Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 36
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 36: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 36. Ya fada kai tsaye a gaban Momy. Yadda take ganin Aliyu yana nuna…
4,486 words
Ya fada kai tsaye a gaban Momy. Yadda take ganin Aliyu yana nuna son Ataa daga lokacin da tai masa maganarta zuwa yau kamar wanda be taba aure ba aka hada shi da wace yake so kuma a dauke masa yin komai haka yake. Misalin takwas Daddy ya dawo, bayan ya shiga part dinsa ya huta Momy ta kai masa abinci y ci sai Aliyu ga shiga gaishe shi, nan ma fuskarsa da Murmushi tana nuna farincikin da yake ciki.
“To sai ka rike yar mutane da amana kuma kai adalci dan kasan ba ita kadai ce ba, kar son wata ya saka ka danne hakkin wata ko nunawa ta kiyayya, ka ji tsoro Allah”
“Na gode sosai Daddy In-Sha-Allah Allah zaka same mi mai adalci da rike amana”
“Allah ya hada kanki ya kawarda fitini kuma ya ba ku zama lafiya”
“Amin”
Ya amsa sannan ya taso ya dawo part din Momy, sai kusan sha biyu dare ya bar gidan a harabar gidan ya tsaya ya dade yana kallon bq sannan na koma gida, da farinciki ya kwana ya tashi ya kuma dawo gidan Momy, duk yadda ya so ya saka Ataa a ido yau be saka ta kasacewar islmiya kuma ta labe a bq abunta ta ki fitowa. Haka ya sake wuni a gidan domin ba shi da inda ya fi nan, ga zuciyarsa kuma ta kwadaitu da son ganin Ataa kamar wanda be taba ganinta ba. After sallah isha'i Daddy ya dawo, ko hutawa be yi ba ya kira Aliyu a waya ya fada masa yana son ganinsa, a natse suka gaisa da Abbah before ya dora da.
“A masallacin juma'a na Muhammadu Maccido da ke amir yahaya za a daura auren, dazun muke magana da Alhaji Sulaiman na fada masa tun da ba gayyato mutane za'ayi sosai ba kara a daura auren a friday kawai a huta”
“Daddy gobe Friday fa?”
A rikice Aliyu ya fada yana kallon Daddy da wani irin farinciki marar misaltuwa.
“Yes”
“Daddy thank you so much Allah ya saka musu da alheri”
“Amin”
Daddyn ya amsa yana bude jaridar hannunsa. Daga haka ya taso ya dawo part din Momy, sai murna ta kaure a falon shi da kanensa da Momy domin suna son farincin dan'uwansu duk kuwa da irin hade musu fuska da yake sai dai sun san yana son su kuma yana musu duk abunda zai saka su farinciki. Be bar gidan ba sai kusan goma na dare, har ya isa gida zuciyarsa bata daina zumudi da son ganin Ataa ba, ji yake kamar ya hanyo goben ya matso da ita ta zama yau ma a daura musu auren tun a yau ba sai gobe ba. Sai da ya huta ya sha Lipton sannan ya kira Nasir na sanar da shi komai kuma ya fadawa Nasir da sanar da wasu friends dinsa, shi kuma ya turawa wasu da kansa a take aka fara kiran wayarsa kowa ya ji abun daga sama. A cikin daren Aliyu ya sake buga wayar Nasir ya fada masa ya idan zai zo dauren auren ya zo masa da expensive ready-made da shoes da cap, yana da sabbin tufafi a nan wadanda be tana sakawa ba, amman ya fi son yai siyo wasu saboda dalili zai jindadi da natsuwa.
MUHSEEN POV.
Ji yai kamar ya rumtse ido ya bude ya ga komai na duniyar nan ya tarwatse cikin kuwa har da auren da Aliyu da Ataa da jin labarin na hana shi sukuni da walwala, wani irin bugawa zuciyarsa take da ace akwai abunda zai yi ya hama faruwar auren a yanzu da yayi, domin sai a yanzu yake jin cewar yayi ganganci kuma yayi sake na saurin sakarwa Aliyu ragama. He can't believe ya rasa Ataa kenan har a bada, taya zai rika kallonta a matsayin matar Aliyu a cikin familynsu?
