Kenza eBookz

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 43

Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 43

Zaki complete by khadeeja candy Chapter 43: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 43. Na fada kamar yadda ya ba ni umarni sai tai saurin kawarda fuskarta…

4,478 words

Na fada kamar yadda ya ba ni umarni sai tai saurin kawarda fuskarta daga barin kallon nawa da take na tsawon lokaci, ba kuma kawarwa irin ta tsana ko kyama da tsangwama ba, irin kawar nan ta kamar mai tunani ko kuma wanda ya rude ko yake jin kunyarka. Ni na riga juyawa na fito daga dakin sannan Aliyu ya fito ya tararda ni har kusa sauka downstairs din. Ya riga ni isa harabar gidan tun kan na karaso ya janyo motarsa ya bude min front na shiga na zauna na ki rufe ganbun motar da gangan na tsaya ina kallonsa murmushi yai ya bude gefensa ya fita ya zagayo inda na ke ya sumbaci goshina.

“Dama ai kin saba bar min mota a bude tun kina budurwa kuma na zo na rufe balle yanzu da kika zama gimbiyata”

Ya fada sannan ya rufe motar ya zagaya gefenta ya shiga motar yai mata keys muka dauki hanyar gida. Sai da ya biya ta wani shago ya siya mana kayan zafi da kaza sannan muka isa gida. Da kansa ya fita ta zagoyo inda na ke ya bude min mota ina saukowa ya saka hannunsa ya ruumgumo ni kamar wata yar baby ko kunyar mai gadinsa da ke hangen baya ji, ni kuwa duk kunyarsa ta rufe ni.

“Wacan Dattijon Baba fa yana hangenmu”

“Sai me dan ya tsinkaye mu? Be san na aure ki ba ni ko kuma be san namiji na taba matarsa ba? Is normal ma ai ba waji abun nai miki ba dafaki kawai nai, kuma shi ai ya saba ganin hakan idan muna tare da Rahma”

Ya fada yana bude gidan vaya ya dauko siyayyar da yai mana da dayan hannunsa yayinda dayan hannun yake makalle da ni kamar zan tsire masa. Da hannu daya ya rufe motar muka nufi cikin gidan ni da shi. Ice cream kawai na sha daga cikin abubuwan da siyo mana, domin jin nai bana bukatar komai kuma bana jin yunwa, sai da mu kai wanka ni da shi a tare kamar yadda ya saba min sannan muka saka tufafin bachi muka kwanta. Misalin biyu da wani abu na dare yunwa ta tasheni a dole na bar jikinsa na sauka daga kan gadon na nufi wutar dakin na kunna ko da na juyo sai na ga mutun yana kallona.

“Yunwa na ke ji kazar da ka siyo zan ci”

Na fada ina dan wara kamar mai jin kunya.

“Zauna ba ri na dauko miki”

Ya fada yana saukowa daga kan gadon ya fita daga dakin, ni kuma na zauna saman kujerar sai gashi ya dawo da kazar a plate da lemu. Dan karamin tebur ya janyo ya dora plate din sannan ya miko min hannu na taso sai ya nufi bandaki da ni, wani lokacin yadda Aliyu yake min abu kamar wata yar baby abun har mamaki yake ba ni, wata kila saboda baya son yawan magana ne shiyasa ya son ya yi maka abu kawai ba sai ya furta ya ce kai ba wata kila kuma kuanar ce kaiwai yake nuna min. Sai na wanke bakina sannan muka fito na dawo inda na zauna dazun na zauna yawuna har tsinkewa suke kamin na ci kazar. Kusa da ni ya zauna ya saka hannunsa yana bare min yana ba ni a baki ina ci sai da koshi sannan na cige masa hannu da gangan, sai yai saurin cire hannunaa daga baki na dauki nawa yatsan ya kada a bakinsa ya cigeni kamar wani yaro karami, aiko ba shi ri nai ihu saboda zafin da na ji, sai yai saurin rufe min baki.

