Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 40
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 40: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 40. “Wow amman ka kyauta haba ni kan yanzu na ji magana, ina kuka hadu?”
4,040 words
“Wow amman ka kyauta haba ni kan yanzu na ji magana, ina kuka hadu?”
“A twitter muka hadu, har na je gidansu mun gaisa sau biyu ma”
“Mashallah tana dai son ka ko?”
“A yadda ta karbe ni kan ya nuna haka, Mama ai yana da wahala in shiga wani gurin ace ba a so na gaskiya”
Mama Fulani ta yi murmushi.
“Yanzu na ji batu za ka yi auren cire raini kuma auren da kai aure yanzu ka dawo cikin hayyacinka, Maryam Rukaiya ku fito ku ga kyakkyawa”
Mama Fulani ta karasa tana kwala musu kira. Rukaiyah ce ta fito yayinda Maryam ta ke can cikin daki abun duniya ya isheta saboda baikon da akai ma Humaira, gashi ita ce babba, wadanda suke warin Rukaiya ma Barula da Zee ta san na gaba kadan tsayar da mijin za su yi a barsu su kadai ita da Rukaiya a gida sai kuma kanensu kanana Baby da Inteesar. Da far'a Rukaiya ta sauka domin daga jin yanayin kiran Mama Fulani ta san wani abun ne ya samu, kusa da Muhseen da ke murmushi ta zauna tun kan tai magana Mama Fulani ta mika mata wayar tana dariya.
“Kin ga wacce yayanki ya dauko yar mutanen arziki”
Rukaiya ta karba tana wara ido.
“Wow amman wannan yarinyar akwai kyau ni kama na santa ma”
“Ba za ki rasa saninta ba tana da mabiya da yawa a twitter”
“Amman tana da kyau sosai gaskiya wane gari take?”
“Bauchi amman a nan suke zama Abuja tare da Babanta”
“Gaskiya Ya Muhseen ka dauko mai kyau”
Murmushin jindadi yai shi dai yana son ace ya auri mace mai kyau kuma yana son ya auri mace da idan abokansa da kowa na shi ya ganta sai sun sara mishi akan kyauta inda za a rika maganarta a duk inda ta wuce.
“Ita da Ataa wace ta fi kyau?”
“Haba dai ka sawo wannan kazamar yarinyar, wannan ai ta fita cika da komai wannan fa babban budurwa ce Ataa kuma yarinya karama da ita kuma ita Ataa yar ba yar kowa ba ce wannan ko yar masu abun ce, wannan ma ai har ta fi Ataa kyau sai dai kawai ace ita hancinta ya fi na Ataa kauri shi ma dan Ataa tana yarinya ne”
Wani irin dadi ne ya lullube Muhseen yana jin cewar yanzu kan yayi zabe kuma ba zai yarda ta subuce masa ba tunda har Mama Fulani tana sonta.
“Daman can fa akwai mata masu kyau saboda ba ku dubawa ne shiyasa ba ku san da su ba, yanzu ba gashi ba, shi ma Aliyu da be yi sauri ba da ya hadu da mai kyau ai wacce ta fi Ataa”
Mama Fulani ta fada.
“Amman ina magana Amina? Ba Momy ta ce ta baka Amina ba?”
Cewar Rukaiya tana kallonsa sai ya amsa mata kai tsaye.
“Bana son ta ana zancen mata masu mahaukacin kyau kya sako min Amina?”
“Aiko Amina na kyau Muhseen”
Ya kalli Mama Fulani cikin wacce tai maganar.
“Tana da kyau ai na sani, amman na irin wanda na ke so ba, ni na fi son mace mai kyau bala'i wacce kowa zai san na aura, wannan ma ba barinta zan yi ta dade ba kar wani yai min kwantar 6auna dan haka ku fara shiri tun yanzu, Mama kuma ki fadawa Abbah idan kun tattauna za mu yi can tsakaninmu”
“Karka samu damuwa Muhseen In-Sha-Allah sai ta aureka, ko nawa ake kashewa za mu kashe mu aurota”
Muhseen ya mike tsaye yana jindadin furucin Mama Fulani daman ya san zatai supporting dinsa tun da yar masu kudi ce, shi kuma ya samu kalar da yake so saboda tana da kyau shi daman kyau ne kawai abunda yake iya saka shi ya so mace. Ba ya jin zai dauki lokaci be yi auren ba kamar yadda ya fadawa Mama Fulani saboda ya cire haushi Aliyu ya nuna masa ya samu wacce yake so cikin kankanen lokaci kuma mai kyau kamar Ataa auren kece raini zai yi auren da zai amsa sunansa a garin Abuja.
