Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 42

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 42

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 42: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 42. Aliyu be gama rufe ba ki ba, sai ga daya daga cikin jikansa ya fito…

4,497 words

Aliyu be gama rufe ba ki ba, sai ga daya daga cikin jikansa ya fito yana fada min Mai Martaba na son ganina. Da sauri na mike tsaye sai Aliyu ya rikani domin bana iya tafiya da sauri jikina kuma ba karfi ga jiri na dibata, daf da zamu shige bangaren Abbah muka ji tsayarwar mota, sai na waigo na hango Muhseen ya fito daga motar da waya a kunnensa, ni kuma na juyar da kaina muka shiga cikin falon, wannan karon babu kowa a ciki sai shi kadai da jikokin nasa. Daga bakin kofar Aliyu ya tsaya ya bar ni ni na wuce can ciki. Kasa na zube kusa da shi na zauna yana ta kallona a hankali ni kuma nai fuskar tausayi ya langwabar da kaina ina kallon kasa.

“Ina Asma'u take?”

“Tana sakkwato”

Na amsa mishi da sauri cike da kaguwar jin abunda zai sake fada.

“Ta fada miki dalilin rashin danginta a kusa da ita?”

“Ta fada min kuskuren da ta aikata, kuma ta yi nadama sai dai ta ce ba zata koma gareka ba har abada saboda abunda ta aikata maka, ta ce ta saka masarautarsu a kunya, da maka butulci ba zata sake dawowa gareka ba saboda ba zaka taba gafarta mata ba, ta yi kukan rashinka ta shiga matsalolin rayuwa ta rasa muhallin zama da abun sakawa a baki saboda butulcin da tai maka, a cikin abubuwan da ta rasa mai martaba har da lafiyarta, kuma ta alakanta hakan da butulce ma iyayenta da tai, a kullum tana fada min rayuwarta ba mai tsawo ba ce ta min umarnin na nemi danginta bayan rayuwarta kuma na roka mata gafararka da na su, ta haife mu ni da kanena shi ma har ya rasu gurin bara be san ka ba, tana bakincikin gina wata rayuwar ba tare da kai ba, da ni da ita duka rayuwarmu a titi ne sai mun yi bara muke ci, gidan kuma za mu kwanta sai dai mu raba a gidan wasu mu kwana”

Tun da na soma maganar yake ta jinke hannusa da sandar da ke hannun nasa, da alama maganganun da na ke masa sun taba masa zuciya ko kuma basa masa dadi.

“Ina Umar?”

“Ya rasu, Nana ce kawai ta rage sai ni”

Na fada cikin kuka, sai ya mika hannunsa da sauri jikan nasa ya risino yana sauraren maganar da ke fitowa daga bakinsa kadan-kadan.

“Ta fada muku inda Asma'u take ku je ku taho da ita”

A take ya karaso inda na ke yana tambayata da yarenmu.

“Ina Asma'u take?”

A take na fada masa, sai ya fice daga falon.

“Tashi kije ciki zan je masaukina”

Mai Martaba ya fada min, sai na mike tsaye ina jin kamar kar na tafi na fito daga dakin, sai na samu Aliyu a tsaye yana jirana.

“Kin yi magana da shi?”

Ba gyada masa kai.

“Eh yace zai je masaukinsa”

“To muje ciki ki huta”

“Mama Fulani ba zata bar ni na shiga dakinta ba, na kai ni gurin Ammy”

Na fada ba dan ina da tabbacin Mama Fulani zata hana ni shigar ba, sai dan na fi son Ammy da ita kuma zan fi sakewa a can. Be min musu ba ya gyada min kai sannan muka sauko tare muka nufi bangaren Ammy. Muna shiga falon Zee da Humaira suka fara min sannu na amsa musu har da Inteesar da ke ta daukin ganina.

“Ataa mun yi missing dinki sosai”

Ban ce mata komai ba bayan murmushin karfin hali da nai mata, sai Aliyu ya kalli Zee ya ce.

