Zaki complete by khadeeja candy - Chapter 7
Zaki complete by khadeeja candy Chapter 7: Zaki complete by khadeeja candy Chapter 7. Ranar da na fito daga cell din har iskar sai na ji ta badan ina ra…
4,384 words
Ranar da na fito daga cell din har iskar sai na ji ta badan ina ra jina kamar mai hanci, abu ga marasa shi, daga station din zuwa uduth akwai dan karen nisa amman haka na taka da kafa idan na gaji sai na tsaya na hutu har na isa cikin asibitin, ban san time din da na isa ba, sai dai da naje sai suka hanani shiga, a gurin na zauna har hudu tai sannan na shiga ciki, gurin da na san na bar Nana na nufa sai na samu babu ita a gurin gadon ma har an dora wata, ban tambayi kowa ina take ba na juyo na kamo hanyar Clapperto ina kuka. A iya tunani Nana ta rasu, idan ma ta rasu ina suka kai gawarta? Kangon gidan na nufo sai na tarar an saka kwano an zagaye shi an rufe ruf ba ta inda mutum zai iya shiga, a gurin na zauna nai ta rare kukana sai da nai mai isata, ban dauki wannan abun komai ba, face kaddara da kuma jarabawar rayuwa wacce ko waji dan adam yake fuskanta sai dai kowa da irin tasa, amman a iya ganina da jina ban tana ganin wanda ya shiga matsanaiciyar rayuwar da na shiga ba, kullum abun gaba yake ba baya ba, idan na natsu ina tunani sai na ga ban kashe kowa ba, ban hada Allah da wani ba, amman abubuwan da suke faruwa da ni kamar na kauce hanya ne, wata kila akwai wani abun da na ke ba daidai shiyasa Allah yake jarrabani, kuka nai mai isa ta sannan na tashi na doshi gidansu kawata Farida. Ina shiga ta yo kaina da gudu ta dafani.
“Ataa ina kika shiga? Mi ya same ki wannan irin ramar fa? Duk kin yi baki kamar ba ke ba”
Kasa amsa mata nai sai kawai na fashe da kuka.
“Ataa ina kika shiga? Hankali Nana duk ya tashi kullum zancen ki take”
“Nana tana nan?”
“Gata a can”
Ta nuna min wani tsohon kitchen dinsu, da gudu na nufi kitchen din ina shiga na samu Nana kwance sai kawai na fada jikinta na fashe da sabon kuka na rumgumeta kankan ina jin kamar wani zai rabani da ita. Ita kukan take ni da ita sai aka rasa mai rarrashi wani, Farida ma da ke tsaye jikin kofa tana kallon mu kuka take.
“Haba Ataa ke kuka ita kuka sai ki saka zuciyarta rauni ai”
Maganar Farida ce tasa na tsagaita kukana na share hawayena ita na saka hannuna na share mata hawayenta. Ta rame sosai wata kila ko abinci bata samu sosai ya akai ma ta bar asibitin ta dawo nan? Ganin na daina kukan yasa Farida ta fita ta bar ni daga ni sai Nana.
“Nana ina Lukman?”
“Yana gidansa na gaskiya, sai idan Allah ya hada mu”
Wani sabon kuka na ji na cika min ido, sai tausayinta da shakuwarta da Lukman ta rufe ni, daman daga ni sai ita sai Lukman muka rage, yanzu kuma ya tafi ya bar mu mu biyu kawai.
“Ina kika je Ataa”
“Karar wannan likitan na kai gurin yan sanda akan rashin kula da ke da yai da kyau, sai ya juyar da abun a kaina suka rufe a cell sai da wata mata ta fitar da ni”
“Ranar da kika bar ni ban iya kwana cikin asibitin nan ba, sai na saci kafa da suna zuwa bandaki na gudo na dawo gida, a nan na tararda gawar dana, na nemi taimakon mutane akai masa wanka aka siya masa likkafai akai masa sallah aka je makabarta aka binnesa, a ranar mai gidan nan ya turo aka kore mu, da safe ana kewaye masa gurinsa dan kar mu sake zama, Farida ce tasa muka dawo nan ta ba ni kitchen dinsu na zauna a nan nake ta rayuwa da tunaninki, na dauka ma ke ma kin mutu kin bar ni ni kadai”
Na kama hannunta hawaye na min zuba kamar yadda ita suke mata zuba.