“Be ma kamata tun farko nai hakan ba, shikenan shi ya samu kyakkyawa kuma wacce na ke so, ya ji dadin kara fadin rai”
Ya fada yana wulgar da kofin tangaran din dake hannunsa a take kofin ya fashe. Wani irin fushi da bakinciki yake ji marar misaltuwa kamar ya haukace yake jin kansa gaba daya ya kasa natsuwa ya saka sukuni.
Ta bangare Mama Fulani ma fada kawai take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa zata shirya taje sokoto sai da Abbah ya taka mata burki, gaba daya ta hana kowa zama lafiya ciki kuwa yar da yayanta haushin auren da zaba daura gobe ya addabi zuciyarta. Ammy ce kawai da yayanta suke murnar abun domin ta san cewar Ataa ta samu mijin daya dace da ita kuma wanda zai kula da ita, abun har mamaki yake ba su yadda Aliyu ya fada son Ataa a haka, a daren ita da yayanta kwana sukai suna ta zancen masu cewa daman sun lura da kaza da kaza suna ta yi.
ATAA POV.
Na kwana da tunanin Aliyu mamakin kalamansa har suka saka ni murmushi ni kadai, washe garin ranar da gagan na ki fita ko'ina saboda kar Aliyu ya gan ni ko kuma ni na ganshi abinci mu da komai Momy aiko mana tai kamar yadda ta saba ko da yake wani lokacin ta kan aiko tace na zo na dauka. Ban wani ci abinci sosai ba na kwanta, sai Momy ta aiko tana kiran Nana, ni dai ban san lokacin da ta dawo ba domin bachi yayi gaba da ni, washe gari bayan na yi sallah asuba na zauna sai da rana ta fito sannan na nufi nufi part din Momy, wani abun mamaki sai na samu kaina da kasa shiga ciki, sai kawai na juyo na dawo kamin na karasa motar Aliyu ta shigo harabar gidan yana sauri ya fito daga motar yai min magana ni kuma yai sauri har da hadawa da gudu na shige cikin bq din. Ban fadawa Nana komai ba sai dai tana ganina ta san ban shiga part din ba domin ban isa ace na shiga har na yi sharar na fito ba. Amina ce ta kawo mana abun karyawa a maimakon Siyama wacce ta saba kowa mana, sai da ta gaisa da Nana sannan ta fada min cewar idan na gama karyarwa na shirya zamu je gidan wata Hajiya Ramatu kawar Momy wai a can za mu yuni. Ina ta mamakin fita da safe haka kuma wai mu wuni a can amman kuma ta taimaka min ko ba komai bana son haduwa da Aliyu a yanzu gashi yau friday kamar jiya ba zuwa makaranta ake ba. Misalin goma da yan mintuna mu kabar gidan a lokacin har na fara ganin bakin fuska a gidan cikin kuwa har da abokinsa Nasir. A gidan Hajiya Ramatu muka wuni ni da Amina wanda ban san dalilin hakan ba, kuma na kasa natsuwa saboda jefi jefi sai Hajiyar ta kira ni Amarya sai murna take da alama itama tana son auren kamar yadda aminiyarta Momy take so. Bayan gama sallah azahar ina zaune ina kallon arewa24 suna kokarin karkare wani shirin hausa mata da miji Amina da shigo da waina a a plate da miya ta aje min
“Gashi nan ki ci wainar daurin aurenki yau an daura miki aure Ataa igiya uku ta hau kan ki, Kin zama Mrs Aliyu Aliyu......”
Kamar wacce ta fara ji a yau haka na ji maganar wani kallo na ke mata da ke nuna cewar sam ban fahimci inda zancen ta ya dosa ba, sai ta kama kumatuna ra ja.
“Seriously yau friday aka daura aurenk after Jumma'at prayer congratulations you're now our sister-in-law”
Ta fada ta rumgume ni cike da murna. Ni dai daga turanci da bana ji har hausar ban iya gane komai ba domin a rikece na ke.