“Zainab kwantawa za tai a dakinki kar motsi ko wani hayani ya tashe ta dan Allah”

“Okay ya Aliyu”

Ta hannu yai min alama da na wuce sai ya bi bayana, har muka shiga dakin saman gado na haye abuna sai ya dauko filo ya dora min a gurin kafafuwana sukai sama.

“Sannu”

Ya fada yana taba kaina.

“Na gode”

Na fada ina kallonsa da fafaren idanuwana.

“Amman Babyna da gaske mahaifin Mama ne? Hakan na nufin kakanki ne kenan?”

Na gyada kai. Mamaki ne karara a fuskarsa kamar zai sake tambayata sai kuma yai shiru ya zauna gefen gadon kusa da ni.

“Akwai abubuwan mamaki a wannan maganar ta ki, amman lafiyarki ta fi muhimmancin a gareni, runtse idonki ki ja numfashi da karfi ki sauke a hankali ki saki tunaninki za ki samu bachi yanzu nan”

Yadda ya fada min haka nai a take kuwa bachi yai gaba da ni daman bachin ne a ido na.

ALIYU POV.

yana ganin ta yi bachi ya taso ta baro mata dakin tare da jan kofar a hankali ya kulle, part din Mama Fulani ya dawo a inda ya same ta cikin falon ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana ganinsa sai tai saurin zaunawa tana kallo kofa ko zata ga Ataa ta shigo, da ta bata shigo ba sai tai kasa da murya kar wani ya ji kamar ba daga ita sai shi ne a falon ba.

“Aliyu na ce wai ita wannan Ataa daga ina take? Na ga ta rike kafafuwan sarkin Agadaz tana kuka suna buranci, na ce ko ta masa aiki ne a can kamin su dawo nan da zama?”

“Aa ta fada min cewar kakanta ne shine ya haifi mahaifiyarta”

Mama Fulani ta daki kirji tana zaro ido.

“Kakanta? Kaka kaka kaka fa? Kakanta fa? Ai idan mai fada ba shi da hankali mai ji yana da shi”

“Amman Mama Ayusher ba zata min karya ba”

“To ni kuma sai na yarda tunda gani fulanin mahaukata ko? Yarinya yar titi yar bara rana daya zata ce ita jikar wannan mutumen ce sai kuma sai na yarda ko? Jikarsa zata zo ta mana aiki? Har tai bara? Na yarda dai ta masa aiki a can Masautarsu, oh na ma tuna ina jin babarta baiwa ce su bayin Masautar ne”

“Wata kila kuma da gaske take yi Mama, tun da har kika ga ya kyaleta kuma ya aiko a kira ai kin san yana da alaka da ita, kuma bana zaton Ayusher zata karya, wata kila wata kaddararce ta saka suka tsinci kansu a cikin wannan halin rayuwar”

“Uhm Aliyu baka da wayo wallahi taya za 'ayi tana jikar sarki ta zauna a nan ko tai bara? Ai da kowa sai ya jiya, kuma ko dukansu yake kullum sai sun zauna a inda yake, yanzu ma ina ga aiki suka masa ko kuma bayin masarautar ne shiyasa lokacin da ta ji sunansa hankalinta ya tashi ita dai ta ganshi”

“Ko ma minene dai za a warware shi very”

Mama Fulani taja wani dogon numfashi ta sauke tana girgiza kai.

“Kai ba haka ba ne, sam ina... Ba za zai yiyu ba”

Ta kasa yarda da abunda Aliyu ya fada mata taya ma zata yarda wai wata Ataa jinin wannan sarkin ce. Sai dai wani abun amman bata yarda ba, Aliyu ya mike tsaye ya nufi kitchen kenan sai ga Abbah ya shigo yana gyara babbar rigarsa.

“Hajiya Fulani za mu je sokoto yanzu nan”

“Sokoto kuma? Gurin me?”

“Mai Martaba ya ce aje a dauko masa mahaifiyar Ataa, da jirginsa da ya zo da shi za a aje kin ga ko tunda gida ne ai da ni za a aje”

“Mahaifiyar Ataaa?”

