Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 2
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 2: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 2. Kafin magriba na kafa kaskon a warata saboda har anfara…
2,953 words
Kafin magriba na kafa kaskon a warata saboda har anfara zuwa nema.ina tsaka da suyar awarar bayan sallar magriba, abun mamaki,gwaggo ta fito daga daki da saurinta. Maryam zo kije gidan lantana yanzunannan zaki karbomin wani sako,kiyi sauri sakonna saurine,kuma kinga da sauran awara karki zauna. "Toh gwaggo insha Allahu bazan zaunaba,dakina nanufa da niyyar in shiga na dakko hijabi,saboda na jikina yana dan kauri kaurin hayaki,amma gwaggo ta dakamun wata irin tsawa," gidan uwarwa zaki kuma bayan na fada miki sauri nakeyi. Da sauri nayi hanyar fita,jikina na rawa.lantana tana gandun sarki ne,da dan nisa tsakaninmu hakan yasa nake tafiya da dan sauri sauri.....
Text yayiwa mommy zeje gurin abokinsa,lukman saboda damunsa dayakeyi akan bayason zuwa wajensa sedaishi yayita zuwa.mommy tana ganin text dinsa tayi murmushi, domin dama sometimes yasaba mata hakan,idan zefada mata Abu befiya kirantaba,sedai ya mata text.reply ta masa akan Allah ya kiyaye hanya.shikadai yaja motarsa,yatafi batare da koda drivernsaba.......
Kusan minti goma sha biyar nayi ahanya,kafin nakarasa gidan lantana.amma nadaje lantana ta barni a tsakar gida ta shige daki,fiye da minti talatin sannan ta fito ta bani sakon.a lokacin raina yakai kololuwa wajen baci,domin nasan tana sane tamun haka,ga tsoro da fargabar abunda gwaggo zatamun yamun rufdugu akaina. Ashe sakon kudine shiyasa naga gwaggo tana rawar jiki.karba nayi na nufi gida.wajen ba mutane sosai,hasalima tunda na taho banhadu da kowaba,gudu na farayi zuciyata na bugawa,tsorone me tsanani ya kamani Wanda bansan kona meneba.......
Cikin takunsa na cikakken namiji,jarumi, yake tafiya,shida lukmanne daya rakoshi ze tafi gida,tafiya sukeyi zasu karasa gurin motarsa,dayay parking a gefen titi.kamar an cillota daga sama kawai jiyayi ta bugi kirjinsa,da sauri nayi baya jinnayi karo da mutum,banzataba banyi tsammaniba,saboda hankalina gaba daya baya jikina,yayi gida.wani daddadan kamshine yaziyarci hancina,wanda tunda uwata ta haifeni bantabajin irinsaba.wata irin bugawa kirjina yayi da karfi,jikina ya fara rawa,kaina naji ya mugun saramun, jinayi kawai nayi luuuu zanfadi,taroni yayi da tattausan hannunsa,ya hadeni da jikinsa.wani irin yammm yaji ajikinsa,tsigar jikinsa ta tashi ta mimmike,lokaci daya yanayinsa ya sauya,lumshe idonsa yayi cikin amsar bakon yanayin daya riskeshi,zuciyarsa na bugawa dasauri da sauri,kafarsace ta gagara daukarsa,kasa mukayi gabadayanmu dani dashi,shi yafarayin kasa ni kuma na fada kan faffadan kirjinsa,wani mahaukacin feeling ne yaji ya bujuro masa,jinta a kwance a kirjinsa, Wanda betaba jin irinsaba tunda yake arayuwarsa. wani irin harbawa jijiyarsa tayi ajikina,jinayi wani Abu kamar an harbomun ya zungureni.................✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
*AUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚
*Bismillahirrahmanirrahim*
0️⃣3️⃣
...........Bansan ya'akaiba kawai gani nayi na mike tsaye,jikina ya kama kyarma tamkar anjonamun schocking, wannan shine karon farko arayuwata dana taba hada jiki da wani da namijin,dayan da suke tarene ya rike hannuna,ganin bana cikin nutsuwata yace. "sannu 'yanmata,ba bakin magana se rawa kawai na jikina yakeyi,tamkar mazari.
Tattaro duk wata juriyarsa yayi,ya mike tsaye,har yanzu yanajin bakon yanayin ajikinsa.
