Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 37
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 37: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 37. Momy ta fada tana zaunawa saman gado Hajiya Ramatu kuma ta zauna a…
4,446 words
Momy ta fada tana zaunawa saman gado Hajiya Ramatu kuma ta zauna a kujera. Sai da suka fara firar daurin aure da taron da akai wanda Momy bata sa ran za'ayi ba sannan Hajiya Ramatu ta ce.
“Ai kowa yayi mamakin jin auren daga sama, amman dai sati na sama za a kai masa matarsa ko?”
“Aa ba yanzu ba ai, yarinyar ma da yanzu ake son ta fara makaranta? An dai yi auren ne kawai saboda hankalin kowa ya kwanta kuma a san mijinta kin ga ba wani zancen wane na so wane na so”
“A a Wallahi karku tauye masa hakki, yaushe rabon ma da a daurawa mutum aure kuma Amarya bata tare a ranar ba? Ai bar wannan yayi ko a kauye, balle wani diban shekaru a gida? Wane namijin zai daukar miki haka?”
“Ai ya san da maganar karatun na ta tun ba yau ba”
“to karatuna yana hana aure ne? Ai aure baya hana karatu kuma karatu be hana aure, tai karatu tana karkashin kularwarsa ai zai fi dadi saman da tana gidanku abun ai be ma burge ba, karki biyewa kowa ki bar mata ta tare dakin miji kar ma a ja abu da sauri”
“Haba Hajiya komai fa ba a shirya ba”
“Shiri yanzu wani wahala ne da shi? Lefe ne ko tana dakinsa zai iya mata, kayan daki kuma rana daya za a iya siyowa indai a kasar nan ne, sai dai dan gyara gida da fenti ko kuma ya koma sabon gidan Alhaji da ya gina a wurno road ba dole sai an tsaya gina wani ba”
“Ai ni bana son ya raba musu gida da Rahma, kara dai ya hade su ya zauna da su guri daya”
“Har kin tuna min da ita, wai ta ji an yi auren nan ne?”
“Wallahi ban sani ba amman ba zata rasa ji ba tun da yan'uwanta ko matan abokan Aliyu su fada mata kin san tana dubai fa har yanzu”
“Haba dan Allah ko dan wannan be isa ya saka ki bar ya tare da matarsa? Ai ko dan wannan haushin ya isa ya saka ki barta ta tare, zaman gida na me kuma? Yanzu zamanta a nan tashin hankalinsa ne fiye da ba a daura auren ba ma”
“Hajiya yarinyar nan bata iya komai ba bata san komai ba ko girki bana jin ta iya, ga kuma karatun da take son yi”
“Karatu ai ana yi a gidan miji ni ba da aurena nai HND ba? Yar wajena Sumayyah ma da aurenta har da yara hudu tai karatu, abinci kuma gobe idan za ki shirya abun karyawa sa a kira miki ita ki shirya komai a gabata ko kuma ki bata kina fada mata tana yi kamin satin nan da zata tare ta iya wani abun sauran ta koya a can, amman Wallahi karki yarda ta dade a gidan nan ina tabbatar miki ko sati biyu tai a gidan nan sai Aliyu ya fara nuna miki damuwarsa, kan Rahma ta dawo ma ai sai a barshi da matarsa ya tare tana zuwa ta tararda wata ba saboda haka akai auren ba?”
Momy ta yi shiru tana nazarin maganganunta, ta san gaskiya Hajiya Ramatu ta fada ita kanta ta yi wannan tunanin amman bata son Ataa da Nana su ga kamar ta matsa musu ne.
“To yanzu dai sai na ji ta bakin Mahaifiyar yarinyar idan ta yarda”
“Ai yarda ma za tai wake son a daurawa dansa aure kuma ya zauna masa a guri? Wannan ai sai rashin kunya ta shiga ciki ma, kin ga yadda yake kiranta a waya dazun? Abun har Mamaki ya ba ni, karki takura masa Wallahi ki bar matarsa ta tare komai sai ta koya a can idan ma school din koyon abincin zai saka ta duk daya”
Momy ta yi murmushin jindadi.
