Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 3

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 3

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 3: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 3. Gwaggo tana dakinta a kwance tayi shurum sekace kayan…

3,146 words

Gwaggo tana dakinta a kwance tayi shurum sekace kayan wanki,ta kure radio tana jin waka.lami tashigo dakinnata. "Hajiya lami manya manyan kasa yau kece a gidannawa,nasan ganinki alkhairine. Gwaggo ta fadi haka tana tashi zaune,tare da rage sautin radionnata.zama hajiya lami tayi agefenta ta bata hannu suka kashe,tace wlh kam ladi,yau kinganni wata samuwace tasa nazo gurinki,arziki ne na kawo miki idan kinaso. Gyara zama gwaggo tayi ta fuskanci lami tace" dagaske lami, fadamun menene? "To,dafarko dai kinsan alhaji sulaiman menasara. "Haba lami nasanshi mana,mutumin dayayi fice a garin kano dama kasar baki daya,saboda tarin dukiyarsa da ma'aikatunsa. "Yawwa 'yar gari Ashe kingane,to nima wata hajiyace take zuwa gidansa,gurin matarsa.jiya jiyannan ta kirani tace mun nasamo,'yar aiki,gidan suna bukatar 'yar aiki kuma yarinya sukeso me jini ajika shine nace bari nazo gurinki nasan zaki bada marya......me kike nufi lami duk 'yan kauye da masu Neman aikatau kirasa wazaki ce zaki kai aiki sai maryam,gwaggo takatseta da saurinta. Dafa kafadarta lami tayi,kwantar da hankalinki kawata abun bana zafi bane,da arziki agidan wasu ai gwara agidanku,ki bar maryam din mana taje tayi aikin. " Sam_Sam lami,bazata sabuba,yanzu idanna bada maryam aikatau Waze dinga kula da sana'ata,Waze dingamun aikin gida,kuma sannan 'yan uwanmu na kauye,se sun tambayeni ina nakai maryam. "Wannan duk ba matsala bane ladi, nasan kudin da kike samu a sana'arki a wata bekai 200,000 to ita duk wata zata dinga biyanki 200,000.kinga ya isheki kinemo 'yar aiki kema idan kinaso ta dinga miki,ko 30,000 kika bata zata miki,kinga kinci riba biyu gata Sana'a gata aikin maryam. Jinjina kai gwaggo takeyi cike da mamaki tace " yanzu lami dan aikin gidan da maryam zata musu shine zasu ringa bata 200,000 anya kuwa lami gaskiyane. "To mene 200,000 a gidan alh,sulaiman menasara,kinga idan baza ki iyaba innemi wata.lami ta yunkura zata yashi. Dasauri gwaggo ta dakatar da ita,Haba lami karki tafi mana,200,000 aiba wasa bace,shikenan na amince,idanma yanzu kikeson tafiya da maryam din gatanan kutafi. Dariya lami tayi tace" shegiya kawata taji nera,daman nasan zaki yarda,kokefa yanzu zakiga kin canza kin fito gari. "Allah ko kawata gwaggo ta bata hannu suka tafa,wayaki kudi,ai kudi sine jin dadin rayuwa,barima na kirata ta hada kayanta seku wuce,aiba jira babu jinkiri. " gaskiya kam,domin suna bukatar me aiki da gaggawa,ayanda hajiyar tacemun. "maryam,maryam maryam, gwaggo ta hau kwalomun kira rass!!! Gabana ya yankeya fadi domin nasan kiran gwaggo ba alkhairi bane,dama nasan za'a rina,da sauri na amsa tare da tashi na nufi dakinnata. Durkusawa nayi agabanta, "gani gwaggo. "Yawwa maryam koma dakinki ki hado kayanki zaku tafi da lami zata kaiki wani gida aikatau,gwaggo ta fadi haka cikin halin ko'in kula.