Ta fada tana dukan kirjinta har da wani kashe ido take.

“Mahaifiyar Ataa fa kace Alhaji?”

“Eh ita fa kin san tana gidan Momy”

“To ina jin wata babbar sata suka masa lokacin da sukai zama gidansa, ina lokacin da suke bayinsa sun masa wata katuwar sata ko kuma hasara, shiyasa Ataa take kuka tana rike kafafuwansa so take ya yafe musu”

Mama Fulani ta fada tana gyada kai.

“Amman abunda shi jikan nasa da suka zo tare yake fada mana wai Mahaifiyar Ataa ita ce yar Mai martaba”

“Aehhhh ya fa ka ce?”

Ta tambaya da karfi tana zaro ido.

“Eh Wallahi ni kan na ce ai sun warke”

“Aa ba wani zancen warkewa ina jin dai yana nufin yarsa ta gari tun da shi sarki ai baban kowa ne, balle mutane masu nijar kasan yadda suke da junansu”

“Ko ma minene dai ai shi Mai Martaba zai fada da kansa, yanzu haka har ya wuce gidansa da ke nan yana jiranta, da ko be yi niyar zuwa gidan ba hotel ma zai sauka ni ne dai na dage ya sauka a nan ashe kin ga abo ne,sai muj dawo”

Abbah na fadar hakan ya juya ya fice da sauri. Mama Fulani ta rumfume hannayenta a kirji sai girgiza kai take.

“Aa ina ai ba zai yayu ba sam”

Duk abunda suke Aliyu na jikin kofar kitchen din rike da ruwa yana sha, shi kanshi mamakin abun yake ya san Ataa ba zata masa karya ba, kuma yadda ya ga Sarki ya nuna mata kukarwarsa ya san dole akwai alaka mai karfi a tsakaninsu, gashi kuma yanzu har ya ce aje a taho masa da ita, sai dai be san taya ta bar gidansu ba mi ya faru har suka tsinci kansu a cikin wannan rayuwar.

Gaba daya Mama Fulani kasa sukuni tai zuciyara na son yarda kuma tana jin yarda idan ta duba wasu abubuwan da suka faru, abun na ta cinta kamin su Abbah su kai har ta kira Momy ta labarta mata abunda ya faru, ita ma kanta Momy ba karamin mamaki tai ba jin abun kai tsaye kamar daga sama a take mamaki ya cika ta. Bayan ta gama da Momy kuma ta koma tana tatauna maganar da su Maryam da Rukaiya Maryam ce tai saurin yarda yayinda Rukaiyah kuma ta tsaya kwankwato.

“Idan kuma da gaske ne fa Mama? Kina ganin da ba jikarsa ba ce zai kyaleta ta rike masa kafa kuma tai ta masa kuka haka har kuma ya ce a aje a dauko masa mamanta? Gaskiya ina ganin gaskiya ne”

“Ai sarakuna suna da wannan karancin, kin san ai wasu suka rika kafafuwan manyan mutane saboda neman gafara ko kuma tubarraki, amman ba gaskiya ba ne”

“Gaskiya ni ma ban yarda ba, ai ko da mai unguwa kake da alaka sai an ji balle kuma mutum irin wannan, ai ko kama ma ba su yi ba”

“Eh ba su da kama fa, yauwa Rukaiya ashe kin gane, ina jin dai ba yin sa ne ada can da”

Haka sukai ta tattauna maganar a tsakaninsu daga Mama Fulani har Maryam da Rukaiya da kuma Baby wacce bata ce komai ba mamaki suke suna Ala ala abun ya zama ba gaskiya ba. Aliyu kan yana ta an ya tare a bangaren Ammy yana cin abinci shi da matarsa wacce bata dade da farkawa ba. Ya jidadin yadda ta farka zazzabi ya sauka duk kuwa da kasancewar bata sha magani ba a lokacin da zata kwanta.

ATAA POV.