“Zan duba Hajiya Ramatu, ko dan saboda Rahma ai ta tafi ta bar shi sai ta dawo ta tararda wata”
“Shine Ai Allah dai ya basu zama lafiya ya hada kansu”
“Amin”
Cewar Momy tana mikewa tsaye ganin Hajiya Ramatu ma ta tashi.
Sorry 🙏😑
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660* Wani irin bakinciki ne ya cika mata zuciya, sai hararar wayar take kamar Aliyu a gabanta.
“Wai ni Aliyu zai yi ma kishiya? Kiji fa”
Muneera ta tabe baki.
“Ai daman nasan za a rina, daman can ba ya fara gajiya da ke, gashi nan tun yanzu kin fara gani ai, kuma ya rasa da wacce zai hada ki kishi sai wannan yarinyar, ai Wallahi ki ma gode Allah daya saka ba ki ma garin ke ma ki kasar gaba daya zancen hakan ya fi ma”
“Ai Wallahi daga nan ma gaba zan kara sai ya raina kansa da wannan kazamar sannan idan ya ga dama ya dawo ya bada hakuri na ko?”
“Au komawa ma za ki yi?”
“Muneera to ya na iya ina son mijina, kuma dan wata banza ta aureshi ai be kamata na kyaleta da shi ba”
“Yanzu ha hada ki kishi da wata banza marar asali kuma yar aikin gidanki, ya hada ki kishi da talaka karamar yarinya kamar wannan be fada miki zai yi auren ba, sai da aka daura aure shi ma kuma ta hanyar kawayenki kika ji haba Rahma ki daina abu kamar so ya haukatar da ke mana, dan za ki kara aure sai ya wulakanta uwargidansa, daman ma zaman nan haka suke kin dai san iyakar wulakanci Bawan Allah nan na miki shi”
Idon hawaye ya cika da kwalla, sai a yanzu take jin ba dadi domin dazun haushi kawai take ji amman a yanzu ta soma ganin rashin kyautarwa da Aliyu yai mata.
“Ke daina damuwa ki manta da komai ki yi kiba ki mulmule yau ko rabuwa Aliyu yai da ke shi yai hasara, Daddynmu na can yana nema miki kodar da Aliyu ya kasa nema miki saboda ya gaji da ke, ashe aure zai yi, yanzu ko rabuwa yai da ke idan kika samu lafiya sai ki auri mai haihuwa shi kuma yaje can ya karata da amaryar”
“Ko a mafarki ban taba zaton Aliyu zai min haka ba, ban tana taba tsammanin haka ba ko a mafarki”
“Ai namiji ba shi da tabbas namiji dan kunama, hmmm ai karki tana yarda zai so ki ke kadai ke kadai ranki”
“Na shiga uku Muneera, zuciyarta kamar zata narke na ke ji, i can't believe tun ina raye Aliyu zai hada ni da wata, Wallahi ko bayan raina ya auri wata be kyauta min irin soyayyar da mukai balle kuma yanzu da na ke raye, bayan kuma ya san lalurata, baya tsoron abunda zai same ni? A yanzu kenan baya gudun bacin raina? Ashe Aliyu zai iya min haka?”
Wasu zafafan hawaye ne ke sauko mata kamar ba gobe.
“Ni kishiya? Ni...?” “Ai namiji kenan, kadan daga halinsa kika gani”
“Komai raba mu za mu yi kenan? Yanzu Aliyu ba nawa ba ne ni kadai kenan? Wayyo Allah ”
Ta fada da hargagin kuka tana saukowa daga saman gadon ta fado kasa tana wani irin kuka. Muneera ta taso da sauri ta dawo kusa da ita
“Yanzu akan wannan abun za ki saka kanki kuka?”