“Shiiiiiiii dare ne”

Ya fada kadan-kadan, dariya nai kamar yadda yake dariyar, sannan ya dauko lemun ya ba ni na sha sai ya aje ya matsar da teburin can gefe, ya kwanta saman kujera ya janyo ni na kwanta a kirjinsa, a nan muka kwana har safe yana rumgume da ni sosai a kirjinsa. Bayan mun yi sallah Aliyu ya kwantar da kaina jikinsa yana karatun kur'anin daya saba, ba dade yana karatun ba na tashi daga kwancen da na ke a cinyarsa na sauko falo na nufi kitchen domin samun abunda zan sakawa cikina saboda wata azzababbar yunwa da na ke ji. Freezer na fara budewa sai na ga dukan abunda yake ciki yayi kankara sai na bude dayar da bata aiki na ga Apple da sauran fruits a ciki, apple din na dauko na wanke shi a fanfan kitchen din na soma ci kamar wata mayunwaciya. Ina cikin cikin apple na hudu na ga mutum ya shigo kitchen din da tsage tsage a fuskarsa yana sanye da kananan kayan. Ba shiri na fasa ihu ina ra kiran sunana Aliyu shi ko mutunen sai daga min hannu yake alamar ya kwantar da hankali, tun yana magana da turanci har ya dawo yi da hausa sam ban dauka ma ya isa hausa ba. Da gudu Aliyu ya shigo kitchen din hankalinsa a tashe.

“Minenen?”

“Wacan mutumen.”

Na nuna shi.

“Mai mana girki ne”

Mai girki sai na ji abu wani iri, namiji da girki to miyasa wacan zuwan ban ganshi ba? Ko da yake kwana kawai mu kai mu ka wuce Lagos.

“To ta ina ya shigo?”

“Yana da makullin falon ne ko bana nan zai iya zuwa yai girki ya tafi”

Ya fada min sannan ya juya gurinsa..

“Abdulgany daga yau za ka daina shigowa cikin gidana nan, Nasir zai tura maka kudinka na wata ba zaka mana girki ba”

Risinawa nai ya fara bashi hakuri yana ta rokonsa ya yafe masa idan akan ya ba ni tsoro ne, sai ya fada masa ba dan tsoro ba ne wai yana kishin matarsa ne ba shi da bukatar ganinsa a gidan yanzu. Babu irin magiyar da be yi ba amman Aliyu ya ki saurarensa har sai da ya hada masa da fada sannan ya fice daga gidan. Misalin tara da rabi Aliyu yai mana oder abincin, muna cikin kiran Abbah ya shigo wayrsa sai da suka fara gaisawa sannan ya sanar masa inda yake ya same sa a can.

“Yi sauri ki ci Abbah na nemanmu”

“Har dani?”