..Zaro idanuwana nayi waje cikin kidima nace"gwaggo wanne aikin kuma. Wata muguwar harara ta cillomun tace"aikin uwarki,gidan alh.Suleiman menasara zakije ki musu aikatau. Dasauri na dafe kirjina,saboda wata irin bugawa da zuciyata tayi."nashiga uku gwaggo,rarrafawa nayi na karasa gareta,kafafuwanta na kama idona na zubda hawaye,nace"gwaggo dan girman Allah,Dan darajar annabi muhammadu S.A.W. gwaggo,karki kaini aikatau,kiduba maraicina gwaggo,kada ki kaini inda ba'asan mutuncinaba,zanzauna dake,zan miki duk abunda kikeso,idan wani lefin na miki kikace haka,kiyi hakuri dan Allah,bazan kuma mikiba wlh, kirufamun asiri kamar yadda Allah yarufa miki,kici gaba da rikeni gwaggo....wata hambara ta kaimu da kafarta,baya nayi ina sakin kuka me tsuma zuciya,tausayin kaina da rayuwata nakeyi. Lami data saki baki tana kallona tace"ladi! Kai amma yarinya akwai bakin ciki,wannan ba 'yar halak bace,ba 'yar daza'ayi arziki da ita bace.banda haka keda zakije gidan Hutu gidan dadi,mene abun damuwa.aikin dazakiyi bawani meyawa bane,gidan burjik yake da ma'aikata.kawaidai sunasan yarinyane..."bar bata bakinki wajen yimata bayani lami,dolenema taje aikinnan dan ubanta,ko yanka naman jikinta zasu dingayi,zaki tashi kije ki shirya kose nazo na tattakaki.da gudu na tashi memakon na nufi dakina kamar yadda gwaggo tace sena fice na nufi gidan su saleemat.

Umma tana tsakar gida akan kujera tana tsintar shinkafa,nafada kanta ina sakin wani marayan kuka. Dasauri ta dagoni tana tambayata "lafiya maryam,meyafaru me gwaggon ta miki? Cikin shashshekar kuka nace" umma kitaimakeni wai gwaggo aiki zata kaini gidan alh.sulaiman menasara,wlh umma banason zuwa masu kudinnan basanin darajar mutum sukayiba,umma burina Inyi ilimi me zurfi arayuwata amma gwaggo ta hanani,kuma hakanma be ishetaba seta kaini aika....kuka ne yaci karfina.rungumeni umma tayi a jikinta cikin sanyin murya ta fara mun magana"kiyi hakuri maryam,kowanne bawa da irin tasa kaddarar,haka taki kaddarar tazo miki,kiyi hakuri kije kiyi aikin zakiga ribar abun agaba.kedai kawai duk inda kika tsinci kanki ki rike mutunci,da gaskiya, kiji tsoron Allah akan duk abunda zakiyi,zaki samu nasara. "Haba umma,menayiwa gwaggo dazata kaini aikatau,aikatau dinma gidan babban mekudi.