“Ina son mijina Muneera ba zan iya ganinsa da wata ba, taya zan rayu da Aliyu shi kuma ya rayu da wata? Taya Aliyu zai min haka? Muneera haukacewa ce zan yi wayyo zuciyata na kasa yarda cewar Aliyu ya auri yarinyar nan”
“Haba Rahma a hotel muke fa, hotel din ma ta dubai idan kina irin wannan ihun kina kuka ai sai su dauka wani abun su shigo”
“Gida na ke so Muneera, gida zan koma Nigeria na ke so ki fadawa Yaya ya kai ni ya shirya mu koma gida, Muneera zan iya mutuwa”
Ta fada tana kara narkewa tana wani irin kuka mai ban tausayi. Ita kadai ta san abunda take ji a yanzu ita kadai tasan yadda taje son Aliyu kuma yanzu ace ya hada son ta da na wata?
“Mi na masa? Mi na masa Muneera? Mi yake damunsa? Anya kina ganin na cancanci irin wannan sakarya?”
Kuka take sosai, tun Muneera na lallabata har ta gaji ta zuba mata ido kamin ta tashi zuwa dakin yayansu inda ya tare da matarsa, after zuwan Muneera da Rahma shi ma ya zo hutu shi da matarsa. Kusan shi yake kula da Muneera da Rahma a lokacin da ya zo garin. Duk yadda Muneera da Yayanta suka so ta kwantar da hankali ta manta da Aliyu ta zauna a nan sai ta kasa gaba daya ta fita daga hayyacinta sai kuka take ta rasa inda zata saka kanta. Sosai yayan nata ya ji haushi yadda take kuma ta tashi hankalinsa domin shi ma yana ganin Aliyu ya nuna musu rashin kunya da kuma tozarci domin shi ma a ganinsa abunda Aliyu yai be kyauta ba taya ma zai auri wata mace bayan matarsa ba lafiya tana a cikin halin da take bukatarsa a maimakon ya nuna mata kulawa sai ya nemi kara aure wannan ma ai abun kunya ne kuma abun kataici. Har daga Mommynta sai da ta kirata da kanta ta fada mata ta kwantar da hankali ta zaunawarta a Dubai ta huta amman ta kasa bawa zuciyarta hakuri, a dole suka fara shirya komawarta gida Nigerian a gobe ita da Muneera wacce ta rakota shi kan ba be shirya komawarsa yanzu ba domin be gama shakatawarsa ta matarsa ba.
ATAA POV.
Siyama na gana ina biye sai wata tafiya na ke kamar mai jin nauyin taka kasa, gaba daya kunyar Nana nake ji na kasa sukuni na kasa sakewa har muka shiga dakin da take. Siyama tai sallama ni kuma na kasa cewa komai sai na zauna kusa da kofa kaina a kasa, Siyama kuma tai dariya ta fice. Gyara zama nai na rike hannyena ina ta wasa da su a cikin gyalena.
“Al-hamdulillah na gode da ya nuna min wannan ranar, yau rana ce mai cike da farinciki a gurina, ban tsammaci zuwanta a lokacin da na ke raye ba, kuma ban tsammanin zuwanta a nan kusa ba, amman sai ga shi komai ya zo ta yadda ban yi zato ba, na gode Allah da yasa ina da rai akai auren nan”
Dagowa nai na kalleta sai na ga hawaye a idonta murmushi kuma a fuskarsa. Sake maida kaina nai kasa domin har lokacin kunya na ke ji ni irin kunyar da na ke daga lokacin da aka daura auren nan zuwa yau har mamaki take ba ni domin ban taba sanin ina da ita ba sai a yanzu. Bayan sallah isha'i Hajiya Ramatu ta shigo bangaren da muke ita da Momy suka gaisa da Nana sai Momy ta ce min na tashi na je part dinta za tai magana da Nana. Ni kuma na tashi na fice ban je part din nata ba na zauna a gurin da ake aje motoci na zauna ina ta tunani ni kadai, cikin kuwa har da tunanin Rahma, ko a wane hali take a yanzu ko kuma zata ji idan ta ci cewar Aliyu ya aure ni, Mama Fulani ma ya za tai na san dai ba zata taba so na ba, ita da Rahma kuma za su iya ci min mutunci ko goranta idan suka ganni wata kila ma har duka sai Rahma ta yi min tace na aure mata miji, ko tana Abujar ma ko tana nan oho. Haka nai ta kawo wacan ina ture wannan har na soma jin bachi a gurin, can kuma su ka fito daga bq din Momy na takawa a hankali tare da kawarta har suka iso gurin motar kawar tata, a lokacin ni kuma na mike tsaye da zimmar komawa Bq din sai Hajiya Ramatu ta rike baki.