Na gyada min kai, da sauri na tashi na bar cin abin ma na shiga nai wanka ina fitowa ya shiga kamin ya fito har na shirya daman can shine ba mai wahala ba ne, shi ma agaggauce ya shirya muka fito tare muka shiga motar. Ba zan iya fadar ungwar da muka je ba, domin ban san ko'ina a cikin garin Abuja ba, sai dai zan iya kwatanta da unguwar manyan mutane domin ta wani bangaren ma tana kama da Las Vegas irin rayuwar nan ta ba ruwa ko da kowa. Gaban wani katon gate Aliyu ya faka tsaya ya danna horn sai ga wasu manya kuma kanttin maza sun bude masa gate din, da sauri na rike hannun Aliyu sai yai murmushi ba tare daya kalleni ba, manyan motoci a cike a gidan na alfarma, bayan motocin ya faka motarsa ya fito ya zagayo inda nake ya bude min na fito daker domin ni gaba daya tsoro ya gama kama ni. Hannuna ya rika ya nufi wani guri da ni da alama shi m be san kan gidan ba, domin kuwa sai da ya kira wayar Abbah ya fada masa mu na waje sai aka turo dogare ya zo ya tafi da mu. Cikin wani irin katon falon muka shiga mai kama da fada, komai na falon mai tsada ne da tsari irin manyan sakuna. Ganin hoton Mai martaba sarkin Agadaz yasa hankalina ya kwanta na fahinci cewar a gidansa ne muke, na yi zaton a falon za mu tsaya sai na ga mun shiga wani falon mai kamar wacan, haka muka wuce falo uku sannan muka iso cikin wani madaidacin falo, a nan na hango sarkin hakimce a akan kujera, babu rawani a kansa kamar jiya sai dai yana sanye da alkyabar sarauta irin mai tsadar nan ga takalmin sarauta kafarsa, Daddy's Rahma na gefe zaune kasa daga dama kusa da Abbah, da sauran jikokinsa, Nana kuma na gabansa kanta a kasa tana ta sheka kuka gwanin ban tausayi da alama gafararsa take nema. Karasawa nai gurin Nana na zauna na dafata Aliyu kuma ya zauna kusa da Abbah yana mikawa mai martaba gaisuwa shi kuma ya daga masa hannu kawai.

“Ina jin kunyar ka Mai Martaba saboda abunda na aikata, ban san cewa na aikata babban laifi ba har sai da na rasa a kusa da ni na fara shiga damuwa da bakinciki......”

“Shin abunda kika be zame miki darasi ba?”

Mai martaba ya tambaya da kansa.

“Ya zame min, na rasa komai saboda babu kai a rayuwata, na rasa gata na rasa muhallin, abincin da zan ci sai na yi bara mai martaba, gida gida na ake bi ina rabawa na zauna, har na kai ga wanda aka ga wanda aka wulakanta ni kamar karya, kuma maciji ya tsare ni, Ataa tai ta dawaniya da ni da ta kai ni asibitin sai akai amfanin da rashin kowa na mu aka cire min koda aka sakawa yar wanda ya wulakanta mu saboda rashi, Mai Martaba da koda daya n ake rayuwa saboda rashinka da kuma dangina a kusa da ni, Mai Martaba aka a kulle Ataa a gidan yan sanda saboda ba mu kowa, na rasa na da na biyu da na haifa a gurin baran kudin neman min lafiya, Mai Martaba shin duka wannan ba darasi ba ne? Da ban bijire maka ba da ban ki bin umarninka ba da duka wannan abun be same ni ba, ba ban bata maka rai bada nawa bacin rai be kai haka ba, da ban gudu na barka na bar dangina ba da wani be isa ya wulakanta mu ba”

Ta fada cikin daga murya tana kuka sosai nima kukan na ke ina rike da hannunta.

“Da duniya tai miki wa'azi miyasa ba ki koma cikin danginki ba?”

“Saboda zuciya na fada ba zaka taba yafe min ba, ba zaka taba karbarta ba, masarautar da na saka a kunya na gudu na bari, idan na shiga wahala na dawo be kamata ta karbe ni ba, ban cancanci ko kallon fuskarka nai ba Mai Martaba, amman na barwa Ya ta mawasiya na fada mata bayan raina ta neme ku ta nema min yafeyarka da duka dangina”

Shiru Mai Martaba yai na tsawon lokaci kamar baya gurin, falon yai tsif baka jin ko da numfashin kowa.

“Ban taba jin na tsani jinina ba, ban taba jin kin jinina ba ko da ko zai kashe wani ya sake kashe wani jinina jinina ne, kuma ina jinsa a cikin jinina..... Bayan neman ki da masarauta tai na kwana biyu, sai na goge sunanki a babin nema har a bada, na bar abunda kika aikata da kuma son ki a zuciyata,... Na yi tunanin idan wahala ta same ki za ki tuna da danginki ki dawo..... Da ace yau mahaifiyarki ta fadi ta mutu da ta mutu da bakincikin da kuma bakincikin guduwa ki barta, babu daren da bata begenki... Idan kowa ya taru sai ta ce kowa yana nan amman ban da Asma'u... Shin kaunar uwa kadai be isa ya saka ki nemi danginki ba......?”