Dakyar na tattara nutsuwata na sunkuya nadauki sakon gwaggo daya fadi kasa,Allah yasama kudin a cikin Leda ta sakamun.ban kara kallon Wanda muka fadi tareba,saboda kunya da tsananin tsoron daya rufeni. Kai na akasa,cikin rawar murya nace" ka..yi..ha..kuri...dan.. Alllah,shiru yayi kawai batare da yacemun komaiba. wani tsorone ya kara mamayeni karnaje kobe hakuraba. Dayan ne kawai yamun magana. "Karki damu 'yan mata,amma dai kidinga kula gashi dare yayi,muje mu rage miki hanya ko? A'a nagode,ina gama fadar hakan na kama hanya na fara tafiya,zuciyata cike da zullumin,kodai Wanda na buge kurmane,amma banda haka mezesa mutum yaki magana.gashi gaba daya kamshin turarensa ya gamemin jikina,Jinakeyi tamkar yana gurin har yanzu.saitin zuciyata na dafa,saboda har lokacin tana bugawa da sauri da sauri.numfashi na sauke,wani bakon yanayi dabansan na meneba yana ziyartata.
Dubansa lukman yayi ganin yanda gaba daya yanayinsa ya sauya,shi duk a tunaninsa ransane ya matukar baci akan abunda ya faru,hakuri ya hau bashi,amma seyaga ya daga masa hannu kawai,gurin motarsa ya nufa ya bata wuta.
Ikon Allah ne kawai yakaishi gida,saboda har lokacin jiyakeyi tamkar tana kwance a kirjinnnashi,wani irin yanayi yake ciki me wuyar fassarawa. Bedroom dinsa ya nufa tare da fadawa kan gadonsa,ina ze ganta,a ina zekara ganinta,ya kara rungumeta kozeji irin yanayin dayaji sanda tana kwance a kirjinsa,gashi ko fuskarta beganiba,saboda gurin ba wadataccen haske,kansa ya dafe,tare da runtse idonsa,zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri....
Kusan minti talatin nayi ahanya,saboda tunanin mutumin da na buge,se lumshe ido nakeyi saboda dadin kamshinsa,dayaki barin jikina,seda nazo kwanar gidanmu sannan na tuna da Abunda na bari,ga tuyar awara gashi gwaggo tace inyi sauri.addu'ar Neman tsari na fara karantowa a zuciyata.cike da tsananin tsoro na shiga gidan da sallama ta.gurin suyar awarar na kalla,kaskon na gani da guntun mai akasa, alamun an gama suyar awarar. Dakin gwaggo na nufa zuciyata na tsananta bugu,babu wutar nepa,amma dakin gwaggo da akwai sola. Tana zaune akan doguwar kujerar dake dakinnata,ta Dora kafa daya kan daya. Tsugunnawa nayi agabanta, "gwaggo ga sakonnaki" na furta cikin sanyin murya.
Wani mugun kallo ta jefeni dashi,tace."gidan ubanwa kika tsaya kusan awa biyu,kuma nakira lantana tacemun tun dazu ta baki sakon. Baya na farayi ina bawa gwaggo hakuri,domin bansan mezance mataba,nasan yau me kwatata a hannun gwaggo se Allah.wata wayar wuta ta janyo agefenta me matukar kauri ta zubamun agadon bayana,da gudu na tashi nayi tsakar gida ina kokarin fita waje,amma seda gwaggo ta cimmun.dukana ta hauyi kota ina,sekace jaka,ihu nakeyi da dukkan karfina ina Neman taimako,ina bata hakuri,amma tamkar kara zugata nakeyi.
Umman su saleemat wadda katangar gidansu take jikin namun gidan,itace ta shigo da saurinta.tsakiyarmu ta shiga ta rike wayar hannun gwaggo.da sauri na tashi na buya abayanta ina sakin ajiyar zuciya,akai akai.
"Ke suwaiba,ki matsamun ki bani guri kuma ki cikamun bulala,gwaggo ce take fadar haka cikin daga murya,se zaro ido takeyi ta fiffika tamkar wata sabuwar kamu.