“Laa yanzu a nan kika zauna? Ba ki je falon Hajiya ba?”
“Kunya ta ke ji daman na lura da takunta ai”
Ni dai na wuce ban ce komai ba sai watsa na ke da yan yatsuna, lokacin da na shiga bq na yi zaton Nana zata fada min wani abun akan zuwan Momy gurinta amman bata ce min komai ba sai dai tana ta kallona tana murmushi. A katifa daya muka kwanta kamar yadda muka saba sai dai jin kunyarta be hanani shigewa bayanta nai bachina ba har gari ya waye. Misalin bakwai da yan mintuna Momy ta aiko Husna tana kirana, bata jira mun tafi tare ba ta juya ta fice. Ni kuma na mike tsaye na dauki Hijab dina ina kokarin sakawa Nana ta ce.
“Kin yi dacen suruka indai abun ya bi haka za ki jidadin zama da ita”
Na kalleta sai kuma na sauke idona kasa, kamar na tambaya abunda ya Momy ta zo yi jiya a nan sai kuma na dauke kaina na fice daga bq din, kamar jiya yau ma da kunya na shiga part dinta sai na samu tana zaune falo ita kadai tana kwaba fulawa. Har kasa na kai na gaisheta ta amsa min da murmushi a fuskarta.
“Shiga kitchen akwai tarugu da albarsa ki gagga min zan shigo yanzu”
Tashi nai na shiga kitchen din sai na samu tarugun ta albarsa a cikin roba an aje kasa ga kuma turmi a kusa, bude turmin nai na yanka albarsa na fara dakawa sannan na zuba ta rugun na dake su a tare, ina karewa tana shigowa sai ta aje fulawar ta kunna fanfon kitchen din ta wanke hannunta.
“Hadewa kikai?”
“Eh a tare na same su”
“Eh ko a tare ne ai za ki iya rabawa saboda wani lokacin ba komai ake hadewa ba, wani abun baya son albasa da yawa wani kuma tarugun ne ba za a saka da yawa ba, shiyasa ake son rabawar, daga yau karki sake hadewa idan kina jajage kinji?”
“To”
Daga haka ta nuna min inda zan murda a jikin gas din sannan ta miko min wani abu mai dan tsawo ta nuna min inda zan matsa wuta ta fito na sai na saka a gas din cikin tsoro nai hakan sai ga gas din ya kama da karfi sai kuma ya nuna min gurin ragewa da kuma yadda zan daidaita wutar. Dayan ma sakawa tai na kunna da kai ta na dora ruwa a kai ta bani boya wacce aka gyara ta ce na zuba a ciki kuma na rufe, sannan ta littafamin yadda zan soya tarugun da albarsa da yadda zan zuba kwai idan ya soyu sannan ta fita ta bar min kitchen din. Sosai na maida hankali ina yin yadda ta ce sai dadi na ke ji yau zan yi girki irin na masu kudi da kaina, sai dai tsoron gas din na ke ina ganin kamar fashewa zai yi ko kuma ya ja ni idan ina matsawa kusa.
“Tace na soya tarugun da albarsa idan ya soyu sai na rage wutar na fada kwai na kada na saka magi a ciki sannan na zuba kwai ciki kuma kar na motsa idan yayi sai na saka wannan katon cibin na juya shi kar na bari ta karye ko ta yamutse, idan ta yi tace na saka a wannan kular nai haka har sau...... ”
Ban karasa ba fadar abunda ke bakina na ji an riga kunkuru an doro min kai a wuyana.