Rukaiya ta tabe baki tana kallon Mama Fulani.
“Ai idan akwai irin wadannan kyawawan ba yadda za ayi maza su zo su ce suna son mu”
“Kin ji ki da wata magana, ita Humaira kyau ta fi ku ne? Kuma ai kyawawa ne kuma ko ba a son dan kyau ba a so ku dan kudin ubanku”
“Amman Mama irin yayan manyan amsu kudin nan ina ruwansu da kudin ubanmu? Ai suma cewa za su yi suna da kudinsu ko ubansu na su to miye abun so kenan?”
“Ai wani dan ace yar wani ya aura mace ko bata da kyau zai aureta, balle ki da kyau na ku, ku kwantar da hankalinki kuma na ku yana nan zuwa In-Sha-Allah, dan Humaira ta samu au sauran suna nan su ba a musu baikon ba kuma Humaira ce kanwarsu”
“Amman Mama kin ga Batula da Zainab fa yayan mutumen nan sun ce suna son su kin san ko ba abunda zai hana auren sai idan mazan ne suka fasa, azo a yi musu aure mu muna nan zaune”
Rakaiya ta karasa tana buga kafa kasa tare da bata fuska kamar za tai kuka.
“To laifin waye? Kullum kuna nan cikin gida ba fita ko yar kwarkwasar nan mai janyo hankali maza ba ku iya ba ai dole bakin jini yai muku yawa, ita wannan ba ta Twitter Muhseen ya fadu da ita ba? Ku da wani be hadu da ku ba? Amman kwaliya ma sai dai kawai ku shafa mai ba wani kwaliya”
“Su ma ai ba kwaliyar suke ba Wallahi har mun fi su kwaliyar arziki, amman gashi nan duk sun samu kuma ko kamin wacan na nijar din su zo ai kowacce sun tana da samarinta amman mu babu ko daya”
“To kwantar da hankalinki ai Abbah ku yace sarkin Agadaz zai zo ya duba kamfanin da kansa da wasu dabam da suke wani gurin kika sani idan suka zo ko wani ya ganku ya ce yana son ku, ku dai ku yi fata kawai Allah kawo shi lafiya kuma Allah ya saka su ce suna son ku kamar wannan family idan na samu ke ko maryam kuka shige ai shikenan na huta nikan tawa samu na hada surukanta da Sarkin Agadaz”
Rukaiya ta yi shiru ba dan maganar Mama Fulani ta kwantar mata da hankali ba sai dan babu wani abun da zata iya yi idan ma sun zo ba lallai ne su ce suna son su ba domin wacan zuwan ma ai ba su ce ba. Ita da Maryam wannan rashin manemi ya ishesu sosai suna damuwa da wannan matsalar domin ta nan kawai Allah ya rage su, suna ta iyaye a rayu masu hali ga family ta ko'ina ga ilmi kyau nan ma gwargwado suna da shi amman sun rasa manemi daga ita har yar'uwarta Maryam, ko an fara zuwa sai mutum ba zai dawo ba idan kuma haduwar online ce ma ba za a zo ba.
RAHMA POV.
Tana zaune falon mahaifinta kanta a kasa sai rabon ido take tana sauraren irin amsar da za su bata. Ba Mommy kadai da take mace ba har Daddynta yau haushinta yake ji na abunda ta fada taya suna fafutukar nema mata lafiya suna fushi da Aliyu akan abunda yai mata yanzu zata zo musu da wani zancen wai Aliyu ya kirata ya ce ta dawo dakinta?
“Idan ma da gaske ne, ai shi zai zo ya tafi da ke mana ba wai ya bugo miki waya ba, ke kike wahalar da kanki akansa shi yana can ya yi aure ya manta da ke ma”
Mommy ta fada a hasale.
“Ba kiji irin magiyar da yake min ba Mommy wannan yarinyar ya fada min hada shi Momy tai da ita saboda huce ta kaini yace min yanzu haka baya ma shiga dakinta, har da kukansa yana ta rikona na dawo”
Haka ta tsara karyar ta murje ido kamar gaske.