Dagoni umma tayi Daga jikinta ta fara sharemun hawayena"kiyi hakuri maryam,ni kaina na girgiza nayi mamaki dajin gidan daza kije aiki,amma ita gwaggon ta inama tasan gidan mesanaran,harda zata kaiki aiki can. "Wlh nima umma bansaniba,kawartace lami tazo shine tace inbita muje ta kaini. Jinjina kai umma tayi tace."nasan son kudin gwaggo ne zesa ta amince,batare da tunanin irin rayuwar dazakiyi agidanba,kokuma halin dazaki shigaba,ita dai kawai taturaki kiyi aiki duk wata abata kudinta,amma abun da mamaki ace yanzu kamar wannan gidan basu da me aiki,anya kuwa babu wani lauje cikin nadi. " umma nima abun da nake tunani kenan,ina tunanin zuwana gidan ba alkhairi bane,dan yau gaba daya jikina asanyaye yake,tunda na tashi gabana yake ta faduwa,Ashe ga abunda zesameni. "Kidena cewa haka maryam kitashi kije kar tayi ta jiranki,Allah yana tare da me gaskiya, zamuyi ta tayaki da addu'a kema kuma kidage,domin babu abunda ya gagari ubangiji. Hawayen fuskata na share,nace. "Yanzu umma shikenan tafiya zanyi,in fuskanci wata sabuwar rayuwar,tafiya zanyi inbarku,kukadaine mutanen danake gani nakejin dadi,inajinki umma tamkar uwata dana rasa,a kullum kina nunamun rayuwa kina fadamun abunda yake na dai_dai,ga 'yar uwata kuma saleemah me kaunata dason ganin farin cikina,yanzu idannatafi na barku,Waze dinga mun abunda kukemun gaskiya umma bazan iyaba" zaki iya umma ta katseni da sauri,kada ki damu maryam ai bamu rabuba,nahar abada,duk sanda kika samu lokaci sekidinga kawo mana ziyara.jin muryar gwaggo nayi har gidan su saleemat tana kwalamun kira.zanyi magana umma ta hanani."tashi kije maryam Allah ya bada sa'a.kisa aranki Allah yana tare dake akoda yaushe.cikin sanyin jiki na mike,inajan kafafuwana dasukamun nauyi. Gaskiya na yadda gwaggo bata kaunata,bata daukeni a matsayin komaiba.anya kuwa zan iya zuwa aikatau dinnan,zuciyatace ta fara bani shawara in gudu kauye kawai wajen 'yan uwan innata........✍️

Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

*Bismillahirrahmanirrahim*

0️⃣5️⃣

...........Saboda naji hankalina be kwanta da aikatau dinnan dazaniba,haka dai na daure nafice Daga gidansu saleemat. A soron gidanmu naci karo da gwaggo ina kokarin shiga tana kokarin fita.wani gigitaccen mari ta wankeni dashi. "Dan ubanki kinaji nace miki sauri akeyi shine kika fice kin tafi sanarwa kanwar ubannakiko,to dakika fada mata ta hanaki tafiya mana,zaki wuce ki tafi kose naci ubanki,gwaggo ta karashe zancen tana rankwashina.hannuna dafe da kuncina,idanuna na zubar da hawaye nake duban gwaggo.

Tsugunnawa nayi akan gwiwoyina na kama kafarta ina rokonta a karo na biyu." Gwaggo kimun rai,karki kaini aikatau dinnan naji hankalina be kwanta dashiba inajin tamkar zuwana ba alkhairi ba.....hanbari gwaggo tayi yasani kasa karasa zancena,baya nayi ina kara volume din kukana,matsowa gwaggo tayi da nufin yimun shegen duka.lami ce tataho daga cikin gidan jin kukana ta rike gwaggo. "Haba ladi,kin manta inda zamujene da ita,sokike suki daukarta kinsan halin maryam yanzu kina dukanta seta langwabe.sakin gwaggo tayi ta kamoni,tashi kije ki shirya mu wuce,kema kece da taurin kan tsiya,banda haka ni banga abunga damuwa ananba,gidan hutufa zaki cigabane yasameki.tafiya na farayi tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,na nufi cikin gidanmu.gwaggo tana bina da wata uwar harara.

bani yanda zanyi bani da zabi,bani da mafita banda nabi lami.jikina a sanyaye,haka na hada 'yan tsummokarana acikin bakko.hawayene kawai yake malala a idanuwana.harna gama hada kayana.ko wanka da cin abinci gwaggo bata barni nayiba,haka nabi lami ina kuka kasharban,mutuwar innata tadawomun sabuwa tamkar yau ta mutu,nasan datananan dahaka bata faru daniba.amma gwaggo ko tausayina batajiba.sema jaddadamun takeyi nayi aiki da kyau,nayi duk abunda aka sani na bisu sauda kafa.......