"Bazan cikaba,gwaggo.yaza'ayi ki samu yarinya marainiyar Allah ki maidata sekace jaka,kullum sekin jibgeta haka akeyi. Tafa hannuwa gwaggo ta farayi tana salati,"ni zakiyiwa rashin kunya suwaiba,har cikin gidana.lallai wuyanki yayi kauri,kifita daga safgata suwaiba,banason shishshigin da kikemun akan maryam. "Ba shishshigi bane gaskiyace gwaggo kuma dole a fada miki,amma ni ba rashin kunya zan mikiba.Abunda kikeyi ba kya kyautawa... " yaza'ayi in kyauta in aiki yarinyar tun dazu taje ta zauna,amma se yanzu zata dawomun gida,dama nasan tun ba yauba,ai bin maza takeyi idan kuma sharri na mata kamshin turaren ubanwa takeyi,gatanan ai ki shanshanata kiji.saboda yadda gwaggo take magana cikin kakkausar murya tare da daga murya mutane 'yan gulma harsun fara shigowa gidannamu.
Juyowa umma tayi tana kallona,hawayene kawai yake kwaranya daga idona har lokacin. Tabbas taji wani kamshi a jikina,amma hakan bazesa ta gasgata maganar gwaggoba,domin tasan maryam tasan halinta ciki da waje tasan abunda zatayi da Wanda bazatayiba. "Maryam kifada mana gaskiyar abunda ya faru.labarin komai na kwashe na fadawa umma, amma kawai senaji nauyin dace mata na fadi ajikinsa,kawai sena cemata bugeshi nayi. Karyata maganata gwaggo tayi,tana cewa "wanne irin kamshine wannan daga ka buge mutum seya zauna ajikinka,inma zanfadi gaskiya infada,ai dama bayau na fara zuwa yawon karuwancinaba.hakuri umma ta kama bata,wasu matama da suka shigo hakuri suka hau bata. Dakyar gwaggo ta hakura amma da cewa tayi seta karyamun kafa taga da wadda zanna zuwa iskancinnawa. Dukan da gwaggo tamun bedameniba kamar yadda take ta faman aibatani,tana dangantani da Kalmar karuwa,durkusawa nayi agurin ina sakin kuka me tsuma zuciya.lallashina umma ta hauyi da banbaki amma Sam bana cinta bana fahimtar metake cewa, wani zafi zuciyata takemun, ahankali na mike na shige dakina bayan kowa ya watse daga gidannamu.....
9:00 pm,suke hallara akan dinning gaba dayan gidan domin yin break fast,kuku kamar yadda yasaba ya gama komai,ya jera akan dinning. Kowa ya hallara amma banda mustapha. Kiransa mommy tayi har 3 missed call amma bedagaba. Kallon suhaita tayi tace" daughter jeki duba ki gani ko lafiya yau son befitoba. Haidarne yace"haba mommy muci abincinmu kawai kinsanfa shi big bro,bawani damuwa yayi da cin abinci ba.harararsa mommy tayi,idan shi bedamuba nina damu,daughter kiyi sauri kikirawoshi.
Suhailat abunnema ya samu tashi tayi tana yiwa haidar gwalo,ta nufi part dinnasa.Baya falo hakan yasata nufar bedroom dinnasa,yana kwance idanunsa,a lumshe tamkar me bacci.tama manta da wani sakon kiranshi da'akace tayi,shaukinsa da wata muguwar sha'awarsace take fizgarta.fadawa tayi jikinsa,tana shigewa jikinsa,yayi nisa a tunanin yarinyar dabe saniba yaji mutum ajikinsa,abunda suhailat bata zato ba,kuma betaba mataba.jitayi yazagaye bayanta da hannayensa yana shafa bayan ta,yana kara matseta ajikinsa.cikin tsananin jin dadi Mara misaltuwa.suhaital ta fara kokarin kissing dinsa,soyake yaji irin yanayin dayaji dazu amma bejiba,ahankali ya bude dara_daran idansa,akan fuskar suhailat ya sauke su,da sauri ya tureta daga jikinsa, tare da mikewa zaune. ransa a matukar bace. Itama suhailat din tashi tayi ganin yanda lokaci daya ya sauya,zatayi magana yanuna mata hanyar kofa,tashi tayi tana turo baki gaba ta fice daga dakin. Tunda mommy taganta tasha jinin jikinta,ganin yanda take babbata rai,dariya haidar da zannuraini suka kwashe da ita. Haidar yace"dama seda na fada miki karkije kokinjema baze zebo. Harararsa tayi tamkar zatayi kuka tace"mommy kinga su yaa haidar ko? Mikewa mommy tayi tace"kyaleni dasu daughter.Ku zauna,kuci abincinku bari naje na sameshi.