“Ban mutu ba Nana, kuma ba zan tafi na barki ba, kuma In-Sha-Allah za ki samu lafiya sosai, zan nema miki magani In-Sha-Allahu”
“Aa ba sai kin nema min magani ba, dawainiyar da kikai da ni ma Allah ya miki albarka, da kuciyarki kin fada cikin wata rayuwa mai tsananin wahala da sarkakiya, kina fuskantar kalubale kala kala na rayuwa”
“Idan ban nema miki lafiya Nana wa zan nemawa? Ba ni da wani wanda ya fiki a gurina, ganinki kawai yana sani kwanciyar hankali”
Dan murmushi tai sai ta koma ta kishingida da alama har yanzu lafiyar bata wadace ba, taya ma zata wadace bayan ba a nema mata magani ba, ba a mata maganin daya dace ta sha ba. Babu abunda ke zuciyata sai Allah ya isa da na ke yi ma azzalumi likitan marar imani da tausayi. A gurin muka kwana ni da ita cikin matsuwa domin ba kitchen mai fadi ba, gashi duk ya kone saboda girkin da akai cikinsa can baya kamin su daina girki ciki, da dare Farida ta kawo mana abinci da alama ma tuwonta ne wanda zata ci ta kawo mana, dan nasan mahaifiyarta ba zata taba dauka tuwo ta ba mu ba, balle yadda ake fama da tsadar rayuwar nan. Bayan mun gama sallah asuba, Nana ta koma bachi, ni kuma na daddaka gawayin da na shafa a fuskata, na yafa hijabina na fito ba tare da sanin kowa ba, da kafa na taka har unguwar Nasarawa, babban unguwa ce ta manyan masu kudi da yan siyasa gida gida na soma shiga ina tambayar aiki, a ganina samun aikin zai fi min bara, domin bana sha'awar baran tun da na rasa dan'uwana Lukman, amman aikin zan iya samun abinci har na kawo wa Nana. A haka har na fada wani babban gida mai cike da fulawoyi da manyan motoci, da fari mai gadin gidan hana ni shiga yai, bayan na juyo sai kuma na ji ya kirani.
“Ke zo ana kiranki”
Da sauri na dawo na shiga cikin gidan, shi ya nuna min kofar har na isa gaban kofar na tsaya ina ta kallon inda mutane za su fito. Zuwa can na ga wata mace ta fito wacce kudi da jindadi da rayuwar hutu suka gama bayyana kansu a jikinta. Tana kallona sai ta ya mutsa fuska.
“Me kike so?”
“Aiki”
Na Fada da sauri, sai ta kalli sama da kasa ta dan tabe baki ta juya cikin falon kamar tana magana da wani, bayan yan mintuna mutumen da na taba fasawa mota kuma mutumen da ya taba jefar da rigarsa saboda na taba shi ya fito cikin farar shadda riga da wando, fuskarsa kamar ta ranar nan babu yabo ba fallasa, sai kwarjini da haifa, kallo daya nai masa na sadda kaina kasa, yau kan ban ji tsoronsa kamar yadda na saba ji ba, wata kila saboda uzurin da ke gaba ne, ko kuma dan na kawo kaina a gidansa ne.
“Look at her face, wannan ai ta cika kazanta”
Yai magana kamar ba shi ba, ashe dai yana magana mai sauti har ta fito haka. Cikin sauri da rawar jiki na ce.
“Zan wanke wallahi zan gyara ko a nan aka ba ni ruwa wankewa zan yi”
“Nawa ake biyanki a wata?”
“Ban taba yin aiki ba”
“Ba ki taba ba?”