“Yana son ki dawo shine ba zai zo ya tafi da ke ba sai dai ki kai kanki? Wannan ai zubar da kimarki ne idan ma baki sani ba”
“Wai ba zai zo ba saboda abunda kikai wa mahaifiyarsa tace idan ya zo nan sai ta tsaba masa, auren ma duk itace tai ita da Mama Fulani saboda huce takaici har wani cewa suke wai na shanye shi”
“Ina kika ji?”
“Shi ya fada min jiya da dare a waya mantawa ma nai ban yi recording ba, da kunya har da kukan shi Wallahi”
Mommy ta nuna ta gatsanta.
“Ke tun kamin a haife ni na san wayo, ba zaki koma ba Matukar ba shi ya zo bikinko ki kuma sai mana alkawarin wacan ba zata takura miki ba, dan ba za mu zuba miki ido ki mutu ba, idan ke ba ki son kanki mu da muka haife ki muna son ki”
“Ai Wallahi wacan yarinyar har aiki ce aka kawo min shi ma ai ya fada, yace duk wani aiki na gidan ita zata rika yi, ni hutawa kawai yake son nai”
“To mun ji tashi ki tafi”
Haka ta taso cikin bakinciki rashin amincewa ta koma da iyayenta suka yi, yanzu kam bata san karyar da zata musu ba, sai dai ta kira Aliyu ta rokeshi akan ya yarda ya zo ya dauke ta idan ya ki zata ba shi hakuri ma, ita dai burinta kawai ta ganta a gida daya da Ataa yadda zata jidadij ci amata mutunci kuma kallon da kawayenta suke mata na mijinta yayi aure ya barta su daina shi kowa ya san cewa yar wanke wanke aka auro mata, ta san Aliyu ba zai hana ta ba, domin shi kanshi baya son talaka kuma ta san babu ta yadda zai iya zaman auren da Ataa balle har wata alaka ta hada su, tunanin sharing ma da gai na cewar abunda yake mata zai iya yi ma Ataa yanzu take jin cewar ta yi kuskure saboda Aliyu ba sa'an Ataa ne ba ko da wasa ba zai yarda ta zauna kusa da shi ba ma, a iya tunaninta a yanzu Ataa na can daki dabam shi kuma yana daki dabam, ko cewar da yai wacce zata kula da mijin kawai aka auro tana tunanin ya fada mata haka ne saboda ta ji haushi tunda ta tafi ta barshi. Ai da ta zumudin amarya yake da ba zai kirata ba, sai yanzu take jin bakinciki rashin daukar kiran da ba tai ba, wata kila ma hakuri zai bata kuma ya roki ta dawo dakinta ko kuma ya bukaci ta bashi dama ya zo ya tafi da ita, ta san irin rayuwar da suke da kuma yadda Aliyu yake da kyama da kin kula mata ba zai iya raba zuciyarsa da jikinsa wa mace biyu ba, mace ma kazama yar bara kuma yar aikin gidansa kamar Ataa.
“Hahaha yarinyar za ki ci ubanki ba dai mijina kika aura ba? Kina yar talakanki kika jawa kanki wahala Wallahi sai kin yi kuka da idonki kuma kin gwammace ba a taba halittarki duniya ba”
Ta fada yana shiga dakinta na da wanda ya kasance mallakin Muneera a yanzu, ita da Muneera suke sharing a yanzu. Gaban madubi ta zauna tana kallon kanta a madubi ta mika hannu ta dauki wayarta ta kira Aliyu, ringing biyu a na uku ya daga sai yai shiru yana jiran tai magana kamar yadda ya saba idan dai kai ka kirashi ba shi ya kiraka ba ko da ma shi ya kiraka idan uzurin naka ne kyalewa zai yi sai ka yi magana da kanka.
“Aliyu”
Ta fada a shagwabe tana tana wani cream dake gaban madubi.
“Ka kira ni jiya”
“Lafiyarki zan tambaya”
“Ka damu da ni kenan? Amman ka auro wata”
“Wata aba kanki take ba, ke ma kuma ba akanta kike ba, idan kina da wata maganar ki fada”
Kasa cewa tai ya zo ya je da ita ko kuma yai hakuri tana son har sai shi da kansa ya bata hakuri ko kuma ya roketa ta dawo da kanta idan ma ba zai iya zuwa din ba.
