Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 38
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 38: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 38. Tun daga lokacin ya fara shirye shirye kamar yadda Momy ta fada…
4,405 words
Tun daga lokacin ya fara shirye shirye kamar yadda Momy ta fada masa, kudi ya cire mai yawa ya bawa wata yayar Momy yar kasuwa ta siyoma Ataa expensive clothes da tsarkoki masu kyau da tsada shoe dinta ma abun kallo ne, kusan kala talatin aka mata nata na sakawa wai na yanzu da kuma na kwaliyar amarci kamin a dinka mata na lefe idan komai ya laba hankali ya kwanta zai mata cikakken lefe domin yana son ya mayarda ita mutum ita ta zama tana fita da shiga irin ta yayan manya. Bayan gidan da suka zauna d Rahma yana da wani gidan dabam mai kyau da tsare, wanda ya so ya aje Ataa a ciki ita kuma Rahma ya barta a wacan ma'ana ya raba musu gida saboda gudun fitina sai Momy ta hana ta saka Daddyn ya ba shi dayan gidansa mai part uku da ke unguwar koko road. Sabon fenti aka yi ma gidan duk kuwa da kasancewar ba a taba shigarsa ba, saka kara kawata shi aka gyara wasu abubuwan, sannan Momy tai order wasu furnitures daga Kaduna masu tsada da kyau aka kawo aka zuba a dayan bangaren na Ataa gaba daya furnitures din bangrenta fafare ne tun daga dago har kujeru da duk wani abu na kwaliyar daki, gurin curtains din ne kawai akai musu surki da ja da sai kuma carpet din shi ma ja, after two days da kawo furnitures aka saka Electronics da wasu abubuwan na kawata gida. Kayan kitchen kuma wata mai siyarda da kayan kitchen aka bawa kwangila da shirya komai on Friday aka saka. Ba Aliyu kadai ba, Momy m da yan'uwanta da Daddy da Abbah sun yi ma Ataa hidima sosai gurin gyara komai na gida. Sai dai duk wannan farinciki da jindadadi Ataa zata tare da Aliyu yake idan ya tuna cewar Babu Mama Fulani za ayi sai ya ji babu dadi, gashi tun lokacin da abun ya faru ta daina daukar wayarsa balle kuma ita ta kirashi da kanta Momy ma idan ta kira bata dagawa, sai dai ya kira Maryam ko. Rukaiyah ya tambayi lafiyarta.
Kamar yadda Momy ta tsara ranar Saturday akai walima, ba a yi wani taro ba domin ba kowa da kowa Momy ta gayyato ba, saboda kurewar lokaci wasu ma jin abun na Momy ne yasa suka zo ba tare da an gayyoto su din ba, wani abun mamaki har da Maryam da Rukaiya da kuma yayan Ammy, wanda Momy take sa ka ran Abbah ne ya turo su da kansa, domin Mama Fulani dai fushi take ba zata taba cewa su zo ba, ko da yake wani lokacin Mama Fulani ta kan yi wani abun dan hada kan zuri'ar ta da kuma yayanta. Sosai Momy tai farinciki da ganinsu kuma ta jidadin zuwan na su.
ATAA. POV.