Files ne da yawa agabansa yana signing ajiki,wayarsa dake gefe ta fara ruri alamar tana bukatar agaji.a hankali ya mika hannunsa ya dakko,mahaifinsane yake kiransa.Daga wayar yayi ya kara a kunnensa. " Assalamu alaikum" ya furta cikin daddadarr muryarsa. Cikin tsananin farin cikin jin muryar dannasa,daddy ya amsa masa sallamarsa,gaisawa sukayi ya tambayesa ayyuka da komai da komai.sanar masa daddy yayi ya shirya yau da yamma,yaje a abuja zasuyi meeting da wasu abokanan kasuwancinsa,saboda shi abubuwa sun rikesa baze samu damar dawowa kasa yanzuba.fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa masa da insha Allah.ajiye wayar yayi bayan sunyi sallama. Shikam Sam zuwa abujannan bemasa dadiba,saboda bayason yayi nisa da 'yan uwansa da mahaifiyarsa,amma babu yanda zeyi dole yaje,saboda babu jayayya tsakaninsa da mahaifansa.yarasa meyasa mahaifinsa,komai na harkar kasuwancinsa yake dorashi,duk da yanada manyan yara amintattu,amma komai shiyake sawa akan gaba,gashi shi kuma bayason Hulda da mutane.bayason hayaniya kokadan.ganin zaman zebata masa time,yasashi mikewa ya dakko white paper yayi rubutu akan tafiyar dazeyi na tsawon sati biyu.sakatariyarsa ya kira ya bata takarda dayayi rubutu takaiwa manager na company........

Adaidata sahu mukahau nida lami har lokacin hawaye kawai nake fitarwa Daga idanuwana,munyi tafiya me nisa sannan muka iso wata unguwa,wadda bansantaba,lokacinma dazamu hau adaidaita sahun banji inda lami tace masaba,saboda hankalina baya jikina.sallamarsa tayi muka nufi wani madaidaicin gida me kyau.matane dayawa a falon da muka shiga kala_kala.sannu lami ta musu muka nufi wani daki dake cikin falon.nidai binta kawai nakeyi tamkar rakumi da akala.wata matace kwance akan gadon dakin da muka shiga,farace sosai amma kana ganinta kasan ta kara Dana kanti,tana dan kiba.tana ganinmu ta tatashi zaune da fara'arta tana mana sannu da zuwa."kai gaskiya lami naji dadin ganinki,dama hajiya tanata kirana.tsugunnawa lami tayi agabanta tana kwasar gaisuwa,nima tsugunnawa nayi kamar yadda lami tayi cikin ladabi na gaisheta.wani kallo naga tana bina dashi Wanda nakasa gane ma'anarsa.murmushi tayi tare da kamo hannuna. "Matsonan 'yata kinji.shiru nayi tare da sunkuyar da kaina kasa.ina wasa da yatsun hannuna.kallon lami tayi tace"lami ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar haka.inafatadai kamar irin wadda nace miki anaso kika samo wato Mara gata.wani irin harbawa zuciyata tayi,araina nace.Mara gata kuma,to ina matarnan zata kaini,mezasuyimun da suke bukatar mata gata,Irina. innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,ya Allah kakawomun dauki a duk....maganar lamice ta katsemun zancen zucin danakeyi. "eh hajiya kamar irin wadda kikace kinaso nasamo,insha Allah baki da matsalar komai.dasauri na dago ina duban. Lami.idanuwana gaba daya sunyo waje,zuciyata na bugawa da sauri _dasauri.alamun tsoro da razani sun bayyana karara akan fuskata. Dafa kafadata matar tayi "kada kidamu 'yata ba wani Abu bane,gidan Hutu zakije dan aikin dazakiyi kadanne.ga fuskarkinanma kinci kuka kin koshi,nasan kewar gidane,amma candinma a hankali zaki saba dashi.maida kallonta tayi ga lami. "lami nagode sosaifa,barina kawo miki sakonki.itama zatayi wankane taci abinci sannnan na kaita gidan hajiya. Kudi me yawa ta bawa,lami Wanda bansan konawa bane,tatafi.kamar yanda ta fada haka tasa aka kawomun abinci me rai da lafiya,da farko kinci nayi amma matarnan tatakuramun dole naci.sejana takeyi ajikinta.bata nunamun kyamar komaiba,abun har mamaki ya bani.wanka tasa nayi ta kawo wata doguwar Riga me kyau,me adon duwatsu.rigar tamun kyau sosai,hijabin danazo dashi na Dora ajikina.umartata tayi na kwanta akan gadonta na dan runtsa,domin taga da alamun gajiya a tattare dani.kwanciya nayi tare da lumshe idona na fada duniyar tunani.saboda halin danake ciki bazan iya wani bacciba.