Matar ta tambaya tana kwantawa jikin mijin na ta, shi kuma ya rumgume yana mata magana kadan-kadan, ban san mi ya ce mata ba sai naga ta dago ta kalleni.
“Zan a baki dubu 8000 a wata hakan ya miki?”
“Ya min amman ina rokon ki fara bani kudin yanzu”
“Saboda mi? Kin taba ganin inda akai haka?”
“Mahaifiyata bata da lafiya, ina son na siya mata magani da abinci, ni kuma na miki alkawarin yin aikin har wata ya kare”
“Na baki kudi ki gudu?”
“Kin fi karfin dubu takwas Hajiya, kuma ni miye ribata idan kin ba ni kudin na gudu? Idan ban miki aikin ba, zan biyaki kudin a lahira, mahaifiyata ce bata jindadi ki taimaka min da girman Allah”
Na fada cikin roko da neman alfarma, amman matar nan ta murje ido ta ce ita bata yarda ba, ba za ta ba ni kudi na gudu ba.
“Ina ne gidanku ina iyayenki suke?”
Na kwatanta mata tare da fada mata cewar ba mu da gida wani guri ne mike rabe.
“Dear Za mu bata kudin, lafiya tana da muhimmanci sosai, naga hakan tun a kan ki, idan ta gudu da kudin ta yi wa kanta”
Mijinta ne yai wannan maganar yana yana shafa bayanta, da alama yana son matarsa sosai. Ita kuma ta lake kafada wai bata yarda ba, ita ba za a bani kudin ba.
“Aa zata iya guduwa da su, baka san halin irin mabaratan nan ba, idan kin shirya ki shigo ciki ki fara aikin”
Tana fadar hakan ta juya ya shige ciki, ni kuma na tako dan stairs din da ke gurin da zimmar shiga ciki sai kuma nai tsaye ganin yadda mijinta ya tsaya a kofar yana ta min kallon kyama.
“Ki koma gida ki wanke wannan bakin na fuskarka ki and make sure kin canja kayanki kin yi wanka kin fito fresh sannan ki dawo aikin nan”
Ya fada yana jefo min kudin da nake saka ran sun fi dubu takwas din ya juya ya shigewarsa, ni kuma na duka da sauri na kwashi yan dari biyar biyar din jikina har rawa yake... *Z A K I*
By Khadeeja Candy
1️⃣2️⃣
Kamar wacce akai wa kyauta makka yana na nufo gida farinciki ya cika min zuciya. Ina tafe fuskarta dauke da murmushi duk wanda ya kalleni ya san ina cikin farinciki a yau. Sallamar shiga gidansu Farida ma da karfi nai ta Mahaifiyar Farida na tsakar gida zaune tana gyara Alayyahu har kasa na risina na gaishe ta sai ta masa sama-sama sannan ta bawa banza ajiyata ni kuma na tashi na nufi kitchen da Nana take. Kwance na same ta kamar yadda na fita na barta. Kusa da ita na zauna ina washe hakora.
“Nana na samo kudi har dubu takwas”
Dan dagowa tai ta kalleni cike da mamaki.
“Ina kika kudi har haka, bara ki kai?”
“A'a ai ba zan sake yin bara ba, sanadin raban nan aka kade Lukman, bana ma marmarin sake komawa bara, wani gida naje na ce musu zan yi musu aiki, amman sai sun fara bani kudi sannan na fara, na fada musu cewar Mahaifiyata bata da lafiya”
“Kuma suka yarda suka ba ki?”
“Matar ba ta yarda ba, mijin ne ya ba ni”
Hannu ta shafa kaina tana murmushi.
“Allah ya miki albarka, wannan kalubale da kika fuskata tun a yanzu da kurciyarki Allah ya tallafa miki ya baki wanda zai mutunta ki ya zame miki gata”
Kasa amsawa nai a fili saboda kunya, sai a zuciyata na amsa da Amin.