Na farka da tunanin Nana a can cikin mafarkina kuma abunda ya faru dazun nai mafarki, babu komai a raina sai son ganin irin yadda Nana za tai idan ta ji cewar na hadu da Babanta ko kuma Mahaifiya ce aje a taho da ita. Ina ma ace ina can na na ga irin kukan farinciki da za tai da kuma irin rudewar da za tai. Ina cikin wannan tunanin Batula ta shigo sai nai saurarin share hawayena.

“Ya jikin”

“Na ji sauki”

Na amsa har lokacin hawaye na sauko min.

“Ya Aliyu ya ce na tashe ki ki yi sallah magariba ki ci abinci idan zazzabi be sauka ba za ku je asibiti”

Sai da tai maganar na tuna da cewar da yamma na kwanta, ashe har magariba ta yi ban sani ba, lallai na dan yi kwanan da nauyi.

“Ki fada masa na ji sauki”

Na amsa ta ina gashi na nufi bandaki da yin alwala so na ke nai sallah sannan na saka Aliyu ya kira min Momy ta bawa Nana mu yi waya, na fara yi mata wannan albishir din kamin kowa ya mata domin an san ba za a je daukarta a yau ba idan ma anje yau sai gobe za su iya ko kuma cikin dare, waya sani ma ko za su tsaya tsaya jiran jirgi kuma ace babu jirgin sannan na da wasu hours. A gagauce nai alwalar ina fitowa sai an samu Aliyu zaune a kasa Inteesar na jera mana abinci shi kuma idonsa na kaina kamar zai cinye ni.

“Ya jikinki”

“Na ji sauki, Aliyu idan mun yi sallah za ka kira nin Nana?”

“Yes amman sai mun fara cin abinci tukuna”

hijab din Zee na saka nai sallah har yai na gama na yi addu'a idon Aliyu na kaina, kamin na juyo har ya bude fular tuwon ya soma zubawa a a plate, ina juyowa ya saka spoon ya fara diban abincin ya bani, kadan kadan na ke ci saboda warin miyar nake ji daker ma na ke iya hadewa a take warin manjan ya daki hancina sai na ji kamar zan yi ama da sauri na rufe bakina na nufi bandaki, shi kuma ya taso ya biyoni ina sheka aman yana shafa bayana yana min sannu cike da tausayawa.

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.* *Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.* Sai da nai aman na gama sannan ya zuba min ruwa na wanke baki ya fito daga bandakin. Inda na aje Hijab din dazun ya nufa ya dauko ya zo kusa da ni yana kokarin saka min.

“Saka muje asibiti”

Na bata fuska domin har ga Allah bana jin komai a yanzu, bana jin wani ciwon kai ko wani jiri da zafi jikin kamar na dazun.

““Wallahi bana jin komai Aliyu, aman ne kawai kuma shi ma saboda miyar ne”

“Wani abu kika gani a ciki?”

“Aa bana son miyar ganye dai?”

Fuskar mamaki yai ni kaina ina mamakin kin shan miyar ganye da na ke bayan tana cikin miyar da na ke so, gudun kar Aliyu ya zargi ko bana son cin abincin gidansu ne yasa na ce.

“Ba komai yanzu ai na daina jinsa, daman warin manja ne kuma ya daina”

Na nufi gurin kular abinci na zauna ya saka hannu ina ci ahankali iyakar dauriya nayi domin har ga Allah yau dai bana son warin manjan nan a kusa da ni wata kila saboda zuwan da mu kai a Las Vegas ne dan sabon da nai a can na wata daya yasa na fara mantawa da abincin naija.

“Aliyu ina son tea”

“Okay”

Ya tashi ya fice rike da wayarsa, yana fita nai saurin nufar bandaki na amayarda da dan abunda na ci na tuwon na wanke bakina na dawo, jinginawa nai da gadon, ina ta tunanin Nana da yadda za tai idan tai arba da mahaifinta. Ba a wani dade ba sai ga Aliyu ya shigi dauke da mug ya zauna kusa da ni ya kai min tea a baki, kadan na kurba shi ma na ji bana sonsa kuma bana son na nuna masa kar yace dole sai munje asibiti, a dole na daure na hanye rabin myg din sannan na kawar da kai sai ya aje kofin ya janyo ni jikinsa ya kwatar ya ciro wayarsa yana lasawa.