Yana zaune kamar yanda suhailat ta barshi,mommy tashigo bedroom dinnasa.zama tayi agefensa,tare da jawoshi jikinta.cikin rarrashi tafara magana "haba my son,meyasa bakason cin abinci,baka tsoron wani ciwon yakama munkai,please kazo muje muyi dinner.shagwabe fuska yayi sekace yaro yace." Mommy a koshe nakefa, ni tea kawai zansha. Shafa kansa mommy tayi cikin tsananin kaunarsa, "shikenan my son bari naje ha hado maka. Dakanta ta dafa masa a kitchen din part dinsa,seda yasha sosai tana lallabashi kamar karamin yaro,sannan ta kyaleshi.tana fita ya nufi toilet yasakarwa kansa ruwa koyaji sanyi aransa.domin gaba daya yarasa meke damunsa......
Tunda nashiga daki nake kukan tausayin rayuwata,kusan minti goma gwaggo ta shigo dakin. "Dan ubanki bazaki tashi kikarasa sauran ayyikankiba,maganarta cikin tsawa ta sani dagowa da sauri,mikewa nayi na nufi hanyar fita.jikina a sanyaye nake aikin yau,tunanin dan gayun dana gani yamun tsaye acikin zuciyata. Seda sha biyun dare ta wuce na samu kaina,domin har girki seda nayi. Bayan na karayin wanka nayi sallar isha'i na kwanta akan tabarmata.saboda tarin gajiya da ciwon kan dake damuna saboda kukan danayi tuni bacci ya kwasheni,cikin mintuna kalilan.
*************
Karfe 7:30am,ya gama shirinsa tsaf na zuwa office. Ko break beyiba saboda batashi yakeba,mommy ma awaya ya sanar mata ya tafi.ma'aikatan gidanne suketa gaishesa,hannu kawai yake daga musu. Drivernsa,yana hangosa ya fito da sauri tare da bude masa gaban motar yana gaisheshi. Shima hannu kawai yadaga masa. Ya shige motar.
7:45 sun isa ma'aikatar tasu,kullum haka yake zuwa baya latti,saboda shi bayason karya ka'ida.driver na rike da briefcase dinsa har office dinsa.ma'aikata se kwasar gaisuwa sukeyi a gurinsa. Zama yayi akan kujerarsa.sakatariyarsa ce ta shigo office dinnasa,gaishesa tayi tare da dakko masa wasu takardu ta 'ajiye masa a gabansa,cikin girmamawa.sannan ta juya ta koma wajen zamanta.
Wata budurwace ta shigo ma'aikatar cikin wata rantsatstsiyar mota. Faka motar tata tayi agurin da'aka tanada domin ajiye motoci.tana sanye da wani Riga da siket na atamfa,dinkin Yakama jikinta sosai,ana ganin shatin komai na jikinta.taci daurinta ture kaga tsiya,ta cokaloshi.gashin dokin data kara ya sakko har gadon bayanta. Fuskarta dauke da bakin glass,takalmin dake kafarta me shegen tsinine.hannunta dauke da wayarta,da wata hadaddiyar handbag.wadda tashiga da kayan jikinta.babu mayafi a jikinta.tafiya ta farayi cikin takunta na Jan hankali.duk inda ta ratsa se'an kalleta.office dinsa ta nufa direct. Sakatariya tana zaune taga mata tashigo ta wuceta,magana ta fara mata tana kokarin dakatar da ita,amma ko juyowa batayi ta kalletaba.batare da Neman iziniba ta murda handle din kofar office din tashige. Yana cikin danne_danne a laptop,kawai yaga mace ta shigo masa,ba sallama. Dagowa yayi cike da tsantsar mamaki yana kallonta. Karasowa tayi gaban table dinnasa, Jakarta ta ajiye akai,tare da zare glass din dake sanye a idanunta,shima ta ajiyeshi. Zama tayi akan daya daga kujerun dake gaban table dinnasa,tare da Dora kafa daya kan daya.kallonta kawai ya tsaya yakeyi yanda ta dage tana abubuwa sekace office din ubanta.