“Nana ina takardar msganin take sai naje na siyo”
“Ban zo da takardar ba, komai a can ya bar asibiti”
“Kai amman ban jidadi ba, yanzu ya zamu yi kenan?”
“Ataa ki daina dorawa kanki damuwa da wahalar da kanki a kaina”
“Idan ban miki ba wa zan yi ma, ba ni da kowa a yanzu sai ke, idan na rasa ki ban san iya halin da zan shiga ba”
Na fada idona tab da hawaye. Sai tai murmushi tana ta kallona cike da kauna.
“Ko asibintin za mu koma?”
“Asibiti babu komai sai cin kudi, kara ma kije gurin masu magani ki siyo abunda ya sawwaka, sauran kudin ki siyo mana abinci da su”
“Amman maganin chemist anya zai yi kuwa?Ai kara dai mu koma asibintin zai fi”
“Ataa na gaji da zaman asibitin nan, kuma wannan kudin idan ma muje karewa zai yi”
“Ko ya kare indai kin samu lafiya ba matsala ba ne”
“Aa kara dai mu ci abinci da su zai fi mana”
“Amman Nana rashin sha maganin zai iya janyo miki matsala fa”
“Da muje a kashe kudin ba a samu biyan bukata ba kara dai mu san mun saka a ciki, tun da kika fita ba ki ci komai ba, ni ma da nake nan ban cin ba, magani ma ai ba yayi sai da abinci”
Gaskiya ta fada, sai dai ni na fi damuwa da ciwonta fiye da abincin, na san kudin ba zai isa maganin duka ba. Ta shi nai na fita daga dakin cikin rashin jindadin duk farinciki da murnar da na ke sai suka koma ciki. Wani shagon provision na nufa na siyo mata biredi da madara da gwangwanin suga, ni kuma na siyo ma kaina gari da gida da suga sannan na dawo gidan, wannan karon Maman Farida ba tsakar gidan, hakan yasa ni jindadin wucewa na shigewa inda Nana ta ke na mika mata ledar sannan na fito da dauki kofi biyu da ruwa na koma dakin, ita na fara hadawa da ruwan sanye sannan ni kuma na hada nawa garin na saka suga na sha, yadda take fisgar biredin tana sai ka rantse da Allah ta shekara bata ci abinci ba. Tausayinta ne ya lullube, an cire mata koda daya dan zalinci, ga yunwa tana fama da ita babu mai bata sai Allah, dan ya tafi ya barta a garin nema yafiyarta. Tabbas ba zan taba manta Doc Asim ba, ba kuma zan taba yafe masa ba, sanadinsa na kwana a cell, na rasa kanena, ga mahaifiyata a halin da ba zan iya juye ganinta a haka ba. Idan zan yi tunani sai na rasa da wanne zan fara abubuwan duniya sun taru sun min tsaye a raina, har wani zafi na ke jin kirjina yana yi idan ina tunani, na rika jin zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito. Bayan mun gama na dauki kofunan na kai waje na wanke na aje mata a inda na gansu, ashe ta hangi lokacin da na aje sai ganinta nai ta fito rai a bace tana ta masifa wai mun taba mata kofi kazamai da mu, a kan idona ta dauki kofunan ta wilgar bayan gidan, na ji zafi sosai amman ban nuna mata ba, domin fadanta akan gaskiya ne, ni na taba mata abu da ban taba ba da bata min wannan maganar ba. Kitchen da muka raba na koma na dauko duka kayan wanke wanken na fito da su tsakar gidan, na je na siyo omo na debo ruwa a rijiyar gidan na zauna na wake su tas, na dauka na kai kitchen din wanda zan iya cewa dakinmu. Sannan na fito rike da soson wankanmu na dibi ruwan a robarmu na shiga bandakin tsakar gidan nai wanka, na wanka jiki sau uku sannan na saka ruwa na dauraye na fito fes da ni ni kaina har wata ni'ima na ke jin tana shiga jikina. Ban ssmu na shafa mai ba saboda yanayin garin da zafi, sai kawai na saka daya daga cikin tufafin da na ke ji da su, na dauki bakin dankwalina nai nikab da shi sannan na saka Hijab sama na duka inda kudin sukd na dauki naira dari na dan hawan acha6a, domin akwai tazara a tsakanin unguwar mu da tasu.