Daya bayan daya yake maganar yana kallon Nana.

“Ina jin kunyar kaina Mai Martaba, ina ina nadamar abunda na aikata, bakincikin guduwa na bar ku yana nan a zuciyata, kunyar haduwa da ku ta saka na yanke kaunar daga neman yafiyarku a raye har sai bayan rai na, Ka yafe min Mai Martaba ka tausayawa min dan Allah, na sani ko yanzu ina daf da mutuwa saboda lafiyata bata ishe ni ba”

Duk da yaren buzanci suke wannan maganar ita da Mai Martaba... Shiru ya sake yi na wani lokaci sannan ya ce a katse.

“Na dade da yafe miki Asma'u, na dade da fada a gaban kowa kuma na fada a zuciyata cewar ko ina raye ko a mace na yafe miki duniya da lahira”

Da gudu ta tashi taje ta fada jikinsa ta rumgumeshi tana kuka, sai yai murmushi kowa da ke falon sai da tauyasa kuma yai murmushi ban da Daddyn Rahma da baya cikin natsuwarsa. Kuka sosai Nana tai nima nai sannan muka share hawayen mu ni da ita. Bayan komai ya lafa muna kokarin shiga natsuwar mu ne. Mai Martaba ya sake gyaran murya da yaren hausa da baya fita sosai ya ce

“Na yi hakan nan ne a gaban ku saboda ku ma ku zama shaida kuma nasan dukanku za ku son jin gaskiyar alakata a Asma'u to yanzu kun ji, ina son kowa ya zama shaida na yafewa Asma'u abunda tai min, Allah ma ka zama shaida na yafe mata duniya da lahira”

Tsakanin ni da Nana sai na rasa wa yafi wani farinciki ni ko ita. Daddyn Rahma ya daga hannunsa alamar yana son yai magana da kai martaba sai gumi yake cikin asiri.

“Mai Martaba na ce kan sai zancen nema mata hakkinta a gurin Doc Asim na cire mata koda da yai”

Kallonsa nai yadda yake maganar muryarsa har rawa take.

“Allah sarki ashe rana zata zo irin wannan dakai da bakinka zaka bude baki ka ce a nemawa Nana hakkinta? Bayan duk irin cin mutunci da wulakancin da kai mana? Waenne kalar mutane ba ka turo sun zo sun watsa mana kayanmu sun koramu ba saboda kawai mun raba a kangon gidanka ka ce mu muka janyo maka maciji a gida ka karemu ka wulakanta mu, idan har za a hukunta Doc Asim to har da kai za a hukunta domin kodar da aka cirewa Nana yarka aka sakawa”

Na fada cikin kuka. Sai shi ma ya fashe da kuka sosai kamar ba shi ba.

“Wallahi Allah ya sani idan na san cewa ku zuri'ar Mai Martaba ne ba zan taba muku haka ba, Wallahi ko shara kuke agidan Mai Martaba ba zan iya wulakanta ku ba, walle har ace jininsa habawa..... Ba hali na ba ne, ko korar da aka muku ni sau daya na fada na ce a fada muku ku nemi wani gurin ku zauna, Wallahi Hajiya ce tai ta turawa aka rakura muku, ita ma kuma basan cewa jinin Mai Martaba ba ne da ba zatai muku haka ba, Wallahi tun jiya da na fada mata abunda ya faru tana can kuka take yanzu haka..... ”

Yadda yake kuka abun ko kyau babu domin babban mutum be sha'awa da kuka ballantana shi da yake wani rakeken kato, ni dai sai kallonsa n ake da takaici a raina.