Ban kara tabbatar da cewar da gaske ne ba, sai da maga ana ta hidimar bikin, tun ranar laraba aka saka nai wa ka da ruwan lalle mai ja sosai, ranar da ta kama jumma aka zo aka kara gyara min gashina har gida, ba kitso aka min ba sai dai an gyara min shi yadda na ke jindadin zamansa a kaina. Lallen ma dan ubansu aka min mai kyau gaske, tun da nake a rayuwata ban taba yin lallae ba sai yau ashe haka yake kyau a fatata farin kafata dana hannuna ya fito fes lallen mai ja ya fito fes, domin ja ne kawai aka min da shi babu digon baki ko daya. Ranar assabar na tashi da wani azababben ciwon kai saboda na wuni na kuma kwana ina kuka da tunanin. Da yamma aka sake saka ni nai wani wankan wata mai kwaliyar ta zo ta shirya ni tai min fentin nan na kanti sai na fito kamar ba ni ba, dogon hancin nan nawa sai ya kara fitowa kowa cewar yake na yi kyau ni dai nawa idone kawai zuciyata kuma cike da kuka. A mota mai kyau aka saka ni aka tafi da ni gidan Momy a can na tararda taro har an fara walimar ma, a cikin mutanen da suka halarta da su Yayan Mama Fulani da Ammy Maryam da Rukaiya har bana son hada ido da su saboda harata da suke. Duk wani wa'axi na Malamar ban ji ko daya ba, I hawaye kawai nake har kwaliyar tawa ta hoda ta soma gogewa, na sha hotuna sosai. Kamin Momy ta saka a sake maida ni gudin Kanwar tata Hajiya Mairo sai dai wannan karon tare da duka yayanta muka tafi da kuma wasu bakin fuska da ban sani ba. Ta ba ni abinci amman na kasa ci ruwa ma kasa sha nai sai gani nake kamar mafarki na ke. Bayan na gama sallah isha'i wata mai kwaliyar ba wacan ba ta sake zuwa ta gyara ni na saka wasu tufafin lace ne ash color mai kyau da ja mayafi sai kuma ta kalmin suma kala daya da gyalena sarkar kuma irin wannan ce mai ruwan gol wata kila ma gol din ne ban gane ba. A gidan Momy aka sake dawowa da ni tare da yan matan dake tare da ni aka kai ni gurin Nana wai ta min huduba sai aka fita aka bar ni daga ni sai ita, riketa nai na fashe da kuka ji nake kamar idan na tafi na tafi kenan ba dawowa. Ita bata iya ce min komai sai kuka take har wata yar'uwar Daddy ta shigo zata fita da ni sai na rike Nana gam ina kuka kamar yadda ita ma take yi tana rike da hannuna.
“Aure ai ya gaji haka, dan Allah ku yi hakuri sai kace wandanda akai wa mutuwa? Haba dai”
Shine abunda mutane suke ta fada ganin irin yadda ni da Nana muke ta kuka sosai, babu wanda ya san abunda na ke ji sai ni yau zan rabu da Nana wai wani aure zan yi auren da sai a yanzu na ke jin nadamar amincewa da Aliyu da nai da na sani na ce ban shirya auren kowa ba sai na zauna ni na Nana mu yi ta rayuwarmu. Batan fitowa da ni bangaren Nana aka kai ni Gurin Momy dakin na cike da mutane a haka tai min nasiha sai na rike hannunta ina ta girgiza mata kai ina kuka ita ma kanta sai dai ta yi hawayen.
Daker aka fito da ni aka saka ni a motar ina da kallon bq din Nana na tsaye jikin windows tana kallona ita da wasu yan'uwana Momy wata kila hakuri suke ba ta, a gidan baya aka sani ni tare da wasu mayan mata sauran yan matan kuma suka shiga sauran motocin, aka dauki hanya da ki hanyar da ban san wace unguwa ce ba domin kaina a kasa yake ina kuka har mutanen da ke cikin moyar suka soma tsarguwa da ni. Mun dade muna tafiyar sannan muna iso wani gida da ban san ina ne ba jin ana guda yasa gabana faduwa kuma na kara rushewa da kuka. Wata matar ce da ba zan iya shaidar fuskarta ba ke rike da hannuna tana nutsawa da ni a cikin gidan har muka isa falon da ke ta kamshin turare sannan muka wuce uwar