“Nana zan tafi”
“Yau za ki fara aikin?”
“To Allah ya taimaka ya tsare a dawo lafiya”
“Amin, ki aje wannan kudin muna cin abinci da su, idan na samu wasu wadanda suka yarda nai aikin yamma sai na rika zuwa ina musu kin ga idan an ban kudi sai na hada da wannan mu koma asibitin”
“To Allah ya nufa”
Duk maganar da nai mata da hausa nai ta ita kuma sa ta maida min da yaren da tafi kwarewa akai wato buzanci. Sai da nai mata sallama sannan na fita, ban yi nisa sosai na samu mashin na tara na hau yana sauke ni na bashi hansi ya karba ya wuce ni kuma na buga kofar gate din a hankali. Mai gadin ne ya leko yana ganina sai ya fito gaba daya.
“Baiwar Allah lafiya”
“Lafiya kalau, ni ce wacce na zo neman aiki dazu kuma suka ce sun dauke amman sai naje na shirya”
Wani kallo yai min tun daga sama na har kasa, nasan kallon baya rasa nasaba da bakin kyallen da na saka na rufe fuskata, wata kila yana munanamin zato ne.
“Bari dai na fara fada musu tukuna”
Haka ya barni tsaye a gurin ya koma ciki, ba dauki dogon lokaci ba sai gashi ya dawo ya bude min gate din.
“Ance kin shigo”
“Na gode”
Na fada ina saka kafata cikin gidan, sai a yanzu ne nake kara kare masa kallo babban gida ne da za ayi iya kiransa da aljannar duniya, ko a harabar gidan kadai aka barka zaka sha kallo tun daga kan furanni da kuma manyan motocin da ke gidan, ko wace kofa an kawata ta da furanni. A inda na naga sun fito dazun na na bi stairs din na isa gaban katuwar kofar mai kyau na yi knocked a hankali, shiru ban ji an bude kofar ba, hakan yasa na sake knocked, nan ma shiru ba a bude min ba, sai da na yi na ukun sannan aka soma motsa kofar aka bude. Mijin matar ne ya bude min yana sanye da kananan kayan, bakin wando da jar t-shirt, fukarsa kamar ta kullum babu alamar murmushi ma balle kuma ayi zancen dariya.
“Ina wuni”
Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake kamar nai son tantace abu, ni kuma nai tsaye a gurin cike da tsawalla, gabana sai faduwa yake ina jin kamar cewa zai yi ya fasa baya so. Sakin kofar yai ya juya ya koma ciki ya barni a gurin tsaye shi be cena shigo ba, kuma be ce min na tafi ba, ganin hakan yasa na yi tsaye agurin kamar an dasani, har sai da na ji muryar matar tana ce min na shigo. Kamar wata hawainiya haka na rika taka tile din mai tsantsi gudun kar na taba da karfi su ce na musu ba daidai. A kan wata babban kujera suke zaune tun na shigo falon daga ita har shi babau wanda ya kalleni balle ya ce min wani abu. Haka ma zauna a gurin kamar daman sun biyana dan na zo na zauna gabansu ne.
“Ke anya macen kwarai ce? Miyasa kika rufe fuskarki?”
Matar ta fada tana min wani kallon uku saura kwata.
“Ba komai, na fi jindadi idan na rufe fuskar ne shiyasa na rufe, ina da konuwa a fuskar ne”
Ta tabe baki.
“Bedrooms din mu za ki fara shiga ki gyara komai da nan falon sannan ki shiga kitchen ki gyara kuma ki wanke duka kayan da suke can sannan ki yi mopping ki saka mana turaren kanshi”
“To ina dakunan suke?”
Da yatsanta ta nuna inda yake har na mike tsaye sai kuma ya kira ni.