“Wanene Doc Asim to?”

Jikan Mai Martaba ya tambaya cike da mamaki. Ni kuma sai na amsa masa

“Wani ne, wani likita ne wanda na kai Nana asibitinsa lokacin ba mu da kudi sai ya ce zai mata tiyata kyauta ya cire dafin maciji a jikinta ashe yaudarata yai ya cire mata koda, ya bani wata takardar na saka hannu ashe ta siyarda kodar ce ban sani wai saboda ba ni da ilmin komai, sai da ya tambaya ba mu da kowa na ce nasa eh shine ya cire mata koda, haka mukai ta jinya bata warke ba, sai na kaita wata asibiti aka duba aka ce kodarsa ce ya cire na kai kararsa gurin police yasa aka rufeni wai ina son bata masa suna, sanadin hakan Nana ta tashi mutuwa har sai da Allah ya kawo wannan Aliyu ya taimake mu ya kaita asibiti ya ba mu ci da sha da gurin zama”

Har lokacin da nake maganar cikin kuka Daddyn Rahma ma kuka yake yi.

“Wannan ba tsakanin mu da shi ba ne, tsakaninsa da Shugaban kungiyar likitoci ne”

Shine abunda Mai Martaba ya fada a takaice fuskarsa na nuna bacin ransa karara....

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*

*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.* *Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.* Wani irin sama yake da kafafuwansa yana boxing da hannu kamar wani karamin yaro, sai kuma ya sauko saman gadon ya nufo ni da wata irin far'a ya daga ni sama yana juyawa da ni, kamin ya rumgume.

“Oh Allah na”

Ya fada yana matseni har ina jin zafin matsar saboda yadda ya rike ni da karfi.

“Aliyu minene?”

Be bani amsa ba, ya sake ni ya fadi yana sujada, sai kuma ya dago ya ya rike ni yana ta kallon fuskata murmushi ya gama cika masa fuska, hade bakina yai da na shi ya fara min abunda ya saba wato kiss sannan kuma ya cire bakin ya daga kansa kama.

“Wayyo Allah na, baby ban san abunda zan yi ba yau, kar na haukace”

Har lokacin da yai wannan maganar kansa a sama yake yana kokarin maida ni kirjinsa ya rungume. Ni dai sam ban gane dalilin wannan farincikin ba, da farko ganin layin biyu yasa na tsorata na fara tunanin ko dai ina da wani ciwon ne sai dai yadd Aliyu yake far'a yasa na daina zargin ciwo sai dai kuma ban kawowa raina komai ba, sai mamaki kawai na ke.

“Baby i love you, I love you Tomorrow, i love you everyday, i love you so so very much”

Na san abunda I love you, da everyday da tomorrow take nufi, kuma na jidadin furtasu a gareni da yai hakan yasa ni na rumgumeshi da duka hannayena, ina jin kamar nima na fada masa haka kuma ina jin kunya. Ji nai ya dago kaina yana ya sumbatar ko'ina a fuskata da jiki kamar mahaukaci sai kuma ya sake rumgume, sake ni ya sake yi fara rawa a gurin yana jujjuyawa kamar wani mace, sai kuma ya rikoni yana cilastani ni ma nai rawar.

“Very Very soon Baby za ki zama uwar Baby”

Ya fada yana rike da fuskata har da wani turo min bakinsa yake kamar nai yi yarinya karama magana da zolaya. Uwar baby kuma ban fahimce shi ba.

“Kamar ya”

Juyar da ni yai ya zamana bayana ne a kirjinsa sai ya saka dayan hannunsa yana shafa cikina.

“Kamar haka, idan kin haihu”

Zaro ido nai sai yanzu na gane komai barobaro da sauri ya juyo.

“Ina ciki kenan?”

Juyar da ni yai ya rungume.

“Muna da ciki dai Baby not just you, ko ma na ce ina da ciki Baby i love you”

Ya fada saitin kunnena. Sai na fashe da kuka.