daga ma'ana bedroom nan dai kamshi ke tashi da kuma mutane a ciki da ba xa su fi mutum biyar ba bayan falon da ma da akwai wasu a nan. A tsakiyar gadon aka zauna da ni sannan aka fesa min wani turaren aka kara gyara min mayafina yadda zai sauko min da kyau. Sai da dattijawan cikin suka min addu'a kuma suka min huduba akan zaman aure hakuri yi na yi ba ri na ba ri da kuma toshe kunnu akan dukan abunda zan ji ko na gani. Sannan suka tafi aka barni da yan mata masu kokarin bude mayafina su ga fuskata ni ko har lokacin hawaye na ke, ina jin wani yanayi da ban taba jin kaina a ciki ba, hakika ban san aure ba, ban san miye aure ba balle abubuwan da suke cikinsa, amman iina jin darajata ta karu na bar kulawar Nana da tarbiyarta na koma gurin ta Aliyu kamar yadda Momy tai min huduba. Wata sabuwar rayuwarce zan fara fuskanta wata kila mai dadi ce ko akasin haka, wata kila mai sauki ce ko kishiyarta, wata kila kuma na samu duka biyun wato dadi da daci sauki da kuma wahala. Bana iya gane lokacin da aka shigo da Aliyu hayaniyar maza kawai na ji a dakin wasu na zolarsa, ban daga kaina a cikin mayafin na kalle ko su waye da waye a abokansa ba, amman nasan sun hausa mutum biyar kuma ba za su sama da mutu goma ba, baki gado ya zauna yana ga kamshin turarensa mai dadin shaka. Nasir ne ya fara yi mana nasiha sannan wani abokinsa ya dora sai kuma suka rufe da addu'a tare dayi mana fatar samun zaman lafiya kwanciyar hankali da kuma zuri'a ta gari. Da dai daya suka fara fita sannan sauran suka fice har da matan sai ya tashi ya raka abokansa, ina jin lokacin da motacinsu suka tashi suka bar cikin gidan sai kuma na ji yana jan kofar falon alamar rufewa yake. Da zai dawo dakin sai da yai sallama sannan ya shigo, ni kuma na kasa amsawa har lokacin kaina na kasa ina ta wasa da yatsun hannuna, a inda ya zauna dazu ya sake zaunawa.
“Amarya.... ”
Sai na ji wata kunyar ta sake rufe. Kara hawowa yai saman gadon ya miko hannunsa ya bude mayafin da ke kaina ya dora shi a bayana yana murmushi sai kuma ya saka hannun na sa ya dago kaina sai na lumshe ido.
“Godiya ga Ubangijin da ya mallaka min wannan halittar ta inda ban yi zato ba, tsarki ya tabbata a gareka ya Allah”
Ya fada sannan ya Hura min iska a saman idona da suke kulle.
“Bude idonki ki kalli Masoyinki, bude idonki ki kalli mijinki na har abada”
A hankali ya bude ido sai na sauke su a cikin na shi, ta cikin kwayar ido muke kallon juna ni da shi wani irin sako yake aika ta cikin idon da ban wayanci na minene ba, ni ko hawaye sai aikinsu suke a idona. Wani lallausan murmushi yai min ya kai hannunsa a fuska ta share min hawayena sannan ya kara matsowa kusa da ji yai min masauki a kirjinsa, rumgume ni yai kamar wata yar baby sai juyani yake a hankali irin yadda ake yi ma yara. Ni kuwa na samu damar yin hawaye iya son raina, sai na ji dumin bakinsa a goshina, ya sumbace ni ba normal sumbata yai min ba yadda yake dora lips dinsa a goshin nawa ya sotsa ya dauke kamar zai janyo jinin goshin nawa ya sha ne, sai kara matseni yake a kirjinsa kamar wani zai kwace masa ni, a take jikina ya fara rawa domin ba a tana rumgume irin yadda ya rumgume ni ba. A hankali ya dago fuskata shi kuma ya duko da fuskarsa ya sumbaci tsinin hancina, ya sumbanci kumatuna sai kuma ya sake komawa ya sumbaci goashina kamin ya hade bakina da na sake rumtse ido ina jin wani irin kyankyami da kuma faduwar gaba a lokaci daya. A hankali yake shan lebena na kasa sai kuma ya yai sama da bakinsa ya sha na saman.
ALIYU POV.