“Dear kina bukatar wani abun ne?”
“Aliyu ba zaka ba ni hakuri ba? Na zaka ce komai a auren da kai ba?”
“Ina nufin kina bukatar wani abun kamar na ci ko na sha ko wani abun daya shafi lafiyarki?”
Ta ji haushi a take ta kashe wayarta tana buga kafa kasa, ta san halin mijinta da jin kai ai, ba zai bata hakuri ba tun da yana ganin shi ne da gaskiya, amman zata jira har nan da sati daya ko biyu idan ya be ce ta zo ba ko be biyota ba zata share shi, balle ma tasan yana yin hakan ne kawai dan ya bata haushi kamar yadda yake mata idan yana fushi da ita a gida, ta san Aliyu can't live without her shiyasa ya turo mahaifiyarsa ta bata hakuri ta koma wacan karon duk kuwa da ya san yana da gaskiya, yanzu ma saboda abunda Mommynta tai ne da yanzu ya sake aikowa ko kuma ya zo da kansa.
ALIYU POV.
ya sauke wayar, ya amsa wayar a gaban Ataa ne saboda Rahma ta kira shi kamar yadda zai iya amsawa wayar Ataa a gaban Rahma saboda dukansu matansa ne kuma wani uzurin zai iya sakawa wata ta kira, da dai ba daga daga cikinsu ba ne, sai kuma Momy ko Mama Fulani Daddy Abbah, bayansu sai ya ga dama yake daukar waya idan an kira ko da yana waje balle kuma yana tare da iyalansa. Aje wayar yai gefena yana kallon Ataa wacce ke ta motsi kamar bata jin dadin zaman, ta turo baki sai hawaye take a hankali.
“Ba kya jinddin zaman ne?”
“Zafi ni dai har yanzu”
Ya san abunda take nufi sai kawai yai yar dariya, ya mike tsaye ya dauke ta ya nufi dakinsa da ita.
“So kike a kara kenan?”
“Wallahi baka da tausayi kai mugu ne”
Ta fashe da kuka.
“Ni ne mugun?”
Ya tambaya yana cige baki yayinda yake sauke ta saman gadon. Sai ta kara fashewa da kuka shi kuma ya saka mata dariya.
“Kin cika raki, ba da gaske na ke ba, ruwa zan hada miki”
Bandakin ya shiga ya hada mata ruwan zafi, ya fito yana fada mata
“Kullum ki rika yin tsarki da ruwan zafi”
“Wallahi ko wuta na saka ba zai daina ba, ni kaina na san zafin da na ke ji, har ya fi na jiya ma, kuma har yanzu bana iya tafiya daidai”
Ta fada tana wani irin shan iska saboda kukan ya mata yawa.
“Na lura ai ba zan sake ba”
“Har abada?”
Yayi wata mahaukaciyar dariya sannan yaja kunnenta.
“Yes har a bada”
Sannan ya fice daga dakin, falo ya koma ya zauna for a while sannan ya taso ya dawo dakin ya shirya cikin wasu tufafin, sai ga Ataa ta fito daga bandakin tana ta sauri.
“Ka ce zaka kai ni gurin Nana ko yau?”
“Ke fa baki da wyo ya za ayi Amarya da fita yau? Kuma da rana? Da ma da rana ne zan iya kai ki ki ganta sai dai kuma ba a yadda kike ba wannan abun kunya kawai zai sa na ji”
“Zan yi tafiya daidai”
“Ba kya iyawa ai, dole sai kin warke idan kin warke zan kai ki gida ki ga Mama da Momy”
Ya fada yana fesawa jikinsa turare sannan ya juyo ya sumbace ya saka bakinsa cikin nata bayan ya cire ya shafa kumatunta.
“I love you”
ATAA POV.
Da kallo na bi shi har ya fice sannan na zauna bakin gadon ina dan sake jikina ina hawaye, gaba daya satin haka nai shi cikin takura domin daga kafan da yai min na kwana hudu ne kawai, ranar da na cika sati daya ya kai ni da dare na ha Nana ranar ji nai kamar karna dawo gida, daker na shiga motar ina ta kuka yana jin ba dadi. Muna kama hanyar gida ya mika hannu ya rika hannuna yana ta murzawa a hankali, kamin ya kwanta da ni jikinsa.