“A kira miki Nana ko?”

Na gyada kai. Be ce min komai ba sai da ya kira Momy suka gaisa ya bani muka gaisa sannan ya sake karba ya ce ta bawa wani a kaiwa Nana wayar ina son magana da ita, yana rike da wayar har aka kai mata ina jin lokacin da suke gaisawa Aliyu har wani kasa yake da kai kamar ba shi, lokacin daya miko min wayar sai ya tashi ya fita daga dakin ya bar ni kadai.

“Nana kina nan lafiya?”

“Lafiya kalau kun dawo lafiya?”

Ina jin yanayin muryarta na san ba kafiya ba, muryarta ya nuna tana cikin damuwa da kuma alamar kamar ta yi kuka ma.

“Lafiya Kalau, Nana mun dawo muna Abuja”

Ta yi shiru bata ce komai ba.

“Nana na hadu da Mai Martaba Sarki Agadaz”

Nan ma bata ce min komai ba.

“Nana”

“Naam”

Ta amsa min cikin kuka.

“Nana kike yi?”

“Idan ban yi kuka ba Ataa mi zan yi? Yanzu haka Yayan yayuna suna nan tare da ni gobe tun da safe sun ce za mu wuce Abuja shi ya bukaci a azo da ni”

“Nana har sun iso? Na dauka ma ba ki ji ba”

“Da yamma suka zo, amman har yanzu ina ta ganin kamar ba gaske ba, wata kila sai idan na yi arba da shi zan yarda, wata kila ya yafe min wata kila kuma wani abun ne dabam zai fada min, hakika ina kaunar haduwa da mahaifina ina kaunar saka shi a ido ne ko da kuwa idan na je tsine min zai yi, amman Ataa har yanzu ina jin kunya da nauyin abunda na aikata”

“Wannan na wuce Nana, ba a iya gyara abunda ya riga ya bace sai dai a tari gaba, ni kaina ina fatar kuma ina tunanin yafiyarce domin ya kirani da jikarsa, jininsa diyar diyarsa, Nana na jidadin ganinsa ko da kuwa wulakanta ni yai ya tozarta ni zan yi farincikin ganin Kakana bayan ke da Lukman da Baba yau ba kara ganin wani wanda yake jinina”

“Allahu Akbar”

Shine abunda ta fada sai ta fashe da kuka ni ma kukan na ke, mun dauki tsawon lokaci a haka sannan na sauke wayar jin kamar kukan zai yi ma Nana yawa na aje wayar kasa ba tare da na kashe ba. Bayan sauke sallah isha'i Aliyu ya dawo dakin ganin yadda fuskata da ido na sukai ya san kukan nai daman haka na ke idan nai kuka abun baya boyuwa ga farin daya mutum.

“Idan har Mahafin Nana ne suka hadu da shi kamar yadda kika fada be kamata ace kina ta damun kanki da kuka kamar haka ba, a tunani farinciki ya kamata ki yi”

“Wani farin cikin Aliyu ya yi har sai an koka, taya kake tunanin mace da aka haife ta tun davta tashi bata san kowa na ta ba, rana tsaka ta hadu da kakanta kai tsammanin murna kawai za tai? Mutumen da ganinsa a tare da Nana shine yankewar zubar hawayenta kuma farincikinta, idan har zai yafe mata ya karbe a yadda take yarsa Aliyu ni ma zan koma ya kamar kowa, mai gata ba kuma gata na naira ba gata na yan'uwan uwa da na uba a tare da ni”

Zaunawa yai kusa da ni daman tun da muke maganar a tsaye yake ni kuma ina zaune saman carpet din da nai sallah.