Tana da soft and sweet lips Aliyu mutum ne mai son kiss sosai, ji yake kamar yana shan wata madara a bakinta, har Lumashe ido yake yana budewa, sai ya fi jindadi da kwanciyar da zakin lips sumbatarar a yanzu fiye da yadda ya sumbace ta a last time a kitchen wata kila saboda ya fi bukatatar a yanzu ne ko kuma saboda ya fi kwanciyar hankali da sakewa ne. Ya dauki tsawon lokaci a haka kamar ita da shi za su dauwama a haka ne sannan ya sake ta ya dago yana bude idonsa da su sauya kala ya jingina goshinsa saman nata yana ta kallon idonta da ke rufe sai shima ya rufe idon yana sauke numfashin a hankali.
“Taso mu yi alwala mu yi sallah”
Ya fada yana bude idonsa, kokarin dagawa tai daga jikinsa sai yai saurin bude idon ya rigata sauka daga kan gadon ya cire babbar rigarsa ya aje gefe ya bude mata bandakin. Takawa ta fara yi a hankali yana ta kallon fuakarta kamar zai hadeta har ta karaso kusa da shi ta shiga bandakin. Shiga yai ya kunna tap din ya tara hannunta ya wanke mata ya tara hannunsa ruwan suka taru ya kai mata a baki ta kuskure sannan ya shaka mata hancin da kansa, ya wanke mata fuska, hannu har ta kai ga shafar kai, ya kwakula mata kunnenta sai kuma ya dagota ya tara kafarta ya ya wanke mata dayar ma yai mata haka sannan ya sauketa ya sumbaci samman gashinta. Shi kan sai da ya tabbatace wani bangare na jikinsa sannan yai alwalar ya fito ya sameta bakin gado zaune. Carpet biyu ya shimfida musu tashi tana gaban tata sannan ya fita daga dakin zuwa dakinta wardrobe ya bude inda aka zuba mata duka kayanta yai ta ya mutsa har ya samu hijab ya dauko mata ya dawo dakinsa, fa kansa ya saka mata Hijab din sannan ya matso da ita ya kawo ta gurin carpet din ya tsayar da ita kamar wacce aka ce masa bata gani, har sallah ma ji yakd kamar yai mata domin yau son ta a zuciyarsa na musamman ne. Sai da ya fara ikama sannan ya kabbata. Raka biyu sukai suka sallame sannan ya daga hannunsa yai ma Allah godiya yai musu addu'a ya shafa ita ma ya shafa sai ya juyo ya kama goshinta ya karanta addu'a sai ya sumbaci goshin, kamin ya saka hannunsa ya cire mata hijab. Tashi yai yaje ya dauko wata leda da ke gefen gado ya bude mata gassashiyar kaza ce da madara irin fresh milk din nan mai kyau. Da kanshi yaje ya dauko cup daya ya zuba mata milk din sannan ya dauki kazar ya kai mata a baki sai ta kawarda fuska.
“Na koshi”
Be ce mata komai ba ya mika hannunsa janyota ta dawo kusa da shi ya kwantar da ita a jikinsa sai ta lafe kamar wata kanwa, dibar naman kazar yake a baki yana taunawa kadan sai ya dago kanta ya hade bakinsu ya tura mata naman a baki, a dole take taunawa ta hade kamin ta hade ya tauna wani ya sake hade bakinsu ya tura mata a ciki. Madararce kawai ya daga kofin ya kai mata a baki ba tare daya gunda ta ba, sai ta bude baki kadan kamar wacce bata saba cin abinci ba tana sha a hankali. Wacce ta zubo mata a gefen baki sai ya saka halshensa ya lashe da kuma wacce ta tsaya a saman lebenta.
“Kin koshi?”
Ta gyada kai a hankali sai wani nutse kai take kasa, gaba daya ta zama wata solobuyu duk yadda ya juyata yi take. Tashi hai ya shiga bandaki ya wanke hannunsa sannan ya fito falo ya nufa ya kashe wuta da tv da aka bar musu sake ya dawo dakin.