“Aa yanzu kowa sai ya san abunda ya faru ko? Idan aka gan ni da ciki”

“Daman ai an san dole wani abun zai faru”

“Amman dai akwai kunya kuma ciki da wahala”

“Ba wani wahala, kunya kuma ai tunda kika yarda kika zauna gidan miji ta wuce”

Ban san dalilin rashin jindadin cikin ba, sai ma tsoro daya kama ni yo ni ya ma zan yi na haihu? Kuka na fara bana wasa ba tun yana rarrashina a hankali har abun ya koma bashi tsoro.

“Haba Babyn wannan fa abun farinciki ne, wannan shekarar ina cikin ta tara da aure amman ban samu haihuwa ba sai yanzu, Momy Mama Fulani Abbah Daddyn da duk family and friends da sisters idan suka ji dadi za su ji kuma su so ki sosai”

“A a nidai ba yanzu ba nidai bana ma so gaba daya”

Zaunar da ni nai saman gadon ya zuba min ido yana ta kallona.

“Dan girman Allah Babyna ki daina kukan nan, kar kukan ya cutar da abunda ke cikinki”

“Ba zan iya iya kallon kowa ba idan nai ciki, kuma ba zan iya haihuwa ba”

“Ciki ai kin riga kin yi, yi hakuri ba za a sake wani cikin ba”

“Da gaske?”

Dariya yai ya gyada min kai. Sannan na sausauta kuka shi kuma ya tashi yaje debo min ruwa. Yana fita na daga rigata na leka cikina sa nai sauri na rufe.

ALIYU POV.

Ya sauko downstairs wayarsa a hannunsa yana kiran Nasir, wannan karon be jira Nasir ya fara magana ba kamar yadda ya saba yana kiran daukar kiran Aliyu ya ce

“Congratulations to us na kuma zama Daddy nima na yi ajiya a cikin Ayusher”

“Wowooooooooooooo Aliyu are you serious? Oh my God”

“Na rantse da Allah Nasir har ban san irin farincikin da zan yi ba, na rasa abunda zan yi Wallahi ji na ke kamar na hadeye Ayusher a yau”

“Wannan abun murna ne a garemu gaba daya ai, amman Momy ta ji da Mama Fulani?”

“Ban fadawa kowa ba sai kai, nima yanzu na ga result din”

“Ni zan yi musu albishir karka ce zaka fada musu na san baka da kunya”

“Ai na zancen kunya a nan Nasir, wane irin kunya a gurin farinciki? Ai ba wannan zancen shi dan na fada na ce tana da ciki kuma wani abun kunya ne? Ita ma yanzu ta gama kuka wai idan suna ji zata ji kunya”

“Ai kai ba saka gane ba ne saboda ka saba yin abu normal ne”

Murmushi Aliyu yai ya kashe wayar, har ga Allah shi be ga abun kunya a fadar matarsa ta yi ciki ba, shi ba duk abunda ya san idan ya aikata ba haramun yai ba to be ga abun jin kunya a ciki ba, da dai zina ya aikata ko wani alfasha shine abun jin kunya, domin shi ya fi dacewa ka ji kunyar Ubangijinka sama da na kowa. Freezer ya bude ya dauko ruwan gora ya zuba sai da ya sha dan ya ji yanayin sanyinsu kar su cutar da abun cikinta sannan ya sirka da wasu ruwan sai ya dauko kofin ya dawo dakin da take. Inda ya barta a nan ya same ta zaune da kansa ya kai mata ruwan a baki yana bata a hankali har ta sha rabin kofin sannan ya aje ya zauna kusa da ita ya zuba mata ido. Be san abunda zai mata ba, rumgumatar ba zai wadatar da shi ba, kallonta ba zai wadatar da shi ba, saurarenta ko yi mata wani abu ba zai wadatar da shi ba, yana jin cewar hadeye ta kawai zai yi ta zauna tana cikin cikinsa ita da abunda ke cikinta sannan hankalinsa ya kwanta sai dai kuma babu wannan damar ya rasa inda zai sakata tsabar farinciki. Haka yai zaune ya sakata a gaba har aka kira sallah la'asar sannan ya sumbaci goshin nata da cikin ya fita zuwa masallaci, daga masallacin ya wuce restaurant ya siyo musu abinci, ya so ya kira ya tambaye ta abunda take so amman babu yadda zai yi tunda bata da waya. After restaurant ya wuce wani babban shago ya siyo mata sabon phone mai tsada wacce ake yayi sannan na nufo gida, ko da ya shigo ya ji motsinta a kitchen sai ya nufi kitchen din kai tsaye taliyar indomie ya tarar tana zubawa a plate tana murmushi.