“Kin ce ba ku da kowa a nan, kin ce ba ki san kowa na ki ba tun da aka haife ki, taya kika gane cewar kina da alaka da wannan mutumen? Babyna mi ya raba ku da danginku? Na dade ina son nai miki wannan maganar amman tunanin sakaki a damuwa ko Mama (NaNa) yasa ban cika damunki ba, kuma ina da burin ko da tsawalla miki da sanin hakan sai na aureki saboda kar na ji wani abu da zai iya zama sanadin da wani a familynki ko nawa zai iya hanani aurenki, na aure ki ba tare da sanin kowa na ki ba sai dan nuna miki tsantsar kauna ni da Momy, Wallahi Ayusher ko da daga sama kika fado zan aureki ba tare da damuwa ba, saboda ke na ke kauna ba wani abun daya shafi dangantarki ba ko kuma asalinki”

Kallonsa na ke hawaye taf a idona wata irin kalar kaunarsa da begensa ne ke shiga cikin raina. Hakika Aliyu yayi min abunda ba kowa ne ke yi ba, auren mace da baka san asalinta ba, ko da dan kyauna Aliyu ya aureni yayi min hallacin tun da be taba bayyana hakan ba ya bari a cikin ransa kuma be taba nuna min ba.

“Ko da ka tambaye ni asalina a wacan lokacin ko kuma anan gaba idan har wannan abun be bayyana ba, ba zan iya fada maka ba, saboda bana son bayyana abunda Nana ta fada min a matsayin sirrin wanda na san jinsa a gurin wani zai iya haifa mata da matsala ko kuma damuwa”

Hannunsa ya kai ya riko nawa.

“Kina da karancin shekaru amman kina da wayo da hikima akan dukan abunda ya shafi mahaifiyarki, hakan na da kyau kaunarki na ta karuwa a raina ta ko'ina”

Dan murmushi nai ina hawayen da suka ji su tsaya min. Sai ya jani jikinsa ya rumgume ni kuma na lafe abuna kamar ba a bangaren Ammy muke ba, domin na fara sabawa da yanayinsa a yanzu.

“Ba ni labari ya kai Mama ta rabu da danginta”

Kamar mai karanta labari haka na jera masa yadda komai ya faru kamar yadda Nana ta fada min. Ya tausaya mata matuka kuma ya nuna min jindadinsa da gwarin guiwar cewar Mai Martaba sarkin Agadaz zai yafe mata ta koma cikin danginta ni kaina na tabbatar da hakan domin na lura da yadda ya nuna damuwarsa da ita.

“Za mu je mu yi ma Mama Fulani sallama sannan mu wuce gida”

Kasa nai da kaina alamar bana son zuwan can. Sai ya mikar da ni tsaye.

“Babyna no matter what Mama Fulani zata miki dole ne ke yi respecting dinta matukar kina respecting din Momy da kuma ni”

Ban ce masa komai ba, domin ba zan iya fadar wata mummunar kalma akan babban mutum kamar mama fulani ba, ba kuma zan iya aibanta dan'uwan Aliyu a gabansa ba, saboda mijina ne kuma ya nuna min kauna be kama na ci zarafin wani dan'uwansa a gabansa ba ko kuma na fadi wata maganar wacce zata sosa masa rai, duk kuwa da kasancewar ban san alakar da ke tsakaninsa da Mama Fulani ba, ba zan taba son Mama Fulani ba har abada saboda irin kiyayyar da ta nuna min da kyama ita da yayanta sai dai hakan ba shi yake nufin na nuna a gaban Aliyu ba, taya zan kauna ci macw da ya kirani da mahaukaciya, mayya, yar talakawa, yar matsiyata, tai min korar kare a gidan nan, ta hanani taba abun gidanta abinci ma sai da na tara dankwalina ta zuba min, daga baya ta ware min komai nawa dabam kamar wata karya, matar da ta mareni na suma saboda kawai ina rokon ta bar ni na yi mata aiki ta biyani na nemawa mahaifiyata magani? Har abada kuma har duniya ta hade ba zan taba manta wannan ba.