“Ta so”
Ya mika mata hannunsa, dagowa tai tana kallon hannun sannan ta mika masa nata mai zanen lalle sai da mike tsaye sai ya sumbaci hannun ya juyo da shi ciki ya sumbaci tsakiyar sai halshensa yake sakawa yana wasa da tsakiyar hannunta. Kamin ya kai hannunsa ya fara shafa gashin kanta yana shinshinawa. Jin ta hade yawu da karfi ta matsa baya yasa ya kalleta sai ya dagata ya kwantar da ita bakin gado ya risina daga gurin kafafunwa ya fara shafa lalleta fa farar kafarta mai taushi wacce ta sha dilka. Saman kafar ya fara kissing sai kuma kasan kafar sannan ya saka babban yatsansa a bakinsa ya fara tsusa kamar yaro ya samu sweet. Saurin fisge kafar tai ta tashi zaune sai shi ma ya tashi tsaye yana tande baki.
“Hau gado ki kwanta”
“Aa kasa zan kwanta”
Matsawo yai kusa da ita ya kai hannunsa ya ja lips dinta.
“Kin taba ganin Amarya ta kwanta kasa ranar aurenta?”
Ya fada mata a kunne kamar mai rada sai ya saka mata halshensa a kunneta ya fara wasa da kunnen nata yana tsosa a take ta soma jin ba dadi, sai ta fisge kunnenta daga bakinsa ta hau saman gadon ta kwanta dan dole ta. Wani kasaitaccen murmushi yai ya nufi wutar dakin ya kashe sai ya rage sauran bed side lamp kawai, ya hau samna gadon ya kwanta ta bayanta sannan ya kashe bed side lamp din, gudu ya mamaye dakin gaba daya, baka hango haske sai ta gurin curtains din windows din dakin shi ma ba sosai ba domin curtains din masu kauri ne sosai. Bayanta ya fara kissing yana ta yamutsa gashin kanta na baya har gurin kiyar kanta yake kissing, saurin juyowa tai dan ya daina ashe bakinta ne abunda ya fi bukata a yanzu, a cikin hudun ya hade bakinsu yana sani irin jan numfashinsa yana fitarwa ita numfashin take ja ta fitar sai dai yana da banbanci da na shi nata na wahala ne da tsoro shi kuma na jindadi ne da samun abunda ka dade kana muradi. Jin wasansa zai fi karfinta yasa ta fashe masa da kuka, tun yana kissing din bakinta har ya sauko gurin wuyanta ya nemi masauki a kirjinta, duk inda ya rika a jikintan riko yake mata bana wasa ba, tun yana mata a hankali tana yin shiru tana amsa sakonsa dan dole har ya fara fin karfin kwakwalwarta, daman can haka yake idan yai marmari baya wasa da wannan babin.
“Aliyu dan Allah kai hakuri ka bari kaji Yaya Aliyu, dan Allah”
Juyar da ita yai ya kifar da ita yai karasa cire abunda ya rage a jikinta, tana ta ta yawo da hannunsa yadda yake so bayanta kamin ya juyo da ita. Jin yana kokarin kaiwa inda take jin ba zata taba iya barin kowa ya kai a nan ba yasa ta fara kuka kamar daman can ta tanadi kukanta ne kawai dan domin irin wannan ranar ta yau. Addu'a ya karanta sannan ya fara yi da kamar hankali kamin ya birkice mata, babu kalar kukan da batai ba tun tana kiran dan Allah dan Annabi har ta koma hada shi da Momy da Daddy, ta kira Nana can kuma ta koma tana hada shi da Mama Fulani amman sam baya ma jin ihunta balle har tausayinta ya shiga ransa, shi be tana tausayin mace a wannan bangaren ba.