“Keee ban da sata kar ki kuskura daukar mana wani a gida”
“Ban taba sata ba a rayuwa”
Na bata amsa cike da jin zafin furucinta.
“And secondly mijina baya son kallo, kuma daga yanzu tun bakwai za ki rika zuwa kina hada mana breakfast, kuma ki gyara gidan, kuma kullum ki wanke mana bathrooms din mu”
Tana fadar hakan sai na ga jikinta ya kalleta, ya kalli sannan ya sake kallonta.
“Ban da girki, saboda shara da mopping kawai na dauke ta”
Yana fadar hakan ya mike tsaye yana wani irin kamshi turare mai dadi shaka ya hau sama, ni kuma na maida hijab dina baya na daure sannan na nufi upstairs din na soma takawa a hankali kusa da sai na ce wannan shi ne karo na farko da na taba taka stairs bayan wanda na taka a asibitin uduth, dakin farko na fara kai hannuna na tura kofar dakin, da alama dakinta ne, domin kayan mata da ke dakin suna da yawa ga gadon duk an tumurmuza shi kamar karamin yaro ya kwana kai. Bedsheet din na fara gyarawa sannan na linke kayan kayan da aje guri daban, na duba iya dubana ban ga tsinsiya ba da abun mopping ba. Hakan yasa na fito na sauko kasa can nesa da ita na tsaya.
“Ina tsintsiya?”
“Ni zan dauko miki na kawo miki?”
“Aa fada min za ki yi inda take na dauko”
A gurin ta bar ni tsaye har na kusan minti ashirin sannan ta ce.
“Tana can kofar baya ki je ki duba”
“Ina ne kofar baya?”
Sai da taja tsaki sannan ta bani amsa tana mikewa tsaye ta nufi upstairs.
“Idan kin ga dama ki duba ta can”
Inda ta nuna min na bi na je na bude kofar dake gefen falon, sai ga ni a wata karamar haraba, kusa da gen hannu nasa na dauka da bokitin na nufi fomfon dake kallon kofar na kauna na wanke bokitin sannan na fito, tsaye nai a falon inata tunani inda za samu omo na ko man wanki na zuba a ciki. Ganin bata fito ba yasa na bar ruwan a nan na koma da Tsintsinyar bedroom dinta na share shi tsaf na kwashe na na fito da datti sai kuma na rasa inda zan zuba, gashi ba ta fito ba balle na tambayeta, a dole na aje ta jikin kofa na koma dayan bedroom na share na gyara komai sannan na sauko kasa na share falon har karkashin kujera na shiga kitchen na share na hada kayan wanke wanke guri daya, a kusa da tab na samu omo sai naje na zuba a cikin ruwan mopping din na koma dakin na mopping sannan na shiga bandakin na wanke na dawo falon nai mopping na goge ko'ina sai kuma na koma kitchen din na wanke kayan cin abincin bayan na gama nai mopping din kitchen din sannan na fito na zauna a falo ina kare masa kallo a pop kadai na san ba kananan kudi aka kashe ba, balle kuma irin manyan kayan alatun kawata falo da aka cika falon da su. Ko agogon falon irin wanda na ke gani a tv ne.
ALIYU POV.
Yana shiga dakin Rahma ta biyo shi tana fadar ita bata yarda da wannan yarinyar ba shi ru yai be ce mata komai ba, yai kamar be ji ta ba sai latsar wayarsa yake.
“Ka ji, ni fa ban yarda da ita ba, jiya ta shafa wani a fuska ta zo nan duk baki yanzu kuma ya saka nikab”
Sai a lokacin ya dago ya kalleta. Kamar zai yi magana sai kuma yai shiru ya sake mai da hankalinsa gurin wayar.
“Kana jina fa”
“Mi kike son? Ke kika damu a samu mai aiki ai”
Ya fada ba tare ya kalleta ba, sai tai fushi tana mikewa tsaye yai saurin riko hannunta ya dawo da ita kusa da shi ta zauna.