“Mi kike hadawa?”
Saurin janye jikina nai na juyi ina ta kyarma irin na tsoro.
“Ina wuni?”
“Ina kwana?”
Ya fada yana jan kumatuna, sai nai kasa da kaina. Waiga yai ya kalli kofar kitchen din sannan ya saka hannunsa biyu ya rika fuskata ya sumbace saman lips dina. Sai yai saurin juyawa ya fice yana murmushi, wani irin kazanta na ji kamar na cire bakina gaba daya, da sauri na na zuba omon da ke kusa da fofon na wanke saman bakin nawa da shi ina ta jin kyankyami. Ina dagowa sai na ganshi yana kallona sai kuma kunyarsa ta rufe ni, murmushi yai ya karaso kusa da ni ya sake rika fuskana ina jin kamar na masa magana ko nai ihu sai kuma na kasa yi sai kunya na ke ji wannan karon na iya saman bakina ya sumbarta ba, bakinsa ya saka cikin nawa ya rika jan yawu bakina yana hadewa yana ta wasa da halshensa a cikin bakina daga karshe ya turo min yawunsa kuma ya kwanto da ni hannunsa wanda hakan ya cilasta ni hadewa. Rumtse ido nai ma matse hannuna da jikina ina kokarin kankamewa guri daya, a dole sake ni sai ya bude kofar bayan ya fita daga kitchen din. Kakarin amai na fara yi wai ko yawunsa da suka shiga bakina za su fito na mayesu ashe Aliyu kazami na musamman duk tsabbatarsa ta banza ce, taya ma zaka saka bakinka a cikin bakin wani har ku yi musanyar yawu, ni da bana iya cin abinci a saitin bakin da wani ya ci ma. Na fi karfin minti goma ina ta kakarin aman sai kyankyami na ke ji ina ta tofarda yawu, sannan Momy ta shigo, ita ce ta lura da tarugun ya wuyu har ya fara konewa ma ni ban kula ba.
“Mi kike har yai haka?”
Na yi shiru ina ta tunanin abunda na ke, sai ta rage wutan ta fasa kwai da kanta ta mika min na zuba, har muka yi breakfast din muka gama Aliyu be sake shigowa kitchen din ba, ni kuma ban daina tara yawu a bakina ina zubawa a gurin fanfan kitchen din ba sai na zuba ruwa dan bana son Momy ta gani. Bayan na gama ita ta gasa tai sauran sai muka dawo falo muka jera komai. A gurin jerawar ma sai da ta gwada min yadda zan yi da kuma yadda zan aje komai a muhallinsa. Sannan ta zuba mana na mu ni da Nana ta ba ni, sai da zan wuce sannan na lura da Aliyu da ke zaune saman cushion yana danna wayarsa kamar ba shi ne yai min abunda yai min dazun ba.
“Aisha kun gaisa?”
Momy ta kirani sannan ta fada kamin na amsa ya dago kansa ya kalleni fuska.
“Aa”
“To idan kika ganshi ki rika gaishe shi hakan na da kyau kinji, kuma kamin ki karya ki wanke bakinki da brush”
“To ina kwana”
“Lafiya kalau”
Ya amsa min fuskarsa babu murmushi ko wasa kamar ba shi ba. Ni kuma na fice ina ta masa kallon abunda yai min dazun. Ko da na isa part din wato bq na samu Nana na share saman balcony din saurin aje abincin hannuna nai na karbi sharar nakarasa, sai ta koma cikin daki ta zauna. Bayan na gama na je ma sameta na dauko abun karyawa na aje mata na shiga na wanke bakina kamar yadda Momy ta fada sannan na zo muka karya.
“Ina jin kamar be dace ace har an miki aure Hajiya na zancen tarewarki a sati mai zuwa kuma ace yan'uwana da yan'uwan mahaifinki, ina jin kamar hakan be dace ba, kuma ina jin babu dadi idan na tuna da haka sai dai babu yadda zan yi”
Bayan mun gama cin abincin take min wannan maganar, gabana ne ya fadi.