Sai da yai kwanka sannan ya kwanta bayanta ya saka ta a kirjinsa ta bayanta ya rumgume yana jin sani irin son ta da kaunarta na masa yawu a zuciya da jiki da duka wani guri da jini da numfashi yake shiga. Kiran sallah asuba ya tashe shi sauka yai daga kan gadon ya kunna wutar dakin wanda hakan yasa Ataa ga bude idonta ta kalleshi, zuwa yai ya yaye blanket din jikinta sai ga babu komai a jikinta, daukarta yai ya shiga da ita bathroom ya hada mata ruwa mai zafi ya saka a ciki, kana ganinta kasan bata da wani karfi ko kuzari a jikinta, ba zancen kunya ko wani abun take a yanzu ba, ta wani zama kamar ba ita ba. A cikin ruwan ya barta sai da yaje masallaci yai sallah ya dawo sannan ya sake lekowa bathroom din sai ya sameta a cikin tana lumshe ido alamar bachin take ji har yanzu. Wani lausayinta ne ya kama shi ya san abunda yai ko Rahma tana kuka da shi wani lokacin balle kuma Ataa. Gashin kanta ya fara rikawa ya tufke mata shi guri daya sannan ya tambayeta.
“Kin iya wankan tsarki?”
Ta gyada masa kai.
“Waya koya miki?”
Ta daga hannu sama domin magana ma a yanzu wahala take mata.
“Mama (Nana)”
Ta gyada kai sai yai murmushi. Da taimakonsa tai wankan ta ya fito da ita da kansa domin shi kanshi yana jin ba zata iya tafiya da kafafuwanta a lokacin, babu tufafin a jikinta ya fito da ita ta zauna bakin gado tana ta natse kafafuwanta saboda azabar da take ji a guri har jin take kamar wani kwaro na mata motsi a gurin, duk inda wata halitta nata na jiki na musamman yake zafi yake mata kama daga kirjinta har zuwa kunkurunta da take jin kamar karewa zai yi idan ta mike tsaye, kasanta ma zafi yake mata na fitar hankali sai hade yawu take tana bin Aliyu da kallo duk inda yai har ya fita yaje ya dauko mata abaya ya saka mata da hijab gaba daya ta koma kamar wata yar baby. Shi ya shimfida mata carpet ya zauna ya zuba mata ido yana ta kallonta har tai sallah ta gama sannan yaje ya dauko kur'ane ya zauna kusa da ita ya kwantar da kanta a cinyarsa ya bude kur'anin ya soma karantawa da kira'a mai dadin sauraro. Tun tana jin kirara tasa har bachi yai gaba da ita, ya dade yana karatun sai da Rana ta fito sannan ya daga kanta a hankali ya aje kasa sai ta bude ido ta tashi zaune, maida qur'anen yai a muhallinsa sannan ya dawo ya miko mata hannunsa.
“Ta so”
Bata fuska tai ya tana kokarin gashewa da kuka, domin a tunaninta abunda yai mata jiya zai kara mata a yanzun ma. Dayan hannunsa ya sake miko mata.
“Ta so mana baby na”
Ta mika hannayen duka biyu ya mikar da ita tsaye sai ya tura jikinta zuwa gurin gadon bachinsa. Cire mata Hijab yai ya aje gefe ya rikata ya kwnatar saman gadon sannan shi ma ya kwanta yana kissing gaban goshinta.
“Hug me”
Ya fada jin ta yi shiru yasa ya sake cewa.
“Rumgume ni sai ki yi bachinki babu abunda zan miki”
Ba musu ta rumgumeshi ta shigar da kanta jikinsa ya runtse ido. Kwakwalwarta na tariyo mata abunda ya faru jiya, shi kanshi abunda ya faru yake tunani wani irin farincikin ne da nishadi a zuciyarsa da ruhinsa, ya sameta fiye da yadda ya za ci zai sameta ya jita fiye da yadda yake tunani a duk ma'aunin da zai aunata a zuciyarsa yanzu zai ga kamar ya rage mata matsayi ne. Saman kanta ya dinga kissing kamar wani mahaukaci ya kuma rumgumeta tsantsan a kirjinsa kamar yadda ta rumgume shi saboda kunyarsa da ta taso mata yanzu.
Na su yi bachin minti talatin zuwa arba'in ba door bell din falon ya fara kara alamar akwai mutum a waje. Bude ido yai a hankali ya sauka daga kan gadon ya sumbace kumatunta sannan ya gyara mata zanen ya lulllube abarsa da kyau sannan ya fito falo bude kofar ma a hankali yai kar kararta ta tashe ta. Siyama ya gani da wasu cousins sisters dinsa su hudu suna dauke da abinci.
