ni ban san mi zan ce mata ba. Ina shiga bq din sai na samu Nana bata nan sai dai dakin a bude yake cikina na shiga na cire uniform dina ya shiga bandaki nai alwala, ina cikin Sallah Nana ga shigo dakin ita ma ta wuce bandakin tai alwala ko da ta fito na sallame ina tasbihi da hannuna.
“Tun dazun kika dawo ko? Daman Hajiya ta ce kila ma kin dawo kika zauna a dakin ke kadai kina jin kunyar shigowa bangarenta”
Na yi murmushi cike da jindadi domin na san idan ta san na kai magariba dole ta tambaya abunda ya tsayar da ni kuma ban san abunda zan ce mata ba.
“Hajiya ce ta aiko aka kiranin na je can muka yi hira wai na daina zama ni kadai a nan”
“Allah sarki Momy ai tana da kirki”
“Tana da kirki sosai kam, kin yi dacen suruka indai abun ya bi haka”
Wata kunyar ce ta rufe ni ban taba tsammanin idan na yi wa mutun irin wannan maganar kunya tana rufe ba duk kuwa da kasancewar uwata ce amman na ji kunyarta sosai.
ALIYU POV.
ido ya kura mata yana ta kallon tafiyarta har ta shige ciki, wani irin abun yake ji marar misaltuwa lallai ya yarda kuma ya tabbatar a yanzu kam yana son Ataa so ba na wasa ba. Motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansa, sai da ya shiga ya faka motarsa sannan ya fito ya doshi masallacin unguwar yai gabatar da sallah magariba da ya fito sai ya tsaya bakin masallacin sai da liman ya fito sannan ya yai saurin taronsa ya mika masa hannu suka gaisa.
“Ah Alh Aliyu ya gida ya aiki”
Haka yake kiransa Alhaji Aliyu ba dan komai sai dan tarin dukiyar dake saka kowa ganin kimarsa da jin kunyar kiran sunansa kai tsaye.
“Al-hamdulillah”
Aliyu ya amsa sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro duka kudin aljihu da na Wallet dinsa ya mikawa liman din.
“Dan Allah amin sadaka da wannan a bawa mabukata”
Da hannu biyu liman ya karba yana bude baki cikin tsananin mamaki domin ba kasafai Aliyi ma ya cika tsayawa ya gaisa da mutane ba balle kuma har ya mika wani abun da sunan taimako.
“Masha-Allah Mashallah, Allah ya saka da alheri Alhaji Aliyu Allah ya biya bukata ya kara bude ya sakawa rayuwa albarka, Wallahi ka taimaka a wannan hali da mutane suke ciki ai taimakon ake bukata ta ko'ina”
Har cikin ransa ya jidadin addu'ar liman after Momy dake masa addu'a kullum sai kuma Nana da ta taba masa a asibiti yau ma an sake masa, duka biyu kuma sanadin taimako ne ta uwa kuma ta kauna ce, sai ya ji natsuwa da kwanciyar hankali sun rabi ruhinsa. Cikin gidansa ya koma ya bude freezer ya dauko ruwa ya sha kadan ya aje sauran ya dawo saman cushion ya kwanta kamar wani sabon ango haka yake jin kansa gaba daya ya manta da komai da ke tare da shi Ataa kawai yake gani da kuma irin rayuwar da zai yi da ita, lokaci zuwa lokaci yake murmushi yana shafa kansa da fuskarsa, har mamakin yadda farinciki ya cika masa zuciya yake. He don't think zai iya biyewa Momy ko wani ma cewar after aurensu za tai karatu shi ji yake kamar kar kowa ma ya kara ganinta daga yanzu, he i can't wait ya ga ta zama halalinsa ta yadda zai rumgumeta a kirjinsa ya sumbace ta. Tashi yai zaune ya nufi dakinsa ya doro wata alwalar ya fito ya nufi masallacin dazun yai sallah, mutane sai kallonsa ake ko zai sake rabawa wasu kuma dan ya san da su, har da masu ba shi hannu ya gaisa da su, a da he can't shake his hand with anyone indai talaka ne amman a yanzu sai mika musu hannunsa yake suna gaisawa kamar ya manta waye shi.
Yana shigowa gida ya sake shiga dakinsa ya dauko wasu kudin ya saka aljihunsa sannan ya fito ya shiga motarsa horn daya aka bude masa gate sai ya tsaya daidai gurin mai gadin ya ciro kudin da za su kai eight to nine thousand ya mika masa, a take mai gadin ya washe baki ya fara zuba masa addu'a shi kan be shi ta kansa ba ya dauki hanyar gidansu Momy. Har ya faka motarsa bq din su Ataa yake kallo ji yake kamar ta leko ya ganta, ya dauki lokaci a haka sannan ya bude motar ya fita ya shiga part din Momy sai wagen bq din yake kmar ance masa fitowa za tai. Hannu ya kai ya tura kofar falon ya shiga fuskarsa da murmushi kamar ba shi ba, duka suna zaune falon suna ci abinci a plate daya da Momy, Amina Siyama da kuma Husna. Tuwon shimkafa ne miyar kuka da man shanu sai kamshi yake. Suna kallonsa ya sakar musu murmushin farinciki, Momy ta ce.
“Ai na dauka ka bata a jirgin ne, tun safe ba a samun wayarka kuma ba ka shigo ba”
Sai yanzu ya tuna wayarsa a flight mode take. Zauna yai a kujera yana dariya.
“Momy kin san me Wallahi na manta sam wayata a flight mode take kuma ban cire ba, kuma da wani dan abun ne ya rike ni bayan na sauka a nan”
Da dai daya kannensa suka rika mika masa gaisuwa yana amsa musu, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ma su yawa ya mikawa Amina.
“Gashi nan ku raba”
Ya sake saka hannunsa ya ciro wasu kudin ya mikawa Siyama.
“Idan kin gama cin abinci ki kawai mai gadi”
“Wow Ya Aliyu na cikin farinciki ni na maka albishir fa”
“Thank you Husna i love you”
Ya fada yana murmushi.
“I love you too Yayana”
Sannan ya kalli Momy ya ce.
“Thank You Momy”
“For what?”
“For everything”
Murmushi tai ta cigaba da cin tuwonta.
“A zubo maka?”
“No Wallahi bana iya cin komai tun jiya da aka fada min har yau bana jin yunwa”
“Taf to Yayana idan aka daura maka aure fa”
Husna ta fada. Dariya yai ya kwantar da kansa jikin kujerar domin ba zai iya fadar abunda yake ji a yanzu ba ma balle kuma idan ta zama halilinsa.
“Momy wannan Assabar din ne ko?”
Momy ta kalli Siyama tana bata amsa.
“Eh In-Sha-Allah”
“Amman ba yi ai iv ba ko sai gobe gobe fa Friday?”
“Ni ko mutun biyar suka daura min aure ya wadatar ni dai a daura din kawai dai shine matsalata”