“Yunwa na ke ji sosai shi ne na dafa indomie”

Ta fada masa ganin ya tsaya yana kallonta da murmushi.

“Wow yau Gimbiyata ta yi aiki da kanta bari na dan dana na ji, ashe kin iya girki ko?”

“Eh na iya tuwo na iya dafaduka na iya dafa taliya na iya sararafa kanzo na iya shimkafa da miya kuma na iya da wake, amman ban iya amfani da wacan abun ba sai na daka a turmi”

“Wow amman dai ai ba sai kin yi aiki da yawa haka ba”

Ya karasa kusa da ita yana rike da ledodin a hannunsa. Fork ta dauko ta saka ya debo taliyar sai ya busa masa a bakinta sai da huce sannan ta kai masa a baki, luma daya ya rumtse ido saboda wani azababen yaji da ya ji, da sauri ya aje ledodin hannunsa ya dauke plate din.

“Wallahi ba za ki ci wannan abincin ba”

“Mi yai?”

“Wannan uban ya jin?”

“Ji nai ina son ya ji shine an cika kadan”

“Wannan cikin be wani kwari ba za ki ce za ki ci wannan yajin, noooooo ga wani abincin na siyo miki ai zo mu ci tare”

Ta mairairaice fuska.

“Haba Aliyu ina so Wallahi”

“Haba Baby ki tausaya min mana”

Aje plate din yai gefe ya bude dayar ledar mai waya ya dauko ya mika mata.

“Ga waya ke ma ki fara bugawa kina daukar hoto”

Ba shiri da zaro ido ta karbi wayar da sauri da daka wani irin tsalle kamin da dire yai saurin cabeta.

“Ke yanzu fa ba ke kadai kike ba, ki daina irin wannan abun”

Ina bata ma jin me yake fada sai ihu take ya rumgume shi sabar farinciki har da yi masa kiss a fuska.

“Na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na”

Haka tai ta maimaitawa sai da ya rufe mata baki, sai kuma ta fashe da kuka kuka irin sosai din nan kamar wacce akai wani abu rasa tai me zata yi, ita a rayuwarta bata taba rika waya ba ko karama balle babba irin wannan mai screen kato. Rikota yai suka baro kitchen din suka dawo falo suka zauna, sai ya karbi wayar ya bude mata ya hada mata.

“Idan na fita ko kuma zan saka Nasir ya siyo miki layi mai kyau na ki na kanki, kuma yanzu sai an saka wayar carji idan ta yi full sai a fara tabawa”

Ta yi saurin tashi daga kan kujerar tare da carjar wayar ta nufi socket ta saka ta zauna s gurin ta tsare wayar. Shi kuka ya tashi ya koma kitchen din ya dauko musu abincin daya siyo musu ya zo kusa da ita ya zauna ya bude abincin.

“Aliyu ka dauko Nana na nuna mata wayata”

“Ba yau ba dai, gobe ai zamu je mu gaisheta sai ki nuna mata”

“Har sai gobe”

Readers Also Read