Sorry two days ina post a night 😑🙏
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660* Ba kowa da kowa aka gayyato a gurin daurin auren ba, sai makusantan Aliyu ciki kuwa har da abokansa duk kuwa da wasu ba su samu zuwa ba bikin ba kawai sun samu sakon ne daga Aliyu wasu kuma daga Nasir gashi lokaci ya kure ba su samu zuwa ba. Sun samu addu'a sosai albarka jama'a kasancewar massallacin juma'a kuma babban masallaci wanda mutake ke taruwa sosai bayan daura auren nasa aka daura na wasu mutanen biyu. A cikin mutanen da suka samu halartar daurin auren har da Kamal wanda Nasir ya sanar da shi amadadin Aliyu, baya farinciki da auren Aliyu da Ataa sai dai kuma baya bakinciki, domin ya san daman Aliyu yana son ta kuma tunda aka ce tana gidansu daman yasan tsakanin Muhseen da Aliyu dole sai ta auri daya. He know what he did to Mama Fulani be kyauta ba, Mahaifiyarsa ma ta masa fada akan hakan kasancewar Mama Fulani kawarta ce kuma makociyarsu bugu da kari kuma mahaifiyar Aliyu domin kamar uwa take a gurinsa. Daman yana neman hanyar da zai shirya da abokinsa kuma ya bashi hakuri kan abunda ya faru, sai dai ba zai iya iya kiran Aliyu kai tsaye ba sanin halinsa na wulakanci zai iya neman ya wulakanta shi ganin ya kawo kansa da kansa kamar yadda yake ganin Mama Fulani ma zata iya masa. But sanar da shi da Nasir yai cewar Aliyu yana gayyatarsa dauren aurensa ya sa bari duk wani aiki da yake da shi a ranar friday din ya halarci daurin auren, yana ga jin kamar ace shi ne ya auri Ataa. After daurin auren aka wuce shukura hotel aka ci abinci mai kyau drinks ma sai wanda ran mutum ke so. Ango ya sha kyau shaddar jikinaa ai wani haske take yana wani maiko kana gani ka san shaddar masu naira ce, ko masu nairan ba kananan ba, farar shadda ce wacce ta sha aiki, ga wasu expensive shoes da be taba zuba zuba kudi mai yawa ya siye takalmin da suka kai wadanda Nasir ya zo nasa da su daga Abuja tsada ba, hular kansa kadai tana siyen tufafin wani mai kudin kala goma. Zuciyar Aliyu kal ransa fes kamar babu abunda ya taba bata masa rai a duniya, wasu family friends dinsa har mamakin yadda ya sake da mutane yake ta dariya suke domin sun san ba halin Aliyu ba ne. Amman sai dariya yake baki har kunnuwa yadda yai muran da zuwan Kamal sai ka dauka ma wani abu be shiga tsakaninsu ba, farinciki aure ya saka ya manta da komai. After lunch a hotel wasu suka kama hanyar Abuja wandan suka zo daga can ciki kuwa har da Abbah da wasu aminansa, yan wasu garuruwan ma suka kama hanya, har da yan Yola wato yan uwan Mama Fulani domin sun san Aliyu dan Mama Fulani ne sai dai Abbah ne ya sanar da su ba Mama Fulani ba, har da kanen Ammy biyu da goma suke Kaduna sai da suka zo. Momy tana gida tana fama da nata Familyn da kuma Familyn Daddy ana ta wasa da dariya sai tsarguwar juna suke ita da tabasanta da kuma tabansan Daddy, abun gwanin burgewa, Husna da Siyama da wasu cousins dinsu mata su suke rabawa baki abincin, a gidan an yi jalof din shimkafa da kuskus, fried rice, waina da kuma tuwan shimkafa. And su snacks cake da donuts. Drinks ko tun daga na zobo kunun aya, kunun waken suya, ginger da na waje babu kalar da babu, daga Candy Restaurant Momy tai order komai, sai ka dauka ma wunin biki ake ba wai daurin aure ne kawai ba. Yadda aka taru abun har Mamaki ya bawa Momy domin wasu dai bata san ta fada musu ba, musamman ma matan da suka zo na zaton ko har da wunin bikin ne. Komai na Nana Momy ware mata tai ta aika mata a bangarenta. Sai kusan magariba Momy ta samu kanta, daman wasu daga familynsa da suka so yan matan sun ce a nan za su kwana, Husna da Siyama sai labari ake yana jindadi an hadu da yan'uwa, Amina ce kawai bata nan kowa sai tambayarta yake sai a fada musu tana can tare da Amarya, sai dai ba a fada musu inda Amarya take saboda Momy ta fadawa su Husna da Siyama cewar bata son a damu Ataa domin bata san da daurin auren yau ba kuma bata saba ba, ba karamin aikinta ne ba ta sakawa mutane kuka.
ALIYU POV.
Da kansa ya raka wasu friends dinsa airport yana ta musu godiya cikinsu kuwa har da Kamal, sai dai ya kasa sakewa yana ta jin kunyar Aliyu har sai da ya ga Aliyun ha wayance kamar ba shi ba, ko kuma ya manta da abunda ya faru sannan shi ma ya saki jikinsa har yai ma Aliyun sallama su kai shaking hands. A hanyar su ta dawo gida tare da Nasir yake driving yana sokonar Aliyu.
“An daura auren nan dai hankali ya kwanta”
“Wallahi kuwa yanzu hankalina a kwance yake fes ba ni da wata matsala malam”
“Ango ango angon da ba Amarya”
“Inji uban wa?”
Nasir ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya wacce ta saka Aliyu da kansa shi ma ya dara.
“Ai kasan dai Momy ba zata baka amarya nan yanzu ba ko? Sai ta girma”
“Girma? Ta girma a gidana na yarda dai ba zata tare a yau ba”
“Kuma daidai ne ace yadda ka sha shaddar nan ajima a kai maka amaryar ka”
“Na rantse da Allah kau, Nasir kai mugu ne Wallahi”
Nasir din ya sake saka masa dariya har da buga sitarin motar. Aliyu yai murmushi yana cire hularsa ya shafa kansa, sai a yanzu yake jin cewar lallai yayi dacen auren Ataa daman yana son yan latsu wato karamar yarinya kamarta wance bata iya komai bata san komai ba bata waye ba a komai ba, kuma bata taba soyayya ba, he know littafinsa ne zai bude a kwakwaltar da kuma zuciyata domin ya san duk abunda ya koya mata shi zata haddace ya zauna a kanta. A harabar gidansu Momy Nasir ya faka motarsa ya riga Aliyu fita ya shiga ciki domin gaisawa da Momy daman tun da ya diro garin be leko nan ba, kai tsaye na nufi gurin abokinsa, daga can suka nufi gurin daurin aure kamin su soma hidimar abokansu. Aliyu na kokarin fita motar wayarsa tai vibration alamar kira, ciro wayar yai daga aljihunsa sai ya ga bakuwar number yar waje saman screen din wayar na nuna masa ana masa kiran ne daga Dubai. Kai tsaye ya fahimci cewar mai kiran tasa ba kowa ba ce face Rahma. Murmushi yai ya danna picking ya kafa wayar a kunne.
“Hello Dear ya Dubai? Hope hutun yayi miki dadi?”
“Aliyu ka yi aure?”
Ta tambaya a sanyaye gabanta sai faduwa yake tana son ya amsa mata da capital NO.
“Yes Yau din nan aka kara dora min wani nauyi da kuma hakki, daraja ta ta dagu daga mai mata daya zuwa biyu”
“Aliyu?”
“Ana wasa da aure ne Rahma? Ai kin san ko zan miki wasa da komai ban da aure ko?”
“Aliyu ina nufin aure na sunna a daura maka irin wanda aka mana”
“Irin shi akai mana da kanwarki Aisha a yau”
“Aure fa Aliyu? Wallahi ka ci amanata ka cuce ni Aliyu ba zan taba yafe maka ba, tun ina da rai zaka fara nuna min hakinka ba ma sai na mutu ba?”
“Wacce zata iya zaman aure ta kula da mijinki kawai na aura”
Ta tsinke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba shi kuma ya maida wayar aljihu ya nufi cikin gida. Yana shiga wasa da dariya zoyata tsakaninsa da tabansansa ya tashi sai dai duk yadda suka tsarge shi sai dai yai dan murmushi baya cewa komai, daman can haka yake indai ya hadu da abokan wasa sai dai yai murmushi ko yar dariya kadan idan akai wani abun. After sallah magariba Nasir ya shiga gari domin ganawa da wasu friends dinsa. Aliyu kuma yana gida gurin Momy sai tunanin inda aka kai Ataa yake, domin ita kadai ce abunda idonsa ke son gani a yanzu, muradin zuciyarsa. Amman baya jin zai iya tambayar kowa ina Ataa ai da kunya. Sai dai ya duba yaga duka sisters dinsa suna nan ban da Amina dan haka ya tambaya.
“Ina Amina?”
“Wai tana can tare da Amarya yau duk abunda akai ba da ita akai ba”
Wata cousin sister dinsa ta fada, a take ya mike tsaye ya fito harabar gidan ya kira Amina.
“Hello Ya Aliyu”
“Kina ina?”
“Ina ina ina kebbi”
“Wasa na ke da ke?”
“Ya ina sama road”
“Ni da Ataa”
“Aisha... Anty Aisha”
Ta kara da Anty gaba daya. Ya san mutane biyu ne a sama road Mama Zuwaira wato kanwar Momy sai kuma Aminiyarta Hajiya Ramatu.
“Gidan wa?”
“Idan Mama Ramatu, amman Momy ta ce karna fadawa kowa inda muke har da kai”
Ya katse wayar ya ya koma cikin falon dan karbo keys din motar Momy domin ya baro tashi motar da duka keys dinsa a main house. A falo ya tsaya ya aika Siyama ta karbo masa key motar Momy, sai Samira ta mika masa nata.
“Ga tawa idan fita za kai”
“No”
Sai da Siyama ta karbo masa na Momy sannan ya fice daga falon ya nufi motarta ya shiga sai da ya cire babbar rigarsa ya jefa seat din baya sannan yai ma motar key ana bude masa gate ya dauki hanyar sama road yana ta tsara yadda zai ce idan ma yaje, daga karshe yai yanke shawarar tsayawa a waje ya kira Amina ya ce ta masa dabarar fitowa da Ataa.
ATAA POV.
Na kasa yarda cewar an daura min aure a yau ai ba yau bane gobe ne Saturday.
“Ko dai ba ni ba Amina ba sai gobe ba”
“Yau akai Daddy ya canja sharawa ne kawai dai ba a fada miki ba ne, amman an fadawa Mama cewa da Nana jiya da dare”
Rungume hannayena nai ina jin komai kamar ba gaske ba, murna zan yi ko kuka sai na rasa na farawa, Amina kan sai murna take har da nuna min hotunan daurin aure da akai yana tare da friends dinsa. Ni dai har bana iya gani da kyau na zama kamar wata dabam ba ni ba, duk wani abu da akai a can gidan sai da Momy ta dibo ta aiko mana, ni dai ko wanar ban iya ci ba yunwar rana ma sai ma nemeta na rasa, sai yanzu na gano dalilin sa a kawo ni nan da Momy tai. Lokaci zuwa lokaci Amina take mita wai ita kadai ce a nan sauran duk suna can suna da hidima. Da yamma Hajiya Ramatu ya hada min ruwan wanka mai kamshin gaske ta sa aka kirana na shiga bandakinta nai wanka ina fitowa ta ba ni wani bakin lace na saka ta fesa min turare sannan ta zaunar da ni a dakinta ta zubo min tuwo ta kawo min wai na ci.
“Na koshi”
“Daure dai ki ci ji idonki duk ya fada tun karin safe fa”
A dole na saka hannuna na soma ci ba dan ina jindadin tuwon ba domin ni ko sinadin miyar ba na ji, aure kawai na ke ta tunani wai an daura min aure, ji na ke kamar na saka kuka kuma babu damar shi gaba daya na ji na damu kuma ba damuwa ba, na saka sakewa a gidan kuma bana jin zan sake a ko'ina ma. Bayan sallah magariba ina zaune dakin ni kadai sai ga Amina ta shigo ta matso kusa da ni tana min magana kadan kadan.