Ba ni da zabi daya wuce na bin umarninsa, a dole na bi yo bayansa muka fito tare daga dakin Zee muka sauko kasa inda Ammy take zaune, gaba dayansu kallona suke har Ammy irin kallon na kamar mamaki.

“Wani sakamako sai Allah Aliyu, ka auri yarinyar ba dan ka san kowa nata ba, ba dan komai na ta ba, sai ga shi Allah ya maka sakamako da inda baka yi tsammani ba, hakurin da kai da zama da Rahama Allah ya baka wacce ta fita komai”

Kamar yadda suke mana kallon mamaki haka ni da Aliyu muke musu shi jin irin maganar da ke fitowa daga bakin Ammy. Zaunawa Aliyu yai a kujera ni kuma na zauna kasa inda Humaira take zaune kasa.

“Shiyasa ba a son ka wulakanta mutum ba ka san abunda zai zama ba nan gaba, kuma ba kasan da inda zai iya taimakonka ba, ba dole sai babban taimako ma wani ko alfarma yai maka ya baka ruwa ka sha ai ya jidadin a lokacin da kake jin kishi, waya zai tsammanci ke din jikar babban mutum ce, har ki yi aiki a gidan nan? Ni abunda ban gane ba wai kin san cewa Sarki Agadez Kakani kuwa ko kuma sai yau? Abbah ku ma daya fada min wannan maganar shi kanshi mamaki yake domin abun ya dore masa kai sosai”

Ammy ce dai take wannan maganar tana ta kallona. Aliyu ya kalleni sannan ya sake kallonta ya ce.

“Ta sani, amman ta yi shiru saboda mahaifiyarta bata son maganar”

“Mahaifiyarki ta yi dacen ya Ataa, da baki gudu kin koma cikin dadi kin bar a nan ba, da kuma ba ki saka mata ido har ta wulakanta ba Allah yai miki albarka”

Gaba daya suka amsa da amin, ni kuwa tawa amin din a zuciya take, ina jindadin Ammy tun a wacan zaman da nai tana nuna min kauna bata taba nuna min kyama ko kyara ba kamar Mama Fulani, haka ma Muhseen be taba kyamata ba shiyasa na kasa mantawa da shi a zuciyata halinsa kamar na Ammy ne idan ma ba dan fuskarsa da sanin cewar Mama Fulani ce ta haife shi ba idan ka ganshi zaka tsammaci dan Ammy saboda yanayin halinsu na far'a da son mutane ga kuma marhabun da kowa. Misalin tara da yan mintuna muka fito daga bangaren Ammy muka nufi bangaren Mama Fulani, kamar yadda nai wacan karon wannan karo ma baya baya na tsaya Saboda tunanin irin kallon da zata min ko ta fada min wata maganar marar dadi. Shi ya tura kofar falon ya shiga sannan ni ma na shigo babu kowa falon sai tv da ac da ke ta aikinsa. Kai tsaye ya nufi upstairs hanyar dakinta ni dai ina biye da shi har muka isa cikin dakin da na ke sharewa na yi mopping amman a da. Ba Mama Fulani kadai muka tarar ba har da Rukaiya da Maryam da Baby suna zaune dakin, suna ganinmu sukai tsit da alama wata maganar suke tsaka da tattaunawa, ina daga bayan Aliyu ban karasa shigo sosai cikin dakin ba, sai ya matsa gefe ya matso da ni kusa da shi yadda zan bayyana tsundun a cikin dakin. Aiko a take Mama Fulani ta sako min ido tana min wani irin kallo ba na lafiya ba, ba kuma zan bayyana dalilin kallon ko manufarsa ba.

“Mama za mu wuce gida”

“To Aliyu sai da safe”

Ta fada amman idonta na kai har lokacin, sai Aliyu ya kalleni yai min magana kadankadan kamar mai bawa yaro umarni ko kuma mai koya masa abunda zai ce.

“Ki ce mata sai da safe Mama”

“Mama Fulani sai da safe”

Readers Also Read