“Tarewa ta sati mai zuwa Nana?”
“Haka ta roka ita da matar da suka zo jiya, kuma ta ce idan na amince zata fadawa Mahaifin Aliyu sun fada min sun dauke nauyin komai, za su yi duk abunda ya dace, kuma za a hada miki kayan sakawarki wasu tun a nan wasu kuma sai kinje can Saboda kurewar lokaci, tace ba za ayi wani hidima ba amman tana son ta shirya yar walima saboda addu'a”
Kuka na fara yi a take.
“Karatuna fa? Yanzu kenan? Barin zuwa makarantar zan yi? Kuma bokan ma ba za a a saka ni ba?”
“aa zancen karatunki tace yana nan za ki cigaba da karatunki ko bayan aure”
“Aa nana ni ban yarda ba Wallahi bana so, ma fasa auren gaba daya Wallahi ba zan yarda ba, ni ba zan iya zaman da shi ba, wayyo Nana dan Allah karki bari na tare yanzu....”
Shine abunda na ke fada ina rikon hannunta domin har ga Allah na tsorota da wani zaman aure a yanzu, yo ya ma zan yi zaman? Me ake cewa ya tsare tsaren suke ni na zan iya ba, ga wannan kazantar da yake min na san idan ina can sai ya sake min ita, karatuna ma lalacewa zai yi. Babu abunda Nana take sai kallo da fuskar tausayi domin kukan ba na wasa na ke ba.
“Na riga na karba mata ba zan iya canjawa a yanzu ba, Allah yasa hakan shi ya fi alheri”
Kara fadawa nai jikinta na fashe da kuka ina ta goga mata jikina kamar wata yarinya karama, bata ce min komai ba bayan hawayen da take har nai kuka na gama na tashi dan kaina na shiga bandakin na wanke fuskarta na saka uniform dina na tafi makarantar islamiya kasancewar ranar Lahadi ce ana zuwa da safe. Sai dai ban sake da kowa ba duk wanda ya kalleni ya san ina cikin damuwa domin har ga Allah bana son tarewar gaba daya ma sai na ji auren ya fita a raina. Da shabiyun rana aka tashe mu na dawo gida kamar wata marar lafiya, abincin rana kawai na ci Momy ta aiko wai nai wanka za mu fita, sai na shiga nai wanka na shirya a cikin daya daga rigunan da Aliyu ya siyo min a ranar da yaje da ni shopping. Amina aka kawo ta zo ta kirani muka shiga nota tare muka dauki hanyar gidan Zara mai lalle kalar fatata ta duba ta bani wasu abubuwan ta ce wannan na rika shafawa a jikina idan zan kwanta wannan kuma idan zan shiga da kamar minti goma haka, ni dai ji kawai na ke ba dan ina da niyar yi ba, daga ranar ban sake zuwa makarantar islamiya ba ban kuma sake saka Aliyu a idona ba, idan dare yayi sai Momy ta aiko min da fruits na sha, bayan kwana uku a gidan ta mayar da ni gurin wata kanwarta dake Abuja road, a can akai ta cusa min wasu abubuwa da na ke hadewa daker idan na gama na shiga bandaki nai kukana son raina na fito, duk na kasa sakewa a gidan lokaci zuwa lokaci Amina da Siyama da Husna suke zuwa su dubani, da dare fruit ake ba ni kamar yadda Momy take min a can sa safe kuma ba a bari na karya daabu mai nauyi da na ci kadan sai ace na barta haka a bani kaza mai magani da daci na ci, gashi tsoron matar na ke domin na lura ita ba kamar Momy ba ce sam bata wasa da yara balle ta sake da su, ba kuma wulakanci ba irin halin nan na dattijai. Kullum sai an kaini gurin Zara ta gyada min jiki, ta shafa min turare na jiki da na kai da kuma na tsiguno, sannan ta ba ni ruwan magani ta ce nai wanka idan ta gama min dilka ni kaina a yanzu ina jin dadin jikina domin fatar jikin har wani sheki take tayi laushi sosai fiye da da, gashin kaina kuwa kamar ba nawa ba, domin kullum cikin shafa masa mai take tana gyara shi, ita kanta yabon kyauna take gaba daya na koma kamar ba ni ba, domin kuwa na fi da kyau da haske duk wani datti na fuskata da jikina sai da aka kawarda shi. Wata kabila ce ta zo ta auna ni ko'ina na jiki sai da ta auna ta sannan ta tafi, haka na rika kwana a gidan kullum idan na yi marmarin ganin Nana sai da a kira min ita a waya shi ma kuma idan Siyama ta zo ko Amina ko kuma Momy ta kira, a gidan matar idan zata hada abunda be kai kmya kawo ba ko wani abu mai nauyi ba sai ta kirani ta nuna min ta tambaye ni na gane, ko ban gane ba cewa na ke na ge saboda kawai a wuce gurin, sai dai kullum sai na sha kukan dare ni kadai ba tare da kowa ya sani ba.