“Ta so ki rakani wani guri kamin Mama Ramatu ta dawo”
Da sauri na tashi daman zaman dakin ya isheni ina nema inda zan sha iska na ga wasu abubuwan ko zan sake. Hijab ta dauko ta bani na saka daman ita akwai veil a jikinta sai kawai ta rika hannuna muka fita sai leke leke take kar Hajiya Ramatu ko yayanta ko wasu yan gidan su gamu, muna kawowa babban falon Wata yarinyar Hajiyar ta ta ganmu.
“Ke ina za ki je da ita?”
Amina tai mata alama da tai shiru kai Hajiya Ramatu ta ji. Ta ja hannuna muka fice daga falon muka bar yarinyar tana dariyar da ban san dalilinta ba. Gaba daya muka fice daga gate din sai da muka yi dan nisa muka kawo gurin wata mota sannan ta tsaya jikin motar ta bude min front seat.
“Shiga”
Kin shiga nai hango Aliyu a ciki rike da wayar da ke haska fuskarsa yana kallona. Amina bata tsaya bin ta kaina ba ta juya da sauri ta nufi hanyar gida, bude motar Aliyu yai ya fito ya zagayo inda na ke, na yi zaton ko motar zai saka ni sai nai saurin rufe gambun motar na juyo na fara takawa sai ya sha gabana yana murmushi. Takowa yake ta yi ina jin baya yana matsowa har na isa jikin motar gabana sai faduwa yake ban taba jin kunyarsa da tsoron a raina kamar na yau ba, domin duk wani tsoro da nake masa na gudun duka ne ko ba cin rai a yanzu kuma ban san na minene ba. Matseni yai sosai har ina iya jiyo numfashinsa kamar yadda yake jin nawa sai nai saurin rufe idona gam, hannayensa ya saka ya kama hannuna ya saka yatsunsa cikin nawa, dayan hannun ma haka yai masa sannan ya jinginar da fuskasa jikin tawa fuskar, hancina da na shi suma goga juna, goshinsa da nawa a hade ya lips dinsa kuma a saman nawa, numfashin da nake fitarwa yake shaka idan ni kuma zan shaka sai ya fido da nasa na shaka a haka muka dauki tsawon lokaci muna musanyar numfashi, jikina sai rawa yake sosai domin ba a taba min haka ba, sanyi na ji a kumatuna, idanuwana na bude sai gashin idona ya taba nasa, na yi zaton shi ne yake hawayen ashe ni ce, a hankali na ji lips dinsa a kasan idona yana sumbatar inda hawayen nawa suke taruwa.
“Ali...Al.... ”
Na kasa kiran sunansa balle na ce ya daina, sulale nai kamar zan duka kasa sai sai yai min masauki a kirjinsa ya rumgume ni tsantsan ko motsin bana iya yi, kaina ma saitin zuciyarsa ina jin yadda take bugawa da sauri. Sai da aka fara kiran sallah isha'i sannan ya sake ni ya leki fuskata sai kuma ya kama hannuna ya dora a kirjinsa. Ya saka dayan yana murza yatsuna a hankali sai kallon fuskata yake. Ni kuwa numfashina sai gargada yake kamar zai fita daga jikina shigarsa ma daker ne, saurin lumashe ido nai na yi sai na ji sanyin yawunsa a lips dina, halshensa ya saka a cikin bakina, ba tsosar lips dina yake ba ba kuma tsutsa zai yi ba, a tsakanin lip din kasa da na sama ya zira halshen yana goga min dogon hancinsa a hancina. A take na fashe fa kuka saurin dagawa yai da kansa ya matsa baya sai ta juyar da ni ya jinginar jikin motar ya kwanto bayana ya rumgume ni.
“Wallahi ina cikin farinciki Babyna, ban san yadda zan misalta miki ba, ban san yadda zan fada miki ba”
“Hajiya Ramatu tace kar na dade”
Da sauri ya daga daga jikina ya juyo da ni ya rike kunkuruna.
“Ta san kin zo?”
Na gyada masa kai sai ya shafa kansa da dayan hannunsa.
“Kai Amman Amina wawuya ce”
Kumatuna ya sumbata da saman hancina sannan ya ce min.
“Wuce ki je”
Yana ba ni hanya na fara sauri kamar an biyoni har tashi faduwa nai. Da hawaye na shiga gidan ban san da hawayen ba sai da Amina ta tambayi abunda na ke yi wa kuka sannan na tuna da zaman hawayen a fuskata, saurin sharewa nai na dan turo baki kamar an min wani abu. Har muka kwanta a dakin da Hajiya Ramatu ta bamu ni da Amina ban daina jin jikina na rawa ba, ina ta mamakin abunda Aliyu yai min sai kyamar bakina na ke saboda halshen daya saka min a ciki daman da na je alwalar isha'i sai da nai ta wanke bakin da amma ban daina jin kyama ba. Washe gari muna gama sallah asuba Aliyu ya kira Amina a waya ta ba ni, ni kuma da na karba sai na saka cewa komai.
“Good morning Babyna batar kin tashi lafiya”
“Lafiya kalau”
“Mashallah, Amaryata mai tsada”
Na ji kunya ta lullube ni kamar ina gansa.
“Ki ci abinci ki koshi kin ji?”
Na gyada kai ba tare da na amsa ba, sai ya ji yayi murmushi mai sauti.
“I love you....”
Ya fada kamar mai rada. Sannan ya kashe wayar, ni dai mamaki ya kasa barina gaba daya ka kasa yarda cewar Aliyu ne. Misalin takwas na safe a kawo mana abincin karyawa kala kusan uku ni dai dankalin kawai na ci na sha ruwan sanyi domin ko tea din ban ji ina shawa'awar sha ba. Ina kokarin cire tufafina na shiga wanka Amina ta miko min wayarta wai Momy ce.
“Hello Momy ina kwana”
“Lafiya kalau Aisha kin tashi lafiya”
“Lafiya kalau”
“Mashallah kina bukatar wani abun ne?”
“Ana mana komai a nan”
“Masha-Allah haka na ke so, sai anjima da dare za ku dawo gida kinji? Amman yanzu ba ri a akaiwa Nana waya ku gaisa”
Na amsa da to, haka na rike wayar har aka kaiwa Nana ina jin muryarta sai na ji wani farinciki ya cika ni cikin far'a muka gaisa da ita sannan na mikawa Amina wayar. Kamar yadda Momy ta fada ban mu koma gida ba sai da dare na yi zaton direba zata aiko ya dauke mu ashe Hajiyar ce da kanta zata kai mu, bayan ko wace awa biyu sai Aliyu ya kira wayar Amina ya ce ta ba ni tun tana dauka tai magana har ta kai idan ya kira sai dai kawai ta dauka ta miko min, tambaya yake wai ko ina bukatar wani abun sai na ce aa sai ya tambaya na ci abinci na ce masa ce daga haka kuma sai yai shiru yana sauraren numfashi har an wani lokaci sannan ya kashe. Ko da muka shiga gidan babu kowa sai wata budurwa da kuma su Siyama da Husna da gudu suka zo suka tarbe ni Momy kuma na zaune saman kujera tana kallona fuskarta da murmushi. Zaunar da ni sukai suna ta rumguna suna ja min kumatu Husna na ce min Amarya.
“To a kyale ta haka nan taje ta ga Mamanta haba”
Momy ta fada. Siyama ta rika hannuna.
“Muje na rakanki”
Sai muka fito tare da ita tana rike da hannuna ni dai har Siyamar kunyarta na ke ji balle kuma Momy, Nana ma da zanje gurinta sai ma soma jin kunya kamar ba zan iya zuwa ba.
MOMY POV.
ataa na ficewa daga falon ita da Siyama Momy ta mike tsaye tare da Hajiya Ramatu suka nufi dakinta, Hajiya Ramatu na mata ya gajiyar biki.
“Alhamdulillah”