Murmushi tayi akaron farko tana wani fari da idonta tace" *mustapha sulaiman me nasara* kallon mamaki kakemun ko? Aidama na fada maka bazan barkaba,kuma bazan dena bibiyarkaba harse ka soni, kota tsiya kota arziki.........✍️
Meson complete Whatsapp 0816667482
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚
*Bismillahirrahmanirrahim*
0️⃣4️⃣
..........mtssss yaja wani dogon tsaki,ya maida hankalinsa akan abunda yakeyi batare da yace mata kalaba,domin shi bashi da lokacinta.kara gyara zama tayi tana kallonsa tamkar zata lashesa.wayar dake gefensa ya latsa tare da karawa a kunne. "Kizo yanzu" kawai ya furta tare da kashe wayar.ya hade girar sama data kasa.sakatariyarsace ta shigo office din da sallama. Cikin girmamawa tace. "Sir gani" dagowa yayi yana dubanta,budurwar data shigo ya nuna mata da hannu batare da yace komaiba. Ta gane meyake nufi,maida dubanta tayi ga budurwar wadda take ta taunar cingum dinta hankali kwance,tana girgirza kafafuwanta.bayani ta fara masa cikin girmamawa. "Yallabai kawai gani nayi tataho zata shigo office dinka,ina mata magana kuma,ko saurarena batayiba,nayi kokarin hanata amma....Daga mata hannu yayi tare da nuna mata kofa.da hannunsa.ficewa tayi Daga office din,budurwar ta bita da harara.tana jifanta da wani mugun kallo.
Wani mugun kallo ya wurga mata tare da fadin"get out from my office.murmushi tayi tare da fadin," aidama bakai kace inzoba,Nina gama nazo da kaina,dan haka bangama kallonka ka bari idannaga zantafi da...."I said get out" cikin tsawa ya fada mata hakan tare da mikewa tsaye yana nuna mata kofa. Idanuwansa har kada sunyi ja saboda bacin rai.jijuyoyin kansa gaba daya sun fito rudu_rudu.tashi tayi tamaida glass dinta tare da daukar Jakarta,tace. "Zantafi mustapha amma kasani,sekayi nadama da danasanin korata da kayi da kuma wulakantani,ni nafi karfin wulakanci, saboda ina sonka,kulkum nazo seka koreni,yauce rana ta karshe dazan kara zuwa office dinka,amma kajira matakin da zan dauka,zakasan kayi da *laila*,saboda ina sonka mustapha, wulakancin yau daban,na Gobe daban.kusan 2 years ina binka ina rokanka kasoni amma kaki,amma bakomai kajira abunda ze biyo baya.tana gama fadar hakan tafice fuu,tamkar zata tashi sama.ganin yanda ta fito ya bawa sakatariyarsa dariya,kyalkyalewa tayi da dariya,daman tasan karshen zancen kenan,domin bayau laila tasaba zuwaba,yana mata wulakanci.amma kota kanta batabiba tayi tafiyarta,saboda bata ita takeba.
Komawa yayi ya zauna tare da dafe kansa,jingina jikinsa yayi ajikin kujerar,tare da lumshe idonsa.yarinyarnan jarababbiyace,Daga zuwanta tasa masa ciwon kai.wayarsace ta fara ringing cikin amo, me dadin sauti.hartayi ringing ta katse be dagaba.kara kira akayi still beyi picking ba.ankira yakai sau biyar,amma yaki picking.amma anki hakura dadena kiran. Tsaki yaja,ahankali ya bude tsumammun idanuwansa,wayartasa dake gefensa,ya dakko ya duba. *love one* yagani yana yawo akan screen din wayar,suhailat ce.katse kiran yayi ya tura mata text. _*I will call you later*_
Suhailat data shirya cikin wani rantatstsen less dinkin Riga da skirt,ya matukar kamata,tayi kyau sosai.se tashin kamshi takeyi.murmushi tayi bayan taga text dinsa,kokadan bata fushi dashi,duk kuwa wulakancin daze mata,baya damunta. dama ta shiryane ta kirasa taji muryarsa.yau ma kamar jiya,ko mayafi bata daukaba.jaka kawai ta dauka ta nufi dakin mommy.mommy tana zaune akan makeken royal bed dinta, waya takeyi da daddy,suhailat ta shigo dakin. Murmushi mommy tayi tare da fadin "gatananma ta shigo bari na bata wayar.mika mata wayar mommy tayi tace" ga daddy nan zakuyi magana.karba tayi ta cikin shagwaba tace"morning my dad,"morning my daughter. "daddy,yaushe zaka dawone munyi missing dinka dayawa fa. "Inanan dawowa my daughter ayyukane sukai mini yawa.ya karatun dafatan dai ananan anayi ko? " eh daddy"yawwa daughter kikara dagewa. "Insha Allah daddynah,bye. " yawwa 'yar albarka bawa mamanki wayar. Sallama mommy sukayi da daddy bayan ta karbi wayar. "Daughter har kin fito. " eh mommy na fito, mom nifa nagaji da rashin 'yar aikinnan,tsofaffinnan bawani Abu suka iyaba,dafa kafadarta mommy tayi tace"jiyama munyi waya da lami tacemun insha Allah yau zata binkito me aiki. "Yadaifi gaskiya mom,bari na karasa school sena dawo. "Adawo lafiaya my daughter,Allah ya kiyaye ya bada sa'a. "Ameen ta amsa tana fita daga dakin.......
Gudu takeyi sosai a mota ranta a matukar bace yake,daidai wani madaidaiçin gida ta tsaya ta fara danna horn ba kakkautawa,da sauri gate man ya taso ya wangale mata gate din gidan. Tura hancin motartata tayi da gudunta,dasauri megadi yayi gefe domin ta kusa bita kansa.parking motar tayi tare da fitowa,ko murfin motar bata rufeba ta nufi cikin gidan.
Suna zaune suna hira suka ganta ta fado dakin tamkar anjefota,jakar hannunta ta cillar tare da fadawa kan gado tana sauke numfashi,dan kwalin kanta ta cire tayi wulli dashi akan gadon.galala kawai suka saki baki suna kallonta. "Laila,lafiya kuwa meyafaru kika shigo mana a hargitse haka,ko wani abun mustapha ya miki. Tashi tayi zaune tana sauke doguwar ajiyar zuciya. Dayar da batayi maganaba ta tabe baki tare da fadin,dama nasan za'ayi haka, seda nace mata kartaje kotajema mustapha wulakantata zeyi,amma ta nace seda taje. "Haba Sakina kada kiga lefin laila,soyayyace taja mata haka.itama ba lefinta bane. Mikewa tsaye laila tayi ta fara zarya adakin, kafin ta dubesu,cikin tsananin bacin rai tace." Sakina! Habiba!, Yau itace rana ta karshe dazan kara zuwa wajen mustapha,amma wlh wlh wlh zesan ya wulakantani,seya gane ni laila nafi karfin wulakancinsa.sena masa tabo a rayuwarsa Wanda baze taba mantawa daniba,sena illata masa rayuwa.tana gama fadin hakan ta fice Daga dakin. Binbayanta sukayi da kallo dukansu.habiba tace"hmm kamar zata iya,kullum tadinga tabar mustapha amma nasan baza ta iyaba,narasa wani irin so laila takewa mustapha."hmmm, kyaleta kawai, batace zata dau matakiba,muzuba ido muga matakin dazata dauka........
**********
Yau tunda na tashi da ciwon jiki na tashi,amma haka na daure naketa ayyukana,domin nasan ban isa nace bazanyiba.karfe goma da rabi,na tashi Daga tuyar su kosai.kayan wanke _wanke na hada na koma bakin rariya na farayi.ina cikin yin wanke_wanken wata kawar gwaggo me suna lami tayi sallama,dam naji gabana ya fadi,Wanda bansan dalilin hakanba.addu'a na hauyi a cikin zuciyata. Amsa mata sallamar nayi ina mata sannu da zuwa.wani kallo naga tana bina dashi Wanda bansan kona meneneba. Nidai na gaisheta naci gaba da aikina. Yau kam naci sa'a data shigo bata zageniba,amma tabbas nasan kafin tatafi seta kullamun wani sharrin.