“Ina kwana yaya? Momy ta ce akawo muku abun karya”
Amsa nata da dan murmushi a fuskarsa kamar yadda yai ma sauran sannan ha basu guri suka isa cikin fakon suka aje abincin a muhallinsa suka juyo suka fito da sauri kamar wadanda ake kora. Kulle kofar yai ya dawo dakin da ya bar Ataa sai ya same ta zaune tana hawaye.
Saman gadon ya hau ya raba kafafuwansa biyu ya saka nata a tsakiya ya matse fuskarta tana jin saukar numfashinsa yana jin nata.
“Minene?”
Kasa amsawa tai sai baya baya take har ya kwanta jikin gadon yai mata rumfa da kirjinsa, ya sumbaci hancinta kumatunta da kuma goshinta sannan ya sauka ya daga kan gadon, tufafin jikinsa ya cire a gurin which is normal for him indai a gaban matarsa ne zai iya kuma yana bukatar yin hakan a gabanta domin ta soma sabawa da halayensa sun yanzu, wanda hakan yasa ta saurin kawarda fuskarta. Yana gamawa da kansa ya janyota ya shiga rabata da gown din jikinta ita ko sai rokonsa take a zatonta yar jiya za a sake yi.
“Wanka za mu yi sannan mu ci abincin karyarwa”
Ya fada yana daukar tawul daya ya daura sannan ya miko mata dayan, kasa daura tawul din tai saboda ta nade a cikin blanket shi kan be bi ta kanta ba sai gai kamar ma be lura da abunda tai ba. Sai da ya fara shiga ya hada musu ruwan wankan sannan ya fito yana daure da tawul din ya bude blanket din ya fito da ita ta daga ta sama cak ya nufi toilet. A tare sukai wankan ba dan ranta ya so ba sai dan dolenta brush din ma sabo daya ya fasa musu sai da ya fara yi sannan ya wanke mata nata bakin, ya saba yi ma mace komai, dafa mata abinci, wanka, brush, kawo mata abincin da ba mai nauyi ba, bata ruwa and so on kuma be tana gazawa ko gajiyawa ba domin a gurinsa matarsa yar lelensa ce kuma yar gata ba yar wahala ba, Rahma ma yai mata balle Ataa da yake ganin yarinya ce ba komai ta sani ba ko ta iya. Tawul daya ya rage a bandakin dan haka ya daura mata shi ya fito a haka ha nufi wardrobe dinta ya bude ya fara saka boxer da vest sannan ya nufi madubi ya shafa abubuwan daya saba shafawa tare da tutaren jiki sai kuma ya dawo ya saka shadda da sauran abubuwa. Ko da ya juyo tana zaune bakin gadon ka ta a kasa, dan karamin tawul din a jikinta, fita yai zuwa dakinta ha dauko mata wasu riga da wando na yadi marar nauyi ya saka mata da kansa. Sannan ya juya ya tara mata bayansa.
“Hau muje falo mu karya”
ATAA POV.
“Zan iya tafiya da kaina”
Na fada ina dan turo baki sai ya ce.
“Bana son kina min gardama idan na ce ki yi abu ki yi kawai, ko ba a fada miki duk abunda na saka ki yi ba?”
“An ce”
Na fada daker.
“Then hau”
Ya fada yana hadawa da turanci, a dole na hau bayansa ya mike tsaye da ni kamar wata yar baby, sai da ya fara tafiya sai ya saki hannunsa a dole na kankanme shi da kafafuwa da hannuna gudun faduwa kaina kuma a bayansa ma lafe kamar maciji, dan Murmushi na ji yayi mai sauti sannan ya nufo falon da ni. Har gurin Dinning ya kai ni sai ya sauke ni tsaye yaja kujera ya zauna ya nuna min cinyarsa.
“Zauna a nan”
“A nan?”