ALIYU POV.
Sai da ta wuce sannan ya mike ya nufi dinning yana fadin.
“Tare kuka shirya abun karyawar ne?”
“Eh wai ina dan koya mata ne kamin taje can ta koya gaba daya”
Yayi shiru be ce komai ba har ya zauna ya bude abinci ya zubawa kansa ya soma ci yana ta tunanin abunda yai ma Ataa a dazu sai murmushi yake a zuciyarsa.
“Aliyu yarinyarnan tana son karatu sosai fa”
Da dago ya kalli Momy.
“Na sani shiyasa na shigar da ita islamiya ai, kuma bokon ma zan saka nan gaba In-Sha-Allah”
“Ina jin tsoro kar aurenku ya saka karatunta tarwatsewa”
“Saboda me? As long as zatai zaman aure ai zan barta tai karatunta, ba ni da matsala da wannan amman Momy..... ”
Sai kuma yai shiru ya kasa karasawa. Momy ta shiga zubawa Daddyn abincinsa tana tambayarsa.
“Amman me?”
“Tsawon wane lokaci zata dauka a gida tana karatun?”
“Karatu yana da lokaci ne?”
“Na yi magana da Daddynka jiya saboda Hajiya Ramatu ta kawo wata shawara har ta saka ni dole sai da naje bq nai magana da Nana ita kuma ta amince ta ce mana ba matsala, da na fadawa Daddynka sai yace shi babu ruwanshi shawara ta mu ce, kuma na kira babbar Yayarku after sallah asuba na fada mata komai ita ta bani shawara makamanciyar wacce Hajiya Ramatu ta ba ni”
Da dago tana ta kallonta, gabansa na dan faduwa irin na tsoron nan idan ba wani abun za a bullo da shi ba, wata kila ace ya kai Ataa wata makarantar boko a Abuja ko kasar waje ko kuma ya barta gida har nan da wani lokaci mai tsawo wanda yake jin cewar ba zai iya haka ba.
“Wani abun ne?”
Sai da Momy ta gama warewa Daddyn nasa abun karyarwa sannan ta ce.
“Wai Mun yanke shawarar Ataa ta tare dakinta next week Saturday”
Wani irin dadi da mamaki da annashuwa da farinciki Aliyu ya ji lokaci daya, amman yai kokarin dannewa saboda kar Momy ta ga haukarsa ko rashin kunyarsa, yayi murmushin dake nuna jindadinsa amman ya boye duk wani jindadin na ainahi a cikin ruhinsa.
“Amman Momy ita ta yarda?”
“Aisha ai bata da matsala duk inda aka bi da ita bi za tai, Nana kuma t amince har ma godiya tai mana jin cewar an dauke mata komai”
“Masha-Allah Allah ya tabbatar da alheri”
“Amin sai ka fara shirye shirye tun a yanzu”
Momy ta fada sannan ta dauki kayan abincin ta fice, wani irin murmushi Aliyu yai ya girgiza hannunsa ya shafa kansa abincin ma sai ya kasa ci.