Kafin la'asar ya gama bucking komai na tafiyarsa,karfe biyar jirginsu ze tashi.misalin karfe hudu ya fito cikin shirinsa tsaf,fuskarnan kamar kodayaushe babu walwala,a tsuke take.musammanma yauda yake jimamun barin gida.gaba daya kannensa da mahaifiyarsa ne zasu masa rakiya zuwa airport. Amma banda suhailat,har time din tana school.Mommy tace akirata,yace ta kyaleta idan yaje ze kirata. domin yasan makarantarma seta baro gaba data tazo tayi ta masa kukan shagwaba,shikuma babu abunda ya tsana sama da kukan mace arayuwarsa.haka suka rankaya suka rakashi,seda jirginsu ya tashi sannan suka nufo gida cike da tsananin kewarsa.........

Nikadai kwance a daki matar gidan ta fita gurin bakinta,har akayi sallar azhar na kasa bacci,sakawa da kuncewa kawai nakeyi,ina tunanin rayuwata.tashi nayi nayi sallar azhar bayan na idar na jero nafiloli tare da mikawa me duka kukana,akan yakareni aduk inda nake.nadade a zaune akan sallaya harsaida naji zuciyata tayi sanyi,kafin na mike nakoma kan gadon na kwanta.mintuna kadan bacci ya daukeni,abunka da babu a house,najini akan lallausar katifa.cikin baccina naji ana bubbugamun bayana ahankali.bude idanuwana nayi,ina karewa inda nake kallo.da sauri na tashi zaune saboda tunowa da inda nake.matar nance tsaye akaina tanamun murmushi. Shafa kumatuna tayi tace,am sorry natasheki Daga baccin ko,lokacine yana kurewa kitashi kiyi sallah semu wuce.kaina kawai na Daga mata,ina bin bayanta da kallo.mamakinta gaba daya ya cikani yanda kokadan bata kyamata.sauka nayi daka kan gadon na nufi toilet na dauro alwala.kafin na idar da sallah Ankara kawomun wani abincin.shima cewa nayi bazanciba,saboda akoshe nake.amma matarnan tatakuramun na tsakuri kadan naci.inagama ci muka dauki hanya,saboda kar dare yayi. wata mota me kyan gaske,muka shiga,abaya muka zauna nida ita se direbanta agaba.yana tukamu.