“Ashe ba za ki iya zuwa wata kasar ki barta ba? Gashe na shirya nan da kwana uku za mu dawo mu musu bankwana mu wuce”
Ni dai ban ce masa komai ba sai kukan na ke a hankali, da gangan na feshe masa majigina a jikin shaddarsa na yi tunanin ko zai yi magana ne, sai dariyarsa na ji ya shafa kaina.
“Kurciyarki na burge ni, dan kin yi hakan sai na ji haushi? Ko na miki fada? Ai ko ba amarya kike ba bana da irin wannan rayuwar balle kina Amarya ai ba kyan laifi ko kin kashe dan masu gida”
Nan ma ban ce masa komai ba, yana rikw da hannuna yana watsa da yatsuna har muka isa gaban wani mai siyarda kilishin ya siya mana sannan muka nufi gida.
Kamar yadda ya fada after three days muka koma gida dan yin bankwana da Momy da kuma Nana akan tafiyar da zamu yi Los Vegas, ya bada dama na zabi kasar da na ke son muje amman ban xaba ba saboda ban san komai akan wasu kasashen ba ni dai burina kawai na hau jirgi na san na taba hawa jirgi ko da sau daya ne a rayuwata. Rabar a gida na wuni a nan Nana take labarta min cewar ai kullum a falon Momy take wuni su yi fira saboda kadaici wani lokacin kuma idan zata kwanta Momy na turo mata Amina ko Husna su kwana tare, wani lokaci kuma ita kadai take bachinta. Na jidadin yadda Momy take kula da mahaifiyata sosai, ita kanta tana jindadin haka. Washe garin ranar muka wuce Abuja daga sokoto, Nasir ne ya hada mana komai a yadda na lura Aliyu be fada min ba, amman na lura da yawan kiransa da yake ya tambaye ni ko shi abu har tafiyar ta hadu. Ya fada min bankwana zai yi ma Mama Fulani sannan mu wuce Lagos domin daga can ne jirginmu zai tashi, be takura ni kan cewar sai yaje da ni na ga Mama Fulani ba ko kuma yi mata bakwana, ni kuma hakan ya fi min sauki da dadi, ko ba komai bana son ganinta ita da Muhseen duk kuwa da ba ni da tabbacin ko zamu tarar da shi a gidan, kwananmu daya a Abuja sannan muka wuce lagos. Daga lagos jirginmu ya tashi da ina ta jin tsoro kamar yadda nai a lokacin da zamu taso daga sokoto zuwa Abuja da kuma zuwa lagos din, domin yadda na ke tsammani da marmarin jirgi sai na tarar ya fi karfin tunani da kuma hankalina, a lokacin da zai daga kana jin motsinsa sosai idan kuma zai sauka kana jin motsin dirarsa a kasa, sai dai idan kana sama baka ma gane tafiya ake sai idan kana kusa da windows, Aliyu a gurin windows ni kuma ina gefensa ya jingina na ni da jikinsa yana ta nuna min kasashe ta cikin wata yar karamar kwanfuta dake lake bayan kujerar da ke gabanmu, da map din yake fada min yanzu muna guri kaza, wani dan biscuit ne aka kawo mana da tea shi kuma ya ce coffee yake so, bayan mun gama sha wata mai uniform ta zo ta dauke sai Aliyu ya sake maida ni jikinsa yana ba ni ragowar biscuit din da ya dauka a plate din a baki ina ci a hankali kamar wata jaririya har bachi yai gaba da ni.
