Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 6
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 6: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 6. “Momy barka da safe”
4,244 words
“Momy barka da safe”
“Safe yanzu 12:13pm?”
Ta fada tana kallon katon agogo dake falon. Shi ma kallon tsadadden agogo hannunsa yai kana ya zauna yana fadin.
“Ban san ta yi ba, gaske na ji cikina ba nauyi”
“Matarka bata nan?”
“Tare muka fito da ita na aje ta gidansu”
Momy ta cigaba da tara books din ba tare da ta kara cewa komai ba, shi kuma yana ta kallo yanayinta.
“Anything Momy?”
Sai ta kalleshi.
“No nothing kawai ina tunani ya kamata ace ka ci abinci ne kamin ka fito”
“Momy yadda kike tunanin Rahma fa ba irin waennan 'ya'yan talakawa ba ne, duk wani aiki mai nauyi Rahma ba za ta iya ba, ko da can ma balle yanzu, kuma dacan Rahma tun da ta tashi a gidansu ba ta aikin komai bayan hutu saboda ciwon kidney din da take”
“Kuma bata iya zuwa gidan sukukanta ta gaishe su ba ko? Gidansu kawai ta sani sai gidan kawaye sai fita waje idan ta gaji da kasar”
Ya shafa kansa yana ta neman kalmomin da zai hada ya fahimtar da mahaifiyarsa ko wacece Rahma.
“Yana da wahala ka ga kafar Rahma a gidan nan sai idan wani abun ake muhimmi, shin bata san zuwa gida sukurukai gaishesu yana da muhimmanci ba? Ko ta dauka Fulani ce Real Mother dinka? Bata taba fada mata cewar ni na haife ka ba? Ko kuma tana ganin kamar bana jin zafin abun ne? Idan zaku zo hutu daga Abuja wani lokacin har ku kuma ba zata tako kafarta gidan nan ba, sai idan za ku tafi shi ma idan kuna tare,, balle kuma ta dauko wani abu ta kawo min ko ta aiko min, ba dan ina da bukata ba, amman kowa yana son kyautatawa”
Momy ta fada mishi with serious face. Mikewa yai tsaye ya nufi dinning ba tare da kalma daya ta sake fitowa daga bakinsa ba sai dai yadda yaga fuskar mahaifiyarsa ta cikinsa yasa shi jin babu dadi be taba daukar abun nan da Rahma take wani abu ba, a ganinsa Rahma ta riga ta saba da rayuwar turai ne, ita kuma Momy ta kasa hakan, ba kamar Mama Fulani ba da bata taba damuwa da shiga safgar Rahma ko da kuwa zata taka ta ta wuce ba dan komai ba sai dan tana ganin daga Rahma har ubanta ba su kai matsayin da zata iya kallonsu ba, domin ita bata huldu da duk wani mai kudin da baya isa amsa sunansa a birnin Abuja.
____________
Assalamu Alaikum. Kwana biyu ban yi posting ba hakan ya faru ne saboda rashin lafiyar Kakata, amman yanzu Alhamdulillah, In-Sha-Allah posting babu kama hannun yaro. And ina son nai amfani da wannan damar na sanar da ku cewar da zarar mun kai page 12 za mu tsayar da Free pages, hakan na nufi sai mutum ya biya sannam ya samu cigaban labarin, daman na fada tun a ZABIN RAI cewar littafin ZAKI na kudi ne, wadanda suka sani sun sani domin na fada, and ina yin littafi free, wanda zai zo bayan shi na kudi, kamar dai yadda RAI BIYU ya zo free HAFSATU MANGA (yarinyar K'auye) na kudi, haka ma ZABIN RAI free ZAKI na kudi.
Ga wanda suke son fara biya tun yanzu za su iya turo 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot ta wannan number 08036126660, 'yan nijar za ku tura 500f na line orange ko zain ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Paid Group.
Thanks 🙏🏻 https://my.w.tt/PWohUhlPv9.
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1️⃣0️⃣
Kamar wata mahaukaciya haka na rika ratsa mutane ina cusa kaina har na karasa inda yake, ihu yake ta yi yana rike da jafarsa yana jiran sunana.
“Wayyo Allah Ataa kafana wayyo ni kafana”
Babu jini a kafar amman yadda yake ihu cikin magagi ya fahimtar da ni irin ciwon da kafar take masa, ga gefen kansa sai jini yake yana ta wani jujjuya ido kamar zai shude.
“Ai wallahi Allah ya kara mutanen ba su da godiyar Allah, kullum cikin bara, da sun hango mota har sauri suke su mikawa mutane hannu, yara kanana an koya musu bara”
Shine abunda mafi akasin mutanen da suke gurin suke fada, masu ganin tausayinsa kadan domin sauran ta'alaka abun ne da rashin wadatar zuci irin na mu, na raba a titi da kaskantarta kai.
“Jama'a ku taimaka min kar ya mutu”
Shine abunda ya iya fada cikin kuka, sai daya daga cikin mutanen da ke tsaye ya zo ya dauke shi ya saka a mota wanda na ke kyautata zaton shi ya kade shi. Gidan baya ya bude min na shiga gurin da Lukman yake sannan ya bude mazaunin direba ya zauna na fisgi motar muka doshi specialist hospital wato asibitin daji. Muka isa aka wuce da shi layin yan hadari ni kuma na bi bayansu hankalina a tashe, sai da suka fada min cewar na je na karbo kati na tuna da kudin da suke hannu, ba ko tantama sun fadi tun a lokacin da hadarin ya afku, da sauri na fita emergency din zuwa neman mutumen ko zan ganshi ya taimaka min, sai na nemesa na rasa, wata kila shi kuma ya tafiyarsa. Komawa nai ciki ina rokonsu su taimaka su kula da shi kamin na kawo kudi sai suka ce min wai sai na zo da police za su iya taba shi, haka suka kyale Lukman a wulakance cikin gurin da duban mutane suke sai ihu yake. Ji nai kamar na je na dauke shi nai tafiyata idan kuma na dauke shi ban san inda zan kai shi ba, ba ni da wani magani da zan iya masa. Tasowa nai na fito daga cikin gurin ina tafiya hawaye masu zafi suna sauko min, yanzu yan kudin da suka rage min da kuma wadanda mukai bara muka samu na zubar saboda kidima, ga shi Lukman ya bugu da mota ga Nana tana asibiti tana jiran na kawo kudin maganin da hoto. Wani abu na ji ya tsaya min a zuciya yana neman numfashina, a take tsayuwa ta gagareni, ba zan iya fadar inda na ke ba, iyakar abunda na sani na ji na zauna saman wani abu mai kamar kaya, sai kuma duhu ya rufe min ido har na soma jin kamar babu sauran numfashi a tare da ni.
Ban san iya awanin ko mintuna dana dauka a gurin ba, kamar wacce aka sakowa numfashi daga sama haka na farka firgigit ina maida numfashin wahala, baren kaina na ji yana min ciwo, gurin da na ke zaune sai sukana ake, hakan yasa na unkura na tashi tsaye sai na lura ashe saman fulawoyin na ke zaune masu kaya, da na soma tafiya sai na ji jiri na ďibata idanuwana kuma suna ta lumshewa kamar mai jin bachi. Haka na fito bakin gate din asibitin ina tafiya kamar marar lafiya, bakin titi na tsaya na tari wani mai Napep yana tare da wata mace a baya, yana tsawa na duka har kasa na hade hannayena ina rokonsa.
“Dan Allah ka taimaka min ba, kanene yai hadari mutumen daya kawo shi asibiti ya gudu ya bar mu, su kuma sun ce baza su duba shi ba sai na kawo police kuma ba ni ko kudin siyen kati”
“Yanzu me kike so?”
Matar da ke baya ta fada tana dage nikab din dake fuskarta.
“So na ke ka taimaka min na dauko shi na saka a ciki na kai shi gida”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, mutane suna ciki hali, ke yanzu kudin Napep din ma ya gagara? Allah ka ba mu karfi da ikon da za mu iya taimakon bayinka marasa shi”
Ta fada tana miko min dubu daya yan dari biyu guda biyar, sannan ya ciro dari biyu ta mikawa mai Napep din.
“Je ka kaita ni zan tari wata na shiga”
“Na gode Allah ya saka miki da alheri”
Tana fita na shiga zauna a ciki mai Napep din ya janyo ta ciki muka shiga har bakin kofar emergency. Da sauri na fita daga napep din na shiga ciki sai na same shi a inda na barshi, sai dai baya motsi babu alamar numfashi a tare da shi.
“Kun kasheshi, kun bar shi nan ba ku taimaka masa ba, ya mutu kun ji dadi”
Shine abunda na fada ina kallon nurses din ina hawaye kamar ba gobe, sannan na duka na saka hannuna biyu na tallabo shi na juyo na fito da shi mai Napep din ya taimaka min ya saka shi a ciki ni kuma na shiga, ina ta shafa fuskarsa ko zai farka amman shiru, can na kai hannuna gurin hancinsa sai na ji babu numfashi ba alamunsa. Har muka isa Clapperto road kuka kawai na ke ina rike da Lukman, mai Napep din ne ya fito ya saka hannunsa ya dauko shi ya kai shi gurin da na nuna nasa wato cikin kangon gidan nan ya aje min shi sannan na saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyar ya miko min.
“Gashi ku kara Allah ya muku mafita”
“Na gode”
Na Fada cikin muryar kuka. Sai ya juya cike da tausayawa ya fice, ni kuma na zauna a gurin ina ta kallon Lukman wai ko zai motsa amman shi, har hannuna na kai na dan matsa gurin kafar inda na ga yana riko dazun ko zai motsa amman shiru. Kaina na daga saman ina hawaye cikin daga murya irin da masu neman dauki nan cikin gaggawa na ce.
“Allah kai ka so haka a garemu, komai ya samemu da saninka ne da yardarka, Allah ka sani ba ni da wata mafita sai ta ka, Allah kana ganin halin da na ke ciki Allah ka kawo min dauki”
Sannan na tashi na je nai alwala nayi Sallah, ban tashi daga gurin ba, sai da na gabatar da sallah la'asar, sannan na mike tsaye ina murza kudin da ke hannuna zuciyata sai wani abu take min babu dadi, da kafa na taka zuwa asibitin uduth wannan karon babu masu gadin dakunan kasancewar la'asar, cike da nauyin kafa na ke taka ward din ina sakesaken abunda zan fadawa Nana, idan ma na boye mata dole zata san gaskiya, idan kuma na fada mata zata iya shiga wani hali sai na kasa za6a tsakanin fada mata da kuma akasin haka. Kwance na sameta ba kamar dazun da na bar ta jingine ba, ban san hawaye na min zuba ba har sai da ta nuna fuskar tawa.
“Miya saka kike kuka Ataa? Wani abun ya samu Lukman ne?”
Saurin share hawayen nai ina girgiza mata kai.
“Aa babu abunda ya same shi”
“Karki boye min, fada min babu abunda zan iya da lamarin Allah”
“Mota ta kade shi Nana, kuma an kai shi asibiti amman baya motsi na dauko shi na dawo da shi gida, kuma kudin da na samu da ragowar duka sun fadi”
Kamar wacce aka yi ma allurar karfi da kuzari, haka ta tashi zaune kamar ba ita ba.
“Lukman din ya mutu ko?”
“Ban sani ba amman dai baya numfashi kuma yai ta ihu lokacin da aka kade shi ya rike kafarsa yana da kuka sosai”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u ”
Ta fada tana mikewa tsaye har mamaki ta bani dan zaka rantse da Allah cewar ba ita ce ke kwance malala dazun ba.
“Mu tafi”
Ta fada tana jan dayan zanen da ke saman gadon ta rufe jikinta. Ni kuma nai saurin rikata n zaunar.
“Ba za su bari mu tafi ba sai mun biya kudin gado Nana, ki zauna zan je samo wasu kudin na biyasu sai mu koma gida”
Zaunawa tai a saman gadon sai ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. Ni kuma nai saurin fita daga gurin ina sauri kamar zan halde kafafun. Lokacin da na fito bakin kofar asibitin sai na rasa abunda zan yi, wace hanya zan bi na samu kudi? Baran zan sake komawa ko kuwa sata zanje na yi ko mutuncina zan siyar, idan ma sata zan yi ina kudin suke da har zan sata? Ina mai siyen mutuncin yake da har zai siya, a nawa zai siya, mi zai biyo bayan wannan? Wani tunanin ya zo min, da sauri ma tari Napep na shiga na ce ya kaini ofishin yan sanda, yana tafe gabana na faduwa abunda da wacce ba ta saba ba, musamman a lokacin dana sauka daga Napep din na doshi cikin ofishin, sai bugun gabana ya karu ina jin kamar ba zan iya ba, ganin irin manyan bingogin da suke rike da su. A haka dai na daure na shiga gurin ina sallama muryata na rawa kamar mai jin sanyi.
“As..sa.. La.mu...Alai..kum.”
Mutum biyu suka amsa min, sauran kuma suna ta kula da wasu mutane da ke kusa da su suna musu wani complain din dabam.
“Wa kike nema?”
Wani mai babban muryar ya tambaya yana kallon yanayina.
“Karar wani likita na kawo”
“Likita kuma? Me yai miki?”
“Kodar mahaifiyata ya cire, ba tare da saninmu ba, kuma ni ban ce ya cire mata ba”
Na fada ina kuka. Sai daya daga cikinsu ya zaro ido.
“What...?”
Sai dayan ya ce.
“Koda? Babbar magana, Robot bude nata file ka dauki statement dinta”
A take na zayyana musu komai yadda ya faru cikin har da maganin da ya bani da kuma abinci, sannan na fadi yadda wacan likitan na uduth ya fada min.
“Amman ke ai ba ki da shaida”
“Amman ai hoton ya nuna bata da koda kamar yadda likitan ya fada, kuma ashe ba ayi ma dafin maciji tiyati ni ban sani ba”
Cikin kuka nake wannan maganar ina share majina da Hijab dina.
“Dan Allah ku taimaka min ku kawto min hakkin mahaifiyata, yanzu haka tana asibiti babu kudin jinya sakamakon kodar nan da ya cire mata”
“Kin san inda likitan ya ke?”
“Ban sani ba, amman na san asibitinsa kuma can yake aiki kusan ma can yake zama kullum”
“To yanzu kin san yadda za ayi kina da na mai?”
Na mika masa dubu da dari biyar din da ke hannuna.
“Wannan kudin ne kawai ban sani ba ko za su isa”
Daya daga cikinsu ya karba sannan ya zagayo tare da wasu polisawan uku suka fito daga ofishin, sai da suka janyo motar yan sanda suka ce da ni na zo na shiga na nuna inda yake, cikin kuzari na shiga motar ina ta jindadi da ganin kamar za su kwato min hakkina ne, ashe ban sani ba gwanwo ne zai juye da mujiya.
_______________ Ayi hakuri na yau be kai yawan na kullum ba, gobe zan cika In-Sha-Allah. https://my.w.tt/PWohUhlPv9.
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1️⃣1️⃣
“Momy muna neman mai aiki wacce zata rika gyara mana gida”
Ya fada yana aunar jalof din taliya da Momy ta zuba masa.
“Yar talakawa za'a nemo maka kenan, kaga ko dan za a ci amfaninta”
“Za tai ci amfaninmu ai biyanta za a yi”
Momy ta yi murmushi.
“Dan wajen Fulani har yanzu ka ki yarda da cewar za ka ci ribar talaka ko?”
“Momy kece ai kin ji ki gane, idan ba wani abu zaka saka talaka ba ka biya shi me zai hada ka da shi, Mama Fulani tana yawan yi min bitar kar na yarda ko rigata talaka ya rika balle kuma har ta kai ga alaka, kin san talaka dan hassada ne”
“Lallai kuwa, ina jiye maka tsoron ranar da zaka fara kaunar talaka, wata kila abun ba zai zo maka da sauki ba”
“Kamar ya?”
“Ba a son fariya, Allah zai iya jarrabarka ya koma talakan cikin talakawa, ko kuma Allah ya jarrabe ka da son yar talakawa wacce zaka duka har kasa kana rokon ta so ka?”
Ya tofar da ragowar abincin da ke bakinsa.
“Allah ya tsare ni Momy, ni ai bana da ra'ayin mace fiye da daya, Rahma ce kawai bayan ita babu wata”
“Wallahi yayan talakawan nan akwai tarbiya, da ace Rahma yar talakawa ce da zata fi ganin girma da girmanka fiye da yanzun”
“Ko a yanzu tana ganin girman ki Momy, kawai dai ita ta tashi a rayuwar turai ne, kuma kin san irin Rahma bata tashi gidan wahala ba shiyasa....”
“Hmmm To Allah ya kyauta”
Shine abunda Momy ta fada daga karshe sannan ta tashi daga dinning din ta nufi kitchen. Sai bayan sallah magariba ya biya gidan family house dinsu Rahma ya dauko matarsa suka dawo gida. Kamar wata marar lafiya haka ta shigo cikin falon tana takawa kamar mai jin wahalar tafiyar.
“Wani abun ne Dear?”
“Aa Daddy be dawo ba, kuma ance yai hasara kudi da yawa a shopping mall dinsa daya kone”
“Shine kuma za ki dauki damuwar ki saka a ranki? Bayan kin san lalurarki?”
Tai murmushi tana kai hannayenta ta zagaye wuyansa.
“Ina kokarin kawarda damuwar fa ko dan saboda na rayu da kai”
Kissing din lips dinta yai sai kuma ya rumgume ta a kirjinsa.
“Ka yi Momy maganar mai aikin? Ni wallahi har kyamar shigowa dakin nan na ke, duk datti”
Yai shiru be ce da ita komai ba.
“Bathrooms din mu duka suna son gyara fa, ga tarin wanke-wanke, ga kitchen din mu and bedrooms duka datti, ko mopping an dade ba ayi ba, kuma kasan ba zan iya ba”
“Shiiiiiiiii”
Ya fada yana shafa bayanta, yasanta da yawan magana wani lokacin kamar radio, ga shi kuma baya son yawan magana sai idan da Mama Fulani ne ko Momy.
“Doc Asim zai rika zuwa yana duba ki kullum”
Ya fada bayan ya saketa, sannan na nufi upstairs.
ATAA POV.
Mun taki sa'a domin kuwa mun isa cikin asibitin a lokacin da yake tsaka da aiki, ina gaba polisawan ba bayana kowa sai kallon mu yake har muka isa ofishinsa, da muka shiga sai muka tarar baya ciki wai yana dakin tiyata, a ofishin mukai tsaye cirkocirko muna jiransa har ya fito daga dakin tiyatar ya shigo ofishin, da fari tsayawa yai yana kallon polisawan kamin ya maida dubansa a zuwa gareni, da alama an labarta masa zuwan mu tun kan ya shigo ofishin.
“Kai ne Doc Asim?”
Daya daga cikin yan sanda ya fada sai ya gyada masa kai.
“Yes wani abun ne?”
“You're Under arrest”
“Akan me?”
Ya tambaya kamar da gadara, ni kuma nai karfin halin bude bakina na ce.
“Kai ka cirewa Mahaifiyata koda dan haka dole a kama ka kuma a kwato mata hakkinta”
“Kodar da kika siyar? Blackmailing dina za ki yi? Are you out of your sense?”
Mamakin furucinsa ya hanani ko da motsin kirki balle har na sake cewa wani abu, waina siyar da koda, yaushe na siyar? Wa na siyarwa ya ma za ayi na siyar da kodar mahaifiyata.
“Oficer kar yarinyar tai wasa da hankalinku ta raina muku aiki, kar kuma ku isko ni har cikin ofishin ku ce za ku ci min mutumci akan aikin, muje station din ku hada da dan sanda ku daya zan saka shi motata sai mu tafi station din amman ni ba zan shiga motar ku ba”
Yadda ya bukata haka akai, ni da sauran polisawan muka koma a motar da muka zo, shi kuma ya shiga motarsa da dayan dan sanda bayan ya dauki wasu takardu. A motar yan sanda sukai ta tambaya wai da gaskiya na siyar da kodar nai ta musu rantsuwar ban siyar ba, ban ma ya cire ba, idan har na siyar mi zai sa na kawo kararsa gurinsu, a nan suka min tausayawa kuma suka ce za su kwatar min hakkina, dan sanda yana ya matse ni sosai jikinsa na ta gogar nawa.
“Yarinya kyakkyawa da ita za a ci amanarta, ki sha kuruminki sai mun kwato miki hakki”
Shine abunda ya fada yana kallona da jajayen kamar dan shaye-shaye. A lokacin da muka isa Station din sai muka shiga ciki, a nan ya fiddo da wasu takardu ciki har da takardar da na sakawa hannu lokacin da za ayi ma Nana tiyata.
“Kin san kin saka hannu a wannan takardar ko ba ki sani ba?”
“Na saka”
Na amsa masa ina kallon takardar.
“Magani kawai na dubu nawa kika siya mata? Abincin da kike ci safe da rana da dare daga Hotel ake kawo miki duk ina kika samu kudin?”
Kasa magana nai sai hawaye na ke gaba daya ya gama dauren kafafu kai har ma da jikin gaba daya. Sai kuma ya juya gurin polisawan ya ce.
“Yi ma Babban likita irina sheri abu ne mai sauki domin ta samu kudi, yarinyar nan ina zaman ta dauko mahaifiyarta ta kawo wai maciji ya tsareta, kuma babu yadda zata yi ita bata da gabas bata da yamma, na ce ni ba zan taba ba, sai an kawo kudi, sai kawai ta ji ina magana da wani mai neman koda a nan tace zata siyar kuma babu yadda ban yi da ita ba akan ta nemo manyanta sai tace daga ita sai mahaifiyarta suke wai basu da kowa a nan, kuma idan ban taimaka na siye kodar mahaifiyarta ba, babu inda zata samo kudin da za ayi mata allurar dafin macijin, a haka tai convince dina na yarda na bata takarda ta saka hannu, na bata kudinta ta ce aa na aje gurina na siya mata magani ragowar canjin na bata wannan ne kawai abunda na sani”
Cikin kuka na nuna shi da yatsa na ce .
“Allah ya isa, karshenka ba zai yi kyau ba, kuma za ka ga abunda zai same ka?”
“Kaji ko? Oficer nima bude min file sai na ji akan me take kokarin bata min suna”
Ya fada yana nuna ni. A maimakon polisawan suyi wani abu sai na ga kamar suna tsoronsa, ashe ya siye dayan sandan daya shiga motarsa, sai kawai na ga sun fita waje har da shi Doc Asim din sun kebe suna ta magana da juna, suna kawowa sai suka fara tuhumata wai waya biyani na bata masa suna.
“Babu wanda ya saka ni, amman wallahi karya ya fada”
“Kina da wata shaida ne? ”
“Ba ni da ita, amman Allah shine shaidata”
“Aikin banza, haka kawai za ki nemi batawa mutum aiki da suna?”
“Wallahi ba bata masa nai ba, gaskiya na fada”
“Wannan duk shairin makiya ne, so kawai take ta bata min suna, dan haka su saka ta a cell sai ta fada muku wanda ya saka ta yin wannan sherin”
Cewar Doc Asim cike da gadara. Ni ko ina jin haka sai tsoro ya kamani take na saka kuka, ni ce da gaskiyata amman na risina har kasa ina rokon Doc Asim yafiya, sai ya fisge kafarsa ya daka min hannu har sai da dan yatsana ya fashe saboda zafin takalmin kafarsa. Haka suka rika ni saboda tsabar zalince suka saka ni a cell din mata ina ta kuka kamar raina zai fita. Daga cikin matan da ke cell din ta daka min tsawa wai na yi musu shiru na cika musu kunne da hayaniya, a haka nai shiru na samu guri na rabe a cikin dakin mai cike da sauro da duhu sai wari yake. Ba a bari ka fito ko da sallah za kai, fitsari ma sai dai kai a cikin cell din gaban kowa da kowa. Dukan tunani sai ya karkarta gurin Nana ban san halin da take ciki ba, ban san iya tsawon lokacin da zan dauka a nan ba. Da dare yai sai naga ana fita da mata masu kyau, can da asuba kuma aka kawo su, ni dai ina zaune jigum har safe ban saka komai a bakina ba, sai can da azahar wani dan sanda ya bude min yace na fito a nan na samu damar yin alwala na raba gafen masallacin mazan nai rama sallah da akd bina sannan na gabatar da azahar, a lokacin ne dan sanda ya kawo min abincin shimkafa da miya har da kabeji da nama, kadan na ci saboda cikina ya daure sosai bayan na gama ya bani ruwa mai sanyi na sha.
“Idan an jima da dare zan zo na dauke ki, sai mu fita mu sha iska, idan mun dawo zan yi belinki da safe kin ji”
Na gyada masa kai cike da fahimtar inda manufarsa ta dosa, ba sai ya fada min na fahimci dan iska ne, ashe abunda suke da matan da suke fita dasu da dare kenan. Yadda ya fada haka ya nufoto ni da dare guraren karfe goma sha biyu ya bude cell din wai na fito, ni ko na ki yarda na fito din, da ya shigo ya jani da karfi sai na fasa masa kuka ina ta masa ihu kamar zai sace ni a dole ta saka ya kyaleni yai tafiyarsa. A haka na kwana hudu a cikin cell babu wanda ya zo belina, abinci kuwa sai idan polisawan sun ci sun rage su ba ni raguwar ko kuma mutane za da ke cell din idan an kawo musu sun ci sun koshi sai su ba ni ragowar. A cikin kwana biyu Allah ya hada jinina da daya daga cikin yan matan cell din, na dauke ta kamar yaya ita kuma ta rike ni tamkar kanwarta kasancewar ta girme ni nesa ba kusa ba. Bata fada min dalilinta na zuwa cell din ba amman na fahimci kamar shaye-shaye take har aka kawo ta nan, da fira tai mana dadi take tambayata dalilin zuwana gurin na fada mata sai ta tausaya min sosai. Ita ce ta taimaka min ta fitar da ni daga cell a lokacin da aka zo belinta sai akai belinmu mu biyu ni da ita.