Tafiya mukayi me dan nisa,sannan muka shigo wata unguwa,me matukar kyau da tsari.yanayin layikan unguwarma kadai abun burgewane.kowanne layi da get dinsa,gashi kowanne gida andankarashi wannan yana wane wannan, wannan yana wane wannan. Araina nake cewa dama da irin wannan unguwannin a garin kano,wani layi naga mun karya kwana munshiga get dinsa.wani makeken gida nagani a hannun damana,Wanda tunda nashigo unguwar banga me kyau da girmansa da tsaruwarsaba.sakar baki nayi ina kallonsa,ko wanene me wannan dankareren gidan oho,kai wannan sedai gidan wani babban dan siyasane.wannan gida haka sekace akasar turai.get din farko na gidan muka wuce,tafiya kadan na kara ganin wani get din agaba.Wanda anan drivan hajiya ya fara horn.rasss,gabana yayanke ya fadi,badai wannan gidan za'akaini aikatauba,shikenan lami ta saidani,gidan 'yan yankankai akakawoni.tunanina ya tsayane daidai lokacin daka wangalemana kofar get din gidan,me matukar girma.harabar gidan kanta katuwace ta isa a gina kamar gidanmu uku acikinta,wannan ma hasashenane kawai amma banga karshentaba.parking space muka nufa,Wanda aka lullubeshi da wata runfa,motocine dayawa a gurin.nidai sakar baki nayi ina kallon ikon Allah.ga wasu mutane datunda muka shigo gidan nake ganinsu,masu korayen kaya,suna shawagi kamar dai security ne.kama hannuna matar tayi tana murmushi. "Maryam mun iso gidanfa,seki fito mu nufi ciki.wani gwauron numfashi na sauke,ina dubanta.bude murfin motar tayi bayan ta sakarmin hannuna,bin bayanta nayi nima na fice Daga motar.ina rungume da 'yan kayana.

Bansan tayaya zan misalta kyawu da tsaruwar gidanba,tare kuma da girmansa.part,part ne da yawa agidan,tsakanin kowanne da dan'uwansa akwai tafiya.mun wuce na1,na 2.na uku naga ta nufa,Wanda yafi duka wadanda muka wuce kyau da tsaruwa.

Matattakala muka fara takawa,wadda take abakin part din,hawa hudu muka iso bakin kofar part din,wani Abu naga hajiya ta danna Wanda bansan komeneneba.mintuna kadan wata mata da bazata wuce shekara talatinba tazo ta bude mana kofar.aljannar duniya na fada lokacin Dana ganni acikin wani hadadden falo,Wanda ko'a mafarki bantaba tunanin shigarsaba a rayuwata.lallai kudi yana gurin masu kudi.ga wani kamshi da sanyin a.c daya ziyarceni a lokaci guda.ban boye kauyancinaba na fara bin ko'ina na falon da kallo.sannu da zuwa matar tayiwa hajiya.jagorarmu ta farayi da'alama ita zata kaimu wajen matar gidan.wata kofa muka kara shiga,nanma wani falonne Wanda yafi na farko haduwa.gaba daya na manta da abunda ya kawoni gidan,na manta da wata fargaba.abinci kawai nake bawa idanuwana.

Matattakalar bene,naga matar ta nufa damu.nidai kawai binsu nakeyi abaya zugwi_zugwi.se tuntube nake tayi.hannuna hajiya ta kama ganin yanda nakeyi.ita a tunaninta tsoro ne ya kamani. "Kikwantar da hankalinki kinji 'yata,babu abunda zefaru dake,tunda naganki naga kin shiga raina,dabadan hajiya ta tsanantaba dani zan rikeki a wajena.saboda kin burgeni gaki da nutsuwa.babu abunda zefaru dake agidannan,kisaki jikinki kinji.gyada mata kai kawai nayi,amma zuciyata na bugawa.wani matsanancin tsorone naji ya lullubeni.addu'a nafara karantowa acikin zuciyata ta Neman taimakon Allah,da tsarinsa.