*Khadeeja Candy* Mun sauka a gajeye domin tafiyar jirgin ta dauke mu awanin masu yawa, na yi zaton idan mun sauka can dare zan gani ko yamma amman sai muka samu safiya ce da alama akwai banbanci yanayi da kuma lokaci. Muna fitowa daga cikin jirgin Aliyu ya cire jacket din jikinsa ya saka min saboda yanayin sanyin garin, daman doguwar riga ce a jikina sai dan karamin mayadi daya rufe iya kaina ya sauko zuwa wuyana kadan. Kasa ce ko kuma na ce gari domin tun a jirgi Aliyu ya fada min cewar ba kasa ce gaba daya ba, gari ne dai kamar yadda kasata take nigeria da gari kala kala. Garin da zan iya kira da kasa, kasa ce yanayi mai kyau mutane kowa hada hadarsa yake babu ruwan kowa da kowa ga bin ka'idodi da dokoki ba kamar kasata nigeria ba, hannu ya daga sai ga texi ta zo ya bude min na shiga sannan aka saka kayanmu a bayan motar shi ma ya zagoyo ya shiga inda na ke, ya jani zuwa jikinsa. Ni kan idona na can jikin windows ina ta kallon tituna da kuma manyan binaye da kwaliyar garin gwanin sha'awa har muka isa wata kyakkyawar hotel mai haske da dagon bene mai kyau da daukar hankali. Na yi zaton irin kudin kasata zai bawa mutumen a lokacin daya ciro wallet dinsa, sai ga shi na ga wasu kudin ne dabam ba irin namu ba. Bayan ya gama mika masa kudin ya kama hannu muka shiga cikin hotel din shi kuma yana janye da luggage. Da yalshen nasara yai magana da su ya mika musu wani dan karamin kati da nake zaton na banki ne kamar yadda ya fada a lokacin fa yake nuna min passport din da akai min a gida Nigerian a gurin jami'in immigration da ke sokoto, da kuma na dan kasa da shi ma ya saka aka min, mayar masa da katin sukai su ka bashi wata yar takardar da makulli sannan ya juyo muka nufi wani bangare na hotel din, wani gurin ya taba sai wani dan daki ya bude mana mai kamar kumbu muka shiga ni da shi sannan ya taba wata number sai abun ya rufe ya fara tafiya da mu sama, shi kuma ya ciro wayarsa yana ta daukata hoto har muka isa abun ya bude muka fita, ni dai ina rike da hannunsa gaba daya tsoro ya gama kamani domin na lura da gurin tsif yake kamar babu kowa ga shi dakuna ne aka jera masu yawa sosai ko wane da number shi, numbobin dakunan ya rika dubuwa har muka isa gurin wanda aka ba shi key sa, budewa yai ya ya fara shiga sannan n shigo, an share dakin fes kamar wani ne a ciki komai a tsara shi gwaninb sha'awa, ac dakin ya fara kunnawa da wuta sannan ya maida kofar ya rufe ya aje kayanmu a gefen gadon. Bandaki ya shiga yai wanka da alwala ya fito sannan ni ma na shiga, bayan na gama wankan na nufo kofa abunda ban sani ba ashe Aliyu yana nan jikinn kofar labe yana jiran fitowata ina budewa sai yai cikina yana bani tsoro ai ko da gudu na koma ciki sai da yai saurin shigowa ya dauko ni ya fito da ni. Kuka na saka masa na buge masa fuska sai ya aaka min dariya wai daman ya lura da ina jin tsoro. Sai da muka lissafa sallah da ba mu yi tsakanin tasowar mu daga can zuwa nan muka rama su sannan muka dora da suba din da muka tarar a garin. Bayan mun gama ya taba telephone din gefen gadon yai magana, ba bata lokaci sai ga wani mai uniform ya kwankwasa kofar dakinmu ya miko mana abinci, Aliyu ya karbo ya kawo mana komai a cikin kwali yake sai wata yar miya ce a cikin kwankwa mai shegen ja. Ni dai ban iya cin wasu abubuwan saboda ban saba ba ban ma tana ci ba, Aliyu kan cin abunsa yake da alama ma sun fi masa dadi. Pizza na ci da shawarma sai kuma miyar da na lasa kadan sai na ji bata min dadi ba. Bayan mun gama mu kai hauk gado mukai bachi gajiya ni da shi, yadda na ke kwana a jikin Nana haka na kwana a jikinsa, ko da muka farka lokaci ya ja sosai bayan mun yi sallah ya cire layin wayarsa ya saka wani layin dabam ya kira Momy yace ta kaiwa Nana muka gaisa sai kuma Mama Fulani ita ya kirata ta daga ya fada mata ya isa lafiya.
“Miyasa ka canja liyin?”
“Ai na nigeria baya yi a kira shi a wata kasar ko wace kasa da kayinta, daman na dade da siyen wannan ba yau na fara zuwa kasar”