“Kin cika son saka bacin rai a zuciyarki Dear, kuma kin san matsalarki, idan mai aikin ce ba ki so ai sai ki koreta kawai”
“8k din da ka bata fa?”
Yai murmushin kasaita yana kallon goshinta.
“Ai kyauta na bata ba dan aiki ba”
“Aa gaskiya sai dai tai mana aikin one month sai mu koreta, dama dai ba ka ba ta kudin ba”
Kara matsawa yai kusa da ita yasa duka hannyensa ya rike fuskarta.
“Idan na ga mutum cikin rashin lafiya, ina tausaya masa sosai, saboda na san zafi da ake ji, musamman idan mutumen nan makusancin ka ne, na auna kaina a matakinta, kin tuna lokacin da muke ta yawon neman lafiyarki?”
“Waya sani ita ko karya take, wata kila ma muguwa ce shiyasa take rufe fuska”
Be sake ce mata komai ba ya kwantar da ita kirjina ya cigaba da latsa wayarsa. After like one hour ta ďaga daga jikinsa ta sauko downstairs ganin Ataa zaune tana kallo ya bakanta mata rai sosai domin ba kowa take son yana morewa da abunta ba.
“Kin gama sharar ne da kika zauna kina kallo”
Ataa ta juyo da sauri jikinta har ba ri yake ta kalleta.
“Eh na gama tun dazu na share ko'ina na gyara”
“To daga yau karki sake rufe mana fuskarki, idan ba za ki iya bude fuska ba ko zauna a gidanku ba yadda za ki zo ki cutar da mu ki tafi ba tare da mun ha fuskarki ba”
“Wallahi ni ba na cutarta kowa”
“Ai ba za a iya ganewa a fatar ba ki ba, shiga dayan dakin ki wanke bathroom din kuma ki gyada dakin”
Tana fada mata sannan na nufi kitchen dinta dan tabbatar idan kayan sun wanku.
ATAA POV.
Daukar tsinsiyar nai na hau sama a doshi dayan dakin wanda na ke saka ran shine dakin mijin, ciki tsoro da fargaba nai knocked, sannan na ja baya kadan na tsaya ina ta jiran ace min na shigo amman shiru, sai hakan yasa ni jin babu dadi, daga fara aikina a yau na fahimci daga matar har mijin kamar ba su san darajar dan adam ba, wata kila kuma saboda na kawo kaina ne, ni da kaina ina nema shiyasa suke wulakanta ni oho. Na fi karfin minti talatin a tsaye bakin kofar sannan ya fito yana ta kamshin turare, har wani matsawa yake kai ya ra6o ta kusa da ni ya sauka downstairs. Be ba ni izinin shiga ba, dan haka ba zan shiga na taba wani abun da zai iya zan min matsala ba. Haka nai tsaye a gurin na kasa sauko kuma na kasa sai duk na ji na tsawwala, wani kankanci da bakincikin suka kwankwaso min kofa, na tabbatar da a ce yar wani ce ni da ba za su bar ni a gurin tsaye ba, za su nuna min kyama ba. Suna min duka wannan saboda ina talaka kuma na raba jikinsu ina neman taimako. Da gaji da tsayuwar ne na sauko kasa cike da fargabar abunda za ta ce min da Kuma irin kallon da mijinta zai min.
Tana zaune kan kujera ita kadai tana waya, da alama wayar tai mata dadi sai kyalkyalar dariya take tana buga kafa kasa, ni dai kallonta kawai na ke, irin rayuwar jindadi da take ciki ta burgeni ga ta cikin farinciki abunda na ke ta marmarin samu amman ya gagara, zaunawa nai kasa tile har ta gama wayar sannan na ce
“Be ce min ya na shiga ba, ni kuma ban shiga ba, gudun kar na shiga ya zama laifi”
“Ya ce baya son ki gyara masa dakinsa”
“Yanzu zan iya zuwa gida kenan?”
“Idan kin ga dama”
“Na gode”