Kafin mu shiga kofar falon seda muka jira aka bude mana,wowww na furta acikin zuciyata saboda girma da tsaruwar falon,babu wani tarkace acikinsa,amma falon ya matukar haduwa fiye da wadanda muka wuce na baya.kalle kallena nakeyi bansan mun iso gaban mutanen gidanba,seda hajiya ta taboni sannan na dawo hankalina,zubewa hajiya tayi akasan carpet, din dake malale a falon.nima tsugunnawa nayi kaina a kasa,araina nace lallai gaba da gabanta.Hajiyace ta fara magana cikin girmamawa,"Hajiya barka da hutawa,dafatan kina cikin koshin lafiya,dafatan na sameku lafiya.wata murya me cike da aji da izza naji tace"lafiya kalau lami,kin cika alkawari dafatan yarinyar ta cika duka sharadan Dana lissafo miki."eh hajiya gaba daya ta cika,babu matsalar komai.maida dubanta matar gidan tayi kaina tacemun "yan mata yaya sunanki.se alokacin na dago na dubeta kai masha Allah,ta dace da gidannan gaskiya,kyakkyawace sekace India,tayi ado cikin wani rantsatstsen less,koda bansaniba amma babu shakka kunnanta da hannuwanta da wuyanta daham,saboda yanda suke daukar ido. "maryam" na furta a hankali, saboda tsareni da tayi da ido tana kallona.kawar da kaina nayi gefe,kyawawan samari guda hudu idanuwana sukayi tozali dasu,tamkar babu su a falon kowannensu yanata latsa wayarsa.kamarsu daya gaba dayansu dayane kawai ya banbanta dasu.sunkuyar da kaina nayi saboda wani mugun kallo da daya Daga cikinsu ya wurgomun. Muryar hajiyar gidan naji tana cewa"shikenan lami,zaki iya wucewa zan miki transfer zuwa anjima,sauran abubuwan kuma zamu tattauna awaya. "To hajjaju makkatu,nagode Allah ya kara girma da daukaka da arziki Mara yankewa,na barki lafiya. Da ameen kawai ta amsa mata.mikewa hajiya,danaji itama ankirata da lami tayi,tayi mata sallama.dafa kaina tayi "to maryam Nina wuce,semun sake haduwa. Kawai senaji kwalla tacikomun idanuwana,senaji banaso tatafi ta barni domin bansan taya zanfara rayuwa awannan gidanba.gyada mata kai kawai nayi,har lokacin kaina yana kasa.ina wasa da yatsun hannuna.

Bayan tafice daga falon hajiyar gidan,ta umarci wadda ta mana jagora datakaini dakin dazan zauna.tashi nayi nabi bayanta.Acikin falon ta nunamun dakin dazan zauna.abude yake hakan yasa tura kofar dakin nayi kawai na shige.katon dakine me dauke da saitin kayan gado masu tsananin kyau da daukar ido.tsayawa nayi ina karewa dakin kallo,ko ina tsaf dashi tamkar da mutum aciki."Yanzu ni zan kwana a wannan dakin nikadai,a wannan dakin zanci gaba da rayuwata,dakin da ko rabinsa a kyau bantaba tunanin shigarsaba,Jan kafata nayi na karasa bakin gadon,na zauna.katifar dake kan gadonma ita kanta ta dabance.ajiye kayana nayi.ina cigaba da karewa dakin kallo tare da sake_sake iri iri araina,da sabuwar rayuwar dazan fara.

Kiran sallar magriba ne ya tasheni daga karanta wasikar jakin danakeyi.wata kofa Dana gani acikin dakin na nufa wadda nake kyautata zaton ta bayice.ina budewa kuwa naga toilet ne.shima toilet seda nayi kauyanci araina nace sekace daki shima.wasu abubuwan dabantaba ganinsuba nagani,banyi karambanin taba komaiba,famfo kawai na kunna nayi alwala nafito.na idar da sallah,kenan ina addu'oina matar data kawoni dakin ta shigo da sallamarta.amsa mata nayi se alokacin nasamu damar gaisheta amsamun tayi fuskarta dauke da murmushi. Tace"Kizo inji hajiya tanason ganinki. " Mikewa nayi nayi bayanta muka fice daga dakin.kamar dazu yanzumma ita da yarantane,sedai yanzu naga wata mace,tana kwance akan cinyar hajiyan ita kuma tana shafa kanta,tana mata magana.agabansu naje na durkusa kaina a kasa nace "hajiya gani. Dasauri naga budurwar dake kwance akan cinyarta ta mike zaune.........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

0️⃣6️⃣

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull